Kura a Rumbu – Chapter Twenty-seven
by Maryam Farouk (Ummu Maheer)Na ɗauka da wasa Mama take yi sai washe gari da safe bayan mun yi wanka na koma rage baccin da ban yi ba cikin dare saboda Kukan Al'amin ban jima da kwanciya ba Zainab ta tashe ni akan Mama tana kira na. A falon Abba na same ta, muka sake gaisawa sai Abba ya ce
"Mamanku ta ce mijin ki yayi tafiya ko?"
Ba tare da na kalle shi ba na amsa haɗi da gyaɗa masa kai dan haka kawai kuma kunyar Abban na ke ji yanzu, ni dai jiki na bai bani aka Baba Jummai. . .