Search
You have no alerts.
    The Den of Novels
    Chapter Index

    *MASU ƁUKATAR A TALLATA MUSU HAJOJINSU ZA SU IYA TUNTUƁARMU TA LAMBOBIN 07045308523 MUN GODE*
    Ranar ina idar da sallar isha’i nayi bacci saboda ɓacin rai seda na farka da asuba sannan naga missed calls ɗin Bilal guda biyu ya kirani tun ƙarfe tara na dare. Duk yanda nake cike da haushin abinda yamun jiya amma haka nan zuciyar dake sonsa ta angiza ni nabi kiran nasa. Murya ƙasa ƙasa muka gaisa ya shaida mun yana masallaci idanya fita ze kirani. Ko yasan ina fushi dashi ne se gashi bayan ya fito masallacin ya kira mun daɗe muna hirar soyayya nan da nan kuma na ware daga fushin na manta da komai. Har Mama seda ta lura da sauyina kan yanda na kwanta jiya na tashi cikin walwala wunin ranar kuwa haka nayi shi ga farin cikin gobe juma’a zamu kammala jarabawa. Safiyar Juma’a tun ƙarfe shida na shirya cikin rigar da mukayi ta graduation. Nayi kyau matuƙa ina kallon kaina a mirror a raina ina yarda da maganar Bilal da yake yawan faɗin ni kyakykyawa ce dukda ba wai ina da irin shahararren kyau ɗin nan bane na fitar hayyaci komai nawa ya dace da zubin halittata I’m just too cute.

    Nayi mamakin tarar da Bilal a ƙofar gidanmu ba dan dama yana kaini makaranta idan yana da lokaci amma dake munyi magana na tambayeshi ko zeje mun sign out yace aa shiyasa nayi mamaki dana ganshi jingine jikin mashin ɗinsa yana ta buga mun murmushi. Ina ganin Hansa’u sun taho da Zainab Amarya data rufe fuska da niƙan yau zamuyi final exam kuma yau ne kamun bikinta gobe ɗaurin aure na ɗane Lifan ina ɗaga musu hannu muka wuce. Bilal be tafi ba seda muka fito, shi ya fara mun signing a farar rigata ta sign out muka sha hotuna sannan ya tafi muka cigaba da budurinmu har zuwa ƙarfe sha biyu kafin muka wuce gida.

    Jakata kawai na aje na ɗauki yan abubuwan da zanyi amfani dasu nayiwa Mama sallama muka wuce gidan kwalliya dan ma mun kama layi dama ƙawar mu ce me kwalliyar. Kusan mu bakwai mukaje, seda mukayi sallar azahar muka ci awara kafin aka farayi dake mutum biyu ne kafin karfe huɗu ya rage ni da Hansa’u kawai. Muna zaune saurayin Baby Isma’il ya kirata a lokacin ita akeyiwa kwalliyar dan haka ta saka wayar a speaker. Na taɓe baki jin muryar saurayin da take mana kuri dashi, daga muryarsa na hasaso garan ƙauye ne. Uzuri ta bashi akan ana mata make up ne yace
    “Zakije kwalliya amma baki gaya mun ba?” Se ta bashi amsa da “kayi haƙuri, munyi magana jiya ai na gaya maka yau kamun Zainab ko ka manta”
    “Anyi haka, yanzu a ina kuke kwalliyar na gani ko zan samu zuwa na kaiki gurin bikin?” Ya tambayeta ta gaya masa daga nan sukayi sallama bayan yace ze sako mata kuɗin kwalliyar yanzu. Suna aje wayar ko minti biyu ba’a yi ba wayarta tayi ƙara alamar shigar saƙo, Zulaiha dake ɗaukar hoto da wayar tayi ihu tana nuna tace
    “Dubu hamsin ya tura miki” nan suka riki ce da ihu tace
    “Duk kunci albarka ci zan biya muku harda amarya” dama kwalliyar tamu 2k ce ta amarya dubu biyar gaba ɗaya in akayi total kuɗin ya kama dubu goma sha uku kenan suka shiga mata godiya ban da ni da seda Hansa’u ta taɓa ni kafin nace nagode.

    Ko a jiki na, ba rainawa nayi ba ko hassada nake mata Aa kawai tunda mukayi faɗa da Hansa’u suka bi bayanta shikenan nima naja baya dasu, badan itan bama yanke alaƙa zanyi dasu dan duk wanda ya nuna baya so na da Bilal babu ni babu shi balle kuma naga suna wani fariya akan su samarinsu masu kuɗi ko da zamu taho daga makaranta saurayin Zulaihan ne ya dawo damu tana ta wani kauɗi bayan idan da naga damar kula samari saboda abin hannunsu kaf cikinsu babu wadda ta isa ta goga kafaɗa dani ko a yanzu alhamdulillah babu abinda Abbana be tsare mun ba shiyasa wani abun hannun samari baya burgeni su suka dogara dashi da har suke kula mutanen da kana gani kasan badan so bane ba. Niko Allah ya rufa mun asiri na samu me sona ina sonsa zamu mori ƙuruciyarmu tare.

    Tsaf muka gama kwalliyar mu, munyi kyau sosai aka mana hotuna kafin muka fita inda motar da ango ya turo ta ɗauki amarya ke jira. Saurayin Baby ya iso dan haka ta shiga motarsa Zulaiha ma saurayinta ne yazo ɗaukar ta se ni da Hansa’u ne muka shiga motar amarya muka tafi. Bayan an sauke mu kowacce seda saurayinta ya bata kuɗin da zatayi liƙi dashi har Hansa’u muna hanya da Alhaji Bala ya kirata seda yayo mata transfer kuɗi masu nauyi kan tayi kwalliya da liƙi haka akayi kamu aka tashi suna ta wanke amarya ni dai dana liƙa abinda na tanada dama na koma gefe na zauna seda aka tashi zamu tafi gida kafin har raina naji babu daɗi ganin still kowacce saurayinta ne ze maida gida suna ta zuzutun kwalliyar su. Kira uku nawa Bilal yace mun ze zo amma gashi har aka tashi shiru dana sake kiransa ma naji wayar a kashe. Wannan ya ɓata mun rai ban ko tsaya jira a gama watsewa ba nabi yan unguwar mu a Adaidaita muka tafi.

    A ƙofar gida na tarar da Bilal tareda abokinsa Nura, duk da naji haushin ƙin zuwan da yayi gurin bikin amma ganin dana masa se naji zuciyata tayi sanyi. Light blue ɗin shadda ya saka data dace da atamfar ankon da mukayi me ruwan dark blue da ratsin fari da light blue ɗin. Na isa inda suke Ina haɗe fuska a son na nuna masa ɓacin raina amma na kasa musamman da Nura ya fara zolayarmu wai munyi too match dama mun haɗa baki ne amma gamu nan tamkar ranar auran mu. Haka na lalace a tsaye yana tsarani har seda Abba ya dawo kafin na wuce ciki su kuma suka tafi bayan sun gaisa dashi.

    Ina tsaka da sallar magriba da isha’i da suka haɗe mun Amirah ta shiga ɗakin tana faɗin nazo inji Abba. Bayan na shafa addu’a na fita falo, Abba ma zaune yana kallon labaran ƙarfe tara. Seda aka tafi hutun rabin lokaci kafin ya juya kaina yana murmushi yace
    “Hali dubu” haka yake tsokanata. Sunan babbar yayarsa ne kuma mafi soyuwa a gare shi cikin yan uwansa. Kwanana uku a duniya ta rasu seya haɗa soyayyar ta data kasancewata yar da ya fara samu duk yake mun.
    Murmushi nayi kaina yana ƙasa na gaishe shi yana amsa yana tambayata biki kafin ya ɗora da cewa

    “Yaya Salahu ya gaya mun sunyi magana da kawun Bilal yace ze kirashi duk yanda ake ciki ɗazu yake sake ce mun kimanin sati biyu kenan har yanzu beji daga gare su ba”. Sena rasa abinda zance masa, ina ji yaci gaba da cewa
    “Ɗazun har zan tsaya nayi masa magana da kaina se kuma sai nace bari na fara jin ta bakinki ko dai saƙon be iske shi ne”. Daƙyar nace
    “Eh Abba ya gaya masa. Dama maganar albashinsa da be fara samu bace ta dakatar dashi” se Abba yace
    “Aa, har yanzu dama wannan matsalar bata kau ba? Na zata dana haɗashi da Malam Mansur yace mun an gyara komai tun last two or three months kenan da mukayi maganar.

    “Eh Abba an gyara amma salaryn ne wai se wannan watan sannan suka sa masa na wata uku” na faɗa masa iya abinda na sani, se yayi shiru kafin yace
    “Ikon Allah, to barka tunda an gyata ɗin. Yanzu ina kuka tsaya kenan a maganar?”

    “Yace zuwa ƙarshen watan nan zasu zo” na faɗa ya amsa mun da
    “Toh Allah ya nuna mana. Yaya Salahu ya damu, kin san fa babu sanda zamu haɗu ba tareda yayi mun mitar ƙin aurar dake ba. Kullum se yace ga Bishira nan da yaya biyu bayan rana ɗaya aka haife ku”
    “To ita Abba ai muna gama secondary aka mata aure bata cigaba da karatu ba” na faɗa cikin shagwaɓa yayi dariya yace
    “Haka ne amma dai da kema anyi miki ta tatan da yanzu kin fara tara mana masu samu bari bari a gidan nan ai”. Sena rufe fuska ta da hijabi ina cewa
    “Haba Abba ni yar yarinya dani ai dama ban isa aure ba har yanzu”
    “Baki isa aure ba amma kin iya dafawa gardi abinci” Mu’azzam daya shigo falon ya faɗa, na galla masa harara ina cewa
    “Abba ka mana tsakani dashi”
    “Se dai in ce ya dena tsokanarki amma babu batun na miki tsakani da ɗan uwanki” Abban ya faɗa nace
    “To ka gaya masa ya fita daga sabgata”
    “Gaskiya ce bakya so kuma se an faɗa, har gulmarki ake a unguwa da anga yara da kula za’a ce daga gidan nan ne” Mu’azzam ɗin ya sake faɗa kafin nace wani abu Abba yace
    “Arziƙi ne ai kai baka san ladan ciyarwa ba ko?”
    “Ciyar da mabuƙata ba. Kai kake bin bayanta Alhaji shiyasa kullum take sake shiga daji maimakon ta dawo hanya” Umma data fito daga ɗakinta ta faɗa sena miƙe na sulalae ɗaki na barsu inaji Abban na kareni yana faɗin ai ba laifi bane idan na bashi da babu ai ba za’a masa ba.

    Washe gari akayi ɗaurin auran Zainab a ranar kuma muka rakata gidanta mw kyau acan sabuwar gandu. Mijinta matashin ɗan kasuwa ne yayi ƙoƙari sosai a gininsa iyayenta ma sunyi namijin ƙoƙari gurin yi mata kaya da suka sake ƙawata gidan muka fito munata santi da yiwa juna shaƙiyancin wacece next. Duk su uku da ranar su ni kaɗai ce amma dukda haka a jikina inajin sena rigasu amarcewa domin dai nasu samarin a yanda suke ko yau akace a fito ayi aure kowanne yana da abin yin auren amma sun tsaya suna jan lokaci har da Hansa’u da zataje a ta huɗu.

    Kusan sati uku da suka biyo baya ina ta juya yanda zan sake ma Bilal magana ganin bamu daɗe dayi ba kuma ha uzurin daya bani se naji dama Abban ya amsa maganar da kansa kawai dan harga Allah yanzu dana gama makaranta bana komai hankalina ya fara komawa akan nima nayi aure na tafi nawa gidan. Safiyar litinin Anty Labiba ta haihu, ina bacci Mama ta tashe ni wai zamuje asibiti daga can kuma bayan an sallameta muka wuce gida Mama tace in zauna mata kwana biyu, ban so ba amma babu yanda na iya haka na tafi gida na haɗo kayan da zanyi amfani dasu na kira Bilal ya mayar dani.

    Seda nayi mata sati biyu, dake morata takeyi bata damu da zaryar da Bilal ya ringayi ba kullum se yaje anan zeci abincin dare ko kuma yazo da yamma idan ya taso daga aiki mu ɗanyi hira ya karɓi abinci ya tafi, duk zuwan da yakeyi kuma sau ɗaya ya samu ya shiga ya yiwa Anty Labiba barka dan kusan duk sanda zezo tana da baƙi yan barka dake ta kwana biyu bata haihu ba tsakanin Amir da Inayah shekara ɗaya da rabi ita kuma ta bawa Sadis shekara biyu tun nan kuma seda ta shekara bakwai yanzu ta haifi Amina takwarar Mama. Ba ƙaramar kunya naji ba sanda Bilal ya gama zamansa a falon Antyn ya tafi ba tareda ya bada ko sisin kwabo da sunan barka ba. Dama tun kafin suna dana ke masa hirar me ya kamata mu siya na takwarar da akawa Mama ya fara kawo zancen wata yazo ƙarshe har yanzu ba’a fara salary, a zato na ze bada wani abu amma se gashi ya tashi ko asi dukda uban naman suna da abincin da na jibga masa har yan gidansu seda suka ci.

    Kwananta goma sha shida da haihuwa na koma gida saboda wata ƙanwar Mijinta bazawara data zo daga zaria, sena fake da zanje na maida kaya na na ɗebo wasu daga nan na fece ba komai ya saka hakan ba kuma illah Munir dake neman takura rayuwata yana kuma haɗa ni faɗa da Bilal. Ranar talata na koma gida Bilal baya gari yaje Jos mijin ƙanwar Hajjan su ne ya rasu babban mutum ne sosai shine duk suka tafi. Ranar alhamis zasu dawo tunda suka tafi kullum mukayi waya kwana uku kacal amma ya ringa mitar yayi missing Kano yayi missing abincin Kano ze kace wanda ya tafi wata ƙasar ta daban. Ran da ze dawo tun safe na tashi da shirin yi masa girki, na yi da ɗan yawa tunda duka tare da Hajja da yayyensa mata biyu da ƙaninsa ɗaya suka tafi se matar wansa nasna kuma duka a gidan Hajjan zasu sauka kan kowa ta tafi gidansu. Ina aikin Mama namun tsiyar da sakani tayi se nayi ƙorafin abincin yayi yawa amma dake na Bilal ne na zage inayi sedai kawai nayi murmushi har na gama na shirya komai nayi wanka a Adaidaita na ɗauki Amirah muka tafi gidan bayan munyi waya ya gaya mun sun dawo.

    Ba wannan ne zuwa na na farko gidansu Bilal ba, badan ma Mama ta kafta mun warning ba da haka nan ko faɗa mukayi na kirashi a waya be amsa ba zan zari jiki in tafi, tun Hansa’u na rakani har ta dena yanzun ko nasan ko giyar wake nasha bazan cw tazo muje ba shiyasa ma naja Amirah ko Maman ce mata nayi Aliyu me Adaidaita zan bawa ya kai musu ni kuma zan wuce gidan kitso badan ba nasan ba zata bari in kai abincin da kaina ba. A kuyance muka gaisa da yan gidan nasu suna ta nan nan dani kamar su goyani ban wani jima ba nayi musu sallama muka fita se da muka fito waje kafin naga Bilal dan sanda muka je ance yana ɗakinsa yana wanka. Se naga kamar ya rame a kwana ukun da ban ganshi ba, ya jingina jikin bango yana kashe ni da kallon so yace

    “Ashe dagaske kike zaki zo”
    “Oh da ka ɗauka da wasa nakeyi? Ai na gaya maka zanzo nawa Hajja gaisuwa dama” na bashi amsa seta miƙe tsaye sosai yana cewa
    “Kin kyauta, kuma naji daɗi sosai”. Ya shafa cikinsa yace
    “Kin san ruwan tea kaɗai nasha muka kamo hanya, ina kwanukan kuma na ganki ke kaɗai?”
    “Suna cikin gida na bashi amsa” se ya wani kalleni yace
    “Cikin gida kuma? Abincin nawa kika kai mun cikin gida Halims? Maimakon ki buga mun ƙofa ki ajiye a nan kafin ki shiga?”

    Se naji abun wani iri amma na kanne nace
    “To banda abinka dama abincin ai ba kai kaɗai nayiwa ba kuma yana da yawa zasu ɗiba nasu su rage maka”
    “Ragowar wasu zanci kenan?” Ya faɗa kamar a fusace, se kuma yayi shiru na tsaida idona akansa ina karantar yanayin fuskarsa, se kuma yayi murmushi yace
    “To an gode My Halims Allah ya bada lada. Bari na shiga ciki muyi sallama da Yaya Zubaida nasan yanzu zata wuce se nazo na raka ku”. Gefe muka tsaya kusan minti biyar ya fito kamar ransa a ɓace, Adaidaita ya tare mana muka shiga ganin ya tsaya be shiga ba yasa na kalle shi nace
    “Ka fasa raka mu ne kuma?”
    “Zanzo kawai anjima, yanzu zanje gidan gidan Muslim ne naga ko zan samu abinda zanci dan yunwa nake ji sosai wlh”. Da mamaki nace
    “Wannan abincin kuma fa?” Ya ɗauke kai gefe yace
    “Sun cinye, kin san duk bamu wani tsaya munci abinci ba muka taho shiyasa dama da a gurina kika ajiye na ɗiba nawa se na kai musu sauran”.

    Harga Allah seda naji wata kunta ta kamani amma kuma yunwar da yace yanaji ita ce a gabana yanzu dan haka nace
    “Amma basu kyauta ba, to ko muje gida se na dafa maka ko indomie ce. Matar Muslim dake fama da kanta babu lallai ai tayi girki ma”. Seda yayi jimm kafin yace
    “Amma ba zaki wahala ba? Kin gama wannan girkin ki sake yin wani?”
    “Dafa maka abinda zaka ci kake kira da wahala?” Na faɗa ina langwaɓar da kaina ina kallonsa. Me Adaidaitan ya kalla kafin yace
    “Shikenan nan, kuje bari na canza kaya se na taho” ya ciro ɗari biyar daga aljihunsa ya bawa me Adaidaitan, seda ya karɓi canji kafin ya koma cikin gidan mu kuma muka wuce. Kallona kawai Mama tayi sanda nake gaya mata zan sake dafawa Bilal abinci wancan da aka kai musu ya ƙare,

    “Wato gidansu kika je? Ke wace irin yarinya ce mara jin magana anya Halima kina son ki siyawa kanki ƙima da mutunchi a idon dangin Bilal kuwa? Banda ke sakarya ce a ina kika taɓa ganin mace na zirgilli irin haka akan namiji?” Mama ta faɗa cikin ɓacin rai, nayi ƙasa da kaina kawai na kasa ce mata komai ta cigaba da bambamin faɗa kafin ta wuce ɗaki, seda ta kullo ƙofa sannan na wuce kitchen jiki na rawa na ɗora masa Indomin. Kaji biyu na saka a abincin da na musu ɗazu, dubu biyar Abba ya bani yace nayi cefane harda lemo katan ɗaya da ruwa shima katan na siya musu. Seda na duba freezer babu sauran nam se kifi, Bilal baya son kifi dan haka kawai na daga masa ita da karas da kabeji na soya masa ƙwai guda huɗu. A falon Abba na shirya komai, seda na fita tsakar gida zan wanke kayan da nayi amfani dasu dan famfon cikin kitchen ɗin ya lalace se na gashi tsugunne gaban Abba suna magana.

    Ban sam me suka tattauna ba na koma ciki bayan ya shigo seda ya cinye indomin tas yasha lemo kafin ya kalleni yana murmushi yace
    “Se yanzu na fara gane kaina”
    “Dole ai, ka sha tafiya ga yunwa kuma ai kayi ƙoƙari ma” na faɗa ina murmushi se yace
    “Yanzu Abba yake mun magana. Ai ma zata ma kin gaya masa abinda na sanar dake se yace mun wai kin ce masa ƙarshen wata za’a zo gashi watan ya mutu wani ya kama shima harya ƙare shiru me yasa zaki masa ƙarya?”

    Kallonsa nayi jin abinda ya faɗa wai nayiwa Abba ƙarya, bance masa komai ba na maida kaina ƙasa ina jan zaren mayafin jikina ina jinsa yana cewa
    “Kin kasa fahimtar abinda nake gaya miki Halima. Bawai bana son azo maganar saka ranar nan bane aa ina duba abubuwan da suke gabana daya kamata na kammala kafin ace an fara maganar aure. Yanzu idan akayi sa rana kowa ze tada hankalinsa ne da son jin yaushe za’ayi biki, da zarar an ɗan samu akasi an ɗaga daga sanda aka faɗa se kiji maganganu su kansu iyaye zakiga sun ɗauka kamar mutum ya shigo da shiririta cikin abun. Ni yanzu babban abinda yafi tsayamun shine na kammala gini na kin san kuma dai gini abu ne me buƙatar tana di da lokaci dan ko da kuɗin a zube kin san aikin gaggawa baya ƙarko”

    “Haka ne” na faɗa ina kallonsa ƙwaƙwalwata na son bawa maganganun sa ajin daya dace dasu. Yaci gaba da cewa
    “Kin san ina da taste, akwai plan ɗin dana tsarowa gini na da idan yanzu nace na katse ko na canza da wani abu daban baze bada yanda ake so ba. Kinga ginin nan shi kaɗai ne nake so ace na kammala duk wata sauran hidima za’ayi abinda ya samu ne na sani lefe ma zaki iya yafe mun ko My Halims tunda dama ke ai kullum cikin sababbin sutura kike ko waɗannan na jikinki ma ai ban taɓa ganinki dasu ba” ya ƙarasa yana wata dariyar data ƙular dani, kafin nace wani abu ya tareni yana cewa
    “Wannan bayanin nake so kiyiwa Abba nasan zw fahimce ni tunda ina da hujja me ƙarfi ko shi Baba Salahun idan aka fahimtar dashi ze gane”.

    “To amma Bilal me ze hana ka kama haya mana ko da na shekara ɗaya ne pending ka ƙarasa ginin naka? Na faɗa bayan dana gama jin nasa uzurin, seya wani kalleni kamar wadda na faɗa masa mugun abu yace
    “Haya? In kama haya fa kike cewa Halims? Yanzu ke ba zakiji kunya ace gidan haya aka kaiki ba?”
    “Wace irin kunya kuma Bilal mutane nawa suke rayuwa a gidan haya? Ita kanta hayar ai se wanda ya isa ne ma yake da hali ze kama naga wasu sedai su nemi a basu aro” na bashi amsa ina ɓata fuska seya girgiza kai yace
    “No Halims wace irin haya ana zaune ƙalau se kace matsiyaci. Mu gama zagin abokananmu saboda rashin zuciya sun kasa mallakar gidan kansu se kuma kawai nima na ƙare a haya bayan Allah ya rufa mun asiri ina da yanda zanyi”

    “Oh ashe ma kana da yanda zakayin niyya ce kawai bakayi ba ko kuma nace auren nawa baka shiryawa ba. Da kuma zaka ce tsiya ce take sakawa ayi haya har kana zaginsu wasu da hakan shi muhalli tamkar rabon haihuwa da silar mutuwa Allah ke saukar dasu don yanda kaso da faruwar su ko kauce musu baka da wayo baka da dabara akai kuma idan Allah yaso ya nuna maka iyakarka seya jarabce ka kaima duk arziƙin ka ya hanaka mallakar gidan kan naka. Mutane nawa keda rufin asiri amma har suka mutu suka ƙare rayuwar su a gidan haya? Ka fito fili kawai ka faɗa mun abinda yake ranka game dani domin na fara gajiya da uzurin ka da basa ƙarewa kullum da wanda zaka zo dashi to kawai ka faɗa mun matsayar maganar mun, idan yi yi idan bari bari kawai nagaji da sa banga ƙaho ba Bilal” na faɗa ina miƙewa tsaye.

    Note
    error: Content is protected !!