Kura a Rumbu β Chapter Thirty-two
by Maryam Farouk (Ummu Maheer)*Barkanmu da Sallah yan uwa* ππ½
Sai da na fita kofar asibitin kafin na tsaya ina raba ido, ina zan nufa ne ma? Gida zan tafi ko kuwa gari zan shiga cigiyar inda Bilal ya tafi? Na kai hannu na share laimar da naji akan fuskata wadda ban tantance hawaye bane ko zufa kafin na shiga tare abin hawa, gidanmu na wuce, ban ko karΙi canji ba bayan na sauka na shige gidan a bakin Ζofa na zauna kamar wata zararriya na fasa kukan da ya saka Mama ta fito daga falo kamar zata hantsila da Sharifa a hannunta ta. . .