Kura a Rumbu – Chapter Thirty-seven
by Maryam Farouk (Ummu Maheer)HALIMA
Sati na biyu a Asibiti kafin aka sallameni zuwa lokacin kuma Alhamdulillah na samu sauƙi sosai ko in ce nayi matuƙar ƙoƙarin gurin yakice damuwar dake raina ko dan in samu na bar gadon Asibitin domin a zahiri basu da maganin matsalata kamar yanda kullum Dr yake nanata mun ni zan yiwa kaina maganin matsalata in cire koma menene na saka a raina yake neman halakani. Zama yayi ya mun karatun Yaya da ƙanwa kamar yanda ya ce,
"Ki dubi yanda hankalin iyayenki da yan uwanki duk ya tashi saboda ke, ki kalli yayanki da har. . .