Kura a Rumbu – Chapter Thirty-nine
by Maryam Farouk (Ummu Maheer)Ko da ya koma gida daƙyar tunanin yanda Hajja zata karɓi zancen auren daya ɗaura ba tareda saninta ba ya danne waswasin da zuciyarsa ta dasa masa akan Zulaiha. Wayarsa ma kashewa ya sakeyi bayan daya shiga gida bai kuma kunnata ba sai washe gari gurin ƙarfe goma bayan daya shirya zuwa gidan Hajjan in da daga can kuma yake so ya biya gurin Halima. A tsakar gida ya tarar da Hajja tareda Fadila suna duba kayan da kallo ɗaya ya musu ya fahimci daga gurin Jalilah suka fito dan yanzu ta lalata Hajjan da suturu masu tsada. . .