Kura a Rumbu – Chapter Thirty-five
by Maryam Farouk (Ummu Maheer)Amirah ta ɗaga Sharifa data saka kuka daidai lokacin da Mama ta fito daga kitchen lokacin kuma Al'amin shima ya shigo Suraj na biye dashi da akwatin mu.
"Ku kuma daga ina haka da sassafe?" Mama ta tambaya, Suraj ya ajiye kayan yana cewa
"Tareda Babansu suke" ya juya ya fita sai Amirah tace
"Yaya Haliman tana ciki itama". Tsaye Mama tayi kafin tace
"Toh lafiya dai?"
"Gaskiya ba lafiya ba kinga fa jefar da Sharifa tayi ta wuce ina mata magana ko saurarona ma batayi ba" Amirah ta amsa mata. Jumm tayi tana kallon Al'amin daya haye. . .