Search
You have no alerts.
    The Den of Novels
    Chapter Index

    Ɗaki na koma dan bazan iya karyawa ni kaɗai ba na fara sabawa tun da mukayi aure da Bilal bamu taɓa raba kwano ba, yanzu bama na jin cin abincin raina duk babu daɗi. Tun ina sauraron jin ya buɗe ƙofa ya fito har bacci ya kwashe ni a kishingiɗen da nake. Ban farka ba se da naji ana ƙwala kiran sallar azahar, nasha mamakin irin baccin da nayi. Se da sake watsa ruwa saboda jiki na da naji duk ya ɗaure sannan nayi alwala na fito ina jina fayau ciki na a rarake. Sallar na farayi sannan na gyara fuskata na saka kaya dukda yanda nake jin yunwa dan Anty Labiba ta hora ni da kasancewa tsaf tsaf ko da yaushe. Daga yanayin falon na gane ya fito yayi abinda ze yi. Dana duba kan dining kwano kaɗai na tarar an cinye doya dana soya tas ga kuma cups biyu da aka sha tea, kwashe kwanukan na farayi na kai kitchen sannan na dafa indomie naci ina mamakin me yayi zafi haka ne da Bilal yake wannan abun?

    Ranar haka na wuni ni kaɗai a gida, se da yamma ne ma maƙwafta na mutum huɗu suka shigo mun, biyu gidan su ɗaya matar wa da ƙani ne Hafsa Maman Salim da Amina ita amarya ce tsiran mu sati biyu kamar yanda suka ce gidansu shine a farkon layi se Zubaida Maman Yusuf da gidan ta ke kallon nawa da kuma Bintu ita ce muke katanga ɗaya. Har gab da kiran magriba muna ta hira kafin suka yi mun sallama suka tafi na rakasu na dawo na gyara gurin da muka ɓata. Zuwan su ya rage mun kewa ya kuma ɗauke mun hakankali daga damuwar in da Bilal ya tafi yini guda na kuma kira wayar sa sedai tayi ta ƙara baze amsa ba daga ƙarshe ma ya kashe ta gaba ɗaya.

    Har nayi sallar isha’i babu shi babu dalilin sa, zuwa sannan hankali na ya tashi na fara tunanin ba lafiya ba. Ƙarfe tara na kira Mama ina kuka na gaya mata tun safe Bilal ya fita ina ta kiran sa kuma baya amsawa daga ƙarshe ma wayar a kashe take.

    “To ban da shirme kuma kukan na menene? Ai lafiya ce take ɓuya. Ki kira Nasir ko wani cikin abokanan sa na gurin aiki kiji ko suna tare tun da hankalin ki be kwanta ba. Amma babu komai ma nasan tun da kina gida ma ai yana haka ku wuni ba kuyi magana ba se daga baya ya baki uzuri” abin da Mama ta faɗa kenan amma hakan be sa naji hankali na ya kwanta ba tun da ni dai tun da mukayi aure ko ƙofar gida ze fita se ya gaya mun. Layin ƙanin sa Abubakar na kira se dai shima na tarar a kashe wannan ya sake dugunzuma hankali na kawai na zauna na fashe da kuka na rashin madafa. Motsin buɗe ƙofa ya farkar dani firgigit daga baccin daya sure ni ba tare da na sani ba ina tsaka da kuka. Dishi dishi nake kallon sa ya tsaya shima yana kallo na kafin ya fara takowa cikin falon se na miƙe da sauri na nufe shi, tsayawa yayi na faɗa jikin sa tare da fashe wa da kuka ina cewa

    “Ina ka tafi? Hankali na ya tashi ina ta kiran wayarka baka amsawa me yasa kayi mun haka?”

    A dake cikin yanayin da banyi zato ba bayan ya janye ni daga jikin sa ya kalle ni yace
    “Kin aike ni ne balle ki bi ba’asin in da na tsaya?”
    Se na bishi da ido kawai na kasa cewa komai, ya yi tsaki tare da zagaye ni ya wuce ciki.

    Kamar wata wawiya haka na rakashi da ido har ya shige cikin ɗaki tare da banko ƙofa. Tamkar wacce ƙwai ya fashewa a ciki haka naja ƙafafu na da suka yi sanyi na zauna kan kujera haɗi da zabga tagumi. So nake na tunano ta in da na kuskurewa Bilal, me nayi masa da yayi zafi haka? Ina nan zaune ya sake fitowa fuu ya shige kitchen ina jiyo shi yana birkita kwanuka kafin ya sake fitowa da kofin shayi a hannun sa se dublan a plate. Nan cikin falon ya zauna bayan daya kunna Tv ya shiga shan shayin sa, yanda yayi tamkar be san da wanzuwata a gurin ba yasa na fashe da kuka sosai har da shashsheƙa se gani nayi ya miƙe tsaye da kofin shayin sa da alama gurin ze bar mun. Bazan iya jurewa ba, ina buƙatar nasan takamaiman dalilin fushin da yake yi dani se na miƙe da sauri na isa gaban sa na durƙusa tare da riƙe ƙafar sa ina ci gaba da kukan nace

    “Ka faɗa mun me nayi maka kake mun irin wannan horon Bilal?”
    “Baki ma san me kika mun ba kenan?” Ya faɗa yana ɗage kai sama a ƙoƙarin hana tausayi na yin tasiri a zuciyar sa. Girgiza kai nayi ina ci gaba da kukan nace
    “Wlh ban sani ba, ka taimaka ka gaya mun me na maka bazan iya cigaba da jure fushin ka irin haka ba”
    “Shikenan tun da baki san me kika mun ba Halima, duk ranar da kika tuna se muyi maganar” ya faɗa yana janye ƙafar sa ya wuce cikin ɗaki se dai be kulle ƙofar ba a buɗe ya barta. Zuciya ta na raya mun na rabu dashi da kansa ze zo in da nake idan ya gama fushin amma zuciyar dake cike da so da begensa ta rinjaye ni haka na sake bin sa ɗaki ina kuka ina roƙon ya gaya mun abin da na masa amma se da mula dan kansa kafin ya maido mun da zancen kilishi”

    “Kayi haƙuri, ban kawo hakan ze ɓata maka rai ba amma zan kiyaye haka ba zata sake faruwa ba a gaba” na faɗa ina goge hawaye. Duk da haka be wani sake mun koma yanda muke gaba ɗaya ba se da aka kwana biyu ranar laraba ya fita da yamma babu jimawa Mu’azzam ya zo ya kawo mun manya manyan kaji guda goma in ji Abba da ƙwai shima crate goma dake ya buɗe gidab gona ana kiwon kaji da kifi yanzun an fitar da layers ne da suka dena ƙwai shine aka kawo mun rabo na. Tuwo nayi niyyar yi ganin kajin yasa na fasa na haɗa lafiyayyen farfe su irin wanda Bilal ke so na kwaɓa fulawa na gasa bread dan na lura yanzu abin laifi baya yiwa Bilal yawa tsaf idan na kira shi nace ya taho mana da bred ɗin se ya maida abin na rigima.

    Se da akayi sallar isha’i kafin suka shigo gidan shi da Abubakar da Halifa ɗan Babbar yayarsu Anty Na’ima. Can falon sa ya buɗe musu suka shiga na kai musu ruwa da lemo ganin ya fito da laptop ɗin sa yasa na fahimci wani abun zasu yi ba yanzu zasu tafi ba dan haka na ɗora musu jallof ɗin taliya na saka musu kazar a ciki, na sauke kenan na jiyo maganar su a tsakar gida alamun sun fito zasu wuce hakan yasa na leƙa da sauri na sanar musu ga abinci na sauke ina kuma zasu tafi?

    “Da kin barshi Anty sauri mukeyi” Abubakar ɗin ya faɗa, zanyi magana Bilal ya rigani yace
    “Ku wuce kawai kasan na cewa Nasir ya jira ka kai masa flash ɗin nan kar ku ɓata masa lokaci”
    “Haba dai duk saurin da sukeyi ai sa jira dai su ci abincin, idan kuma ba zaku ci anan ba bari in juye muku to se ku tafi dashi kawai” na tare shi. Naga irin kallon daya mun amma ban kawo komai ba na koma kitchen, falon suka shigo suma suka zauna Bilal ya bini kitchen, yana tsaye a kaina na juye musu taliyar gaba ɗaya a kula tun da dama su na dafawa na saka a kwando na haɗa musu da ruwan gora da lemo yana nan tsaye a kitchen ɗin na fita na basu mukayi sallama suka tafi. Bana zaton sun kulle mana ƙofa Bilal ya hau ni da faɗa tamkar ze doke ni, akan me yace su tafi zan ce su tsaya in zuba musu abinci?

    Mamaki ya sa na kasa ce masa komai, waccen ranar yayi faɗa dan na yiwa yar uwata kyauta yau kuma yana yi saboda nayiwa nasa dangin menene matsalar Bilal ne? Ban san ya akayi ba kuma ya rage banbamin da yakeyi yana cewa
    “Bana so, karki sake mun irin haka a gaban yara salon suce ban isa da ke ba kin raina ni in ba haka ba ya za ayi na baki umarni ki take kiyi wanda ranki ya raya miki? Yanzu da kika juye musu abincin duka ni wanne zanci”
    “Allah ya baka haƙuri” na faɗa a sanyaye kafin na shige kitchen na barshi. Na zata ze shige ɗaki ya kulle irin na waccen ranar se kuma na tarar dashi a zaune yana kallo, se da na gama jera abubuwan da zamuyi amfani dasu akan dining kafin nayi masa magana ya taso. Sosai yaci naman nayi mamakin da ban ji ya tambaye ni daga in da aka samo su ba tun da yasan bamu da sauran naman kaza a gidan se wanda yake cikin miya. Kafin mu kwanta se da ya sake ci ya kuma jaddada mun in aje masa sauran a fridge karya nema gobe nace masa na bawa wani.

    A haka muka cinye satin, zaman mu ya koma kamar da har ma ya zarce da daɗi da farin ciki. Cikin abin da yasa nake ƙara son Bilal mutum ne shi da baya son jikin sa, ina kwance zeyi shara yayi mopping wani lokacin har girki yake ɗora mun, ranar daya ga ina haɗe kayana da sukayi datti kafin na samu wanda ze yi mun wanki kamar wasa yace na fita dasu tsakar gida, na yi tunanin almajiri ze nemo na fitar na ci gaba da gyaran ɗaki na se kawai ganin sa nayi ta window yana shanya kayan ashe da kansa ya wanke mun. Wannan yasa na ke ƙara son sa saboda ya bani mamakin na same shi yanda ma banyi zato ba. Abu ɗaya yake bani tsoro da halayyar sa yanda yake birkicewa lokaci ɗaya akan ɗan ƙaramin abu da be taka kara ya karya ba, wani lokacin ya sakko da wuri wani lokacin ko se naji na tsani kaina na tsani dalilin daya sa na zaɓi rayuwa dashi kafin ya sakko idan komai ya wuce kuma se ya zama kamar wani saɓani be taɓa shiga tsakanin mu ba.

    A haka muka ci sati huɗu da aure se lokacin kuma hutun daya ɗauka ya ƙare ya koma bakin aiki, da safe idan ze fita har kuka nake yi saboda sabon da nayi na kasancewa tare dashi a ko da yaushe bana taɓa samun nutsuwa se naga ƙarfe huɗu tayi lokacin shigowar sa gida yayi. Bahaushe yace yau da gobe bata bar komai ba, a hankali cefanen mu ya fara ja baya. Ɗan yun kayan miya ne suka fara ƙarewa ya rage albasa kawai nake da, da yake ina da dafaffu a freezer markaɗe da jajjage se banyi azancin sanar dashi ba. Ranar wata asabar yana gida, da rana yace na dafa mana shinkafa da wake jollof nayi amfani da bushashshen kifi. A plate ɗaya na zuba mana, har mun fara ci yace na ɗakko masa yaji wai abincin yayi masa salam da yawa dake da manja nayi. Dukda ya saka yajin ya ce beyi masa yanda yake so a bakin sa ba dan haka ya tashi ya tafi kitchen da kansa, se da ya ƙwala mun kira naje yake tambaya ta ya yaga babu kayan miya?

    “Sun ƙare ai, saboda ina da markaɗe a ajiye shiyasa ma ban gaya maka” na bashi amsa. Bece mun komai ba muka koma muka ƙarasa cin abincin kafin ya shirya yace mun ze ɗan fita amma ba jimawa zeyi ba.
    “Dan Allah na shirya mu tafi tare” na shiga yi masa magiya amma kamar kullum ya ce Aa. Tun waccen ranar da muka je gidan su da namu ko ƙofar gida ban sake fita ba ba kalar magiya da nacin da ban masa ba amma yaƙi. Kafin muyi aure idan aka ce mun Bilal Bilal zeyi kulle zan ƙaryata se gashi a take takensa na ga hakan. Da nayi masa ƙorafin duk sauran yan uwana da akayi mana aure tare sun je sun gaida iyayen mu ce mun yayi al’ada ce ba addini ba ni ba zani ba, abin da yasa na haƙura da na yiwa Mama mita tace na haƙura ai dama yayi wuri wata ɗaya ace na fara yawo. Ni yanzu gidan Anty Labiba na damu da naje, tun ranar da aka kawo gara bata dawo ba, a waya ma sau biyu ta kira ni akan wani saƙo da tace za’a kawo mun se bayan an kawo ɗin ta sake kira tayi mun bayanin yanda zanyi dashi. Ko a chat idan ba ni nayi mata magana ba bata kulani, nasan fushi takeyi dani shi yasa kuma nake so naje gida na bata haƙuri mu sasanta dan bazan iya jure fushin nata ba.

    Ba yanda na iya tun da yace Aa haka na koma ciki na zauna rai na duk babu daɗi se dai kamar yanda yace be jima ba ya dawo da cefane harda irish potatoe da doya tun da yaga su ma saura kaɗan. Se da na aje komai in da ya dace kafin na koma gurin sa. Washe gari kamar kullum da wuri na gama haɗa abin karyawa na soya dankali da ƙwai se ruwan tea, har na gama komai Bilal na ɗaki be fito ba, ganinya kusa makara yasa na haɗa masa shayi dan ya huce kafin yazo sha na wuce ɗaki gurin sa. Seda na taimaka masa ya ƙarasa shiryawa kafin muka fito tare ina masa daru akan yayi kyau da yawa ina tsoron kar yammata su yi ta kallar mun shi a waje. Fusarsa washe da fara’a da alamu yana jin daɗin yanda nake kambama shi a ko da yaushe ina zuzuta kwalliyar sa. Se da na ja masa kujera ya zauna kafin 1na buɗe bowl ɗin dana zuba dankalin na janyo plate zan zuba masa,
    “Meye wannan Halima?” Ya faɗa da ƙarfi har se da na razana. Jiki na ya ɗauki rawa na saki fork ɗin hannuna tare da dafe ƙirji na dake harbawa ina ambaton innalillahi wa’inna ilahi raji’un a fili tare da baza ido ko zan ga abin da ya saka shi wannan razanar haka amma iya hange na banga komai akan dining ɗin ko kewayen in da muke ba.

    “Banga komai ba Bilal” na faɗa cikin rawar murya dan dagaske na tsorata. Cikin ɓacin ran daya nuna har kan fuskar sa ya nuna bowl ɗin dankalin yana cewa
    “Wannan uban dankalin da kika soya waye ze cinye shi? Almubazzaranci zaki fara ko Halima saboda baki san zafin kuɗi ba baki san yanda ake neman su ba? Yanzu cikin mu mu biyu ne zaki soya wannan abun? Ko da yake baki da asara shi yasa, se ki zauna kici” daga haka ya miƙe ya saɓa jakarsa ya nufi ƙofa yana ci gaba da banbami. Ƙarar da ƙofa tayi bayan daya bugota ya dawo dani daga suman wucin gadin da mamakin Bilal ya sakani yi. Na sauke ajiyar zuciya me ƙarfi tare da jan kujera na zauna saboda ji nayi ƙafafu na sun yi sanyi kamar ba zasu iya cigaba da ɗauka ta ba. Se na rasa ma tunanin me zanyi, akan dankali dai Bilal yake kirana almubazza?

    Buhu ɗayan da muka cinye a sati biyar be saka ya danganta ni da almubazzaranci ba se yanzu saboda na soya daga cikin kwano ɗayan daya siyo da kuɗin sa? Dankalin da yake cewa baya gajiya da cin sa, se muci da safe mu ci da rana da dare ma mu ci, Allah ke da kullum duk safiya har idan ya rigani shiga kitchen dankali ze feraye ko nayi marmarin doya idan ba shi yaga dama yaci ba se yace sedai kowa yaci abin da yake so amma shine yake mun tijara akan sa yau?

    Ina nan zaune kusan awa guda gaba ɗaya kaina ya kulle har na rasa kalar tunanin da zanyi. Bugun get da kuma wayata da ta ɗauki ƙara yasa na tattara hankali na guri ɗaya ganin Hansa’u ke kiran yasa na miƙe dan nasan itan ce take buga ƙofa tun da mun yi magana tun jiya ta gaya mun yau zata zo ta kawo mun atamfa da kace ɗin ankon bikin ta da aka saka nan da sati shida. Fara’ar dole na ƙirƙira na ɗorawa fuskata bayan na buɗe musu ƙofa suka shigo tana mun mitar sun daɗe suna bugu kuma dan wulaƙanci tana kira ban amsa ba. Bana yanayin da zan ja magana se kawai nayi murmushi muka shiga falo. Ƙanwar ta Abida ce ta wuce kan dining kai tsaye tana cewa

    “Ni wlh yunwa nakeji Anty Halima ban karya ba ta taso ni me kuka rage?” Bata ma jira na bata amsa ba ta dirar wa dankalin Bilal, Hansa’u zata hau ta da faɗa na hanata, ina lura da yanda take kallo na nasan baze wuce ta karanci damuwa tattare dani bane tun da kuma ban ce mata ba itama ba tayi karambanin tambayata komai ba, basu jima ba suka wuce bayan ta bar mun atamfa ɗaya da lace ɗin na zata ma wuni zatayi tace mun Aa yau take so duk wanda zata kaima ankon gida ta gama dasu. Abida bata daddara ba ta sake ɗaukko kwalin exotic a fridge tasha ta tafi da sauran, yana cikin lemon da Bilal yafi so kuma shi kaɗai ya rage kwali ɗayan ina kallon ta amma bazan iya cewa ta ajiye ba domin rowa ba hali na bace ba kuma zan koyeta a gidan aure ba sannan Abida na ɗauke ta ne kamar Amirah ƙanwa ta babu yanda za ayi na hanata wani abu da nake dashi.

    Saboda yanda muka rabu da Bilal yasa na cire komai daga raina na yi masa girkin daya fi so kafin ya dawo na sake gyara gida na baza turare nima nayi wanka na cancaɗa kwalliya na kame a falo ina jiransa. Rai a haɗe sallama a ciki ya shigo falon, nayi kamar ban lura da yanayin sa ba na nufe shi ina masa sannu da zuwa. Be tare ni yanda muka saba ba be kuma gwasale ni yanda nayi zato ba se ya miƙo mun jakar hannun sa na karɓa ina murmushi tare da yi masa sannu da zuwa, yanda ya amsa ya sosa mun rai har naji idanuna suna neman su kawo ruwa amma na dake. Kitchen ya wuce na bishi da kallo kafin na wuce ɗaki na aje masa jakar sannan na shiga banɗaki na tara masa ruwan wanka. Ina ciro masa kayan da ze saka ya shigo ɗakin, kamar daga sama naji yace
    “Kuma kika cinye dankalin duka”. Na saci kallon sa shi ɗin ma ni yake kallo se nayi gefe da kai na nace
    “Idan an barshi ai lalacewa zeyi”. Ƙwafa naji yayi kafin ya shige banɗakin kamar ze tashi sama, ni se ma ya bani dariya. Abincin ma sama sama yaci ya ture ya shige kitchen, kamar ɗazu da safe ya sake kwazara mun kira saura ƙiris na ƙware da abincin baki na na maida shi cikin plate ɗin na tashi da sauri.

    “Dan girman Allah Bilal ka dena mu irin wannan kiran bana so” na faɗa tamkar zan fashe masa da kuka ganin sa a tsaye jikin fridge, ya kalle ni kafin ya buɗe fridge ɗin yana nuna ciki yace
    “Ina exotic ɗina?”
    “Nayi baƙi sun shanye” na bashi amsa kai tsaye. Yanda ya yi mici mici da ido yana kallona se ka rantse iyayen sa na zaga.
    “Shi lemon nawa kike gaya mun kin yi baƙi sun shanye?” Ya faɗa yana nuna kansa, Allah ya sani na fara zuwa bango. Wane irin abu ne daga dankali se kuma lemo se kace ana fatara ko tsiya?
    “Baƙi nayi suka zo da yara ni ban ma sani ba muna falo suka shigo suka ɗauka kaga kuma babu yanda za ayi nace su mayar tun da dai abin nan munfi ƙarfin sa ba fatara akeyi ba” na bashi amsa ba tare dana kalle shi ba. Seda ya kwashi sakanni yana kallo na kafin yace
    “Yayi kyau” ya fice daga kitchen ɗin ya barni a tsaye.

    Note
    error: Content is protected !!