Search
You have no alerts.
    The Den of Novels
    Chapter Index

    Na fi minti goma tsaye a ƙofar gidan mu ni ban shiga ba kuma ban bar gurin ba. Maganganun da mu kayi da Bilal ne suke mun amsa kuwwa a kunnuwa na da ƙwaƙwalwata bana kin ko wanne sauti dake zagaye dani banda muryar sa.
    “Ba ni da kuɗin da zan ƙarasa gini Halima, ba kuma ni da sararin da zan kama haya a yanzu. Abu biyu ya rage, ko dai iyayen ki su ɗaga auren mu ko kuma mu haƙura gaba ɗaya, ƙila a gaba idan muna da rabon kasancewa tare se muyi aure. Ina son ki Halima amma bani da halin mallakar ki a yanzu” kalaman ƙarshe daya gaya mun kenan. Bana ko gani sosai na shiga bubbuga ƙofa, se da na buga sau uku kafin aka buɗe. Musa ne, jikan Goggo Habi Ƙanwar Mahaifin Mamanmu. Ɗan ta ɗaya Baba Sulaiman kuma shine mahaifin Musan accident suka yi dashi da matar sa duk suka rasu. A Birnin gwari take da zama dama naji Anty Labiba tana faɗar tace tun biki na saura sati biyu zata zo ashe har ta zo ɗin kuwa.

    Kallo na ya tsaya yi saboda niƙab ɗin dake fuska na raɓe shi na wuce ina haɗa hanya, motar Abba da na gani a ajiye yasa na gane yana gida dan haka kai tsaye na wuce falon sa. Tare da Aminin sa Baba Hashim na same su suna magana daga kuma yana yin fuskokin su na fahimci ko ma me suke tattauna ba magana me daɗi bace. A tare suka amsa sallama ta suna kallo na, ka ƙarasa gaban Abba, tamkar wadda tazo isar da saƙon rasuwa haka na fashe da kuka irin me gigitar nan har jiki na yana jijjiga. Abba ya miƙe hankali tashe ya ruƙo ni yana cewa
    “Lafiya Halima? Me ya samu su Labibar?” Haka Baba Hashimu ma cikin kaɗuwa suka ringa tambaya ta me nene amma na ƙi cewa komai har se da nayi kuka iya kar yi na se da naga Baba Hashimu ya nufi ƙofa yana cewa
    “Bari na kira Amina” se lokacin na buɗe baki daƙyar nace
    “Ba se ka kira ta ba”. Se da na sake kwashe kusan minti biyar ina kokawa da kukan dake taho mun da zarar na buɗe baki kafin daƙyar na iya cewa
    “Abba Bilal ne”
    “Me ya same shi?” Abban ya tambaye ni. Ina kuka tamkar raina ze fita na tsara musu duk yanda mukayi da Bilal da abin da ya gaya mun ban rage komai ba. Su kayi shiru kamar ruwa ya cinye su banda sautin kuka na da ƙarar fanka baka jin komai har kusan minti goma da alama duk su biyun bakin su ya mutu sun rasa abin da zasu faɗa ne. Daƙyar Baba Hashimu ya katse shirun yace mun
    “Ki bar kukan haka Halima kiyi shiru muyi magana”. Se da na sake shafe wasu mintunan kafin na iya tsagaitawa da kukan, yace

    “Zaman nan da muka yi zancen ki muke yi Halima. Mahaifinki ya kira ni yana cike da damuwa akan lamarin auran ki. Yau saura kwana goma sha huɗu amma babu wata magana me ƙarfi daga gidan maza su basu zo akan suna sane da lokaci ba kuma basu ce wani abu dangane da shirun da suka yi ba. Yanzu Alhaji Salahu muke ji yazo mu ji ta bakin sa akan abin da ya kama muyi se kuma gashi kin zo da wannan maganar. Ina ganin ai ba abin kuka da tayar da hankali bane ba, dama kullum cikin yi muku addu’a muke akan Allah ya zaɓa muku mazaje na gari. Irin haka babu daɗi, amma sha’anin aure da ace ayi azo ana dana sani daga baya gara a haƙura se kiga ubangiji ya musanya miki da wanda ya fishi zama alkhairi a gare ki”.

    Kukan dana sake fashewa dashi se ka rantse da Allah irin marin nan na shammata ya zabga mun, ko da yake ai gara ya dake ni naji zafin a kan fata ta da ciwon da yake neman haifar wa zuciya ta. Na rabu da Bilal fa yake cewa. Daga shi har Abban Kallo na suka ringa yi cikin mamaki za a ko ace ɗimuwa tamkar dai basu fahimci dalilin sabon kukan dana dasa ba. Ban ji nauyin Baba Hashim ba domin dama Abba babu batun jin kunya tsakani na dashi nace
    “Wallahi ina son sa Abba, idan na rasa Bilal ban san ya zanyi da rayuwa ta ba ni dai a nemi wata mafitar amma kar ma a fara cewa in rabu dashi” na haɗe kai na da kujera na ci gaba da rera kuka. Baba Hashim ya ringa salati yana tafa hannu Abba dai yayi shiru ya tallafe haɓar sa da hannu biyu yana kallo na. A haka Baba Salahu ya shigo ya same mu, a taƙaice Baba Hashim ya yi masa bayanin abin da nazo musu dashi yayi shiru kawai yana jimanta abun a ransa yana kallo na, jin kukan nawa bana ƙare bane yasa ya fara magana cikin lallashi yana cewa

    “Yi shiru Halimatu kwantar da hankalin ki babu wanda ze raba ku amma ki fara amsa mun tambayar nan tsakani da Allah kar ki mun ƙarya ni kuma zan yi iya ƙoƙari na ganin na samar miki muradin ki”. Na tsagaita kukan ina share hawaye haɗi da face maji na da hijabi na, shiry ya ɗan yi cikin jin nauyin maganar da take bakin sa kafin daƙyar ya iya cewa
    “Halimatu, kar kiji nauyi ko kunyar mu ki gaya mun tsakanin ki da Allah wani abu na rashin dacewa ya taɓa shiga tsakanin ki da Bilal ne?”

    Da sauri Abba ya kalle shi se Baba Hashim ya masa alama da ido akan kar yace komai ni kuwa a yanayin da nake ciki ban ma ji tambayar tasa a wani daban ba kai tsaye na ce masa
    “Wallahi Baba Bilal ba ɗan iska bane ni yake so tsakani da Allah ba wai wani abu nawa ba. Ni ko hannu be taɓa riƙewa da gangan ba aure na yake so kawai ba wani abu ba”.

    “Alhamdulillah” suka haɗa baki su ukun suka faɗa Abba har seda ya gyara zama ya koma cikin kujera ya kwanta haɗi da rufe idanun sa. Nasiha Baba Hashim da Baba Salahu suka shiga yi mun se dai jin su kawai nakeyi badan ina ɗauka ba, sanyin da naji da duk su biyun suke jaddada na kwantar da hankali na babu abin da ze faru zasu kira Bilal suyi magana dashi. Dana fito daga falon nasan in na shiga gurin Mama ƙarshe raina ne ze sake ɓaci se kawai na maida niƙab ɗina na fice na tafi gidan su Hansa’u.

    Hajiya Amina na zaune ta zabga tagumi tana sauraron Goggo Habi dake zuba tijara, tun yammacin jiya data sauka gidan ta ce a fito mata da kayan lefe ta gani aka ce babu shi kenan ta dasa tijara in tayi ta gaji ta huta an jima ta ci gaba, yanzu ma zuwan Inna Salamatu Yayar su Alhaji Aminu ta biyu yasa aka sake maido da zancen sabo.
    “Ni tun da uwata ta haife ni ban taɓa jin labari ko ganin neman aure irin wannan ba, ni fa tun ga ni na da yaron sau ɗaya ban ga miji a nan ba yana yawo da wata shegiyar suma kamar zakaran da yake tashen balaga na ɗauka shiritar yarinta tasa ta biye masa da zarar ta samu nutsatstse me hankali zata rabu dashi ashe abu dai bana ƙare bane. Ban da ma sakaci irin naku na iyayen yanzu ke Amina kina ina har kika bari har tayi sabo da wannan lalata mogal ɗin?

    Irin waɗannan samarin dama kowa yasan basu aje ba basu bawa kowa ajiya ba se dai suyi wanka su ringa yawo kwararo kwararo duk in da suka ga yarinya me ɗan gwaɓi gwaɓi su shiga jikin ta su hanata kula mazan arziƙi daga ƙarshe su gudu su barta, in kuma Allah ya ƙaddara an yi aure ayi ta tsallen tsiya ana jeka ka dawo akan me?

    Tun da suka ce zasu zo neman auren me yasa baku dakatar dasu ba ku ce kun wa yar ku miji se yanzu zaki zauna kina tagumi da maganganun banza da ba zasu miki amfani ba to wlh tun wuri ki tashi tsaye ki ƙwato yar ki tun ba a kai ki an baro ba, ke Salamatu da zaki ce aure saura sati biyu mutane zasu yi surutu idan aka fasa in yar ta shiga garari uban waye ze taimaka musu balle a guji maganar da zasu yi? Allah ya tsinewa duk wanda be yi surutu ba, dama ai mugun hali irin na mutanen yau yasa suka yi shiru kaf maƙwaftan ku ace an rasa wanda ze bugi ƙirji ya faɗawa Aminun gaskiya idan duk su yan uwansa maza yan ubanci yasa sun yi shiru suna kallo yar sa zata shiga gararin rayuwa su sauran da za a haɗa auren su tare idan da haka nasu maneman suka shuka rashin arziƙi ai ba zasu ja baki su kulle ba se shi za a masa mugunta a bar shi son ya ya rufe masa ido to ba a isa ba se kuma naga uban da ze ƙulla auran nan” Goggo Habi ta faɗa.

    Mama dai juya kai kawai take yi ta kasa cewa komai, tun da Anty Labiba ta kira ta ta gaya mata ta yiwa Bilal magana da kanta be ce komai ba daga nan ta ƙarasa cire ranta akan al’amarin auren sa da Halima ta kuma godewa Allah daya sa matsalar ta ɓullo daga gurin sa ko hakan ze sa Halima ta hankalta ta Kuma haƙura se dai ko da ta yiwa Abban zancen cewa yayi kar ayi saurin yanke hukunci a jira aji ta bakin su tun da akwai sauran lokaci.

    “Amma Hajiya na ke ganin abi komai a sannu ya fi, shi lamarin aure sirri ne ba’a san abin da Allah ya ɓoye ba be kamata ace muyi katsalandan a ciki ba. Aure nawa akayi a cikin irin haka daga baya kuma se kiga Allah ya warware komai ya wuce kamar be faru ba balle yaron nan ba wai zauna gari banza bane yanda kike tuna ni. Da aikin sa, a gwamnatin tarayya yake aiki bama state ba kin ga ko ai yana da albashin da ze riƙe aure mace biyu ma ba ɗaya ba, shi shirin aure kowa ya sani Allah ke yi ba mutum ba duk kuɗin ka duk tana din ka se kiga abu ya zo maka ba a yanda kayi tsammani ba musamman ace aure ya taso ga gini abin duk se a hankali fatan mu dai Allah yasa haɗin ya zama alkhairi duk wani ƙyale ƙyale da bidi’a ba shi ne ba”.

    Kallon ta Goggo Habi tayi tsaf tace
    “Lallai Salamatu dole ki ce haka, tone tone babu kyau amma da se in ce ai ba zaki ga aibun abun ba tun da irin auren da aka miki kenan da Mijin ki na Farko Haladu me kifi har yamma tayi za’a tafi kaiki ɗakin da aka bashi aro a cikin gidansu ba’a kwashe hatsin da aka ajiye a ciki ba. Haka muka raka ki aka ajiye ki a ɗakin uwar sa, ina kwananki uku Allah jiƙan rai Halima taje ta ɗakko ki aka kashe auren irin haka kike so a maimaita to ba da mu ba wallahi ba a taɓa ba ba kuma za a fara akan Halima ba”

    “Haba Goggo dan Allah ki de na faɗar haka” Mama ta faɗa se ta juya kan ta kafin tayi magana Abba da Baba Salahu suka yi sallama hakan yasa tayi shiru. Sama sama ta amsa gaisuwar da suka mata dan tun jiyan tace komai daya faru laifin Abba ne shi kuma Baba Salahu ta ce yan ubanci yasa yaƙi gayawa Abban gaskiya. A tsanake Abba ya sanar musu da abin da Halima ta gaya musu ya rufe da cewa
    “Da nasan ze zo da wannan maganar da ban fara rabon katin ɗaurin auren nan jiya ba. Gashi jar abokanai na na wasu garuruwan duk jiya na aika musu dan kar ya zama a ƙurarren lokaci har an fara turo mun da gudumma yanzu se dai na maida musu na bawa kowa haƙuri kenan”.

    “Aa wace irin magana kake yi haka ai ba cewa yayi ya fasa ba uzurin sa ya bayar be kammala gini ba, abun duk me sauƙi ne kiran sa ya kamata ayi aji ta bakin sa ko a kira su waliyyan nasa, idan lokacin ne baze ishe shi ba se a ɗaura auren a bar biki zuwa sanda ze kammala se su tare idan kuma haya ze nema duk ba wani abu bane suyi zaman su wata rana se kaga komai ya wuce kamar ba ayi ba” Inna Salamatu ta faɗa se Goggo Habi ta miƙe tana cewa

    “Da ba cikin ku dayayda Aminu ba se in ce kema hassada kike masa Salamatu ko da yake dama ai duniyar nan ta lala ce kai dai kayi ta kanka kawai to in ga dan bantan uban da ze zauna dashi ko iyayen nasa maza azo a haɗa duk tsiyar da suka kawo a maida musu yanzun nan ba se an jima ba gara da akayi haka Allah ya haɗa kowa da rabon sa ma alkhairi kan ta farau fasa aure ko a kanta za’a ƙare balle ace? Maza Amina taso muje ki tattaro komai da kika san ya kawo gidan nan a fitar dashi”.

    Mama ta sauke tagumin data zabga tun da Abba ya fara maganar tace
    “Ai babu wani abu nasu a gidan nan Goggo”
    “Mantawa nayi, to bari in ɗauko hijabi na ke Salamatu ki tashi ki raka ni can gidan nasu muje mu zage su dan ba zamu bar su haka ba ladan ɓatawa jikata lokaci da yayi dan uban sa” Goggo Habi ta sake faɗa, se Abba yayi saurin cewa
    “Duk abin be kai na haka ba Goggo ayi haƙuri” ta musu banza ta shige ɗaki. Daga ciki ta ƙwalawa Mama kira ta tashi ta tafi. Bayan barin su gurin Inna Salamatu ta kalli Abba tace
    “Kada ka biyewa zancen Habiba kasan ta da rikici tun zamanin ƙuruciya balle yanzu da girma ya cimmata, maganar yaron nan uzuri ne babba yazo dashi tun da dai muhalli a aure yana gaba da komai. A gani na kar a biyewa shaiɗan ace za’a fasa auren nan akan wannan, arziƙi da babu duk daga Allah ne nan duk daga babun muka taso gashi yanzu ubangiji ya bawa kowa bakin rabon sa. Ni dai shawarata Aminu ku kira iyayen yaron nan kuji ta bakin su, in har ba su suka ce a bar maganar auren nan gaba ɗaya ba karku bari ace daga gefen ku matsala ta ɓullo ba”.

    “Amma Yaya maganar gaskiya fa lamarin nan abin dubawa ne. Yau da ace yaron nan ya nuna iya ƙoƙarin sa a sabgar nan za’a fi samun ƙwarin guiwar kyautata masa zato amma fa ki duba tun da aka fara maganar nan wane yunƙuri yayi ko iyayen sa suka yi, ko sadaka za’a basu auren yarinyar nan ai yaci su nuna yabawa amma yau har saura kwana goma sha huɗu ba kira ba aike kuma jiya fa ko jiya naga katin auren ƙanwar sa Alhaji Malam ya raba a kasuwa kuma sunan ta ita kaɗai aka buga ban da nasa” Baba Salahu ya faɗa, Abba dai be ce komai ba ya harɗe hannu biyu yana sauraron yan uwan nasa. Shi kaɗai yasan yana yin da yake ciki a zuciyar sa ga irin kukan da Halima takeyi gaba ɗaya komai ya dagule masa.

    Sallama Baba Salahu ya musu yace Abba suyi magana da Mama, duk abin da suka yanke ya sanar masa, bayan fitarsa Inna Salamatu tace su je can falon sa suyi magana saboda Goggo, bayan sun nutsu tace masa
    “Kar ka bari shaiɗan ya shiga zuciyarka kamar yanda ya samu guri a zukatan sauran. Ba se na tuna maka ba ka fini sanin a yanayin daka auri uwar yarin yar nan ba, idan ban manta ba se da ɗaurin auren ku ya rage saura kwana uku kafin nayi ɗaukar adashi na baka ka biya kuɗin hayar gidan da kuka fara zama. A shekara goma na farkon auran ku se da kuka zauna a gida bakwai, da daɗi babu haka Amina tayi haƙuri da kai daicdai da rana ɗaya bata gaza ba har Allah ya yanke ya kawo ku in da kuke yau, yanzu idan ba wanda ya sani ba wa za’a faɗawa irin wahalar da kuka sha a rayuwa ya yarda? Baka zaton gwaji ne ubangiji yake yi maka yaga ta yanda zaka godewa ni’imar da yayi maka. A sanda Amina ta aure ka dai dai da kayan sakawar ka irgaggu ne Aminu amma yanzu fa? Ko cewa kayi ba zaka maimaita kaya ba kana da sararin da kullum zaka saka sabo.

    Yanda Allah yayi maka bakayi zato ba wata rana shima zeyi masa, a aure nagartar ma’auri ita ce abu ta farko da ake dubawa. Yaron nan bashi da laifi an san shi an san iyayen sa ubansa mutumin kirki ne har ya faɗi ya mutu ban taɓa jin an ce ga wani halin sa mara kyau ba badan ma mutuwa me tonon asiri ba ta yaya za’ayi ace kamar ɗan Alhaji Mansur ya rasa muhallin da ze shiga ya zauna da iyalansa? Kasan sanda ya rasu basu tasa sosai ba yan uwansu suka hau kan komai suka bar musu abin da suka ga dama shi da ƙannen sa da suke ciki ɗaya, yayyen sa na sama uku duk mata ne shi ɗin dai shi ya tashi yake ta fafutuka da nemo abin da ze rufawa uwarsa da yan uwansa asiri yanda ka gan ka ɗin nan hake yake me zumunchi abin sa na yan uwan sa ne har irin wannan Mijin ne za’a ce ba za’a bashi aure ba?

    Karka kuskura ka biyewa mutane dan idan abun kuka ya same ka dariya zasu maka idan na farin ciki kuma yazo se sun san yanda suka yi suka ture ko shi Salahun da yake wannan maganar naga Maryam haka ya aurar da ita ba lefen yanzu ka gaya mun duk cikin yayan dangi wa cece take jin daɗi a gidan aure kamarta? Ka ci gaba da addu’a kawai ka barwa Allah komai shi yasan sirrin daya lulluɓe a cikin auran nan dama kuma duk wani abun alkhairi ai baya samuwa ta daɗi mu ci gaba da addu’a kawai tun da dai yarinya tana son sa babu abin da za’a fasa in Allah ya yarda za’a yi komai arziƙin kenan, ubangiji ya hore maka ka kira shi kaji, idan har aikin gidan nasa ba me yawa bane da za’a iya ƙarasa wa a masa in ma kuma baze gamu ba a nemi haya ko ka basu gida su zauna arziƙin kenan amma zancen a fasa aure be taso ba sharrin da za’a bibiye mu dashi kaɗai ma se ka rasa in da zaka tsoma ranka to ina dalili tun da dai Allah be hana yanda za’ayi ba” maganganun da Inna Salamatu ta faɗa masa kenan da suka bar shi cikin kogin tuna ni zuciyar sa ta kasu biyu.
    *******************
    Se yamma lis na koma gidan Anty Labiba, ko da naje gidan su Hansa’u dama ban gaya mata komai ba data tambaye ni me ya same ni fuskata ta kumbura se kawai nace mata kuka nayi yan uwan Abba ne suka zo yi mun nasihar aure ta ringa tsokana ta daga nan muka ɗan taɓa zancen biki ƙawayen mu nata ƙorafin ba’a gani na naƙi nazo a fara shirye shirye nace mata gobe tazo muyi maganar a gidan Anty Labiba kawai. Ban iya runtsawa ba cikin dare, Bilal be kira ni ba na kira shi kuma wayar sa a kashe ga Abba ma nayi zaton yanda baya son damuwata kafin wucewar yinin ranar ze aiwatar da abinda ya kamata ya share mun hawaye na se dai har dare shiru wannan ya ɗaga mun hankali na ringa tunanin ko dai su Baba Salahu sun zuge shi ne tun da naga alamar daga shi har Baba Hashim ɗin ba son auren suke ba wannan tunanin ya ninka tashin hankali na tsabar damuwa har ji na ringayi numfashi na yana sarƙewa, rabuwa ta da Bilal is the last thing i could ever imagine in my life. Ina son Bilal irin wanda ban san adadin sa ba ba kuma na fatan ace wani abu ya shiga tsaka ni na dashi.

    Washe gari da wani irin ciwon kai na farka bana ko iya buɗe ido na da kyau ga ciki na daya ɗauki ciwo shima dan rabo na da abinci tun na safiyar jiya haka na wuni na kwana. Daƙyar na iya fita kitchen ina dafa bango na haɗa shayi, a ƙasan kitchen ɗin na zauna na shanye kafin na jingina jikin bango ma rufe ido na ina jin kaina na bugawa kamar me. Anty Labiba ta shiga, kallo ɗaya ta mun ta wuce yin abin da ya kai ta kitchen ɗin se da ta gama zaryar fitar musu da abin karyawa ganin har sannan ban motsa ba kafin tace mun
    “Ki tashi ki mun wanke wanke yau wadda zata miki gyaran jiki zata fara zuwa, kalli yanda kikayi firkai firkai dake a banza zaki kashe kanki saboda wani banza da be san mutunchin ki ba”. Se da ta maimaita sau biyu ban amsa ba a fusa ce tayo kaina tasa ƙafa ta haure ni, ina jin duk abun da take faɗa se dai bani da ƙarfin amsa mata a zaunen da nake jiki na ya saki gaba ɗaya duniyar ma juyawa takeyi a ido na. Haurin da ta mun yasa na zame daga bangon dana jingina na sulale a ƙasa ganin haka yasa ta fasa ihu babu shiri daga nan kuma ban sake tuna komai ba kawai na farka na ganni a gadon Asibiti Bilal na zaune a gefe na.

    Note
    error: Content is protected !!