Kura a Rumbu – Chapter One
by Maryam Farouk (Ummu Maheer)“Malam idan kaje ƊAN ALJANNAH zan sauka” na faɗa ina nunowa me Adaidaitan da muke ciki saitin in da ze ajiye ni, bayan daya gama daidaita parking na sauka ba tareda na kalli Hansa’u data kalli ɗaya ɓangaren ba nace
“Da ace kuturwa Allah yayi ni se inji haushi dan kince ba zaki tayani aiki ba, dake ko babu ke bazan rasa wanda zasu rufamun asiri ba” na faɗa ina miƙawa me Adaidaita ɗari biyar. Bata tankamun ba na juya ba tareda na amsa tambayar da me mashin ɗin yake mun ba akan iya kuɗi na ze ɗauka ko na mu biyun na shige kantin. Na rigada na rubuta list ɗin abubuwan da zan siya dan haka kai tsaye na shiga ɗauka cikin abinda be wuce minti sha biyar ba na gama dan ma na tarar da layi gurin biyan kuɗi. Wani Adaidaitan na tare ya ƙarasa dani kofar Nasarawa gidan Anty Labiba. Munir na ƙofar gida da abokinsa ina hango su naji raina ya sake ɓaci dan nasan ƙarshe yanzu Anty Labiba se ta tado da zancen da bana so amma ganin ya riga da ya ganni in na ce mu juya ma ze ga ai saboda shi ne yasa nacewa me Adaidaitan ya faka na sauka ina cin magani na biyashi kuɗin sa.
“Barka da zuwa Hajiya Halima” Abokin nasa wanda seda na sauka na gane Yahuza ne ya faɗa yana mun murmushi, na ɗauke kai sama ciki ciki nace “yawwa”. Kafin na miƙawa me Adaidaita kuɗin sa Munir daya iso kusada dani ya rigani, ɗari biyar ya bashi sannan ya duƙa ya shiga ɗaukar ledojin siyayyar dana zube a ƙasa. Murmushin sa me kyau yayi kafin yace
“Ashe kece zaki zo shiyasa na kasa tafiya”. Na wuce cikin gidan ba tare da na tankashi ba ina ji ya biyo bayana. Anty Labiba na zaune kan tudun gurin wanke wanke tana cire hancin kayan miya ta ɗago tana amsa sallamar mu.
“Aa, Munir. Ashe baku tafi ba?” Ta faɗa tana tsame hannunta daga abinda takeyi, a ƙasa ya aje kayan yana cewa
“Eh wlh, haka nan fa muka tsaya ashe rabon na ganta ne yasa” ya faɗa yana nuna ni. Na tura baki gaba ina wucewa falon Antyn ina jiyo ta tana cewa
“Billahillazi dai Munir se in ce baka da zuciya, yanzu saboda Allah ba zaka bar yarinyar nan ga mata nan fululu a gari masu sonka kamar suyi me ba? Wlh idan nice kai inuwar Halima bazan sake kallo ba balle har maganar arziƙi ta haɗa mu”.
Ya shafa kansa yace
“Ba zaki gane ba Anty” se tayi saurin tare shi tace “dama ta ina zan gane? To dai tun wuri gara kawa kanka faɗa ka nemi wata dan nan kusa banga Halima nada rabon gane wautar data tafka ko in ce take shirin tafkawa ba. Ita tayi asara wlh samun saurayi nagartacce kamarka me abinyi a zamanin nan” .
“Bari na wuce, adai cigaba da taya mu da addu’a a kuma sake tayani rarrashinta Anty” ya faɗa jin zata ɓaro wani zancen sannan ya juya ya fita nan kuwa Anty Labiba ta dasa mitar da bata gajiya dayi tunda na watsa mata ƙasa a ido nace bana son ƙanin mijinta kuma ɗan ɗakinta. Seda na jiyo ƙarar tashin mota alamar sun tafi kafin na aje mayafina na, kujera na aje kusada inda ya zube mun kayan na shiga gaida Anty Labiba ta wani amsa mun a ɗage ni se ta bani dariya ma irin wannan ɗaukar dumar magaji da nishi. Shikenan kuma se akace dan ya mata dole nima ya mun in so shi? Kowa fa da ra’ayinsa a rayuwar nan, ni da wanda nake so shima rashin zuciya yasa har ya bari maganar ta fito bayan tun ni dashi daya furta mun na sanar masa ina da wanda nake so ba kuma na ra’ayinsa.
Kayan na shiga fito dasu daga leda Anty Labiba ta kalleni tace
“Ban gaya miki karki sake zuwa gidan nan kice zaki wa wancan santolon cima zaunen abinci ba?” Nan da nan na haɗa rai nayi kicin kicin bata damu ba taci gaba da cewa
“Tsabar rashin sanin ciwon kai, mazan arziƙi na wahaltawa yammatansu amma shi mace ce take wahalta masa yana kwance ba cas ba as gaki yar wahala ki ringa dafa abinci ki kai masa ba godi bare na gode balle a baki tukuici to ba’a gidan ba dan gas ɗina bana gomnati bane kije can gidanku kiyi”. Kan ince wani abu Uncle Sale ya fito daga falo yana cewa
“Meye haka Labiba?” Kitchen ɗin ta dake tsakar gida ta shige ba tareda ta amsa masa ba na gaishe shi ya amsa yana tambayata su Anty kafin ya bita kitchen ɗin ni kuma na wuce falo ɗauko wayata dan na manta ban tambayi Bilal abincin me miya yake so ko kuma jallof ba.
Sau biya na kirshi be amsa ba hakan yasa na barshi na tafi akan nayi masa jollop ɗin kawai tunda na siyo kaza harda cabbage da zanyi coslow. Seda na jira Anty Labiba ta gama miyarta ta fita daga kitchen ɗin kafin na shiga nawa aikin, nasan magana Uncle Sale ya mata shiyasa ta barni dukda haka shiga goma fita goma seta mun habaicin ni yar wahala ce ina wa wani can ƙaton banza girki, tsakani da Allah ta ina mijin da zan aura ya zama ƙaton banza? Laifi ne idan na dafa abinci na basa?
Ana kiran la’asar na kammala komai, cikin sababbin kulolinta na shirya abincin dama na gyara ƙaramin falonta na saka turaren wuta na kulle, ban bari ta lura ba na shige da kulolin da plates na sake kullo ɗakin kafin na koma ɗakin su Amir na shiga wanka. Ina tsaka da shiryawa ta shigo tana cewa
“Naga kin aje mana tsurar shinkafa da salad ina kazar?”
“Guda ɗaya ce fa Anty” na faɗa zuge zip ɗin skit ɗina, ta ballamun harara tace
“Ko ɗan tsako ne wlh se na ci, ban muƙullin falo na” sena yi waje da sauri ina cewa
“Amma tsakani da Allah dai an san abun nan na mutum ɗaya ne kuma za’a sa masa rani, bafa shi da lafiya banda ma bani da kuɗi me kaza ɗaya zata masa ma” na wuce falon tareda maido ƙofa dan karta biyo no taga kulolinta ta dasa mun sabuwar tijara. Fukafukai na ɗakko mata da ƙundu na zubo mata albasa da koren tattasan da nayi garnishing pepper chicken ɗin dasu ina ajiyewa kuwa ta fara auna mun zagi wai mayya na maida ita ko me? A karo na biyu Uncle Sale daya dawo daga sallah ya sake ceto na, sanin yau weekend yana gidan ma yasa har nayi karambanin zuwa badan haka ba gara in zauna a gidanmu ƙarshe dai nayi raba daidain duk abinda na dafa dasu Mu’azzam amma babu wanda ze zageni ya mun gori.
Ƙarfe biyar Bilal ya kirani akan ya iso yana waje, na sake gyara fuska ta na ƙara turare kafin na fita bayan na gayawa Anty Labiba zuwan nasa ta zage ni ta zage shi sannan ta shige ɗaki. A jikin sabon mashin ɗin daya ce mun ya siya Lifan na tarar dashi, yasha kwalliya da wata shadda ruwan ƙasa datayi matuƙar karɓar kalar fatarsa me ɗan duhu. Sabon askin da yayi ya ƙara fito da tsantsar kyansa ga gemun dake ƙara matar dani a soyayyar sa se na ringa jin kamar na tafi da gudu na rungume sa ko zanji sauƙin raɗaɗin da sonsa yake haifar mun cikin zuciyata. Cikin taku ɗaɗɗaya na isa inda yake ina murmushi kamar yanda shima yake doka mun murmushi. Cikin ƙasa da murya kamar me tsoron wani yaji abinda zan faɗa nace
“Barka da zuwa yarimana”, ya saki murmushin jin daɗi tareda gyara tsayuwarsa kafin yace
“Kin san wani abu?” Na girgiza masa kai alamar aa se ya ce
“Kaina yana ƙasa kawai naji wani haske ya dalle mun ido, na ɗago da mamakin wace fitila ce aka kunna haka domin dai rana tayi nisa da nan gurin balle nace kaifinta ne ya haska ni seda na kalla naga ashe kece. Kyanki da annurin fuskarki kullum ƙaruwa suke Halims, anya bazan fara saka baƙin glass ba kafin ƙyallin fuskarki ya makantar dani?”
Wata dariya nayi kaina ya fasu, irin kalaman nan na Bilal su suke ƙara saka naji duk duniya bani da sauran buri daya wuce na kasance matar sa idan hakan kuwa ta tabbata nasan na kere sa’a, ni da baƙin ciki har abada domin ko babu abinci irin wannan maganganun nasa sun isa su ƙosar dani.
Cikin murya me cike da shagwaɓa nace
“Bana son wasa”
“Wane irin wasa? Kina raina irin baiwar da ubangiji ya miki ko? Baki san hasken idanunki kaɗai sun wadaci a zauna a cikin ɗaki ba tareda an kunna fitila ba?” Ya sake faɗa yana mun kallon dake kashe mun jiki, sena juya ina cewa
“Ni dai barni haka muje ciki kaida baka jin daɗi ka tsaya kana ta surutu”
“Au, surutu ma nakeyi ko? Shikenan bari na koma inda na fito tunda yabonki da nakeyi sututun banza ne a gurinki” Ya faɗa yana ɓata fuska kamar ransa ya ɓaci nan da nan hankali na ya ɗaga na juya da sauri ina cewa
“Haba mana ya zaka ce haka? Nifa ina magana ne akan baka jin daɗi kana gajiyar mun da ƙafafunka da tsayuwa amma kaima kasan bana taɓa gajiyawa da sauraron kalamanka. Ni a duniya ma bayan karatun alƙur’ani akawai wani sauti da nake mararin sauraro ne bayan muryarka?”
Yanda yayi ya tabbatar mun yaji daɗin maganata yace
“A ina zan aje mashin ɗina, ko da yake ma baki ko lura dashi ba balle ki tayani murna”
“Wlh Yarima murnar ganinka da daɗin kalamanka suka sa kai kaɗai nake ji da gani a gabana. Mashin yayi kyau, Allah yasa lafiya ta kashe Allah kuma ya tsare ka daga sharrin ƙarfe da titi” ya amsa mun da
“Amin Halims”. Seda na buɗe masa get ya shiga da mashin ɗin kafin muka jera zuwa cikin gidan tabbas nida Bilal haɗin nan da bature yake cewa *MADE FOR EACH OTHER*. Ko magulmata dan suke ganin bamu dace da juna ba suna faɗar haka ne ta wasu fuskokin da a ganinsu muka banbanta bawai a zahirance ba domin duk wanda ya kalle mu seya ce mun dace da juna, daga kuma sanda na haɗu dashi na yardarwa zuciyata tare aka halitto ruhikanmu babu kuma wani al’amari da ze raba mu face mutuwa.
Bilal ya ringa kallon falon kafin yace
“Amma gyaran gida su Anty Labiba sukayi?” Seda na miƙa masa kofin dana cika da ruwan lemon exotic me sanyi ya karɓa kafin nace
“Eh mana, gidan gefensu ne suka fitar da rabin filinsu shine ya siya yayi ƙari. Wannan falon ma ai sabon gini ne ka manta da babu shi”
“Lallai Alhaji Sale bayajin garin nan, a yanda ake kukan babu shi har ya samu rarar gyaran gida ba shakka ƙasar a hannunsu take” ya faɗa bayan daya shanye lemon. Shiru na masa dan nasan yanzu ze fara surutansa da basu nake son ji ba, ilai kuwa yace
“Yanzu me gida kamar wannan be ishe shi ba har ƙari yayo ni ɗan akurkin nawa ma tunda na kai linta na gagara cigaba, koda yake su yan oil and gas dama ai arziƙin ƙasar a hannunsu yake. Da ace muma za’a buɗa mana mu ɗan samu se kiga a wata shida na warware har na fara aje tumbi fa”.
Da “uhm” na amsa shi na sauka na fara zuba masa soyayyar jallop ɗin basmati da taji gurzajjen karas da albasa na ɗora masa ƙirjin kaza in da yafi so da haɗin coslow daya ji kwai da madara da. Tun kafin na gama zubawa ya sakko kan carpet ya zauna yana cewa
“Kin san fa tunda kika ce zaki mun girki ko karyawar kirki banyi ba yau ciki na empty yake” nayi murmushi na aje masa plate ɗin ina cewa
“Ai da dai ka ci wani abun ko ba yawa bafa na so ka ringa barin mun cikin ka da yunwa ka sani”
“Ai na ɗauka da safe zaki abincin ne shiyasa da naga har goma tayi baki kirani bane ma nasha Tea” ya faɗa yana kai lomar farko bakinsa. Yanda ya lumshe ido yana tauna abincin kana gani kasan daɗin ya kai masa ko ina, seda yayi loma uku kafin ya kalle ni yace
“Wato Halims bana zaton a duniyar nan akwai macen data kaiki iya sarrafa abinci, wai carkwai maɗagwai. Badan kar inyi saɓo ba se in ce wannan abinci ko hurul’ayni ta dafa ai se haka”.
Kaina ya sake fasuwa, na zuba masa zoɓo roba ɗaya ne na sata a fridge ɗin Anty Labiba yana cin abincin yana santi seda yafi rabi kafin yace na sakko muci na girgiza masa kai ina murmushi naci gaba da kallonsa yana zuba loma, yanda yake cin abincin ya kamata ace ya bani haushi irin yanda yake cika baki kamar wanda be taɓa ci ba amma kuma dake zuciyar cike take da so da begensa burge ni yakeyi ina ganin so da shaƙuwar dake tsakaninmu tasa baya kunyata yake iya cin abinci a gabana. Tas ya tada abincin da iri na mu huɗu ma ba lallai mu iya cinyewa ba, shi kansa ina mamakin sa dukda nasan maza suna da cin abinci amma na Bilal kam daban ne kodan yana ƙwallo ne?
Mun daɗe muna hira yana kashe ni da kalaman dake ƙara mun sonsa da ƙaguwar na zamto tasa, ina so ma sako maza zancen tunin da Abba yace na masa akan turo magabatansa a saka ranar auren mu kusan wata uku kenan shiru bece komai ba, yanda yake ta sako mun ƙorafin har yanzu wata shida kenan daya samu aiki wai ba’a fara biyansu albashi ba. Sati uku baya sukaje Abuja akayi capturing nasu IPPIS sun saka ran samun albashi a watan da aka shiga sedai shiru har anci kwana goma babu labari. Wannan dalilin yasa nake masa uzuri tunda koda ace an saka ranar bashi da ƙwaƙwƙwarar hanyar da ze tara kuɗin da ze ƙarasa gininsa har azo maganar lefe da sauran hidimar aure. Samuwar aikin dama da ita muka dogara to gashi kuma har yanzu ba’a samu yanda ake so ba amma kuma dukda haka kamar yanda Abba yace suzo a saka rana ko da shekara biyu suka ce lokaci ne da an kirashi ze zo yafi ace ayi ta tafiya haka babu cigaba. Tun muna ND 2 aka kawo kuɗin aure gashi yanzu satuttuka suka rage da mu gama HND.
Duk ƙawayena da muka fara karatu tare wasu sunyi aure harda yayayensu waɗanda basuyi ba da yawa da sa ranarsu da zarar mun ƙarasa karatu se waɗanda Allah be kawo musu mazan ba, a ciki kuma zan iya cewa nice kaɗai na fara karatu ina da tsayayyen saurayi dan tun ina SS3 muka haɗu da Bilal lokacin daya zo NYSC makarantar mu gashi ana lissafin shekaru kusan biyar kenan yanzu.
“Halims” ya kira sunana hakan ya ankarar dani zurfin da nayi a tunani. Na sakar masa murmushi ina gyara mayafin kaina daya zame yace
“Ina ta magana kinyi shiru akwai wani abun ne?”
Kai na girgiza masa ina murmushi nace “babu komai, ina sauraronka”
“Me na faɗa daga ƙarshe to idan dai kina jina?” Ya tambayeni, na sakeyin murmushi nace
“Cewa kayi kana so na” seya fashe da dariya yace
“Canka kikayi kawai saboda kinsan harshena baya gajiya da furta abinda yake cikin zuciyata. I love you whole heartedly Halims, wlh duk sanda nazo gurinki Allah kaɗai yasan yanda name yaƙi da zuciyata amma ji nake kamar karmu rabu, na masu na kasance tare dake a matsayin matata ta sunna”.
Ƙasa nayi da kaina ina murmushi cikin jin kunyar kalamansa, ya matso kusa dani yana cewa
“Dagaske nake Halims, kinga rashin lafiyar nan da nayi duk magungunan da nasha ba wani aiki suka mun ba ina kwance se ince inama kina kusa dani nasan dakin shayar dani maganin dake tattare dake zan warke”
Zumbur na miƙe daga kusa dashi ina ɓata fuska cike da shagwaɓa kamar zanyi kuka ya fashe da dariya yace
“Matsoraciya, ke ba dama a ɗakko magana se ki wani birkice”
“Ni dai bana so” na faɗa ya miƙe yana cewa “Na bari My Halims, bazan sake ba. Amma da gaske a matse nake da son kasancewa dake. Ki tayani da addu’a akwai abinda nake jira da zarar ya tabbata za’ayi komai shikenan ki zama tawa ki dena mun ƙwalele kina hanani bacci da dare” ganin na nufi ƙofa yasa ya shiga dariya yana cewa
“Haba mana nace miki na dena ai yanzun ma baki nane ya suɓuce. Magriba tayi kizo muyi selfie na samu na rage zafi kar na tafi ina mafarkin kwalliyar nan taki”. Dakyar na tsaya ya ɗauke mu selfie a wayarsa sannan yayi mun ni kaɗai, har munje bakin kofa yace
“Ban ma san me zanci ba da daddare ba wlh. Wai tuwon Anty Murja tayi bayan tasan bana so ga kuma baki na babu daɗi”. A raina nayi murmushi nace “dama jira nake naji zakayi magana ko kuwa” a fili kuma nace
“Afuwan, ganinka ne duk ya rikitani. Bari nayi maka packaging sauran se kaci idan ka koma”
“Haba dai, su Amir ba zasu ci ba? ” Ya faɗa kamar gaske. Sena wuce shi kawai a raina ina gulmar halinsa. Ko pure water na bashi seya tafi da sauran balle abinci shine zece wani su Amir ba zasu ci ba. A fararen robobi na juye masa sauran abincin da banda wanda na ɗanɗana da ina girkin ban sake jinsa a baki na ba. Roba uku na masa ɗaya shinkafa ɗaya kaza se coslow a ɗayar lemon ma na juye masa a gorar Faro na haɗe masa komai cikin ledar dana ɗakko.
“Wannan halin naki yake tabbatar mun zaki kula da cikina idan mukayi aure, Allah dai yayi miki albarka ya barmu tare my Halims” ya faɗa sanda ya karɓi ledar. Muka jera yana mun surutu, seda na buɗe masa get ya fita da mashin na rufe kafin na fita na same shi ya ɗaure ledar yanda abin ciki ba zasu zube ba kafin ya hau mashin ɗin yana kallona yace
“Da yanzu zaki wuce gida se mu tafi na ɗana ki”. Tunda yazo nake raya in masa magana akan da canza mashin ɗin da yayi dama gini ya cigaba ko yayi amfani kuɗin ya haɗa kayan saka ranar tunda dai tsohon nasan babu abinda yayi ai amma gudun kar yaga na shiga rayuwarsa yasa nayi shiru se nace
“To bari kawai nayiwa Anty Labiba sallama se mu tafi dama na gaji gashi kuma gobe ina da practical exam ina so nayi karatu” na juya cikin gidan.
Toshe kunne kawai nayi na haɗa kayana na gudu na bar mata wanke wanke ina tana faɗin zan sake zuwa ne na tafi, faɗan mu ba wani jimawa yake ba da kanta ma zata nemo ni musamman yanzu da yara zasuyi hutun makaranta ga tsohon ciki tana dashi dole ta nemo me tayata da kayaniyar yaran. Na ɗane tsuntsun soyayya ya lula damu muna tafe yana mun surutan da ba wani ji nake sosai ba saboda iska har muka isa sabon titi gidan mu. A bakin gate ya tsaya na sauka ya kalli ginin benen da ake ɗora mana da har an fara fenti yace
“Ashe aikin nan yayi nisa haka, wato mu talakawa ne muke jin garin nan masu kuɗi sha’aninku kawai kikeyi”. Fuska ta ba yabo ba fallasa ban dai ce masa komai ba ya shiga laluben aljihu, harga Allah na saka ran tunda yace mun ya siyi mashin idan ya tashi zuwa ko 5k ce ze bani shiyasa ma banji komai ba na kashe kuɗin transport ɗina na sati da Abba ya bani nayi masa abinci ko be biyani duka ba a ƙalla zan rage wani abun musamman da yake ta koɗa daɗin abincin yana faɗin na cancanci tukuici ganin yana laluben Aljihun yasa nayi ɗan murmushi ina jira se naga ya zaro wayarsa ya buɗe kafin ya juyo yana cewa
“Bari in sake miki hoto wlh kin mun kyau yau ɗin nan irin sosai fa My Halims.
Takaici ya kamani amma haka na gyara ya shiga ɗauka na hoton seda aka kira sallah kafin yamun sallama ya burga mashin ɗinsa ya tafi na juya jiki ba ƙwari na shiga gida a raina ina ayyana ƙila se jibi da yace ze zo ko kuma ya mun transfer.
*MASU ƁUKATAR A TALLATA MUSU HAJOJINSU ZA SU IYA TUNTUƁARMU TA LAMBOBIN 07045308523 MUN GODE*