Kura a Rumbu – Chapter Nineteen
by Maryam Farouk (Ummu Maheer)Ba zan iya cewa ga ta yanda muka fita daga gidan ba ni dai kawai na san munje gidan mu; muna sauka daga Adaidaita sahu Amirah ta sake ni na dafe gini saboda jirin dake kokawar kayar dani ita kuma ta tura ƙofar get ta shiga tana rushewa da kuka tamkar wadda tazo isar da saƙon mutuwa. Daƙyar na cira ƙafata na rufa mata baya ina yi ina dakatawa saboda ciwon marar dake taso mun, na dafe ƙofar shiga falon na tsaya ina kallon mazauna ciki da suka rufu kan Amiran cikin tashin hankali suna tambayar ta ba. . .