Kura a Rumbu – Chapter Nine
by Maryam Farouk (Ummu Maheer)Ina ji wayata na ƙara na san kuma Bilal ne amma naƙi amsawa, Allah ya sani har raina naji haushin anin da ya mun. Wane irin tozarci ne lefe a leda? Idan bashi da kuɗin akwati ya ara mana ko kuma ya bar lefen gaba ɗaya tun da ni dama ban saka rai da zeyi mun ba. Shine kuma saboda rainin hankali har yana cewa ze bani mamaki da irin lefen da ze mun aiko ga mamaki nan ya bar mun abin faɗa a cikin dangi da unguwa. Kusan minti talatin ina kuka ina jiyo hayaniya sama sama daga falo, Anty Labiba ce ta tasa dangin Bilal da rashin arziƙi ita da Anty Ummi ƙanwar su Abba. Da alama kuma manyan dake gurin abin da yake ransu kenan shiyasa basu tsawatar musu ba basu dai saka baki ba dan kar ace sun taru sun zaka ɗaya.
Ko a ƙauye ban taɓa jin an kai lefe a leda ba ai wlh gara ku zubo su kwalla ko fanteka kunyi gargajiya akan dai wannan nuna tsiyar” Anty Labiba ta faɗa cikin jin haushi. Su kansu kayan ba wai wasu na arziƙi bane, Atamfofi ne guda bakwai da lace biyu se shadda biyu da material ɗaya se kuma dogayen riguna kala huɗu da mayafai huɗu haka jaka da takalma duk saiti hurhuɗu. Tsiyar zubo su a leda ce ta rinjayi ta kayan, ko da yake iya ƙarfin sa yayi ba’a kushe masa ba. Tankawa da yayar Bilal tayi yasa abin ya sake tsamari aka shiga faɗi in faɗa kamar dai za’a kaure da faɗa se da Baba Abubakar ƙanin su Abba ya shigo gidan ya tsawatar musu. Dake Abban ma yana gida tare da su Baba Salahu take ya kira shi a waya suka zo Baba Salahu ya ringa faɗa akan me yasa su Anty Labiba za suyi haka su dai yan kawo lefe guiwa babu ƙwari suka miƙe. Baba Salamatu da neman ayi ta cewa Mama Fauziyya ina kayan snacks da aka musu da tukuici? Nan fa baga dangin Maman ba ba ga nata yan uwan ba suka hayayyaƙo mata baiwar Allah har hawaye se da tayi ƙarshe ma tace ba zata kwana gidan ba tafiya zatayi ba za’a ƙarasa biki da ita ba daƙyar aka bata haƙuri ta zauna.
Ƙarfe goma da rabi bayan na gama shan kuka na na ƙoshi ina kwance Hansa’u tace mun in zo in ji Abba ya kira na, na zumbula hijab fuska a kumbure muka fita se naga ta nufi hanyar waje na kalle ta kafin nayi magana tace
“Suna ƙofar dasu Baban Galadanci”. Ban yarda ba amma na bita, ina saka ƙafata a waje muka haɗa ido da Bilal na juya da sauri kafin na ida komawa ciki ya riƙe hijabi na yana cewa
“Dan girman Allah ki tsaya ki saurare ni Halima”.
Tsaye nayi na kasa ci gaba da tafiya amma ban juya na kalle shi ba, se ya zagayo yana fuskanta ta tamkar ze durƙusa mun yace
“Na fiki baƙin ciki da takaicin abin da yan uwana suka aikata mun domin ba ke suka wulaƙan ta ba ni suka yi wa, ga Nasir ne shine shaida, dubu hamsin na nawa Yaya Saratu su siyo akwati amma suka aikata wannan abun amma babu komai kowa yayi me kyau dan kan sa” ya ƙarasa kamar ze yi kuka. Se kuma naji tausayin sa ya tsurga mun, dama zuciya ta tana ta raya mun babu sanin sa amma na danne yazun kuma da yake gaba na se naji na yarda dashi amma duk da haka ban nuna ba cikin dake wa nace
“Dama ai kace zaka shayar dani mamaki ga shi kuwa ka bar mun abun faɗa a cikin dangi da ƙawaye ka ja mun abun gori har jikokinmu” na rufe ido da hijabi na na fara kuka take hankalin sa ya sake tashi. Ya ringa rantse rantse har yana durƙusawa ya riƙe ƙafafuna ganin zan bar gurin.
Murna fal zuciyata, se da na wana shi iya yanda naji ya mun kafin cikin shagwaɓa nace na haƙura.
“Nagode Halims kuma alƙawari, ba dai akwatin lefe bane? To ki biyo ni bashi in sha Allahu zan biyaki da dozen ma ran da kika haifar mun Bilal junior ko little Halims” se na rufe ido na cikin kunya jin Nasir na cewa
“Daga gobe ne ai zamu fara irgen lokaci” ganin zasu fara shaƙiyancin yasa Hansa’u da takaici ya hanata cewa komai tun tsaiwar mu tace dare yayi mu shiga gida. Haka muka raba dare muna waya da Bilal yana faɗa mun irin murnar da yake ciki da yanda ya tsara goben mu zata kasan ce. Na ringa juyi a gado ina jin kamar goben tayi mun nisa.
Washe gari aka tashi da shirin ɗaurin aure, yini da kai amarya duka a ranar za’ayi. Da wuri muka koma gidan su Hansa’u ni da ƙawaye na da muka kwana tare har sanda muka fita kuma ledojin lefe ma na zube a falo na dai ji Goggo Habi na cewa Anty Labiba a kwashe waɗannan kayan tsiyar kafin mutane su fara shigowa a samu na yayatawa a gari. Sanarwar ɗauruwar aure a tsakanina da Bilal yana cikin abubuwa ma fiya daɗi da kunnuwa na suka taɓa sauraro tsayin rayuwa ta. Tsabar farin ciki bayan da nayi sujudushshukur se kawai na zauna na fashe da kukan murna. Ƙarfe biyar muka tafi Galadanci in da aka haɗa mu da sauran cousins ɗina biyu iyayenmu maza suka mana nasiha daga can kuma bayan magriba aka ɗauki kowa zuwa gidan mijinta.
Kwata kwata na kasa yarda wai yau nice na zama matar Bilal? Da su Anty Labiba zasu tafi ta riƙe hannu na tana cewa
“Buri ya cika kin zama matar Bilal Halima, se kiyi haƙuri domin yanzu wata rayuwa ta daban zaku shiga ba wacce kuka saba da ita a waje ba. Yanzu ne za kuyi zaman gaskiya da gskiya halin kowa ya fito, zaki iya tarar da Bilal a yanda kika tsammaci samun sa koma fiye da haka ki na kuma iya tarar da akasin hasashen ki ma’ana yazo miki da wasu halaye na daban da basu kika sani a tare dashi ba. Fatan mu yanda kika masa halacci ya maida miki, kiyi haƙuri da duk abin da zaki ji ko ki gani duk wani gidan aure da kike gani da kalar ƙalubalen sa haƙurin da ma’aurata suke yi shi yake lulluɓe komai kiga tamkar ba’a saɓawa. Mace ita take mayar da gidan ta dausayi ko ta mayar dashi filin yaƙi. Yanda kika ɗora mijin ki haka ze miƙe. Idan kin tafi dashi ta laluma zakiji daɗin sa in kika koya masa hargagi da masifa har tsufa hara ze ringa miki dan haka ki koyi ta yanda zaki ringa bayyana fushi idan ranki ya ɓaci. Ina miki nasiha da kiyi koyi da halin Mama, na tabba har kike riƙi halayanta na gari badai a kawo ƙarar ki ba. Ina sake maimaita miki da kiyi haƙuri Halima, kiyi haƙuri kiyi haƙuri ki ƙara da haƙuri Sadiyayye. Yanzu ba zaki gane haƙurin me nake nanata miki ba. Allah ya albarkaci rayuwar auren ki, Allah ya mallaka miki Bilal ya hane shi da yi miki butulci irin na maza” se ta fashe da kuka muka rungume juna daƙyar aka raba mu suka tafi ya rage saura ni da ƙawaye na.
Dubu hamsin abokanan Bilal suka bada kuɗin siyan baki ga ruwa da lemo katan katan da kayan shayi, a cikin kuɗin Hansa’u ta cire dubu goma ta saka mun a jakata, itama se da muka sha kuka kafin muka rabu ya rage daga ni se Habibi na cikin gidan mu. Faɗar irin tarairayar dana samu a gurin Bilal ɓata baki ne, tamkar ƙwai haka ya ringa riritani yana shayar dani madarar soyayya har ya samu nasarar maida ni cikakkiyar mace jikin mu ya ƙara sa zama abu ɗaya kamar yanda zukatan mu suka daɗe a tare. Washe gari haka ya wuni tare dani duk da yan uwanmu da suka fara zuwa tun safe da nashi dangin be fita ba se da yamma tayi aka zo kawo gara sannan ya fita ana idar da sallar isha’i kuwa ya dawo.
Haka rayuwa ta fara miƙawa, tsakanina da Bilal a kullum so da shaƙuwar mu ƙara karfi yakeyi. A sati guda da auren mu ina jin da ace wani kuskure ya gifta har ya zamana ban auri Bilal ba da bazan taɓa yafewa kaina ba. Bilal ƙarshe ne gurin iya tattalin mace, ya iya soyayya. Irin soyayyar nan me tsayawa a rai da kake wuni cikin shauƙi da tunani ita Bilal yake gwada mun. Se da muka kwashi sati biyu ban da sallah babu abin da yake fitar dashi daga gida tun da komai muna dashi babu ce kaɗai ba’a sako mun a cikin garata ba har da soyayyen nama da dafaffen kayan miya da ɗanye se dai idan zan yi girki kawai na ɗiba. Baƙi yan ganin ɗaki ma sun haƙura saboda yanda baya kunyar idon kowa haka ze zauna a cikin su ko kuma ya riƙe ni a ɗaki se dai su gaji da jira su tafi. Dake dama dangin sa ne masu zaryar ni nawa tun da aka kawo gara babu wanda ya sake zuwa se ranar dana yi kwana biyar ne Gwaggo Habi tazo mun sallama zata koma Birnin gwari.
Ranar da muka yi sati biyu tun safe ya ce mun zamu fita. Na ringa murna dan ji nake kamar na shekara a guri ɗaya, na ɗauka ma da wuri zamu fitan dan haka kafin azahar na gama girki na shirya se yace mun se da yamma. Tsaf muka shirya, tsakanin ni dashi se ka rasa tantance wanda auren yafi karɓa. Munyi kyau jikin mu ya murje muna ta ƙyallin amarci abun mu. Muna tsaye a bakin titi muna jiran abin hawa ya kalle ni yana murmushi yace
“Kin ga da ace Abba ya sako miki mota a kayan gara hankali kwance zamu fita muna yangar mu a titi”.
Murmushi kawai nayi ba tare da nace masa komai ba, gidansu muka fara zuwa tamkar zasu cinye ni saboda ƙauna. A can mukayi sallar Magriba kafin muka wuce gidan mu Hajja nata mu tsaya mu ci tuwon dare yaƙi, a cikin dubu goman da Hansa’u ta cire mun na bata dubu biyar ta ringa murna kuwa. Har goma muna gidan mu saboda Abba be dawo da wuri ba. Na lura da yanda Mama take ta bi na da kallo kamar na canza mata, se da muka shiga ɗaki take tambaya ta komai lafiya dai nace mata ƙalau.
“Haka ake so aji, Allah ya baku zaman lafiya ya kaɗe fitina. Da go be su Imam suke cewa zasu zo amma tun da kun zo yau se su bari se wani sati” na mairairaice nace
“Haba Mama zuwan mu daban nasu daban ai, dama goben ya ce zeje wani ɗaurin aure jigawa nasan kuma zeyi yamma kinga sa tayani hira”. Da zamu tafi Mama ta haɗa mun su kuka daddawa da kuɓewa wanda dama tace se daga baya za’a kawo harda dambun nama da kilishi. Abba ne ya ce Mu’azzam ya kaimu tun da dare yayi, naso ace mun biya gidan Anty Labiba amma tun kafin mu fita daga gida da na yiwa Bilal maganar cewa yayi ba yau ba, da muka fito kuma dare yayi shiyasa kawai na haƙura se wani lokacin. Da yake mun ci abinci wanka kawai mukayi muka kwanta rungume da juna kamar ko yaushe.
Washe gari da wuri ya shirya saboda ɗaurin abokinsa da yace tare sukayi karatun university. Khalil na da kirki sosai, tun daga Maiduguri ya zo mun biki kin ga ai ba naƙi zuwar masa ba nan dai da Jigawa” ya faɗa. Ina gyara masa zaman hularsa nace
“Ai kam dai ka kyauta, ba dan yanda kake ta nanata amincin ki dashi ba bazan yar da ka tafi wani guri yini guda ba tare da ni ba”. Se da yaja hanci na ni kuma na shagwaɓe fuska kamar zanyi kuka se ya rungumeni yana cewa
“You have no idea on how much I’m going to miss you sugar, na faɗa miki kawai dan Khalil ne badan haka ba yau Sunday dai ɗaurin aure ko a ciki garin Kano ne se dai a mun haƙuri”. Nema mukayi mu lalace a tsaye da soyayya se da wanda zasu tafi ya kira shi kafin ya sake ni duk ya kashe mun ya saka mun shauƙin son kasancewa tare dashi.
Se da na raka shi get ina masa addu’oi kafin na koma cikin gida, minti uku tsakani wayata ta shiga ƙara na amsa ganin shine yace
“Babe kin san guy ɗin nan wai motar sa babu mai se yanzu yake faɗa mun?” Nace
“Toh, Allah ma ya sa kun sani da wuri ai ba se da kuka hau hanya in da babu gidan man ba”.
“Haka ne, amma yayi yawa ai, me yasa tun tuni be faɗa ba kawai yace mana za’a tafi a motar sa? Ai se yace dama zamu haɗa kuɗin mai kinga da se musan da lissafin sa” Ya sake faɗa. Se nayi murmushi nace
“To yanzu dear kwata kwata nawa ne zeyi muku full tank da kake wannan mitar, ka bad kuɗin a saka man ku tafi mana kaga fa lolaci yana ta ja kar ku makara kuma”
Ƙaramin tsaki yayi kafin yace
“Ni fa 2k kawai na fita da ita shima saboda ba’a son tafiya babu kuɗi. Kuma ATM ɗina jiya na manta shi hannun Abubakar dana bashi ya ciro kuɗi, amma bari mu dawo na gani na san bazan rasa yan canji dana bari a gida ba” daga nan ya kashe wayar. Tunanin kar su sake ɓata lokaci yasa kawai na cire dubu biyar cikin kuɗin da Abba ya bani jiya na riƙe a hannu na, ina jin tsayuwar mota na yafa mayafi na na fita muka ci karo a bakin get na miƙa mishi ina murmushi se ya karɓa tare da pecking goshi na ya juya yana ɗaga mun hannu.
Dake su Imam da Amirah harda Inayah d Amir ɗin Anty Labiba sun zo tare muka wuni muna ta sabgogi se la’asar Mu’azzam ya zo ya ɗauke su, na basu kilishin da na taho dashi jiya daga gida su kaiwa Anty Labiba tun da nasan tana so kuma Mu’azzam yace su ze fara saukewa a gida bayan sun tafi na hau gyaran gida kafin wani lokaci na gama komi nayi wanka, ina da miya dan haka couscous zan dafawa Bilal idan sun dawo.
Dab da sallar isha’i ya shigo gida, se da na haɗa masa ruwan wanka na fitar masa da duk abin da ze yi amfani dashi kafin na barshi a ɗaki na koma kitchen na ƙarasa haɗa abinci. Har da fruit salad nayi dan nasan shi daga zarar an ci abincin dare ze fara mitar bakin sa na masa motsi yana so yaci wani abu kuma ya gaji da cin kayan gara. Mun cin abincin yana mun hirar yanda ɗaurin aure ya kasance, ashe mota ce ta lalace musu a hanya shiyasa ma sukayi dare. Bayan mun gama na kwashe koma na kai kitchen sannan na dawo na zauna akan cinyarsa ina jan gashin gemun sa, ya ɗora kan sa a kan ciki na yana cewa
“Har yanzu baki fara jin komai a nan bane?” Dariya nayi na ture shi ina cewa
“Haba sarkin kazallaha, 2 weeks fa yau me zan fara ji?”
“Ki dai zauna wasa yarinya ni nasan na daɗe da yin aika aika”. Haka muka ringa hira cikin nishaɗi haɗi da wasannin soyayya. Ƙarfe goma yace mun na kawo masa wani abun ya ɗan taɓa bakin sa na masa motsi, se na ɗakko fruit salad ɗin da na sakawa madarar gari da condensed gashi yayi sanyi gwanin daɗi na haɗo da ruwa.
Se da ya fara shan fruit salad ɗin kafin ya ce na kawo masa kilishi.
“Ai ko ɗazu na bawa su Inayah su kaiwa Anty Labiba na san ta da son kilishi” na bashi amsa, se naga ya dakata da abin da yakeyi ya wani kalle ni fuskar sa kamar da fushi yace
“Kilishin kika bayar? Da izinin wa? Wato ita gata sarkin son cin kilishi ni kuma da bansan daɗi ba shiyasa zaki ɗauke mun abu ki bayar na tare da nayi miki izini ba”.
Mamaki maganganun sa suka bani, kilishin da a gidan mu aka bani dan nayi kyautar sa shine ze fara tada jijiyar wuya yana faɗar maganganu akai? Kai tsaye nace masa
“Yanzu saboda na bawa ƙanwar Mamana abu shine kake wannan faɗan? Kuma fa kilishin nan naga daga gidan mu na taho dashi, nawa ne meye laifi idan nayi kyaitar sa ga wanda naso?”
“Ni kike faɗawa haka Halima? Ni kike yiwa gori akan kilishi?” Ya faɗa yana miƙewa tsaye.
Tsayen na miƙe nima ina cewa
“Karka canza mun magana ni ba gori na maka ba kawai na tunatar da kai ne kuma ba da wata manufa nayi magana ta ba”.
Ikon Allah, ƙaramar magana ta zama babba. Daga dai zancen kilishi kamar dai dama Bilal yana neman hanyar da ze tijara ni ne se gashi ya samu nan ya ringa fisaji yana rashin mutunchi da faɗar maganganu tamkar ba Bilal ɗina ba. Har yana cewa wai dama tun da muka yi aure ya lura na ke masa wani gani gani, duk abin da zan bashi se in bashi kaɗan, ko kuma idan ya ɗakko da kansa in ringa kallon sa wato taƙama ta daga gidan mu aka kawo shiyasa to daga yau baze sake cin komai daga abinda ya fito daga gidan mu ba balle na goranta masa, maganganu dai marasa daɗi marasa ma’ana ya zubar mun da fruit salad ɗin akan carpet yayi wucewar sa ɗaki yana ci gaba da tijara.
Kuka na zauna ina yi, ni banga abin laifi duk a cikin wannan abun ba, idan ma beji daɗin abin da nayi ba a zato na ai ba ta haka ya kamata ya nuna mun ba se muyi magana cikin lumana amma ya za’ayi ya fara faɗa har yana cewa baze sake cin abinda aka kawo daga gidan mu ba. Na zata daya shiga ɗakin ze fito ya lallashe ni tun da ya barni ina kuka amma har agogo ya buga ƙarfe sha biyu ina zaune ban sani ba, na share fuska ta na tashi a raina ina tuna nasihohin da Mama tayi mun akwai in da take cewa
“Karki kuskura kiyi kyauta da abun mijin ki ko da ƙwayar zarra ba tare da izinin sa ba, sata ce, har kuma be yafe miki ba Allah se ya kama ki” ‘Amma kuma wannan ai ni aka bawa’ na raya a zuciyata, ‘ko da yake tunda an kawo gidan ina ganin ya zamu namu kenan ni dashi’ wata zuciyar ta tunasar dani.
A hankali na tura ƙofar ɗakin da ya shiga, akan gado na hango shi yayi ɗai ɗai yana bacci abun sa, wani abu ya tsaya mun a rai. Wato ko a jikin sa bacci ma kwanta yana yi. Sabbin hawaye ne suka ɓalle mun, hakan nan na canza kaya na kwanta kusa dashi ina cigaba da ɗauke hawayen daya ƙi tsaya mun dan banyi zaton Bilal ze fara mun haka ba. Da asuba be tashe ni ba kamar yanda muka saba yayi ficewar sa masallaci daya dawo kuma ɗayan ɗakin ya shiga ya kwanta. Ban farka ba se kusan bakwai na safe saboda rashin kwantawa da wuri ga kuma ciwon kan da kuka da damuwar dana kwana dasu suka saka mun. Nayi mamakin ganin rana tarwai kuma babu Bilal a gefe na, haka dai na watsa ruwa nayi sallah bayan na gama addu’oi na na fita ganin baya falo se nayi tunanin to ko fita yayi?
Yan ayyukan da zanyi na fara na sake gyara falo na saka turare kafin na wuce kitchen na shiga fere doya. Har na gama haɗa abin karyawa be shigo ba, ɗaki na koma na ɗakko wayata na shiga kiran sa ga mamaki na se na jiyo ƙarar wayar daga ɗayan ɗaki na. Katsewa nayi na nufi ɗakin, na murɗa handle ɗin ƙofa naji shi a rufe da key, mamaki ya sake cika ni, a hankali na shiga ƙwanƙwasawa, nafi minti biyar a tsaye ina buga ƙofar amma ko motsi ban ji ba balle na saka ran ze buɗe mun.