Search
You have no alerts.
    The Den of Novels
    Chapter Index

    *MASU ƁUKATAR A TALLATA MUSU HAJOJINSU ZA SU IYA TUNTUƁARMU TA LAMBOBIN 07045308523 MUN GODE*
    Ban yarda da gaske Bilal yake da yace ze turo saka rana ba se ranar Juma’a da Baba Salahu yazo gidan mu bayan sun gama maganar da za suyi da Abba yasa aka kirani. Seda muka gaisa kafin cikin tsare gida kasancewar sa me ɗan zafi ya kalle ni yace
    “Ranar lahadi idan Allah ya kaimu iyayen yaron da yake neman ki suka ce zasu zo saka rana, ina fatan da sanin ki?”.
    Duk se na duburburce, abun yazo mun a ba zata domin banyi tsammanin faruwar hakan ba. Waccen ranar birkice masa nayi dagaske, duk yanda ya so ya lallaɓa ni naƙi biyuwa ƙarshe na kore shi nace karya sake zuwa in da nake tun da ba aure ya shirya yi ba na gaji. Haka ya tafi yana waige na kuma na kashe wayata, dukda se da nayi kuka tamkar raina ze fita zuciya ta ringa ingizani dana kira shi amma dake har raina na shirya motsawa in tabbatar da matsayina a gurin Bilal tilas na jure.

    Zuwan sa uku bayan nan bana fita na kuma yi blocking ɗin sa a wayar Mama tun da ya kira sau ɗaya, sati ɗaya kenan yau daidai se gashi Baba Salahun ya zo mun da labari mafi daɗi a kunnuwana.

    Sun kunyar da kai nayi ina murmushin dana kasa hana kai na, Abba dai kallo na kawai yake yana murmushin shi ma, seda Baba Salahu ya sake maimaita mun tambayar kafin cikin jin kunya nace
    “Eh, da amincewata Baba”.
    “To madalla, dama abinda nake so na tabbatar kenan da yardar ki kafin su zo saboda kin san ni bana ɗaukar shaƙiyanci irin naku na yaran yanzu. Se anyi magana ta manya daga baya kuzo da wasa shi yasa kafin manema su zo se na tabbatar da amincewar yarinya yan da zan ci ƙaniyar duk wadda ta dawo zata kawo mun iya shege. To Allah ya sanya alkhairi ciki yasa zamu ga lokaci”. A zuciya ta na amsa da “Amin” Abba ya amsa a fili daga nan ya sallame ni na fice. Tsabar murna ban san lokacin dana daka tsalle na rungume Mu’azzam da mu ka ci karo da shi ze shiga falon ba, ya ture ni yana cewa
    “Ke meye haka?”
    “Alhamdulillah Allah lokaci yayi na kusa zama matar Bilal” na faɗa cikin maɗaukakiyar murna kafin na zube a gurin nayi sujjadar godiya.

    Mu’azzam ya zabga tsaki yace
    “Se kace wadda zata auri wani Bilal ɗin farko, rabon shan wuya yasa kika kafe yarinya amma dai Allah ya bada sa’a”. Kan na amsa shi na jiyo Abba na cewa
    “Kai Ibrahim wace irin magana ce wannan?” Sena fake shi na zabga masa mari a ƙeya kafin na kwasa da gudu nayi ɗakin Mama ina cewa
    “Ɗan baƙin ciki se dai ya haɗiyi zuciya ya mutu”. Bama ga muciji da Mu’azzam kasancewar mu sakwanni ga kuma banbancin hallaya. Yana da zafi ji yake ma kamar shine sama dani ko dan ya kere ni a girma ni kuma gani da son girma ina so yanda yake ƙanina dole ya bini kamar yanda nake juya Imam da Amirah na uku data huɗun mu.

    Mama na zaune tana lazumi na faɗa jikinta ina ci gaba da ihun murna, se da ta ture ni kafin tace
    “Mene ne haka Halima?”
    “Mama ki tayani murna jibi Bilal ze turo a saka mana rana” seta saki baki kawai tana kallona ni da kaina na fahimci wauta da rashin kunyar da nayi se kuma na miƙe na fice daga ɗakin da sauri ina dariya ina jin ta tana cewa
    “Allah ya shirye ki Halimatu Allah ya shiga lamuranki”.

    Seda nayi rawa nayi juyi akan gado kafin na dire na ɗauki wayata, tun da na kashe ta ban sake bi ta kanta ba. Na kunna kafin ta gama booting ta kawo ji na ringayi kamar na damfarata da ƙasa ko zata fi sauri ina danna lambobin Bilal naji sallamar Hansa’u a falo se na fita da gudu, Mama da suke gaisawa ta kalle ni tace
    “Wai wace kalar rashin nutsuwa kika samu kuma Halima?”
    Baki na kamar gonar auduga na rungume Hansa’u Mama ta girgiza kai kawai ta shige kitchen ta barmu.
    “Albishirinki ƙawata” na faɗa ta amsa da goro, nayi fari da ido kafin na shaida mata jibi za a yi sa rana ta da Bilal. Tayi jumm da farko kafin kuma ta saki murmushin da na tabbatar be kai har ƙasan ranta ba tace
    “Na tayaki murna ƙawata, Allah ya tabbatar da alkhairi ya nuna mana lokaci”
    “Amin Hansy, amin” na faɗa ina sake laluben lambar Bilal. Muryar Abba da Baba Salahu da na jiyo suna fitowa daga can falon tasa na miƙe ina ce mata
    “Muje ɗaki”. Ta ringa kallo na kawai na kira Bilal, se da wayar ta kasu katsewa kafin ya amsa murya ba amo sosai.

    “Ba ni da lafiya Halims, kewarki zata hallaka ni” ya faɗa kamar irin wanda yake gargadar mutuwa bayan dana tambaye shi me ya faru naji muryarsa a ƙasa. Take hankali na ya tashi, na miƙe daga zaunen da nake ina cewa
    “Me ya same ka? Tun yaushe? Shine baka gaya mun ba?”
    “Ta ina zan same ki bayan kin kashe wayarki kin yi blocking ɗi na a wayar Mama sannan zuwana uku duk baki bari na ganki ba?, ni dai ki yafe mun kawai idan na mutu dan yan da nake ji kamar bazan tashi ba” ya sake faɗa yana sakin numfashi ban san lokacin dana fashe da kuka ina cewa

    “Haba dan Allah kar ka mun haka, kana ina yanzu? Kaje asibiti ko kana gida?”
    “Ina gida Halims bazan je asibiti ba tun da na fahimci rayuwa ta ki ke nema gara kawai na sauƙaƙa miki in bar miki duniyar se ki fi jin daɗi kamar yanda kika ce na fita daga rayuwar ki”. Ban tsaya sake jin abin da ze faɗa ba na kashe wayar na figi jaka ta dake kan gado nayi ƙofa, Hansa’u ta biyo ni tana tambaya ta lafiya amma ban tsaya ba na nufi get se kawai ta biyo ni. Se da muka hau adaidaita kafin cikin kukan da nake na gaya mata Bilal ne bashi da lafiya. Bata iya riƙe kanta ba ta zabga tsaki tace
    “Bilal bashi da lafiya Halima shine kika riki ce haka kina kuka?”
    “Ban gane na riki ce ba? In ce miki mijin da zan aura bashi da lafiya har ki tambayi ba a sin rikicewa ta ko kuka?” Na hayayyaƙo mata. Se ta sake yin tsaki tace
    “Wlh ƙarya yake, yanzun nan daga gidansu Maryam Abdullahi nake har gaisawa mukayi yana ƙofar gidansu suna hira da Abokanan sa”.

    Nayi mata banza ina ci gaba da share hawaye tun da ba son sa take ba ai dama komai ma daya shafe shi zata ce ƙarya ne. Ban ko tsaya karɓar canjin adaidaitan ba na wuce ƙofar ɗakin sa na shiga bubbugawa. Abubakar ƙaninsa ya fito daga cikin gida gani na yasa ya tsaya.
    “Yaya Bilal ɗin ne bashi da lafiya?” Ya tambayeni cikin mamaki bayan dana tambaye shi ina Bilal. Se na ciro wayata na shiga kiran layin sa, Nasiru ne ya amsa yace suna asibiti jikin nasa ne ya riki ce”
    “Subhanallahi, babu jimawa fa Yaya Nasirun ya kira shi duk muna tare a cikin gida bari na shiga na gayawa Hajja se nazo muje asibitin” Abubakar ya faɗa yana komawa cikin gida.

    Nasan kara kawai Hansa’u ta mun ta bini asibitin, na ringa rusa kuka ganin Bilal kwance da robar ƙarin ruwa a ido na se naga ya rame yayi baƙi Abubakar da Hajjansu nata jimamin to me ya same shi tun da su dai lafiya lau ya fita daga gida se Nasiru ne yace musu dama kwana biyu yana masa ƙorafin ciwon kai da ƙirji shine suna zaune suna hira wai kawai suma. A asibitin na wuni sur har sallar isha’i se da Abba suka zo tare da su Mu’azzam kafin na bishi muka tafi gida Hansa’u dama ko minti goma bata yi ba da mukaje tace mun zata wuce. A hanya Abba yake ce mun wai typhoid da malaria ne suka kwantar dashi lokaci ɗaya kamar yanda likitan daya tambaya ya faɗa masa. Nayi shiru a raina na raya ƙila basa so a faɗi ainihin abinda yake damunsa ne dan ni likitan ce mun yayi zuciyar sa ce ta kumbura, wai dama yana da matsalar zuciya amma duk tsayin zaman mu shine ya ɓoye bai taɓa gaya mun.

    Na share hawayen daya gangaro mun ta gefen ido na sanadin tunanin wai Bilal na da matsalar zuciya da nayi. In da na sani ina zan masa boren da nayi waccen ranar har in share sati ba tare da na amsa wayar sa ko na bari mun haɗu ba. Ko kallon in da nake Mama bata yi ba da muka koma gidan, ban iya bacci da kyau ba cikin dare duk motsi na hankali na yana kan Bilal ga wayarsa dama tun ina can Nasiru ya kashe a dafe na kai safiya tun farar asuba kuwa na shiga kitchen na fara haɗa masa kunun gyaɗa da alala na haɗa masa da farfesun kayan ciki. Saboda kar Mama tayi faɗa na duka gida nayi kan bakwai na gama na shirya wanda zan kai masa na ware na gida sannan na wuce wanka a gurguje. Ina fitowa naji Mama na faɗa
    “Saboda jiya ban ce mata komai ba shine yau zata ɗibar mun kaya tayi girki ba tare da ta sanar mun ba to babu in da za’a kai abuncin nan” na jiyo tana faɗa. Nayi saurin zura doguwar riga ba tare da na shafa komai a jiki na ba na saka hijabi na fita. Daga ne sa na gaishe ta ta galla mun harara tana cewa
    “Wato bakya jin magana ko Halima?”

    “Yanzu Amina ba zan ce magana ta wuce ki barta haka ba se kin sake tadawa?” Abba ya katse ta, se ta juya kansa tace
    “Dama ai kai baka ganin rashin dacewar duk abinda takeyi a gidan nan. Yanzu mutunchi ne ace ta tafi ta tare a asibiti tun hantsi ina ga da baku je ba ma a can tayi niyyar ta kwana ko? Sannan yanzu kaga uban abincin da tayi zata kai musu kan ta aka fara soyayya ko kuwa da zata ringa abu kamar mara cikakken saiti. Badai namiji bane, ka bishi a sannu ma ya ka ƙare balle ka nuna masa ba zaka rayu idan babu shi ba”

    “Ni da kika nuna mun ba zaki rayu idan babu ni ba nayi miki butulci ne Amina da har zaki fara kafa hujja da halin Maza?” Abba ya faɗa, tuni na sulale nayi kitchen jin maganar na neman canza salo. Na bi ta ƙofar baya na fice ina zagayowa muka ci karo da Mama ta kuwa falla mun marin da da wayo na bazan iya tuna sanda ta dake ni ba.

    “Har idan na isa dake Halima umarni nake miki ba shawara ba ki fita daga sabgar yaron nan, ban yarda ba kuma ban amince da cigaban tarayyarki dashi ba” Mama ta faɗa cikin fushin da ban san tana da shi ba. Hankalina ya tashi matuƙa, na aje kwandon hannuna na fashe da kuka ina cewa
    “Mama me yasa zaki ce haka me Bilal yayi miki?”
    “Ba abin da ya mun amma ina kallo bazan bari ki tura kanki a rami ba. In sha Allahu idan ma da ƙulumboto ya nemi soyayyar ki zan ci gaba da kaiwa Allah kuka na ya warware komai ya raba ki dashi. Na gaji, wannan wane irin bala’i ne? Bilal se kace na billahillazi bakya ji bakya gani akansa? To ba dani ba ko kina so ko bakya so dole ki barshi tun da ba hauka akeyi ba”.

    Kuka na fasa harda kururuwa Abba ya fito cikin ɓacin rai yace
    “Baki ji ba kenan?”
    Ta wuce ciki ba tare da ta amsa masa ba tana jaddada mun wallahi na fita se na sha mamakinta yau.
    “Dan Allah Abba ka bata haƙuri na faɗa ina kama ƙafarsa, seya ɗago ni yana cewa
    “Ya isa, ki koma ciki tunda tace karki fita bari na taso Ibrahim se yaje ya kai musu abincin”. Yanda kasan wadda aka wa mutuwa haka na shiga ɗaki na ringa kuka akan hanani komawa dubo masoyi na da akayi. Wuni sur ban fito daga ɗaki ba ko abinci ban iya kaiwa baki na ba seda mukayi waya da Bilal ya gaya mun an sallame shi se lokacin na tsagaitawa kaina har na fita na nemi shayi na sha.

    “Ba wasa nakeyi ba bana son auren nan Alhaji kwata kwata abin yaƙi kwanta mun a rai. Wlh ba ƙaramar murna nayi ba da ya ɗauke ƙafarsa ya dena zuwa itama naga ta fita a batunsa, ni da ka sani da suka ce zasu zo kawai ku ce musu an mata miji tun da dama tun asali ai ba kuɗi suka kawo ba magana kawai akayi” Hajiya Amina ta faɗa bayan da suka zauna da Alhaji Aminu yayi mata magana akan rashin dacewar abin da tayi a ganinsa.

    “Me yasa zaki ringa faɗar haka Amina? Ban taɓa zaton zaki shiga layin waɗanda basa son haɗi tsakanin Halima da yaron nan Bilal ba. A duk sanda na kalle su rayuwarsu ta kan tuna mun a yanda muka fara tamu tarayyar” se tayi saurin katse shi tace
    “Karka fara haɗa rayuwar mu da tasu domin akwai banbanci”
    “Wane banbanci? Irin son da kika nuna mun? Wace irin sadaukarwa ce baki mun ba Amina? A sanda na nemi auren ki ban ko kama ƙafar Bilal rufin asiri ba. Bana manta ƙanin da yan gidanku suka mun me riga ɗaya. Kin ciyar dani, kin tufatar dani kin kuma zauna dani cikin halin matsi har muka kawo yau menene banbanci cikin abinda yake faruwa a rayuwar Halima yanzu?” Alhaji Aminu ya faɗa cikin kwantar da murya.

    Hawayen da suka tarar mata a ido ne suka fara sauka, ta saka gefen hijabinta ta share tana cewa
    “Ko da na so ka na so ka ne a matsayin ka na Aminu kai ma ka so ni a Amina. Babu son rai ko so. zuciya a tarayyar mu. Baka dashi amma kowa ya shaida kai me zuciya ne kuma kana kan tafarkin nema. Baka taɓa roƙo na nayi maka abu ba kuma na sani a duk sanda na maka abu kana karɓa ne saboda ka faranta mun kuma a duk sanda Allah ya baka dama ka kan kwatanta kyautata mun kaina daidai yanda zaka iya. Mahaifi na ya faɗa mun ya baka aure na saboda ya yarda da kai ya kuma yarda da nagartarka ya kuma san akwai da babu ba zaka wulaƙanta masa ni ba saboda ya yarda tsakani da Allah kake so na. Wace madogara kake da ita da har ka yarda zaka bawa wancan yaron auren yarka?

    Ban ce baya son ta ba amma son da take yi masa ya kere wanda yake mata nesa ba kusa ba, kai namiji ne. Be zama lallai ka hango illar dake tattare da irin wannan tarayyar ba. Bance a duk in da son mace yafi yawa yana kasan cewa matsala ba amma muna amfani da abinda yafi faruwa musamman a irin al’umar da muke ciki yanzu. Yanzu ka kalli abubuwan da Halima takeyi, akan Bilal bata ji bata gani ba kuma ta shakkar ɓatawa da kowa. Har ta kai yanzu bata shakkar ɓacin rai na akan duk abinda ze faranta ran Bilal. Tun be aure ta ba take haka ina ga kuma sun zauna me kake tunanin zata zama? Ni dai gaskiya ina jiye mata tsoro domin zuciyata ta kasa nutsuwa akan al’amarin nan mafi sauƙi a haƙura mu cigaba dayi mata addu’a Allah ya fito mata da wanda ya fishi alkhairi”.

    Shiru Alhaji Aminu yayi kawai, sam ya kasa ganin abinda take kira da matsala cikin al’amarin Halima da Bilal. A iya binciken sa ba’a samu yaron da wani halin banza ko shashanci ba. An san asalinsa, yana da sana’a ga yarinya tana son sa to me ake nema? Sau tari shi ma ya kanga kamar Haliman ta zurma da yawa amma yanayin ta ne a haka tun tana yar yarinya ta kan tsananta son abu, ko cikin kayan wasan ta ta kan tattala tare da kulawa da wanda ta fi so bata taɓa fitar dashi idan suna wasa ta sa’anninta shiyasa yakan mata uzuri akan abubuwa da yawa nata haryar kenan ta bayyar da soyayya. Cikin nutsuwa ya ringa kwantarwa da matar tasa da hankali tare da nunar mata da babu komai. Kamar yanda yasan tana wa yaranta addu’a karta gaza, taci gaba da yiwa Halima in sha Allahu duk ma hasashen da wasu sukeyi baze yi tasiri ba.

    “Yanzu haka nan da wace hujja zamu ce zamu hana shi aurenta? Go be fa suka ce zasu zo saka rana naga da ƙorafin ki ya tsaya wasa ba aure zeyi ba yanzu kuma ya yunƙuro se ki zo da wata magana daban Amina ban fa san ki da haka ba na kuma san ba kowa yake zugeki ba illah Labiba kuma zan kirata. Ita dai tunda Halima taƙi ƙanin Alhaji Saleh shikenan ta tsangwami zancen auren ta Bilal” Abban ya faɗa. Seta girgiza kai tace

    “Babu ruwan Labiba wlh, kuma ko da taƙi al’amarin tana da hujjoji da ababen dubawa ne ai kuma son da takewa Halima yasa har take adawa da abinda take ganin ze iya zaka matsala a rayuwarta dan dai ka sani ko ni da na haifi Halima dan dai soyayyar uwa da abin cikin ta daban ce amma bazan ce nafi Labiba ƙaunar Halima a zahiri ba” Mama ta faɗa. Se yayi murmushi yace
    “Bana in kari da ƙaunar dake tsakanin Labiba da Halima wani haɗi ne daga ubangiji wannan na kuma san duk abinda zatayi akanta zatayi ne don ganin rayuwarta ta in ganta. Ƙaramar uwa da yarta, ai babu me shiga tsakaninsu dan idan aka juyo ta wani fannin muna nan za ta iya baki kunya kuma ta juya tabi bayan yarta. Ni dai abin da zan ci gaba da faɗa miki shine ki ci gaba da yi mata addu’a kawai in sha Allahu e mun ce gara da akayi ba kuma zamuyi nadamar wannan tarayyar ba” da maganganun daya danneta kenan harta sakko tabi ta tasa taci gaba da addu’ar da dama kullum cikinta take.

    A daren ta kira Anty Labiba ta gaya mata zancen zuwa sa ranar a take kuma tace a cireta ciki bata cike da iskancin Bilal da Halima. Tun dai taji ta gani ai shikenan mai Allah ya tabbatar da alkhairi. Dariya kawai Maman tayi ta kira Yayarta Hajiya Rumana kawai tace zata yiwa Matar Yayansu Lawan Anty Laure magana tun da taga ta fara harkar snacks na biki, duk da ba’a gidan zasu zo saka ranar ba amma zatayi abin tukuici akai can gidan Baba Salahun.

    Washe gari lahadi ƙarfe huɗu na rana Kawunnan Bilal biyu da Aminin mahaifinsa ɗaya suka je saka ranar auren mu gidan Baba Salahu. Kusan a kowanne ɓangare ana al’ada, wasu su kan yi tsohuwar da aka saba akai akwati da kayan sa rana. Wanda suka zamanantar da abun kuma kuɗi suke badawa waɗan su kuma a sanda aka kai kuɗin aure ake haɗawa da na sa ranar ko kuma a haɗo kayan tare da lefe to su dai su Bilal bamu san wanne zasuyi a ciki ba, dama sanda akayi tambaya basu bada komai ba Abba yace baya buƙatar wani kuɗin na gani ina so ko na aure yanzun ma haka nan suka zo da saka rana shekara ɗaya se dai Baba Salahu yayi tsallen albarka yace basu san zance ba.

    Watanni shida shine abin da suka yanke zasu aurar da yar su, bayan duk dogon zaman jiran sa da aka sha har idan suna ganin hakan ya musu gajarta to fa suyi haƙuri kawai domin a cikin dangi akwai wanda dama suka ci burin haɗa ta dashi. Aminin mahaifin Bilal ne yace ba za’a yi haka kuma tabbas kam iya lokaci an basu domin be manta ba an tafi shekara ta uku kenan da sukayi tambayar auren kuma shi kansa be san ranar har ta shekara suka shiryo ba da tun kan su zo dama ze gaya musu yayi yawa musamman dama ga bikin ƙanwar Bilal ɗin da za’a yi duk lissafin sa tare zasu haɗe. Haka dai aka rabu, duk sauƙin kai da rashin ɗaukar duniya da zafi irin na Baba Salahun bayan sun tafi se da ya kira Abba yayi masa mitar mutanen fa ko goro basu zo dashi ba balle wani abu na al’ada. Abban yace babu komai.

    Irin murnar dana shiga bayan da na samu labarin a watanni shida masu zuwa zan zama mallakin Bilal ba me faɗuwa bace. Har party na haɗa, cikin sa’a washe garin ranar tayi daidai da ranar zagayowar haihuwata dama dan haka na roƙi Mama da muke hi hi yanzu akan zanje gidan Anty Labiba. Bata hanani ba, dama na gayawa Hansa’u da su Baby zamu je gidan zoo ranar birthday na Baby na bawa kuɗi ta yi mana kayan taɓawa na siyi cake da a jiki aka rubuta mun Happy engagement Mrs Bilal to be ban sanar ma Bilal ɗin bama se da na samu na bar gida haka ko suka je shi da abokanansa biyu muka sha hotuna muka ci snacks muka yanka cake bamu ji ma ba na wuce gidan Anty Labiba dan kar zance ya tashi tace ban je ba. Na dai sha zagi a gunta amma ban damu ba, tace kayan gado yan goron dutse zasu mun duk tarin da Mama takeyi a saboda aure na ba zata bari ta ɓarna tar da kuɗin ta ba har kayan kitchen da take siya da wanda itama ta siya mun Amirah zasu ajiyewa nace duk naji.

    Shikenan rayuwa ta dawo mun sabuwa, soyayya da shaƙuwar mu da Bilal se abin da ya sake gaba. Na samu ƙatuwar takadda na zana calender ta wata shida kullum da safe na tashi zan soke ranar ki nake yi tamkar na janyo lokaci ni dai buri na da fata na kawai na zama matar Bilal.

    Wata Juma’a sati biyu kenan da yin sa ranar mu watanni biyar da sati biyu kuma a cikin kwanakin da suka rage ma aurena da Bilal kamar ko yaushe munyi waya yace mun ze zo gurin ƙarfe biyu kuma se ya kirani yace na faɗawa Mama idan ya zo ɗin zamu ɗan je wata unguwa. Na ringa juya maganar, ba sabon abu bane fitar mu taren amma tun bayan da akayi sa ranar mu Mama ta zaunar dani tana mun faɗa da wasu maganganu in rage rawar kai karna kuskura ganin an saka mana rana da Bilal na ɗauki halin da bani dashi a da. Ko zuwa yayi yanzu se tace mu zauna a falonta muyi hira ko a compound a maimakon falon Abba da muka saba zama kamar kuma kaɗan take jira dani abu ƙarami zanyi ta fara mun faɗa shi yasa duk na rasa ta yanda zan ce mata zamu fita tare.

    Ina tsaka da tunanin Amirah dake gidan Anty Labiba taje hutu tayi sallama, naji daɗin zuwan nata sosai, tare suke da Inaya da Amir wai Babansu Amir ɗin ne ya kawo su. Seda na fita na gaishe shi yana ta tsokanata wai amarya bayan ya tafi na cewa Mama zanje gidansu Hansa’u in karɓo atamfar ankon Baby an kawo mana tana can daga nan zamu kai ɗinki. Da Inayah muka tafi Amirah tace ba zata raka ni ba, seda nawa Bilal text na gaya masa ina gidansu Hansa’u cikin sa’a bata nan wai ta tafi wankin kai bayan tare mukayi zamuje shine bata kira ni ba. Zama nayi muka ɗan yi hira da Ummansu kafin muka tafi bayan da Bilal ya kirani akan yazo.

    *MASU ƁUKATAR A TALLATA MUSU HAJOJINSU ZA SU IYA TUNTUƁARMU TA LAMBOBIN 07045308523 MUN GODE*

    Note
    error: Content is protected !!