Kura a Rumbu – Chapter Forty-six
by Maryam Farouk (Ummu Maheer)"Kar kice haka mana Halima. Ke da na san ki jaruma shine zaki bari daga sama wata ta zo ta ƙwace miki miji kuma ki sakar mata? Haba mana dan Allah karki bani kunya.
Na san abinda ya aikata miki dole kiji zafi ba ke ba hatta Hajja dake goyon bayansa a ko da yaushe a wannan karon tana adawa da auren nan dan wlh ba dan mun tausheta ba rantsuwa tayi akan sai ya saki yarinyar ba zata tare ba. Mu muka yi ta bata haƙuri saboda a ganina bai kamata ace a gyara ɓarna da ɓarna ba. . .