Kura a Rumbu – Chapter Forty-five
by Maryam Farouk (Ummu Maheer)ALHAMDULILLAH Mun gama biki lafiya nagode da fatan Alkhairi.
"Dan girman Allah Anty Amina kiyi mun wannan alfarmar, wlh nayi duk dabarata amma taƙi saurarona, idan naje gidan bata fitowa haka idan na kira wayarta bata amsawa. Ɗazu da safe suka zo ba dan na kulle gidan ta ciki ba ma da tuni sun kwashe kaya.
Ke shaida ce ina son Halima duk abinda kuma ya faru sharrin shaiɗan ne da kuma Hajja amma wlh ba a son raina bane" ya faɗa bayan da ya tsayar da Anty Amina a ƙofar gida.
Kallonsa ta ringayi har ya. . .