Kura a Rumbu – Chapter Forty
by Maryam Farouk (Ummu Maheer)Tunda yaga babur ɗin Kawu Sani a ƙofar gidan gabansa ya shiga faɗuwa domin ya san abinda akw ɓoyewa ya rigada ya bayyana. Sai dai kuma shima yana buƙatar hakan ko dan ya samu a wuce gurin Zulaiha ta tare amma kuma ya san da wahala su kwasheta da daɗi da Hajja. Tun daga tsakar gida yake jiyo maganganun Hajjan tamkar zata ari baki tsabar masifar da take zazzagawa, yana ɗaga labule suka haɗa ido kallon data jefa masa sai da yaji yan cikin sa sun juya, ta ce
"Yawwa gara da kazo, dama Bilal idan. . .