Kura a Rumbu – Chapter Fifty-six
by Maryam Farouk (Ummu Maheer)Kwana uku Jalilah tayi a Kano ta wuce Abuja bayan ta bar alhakin sauke kayan da suka fara isowa a hannun Bilal. A tsakanin kwanakin har rama yayi; duk wanda ya sanshi kallo ɗaya zakayi masa ka fahimci yana cikin damuwa matuƙa, duk in da yake tunani zai buga lissafi ya fita abu ya gagara, idan ya haɗo nan sai can ya rushe ga Alhaji Lawan ya taso shi a gaba da zancen kuɗinsa dan tuni ya kwashe kayansa ya bar gidan kamar yanda ya ce har Ahlan mamallakin gida na asali ya saka an sake gyara. . .