Kura a Rumbu – Chapter Fifty-one
by Maryam Farouk (Ummu Maheer)Ranar Alhamis suka je jere ko ya ce ganin gida tunda dai shi yayi jere, yan buhun hunan da suka je da abinda suka kira kayan kitchen tsabar takaici kallo ɗaya ya musu ko gaisuwa mai kyau basuyi ba ya fita ya barsu da yayyensa banda Anty Amina da sukaje tarar masu jere. Bai san munafukin daya gayawa Hajja shi ya siya mata kayan ɗaki ba ai kuwa ya sha tijara wannan kuma ya sake ruguza ɗan shirin da suka farayi ta kuma ja masa kunne akan ba fa zata saɓu ba, ita da wahalar haihuwa da raino can. . .