Kura a Rumbu – Chapter Fifty-nine
by Maryam Farouk (Ummu Maheer)Sai dana tabbatar ya fice daga building ɗin gaba ɗaya kafin na fita daga office ɗin ina kalle-kalle kamar mara gaskiya, ganin babu kowa ya saka na shige Elevator da sauri, a reception na haɗu da Juwairiyya ta kalleni fuska ba yabo ba fallasa kafin tace
"Ina kika tafi tun ɗazu?"
Wucewa nayi ba tareda na bata amsa ba ta sake cewa
"Dr Sulaiman yana neman ki?" Na amsa da "Toh" ba tareda na tsaya ba na fita.
A can kan hanya ya tarar dani, fuska ba annuri ya sauke glass yana kallona kafin ya ce
"Get in. . .