Kura a Rumbu – Chapter Fifty-eight
by Maryam Farouk (Ummu Maheer)HALIMA
Cike da haushin Dr Salman na koma gida ranar Juma'ar, haka nan ya san banda mu zasuyi meeting ɗin amma ba'a gaya mana ba saida muka rigada muka je tukunna sannan babu damar tafiya haka mukayi zaman banza har sha biyu kafin muka tashi. Dama-dama da na ji na samu nayi clearance ɗina kafin na wuce gida.
Bayan sallahr magriba Anty Labiba tace mu shirya muje gidan Uncle Mudassir yaronsa na biyu Khalil ya faɗi ɗazu da safe ya samu karaya, muna shirin fita Mama ta kirata tana tambayarta yaushe zamuje duba Khalil ɗin tace. . .