Kura a Rumbu – Chapter Eleven
by Maryam Farouk (Ummu Maheer)Daƙyar na koma cikin falo na zauna ina jin kaina yana saramun. Me yasa Bilal yake haka? Kullum ace abinci ne ze ringa haɗa mu rigima?
Ina nan zaune ya fito daga ɗaki yanayin shigar sa na gane nisa ze yi. Ko kallo na be yi ba ya fice sabbin hawaye suka ɓalle mu. Zuciya ta tana raya mun na barshi naga iya gudun ruwan sa amma gangar jiki na taƙi bani haɗin kai, bazan ce ga sanda na miƙe na bi bayan sa ina kiran sunan sa ba amma ko a jikin sa ya. . .