Farar Huta 2 – Chapter Two
by Nadmin*Shekaru Goma da suka wuce.*
Lokacin sanyi ne, hazo ya lulluɓe garin ruf ta yadda ba zaka ce safiya ce a sannan ba, don hatta motoci da fitilu a kunne suke yawo koina, na ƙasa kuwa baya ganin abinda ke gaba ko yaya tazararsa dashi take.
A cikin motar dake tafiya kan titin expressway na barin gari, Ma’aruf ya zare earpice ɗin dake kunnensa ya sake shi a jikinsa sannan ya juya ya kalli Jamal dake tuƙin motar.
“Let me drive dan Allah.”
Jamal ya girgiza kansa.
“Kaima ka san there’s no way da zan baka motar nan, yaushe kayi ƙwarewar da zaka hau babbar hanya?”
“Kusan shekara daya fa kenan Yaya dana fara koyon tuƙin nan, ko wace irin ƙwaƙwalwa ce dani ai ya isa na iya haka.”
“Da da Muhammad muka zo sai ka gaya masa hakan, amma ni na sanka Ma’aruf babu abinda yake gabanka banda karatun likitan nan, shi yasa kaƙi barin kanka ka koyi komai, ba don wannan babar taka ma ta dage ba ai da yanzu baka ma fara koya ba, something so shameful!”
Ma’aruf yayi dariya yana ɗauke wayarsa daga tsakanin cinyarsa kafin yace.
“Na sha gaya maka makarantar ne ba ƙaramin tsauri ne dasu ba, ƙanwar Havard fa ake ce mata, ba kowa suke ɗauka ba and in my own case da nake baƙar fata dole in dage inyi karatu, babu ruwansu da komai sai abinda ka iya.”
Wani mai mota yazo yasha gabansu a lokacin, Jamal ya kalle shi cikin takaici yana girgiza kai kafin yace.
“Kai kuma ka dage dole sai nan, Universities nawa zaka je ka zama likitan ƙwarai Ma’aruf.”
Ma’aruf yayi dariya yana kallon gefen hanya ta cikin gilashin motar dake ɗaukar ido saboda sabunta, don kwanakin motar biyu kawai da siya bayan Baffa ya gama yi wa Jamal din tsiya akan ya canja tsohuwar motarsa, sai gashi da ya tashi yaje ya siyo wadda tasa kowa gyada kai cikin mamaki.
“Wai likitan ƙwarai, you are too much Yaya, sannan dan Allah sunanta Mami, ba ‘babarka’ ba.”
Jamal ya cije leɓɓensa a wannan lokacin yana kallon gabansa a lokacin da suka gota wani ƙauye suka fara barin gari, yayin da shiru ya ratsa motar kamar yadda hakan ke faruwa a duk lokacin da Ma’aruf ya ƙalubalanci wani abu da Jamal ɗin zai faɗa akan Hajiya Kilishi.
Ba tun yau ba ya sani babu jituwa tsakanin yayan nasa da matar da yake mata kallon mahaifiya akan wani dalili da bai sanshi, don da ace tun daga farko yabi ta Hajiya kilishin ma, baza a taɓa samun shaƙuwa irin haka tsakaninsa da Jamal ba, sai dai soyayyar ƴan uwantakan dake tsakaninsu tafi karfin mizanin yadda yake jin matsayin Mamin a ziciyarsa.
“B… Haka suke maka a makaranta ko?”
Muryar Jamal ta katse shirun motar kamar yadda koyaushe ya saba daidaita al’amura a tsakaninsu. Sai ya juyo da murmushi ya kalle shi.
“Kai a duka friend’s ɗinka ba wanda yake kiranka da Bakori?”
Jamal ya girgiza kansa.
“Man, ni sunana mai daɗi ne babu wanda yake jingina min sunan wani ƙauye.”
Ma’aruf yayi dariya yana sake maida kansa baya, kafin Jamal din ya sake magana.
“Ka gaya min bayan zama likita mai kake son kayi a rayuwarka?”
Ma’aruf bai taso da kansa ba, idanunsa na kallon rufin motar ya cije leɓɓensa alamun tunani, sai kuma ya girgiza kansa yace
“I don’t know, let me just start figuring out that tukunna. (Ban sani ba, bari na dai fara gamawa da hakan tukunna.)”
Jamal ya gyada kansa har yanzu idonsa na manne da titin kafin yace.
“Ina so ka sani Ma’aruf ba kowa zaka dinga yarda dashi a duniyar ba, wani lokacin mutanen dake kusa da kai suna iya zamewa abinda makiyanka, ba a kowacce fuska mai murmushi ake samun so ba, ba a kowanne ido mai kyalli ƙauna take ba, wani zai maka murmushi Ma’aruf amma wuƙa yake caka maka baka sani ba, kuma ba lallai ka gane ba sai a lokacin da komai ya ƙure, ka san irin takun da zaka yi tare kowa. Kar ka tambaye ni me yasa nake gaya maka haka, kawai naji ina so ka sani ne don watakila zai amfane ka a gaba.”
Sai a yanzu Ma’aruf ya sauko da kansa daga kallon saman motar, ya kalle shi sannan ya gyaɗa kansa.
“Its a good advice, (shawara ce mai kyau.) Nagode sosai.”
Shima ya juyo ya kalle shi, wani irin kallo da Ma’aruf yaji kamar yana ratsawa har cikin ruhinsa, kamar bai gama gaya masa komsi ba, kamar akwai sauran wasu bayanan da bai gama kwancewa a cikin kalamansa ba, amma sai kawai shima ya gyaɗa nasa kan sannan ya juya ba tare da yace komai ba. Yawu ya zarce cikin maƙogwaronsa kafin ya juya shima ya kalli titin dake bangarensa.
“So are you letting me drive?” (Zaka bani tuƙin?)
Jamal ya girgiza kansa.
“Idan ka kashe mu fa?”
Ma’aruf yayi murmushi ya na cije gefen leɓɓensa.
“Shikenan, sai aje a gayawa su Baffa munyi hatsari mun mutu gabaɗaya. The end.”
A yanzu shima da nasa murmushin Jamal yace.
“Idan kuma ni na mutu kai ka rayu fa?”
Tambayar ta doka wata irin fargaba a ilahirin a jikin Ma’aruf lokaci guda, amma sai yayi kokarin kore ta da sauri ta hanyar yin wani murmushin kafin yace.
“Sai in ajiye dukkan burin rayuwata a gefe in karbi matsayinka, inyi irin rayuwarka ta yadda kowa zai ga cewa Ma’aruf ne ya mutu ba Jamal ba.”
“Har da ambition ɗinka na zama likita?”
Ma’aruf yana jin wani iri a ƙirjinsa yace.
“Har dashi, ai ba zan iya rayuwa da wannan nauyin ba, komawa zanyi kamar kai in kashe wannan Ma’aruf ɗin don bashi da amfani idan har babu kai.”
“The man behind the shadows!”
Jamal ya fadi sunan wani film da yayi shige da abinda Ma’aruf din ya faɗa, film ɗin da a tare suka ganshi a cikin jirgi lokacin da Ma’aruf ɗin zai raka shi Cairo karɓo wasu takardunsa na makaranta, kuma tuno film ɗin yasa su yin dariya a lokaci guda kuma a tare.
“Naga wasu sababbin kaya a cikin leda a ɗakin ka jiya, a ina ka siyo? Na daɗe ina neman irin Hoodie ɗin nan.”
Ma’aruf ya ɗan tsaya alamun tunani kafin ya iya tuno kayan.
“Ohh! Ruƙayya ce ta kawo min, ban san inda ta siyo ba amma dai zan tambaye ta.”
Jamal ya sake shafo gashin kansa, wani abu da yake ɗabi’a kuma halayyarsa da kowa ya sanshi da ita.
“Yarinyar nan tana yawon kawo maka kyauta Ma’aruf.”
“Na sani,.” Itace kawai amsar da ta fito daga bakin Ma’aruf ɗin bayan ya juya yana kallon titi.
“Ka san me? Ka san tana sonka?”
Ba shiri Ma’aruf ya juyo yana kallonsa.
“Yarinyar ƴar secondary Yaya? Ni kuma da nake shirin fara karatu a yanzu mai zai kawo wannan zancen? And the last time I checked kaine mai bani shawara cewa kar inyi saurari mata a yanzu.”
Ya rufe bakinsa daidai lokacin da Jamal ya gama rage gudun motar ya sauka zuwa gefen titin a hankali sannan ya juyo shima ya kalle shi.
“Do you still wanna drive? (Har yanzu kana son kayi tuƙin?)”
Kuma murmushin da Ma’aruf ɗin yayi shi ya tsaya a matsayin amsarsa ya kuma kashe maganar Ruƙayyan da suka fara.
“Kuma kar ka kashe ni!”
Shine kalma ta ƙarshe da Jamal ya faɗa kafin ya buɗa ƙofar motar ya fita, shima Ma’aruf ya buɗe tasa ya zagayo don su canja mazauni, dukkaninsu suna dariya.
Minti goma bayan hakan, motar tayi katantanwa akan titi ta nufi cikin daji!
****
*Present Day.*
*Bakori Enterprises*
*10:05 am*
“Well since everyone is here, let’s get started.”
( Tunda kowa ya hallara, mu fara kawai.)
Ma’aruf ya faɗa a lokacin da mutum na ƙarshe ya zauna a zagaye teburin cikin Office din, kuma yana rufe bakinsa Daniel ya mike tsaye, Ya tafi gaba yayi connecting flash dinsa a lokaci guda da bayanan cikin slide dinsa suka nuna tar akan farin screen din wajen.
Ma’aruf yayi baya a kujerarsa yana saurarensa kamar yadda sauran mutane goma sha ukun dake zaune a round table din suka yi suma.
Meeting ɗin kamar kowanne ne da suka saba yi, bayani Daniel din din yake yi akan Growth and Development din kamfanin da suka fara cicciɓowa a ƴan watannin nan, kowacce kalma da Daniel ɗin ke fada da kuma diagrams din da yake nunawa daga slide din abubuwa ne dake faranta zuciyarsa suna sawa yana jin kamar ƙwaƙwalwar sa na daɗa washewa ne daga matsalolinsa, don tabbas daga bayanin da kuma yadda komai ke yin sama kowa a wajen ya san cewa sun yi mutuƙar kokari, mutukar kokarin da tun a yanzu a cikin kansa yake jin addu’o’in da Baffa zai yi masa a lokacin da ya kai masa report ɗin.
Yana zaune kyam yana cigaba da sauraren komai kamar wannan shine lokaci na farko da yaje jin bayanan, don baya son ko kalma guda ta wuce shi, baya ko kifta idanu yayin da hasken slide ɗin ke nunawa a fuskarsa, daga gefensa Faruk ne ke nasa danne-dannen a computer yana kokarin hada nasa presentation din da zai yi akan Compensation and Benefits. Ayyukan da suka riƙe shi tun jiya su suka sa bai kammala ba har yanzu, Allah ya sani yana ganin kokarinsa, don Faruk mutum ne mai himma da hazaka, don da babu irinsa a kusa dashi ya sani cewa dole ne labarinsa zai canja.
Tafin da Office ɗin ya karaɗe dashi a lokaci guda ya shaida karshen bayanin Daniel, idonsa na tsaye akan percentage ɗin da Daniel ya nuna na karshe akan screen din yayin da murmushi ya subuce a nasa lebben ba shima kamar sauran mutanen, don sun wuce kuma sun kere adadin nambobin waccan karon da suka zauna meeting.
“… Lastly I will like us to give this credit to our Diligent Manager Mr. Ma’aruf Mansoor Bakori, because without him, we wouldn’t be where we are today.”
(Daga karshe ina son mu mika jinjina komai ga hazikin shugabanmu, Mr. Ma’aruf Mansoor Bakori, don ba don shi ba, ba zamu ƙaraso wannan gaɓar a yau ba.)
A lokacin ne kowa ya juyo yana kallonsa yayin da sautin wani tafin ya sake karadewa, hatta Faruk sai da ya tsaya da aikin da yake yi shima ya shiga tafin tare da kifta masa ido.
Sai kawai ya mike tsaye yana sunkuyar da kansa alamun godiya, kuma a wannan lokacin ne kalamansa tare da na Jamal suka haska a cikin kansa.
_Idan kuma ni na mutu kai ka rayu fa?_
_Sai in ajiye dukkan burin rayuwata a gefe in karbi matsayinka, inyi irin rayuwarka ta yadda kowa zai ga cewa Ma’aruf ne ya mutu ba Jamal ba!_
This is you Yaya! (Kaine wannan Yaya!)
A hankali ya furta abinda yake fada a duk lokacin da ya zama sanadin samar da wata nasara a Kamfanin.
***
“Ka san ƙoƙarin da muka yi da mutanen RTL ɗin nan shine babban abinda ya sake ɗago da percentage dinmu.”
Faruk ya faɗa bayan kammala meeting ɗin suna zaune a cikin office dinsa. Faruk ɗin ne zaune akan kujerar Ma’aruf ɗin yana neman abu a cikin desktop din kan teburin yayin da Ma’aruf din ke zaune daga tsakiyar office din inda aka zagaya da wasu cushion chairs guda hudu da kuma tebur a tsakiyarsu, waya ce kare a kunnensa kuma da lama dukkan abinda yake saurare daga cikin wayar mai muhimmanci ne.
Kuma jin shirun da yayi bai amsa ba yasa Faruk matso da kujerarsa zuwa karshem teburin yana barin inda screen din ƙatuwar desktop din da ta kare fuskarsa. Kuma yanayin fuskarsa kadai ya gani ya san tare da wa yake wayar.
“Ka tabbata sunan da ya gaya maka kenan?”
Ma’aruf din ya tambaya fuskarsa babu wannan annurin da ya cika ta a ƴan mintuna kadan da suka wuce wajen meeting din nan.
Aka sake wani bayanin a cikin wayar da yasa shi cije leɓɓensa sannan yace.
“Ku cigaba da rike shi kawai, zuwa gobe zamu yi waya.”
Daga wannan maganar, Faruk ya riga ya san wa yake nufi ya kuma san ina zancen ya dosa, don shi yayi nasarar gano address din accountat din wadannan kamfanin da a baya suka gano cewar ta daliilinsu kamfanin Bakori yayi wannan asarar da aka kasa gano tushenta, wanda daga baya suka gano cewa kamfanin ne suka cuce su da alert din kudin karya bayan an gama yarjejeniyar komai, suka gabatar da shaidun biyan kuɗin ba tare da kuɗin ya shigo ba.
Don haka sanin cewa basu da hujjar zasu tunkare su kai tsaye yasa suka shiga neman accountant ɗin mutanen wanda yake kan aiki a lokacin da abin ya faru Mr. Ishmael Grahm, kuma da kyar ya iya gano address ɗinsa a jiya bayan tafiyar Ma’aruf din Jigawa, kums a jiyan tun ya a can ya kira shi ya shaida masa hakan kuma bai jira komai ba ya nemi ƴansandan da ya sani suka hada shi dana garin Delta inda suka gano mutumin anan yake suka je suka kama shi duk a jiyan, don haka a yanzu ya tabbata dasu yake wayar suna shaida masa wani bayanin.
Ma’aruf ya sauke wayar daidai lokacin da Faruk ɗin ya taso ya taho zuwa kujerar dake gabansa ya zauna.
“Me ya faru?” Ya tambaya yana kallon yanayin fuskar Ma’aruf din.
“Me muke dashi akan wannan Mr. Okafor din?”
Faruk ya girgiza kansa.
“Babu komai, har yanzu mutanen dana saka basu gama gano inda yake ba.”
Sai kawai ya cillar da wayarsa akan tueburin dake tsakiyarsu kafin yace.
“Dole ne mu nemo mutumin nan Faruk, don duk amsar da muke nema tana wajensa, har yanzu na kasa gane yadda tsohon nan shi kadai ya shiga rayuwata da yawa haka.”
“Me ya faru?”
Faruk ɗin ya sake tambaya yanayin kan fuskarsa na jira bai tafi ba. Kuma sai da Ma’aruf ɗin ya zura hannunsa a cikin gashin kansa sannan yace.
“Wahalar banza muka yi tayi Faruk, wannan dai Mr. Okafor din shi ya san komai, bai kamata ma mu cigaba da binciken ba bayan tafiyarsa, da ace mun dage wajen nemansa da watakila tuni mun gama da case din nan. Yanzu shi wannan mr. Ishmael din yayi musu bayani cewar Mr. Okaforn ne ya shirya musu komai a kamfanin, shi ya hada su da wani computer hacker daya turo mana da alert din kudin nan ba tare da kudin sun shigo a gaske ba, mu kuma a lokacin muka dauki kayan muka basu ba tare da anyi confirming ba, sai daga baya aka nemi kudin aka rasa shi yasa akayi wannan babbar faduwar.
Kuma har yanzu bamu da hujjar da zamu kai su kamfanin kotu tunda a baki ya shaida mana komai. Dole ne mu nemo shi Mr. Okaforn ya hada mu da wanda yayi musu aikin ko baza’a same shi ba a sami wata takarda da zata tabbatar mana da abinda suka yi wadda zasu tsorata su dawo mana da kudinmu ko kuma alkali yayi amfani da ita idan mun kaisu kotu a karbar mana ta hanyar shari’a.”
Faruk ya haɗe girarsa biyu waje guda yana nazarin kowacce kalma da Ma’aruf ɗin ke fada cike da zurfin bincike irin wanda ƙwaƙwalwar sa ta saba akan abubuwa, kuma sai da ya gama fahimtar komai sannan yace.
“Idan haka ne B, idan wannan mutumin shi e a bayan komai me yasa yazo da kansa da a farko ya same ni yace zai shaida min abubuwan da muke nema? Idan har shine ƙusar aiwatar da komai me yasa zai bayyana kansa da wuri har yayi kokarin fallasa sirrinsu kai tsaye?”
“Ni kaina abinda nake tunani kenan.”
Ma’aruf ya fada yana lashe leɓɓensa na ƙasa da yaji yana neman bushewa.
“Watakila a ranar da naje wajensa, da ban ga Hamida a gidan ba, da ace na zauna na saurare shi munyi magana watakila da tuni mun kawo ƙarshen wannan maganar, da tuni mun gama da case ɗin nan komai yazo hannunmu.”
“Dole akwai abinda yake a ƙasa B, don ni yanzu jikina ma ya fara bani ba mu kadai muke neman wannan mutumin ba.”
“Nima tunanin da nake yi kenan, don dole ne sai mun yi da gaske…”
Ya ɗanyi shiru sai kuma ya ɗago ya kalle shi da sauri.
“Ka san me za’ayi? Ka nemo mana appointment da Yakubu kawai. Kar ya wuce yau zuwa gobe.”
Faruq ya zare idanunsa.
“What?? B Yakubu? Yakubu dai Yakubun SS? Ka san kudin da mutumin nan yake karɓa kuwa yanzu?”
“Na sani, da kudina zan biya shi Faruk bada na kamfani ba, ‘Cox a yanzu ban ga wata hanya da zamu iya neman mutumin nan cikin sauki ba tunda har su Salihu suka kasa, dole irin Yakubun zamu nema tunda dama shi irin aikinsa kenan, ko ni da kai muka tafi ba lallai muyi abinda shi zai yi ba.”
Faruk ya gyaɗa kansa a hankali alamun ya fahimta daidai lokacin da wayarsa tayi kara daga can kan teburin, don haka ya miki yaje ya ɗauka, kuma ganin number data fito a jiki yasa shi fadin.
“Excuse me.” Sannan ya nufi kofa ya fita.
Kuma hakan ya tunawa da Ma’aruf missed call din Ishaq da ya gani a wayarsa shima har guda biyu, don haka ya jawo wayar ya shiga kokarin kiransa.
“Kana ina Kano ko Jigawa?”
Itace tambayar da Ishaq din ya fara yi bayan ya dauki wayar, kuma a lokaci guda kalmar Jigawan ta gifta masa da fuskar Amina, wani abu ya fada a zuciyarsa yana tuna masa da cewar rayuwarsa akwai canji a yanzu, a ƙalla duk bayan wannan hargitsin yana da wani waje da zai samu nutsuwa.
A dazu lokacin da suna hanya, lokacin da ya sata ta kwafar masa wasu lambobi daga cikin wayarsa zuwa daya wayar, yana tukin yana kallonta, yana kallon yadda ta nutsu sosai tana aikin da ya saka tan, kuma a wannan lokacin ne ƙwaƙwalwarsa ta fahimtar masa cewa irin abinda yake ji a zuciyarsa duk lokacin da yahe asibitin sa na MMB-6 haka yake ji idan yana tare da ita, wani irin buɗewa zuciyarsa take yi yana jin yana manta kowa dama komai sai iya abinda zai iya kawai.
Kuma ya san dalili, saboda ya fahimci duk abinda yace kawai shi take yi, duk abinda ya gaya mata shi zata yi ba irin Rulayya bace ita, Rukayya tana da ra’ayi tana da choices da expectations masu tarin yawa, shi yasa ko a lokacin aurensu da ya sa rai cewa zai samu nutsuwa a tare da ita, sai abubuwa suka canja, suka yi juyin waina don ita kullum cikin tuna masa da abubuwan da ya bari a rayuwarsa ta baya yake yi, abubuwan da yake a Ma’aruf ɗin da ta sanshi dasu wanda baya yi yanzu, shi yasa shi da ita basu taba daidaitawa ba, don yana son barin baya ne ita kuma tana jawo shi.
Amma Amina da a yanzu bata san waye shi a baya ba, bata san komai game dashi ba, bata da tunanin komai balle har tasa ran cewa zaiyi abu baiyi ba sai yake jin hankalinsa na kwanciya duk sanda yake tare da ita, zuciyarsa tana kara amsawa da abinda ya fara ji akanta tunda daga ranar farko da ya ganta.
“Mun dawo ɗazu.”
Ya amsawa Ishaq din dake jiran amsarsa a cikin wayar.
“Honeymoon din har ya kare?”
Ba shiri ya zare idonsa.
“Ni na gaya maka abinda ya kaimu kenan?”
“Sai ka gaya min? Wane sabon labari ne wai baka son tuƙin dare, inaga har Kaduna munje ni da kai bayan isha.”
Sai kawai ya koma da baya ya kishingiɗa da kujerar da yake kai yana guntun murmushi, ya cusa yatsunsa ɗaya cikin gashin kansa.
“To ka gama aibata ni sai ka gaya min dalilin da yasa naga missed call ɗinka har guda biyu.”
Daga cikin wayar Ishaq yayi magana da wani don alama tafiya yake yi kafin yace.
“B kana sane jibi ne zaman shari’ar nan?”
“Yes, na sake duba takardar, na sani.”
“Kuma har yanzu kana nan akan bakan ka ba zaka nemo kowacce irin shaida ba?”
“Eh.” Ya tabbatar yana gyada kansa.
“Har yanzu baka gaya min dalilinka ba.” Ishaq din ya sake fada a lokacin da yake tura kofar wani waje, don yaji karar da kofar ta bayar a cikin kunnensa kafin ya fara magana.
“So nake naga iya abinda zasu yi shi yasa na ɗauki wannan matakin Ishaq, Hamida ƴata ce, idan har zan rike ta it should be in a respectful way, bana son wani yaga cewa nayi amfani da ƙarfi ne na karɓe ta har ita Rukayyan kuwa, don idan hakan ta faru wasu abubuwan zasu biyo baya ka sani.
Shi yasa ba zanyi wani yunkuri ba Ishaq, don kamar yadda ka fada ne a yanzu doke shari’ar zata fi karkata ne a ɓangarensu ba. Wannan wasan nasu ne su suka kawo ƙarar nan don haka mu basu filin da zasu taka rawar su ba tare da mun ɓata musu ba, Cox idan na tashi nawa shirin Ishaq, ina tabbatar maka zanyi komai ne ta hanyar da za’a sami fahimta tsakanina da kowa, tunda a yanzu ina gujewa duk wani abu da zai jawo min tashin hankali Ishaq.”
Tun daga farkon bayanin, aganganun ƙarshe su suka ɗauki hankalin Ishaq ba duka sauran abinda ya faɗa ba.
Kalmai ne kaɗai, amma tasirin da suka yi a zuciyar Ishaq suna da yawa, don shi ya san waye Ma’aruf, yana tare dashi tsawon lokaci tun daga shekarun farko na ciwonsa har zuwa yanzu, kuma a baya babu irin naci da ƙorafin da baiyi ba akan ya dinga duba yanayin ciwonsa kafin ya aikata abubuwa, amma rashin yin hakan shine babban abinda ya kawo su ga matakin ciwonsa na yanzu.
Sai dai ya fahimci cewa tunanin Ma’aruf ya fara canjawa tun daga ranar da ya farka a London ya gaya masa matakin da ya kai a cutarsa, ya lura ya fara canja abubuwa da yawa a rayuwarsa tun daga wannan lokacin, kuma a yanzu da yayi wannan auren nan, ya ƙara fahimta cewa yana samun nutsuwa tare da yarinyar nan fiye da aurensa na farko, duk da har yanzu ba zai iya cewa ga takamaimai tunaninsa game da ita ba.
Sun ƙarasa wayar yana yarda da tsarin Ma’aruf ɗin ba wai don zuciyarsa taso ba ko kuma a matsayinsa na lauya hakan ya san hakan daidai ne, sai don ya san cewa kome zai faɗa a wannan lokacin ba zai canja tunanin Ma’aruf din ba.
****
*Karfe biyar da rabi na yamma.*
Ƙafafun Amina suka fito daga cikin toilet ɗin ɗakin bayan ta gama yiwa kanta faɗa da gargadin wankan yamma, amma babu yadda zata yi ne, don a yinin ranar kaf wannan shine kaɗai lokacin da ta iya samu na yin wankan, wankan da take jin kamar ya zame mata dole ne don karkade tarin abubuwan dake yawo a cikin kanta, sai dai duk yadda ta kai ga goge jikinta tare da zubar ruwan bata jin ko kalma guda ta fara koɗewa a cikin dubunnan dake kanta balle tasa ran cewa zasu fita.
Idonta ya kai kan wayar dake yashe a gadon ɗakin, wayar Ma’aruf ce da ya bata a safiyar yau bayan yasa ta debe masa nambobinsa zuwa cikin daya wayar tasa, bai ce ya bata ba har yanzu, amma zuciyarta na ayyana mata cewa hakan ce zata kasance.
Ta zauna daga gefen gadon ta ɗauko ta, ƙirar Samsung ce kamar sabuwa ma, ta tuna yadda tayi nacin samun wata Samsung kamar ba gobe lokacin da take ganin hotunansu a wayar Aminu, amma yau gata da Samsung ɗin a hannu kila ma wadda tagi waccan amma zuciyarta fayau take, babu ɗigon wani abu da zata iya dorarwa akan wayar koma wani abun a gefe.
Ta dawo ta tarar Tvn gidan ma an hada ta, an siyo reciver da komai jiya da basa nan an haɗa, Samirah ce ke gaya mata a ɗazu da ta shigo kawo mata jakarta da ta manta a ɓangarensu, don a ɗazu bayan fitowarta daga dakin Hajiya Kikishi rike da magungunan nan a hannunta, bata jin jijiyoyin dake cikin kwakwalwarta sunyi aiki mai kyau har ta iso ta dawo bangarensu.
Allah ne kawai ya taimake ta bata hadu da kowa a hanya ba kasancewar sagiya ce, in banda masu wanki da ta jiyo tarin hayaniyarsu daga can gefe da kuma su Mama Rabi dake shiga bangaren Inna Danejo suna gyara kasancewar yau zata dawo kuma cikin sa’a dukkansu basu kula da ita ba.
“Tarko biyu ta ɗana miki Amina.”
Abinda Amma ta fara fada a wayar kenan bayan ta ƙaraso ta kira ta kuma ta gama sauraren dukkan bayaninta.
“Baki fahimce ni ba na sani kamar yadda kika kasa fahimtar hakan tun lokacin da kina gabanta..”
Muryar Amman ta cigaba da fitowa a lokacin da hatta yawun bakinta ya tsaya cak! saboda ruɗani.
“Tace miki a yanzu magungunan sa sun dawo hannunki Amina, amma ta ɗauko sauran da yake sha ta baki su? Ko kuma shi ta gaya masa cewa zai dinga karbar maganinsa a hannunki?”
Kuma tambayar ta wuce da wani shiru mai tambarin nazari kafin ta iya amsawa a a hankali.
“A’a Amma, wadannan din kawai ta bani.”
“To kiyi tunanin ki gani Amina, da sunan maganin me zaki dauki waddannan ki bashi kai tssye? Wane bayani zaki yi masa da zai gamshe shi ya karɓa? Idan ma ya karɓa ɗin yasha kuma ciwon nasa ya biyo baya me kike tunanin zai faru? Daga shi har sauran jama’ar dake kewayensa me zasu yi tunanin akanki Amina?”
“Kowa zai zarge ni Amma.”
Amsar ta fito kai tsaye tun daga zuciyarta, don babu wuya ta zaƙulo ta daga cikin tarin abubuwan dake yawo a cikin kanta, kuma kai tsaye itama Amman ta cigaba.
“Tabbas kowa zai zarge ki Amina, ai babu wani kewaye-kewaye akan hakan. Kilishi mugun ice ce na gaya miki, irinsu ne mutanen da zasu sa ka kashe kanka ba tare da ka san kana soka wuƙar ba, kuma na gaya miki tun farko, dole ki maida ƙwaƙwalwar ki ta koma irin tata Amina, dole ki dinga tunani irin wanda take yi idan ba haka ba a kurkusa zata dulmiyar dake ba tare da kin ya fahimta ba.
A yanzu ta baki iya wadannan magungunan ne don ta gwada ki, taga ta yadda zaki cika umarninta kuma ki kare kanki a lokaci guda, taga ta yadda zaki iya bashi magungunan ba tare da kin shafawa kanki jan fenti ba kema. Tunaninki take son ta gwada, taga idan har zurfinsa ya kai ta saka ki cikin lamuranta, sannan kuma a lokaci guda ta tabbatar idan har da gaske kin goyi bayanta kamr yadda kika ce, kuma ina tabbatar miki Amina, idan kika fadi ko guda daya a cikin wadannan tarkon nata biyu, shikennan kin fara rusa darajarki a wajenta.
Ba zata kore ki a lokaci guda ba, amma zata dauki wani mstakin kwatankwacin yadda tayi wa Aminu don ta ƙara tsorata ki, sannan zata ƙara gwada ki, idan akayi rashin sa’a a karo na biyu kika sake faduwa shima, zata juyo kanki ne a lokacin, zata lahanta ki ta yadda zaki ji a jikinki ki san da gaske take sannan ta sake gwada ki….”
Muryarta ta ɗan tsaya kafin ta cigaba.
“… a karo na karshe ne Amina, idan ta sake baki wani abin kika kasa, ina tabbatar miki da cewar Kilishi zata iya rufe kawar dake gabadaya!”
A wannan lokacin Amina taji sanda zuciyarta ta buga a kirjinta kafin fatar bakinta ta shiga maimaita kalaman hasbunallahu wa ni’imal walkil da fatar babu tsayawa, kuma sai da Amman ta tabbatar kalaman sun gama shigewa cikin kanta wucewar wasu sakanni sannan ta cigaba.
“Amina, wannan abin da nake gaya miki gaskiya ne, don mutane irin Kilishi suna aikata abinda yafi haka ba tare da sunji ko ɗar! a ransu ba, shi yasa nake son tun a yanzu ki tattara hankalinki waje guda ki saurare ni, kiyi duk abinda nace, ki yarda da maganata ta cewar da kifi ake kama kifi, kin fahince ni ko?”
Ta san ta ɗaga kanta a lokacin kamar Amman na kallonta, amma bayan hakan ba zata iya tantance yadda zuciyarta ta dinga tsere a ƙirjinta ba, ta san kawai ta damƙe wata kwalbar turare dake gefenta a lokacin don tattara dukkan nutsuwarta, kuma bata san ya akayi hakan yayi tasiri ba, don tayi nasarar ture dukkan hargitsin daje cikin kanta ta cigaba da sauraren mahaifiyar tata.
“Ki narka magungunan a cikin lemo Amina ki bashi yasha ba tare da ya sani ba, ki kwantar dashi kamar yadda ta gaya miki ba tare da shi kansa ya sani ba Amina, ki nunawa Kilishi da gaske kike kin goyi bayanta, ki buɗe mata zuciyarki ta yadda zata sakanksnce ta karɓi yardarki, ki nuna mata zaki iya, zata ga hikimarki, zata jinjina miki, kuma zata jawo ki jikinta. Wannan shine matakin farko da zamu fara cin nasara akanta Amina.”
Ta sani cewa ta yarda da dukkan maganganun mahaifitar tata, ta san haka ne, ta san gaskiya ne… Ta san wannan itace sahihiyar mafitarsu, amma zata iya? Zata iya? Idanun Ma’aruf kawai idan ta hango sai zuciyarta ta ƙara nanata mata cewar ba zata iya ba, ba zata iya ƙarawa akan wahalar da yake sha yanzu a rayuwarsa ba, idanunsa kadai idan ta kalla tana jin kamar zata iya tsinto tarin abubuwan dake damunsa ɗaya bayan ɗaya, yana yawo dasu a kirjinsa da kuma kafaɗarsa.
To ta yaya kuma zata iya zama karin wata matsalar bayan duk bayanin da yayi mata jiya cewa yana son samun sauƙi a wajenta? Bayan haka ma idan tana tare dashi ta lura cewa ƙwaƙwalwar ta bata iya tuna duk wannan hargitsin sosai mantawa take da komai kawai sai shi da ka nasa maganganun.
Wani abu ya wuce ta makogwaronta da ba ta san meye ba, taji hannayenta da ta rike wayar dasu duka biyun suna rawa, sai kawai ta ajiye ta a gefe sannan ta mike, man da take shafawa tun zuwanta gidan ta dauko akan mudubi, har zata bude sai kuma ta tsaya tunanin anya ba fari yake sata ba kuwa, don ita kanta taga ta canja kwana niyu sannan ma Aminu yana ta tsokanarta cewa tayi haske, kuma ta san wannan ba sharrinsa bane.
Don haka ta shiga duba jikin robar kuma gabaɗaya babu inda aka rubuta hakan sai ma wasu abubuwa dake shaida mata tsadarsa, har yaushe zata dinga tunawa ne cewa masu kudi ta aura? Don tabbas a cikin wannan auren nata mazajen biyu ne, Kilishi da Ma’aruf sannan matan ma biyu ne ita da Amma, kuma kowa da irin rawar da yake takawa.
Sai kawai ta cije lebbenta da murmushi tana tuno kalaman Hajiya Kilishin na ƙarshe kuma mafiya tasirin da suka fi zama a zuciyarta.
_Ba zan hana iya Ma’aruf kula ki ba idan har yayi niyya, amma ba zan dauki wani abu wai shi ciki ba…!_
Bata shaidawa Amma wannan zancen ba don ta yarda daga Kilishin har Amman wannan ba huruminsu bane, wannan yaƙinta ne kamar yadda Amma ta gaya mata, kuma ta yarda ba komai Amman zata iya mata ba, don kamar yadda ta fada mata ne ita hanya kawai take nuna mata amma duk wani taimako da zata yiwa kanta yana hannunta, dole ne sai ta tsaya da kafarta ta fuskanci nata yakin, don haka ba zata dorawa Amma wannan nauyin ba.
Kuma Hajiya Kilishi bata isa ta yanke irin wannan kaddarar tata ba, wannan huruminta ne, hakkinta ne, idan ta yarda da Ma’aruf, bata jin akwai wani mutum kuma a gefe da zai gaya mata yadda zata yi da jikinta ko ma abinda zai zama rayuwarsu a gaba.
Wani murmushin ne ya sake subucewa a bakinta da wannan tunanin, wai rayuwarsu? Ma’aruf din da har yanzu bata dan me take ji game dashi ba, ta san dai kawai zuciyarta ta narke jiya da tayi bacci a cikin hannunsa, kuma bata gama bushewa ba sanda ya sake rungume ta a yau, amma a cikin wannan gulbin zata tsinto cewa tana tsananin ganin kwarjini da kuma girmansa, watakila shi yasa take manta komai idan yana gabanta.
Wata doguwar riga ta ɗauko (flowy and Maxi) kalarta fara ce, a jikinta anyi mata prints ɗin lilac flower kalar Pink da kuma Pitch, hannunta ya bude har zuwa rabin nata hannun, kalarta tayi kyau sosai da kuma ɗaukan hankali, amma ita ba wannan yasa ta dauko ta ba, rashin nauyin ta ne tasa ta zabo ta don shafal take sosai, tana daga cikin kayan da Aunty Safiyya ta bata, kuma ko sanda ta bata ɗin sai da su Aunty Ma’u suka yi ta ɗaga ta suna fadin laushi da kuma rashin nauyinta.
Don haka abinda ta tuna kenan a yanzu ta lalubo ta, don tare da nauyin dake zuciyarta dama cikin kanta bata jin zata iya da wata atamfa ko makamancin hakan. Tana da mayafi shi fari ne gabadaya, ta sake taje gashinta ta daure shi sannan ta daura mayafin akanta.
Hannayenta har yanzu rawa suke, amma ta san tunda basu yi komai ba tun sanda tana girkin da tayi da kyar a cikin tarin tunaninta, to yanzu ma babu abinda zai same su.
Bata ko saka slippers din da take yawo dashi a cikin gidan ba ta fita daga ɗakin, sanyin tiles din gidan na ratsa fatar ta har ta isa falo, idonta ya kai kan ƴar jar fitilar Tv da ta kama tana tuna mata cewa zata iya kunnawa a yanzu, amma bata hango kallon ko a ƙarshen lissafinta na yau, don haka ta juya Kitchen don karasa abinda ke gabanta.
_….ina son ɗanwake ma._
Shine abinda ya gaya mata jiya a cikin abincin da yafi so, shikenan sai ya zama saukinta itama, Samirah kawai ta kira a waya tace a taimaka mata da kanwa da kuka, nan da nan kuwa ta gama abinta, dama tana da yaji mai daɗi da Samiran ta kawo mata tun kwanaki, ta yanka vegetables a gefe guda don bata sani ba ko yana so, sannan ta hada haddadden zoɓonta da ta kusan shanye rabi kafin ta zuba a jug.
Yanzu ma fridge ta buɗe ta sake debo shi a kofi da niyyar ta koma ɗaki ta fito da kayan da ta tara na wanki kafin magriba tayi, kuma ta fito daga kitchen ɗin daidai lokacin da taji ƙarar ƙwanƙwasa kofar gidan, ƙara guda uku da yatsa daya, don haka ta riga ta san ye duk kuwa da cewar bata ji karar bude gate ba.
Sai kawai ta ajiye kofin hannunta a gefe Tv wata zuciyar ta gaya mata cewar ta kwance mayafin ta yafa shi amma wata zuciyar ta kore hakan kai tsaye.
****
Da wuri ya bar Office yau, don yana yin sallar La’asar ya fito tunda sun riga sun gama dukkan abinda zasu yi na yau, dawowar Baffa a gobe kawai ake jira a gabatar masa da komai kafin su fara fuskantar wasu sababbin ayyukan.
Kuma bayan shigowarsa gida kai tsaye ciki ya nufa, yayi minti goma da kyar a ɓangaren Hajiya Maimuna kafin ya fito ya nufi inda yafi wayo, a falo ya kuwa tadda Mamin ita kadai tana zaune tana waya da wani faffadan murmushi a fuskarta, kuma har ya zauna bata gama ba sai dai ya lura bata ƙara cewa komai ba bayan sauraren da take yi.
Ta ajiye wayar yana tsokanarta cewa Allah yasa kwangila ta samo musu kafin su gaisa, sunyi hirar shari’ar Hamida dake shirin faruwa a jibi inda ta dage akan cewar kar ya yarda ya mayar musu da ita gwara ya dawo da ita wajensa kamar yadda ta jaddada masa tun farko, kuma haka kurum sai ya samu kansa da amsa mata kawai ba tare da ya baiyana mata irin tsarin da yayi ba.
Daga nan suka shiga hirar wani sabon gidan gona da take son buɗewa, tana cewa zata ɗora shi a matsayin manajan wajen yana roƙonta ta taimaka ta rufa masa asiri abubuwan dake gabansa sun ishe shi.
“Mami Slides ɗina ne zasu haɗe dana kaji, sai nazo ina presentation a meeting kawai in buɗe kaji suna cin abinci. Baffa will sack me for days.”
Dariyar da take ƙyalƙyale da ita, dariya ce dake fitowa tun daga ƙasan zuciyarta, kuma shi kansa ya sani cewa ko tare da Baffa bata irin wannan nishadin balle kuma duk wani wanda zai biyo bayansa, shi daban ne a lissafinta ba sai ya rantse ba ya sani, ya san Mami na kaunarsa da dukkan irin ƙaunar da uwa ke yiwa ɗanta, wani abu na gaya masa cewa zuciyarta tana yin fiffike ne ta tashi sama ta zagaya a duk lokacin da yake zaune a gabanta irin haka, shi yasa a kullum yake addu’ar Allah ya bashi ikon faranta mata a tsawon rayuwar da zaiyi.
Ya baro cikin gidan da wannan farin cikin a zuciyarsa ya iso bangarensu, kuma har zai buɗe ƙofar da mukullin dake jikin na motarsa, sai kuma ya fasa kawai ya kwankwasa, sau daya biyu, uku yayin da yake tsaye dab da ƙofar hannayensa harde a kirjinsa. Kuma ba’a wani jima ba, aka murɗa handle din a hankali sannan jikin ƙofar yayi baya.
Ba shiri Ma’aruf yaji wani murmushi ya sauka a lebbensa, don duk yadda zuciyarsa ke hassaso masa yadda zai dawo ya ganta, a yanzu ta wuce hakan, a lokaci guda kalolin rigarta dama yadda ta rigar ta zauna a jikinta suka ɗauki hankalinsa, yaji wani abu ya motsa a cikin kirjinsa, sai kawai ya cije lebbensa yana murnushin kafin yace.
“Assalamu alaikum.”
“Wa’alaikum salam.”
Ta amsa a hankali tana sakin hannun ƙofar, ƙafarta tayi taku biyu zuwa ciki amma sai ya cigaba da tsaiwa bai shigo ba, kuma har tana kokarin juya ciki jikinta ya bata cewa a tsaye yake don haka ta juyo ta sake kallonsa, yana tsaye a yadda yake, ya harde hannuwansa a ƙirji yayin da wayoyinsa da kuma muƙullin motar da ya rike ya fito ta kowanne gefe, mamaki ya nuna akan fuskarta don haka ta dawo ta tsaya kuma kafin tayi magana sai kawai yace.
“I’m sorry, ina neman wata ne mai suna Amina, ance min anan take, zaki ganta wata ƴar ƙarama haka tana da idanu masu kyau, kuma ta iya murmushi.”
Ba shiri murmushin ya suɓuce a bakin Amina, murmushi da ya fito tun daga zuciyarta saboda da gaske ya bata dariya, yadda yayi da fuskarsa idan tare da wani ne zai rantse cewa da gaske kwantancen yake yi, kuma haka kurum sai taji wani abu a cikin ranta yana wucewa, don haka ta girgiza kanta a hankali tace.
“Bana jin na santa.”
“Saboda me?” Muryarsa ta fito tare da godiyar biye masan da tayi.
“Saboda ni kaɗai ce Amina anan, kuma ni duk ban kai yadda ka fada ba.”
Ta sake faɗa a hankali tana murza yatsunta. Ya kalli yatsun nata sannan yace.
“Zaki yi mamaki idan nace miki a yanzu kinfi ƙarfin kwatance na ma, you look stunning Masha Allah.”
Amon muryarsa na fitowa da zurfi.
Murmushin ta ya ƙaru a lokacin da take kallonsa har yanzu da mamaki a fuskar ta, sai kuma yayi saurin girgiza kansa kamar ya tuna wani abu sannan yace.
“I’m really sorry na manta ban tambaye ki ba idan Aminar da nake nema matar aure ce, kar in kwana a inda ban shirya ba.”
Murmushin ta ya sake karuwa kafin ta ɗaga kanta sau biyu tana cije lebbenta.
“Ya Salam!” Ya faɗa yana sakin hannayensa.
“Saurin me kika yi haka? Me yasa zaki yi aure tun yanzu?”
Sai da ta zare idanunta tana dariyar da bata san daga ina take fitowa ba kafin tace.
“Saboda me?”
A lokaci guda ya karaso, ya tako zuwa cikin falon, ya tsaya dab da ita sannan yace.
“Cox I want you, bai kamata ki auri wani ba, ko Allah ya san nine mijinki.”
Sai da Amina ta cije lebbenta sannan ta rufe idanunta tana murmushi, kuma kafin ta buɗe idon ya sunkuyo daidai gefen fuskarta yace.
“I apologize if this is a little bit forward, but you just look so…. Woww!”
Abinda taji kenan kafin taji ta a cikin hannayensa. Numfashinta ya yanke daga huhunta a lokaci guda, ƙafafunta suka karbi hannayenta wajen rawa, zuciyarta ta sake komawa ruwa, ta sake komawa irin duniyar jiya, duniyar da take manta komai sai Ma’aruf kawai da irin abubuwan da yake nuna mata.
Ya tallafi fuskarta kaɗan yana sawa ta kalle shi, don ko kaɗan ta kasa rufe idanunta ma yanzu, idanunsa cikin nata yace.
“You are making my world so much more beautiful Amina.”
(Kina kara ƙawata duniyata Amina.)
Shikenan! Sai komai a cikin kan Amina ya sake rushewa, kalaman Hajiya Kilishi har ma dana Amma dake kokawar miƙewa, dukkan wani abu mai hankali a cikin kanta ya shiga gaya mata cewar da gaske ne ba zata iya taba lafiyar Ma’aruf ba!
*****
A cikin dakin, a cikin wayar, muryar Hajiya Kilishi ta ratsa da tsananin yaƙinin dake fitowa daga zuciyarta.
“Mahaifinta shine a lissafi Awwalu, munyi wata ya shaida min cewa sun dawo ɗazu, don haka gobe zai fita aiki ina so ka fara bibiyarsa tun daga safiya, duk inda zaije ka kasance tare dashi kuma a shirye, wa’adin lokacin zuwa yamma ne kamar na yaron nan. Idan har ban sami abinda nake so zuwa sannan ba, zaka ga umarni na.”
Daga cikin wayar Awwalu yayi dariya mai cike da mamaki yace.
“Mutumin nan fa shine ɗanuwanki Kilishi, ina laifin ki sake taɓa wani daga cikin ƴanuwan nata kawai? kuma shi bashi da wata matsala ma naga, let the man be! Ki duba iyalinsa ki kyale shi.”
Ko bai ganta ba ya san ranta a hafe yake sanda tace.
“Tun yaushe muka fara la’akari da wani abu a cikin lamuran mu Awwalu? Ka amsa min kawai, bana buƙatar dogon surutu.”
Sai ya sake kyalkyalewa da wata dariya mai armashi irin tasa sannan yace.
“An gama Hajiya, umarninki shine abin aikatawa ta!”
**
_Ku gaya min cewa Amina tana shirin kaimu ta baro…_
_Ko kuma laifin na Ma’aruf ne?_
_Ga dai mafita tiryan-tiryan Amma ta fitar, amma kamar Amina kuma kuna ganin cewa da matsala?_
_To wace matsalar kuka zaba?_
_Ta Amma dake cikin mafitar?_
_Ko kuma ta Kilishi da zata biyo baya?_
MASU ƁUKATAR A TALLATA MUSU HAJOJINSU ZA SU IYA TUNTUƁARMU TA LAMBOBIN 07045308523 MUN GODE
