Search
You have no alerts.

    MASU ƁUKATAR A TALLATA MUSU HAJOJINSU ZA SU IYA TUNTUƁARMU TA LAMBOBIN 07045308523 MUN GODE

    “Karya yake…”
    Abinda Nura ya fada kenan yana kallonsa a lokacin da yake tsaye a gabansa. Shi din da ya dawo ya sake nemansa lokaci kadan bayan rabuwarsu, don a tunaninsa tun bayan lokacin da suka sauke shi sun dade da barin garin, sai gashi cikin abinda yake kasa da awa guda kiransa ya sake shigowa wayarsa da tambayar yana ina? Kuma bai bata lokaci ba ya shaida masa inda taken duk da mamakin da ya kama shi, wajen da cikin abinda yake kasa da minti goma yazo ya same shi.
    Tun kafin ya tsaya ya hango motar don haka ya taho ya iske shi a daidai jikinta bayan ya fito.
    A wannan lokacin Nura zai rantse da Allah duk da ya dade da sanin halin mahaifinsa ba karamin mamaki ne ya sake lulluɓe zuciyarsa ba lokacin da Jawad din ya shaida masa abinda ke faruwa.
    Farko, yayi mamaki sosai da ya kasance yarinyar ta zama Zainab ɗin da ya sani cewar a kwanakin nan an rasa zaman lafiyar gidansu saboda ita, ya san ya kalle ta a lokacin da ya fara haduwa dasu amma baiyi mata kallon da zai gane wacece ita ba don a tunaninsa matarsa ce, matar aure ce, matar da babu dalilin da zai sa shi kare mata kallo, don duk buɗewar idanunsa duk irin tarin zunuban da yatsunsa zasu lissafa ya aikata a rayuwarsa babu harkar mata a cikinsu, a kodayaushe a kowanne hali yana daraja mata, yana basu ƙima da kuma darajar da ya san Allah ya halitta su da ita, don haka mace ko wace iri ce ba saka ta a ransa.
    Mamakinsa na biyu akan mahaifinsa ne, mamakin yadda kai tsaye ya haɗa ƙarya irin wannan don kawai ya kore alkhairin da ya san cewa ba zai shafe shi ba… Don halin da yake ciki bashi da alaka da zuwan Jawad ko rashinsa kwata-kwata, kawai yayi hakan ne don son zuciya da kuma ƙoƙarin kuntatawa yarinyar da ko maraicinta ba zai kalla ba don ya sassautawa rayuwarta.
    Satin sa biyu da dawowa garin lokacin da mahaifiyarta ta rasu… Ya dawo ya tarar bata da lafiya kuma zai rantse kafin mutuwar tata akwai ranar da kunnensa yaji tana roƙon mahaifin nasa akan ya dawo mata da ƴarta don tayi jinyarta, wanda sai a sannan shi ya tuna cewa ma tana da ƴa guda daya da tsohon mijinta, kuma a lokacin ne ya fahimci inda yarinyar take don da kunnensa yaji mahaifin nasa na gaya mata cewa idan yarinyar ta dawo bai san kuma da wanne kudi za’a dinga samu ana siyo mata magunguna ba don shi bashi da shi.
    Rigimar da ake ciki kuma a gidan ta fara ne tun bayan rasuwar mahaifiyar tata inda yanuwanta da suka zo suka nemi yarinyar kai tsaye kuwa sauran matan kuma suka shaida musu cewa ai mahaifin nasa ya kai ta can birni aikatau.
    Saboda haka tun kafin a kai ga share makoki aka fara sa’in sa a tsakaninsu, suka tsaya akan cewar sai ya dawo musu da yarinyar, da kyar aka sulhunta wajen bashi wasu kwanaki da cewar ya dawo da ita, kuma basu ko tsaya an kai kwanaki bakwai ba ana share makoki da kwana uku gabakidayansu suka koma kauyensu.
    Sai dai shi tun daga kan haka bai kara bi ta kan zancen ba yaji inda aka tsaya ya shiga harkokinsa, don haka a yanzu da ya riski wannan labarin daga bakin Jawad, har da kuma sunansa da zancen cewar shi zai auri yarinyar dashi ko kammaninta ba zai iya zanawa a zuciyarsa ba, kafafunsa sunyi mutuwar tsaye ne na wucin gadi yayin da zuciyarsa ke maimaita kowanne batu ɗaya bayan ɗaya kafin ya girgiza kansa a hankali yana kallon Jawad ɗin.
    “Ƙarya yake, wannan zancen ba haka yake ba, a gaskiya babu wani alkawarin aure tsakani na da yarinyar nan, ya faɗa maka hakan ne don ka rabu da ita kawai…”
    Wadannan maganganun su Nura ya faɗa masa bayan ya ƙare masa dukkan wani bayani, kuna sune magan ganun da a lokaci guda suka ciccibo shi daga wata duniyar suka dawo dashi wata, yaji kamar ya saka hannu ne ya sauke masa wani tarin nauyi da yake yawo dashi a kirjinsa. Yana kallonsa lokacin da ya cigaba da fayyace masa komai…
    “Ka gane… Da shi da mahaifinta abokan juna ne, to bayan rasuwar mahaifinta nata ne sai ya auri mahaifiyarta, a lokacin kamar daga ita har yanuwanta sunyi tunanin zata samu sauki ne a wajensa ko kuma sun ga cewa sun sanshi ne sai kawai suka amince, to ni ban san me yake faruwa ba bsyan na tafi amma dai na fahimci bata jin dadin auren, kuma da ya tashi tura yarinyar aikatau ya hana ta gayawa yanuwanta kamar dole yayi musu ne ya tura ta irin yadda yake yiwa sauran ƴaƴan nasa.
    To sai bayan rasuwarta ne a yanzu sannan suka dage akan cewar ya dawo musu da ita, sai kuma gashi yanzu kun zo, to ina tabbatar maka da cewar yanzu can wajen yan uwan mahaifiyar tata zai maida ita, kai kuma ya kore ka ne don ya san da zarar ya mayar da ita ba zai amfana da kai ba shi yasa yayi amfana da wani abu naka ba, shi yasa yayi amfani da sunana ya gaya maka wannan labarin amma ina tabbatar maka duk abinda ya faɗa babu gaskiya a ciki, don ni yanzu ma babu batun aure a gabana.”
    Tun daga farkon bayanin har zuwa karshe ya saurare shi ne da dukkan nutsuwarsa, da dukkan hankalinsa da kuma tunaninsa wajen tantance gaskiya ko kuma akasin kalaman nasa, sai dai duk iya nisan da hasashensa ke kaiwa, dawowa yake yi wajen gaskata shi da kuma yarda dashi, idan aka cire muryarsa a idanunsa kaɗai yana ganin tabbacin kowacce kalma da yake furtawa.
    Yana jin yadda zuciyarsa da kuma kowanne abu mai hankali a jikinsa ke yarda dashi, don haka a lokacin da ya kai karshe, bai ɓata lokaci ba ya shaida masa abinda yake son yayi masa bayan Nuran ya shaida masa cewa mutumin ba zai ɗauki lokaci ba wajen sa wa a maida ita wajen yanuwan nata tunda har an riga an ƙaiyade masa wasu kwanaki da sharaɗin ya dawo da ita.
    “So nake kayi kokarin da zai mayar da ita wajen yanuwan nata da wuri, sannan ka bi su har can ka gano ƙauyen sai ka kira ni ka gaya min, zan biya ka ko nawa ne Nura…”
    Yana tuna alkawarin da Nuran yayi masa, tarin alkawarin cewa komai zai tafi daidai kuma bai san me yasa ba haka kurum ya yarda dashi, ya ɗebo adadin wasu kudade daga cikin wanda ya fito dasu a cikin dashboard ɗinsa ya bashi da cewar ya kula da ita har zuwa lokacin da komai zai daidaita, kuma bai sake bukatar komai ba ya juya motarsa ya bar ƙauyen, ya riga ya fahimci cewa gaggawa shine mataki na farko da zai bata hanyar mafitarsa.
    Bashi da wani ƙarfi ko kuma wani iko akan mutumin nan ya sani, babu yadda zai iya dashi a yanzu tunda har Zainab ta riga ta shiga hannunsa, don haka zai bi shawarar Nuran, zaiyi hakuri har zuwa lokacin da zata bar cikin ikon nasa, wanda yake saka ran saka ran hakan da wuri kamar yadda ya gaya masa, shi yasa bai ko damu ba a yanzu kafin tasowarsa da Nuran ya sake kiransa a waya ya shaida masa cewar mahaifin nasa ya ajiye Zainab ne a can cikin dakin uwargidansa inda ba zai iya zuwa ba don haka ba zai iya hada shi da ita a waya ba kamar yadda suka yi kafin rabuwarsu.
    Wani abu ya wuce ta makogwaronsa a hankali yayin daya tuna babban al’amari na biyu dake shirin faruwa da rayuwarsa, bai san takaimaimai me zai faru ba, bai san na abinda zai je ya tarar a garin Kanon da yake nufa a yanzu ba, abinda ya sani kawai shine, tun kafin haduwarsa da Nura, bayan ya baro kofar gidan mutumin nan, kira ya shigo wayarsa da wannan lambar da aka bashi,lambar da yake saka ran ko yaya ne zata bashi hanya ta kuma saukaka masa wahalar tafiya neman abinda ya fito dashi har hakan ya shafi rayuwar Zainab.
    Sai dai kuma ya fahimci kamar yadda yake neman wani abu haka ma matar da ta amsa wayar take, bai tabbatar ba don wataƙila baya cikin haiyacinsa a lokacin amma ya fahimci ba lallai ne idan tana da wata kwaƙƙwaran bayani da zata iya bashi ba, zai je ne kawai don ya sami wani abun akan iya abinda yake dashi, don ya tabbata ita ta daɗe tana nema, don haka tabbas zai samu wani abun da zai fi nasa.
    Shi yasa ya yanke shawarar tahowa inda ta gata masa take a lokaci guda, ba zai koma Abuja ba, hatta wajen aikinsa ya riga ya rubuta takarda tun da asubahin yau ya tura musu na daukar hutu tsawon wasu kwanaki, kuma ya sani bashi da matsalar hakan don a shekaru biyu da suka wuce ko hutun karshen shekara da ake bawa kowanne ma’aikaci shi bai taɓa karba ba.
    Su Hajiya Mardiyya kuwa bai ƙara ganin kiran daya daga cikinsu ba tun dazu, ya gaya musu zai dawo, kuma ya san hakan kadai ua ishe su su fahimci cewa ya riga ya yanke hukuncin da babu wani kuma da ya isa ya saka shi ya canja, tunda sun sanshi, sun san halinsa da kuma abinda zai iya tun kuruciyarsa.
    Matar ta turo masa da address ɗin inda take, a tunaninta a garin Kano yake shima, don kai tsaye ta gaya masa cewa zata jira zuwansa a yau din, shi yasa ya tabbatar da cewa itama nema take kamar shi.
    Ya bude idanunsa a hankali sannan ya zura hannunsa cikin aljihun rigarsa, rigar da ya canja a cikin garin Kaduna inda ya nufa bayan rabuwarsa da Nura, Gidansu wani abokinsa Hashim ya nufa kai tsaye inda yaci sa’a Hashim din kuwa na nan, a gidan ya bar motarsa sannan yayi wanka ya canja kaya zuwa wasu riga da wando da ya tsaya a wani boutique ya siya, rigar kamar ta sanyi ce amma bata da nauyi, tana da hula mai girma wadda ya jawo ta ya rufe kansa da ma kusan rabi na fuskarsa, bayan kayan babu abinda ya dauja sai wayarsa da kuma wallet dinsa inda ya jera mint din kudaden da ya ciro.
    “Maigida…”
    Saurayin dake zaune a kujerar gefensa ya faɗa a hankali, ya juya ya kalle shi yana yin baya da hular rigarsa, wanda hakan yasa Saurayin ya kara yin murmushi kafin yace.
    “Nace dan Allah ko zaka taimaka ka dan dauke ni a hoto, this is my first time hawa na jirgi, so ina so nayi posting a acconuts dina na social media ne…”
    Ya faɗa yana ƙoƙarin miƙo masa wayar hannunsa, babu yadda zai yi sai kawai ya gyada masa kai sannan ya karbi wayar ya danyi baya kadan yayin da saurin ya gyara zamansa a jikin kujerarsa dake kusa da taga, ai kuwa yayi masa hotuna guda biyar masu kyau sannan ya mika masa.
    “Nagode, Nagode sosai, It means alot sir!”
    Cewar saurayin yana murmushin jin dadi har da hade tafukan hannayensa biyu, kuma bai san me yasa ba sai kawai ya nuna masa kwalin wani abu a hannunsa da ska rubuta ‘Free-dat’ sakon kai abun ne yasa mutanen da suke do suka bada kudin jirgi a kawo…
    “… Idan ba haka, babu abinda zai sa in hau jirgi a wannan matakin da nake a rayuwata.”
    Bai san lokacin da murmushin da bai shirya masa ya subuce a lebbensa, ba wai kuma murmushin abinda ya fada bane, murmushin jiye wa matashin dadin rayuwarsa yayi, dadin wannan lokacin da yake ciki da bashi da wata damuwa mai yawa, tazarar shekarunsa bata da wani yawa sosai ya sani, amma shi yanzu ne lokacin da komai yake hargitse masa, rayuwarsa ma gabaɗaya ta canja a cikin kwanakin da basu fi ƙarfin ƙirgen yatsunsa ba. Ya rasa identity ɗinsa sannan kuma yana shirin rasa yarinyar da yake ganinta a matsayin wani ɓari na rayuwarsa.
    Ya tabbbata laifinsa ne ke bibiyarsa, ko ma ya fara, don shi da kansa ya sani cewa wanda ke aikata laifi irin nasa karya ne rayuwarsa ta dinga tafiya daidai,karya ne ka sabawa Allah akan haninsa kuma ace baka fuskantar wani kalubalea ruywarka, idan kuma hakan ta faru to kuwa tabvatas ka ji tsoron haduwarka da shi… Don ko hausawa sun ce ‘Alhaki kwikwiyo ne, duk inda kayi sai ya bi ka.’
    Ya sani cewar ya biyewa shedan a rayuwarsa,ya aikata rarin abubuwan da sanari da yawa a wannan zamanin ke ganin cewar ba laifi ne, kamar suna halattawa kansu ne ma wasu sabon Allahn a cikin lissafin morewarsu ta duniya, amma zai rantse da ubangijinsa tun daga lokacin da zuciyarsa ta fara fuskantar Zainab da kuma al’amarinta, ko shisha bai kara dandanawa a bakinsa ba, yana jin kansa ne kamar ya zama commited na tarin irin abubuwan nan da yake ganin bashi da lokacinsu, ko abokinsa Haro a yanzu su kan dade ma basu yi waya ba ganin yaki maida hankali game da shirin da suke yi akan Rukayya.
    Rukkaya. Ya lashe lebbensa kadan sabida ambatar sunan da zuciyarsa tayi, tana ina a yanzu? Me ke faruwa a cikin tata rayuwar? Don ya tabbata ba shi kadai ne yake fuskantar sakamakon laifin da suka dade suna aikatawa a rayuwarsu ba, kwarai ko da ga nesa ne zai sp sanin halin da take ciki don ko layin da take samunsa dashi ma a yanzu baya wajensa, ya daɗe da bawa wani masinja a Office ɗinsu kyautarsa tare da sabuwar waya bayan ya kawo masa korafin rasa wayarsa da yayi.
    Jirgin ya sauka a Kano da misalin ƙarfe 7:24 na yamma, yayi sallama da wannan saurayin mai sakon Free-dat sannan bai bata wani lokaci ba kasancewar bashi da kaya ya fito daga wajen, a cikinnairpot din ya samu mai motar da yayi haya har zuwa address ɗin gidan da matar ta turo masa.
    ***
    *No 1856L, Sulaiman Crecent Kano.*
    *Gidan Hajiya Salamatu.*
    Babu irin sake-saken da Hajiya Salamatu bata yi a zuciyarta ba bayan sun gama waya da mutumin da ya tabbbatar mata da cewar shine ya turo sako cikin wayarta game da matar nan Hanne, kuma ya tabbatar mata da cewar zai same ta har inda take a yau.
    Ta dauki wayarta da niyyar kiran tarin mutane amma tana fasawa, sai karshe da tunaninta ya tsaya kan kaninta mai bi mata da shima yake zaune anan cikin unguwar da take sannan ta kira shi, kuma a wayar ta kasa shaida masa komai sai da yazo gidan tukunna.
    Kallon da yayi mata bayan ta gama yi masa dukkanin bayanin da Awwalu yayi mata da kuma yadda suka je har Garun Albasu nemsn Hanne da ma sakon da ta samu a yanzu,kallo ne da bata taba gani a idanunsa ba, kamar yana shirin cewa watakila ta samu cutar tabin hankali ne ko kuma zaiyi mitar ta taso shi akan abinda yake kamar almara, amma sai ya girgiza kansa sannan muryarsa cikin kokarin kwantar mata da hankali yace.
    “Zamanin nan babu abinda ba ya iya faruwa Ya Salamatu, mutane sun haukace akan kudi yanzu, babu ta hanyar da ba za’a biyo ba don a yaudare ka yanzu, kar ki bari wasu suyi wasa da hankalin ki. Ni shaida ne da Kawu Muhammad da Yaya Murtala Allah ya jikansu, su suka binne jaririn da kika haifa matacce tun a wannan ranar….”
    Saita girgiza kanta taba katse shi tun kafin ya karasa.
    “Wallahi Nasir tun a wannan ranar da na rike jaririn da aka bani ban ga kamanni na ko kuma na Ibrahim a fuskarsa ba… Kuma banji komai ba, banji sani abu da ya danganta ni da wannan yaron ba.”
    Yana kallonta sai kawai yayi dariya ya girgiza kansa.
    “Ba fa jiya ko shekaranjiya muke zancen al’amarin nan ba Ya Salamatu, shekaru kusan talatin da nawa kenan… ?”
    Sai ta ƙara Daga kanta alamun amincewa sannan tace.
    “Shikenan naji mu ajiye zancen nan Nasir, yanzu dai ai ba abinda ya kai ga faruwa, mutumin zai zo kuma zai same ni ne ni da kai saboda haka idan ma har akwai wani abu a ciki sai ka taya ni ganewa.”
    Da haka ta rufe bakinsa, bai ƙara cewa komai ba, suka zauna jiran mutumin da a cikin zuciyarta bata da tabbacin cewa zai zo ɗin, don haka tayi tarin sake-saƙen da bata san iyakarsu ba har lokacin a ya tafi sallar magariba a masallacin wani gida dake makotan ta ya dawo.
    Yar aikinta ta kawo masa tarin abincin da yana ci yana kallon wasan ball a Tvn falon nata, hankalinsa kwance kasancewar ya gayawa matarsa inda yake, amma ita nata hankalin ya kasa kwanciya ta shiga daki ta fito har compound din wajen ta dawo yafi kirgenta, gani take yi kamar mafarki ne, kamar ba gaske bane abinda ke shirin faruwa, don hatta hasken fitulun gidan nata gani tayi sun disashe a idanunta, sun koma yanayin da mutum ke gani kamar a mafarki, kana ganin abu amma ba kamar daga nesa ba tar ba.
    Hatta Nasir din sai da yace ta kwantar da hankalinta, idan basu ga kowa ba Allah ya tseratar da ita kenan, sannan a agogon falon nata ya nuna mata adadin mintunan da zai iya karawa a gidan don a kunnenta mutane har biyu sun kira shi da cewar suna jiransa.
    Sai dai ƙarfe takwas da minti uku daidai, lokacin da wayarta tayi kara, zuciyarta ta buga tare da amon sautin kiran sannan numfashinta yayi nauyi a kirjinta ta yadda da kyar ta sauke shi ganin lambar da take jira ce ke kira, Nasir yayi mata alamun ta ɗauka. Kafin ta sake fitar da wata ajiyar zuciyar ta kara ta a kunnenta.
    “Assalamu alaikum…”
    Jawad ya furta daga can ɗaya bangaren, muryarsa can ƙasa ta fito, tana shaida masa tarin gajiya da kuma tarin lissafin dake cikin kansa.
    “Wa… Walaikum salam.”
    Hajiya Salamatu ta amsa a hanzarce.
    Daga wajen wani madaidaicin gida kuma mai farin gate din da yake tsaye, Jawad ya kalli plate number dake jikin katangar kafin yace.
    “Ina kofar gidan da kika bani address ɗin… Shine 1856L Sulaiman Crecent ko?”
    Zuciyarta ta faɗa har cikin cikinta kafin ta sa
    “Nan ne, bari nayi magana su shigo da kai.”
    Da haka ta kashe wayar, hannunta na rawa ta shiga neman lambar maigadi.
    “Gashi nan ya iso Nasir, yanzu zai shigo.”
    Ta fada, kuma lokacin da Maigadin ya dauka bayan bugu daya, taji ne kamar tayi ihu wajen saka masa albarka.
    “Akwai bako a waje ka shigo dashi yanzun nan.”
    “To Hajiya.”
    Ya amsa da sauri shima jin yansyin muryarta, Hajiya Salamatu ta ajiye wayar sannan ta tafi da sauri wajen tagar dakin dake fuskantar saitin bakin gate ta buɗe labulen, tana ji Nasir na cewa kar ta fita ta bari ya karaso tukunna.
    Akan idonta maigadin ya fito daga dakinsa, ya bude kifar gate din ya fita sannan bayan sajanni uku kofar ta sake budewa suka shigo tare, tana hango su suna tahowa zuwa ciki kuma tun daga can zuciyarta ta shaida mata cewa ba wani babban mutum bane kamar yadda ta zata,matashi ne yaro daga shigar dake jikinsa ta wando da riga mai hula da kuma ƙirarsa ma, suna kara matsowa tana kara ganin tsawonsa kamar na daɗuwa, tsawon da a lokaci guda tasirinsa a idanunta ya zarce cikin zuciyarta ya sami mazauni.
    Nasir ya riga ta tafiya ga kofar falon a lokacin da suka karaso, don bayan ta saki labulen ta juya da sauri ta tadda shi hana kokarin bude kofar tin kafin ma su buga.
    “Yallabai barka dai, barka… Dama Hajiya ce tace a shigo dashi, bakonta ne.”
    Maigadin ya fada a lokacin da kofar ta bude a gabansu, tana tsaye daga bayan Nasir ɗin sanda Maigadin ke fadar hakan sai dai ta tabbata daga ita har Nadir din bashi suke kallo ba, idonsu na kan matashin ne da ya saka hannu ya ture hular da ya rufe kansa, fuskarsa ta fito tar a cikin hasken fitilar wajen.
    Ibrahim.
    Shine mutumin da Hajiya Salamatu ta gani tsaye a gabanta.
    Ibrahim Shanawa.
    Mijinta na farko a duniya, mijin da ta fara zaman aure tare dashi, shine sak a tsaye! Cikin shekaru da kuma ƙuruciyar da ta aure shi, wannan lokacin da kyawunsa da kuma dukiyarsa suka rufe mata idanu daga ganin kowa a duniyar saɓanin shi… Amma ta yaya zai cigaba da kasancewa a haka bayan ita ta tsufa ta manyanta?
    Wannan tunanin shine ya daki tsakiyar kanta a lokaci guda yana son tabbatar mata da cewar abinda take gani ba daidai bane, sai dai muryar Nasir da ta fito a lokaci guda ta katse wannan tunanin daga tabbatuwa, ta gaya mata cewa ba ita kaɗai take ganin abinda idanunta ke nuna mata ba…
    “Innalilahi wa’inna ilaihir raji’un…!”
    ***
    *Bakori Enterprises*
    *Administrative Office.*
    _Zan iya fara restarting wani amma still shima ba lallai sautin ya buɗe ba sai da Frea-dat ɗin._
    Idon Ma’aruf ya karanta abinda Abdurrahim ya rubuta a fuskar wata Tablet da koyaushe tana hannunsa da ita yake nagana ta hanuyar rubuta dukkan abinda zai ce da dan yatsansa, ya karanta yaje har karshe sannan ya gyada kansa da sauri.
    “Kar ka damu, just carry on yanzu zai ƙaraso insha Allah.”
    Ya faɗi hakan sannan ya juya gefe, daga can barndar katon ofishin da suke ciki inda Faruk ke tsaye yana faman magana a cikin waya, maganar da bata komai bace illa bayani da kuma kwatance wa wani mai online shop guda ɗaya da suka samu da suke da Fre-dat ɗin da Abdurrahim yake nema, wani abu da su basu taɓa saninsa ba don haka a yanzu Faruk ɗin na waya dasu ne don su san yadda za’ayi a kawo.
    A safiyar yau ƴan sandan da suke aiki tare dasu suka kira Faruq da cewar basa tunanin akwai wani abu a cikin wannan tarin jakar cd’s din da suka samu a gidan Awwalu, suka gaya masa cewar sun yi iya bincikensu amma basu iya ganin komai a cikin kowanne CD ba, don haka ba tare da ɓata lokaci ba ya aika a aka dauko masa jakar don shi ya riga ya yarda cewa ba zai taɓa yiwuwa ace an tara Cd’s fal a cikin jaka guda ba tare da wani amfani ba, don haka suka bar wa yan sandan sauran aikin na nemo mai motar da ya ɗauki Awwalun kamar yadda mutumin nan da suka samu a unguwar ya shaida musu cewa ya gane lambar motar.
    Faruk yasa an dawo da Cd’s ɗin office ne da tunanin idan komai ya natsa zasu nemo wajen da zasu iya kaiwa a buɗe musu ko a wacce kasa ne, sai gashi tun ba’a je ko’ina ba, tun ranar da akayi hakan bata kai ga faduwa ba, tun shi kansa bai kai ga zuwa ma yaji me ake ciki ba, Allah ya kawo Abdurrahim cikin wajen, kuma kamar da wasa Faruk yace hannunsa ya kai kan jakar ya buɗe ta yana zaro guda ɗaya a lokacin da suke hira game da kamfanin da kuma dawowarsa.
    Yace kallo ɗaya kawai yayi wa Cdn ya rubuta masa sunansa da kuma abin da ake yi dashi, sannan ya tambaye shi me suke boyewa a cikinsa… Kuma dogon bayanin da yayi masa shi ya kaisu ga kokarin da Abdurrahim din ya fara yi da Computersa wajen kokarin bude cikinsa.
    Kuma kafin karasowar Ma’aruf, kafin zuwansa wajen yayi nasarar bude guda daya da ya fara dauka har sun ji muryar dake ciki, sai dai sakanni goma sha biyar ne kawai a cikinsa inda shiru ya cike fiye da sakanni goma sha biyu, sai a cikin sakanni ukun karshe ne kawai suka ji wata murya daga can nesa tana magana da wasu kalmomi da ba wanda ya iya fahimta a cikinsu balle ma su tantance sautin.
    A yanzu yana kokarin buɗe na biyun ne wanda a cikinsa har ya gano cewar anyi amfani da kusan minti talatin na sauti, don haka a yanzu yana kokarin buɗe kowannensu ne yadda da ya samu Free-dat ɗin da suke nema, za’a karasa bude su nan take.
    “A Kaduna suke ashe mutanen nan, flight nake dubawa daga Kadunan zuwa nan, sun ce zasu aiko da wani yaron su ya kawo…”
    “Ba lallai ne a samu flight da wuri kafin yamma ba, mu duba wani wajen kawai…”
    Ma’aruf ya fara fada amma Abdurrahim yayi saurin katse shi ta hanyar riko hannunsa sannan ya rubuta masa a cikin Tab dinsa cewar.
    _”Nasu original ne, ba’a ko’ina ake samun abin nan ba, wasu zasu iya faking ɗinsa.”_
    Sai kawai Ma’aruf ya zura hannauensa gabaɗaya cikin gashin kansa sannan ya gyada kai kafin yace da Faruq.
    “Shikenan kayi musu booking Flight din zamu jira…”
    Ya fadi hakan wani abu na wucewa ta makogwaronsa da vai san meye ba,kuma a cikin wannan ofgice din suka shafe awanni suna cigaba da aikin tare da Abdurrahim din dake iya bakin kokarinsa wajen ganin yayi decrypting kowanne CD, har sai da ya zama kusan duka aikin tare suka yi shi su uku, wasu awanni da a cikinsu Ma’aruf ya kara fahimtar tarin abubuwa da yawa game da Abdurrahim din wanda ko a baya idan kowannensu yazo gida hutu bai sani ba kasancewar basu cika zama waje guda ba, a kullum shi yana tare da Hajiya Kilishi ne yayin da shi kuma Abdurrahim din ba zuwa nan yake ba.
    Kuma a cikin awannin nan Ma’aruf ya kira wayar Baffa da kuma Ishaq wanda a yanzu su uku ne har da Baba Usman a wajen Hajiya Kilishi fiye da ƙirgensa, hatta mutanen gida sunyi waya dasu yana shaida musu halin da ake ciki gane da Mamin kasancewar bayan zuwan wani likita an sake shiga da ita wata tiyatar tunda sunce ta farka amma still bata iya bude idanunta.
    Sau ɗaya suka sake magana da Amina, bayan ta aiko musu da abincin da yaga banda tuwonsa har kuma da karin wasu girke-girken guda biyu duk da yace mata jar tayi, sai dai sunyi amfani mutuka don dasu Faruk da Abdurrahim suka cika cikinsu tunda ba inda suka fita, daga sallar la’asar har ta magriba anan cikin office din suka yi jam’insu, bayan haka bata kara kiransa ba, bata ƙara cewa komai ba tayi masa uzuri kamar yadda ta fahimci yana buƙata wanda shi kaɗai ya san daɗin hakan da yaji a zuciyarsa.
    Kuma bayan Sallar magaribar ne saƙon ya iso, wani matashi dashi aka aiko da Free-dat ya iso har cikin office din bayan Faruk ya tura anje an dauko shi daga airpot din.
    Ya iso yana ta godiya da kuma murna kamar ya san su dama, a cikin drawer office fin Fatuk din Ma’aruf ya ƙirgo dubu arba’in yace ya sake booking wani jirgin ya koma suma sun gode. Kuma bayan godiya har sai da yayi abinda yasa dukkaninsu yin murmushi kuwa duk da irin zagayen halin da suke ciki.
    Bayan fitarsa ne Abdurrahim ya gama installing Free-dat ɗin nan a cikin labtop dinsa sannan ya shiga saite-saite da kuma taɓe-taɓe cikin kokarin bude CD na farko da suka saka a ciki.
    Karfe takwas da rabi na dare a sannan, kuma a wannan lokacin tabbas ne da za’a auna jinin kowannensu zai yi sama fiye da zatonsu, idanunsu gabadaya yana kan labtop din yayin da koren layin ke tafiya a hankali zuwa inda zai kai karshe kafin sautin ciki ya buɗe.
    Idan ka ɗauko hoton office din daga sama sai ka kalla sosai sannan zaka iya gane inda suke ma, don a hargitse yake gabadaya da tarin takardu da kuma wayoyin abubuwan da aka jojjona a cikin computer Abdurrahim, sannan ga kwanuka da flask din abincin da suka ci kowanne ya kalli hanyar garinsu.
    Wannan koren layin na kan lamba ta 75 lokacin da wayar Ma’aruf tayi kara a aljihunsa, ya zaro ta hannunsa na wani abu kamar rawa ya kalli sunan da ya fito… Ishaq ne.
    “Hello… Ya akayi?”
    Bai ma san hakan ya faɗa ba lokacin da ya kara ta a kunnensa.
    Ishaq ya shafo nasa gashin daga can cikin asibitin da yake tsaye, idonsa ya kai kan Baffa da kuma Baba Usman dake kokarin shiga office din wani likita da yasa akayi kiransu kafin yace.
    “An fito daga aikin Ma’aruf….”
    “Alhmdlilah….”
    Muryarsa ta faɗa da karfin da yasa daga Faruq har Abdurrahim din juyowa su kalle shi.
    Ishaq ya girgiza kansa daga can kafin yace.
    “Mami ta rasa idanunta B, bata gani….”
    Muryar Ishaq din ta fada a daidai lokaci guda da wannan koren layin ya kai karshe a jikin Computer Abdurrahim, kuma babu wani bata lokaci sautin dake kai ya shiga playing tar a cikin office, cikin murya guda da hatta Abdurrahim da ya debi shekaru baya gida kai tsaye zai shaida cewa Hajiya Kilishi ce, Mami… Mami dai! Mamin Ma’aruf!
    _”…A banza na sa aka kashe min Jamal Awwalu? Ko kuwa a banza na rufe idon Ma’aruf daga ganin kowa hatta uwarsa kuwa? Ba duk akan wannan burin nawa bane ko kuwa ka manta kaima ɗin alfarmar burin nawa kake ci har yanzu… To ta yaya zaka ce min mu dakata tukunna?_
    _Ka sanni bana jira Awwalu, bama ni da kwanakin dazan sake wani jiran…. Ishaq ya kira waya yace Ma’aruf ya farka, kuma Baffa ya gaya masa cewa duk yadda zasu yi likitoci su sallame su tsakanin gobe ko jibi su taho don haka bani da lokaci Awwalu, ka nemo duk mutanen nan dole ne kuɗin kamfanin Bakori su shigo account dina a goben nan….!_
    A daidai wannan lokacin ne daga can waje wani mai adaidaita sahu ya faka a gaban ginin kamfanin, Awwalu ya fito daga ciki idanunsa na kallon dogon ginin wajen da ya haska tar! da fitulu….
    A wannan lokacin ne kuma daga can unguwar Nasarawa GRA, Ashraf ya buɗe ɗakin nahaifiyarsa Hajiya Nafisa, tana tsaye daga jikin mudubin dakin tana feshe jikinta da turare sakamakon shirin da take yi na zuwa wajen mijinta wanda ya dawo ƙasar a wannan ranar.
    Buɗewar kofar tasa ta juyo ta kalle shi a lokaci guda kuma sakewar fuskarta na canjawa da yanayin mamaki sakamakon yadda ta ganshi kusan a birkice.
    “Lafiya Ashraf daga ina?”
    Ta tambaya, sanin cewar a dazu ya bar gidan bayan yazo yayi wa mahaifin nasa sannu da zuwa.
    “Mamaah ina kika ce Ruƙayya ta tafi?”
    Wani asibitin kawarta a Abuja, don a duba ta sakamakon ciwon kan da take yawan fama dashi…. Haka tace musu a ɗazu bayn da kowa ya hallara a falon mahaifin nasu suna murnar tarbarsa, har Ahmad na cewa dole tayi ciwon kai tunda ta saka damuwa a ranta,mahaifin nasu kuma yace a kirawo ta a gaya mata ya dawo don haka itama ta dawo.
    Fuskarta a ɗaure kaɗan tace.
    “Ba munyi zancen nan da ku ɗazu ba? Me zata yi maka?”
    Sai kawai ya ɗago wayarsa dake hannunsa ya nuna mata.
    “Abokina ne ya turo min hotunan wani hatsari da ya haɗa da kawunsa a Niger dazu… Mamaah har da Rukayya a ciki….!”
    Ya fadi hakan a lokaci guda da idonta ya sauka akan hoton Rukayyan dake kwance a gefen titin tare da alamun mutane kwance a gefenta, taba sanye da wata doguwar rigarta da ta sani ta atamfa wadda ta yayyage ta kuma ɓaci gabaɗaya da jini, idanunta a rufe suke yayin da fuskarta take a daddauje wajaje da yawa,yanayinta bashi da maraba da na sauran gawawwakin daje zube a wajen…!
    MASU ƁUKATAR A TALLATA MUSU HAJOJINSU ZA SU IYA TUNTUƁARMU TA LAMBOBIN 07045308523 MUN GODE

    Note
    error: Content is protected !!