Farar Huta 2 – Chapter Twenty-three
by NadminMASU ƁUKATAR A TALLATA MUSU HAJOJINSU ZA SU IYA TUNTUƁARMU TA LAMBOBIN 07045308523 MUN GODE
Haske ya ratso cikin ɗakin, ta tsakanin labulen dake dagewa a hankali sakamakon iskar dake kada su kasancewar windon a bude yake.
Farko hasken rangwame ne kafin a hankali cikin abinda bai minti biyar ba ya shiga karuwa a hankali, yana yin yawan da ya fara damun fuskokin mutane biyun dake kwance akan doguwar kujerar falon, Amina da kuma Hameeda duka su biyun sun kudundune ne cikin sigar da a kallo daya zaka san cewa bacci ne ya dauke su a wajen ba tare da sun shirya masa ba.
Hasken yasa Amina ƙifta idanunta a hankali kusan sau hudu kafin ta bude su,ganinta na sauka akan Hamidan da kanta yake daf da tata fuskar ta yadda saman gashin kanta kawai take iya gani.
Idanunta suka tsaya a layukan dake tsakanin kalbar kanta tana ƙoƙarin saita tunaninta kafin ta tuna dukkanin halin da suka shiga a daren jiya.
Ma’aruf bai dawo ba, babu shi babu kuma su Baffa, da misalin karfe goma na daren jiya suka fara buga wayoyinsu ita da mutanen cikin Gida, ta Baffa da kuma Baba Usman basa shiga kwata-kwata, wayar Ishaq da kuma Ma’aruf ɗin kawai ake samu suna shiga suna katsewa har ƙarshe amma babu wanda yake dauka.
Da farko suna kira ne don su ji halin da Hajiya Kilishi ke ciki amma ba’a fi minti goma ba sai ya koma suna kiran ne don su san halin da su ɗin ma suke ciki.
Hankalinsu ya tashi zuwa nisan da ba zai kwatantu ba, sai daga ƙarshe da Munaya tayi tunanin a kira Malam Sani sannan suka samu shi ya dauka a bugun farko da bai katse ba, kuma kai tsaye ya gaya musu cewa ai sun riga sun baro asibitin tare dasu Baffa, ya gaya musu cewa bai san dai me ya faru ba amma ya fahimci kamar wani ne ya kira su da cewar su taho kamfani don tare har da Ishaq suka taho kamfanin yana bin bayansu a motarsa.
Da magiya Hajiya Maimuna ta roke shi akan ya hau zuwa saman ya bawa ɗaya daga cikinsu wayar amma bayan yaje ɗin yace kofar koridon da take kaiwa ga ofishin da suke ciki ma gabaɗaya a kulle take don haka ba zai iya shoga ba.
Wani abu da ya kara tsurar dasu kenan, suka yi firgi-firgi dukkaninsu mata kawai a cikin gida don hatta su Hamida dake harkokinsu tare dasu Sahla sai da suka sami waje suka nutsu… Hajiya Maimuna tace tafiya zata yi, tasa Munaya ta kira wani ɗan yayarta da suke kira da Abdoul akan yazo ya dauke su su tafi.
Sai dai inda Allah ya taimaka, minti biyar bayan hakan kiran Baffa ya shigo cikin wayar Hajiyan, tana tuna idanun kowannensu a lokacin nan, da kuma sautin karar bugun zuciyarsu da bayan nata da ya cika kunnuwanta tana jin kamar tana jin na Surayya da kuma Samiran dakezaune a kowanne gefenta.
Kuma sai Allah ya taimaka suka ji abinda dukkaninsu suke fata, Baffa ya shaidawa Hajiya Maimuna cewa babu komai ba abinda ya faru gasu nan zuwa, a lokaci guda sai hankalinsu ya kwanta kowa ya shiga hamdala yana godewa ubangiji, amma tun a lokacin haka kurum taji cewa ita bata gamsu da hakan ba, jikinta bai sake ba kamar yadda na su Samira yayi a lokacin.
Tayi niyyar su zauna acan har ƙarasowarsu amma sai Inna Danejo tace dare yayi, gwara Ma’aruf yazo ya same ta a gida bayan dukkan gajiyar da yasha, don haka su Munaya suka rako ta tare da Hamidan da tayi bacci a lokacin, kuma sai da suka shigo suka koma sannan ta tuna da wayarta da ta bari a cikin gidan.
Da tunanin dawowar Ma’aruf cikin abinda ba zai fi ƙasa da minti talatin ba yasa bata yi niyyar komawa ba, ta canja kayan jikinta zuwa na bacci sannan ta canjawa Hamida ma, tun rana take jin wani abu kamar zazzabi na shirin kamata, ko abinci bata ci mai yawa ba don haka kurum taji bata son kamshin miyar da aka yi a cikin gidan, tana da ragowar abincin da tayi wa su Ma’aruf aka kai musu amma ta saka a fridge ta sani yayi sanyi yanzu.
A yadda take jin kowacce gaɓa a jikinta tayi nauyi sai kawai taji gwara ta hakura da abincin don haka ta dawo falo ta kwanta, kuma tun tana kirga minti biyar da goma har ta koma sha biyar da ashirin, har idanunta suka fara rufewa babu alamun dawowar Ma’aruf, kuma a lissafin da take yi na komawa cikin gida ta dauko wayar bacci ya dauke ta, bata farka ba sai karfe biyu na dare da kukan Hamida ya tashe ta, kafafunta na sasarfa ta koma dakin inda ta same ta zaune akan gado tana kiran sunan ‘Mammy’.
Sunan da tana ji ta san mahaifiyarta take nema tunda ba haka take gaya mata ba, da kyar ta lallaba ta ta koma baccin, wanda a lokacin ne kuma tashin hankali ya daki tsakiyar kanta da tunanin halin da ake ciki da yasa Ma’aruf bai dawo ba har a sannan.
Ta zura hijabinta sannan tayi hanyar kitchen da niyyar nufar cikin gidan, amma tana buɗe ƙofar baya ta kitchen ɗin, da duhun daren lokacin ya shiga idanunta da kuma shirun dake waje, sai ta kasa fita, ta rufe ta sannan ta dawo zuciyarta na gaya mata cewa dukkan halin da ake ciki zata sani idan garin Allah ya waye.
Sai dai bayan ta dawo ta zauna din, ko da wasa bacci ya kasa daukarta, hankalinta ya kasa kwanciya, ta dinga zama tana canja waje, tayi sallah raka’a biyu kuma ta kasa kara wata daga hakan, tana zaune kawai akan sallayar zuciyarta da yatsunta cike fal da lissafin abinda zai iya faruwa, a haka Hamida ta sake farkawa tana kuka, wannan karon sai da ta ɗauke ta suka dawo falo sannan ta sake komawa, kuma minti biyar bata yi ba ta sake tashi da wani kukan.
Wani abu da ya sake tsorata ta kenan don tun sanda tazo gidan ko sau ɗaya bata taba tashi cikin dare ba, hannayenta na rawa ta samu da kyar ta bata lemo sannan tayi shiru kwance a jikinta, abinda ya hana ta sake tashi kenan saboda tana tsoron idan ta yi motsin da zai tashe ta ba lallai ne ta sake komawa ba, kuma zaman waje ɗayan yasa dukkan tarin bugun da zuciyarta ke yi da kuma saka da warwarar dake ranta bacci ya sace ta a cikinsu wanda bata farka ba sai yanzu.
Sai a yanzu da idanunta da kuma zuciyarta suka cika da wani irin nauyi da bata taɓa jin sa ba a rayuwarta, ta miƙe da sauri wanda hakan ya farkar da Hamida da kanta ya sauka daga jikinta.
Karfe bakwai da minti uku na safe…
Lokacin da agogo ya nuna a ciki idanunta kenan, ta kalli ko’ina a falon, su kadai ne har yanzu babu Ma’aruf kuma babu alamun wani ya shigo, wani abu ya zarce ta makogwaronta yana ƙoƙarin zana kalar tashin hankalin da take shirin fuskanta a cikin kirjinta, wajen da ta bar wayarta ta tabbata su Samira zasu gani, idan komai lafiya kamar yadda Baffa yace ya kamata ace su Samira sun kawo mata wayar, ko ma wani ya shigo ya gaya mata dalilin rashin dawowar Ma’aruf din.
Wani tunanin ya daki kwakwalar ta a lokaci guda, me yake shirin faruwa ne? Ko ma me ya faru din? Sai yanzu take ganin me yasa Inna Danejo zata ce a rako su su dawo gida a jiya bayan su Baffan basu iso ba? Idan da gaske ne komai lafiya yake me yasa har yanzu Ma’aruf bai dawo ba? Ko kuma a kawo mata wayarta? Manta ta tayi ma ko kuma me ya faru?
Ba shiri bugun zuciyarta ya karu a lokaci guda, duk wata alama da zata tabbatar mata da cewar ranar yau daban ce ta shiga haskawa a idanunta, hatta yanayin hasken ranar ta ganshi daban da yadda ta saba saninsa a irin wannan lokacin, me yake shirin faruwa ne? Mutuwa akayi? waye ya mutu? Hajiya Kilishi? Idan ita ce me yasa za’a boye mata…. tsaya! Ko dai Ma’aruf ne?
Ba shiri ta ɗaga kafafunta zuwa daki don ta dauko hijabinta tayi nufi cikin gidan,don duk da hankalinta na neman barin jikinta ta sani ba zata iya fita a haka ba, rigarta bata ko kai gwiwa ba, duka kayan baccinta haka suke, haka take saka su don ta fahimci cewa zata iya raba soyayyar da Ma’aruf yake yi mata da kuma wadda yake yiwa kafafunta daidai.
Sai dai me? Tana motsa kafar tata wani irin jiri ya ɗebe ta, da kyar ta iya ƙokarin tsayawa akan kafafuwanta kafin ta fahimci yunwar da take ji, don siraran yatsunta har rawa suke yi banda jikinta da take jinsa yana komawa kamar fallen takarda, ba shiri ta fasa tayi hanyar kitchen Hamida da ta farka a lokacin itama ta biyo tana mutsikka ido.
Tana shiga kitchen din ta buɗe fridge ta zaro container da ta zuba abincin a ciki, jollof din shinkafa da taliya ne sai tayi sauce din nama da vegetables, bata ko tuna da sauce din ba a yanzu ta nufi tukunyar da tayi girkin da ita jiya, har yanzu tana kan gas din bata wanke ba sakamakon kiran da Samira tayi mata a jiyan cewa an sake shiga da Hajiya Kilishi tiyata.
Sau ɗaya ta dauraye ta ɗora ta akan wuta, ta zuba abincin akan na ciki wanda ya kama, jikinta na rawa ta tsaya tana kallonsa kuma sai zuciyarta ta gaya mata cewa ba zata iya jira ya ƙarasa ba don kamar za’a zare numfashinta haka take ji, sai kawai ta kashe wutar sannan ta dauko tukunyar gabadaya ta zauna a kasa, akan tiles din wajen tasa hannunta ta fara cin abincin a haka tana ci hannunta na rawa bata ko jin sanyin dake jikinsa.
“Mammy zan ci nima..”
Hamida ta fada tana zama itama a gabanta har da tankwashe kafa, ta shiga bata a baki da hannunta, babu wanda ya gama wartsakewa a cikinsu babu wanda yayi ko brush, wani abu da yasa hawayen da bata da tabbacin na meye suka gangangaro kan kumatunta duka biyu a lokaci guda, babu abinda ta gani, babu abinda taji amma ta riga ta sani cewa ba sai wani ya gaya mata ba, ba sai ta jira komai ba, faruwar al’amari irin wannan da kuma yadda jikinta yake mata tun a jiya alama ce ta cewar wani babban al’amarin ya faru… don ko a wasan kwaikwayo ta sani cewa abubuwa basa tafiya daidai idan komai yazo ƙarshe.
Tasa ɗaya baya hannunta ta shiga share hawayen amma kamar ta ziga shi ne sai yawansa ya ƙaru, ya cika idanunta taf ya zama bata ko iya ganin Hamidan dake gabanta sai dishi-dishinta tsayuwarta a wajen, sai kawai ta kifa kanta a jikin tukunyar ta fashe da kuka gabaɗaya.
Kukan da a cikinsa da kuma tambayoyin Hamida ta tsinci bugun kofar da ake yi daga waje…. Ba shiri ta ajiye tukunyar ta sauko daga saman da take, Kafafunta na sassarfa ta fita daga kitchen ta karasa cikin falon.
Bata san me take jira ba kuma bata san me ta zata ba har sanda hannunta ya bude kofar, kuma siffar mutane biyun dake tsaye a waje, Munaya tare da wata ƴar uwar Hajiya Maimuna da suke kira da Auntyn Sama, kallon da suke mata kadai yasa zuciyarta ta kulle tamau waje guda, komai ya tsaya a cikin kanta cak!
Ba abinda take iya gani sai fuskar Auntyn Saman da take a birkice da kuma kumburarrun idanun Munayan dake shaida cewa har a lokacin kuka take itama… Shikenan! Abinda take hasashe ya faru….
Sai kawai kafafunta suka kasa daukanta ta sulale a lokaci guda zuwa dandaryar ƙasan wajen…. Kuma kafin komai ya ɗauke daga idanunta tana iya tuna cewa taga fuskar su Munayan akanta suna girgiza kai cike da ƙarin tashin hankalin da ya ninku a idanunsu sannan taji muryar Hameeda na kiran sunanta.
***
“Babu wani labari har yanzu…”
Abinda Baba Usman ya faɗa kenan a cikin wayar dake kare a kunnensa, ya gyada kansa sau ɗaya sannan yace.
“Eh, shi DSP ɗin yanzu yace an samu mutum daya yanzu a can wajen hanyar kura da yace yaga wucewar motar, wai wani mai mashin ne ya dan hada go-slow akan hanya to idan motoci sun taho suna tsayawa amma yace ita motar taba zuwa kawai sai tayi kwana ta biyo ta cikin mutane, yace ta kan kayayyakin sa da yake siyarwa anan bakin hanya tabi ta kai shi yasa har ya iya ganin lambar dake jikinta, shi kansa ma yace sauran kwanansa a gaba ne yasa bata bi ta kansa ba…”
Yayi shiru yana sauraren bayanin da ake yi a cikin wayar kafin ya sake cewa.
“To, yace dai an saka ƴansanda a kan hanya har zuwa Kuran, to amma tunanin da muke yi shine ba’a sani ba idan iya nan suka tsaya, ko kuma sun wuce ma Kuran…”
Ya gyaɗa kansa sannan yace.
“Gaskiya ne… Yanzu dai alfarma muke nema ka saka baki a sake bamu wasu ma’aikatan kamar na division biyar haka, babu matsalar payment, za’a basu ko nawa ne.”
Ya fadi hakan daidai lokacin da Ishaq ya shigo cikin falon na Baffa.
Kuma ko daga nesa idanunsa kadai zaka kalla ka san cewa duniyarsa ta birkice ne a lokaci guda tsakanin joya da yau, yana cikin tashin hankalin da zai rantse har da ubsngijinsa za’a samu fiye da kutane dubu da zasu zo duniya su gama rayuwarsu har su koma ga mahaliccinsu ba za su taba fuskantar irinsa ba.
Jiya watarana ce da babu daya daga cikinsu da zai yi tunanin zata shafe daga tarihin rayuwar ahalinsu bakiɗaya ba ma su kaɗai ba.
Faruk ya kira su a waya bayan lokacin da ya kira Ma’aruf yake shaida masa result din da aka samu game da tiyatar da aka yiwa Mamin da suke wajenta tun safe, bai samu wata kwakwarar amsa a wajen Ma’aruf din ba wayar ta katse, bayan kamar minti goma a lokacin da su Baffa suka gama da likitan nan suke shirin komawa gida, a lokacin Faruk ya kira shi da rokon cewa kar ya bari su Baffa su tafi ya kawo su Kamfani a yanzu-yanzu…
Kuma da ƙyar ya samu su Baffan suka yarda suka bishi, a cewarsu halin da ake ciki da kuma jiran da mutanen gida suke yi zai tsayar da ko meye a kamfanin, sai da Baba Usman ya saka baki da cewar ya san su Ma’aruf baza su kira su akan wani abu da bashi da muhimmanci ba sannan Baffan ya yarda suka tafi.
Yana tuna yadda suka shiga cikin administrative office ɗin suka same su komai a barbaje, koina kaca-kaca kafin ma su kai ga fahimtar abinda ke faruwa, kuma shi kansa a yanzu ba zai iya banbance tsakanin bayanin mutumin da suka tarar wa a cikin Office ɗin mai suna Awwalu wanda ya san su Ma’aruf sun dade suna nema da kuma bayanan muryar Hajiya Kilishi dake cikin wasu tarin CD’s da Abdurrahim yayi ta sakawa ɗaya bayan ɗaya wanne ya fara ji ba.
Idan wani zai ce ya kwatanta tashin hankalin da ya shiga da kuma mamaki a wannan lokacin ya sani cewa a matsayin sa na lauya shi kansa ba zai iya kare kansa ba,
Balle kuma su Baffan da ya san al’amarin yafi shafarsu akansa, kowannensu kasa magana yayi, baya iya tuna kalma guda da wani ya furta a wannan lokacin banda Baffa da ke maimaita ‘Inalillahi wa’inna ilaihir raji’un’ cikin amon muryarsa dake ratsa zuciyarsu ta kowanne bangare, bayan haka kuma sai lokacin da Faruk ya kira ƴansanda a waya da cewar su tafi da Awwalun da ya kammala yiwa su Baffa duk bayanin da zai yi a lokacin.
Wanda a sannan ne kuma Ma’aruf ya miƙe, babu wanda ya san inda za shi a lokacin don shi bai maganshi ba sai da ta isa wajen kofar office ɗin, babu wanda yayi wa magana, babu alamun ma ya san da su zaune a wajen don baya tuna cewar ko bayan da suka shigo tare dasu Baffa ya ɗago da kansa, su Abdurrahim ne kawai suka yi musu magana kafin tashin hankalin dake yawo a cikin ɗakin ya ziyarce su.
Kuma babu wanda yayi tunanin su tsayar dashi a lokacin, babu wanda yayi tunanin komai sai bayan fitarsa da minti biyu sannan shi da yake zaune hankalinsa ya dawo jikinsa, ya fita da sauri ya bishi amma bai ga komai ba sai maigadi da ya hango daga can yana ƙoƙarin maida gate din wajen zai rufe… A lokacin ya san cewa dukkanin su sunyi babban kuskuren da zai shafi al’umma da yawa a wannan daren.
Ilai kuwa! Ƙasa da minti talatin bayan hakan, a lokacin da Baffa ke ƙoƙarin kwantarwa dasu Hajiya dake can gida hankali, a lokacin kiran DSP ya shigo wayarsa da sakon cewa Ma’aruf yayi wa mutane biyar jina-jina a asibiti ciki gar da ƴansandan sa guda biyu sannan kuma ya ɗauki mara lafiyar da suke gadi wadda suke zarginta da ta’ammali da mugayen kwayoyi kuma ya har yayi nasarar fita da ita daga asibitin ba tare da an iya tsayar dashi ba.
Ishaq ya sani cewa idan za’a zaunar dashi zai kwana yana saka hannu a takardun da zasu bada tabbaci na cewar Baffa mutum ne jajirtacce irin wanda bai taɓa gani ba a rayuwarsa, a iya abinda ya sani na tarihin rayuwarsa yana da lissafin tarin wasu abubuwan da ba kowa ne zai iya fuskantarsu a duniyar nan kuma rayuwarsa ta cigaba da tafiya daidai ba, amma Baffa ya fuskance su, yabi ta cikinsu ba tare da wani abu guda daya ya goce daga rayuwarsa ba, ko a iya harkar kamfaninsa kadai akwai tarin abubuwan da mutane da yawa zasu iya kasawa a bugu daya, amma da kafafunsa ya tsaya, ya jajirce, har komai ya kawo matsayin da yake a yanzu.
Amma a lokacin da DSP ya kira shi da wannan bayanin, a jiya cikin wannan daren faduwa yayi har kasa daga yadda yake mike bayan ya amsa wayar Hajiya Maimuna, babu wanda ya gani babu wanda ya lura, sai da ya kai har kasa wanda hakan shine kalubale na biyu da suke fuskanta, don tun jiyan bai farka ba, sun kwana dashi a asibiti bayan likitoci sunyi kokarin dawo da numfashinsa, amma tun a daren jiyan Hajiya Maimuna take magiyar a dawo dashi gida, don haka a dole likitan da ya kwana dasu a asibiti ya biyo su gida dab da sallar asubahi aka kwantar dashi a dakinsa tare da sauran hade-haden da akayi masa a asibitin.
Sunyi masa allurar bacci mai ƙarfi da aƙalla zata ɗauke shi tsawon kwanaki biyu don likitan ya tabbatar da cewar idan har ya farka a yanayin da yake komai zai iya faruwa, saboda halin da zuciyarsa ta shiga.
A yanzu haka kuma cikin gidan ya koma tamkar gidan makoki ne don iya abinda suka ji ya tayar da hankalinsu mutuka, tunda dama tun a jiyan sun kwana ne a zaune.
Yanzu dashi da Baba Usman da kuma su Faruq suke ta fafutukar neman Ma’aruf da kuma Mamin ko ta wacce hanya, kuma hankalinau na tsaye ne kamar yadda suma suke a tsaye, Abdurrahim na kan Computer tun a daren jiyan yana kokarin gano signal din wata karamar waya mai ɗauke da layin Ma’aruf din na biyu wadda ake tunanin cewa tana cikin motarsa, saboda ana ta kira ba’a dauka wani lokacin ma bata shiga.
Sai dai duk kokarinsa ya kasa kama signal din wayar har yanzu saboda matsalar Nigeria da ba koina ake samun service ba idan har ba mutane bane a wajen… Faruk kuwa yana can sunyi hanuar Kuran tare da ƴan sandan, shima a yanzu dawowarsa daga asibiti kenan wajen mutanen da Ma’aruf ɗin yayi wa rauni a daren jiya, dole ana bukatar sa hannun wanda yake da alaka dashi ne a wadu takardu da za’a cike a asibitin don haka DSP din ya kira waya yace a tura wani.
“Su biyar din ne kamar yadda suka ce?”
Baba Usman ya tambaye shi bayan ya karaso cikin falon Baffan inda ya same shi, kuma shima bayan ya gama wayar da yake yi. Kansa a sunkuye ya daga shi.
“Eh, bayan ƴansandan biyu sai maigadin kofar wajen da aka ce yayi kokarin hana shi shiga,sai kuma wani Nurse guda ɗaya.”
Baba Usman ya gyada kansa tare da ajiyar zuciya sannan yace.
“Nayi magana da sakataren IG ɗin, ina ga kamar ya karbi case din da muhimmanci don haka yace da zarar ya shigo office zai yi magana dashi a sake bamu wasu ma’aikatan.”
Lebbensa a bushe kamar makogwaronsa Ishaq ya gyada kansa a hankali sannan yace.
“Mun yi waya da Faruk Baba, yace min sun wuce Kura ma yanzu wai wani manomi yace musu yaga shatin tayar mota a cikin gonarsa kafin ya fito, don haka zan bi bayansu…”
Idan ka kalle su a wannan lokacin daga Baba Usman din ha Ishaq din ka san kawai kowanne yana amsa sunansa ne na ‘Namiji’ amma bayan hakan babu abinda zai hana su fitar da tarin hawauen dake kwance a cikin kirjinsu, kuma a wannan lokacin ne, kafin Baba Usman ɗin ya buɗe baki ya bashi amsa suka jiyo wani sabon kukan daga cikin gida wanda kafin ya iso inda suke Hajiya Madina matar Baba Usman ta kira shi da cewar Amina ta faɗi!
MASU ƁUKATAR A TALLATA MUSU HAJOJINSU ZA SU IYA TUNTUƁARMU TA LAMBOBIN 07045308523 MUN GODE
