Search
You have no alerts.

    MASU ƁUKATAR A TALLATA MUSU HAJOJINSU ZA SU IYA TUNTUƁARMU TA LAMBOBIN 07045308523 MUN GODE

    Ruwan ya cigaba da dukan rufin dakin da wani irin ƙarfi fiye da kodayaushe. Karar tsawa da ake yi lokaci-lokaci tana cika iska da sautin da duk karfinsa baya disashe tarin surutun daje cikin dakin, tarin surutun dakin kurkukun wanda yake cike da fuskokin mata kala-kala. Manya -manya da yara farare da bakake, dattojai da yanmata wanda kowanne a cikinsu yake cigaba da rayuwarsa daidai kamar babu wanda yake da digon koda memory guda na wani abu daga bayan dogwayen katangar da suka zagaye su, kamar nan din shine mafari kuma farkon rayuwarsu, kamar basu san akwai wata duniya dake wanzuwa bayan su ba.
    Rayuwa bata da adalci, bata dashi ko kadan, wannan shine abinda Kilishi je maimaitawa a cikin kanta da fitowar kowacce rana da kuma faduwarta. Ta yarda rayuwa bata da adalci don babu abinda ke saka ta tsayawa, komai girmansa kuma komai kankantarsa ba abinda ke tsaida ita kamar dai ruwan daje zuba a yanzu, abubuwa suna cigaba da tafiya ne ba tare da wani ma yaje ko kusa da wajen da zai ji labarinka ba.
    Damina ta dade da tsayawa ta yadda kusan kullum ake kwara ruwan dake daukar awanni, kuma a duk lokutan da ruwan ke sauka, Kilishi na samun waje ne dab da wata yar karamar taga dake can sama ta zauna, ta zauna tana kallon tasirin zubar ruwan da kuma nauyinsa da take ji a zuciyarta, tana ayyanawa kanta cewa hawayenta ne wannan ke zuba, don irin kukan da ya kamata tayi kenan tunda a kirjinta dama idanunta babu danshi ko kadan balle ayi tunanin hawaye.
    Ta kan so ayi ruwan lokacin da suke fita waje don ta zauna a cikinsa ya sauka a jikinta, ya sauka akan fuskarsa ta yadda zata ji sosai kamar hawayen nata… Idanunta a tsaye kyam suna shsida kamannin da ta sani cewa ba nata bane, ba itace wannan Kilishin da tayi wata rayuwa da zata rantse da ubangijin da ya halicce ta babu wata mace a cikin kurkukun nan da tayi makamanciyarta.
    Ba itace wannan Kilishin dake samun komai a zama daya da zuciya da kuma kwakwalarta ke sama mata mafita ba, sannan ba itace wannan Kilishin da ta shafe tsawon shekaru wajen gwagwarmayar samawa karshen rayuwarta tare da yayanta wata daddadar rayuwa da bata ko misaltawa ba.
    A yanzu ita wata sabuwar halitta ce kawai, wata sabuwar halitta da ta rasa kowa kuma ta rasa komai, amma kuma zuciyarta ta kasa yarda ta karbi hakan, don idan ma zata yarda tana tunanin ya kamata ace ko da rabin mutanen duniya su jajanta mata, amma ba wai rayuwa ta cigaba da tafiya tamkar babu wani abu da ya faru ba.
    _A tuhume ta akan kisan ɗana kawai yallaɓai…_
    Tun da aka fara wannan tashin hankalin, wannan maganar ta Baffa ita kadai ce abinda ya fitar da hawaye daga idanunta bayan maganganun Ma’aruf, yace a ture dukkan wasu laifukanta a gefe, a tuhume ta kisan Jamal kawai wanda ta san yayi haka ne don ya tanadar mata wani abun daban.
    Ko a lokacin da aminiyarta Salamatu ta baiyana a gabanta da tare da yanuwanta game da zancen raba ta da dan ta tsawon shekaru bata ji wsni abu sosai ba,don me take tunanin? Awwalu zai cigaba da lullube duk wani sirri nata da ya sani ne? Bakin cikinta daya ne ma da ya zamana akace Salanatun taga ɗan nata, wani abu da duk da mamakin da ya bata sai da taji ciwonsa har cikin kirjinta.
    Salamatu bata taba taya ta mugunta ko guda daya ba,hasali ma ta kan kushe mata wasu idan ta kawo su, amma duk da haka tare suka faro tafiyar tana gaya mata dukkan sirrinta da kuma abinda take ciki don haka ko yaya ne yaci ace itama ta karbi nata kamashon bakin cikin, ba’ace ita da Awwalun dai sune kadai zasu dandani zafin shari’ah ba.
    A lokacin da dansandan nan yaki karbar tayin kudin da tayi masa, a lokacin da ya kalli nambobin da ta rubuta ya dago ya sake kallonta sannan ya girgiza kansa, a lokacin wata wuta ta kunno a cikin kirjinta, wata wuta dake zafi tana kona duk wani ragowar emotion da take dashi tana kuma kara zafin kunci dake cikin zuciyarta wanda karara yake nuna mata cewa da gaske ne tata ta kare babu wata sauran mafita kuma.
    Daga wannan lokacin ta koma kamar wata gunki da aka sassaka ko kuma karfen dake motsi kawai, numfashi kawai take tana kallon tarin mutanen dake zuwa koyaushe wajen mata tambayoyin da bata ko fahimtarsu, ciki har da ƴan jaridar da tayi zaton zasu watsa labarin nata zuwa kusufa-kusfar da zai sa duniya ta tsaya wajen jimanta mata, amma kamar yadda tace rayuwa bata da adalci, ba abinda ya faru!
    Bata yi magana da kowa ba sai da akaje kotun sannan ta amsa dukkan tambayoyin alksli kai tsaye babu wani musantawa ko kuma kokwanto, tana bayar da amsar tana kallon idanunsu Baffa, Baba Usman, Ishaq, Abdurrahim da kuma tarin wadu yanuwanta da acikinsu har da mahaifin Amina, Alhaji Sulaiman.
    To don me ba zata amsa ba, ai ba su kawo wanda zasu daure ta da jijiyoyin ta a jikinta ba, basu kawo wanda da yana wajen ta sani bakinta ba zai taba budewa ta amsa laifukan da aka zaiyano a cikin kunnensa ba… Ma’aruf!
    Ya sani, ya san komai, ya san komai din da ya zamana ta san baya cikin haiyacinsa ma a lokacin, amma duk da haka da ace yana wajen, yana cikin kotun nan a lokacin da ake sauraren shari’ar, zata rantse da ubangijin da ya halicce ta cewa ko alkalin zai ce a kwantar da ita ana yankar naman jikinta ɗai-ɗai da ɗai-ɗai, ba zata taɓa iya amsa wadannan laifukan a gaban idon Ma’aruf ba.
    Amma har Baffa tana kallonsa ne kawai tana amsawa tare da tunanin abinda zai ji amma ba wai ita ba, har aka gama shari’ar aka yanke mata hukucin shekaru goma sha takwas bata jin ko da wucewar sakan guda taji nauyin wani daga vikin mutanen dake wajen nan.
    A yanzu ma ƴaƴan ta kawai take tunawa, tana jin yadda rashin ganinsu ke ɓangarar da wani abu a cikin zuciyarta, yanuwanta da yawa sun zo, musamman wadanda take yiwa alkhairi, wasu ma bata ko fita ganinsu saboda bata ga abinda hakan zai tsinana mata ba.
    Don haka a yanzu rashin ganin yayan nata shine abu mafi tashin hankali da take fuskanta bata ko lissafin shekarun da zata kwashe a cikin wajen nan,don gani take kamar an fade su ne a kotun nan kawai, kamar an fade su ne kuma an rubuta amma baza su kasance a gaske ba… Gani take kamar zata iya fita, kamar idan ta yunƙura zata samu hanyoyin da zata fitar da kanta.
    Amma matsalar shine har yanzu zuciyar tata ta kasa fahimtar komai a wajen na balle har ta fara tunanin hanyoyinta, Baffa yana kassarata da wucewar kowanne lokaci a duniyar nan wajen hana ta ganin fuskokin ƴaƴan ta, ita Kilishi ce, mai zurfin tunani da hangen nesa, shi yasa a lokacin da yace a ture dukkan wani laifi a hukunta ta akan abu daya kawai ta zubar da hawayenta.
    Shi mijinta ne, ta san halinsa tsawon shekaru,ta san yadda yake iya hukunta mai laifin dake hannunsa cikin salama ba tare da kowa ya sani va, hukuncinsa mai sanyi wanda zai daskarar da jinin jikinka hankali kwance yadda duk ihunka babu wanda ya isa ya ji ka, shi yasa yake da kai zuciya nesa a komai na rayuwarsa, da wuya kaga ransa ya baci akan wani abu don idan har ya bacin to shi kansa ya sani cewa hukuncin da zaiyi daban ne,ta san wannan… ta san wannan tun a shekarun farko data aure shi.
    Shi yasa zuciyarta take rabewa da kowanne motsawar lokaci idan ta tuna hakan, idan ta tuna yadda rayuwar kowa ke cigaba da tafiya babu ita kuma kamar ba’ayi ta din ba, don yanuwanta sun gaya mata cewa har sake gini anyi a gidan an rushe bangarenta.
    Mamakin yadda rayuwa ke juyawa dan adam baya a lokaci guda shi ke dada cinye ta, kamar badu saba ba, kamar ba itace mai yarje mata komai ba, kamar ma bata santa ba, ace komai ya ƙare a lokaci guda? Komai din da zai hada har da ya’yanta, banda wannan tarin dukiyar da ta shafe shekaru tana ajiyarta, shi yasa a kullum take fada tana karawa rayuwa bata da adalci, bata dashi ko kankani….
    Tana zaune ne kawai a yanzu ba tare da wata mafita ba, abu biyu kawai take hasashe shine watakila idan har ta mike da ƙarfinta da kuma dabararta ba lallai ne ta kai wannan shekarun da aka gindaya mata a kotu ba, amma kuma matsalar shine bata da karfin, a kullum kuma a kowanne wayewar farin Allah Baffa yana kara kassarata ne da hukuncinsa na hana ta ganin yayanta… Shi yasa duk yadda ta kai ga ture wani tunani a zuciyarta tana ji kamar zata yarda dashi akan cewa.
    Karshen tika tika dole TIK ne! Dole ne ta yarda cewa komai ya kare mata, kuma dole nrme ta yarda da abinda Ishaq ya kalli cikin idanunta ya fada mata a ranar da za’a kawo ta gidan nan…
    *’Wata shari’ar sai a lahira Mami…!’*
    Rugugin tsawar da ake yi ya cika iska a lokacin, walkiya ta haska tar ta kuma haskawa a cikin duhun hadarin, sai kawai ta sake ɗaga idanunta tana kallon zubar ruwan ta cikin tagar ɗakin, ta cikin hayaniya da kuma dararrakin mutanen dakin, kuma ba tare da tayi zato ba a lokacin wata guntuwar ƙwalla ta cika idanunta tana gangarowa kan fuskarta, wannan shine karo na uku da taji dumin hawaye a kan fatarta, kuma wannan lokacin shine karo na farko da tambayar da taƙi bari ta yiwa kanta tun a zamanin farko ta ɗarsu a cikin zuciyarta… Wannan tambayar da take gujewa, tambayar da bata taɓa lissafa ta ba balle ta yi tunanin matsayinta na Kilishi zai kai ta ga yinta….
    Ta yaya zata mayar da rayuwarta baya shekaru goma da suka wuce?
    Dana sani….! Yau Kilishi ce da dana sani!
    Dana sani a lokacin da komai ya kure!
    Dana sani irin wadda kowanne musulmi ke gudu a duniyar nan!
    Dana sani tun ta duniya kafin a je ga ranar da ƙafafunta zasu durƙushe a gaban ubangijin da shaidan ya janye hannunta ga barin umarninsa!
    Abinda Kilishi bata sani ba ma shine kamar yadda Ishaq ya faɗa ne… Wata shari’ar sai a lahira!
    Hakki yana rama kansa ne cikin halaye biyu… Tun a duniyar da kuma lahirar dake jiran kowanne bawa!
    Zata karbi abinda yake nata a yanzu, kuma zata karbi abinda yake nata a can, ga rayuwar kurkukun da bata fara ganin komai a cikin ta. Gata nan… ita ɗin ce dai Kilishin da take ce, da lafiyarta da karfinta har ma da tunaninta da komai da take takama dashi, kuma a cikin duniyar da take ganin ita da ita aminan juna ne ta kowacce hanya, sai gashi tasirin wasu katangogi kaɗai!
    Tasirinsu kaɗai ya hana mata dukkan abinda take takama dashi da kuma iyawarta, tasirin shari’ar duniyar kaɗai, ba ma akai ga mutuwa ba, balle kwanciyar kabari ko kuma tashi a gaban Mahaliccin da ta bijirewa da dukkan iyawarta!
    ***
    *Kano.*
    *Mai ƴaƴa Street, Bawo Road.*
    *04:30pm.*
    _So here we stand in our secret place_
    _Where the sound of the crowd is so far away_
    _You take my hand, and it fees like home_
    _We both understand, it’s where we belong…_
    An dauke ruwan, amma har yanzu garin da danshi, iskar da take kadawa mai sanyi ce, Zainab tana jinta akan fatar ta da kuma wuyanta yayin da mai kwalliyar dake gabanta ke ta aikinta na fente fuskarta, sassanyar wakar qmwestlife ta queen of my heart kuma na tashi daga cikin Mp3 din studion…
    “Kiki, miko min brown liner nan…”
    Mai yin kwalliyar ta fadawa wata yarinyarta dake gefe, Zainab ta bude idanunta bayan Aysha ta juya karbar liner, idonta ya gane mata wata ita din daban a cikin mudubin dake kallonta, wata kyakkyawa mai kama da ita din da da take ganin kamar ba ita ba, powder da aka saka da komai ta bi fatar jikinta tsaf ta kwanta tana fito da kowanne tsini da lankwasar sa, musamman hancinta da taga ya ƙara tsawo fiye da yadda da ta sanshi, ga kwsllin da ya fito da idanunta tar yana shaida hasken ƙwayar cikinsu.
    Gabanta ya fadi ya kuma faduwa hannunta yayi nauyi yayin da surutun da yan mata biyun dake bayansu ya cika kunnenta, ds kuma muryar Ameerah dake waya can gida akan a kawo mata takalminta da ta manta.
    Can gida, can gida yana nufin gidan Hajiya Salamatu mahaifiyar Jawad da kusan komai na harkar bikin da ake yi yake hannunta da kuma yanuwanta.
    Watanni shida kenan da Jawad ya same ta a cikin tashar nan, watanni shida kenan da rayuwarta ta canja, don tun daga wannan lokacin tun daga wannan ranar abubuwa suka fara sauki a rayuwarta, Jawad ya mayar da ita har gida can wajen yanuwan mahaifiyarta, inda baya nan aka sha artabu tare da mijin mahaifiyarta akan cewar ya barta ta ɓata, babu wanda ya nuna masa cewa tana can hatta dansa kuwa Nura, sai da hankalinsa ya tashi ya fita daga haiyacinsa bakiɗaya ya tabbatar ana shirin kaishi kotu sannan yazo ya bada hakuri.
    A lokacin ya san tana wajensu, kuma ga mamakin kowa sai ya faɗi maganganu san ransa sannan ya tashi ya tafi. Kuma tun daga lokacin tun daga lokacin da hankali sa ya fara kwanciya, sannan Jawad din ya koma Abuja ya dawo bayan wasu kwanaki, sai ya zama babu abinda ake yi sai maganar bikinsu wanda ba’a samu wata matsala da yan’uwan mahaifiyar tata ba wajen amincewa.
    Kuma sai bayan nan ne sannan ya shaida mata dukkan abinda ke faruwa a tasa rayuwar, abinda ke faruwa tun a lokacin da ya ɗauko ta daga Abujan nan game da rikicewar rayuwarsa da kuma yadda Allah taimake shi ya samu mahaifiyarsa a cikin ƙanƙanin lokaci, dama babban abin manakin na cewar tsawon rayuwar tasa da ya shafe tun daga yarinta a gidan yayan mahaifinsa yayi ta ba wai a wani waje da yake bare ba.
    Ta daɗe tana mamakin kasancewar hakan, sai dai duk mamakinta bai kai na yadda har a lokacin Jawad ya dage akan aurenta ba, don har a cikin yanuwanta daga mazan har matan waɗanda basu furta cewa tayi sa’a ba kadan ne…
    Ita kanta ta sani, ta san hakan ne kawai suna tuna mata ne da irin sa’ar da tayi, shi yasa bata da wa ta cewa a dukkanin abinda ake yi, don ta sani bata da wani gata a yanzu idan ba Jawad ba, ko su yanuwan nata da suke faram-faram da ita don na doki ne da kuma tausayawa rashin mahaifiyarta da tayi da kuma wahalar da ta sha a hannun mijin mahaifiyar tata, sannan bayan haka ma ta sani cewa da yawa suna mutunta ne kawai saboda ganin Jawad ɗin.
    A can garin nasu aka daura auren, yanuwansa da yawa sun je har dasu Hajiya Mardiyya daga can Abuja da kuma dangin sabuwar mahaifiyar tasa, don haka fadar tarin mutanen da ta gani ranar daurin auren nan, wani abu ne da ba ita kadai ba har dangin nata sunyi mamaki… Kuma a ranar ta sha kuka kamar me tayi kukan rashin mahaifiyarta sannan tayi kukan farin cikin da bata san irin yadda zata fallasa adadinsa a kirjinta ba, Tayi hamdala ta godewa Allah fiye da yadda zata iya kirgawa a lissafinta.
    Bayan haka kuma tayi kukan fargaba na irin rayuwar da zata je ta tarar a gaba, don ta sani a yadda zata shiga rayuwar Jawad bata da komai kuma bata da iyaye tsayayyyu dole ne ta fuskanci wasu abubuwan daga mutanen dake kewaye dashi wanda na lallai suyi mata dadi ba… don ko a ranar daurin auren nan ta raina kansa a cikin kowanne bangare na yanuwansa sau dubu tana sakewa…
    Kuma a wannan ranar ne aka basu ita suka taho Kano yayin tare da wasu yanuwan nata yayin da su Hajiya Mardiyya duka wuce Abuja. Sun taho tare da kuma tarin kayan da su Jawad ɗin suka kai wanda har a yanzu bata mayar da hankalinta wajen ganinsu ba kasancewar yadda aka dinga rububin kallon kayan a can garin nasu.
    Kuma bayan sun zo ne suka tarad da gagarumin bikin da mahaifiyarsa ke shiryawa wadanda ta ga kamar sun fi karfin tunaninta, don kusan komai an gama shirya shi hatta kayan da zata sa an gama dinka su, sai bayan da tazo aka gwada aka ga wajen da yayi mata yawa sannan aka mayar aka daɗa gyara su.
    Kallon komai kawai take tana kuma kallon kowa tare da ita da yanuwan nata da suka zo kawai, an hada ta da wata yarinya Ameerah da kusan ita ke jan ragamar komai nata, ita ta gaya mata dukkan shirye-shiryen da suke yi na cewar za’ayi walimar iyaye ne (mother’s eve) a yau washegari da safe kuma za’ayi budar kai tare da yini sannan jibi zasu tafi can Abuja tare da Jawad din su kuma tari nasu Hajiya Mardiyya da suke shiryawa suma kafin a dangana ta da sabon gidan da ya kama kusa da wajen aikinsa.
    Sai a lokacin da taji hakan ne sannan wani sabon kukan ya sake cike kirjinta, ta sani yanuwan mahaifiyar tata sunyi nasu kokarin, don da karo-karo da kuma gudumawa kala-kala aka hada mata kudi dubu hamsin bayan sadakinta da aka kawo na dubu hamsin din shima da cewar ta siya wasu kayan amfanin idan taje gidanta, ko da kayan kitchen ne aƙalla ta dinga kallon wani abu da yake nata tunda sun sani cewa Jawad ya riga ya dauke musu komai yace zaiyi komai din ba sai sun wahalar da kansu ba.
    Amma duk da haka a yanzu da tazo ta ganta a cikin tarin yanuwansa tana jin nauyin da zuciyarta ke ƙara yi da tunanin kowa yana yi mata wani kallo ne daban na cewar an kawo ta ba tare da komai ba kuma a yamzun ne masu niyya zasu kafa mata kahon zukarsu.
    Idan Jawad da mahaifiyar tasa dake ta fara’a tana nan-nan da ita suna sonta kuma basa ganin aibunta, hakan baya mufin zadu iya rufe idon kowa daga ganin hakan. Don haka tun da suka zo a ɗarare kawai take, idan wani yana yi mata magana hannayenta har rawa suke, gani take kamar zasu daka mata tsawa ne kawai ta tashi ta fara aiki ba wai itace wadda suka taru dominta ba. Daga ita har yanuwan nata kuwa tunda dama itace karfin gwiwarsu a wajen, tunda suka fahimci a tsorace take shikenan su ma basu da ta cewa sai abinda akace.
    A yanzu ta baro su ne acan gidan da cewar za’a tafi dasu wajen Partyn da idan an gama yi mata kwalliyar zata je ta same su acan. Ameeran tace mata Jawad ne zai zo ya ɗauke ta idan an gama. Jawad din da tun a can garinsu ranar ɗaurin auren nan bata ƙara ganinsa ba kasancewar tunda suka zo gidan a cike yake da mata fal don haka bata ma san a ina yake ba.
    “Rufe idonki…”
    Mai kwalliyar ta fada tana dawo da ita daga tunaninta. Ta kuwa rufe idon zuciyarta na kiyasta adadin kudin da aka kadhe a wajen mai kwalliyar kada banda kayan dake cikin wani akwati dasu Ameeran suka taho dashi.
    Ƙasa da minti talatin bayan hakan mai kwalliyar nan ta gama fente fuskarta a yanayin da ita kanta da rufe mata ido kawai akayi aka bude zata rantse cewa ba ita bace, Ameerah tare da sauran ƴanmatan nan biyu suka taimaka mata ta zura doguwar rigar wani hadadden material kalar ja mai haske ta kasa, kalar ta dace sosai da kalar fatarta da take wani abu tsakanin fari da kuma brown, daga nan aka shiga daura gwaggwaron da bata san minti nawa aka shafe ana dora hawansa ba.
    Lokacin da aka gama tsoro ne ya kamata sosai ganin kanta da tayi a mudubi, wani abu ya wuce ya sake wucewa a wuyanta lokacin da su Ameerah ke ta fadin Masha Allah suna daukar ta a wayoyinsu, ta kasa dauke idanunta daga mudubi koda na sakwan guda, ji take kamar ta tattaro dukkan mutanen da suka santa a hargitsenta don su taya ta shaida cewa ba itace wadda idanunta ke ganin mata ba.
    “Ashe dai Yaya J ya san me idonsa ya gano masa.”
    Ameerah ta faɗa tana saka ta murmushin da bata shirya masa ba. Dun dade a wajen, har akayi wa su Amirah tasu kwalliyar sannan mai wajen tayi ta ɗaukarta a hoto itama sannan wayar Amirahn tayi kara da sakon Jawad na cewar sun iso wajen, fabanta na dukan tara-tara su Amirah suka taimaka mata suka fita waje Bayan ta yafa wani mayafi shima kalar ja mai shara-shara.
    **
    “Eh munzo ɗauko su yanzu, yanzu zamu taho.”
    Jawad ya fada a cikin wayar da yake yi bayan ya fito dafa cikin motarsa da ta tsaya a kofar wani gida da akace shine gidan mai kwalliyar dasu Zaunab suka zo. A yanzu haka ma da mahaifiyar tasa Hajiya Salamatun yake waya, da kyar yake jinta a cikin tarin kidan dake can wajen bikin inda kusan duka danginta ne gabaɗaya ta tara, yanuwansa na Abuja kaɗan ne a wajen, kusan maza ne ma kadai don su ma suna can Abujan da shirin yin nasu bikin da zarar sun koma.
    Ya roke su, ya roki kowa a cikinsu Hajiya Salamatun dama Maaman (Hajiya Mardiyya) akan ba sai sun shirya wani gagarumin taro ba idan aka daura aure kawai aka bashi matarsa zai fi kowa jin dadi amma babu wanda ya yarda dashina cikinsu, kowacce tace tana da yanuwanta da dole ne su sani cewa tana bikin ɗa, don haka a dole su suka ja tsawon watannin har aka kai yanzu wata na shida kafin komai ya tabbata.
    Ya fahimci kishin dake tsakaninsu tun daga ranar da suka koma Abuja shi da Hajiya Salamatu da kuma wasu yanuwanta bayan dawowarsa daga wajen Zainab bayan kuma sun mika case din ƙawar Hajiya Sakamatun da tayi sanadin komai wadda yaji suna kira da Kilishi, wani suna da yayi kama da orin wanda ya kan jina bakin Rukayya lokutan baya, sai dai bai rike komai ba sunan yana da alaka ne da zancen tsohon mijinta da baya son ji a lokacin.
    Kuma a yanzun ma bai matsa ba ko kadan, ya san dai Hajiya Salamatun ta gaya masa cewa tuni matar dama tana gaban hukuma sanda suka kai ƙarar, abinda ya sani kenan kawai har su saka ranar da ta maida su farin Abuja, zuwa cikin gidan da a ranar da ya fita ya barshi ko kadan baiyi tunanin dawowarsa a kusa ba, yana hango wucewar shekaru ne wanda kafin nan watakila ziciyar tasa ta iya hucewa game da abinda ya faru.
    Sai gashi ya dawo a tsakanin lokacin da hannu ma zai iya kirga shi, ya dawo tare da wani abu da ya ɗaure tunanin kowa a gidan, don ba Hajiya Mardiyya kaɗai ba, kusan duka al’ummar gidan a gigice suka taho bangaren mahaifin nasu jin labarin cewa Hajiya Salamatun da suka sani tsohuwar matar Kawu Ibrahim yadda kowa ke kiransa itace mahaifiyarsa.
    Babu wanda bai santa ba, daga matan gidan har wasu da suka manyanta a cikin ƴaƴan gidan, kawai zumuncin ya lalace ne tun da ya dade da rabuwa da ita tun kafin rasuwarsa kuma ya auri wasu matan bayan ita sannan kuma dadin dadawa babu zuria a tsakaninsu.
    Tun daga wannan lokacin labari ya gama zagaye danginsu gabaɗaya, kuma maimaikon a samu shiri tsakanin Hajiya Salamatu da kuma Mardiyya sai wsni abu kamar kishi ya shiga tsakaninsu don kowacce tana ganin tana da nata ikon akansa.
    Ko lokacin da suka tafi Yakura dukkaninsu sun je amma kowa da nasa tawagar ne. Ko yanzu Alhaji Bashir ya saka baki cewa su Hajiya Mardiyya su zo nan Kanon, ma ta dage cewa itama uwa ce don haka ita ya kamata azo a samu. Sai kowa ya rabu dasu a hakan, Alhaji Bashir ya gaya masa cewa lokaci ne amma komai zai daidaita a hankali.
    “Ka kira su kuwa? Time yana ta tafiya…”
    Haro dake tsaye a gefensa ya faɗa, kuma kafin ya amsa sai ga kiran Hajiya Mardiyya ya shigo, ba shiri yayi murmushi yana girgiza kansa kafin ya bawa Haro amsa.
    “Na kira Ameeran, tace gasu nan fitowa..”
    Haro yayi murmushi yana kokarin gyara hular kansa sannan yace.
    “Ai sai ka gaya min in gyara Malam.”
    “Haro, na gaya maka yarinyar nan ba kalar ka bace, yes tana da wayewa amma ba irin taka ba.”
    Haron ya juyo ya kalle shi, bayan ya kalli sauran abokan nasu ya tabbatar hankalinsu baya kansu.
    “To ni an gaya maka mai irin wayewata nake nema? For real? Kana tunanin kai ka samo mai nutsuwa shikenan ni bani da hankali zan auri yaran titi ne? Malam idan zaka bani support kawai gwara ma kayi…”
    Kafin ya bashi amsa wani kiran Hajiya Mardiyyan ya shigo sai kawai ya ƙara a kunnensa da murmushi yana faɗin.
    “Maamah wallahi jibi zamu taho…”
    Daga cikin wayar Hajiya Mardiyya ta kyalkyale da dariya alamun farin cikin da take ciki kafin tace.
    “Na sani Babana, kira nayi in gaya maka cewa na aika an sake ɗauko wasu daga cikin yanuwanta don ance min mutum goma sha biyar ne kawai anan, sunyi kaɗan ita kanta yarinyar tana buƙatar yanuwanta…”
    Murmushi ya sake yi yana cije lebbensa don ya san tayi hakan ne kawai saboda Hajiya Salamatu… Daga haka ta cigaba da bashi labarin shiryen-shiryen da suke yi wanda a ciki baya hango komai sai tarin gajiyar da shi dama Zainab ɗin zasu fuskanta, Kawai babu yadda zai yi ne yce da waninsu ya fasa.
    A cikin saurarenta da yake yi, yaji muryar Haro yana fadin.
    “Here goes my chance…”
    ( Ga dama ta nan…)
    Don haka yayi saurin juyowa a lokaci guda da idonsa ya nuna masa wata tsantsareriyar halittar da tayi kama da Zainab din dske amsa sunan tasa a yanzu…
    Watakila ya fara yarda da idear shirye-shiryen bikin nan….
    **
    Lokacin da su Zainab suka fito ƙofar gidan, daga can gaba kadan suka hango motoci guda biyu da suka tsaya yayin da mutanen ciki ke tsaitsaye a waje suna jiransu, Jawad na tsaye daga tsakiyarsu yana waya, idonta ya sauka akansa lokaci guda da numfashinta ya tsaya a kirjinta yana sawa ta manta da nata kyan da tayi gaba ɗaya.
    Brown shadda ce a jikinsa da kuma dark brown hula, yayi kyau ya gyara fuskarsa sannan tsawonsa ya sake fitowa, sai ta kasa yarda, ta kasa yarda cewa wai a yanzu matsayinta da nasa ya zarta na yadda ta san shi, a yanzu shi din mijinta ne, mijinta shine wanda ya rufe idonsa daga kowa da kuma komai ya zabe ta a cikin tarin mutanen duniyar nan alhali bata da kowa kuma bata da komai.
    Sai kawai kwallar da bata shirya mata ba ta cika idanunta tana gangarowa kan fuskarta, yayin da sauran mutanen dake kewayensu suka shiga maganganun da ko kadan ba jinsu take ba, shi din kawai take kallo kamar tana son nemo dalilin sa na aurenta akan fuskarsa, kamar tana so taga wani abu da rayuwa ta tauye masa har ƙaddara ta hukunta shi da aurenta alhali yana da tarin dama a duniyar nan.
    “Idan kika cigaba da tsayawa kina kallonsa haka, zan tafi in maye gurbinki yanzun nan…”
    Ameerah ta raɗa a kunnenta daga gefe, wani murmushin da bata shiryaemwa ba ya sake sauka a bakin ta, ta juyo tana kallonta idanunta cike taf da hawaye, sai kawai ta gyada mata kai tace.
    “Alhmdlilah ake cewa…”
    Ta gyada nata kan itama sannan a hankali bakinta ya furta kalmar.
    “Alhmdlilah.”
    “Ai gasu nan sun fito ma, Masha Allah…”
    Muryar ɗaya daga cikin abokan Jawad ɗin tasa su juyowa daidai lokacin da Jawad din shima ya juyo har a lokacin wayar kare a kunnensa.
    Idanunsu suka hadu waje guda kuma maimakon taga mamakin rashin gane tan da take zato a fuskarsa, sai kawai yayi wani murmushi mai fadi yana cigaba da kallonta, murmushin da ya mamaye fuskarsa gabaɗaya yana sa nata lebben talewa itama har a lokacin da ragowar ƙwallar dake cikin idanunta.
    “Alhmdlilah..!”
    Bakinta ya sake furtawa a lokacin da kafafunsa ke tahowa gabanta, idanunta kuma na hango mata wata kyakkyawar dake jiranta a gaba…
    Tabbas Rayuwa me adalci ce… Bata saka alkhairi da mugunta!
    MASU ƁUKATAR A TALLATA MUSU HAJOJINSU ZA SU IYA TUNTUƁARMU TA LAMBOBIN 07045308523 MUN GODE

    Note
    error: Content is protected !!