Search
You have no alerts.

    MASU ƁUKATAR A TALLATA MUSU HAJOJINSU ZA SU IYA TUNTUƁARMU TA LAMBOBIN 07045308523 MUN GODE

    Mintina goma da dauke ruwan, aka kwsnkwasa kofar gidan, Rukayya dake jingine akan doguwar kujerar falon ta kalli gefe inda ƴar aikinsu ke zaune tana kallon Tvn dake aiki a ɗakin, ganin bata nan ya dan bata mamaki don ko kadan bata ji lokacin da ta tashi ba.
    “Jummai…”
    Muryarta ta kira ta a hankali tana ƙoƙarin gyara zamanta, sai dai da alama Jumman tayi nisa a cikin gidan da ba lallai ne ta jiyo ta ba, ƙarar doorbell din ta sake cika dakin, sai kawai ta mika hannunta a hankali ta jawo ƙarfen da take rikewa wajen tashi da kuma tafiya dashi, hannyenta da har yanzu ke rawa suka damke jikinsa a hankali kafi ta tattara dukkan ƙarfinta akai ta iya mikewa.
    Ta mike daidai lokacin da Jumman ta dawo tana fadin.
    “Hajiya gani nan, koma kiyi zamanki..”
    Ta koma din a hankali ta zauna yayin da Jumman tayi gaba ta bude kofar, kuma da yake kujerar da take zaune itace daidai saitin kofar, sai ya zamana Jumman na buɗewa hoton ƙaninta Ashraf ya shiga idanunta a lokaci gyda da gabanta ya fadi zuciyarta ta buga a kirjinta, ba wai ganinsa ne ya haddasa hakan ba…
    Don kusan kullum yana zuwa duba du ita da mahaifiyar tasu tunda suka tare a gidan, kusan koyaushe ya tashi daga aiki nan yake faraboyowa kafin ya wuce gidan nasa, don haka yanyin fuskarsa a yanzun shine ya tsorata ta, wani yanayi ne da rabon da ta ga irinsa a tare dashi tun a lokacin farkon ciwonta, sanda suna Niger kafin ma ayi transfering dinta zuwa asibitin da tayi kusan jinyar watanni biyu a cikinsa anan Nigeria, lokacin da ta farka ta tarar da sakon dashi da kuma Ahmad suka kawo na saki tsakanin iyayen nasu.
    Wani abu da tunda ya faru daga su Ashraf din har ƴanuwansu suke ta fafutukar neman yayi hakuri ya mayar da Hajiya Nafisan amma duk yadda akayi, duk kokarinsu baya sauraren kowa yace ya riga ya yanke hukuncinsa, tunda har zata iya rufe idanunta akan saɓon Allah ta kuma tura ƴarta har wata ƙasa wajen neman magani don biyewa bukatun duniya, to tabbas bai ga amfanin zamansa da ita ba.
    Ita kanta Rukkayan sau ɗaya yaje ya duba ta a asibiti, a ranar a gaban Hajiya Nafisan ya bata hakurin kuskurensa ma cewar bai bata uwa ta gari ba a matsayinta na ƴarsa sannan yayi fatan cewa abinda ya faru zai zama izna gare daga yanzu wajen gane tarin laifukan da ita kanta tare kuma da mahaifiyar tata suka taya ta aikatawa.
    Sannan ya gaya mata cewa ta dawo wajensa da zama duk ranar da aka sallame ta tunda duk wata dawainiya da tsadar asibitin ma shi yake biya amma bayan an sallane tan, sai wannan tausayin da ubangijinke halittawa tsakanin ya’ya da iyayensu musamman ma Uwa… Ya hana ta juya baya ta koma wajen mahaifin nata.
    Ashraf ne ya kama musu wannan gidan acan hanyar Tarauni suje zaune, kuma anan mahaifiyar tata tayi jinyarta tare da yanuwanta dake yawan zuwa akai-akai suna taya su kwana, a yanzu ta sami sauki sosai har tana miƙewa tsaye kuma maganarta ma ta fara fitowa sosai.
    Sai dai har yanzu bata koma Rukkayyan da take a da ba, bata koma wannan kyakkyawar Rukayyan dake ji da kyan da take ganin ta hanyarsa zata iya samun komai a duniyar nan… Komai din da bai hada da Ma’aruf ba, wanda hakan sho ya rude ta wajen biuewa kowacce irin shawara da mahaifiyarta tata da ƙawarta Hajiyar Sudan suka kawo, tunda ko a karon farko ta sani cewa da ƙyar ta same shi a rayuwarta.
    An kawo Hameeda kusan sau uku tazo ta duba ta daga can gidansu Ma’aruf din da a yanzu Baffa ya aiko an shaida musu karara cewa yarinya ta dawo hannunsu tunda su suka kawo ta da kansu amma lokaci bayan lokaci za’a dinga kawo ta suna ganinta, kuma itama yarinyar ko kadan bata nuna tana sha’awar zama ba musamman ganinsu a wani sabon gidan ba inda ta saba ganinsu ba.
    Sannan kamar kusan kowa, sun ji labarin abinda ya faru a gidan su Ma’aruf game da Hajiya Kilishi, tayi mamaki amma ba wani sosai ba don tun lokacin da ta zauna a gidan dama ba wani shiri suka yi sosai ba, don haka ta yarda duk abinda aka fada din zata aikata. musamman da su ma suke ji da tasu matsalar sai basu wani daukaki abin sosai ba.
    Ashraf ya shigo a lokacin da wannan yanayin na fuskarsa, yanayin da ba ita kadai ba hatta Jamilan da ta buɗe masa kofa a hankali ta rufe sannan ta juyo ta fita daga falon tana basu waje.
    “Sannun da zuwa, ya aikin?”
    Rukkayan ta faɗa a hankali tana kallonsa bayan ya ajiye jakar hannunsa.
    “Alhmdlilah, bata nan?”
    Ta san wa yake nema don haka ta girgiza kanta.
    “Tana wanka yanzu zata fito…”
    Ta fada sai kuma ta sake cewa.
    “Me ya faru?”
    Don zuciyarta ta kasa tsayawa waje guda da tunanin abinda ya farun, shima kamar ba zai ce komai ba, sai kuma ya mika hannu ya bude zip din briefcase din da ya shigo da it, hannun nasa ya zaro wani envelope da a lokaci guda ya sa zuciyart bugawa, yaba tuna mata da emwanda ta gani na karshe a hannunsa shi da Ahmad, na sakin mahaifiyar tasu…. Yanzu kuma me ya faru?
    “Daddy ne zai yi aure Rukyya,ga kayin daurin auren nan, sati mai zuwa…!”
    Ya fadi hakan daodai lokacin da Hajiya Nafisa ta shogo falon, sakon kuwa ya shiga kunnenta yana sa zuciyarta nugawa ta kuma tarwatse a kirjinta!
    Rukayya ta hadiye abinda bata san sunansa ba a makogwaronta, shikenan! Kamar ita Mahaifiyarta tayi biyu babu akan mutum guda, ta rasa mahaifinsu ta sake rasa shi kamae yadda itama ta rasa Ma’aruf sau biyu a tata rayuwar… Da gaske Daddy yake kenan, da gaske ba zai mayar da ita gidanta ba…
    Tabbas masu iya magana sunyi gaskiya da suka ce ka kiyayi zuciyar mai hakuri lokaci aka kaishi karshe…. Mahaifinsu mutum ne mai tsananin hakuri da kuma kawar da kai akan tarin abubuwa, shi yasa tun farko mahaifiyar tasu ta samu sake yin abubuwa da yawa da taga dama… Tunda sau da yawa ma zasu yi abu har su gama bai ma sani ba balle ya hana, baya takura musu baya takura mata, ko lokacin da tayi aure har biyu bayan Ma’aruf, yanuwansa sai da suka nuna bacin ransu na ganin bata wani dadewa take sake fitowa amma shi bai ce komai ba, bai yi mata ko ƙorafi ba ba balle faɗa.
    Idan kayi laifin da zaka bashi hakuri ma wani lokacin ba ma sai ka furta ba, alamun niyyar ka kaɗai kan sa ya yafe ma tun kafin ma kace wani abu… Don haka ba ita kadai ba, tabbas kowa ma ya sani cewa da gaske mahaifiyarsu ta kai shi ƙarshen da ba lallai ne ya dawo ba.
    A lokaci guda wata kwalla mai dumi ta gangaro kan kumatunta, tana tuna mata da tarin lokutan da suke cikin jin dadi da fantamawa son ransu… Rayuwa bata da adalci…
    “Rukayya..”
    Ashraf din ya sake kiran sunanta yana sska ta ɗagowa a lokacin da Hajiya Nafisa ta karaso cikin falon ta dauki envelope din katin daurin auren tana dubawa, ta a duba sunan wata mai sa’ar da rayuwa ta zaɓo ta wajen bata kyakkyawar damar da ita tayi rikon sagegeduwa da ita.
    “Naga anyi posting daurin auren Jawad a facebook, kin sani?”
    Kalaman suka tsayar da tunani dama numfashin Rukayya cak a lokaci guda… Taba jin wani abu na yawo a cikin kanta da bata san menene ba, jiri ya debe ta daga inda take zaune, kanta ya zagaya ya sake zagayawa a cikin ɗakin kafin idanunta su dawo dashi kan Ashraf dake kallonta har a lokacin, sai kawai ta girgiza kanta da ƙarfi a yanzu kwallar dake fitowa daga kowanne idonta tana tarwatsewa a iska…
    Tabbas Rayuwa bata da adalci! Musamman ga mata irinta wanda basu da hankalin fahimtar cewa duk kwaɓewar al’amari, namiji yana da damar tsame kansa ya bar macen a cikin rauninta wanda ba zai iya kaita ga matsayin wasu damar dashi zai samu ba…
    Zai barta a cikin ƙuncin da zata zauna tana maimaita kalaman Rayuwa bata da adalci!
    ***
    *Abuja.*
    *New Horizon Street, Wuse 2.*
    *05:30pm.*
    Iska ta kaɗa farin labulen ƙaton windon dake manne da wani ƙaton falo, wanda yake a saman benen gidan. Tagogin windon gabaɗaya a bude suke, an wangale su ta kowanne gefe yayin da sassanyar iskar daminar da ake yi ke kada labulayen dake jikinsa kalar ruwan toka, kalar da ta dace da kusan komai na cikin falon da yake da sassaukan ado, (Grey &ash) sai kuma tsilla-tsillan abubuwan da suke kalar baki kamar sauran kayan electronics.
    Mintuna basu fi goma kenan ba da ɗauke ruwan samn da aka fi kusan awa guda ana zabga shi, don haka garin a lulluɓe yake da duhun hadari da kuma na yamma wanda a lokacin ƙarfe biyar da rabi ne…. Koina a jike yake sharkaf dauke da danshin dake komawa sanyi-sanyi yayin da bishiyun dake harabar wajen ke ta rangaji a cikin iskar na jin dadin yanayin da kuma jikewarsu.
    Falon dogo ne wanda a can ƙarshensa ya hade da wajen dining da kuma kitchen duk a ciki, iri ɗaya sak da tsarin gidajen turawa kamar yadda akayi ginin a haka tun daga waje.
    Akwai matattakalar bene daga gefe wadda akayi kusan rabi na jikinta da gilashi fari kamar yadda mafiya abubuwa suke a gidan, matattakalar zata kai ka zuwa sama inda anan zaka tarar da kofofin manya-manyan dakuna guda uku masu dauke da hadddun toilets da kuma walk-in wardrobes…
    A watannin farko da suka zo gidan, Amina zata rantse ta shafe fiye da wata guda kafin ta gam sanin komai na gidan ta kuma saba da tsananin kyawunsa da take gani. Har faduwa ta taba yi har kasa watarana data yi alwala ta fito daga toilet saboda tsabar santsin marbles din dake gidan wanda ko mai ta shafa a a kafarta tana jin kamar zata zame.
    Watansa hudu kenan a ciki, amma komai yana nan da kyallinsa kamar sabo, hatta kayan kitchen wanda su tafi komai tabawa a gidan balle kuma sauran dakunan da ta kan yi kwanaki biyu ma bata leka ba. Hatta doguwar kujerar falon da Ma’aruf kullum yake kwanciya akai bata taba nuna alamun nauyinsa na nunawa ba, ko kuma tace nauyinsu tare…
    Daga cikin falon, Amina na tsaye a jikin sink din dake tsakanin drawers na kitchen din, ta kunna fanfon tana wanke wani farin kwano data dauko yayin da sassanyar iskar daminar ke shigowa tana kada ƴan kananan gashinta da suka taso sama saboda laushinsa, babu dankwali akan nata sai gashinta da ta daure da wani yalon ribbon, rabon da ta taje shi ma kusan kwanaki biyu kenan.
    Rigar jikinta wata loose T-shirt ce ta maza fara kal wadda bata fi rabin cinyoyinta ba, ta tattare duka hannayen rigar zuwa gwiwar hannunta yayin da maɓallan sama ma bata gama rufe su ba.
    Ta juyo daga jikin sink din ta dawo kan worktable din dake tsakiyar wajen, ta shiga yanka albasar kanana a cikin wani farin kwano… A lokacin ne wayarta tayi ƙara daga can kan Centre table din dake tsakiyar kujerun falo, da saurita ajiye wukar kafafunta suka dauk ta zuwa can, siraran tafin kafar nata na bi ta kan santsin marbles din dake wajen har ta sauka zuwa falon wada ya danyi kasa da matattakala biyu kawai.
    Ƙafarta ta shiga cikin tattausan carpet din da yake kalar grey, kamar kullum yatsun kafarta suka lume ciki kafin ta kara wayar a kunnenta da murmushin da ko mutumin bai tambaya ba zai canki waye mai kiran.
    “Amma… Barka da yamma.”
    Ta fada da murmushi bayan sallama. Daga ɗaya bangaren, Amma tayi nata murmushin itama tana kokarin dauke kwanon dambunta da Hamida ke kokarin dauka sannan ta amsa.
    “Barkanmu dai, kun yini lafiya?”
    Amina ta gyada kanta.
    “Alhmdlilah Amma lafiya kalau.”
    “Ya jikin naki? Ya nasa jikin shima?”
    Ta cije lebbenta tana zama akan hannun kujerar dake gefenta, wata iska mai ƙarfi ta shiga kaɗa ta tana ratsa ƴar rigar jikinta tana shiga koina.
    “Alhmdlilah Amma dukkanmu da sauki, da sauki sosai.”
    “Ga Hamida nan an kawo ta yau tazo zata hana ni cin abinci…”
    Cewar Amman tana sawa fara’ar dake fuskar Amina ta karu a lokaci guda.
    “Hamida tazo?”
    “Ɗazun nan da safe aka kawo ta, Abdurrahim ne yace zuwa goben zai zo ya dauke su gabaɗaya har dasu Maryam su zo taren ku. Dambun shinkafa muka yi yau, shine ta hana kwanon kowa saƙat! Yanzu suka gama ci tare da Adam ta dawo kan nawa kuma n tsoro nake kar yayi mata yawa ya bata mata ciki, tunda har a rama Babanku yasa aka saka.'”
    Amina tayi dariya.
    “Ni ban san yaushe ta koyi haka ba, da fa idan bata san abu ba bata ci kwata-kwata…”
    “Hajiya ma haka tace, ranar da suka yi Amala a gidan wai da kyar aka samu ma ta dandana, amma yanzu gashi mu ban t kasa ko zama.”
    Daga cikin wayar tana jiyo maganganun Hamidan tana fadin a bata da kuma na Hafsa tana cewa ta ɗauko plate su ake zubowa tare.”
    Amina tace.
    “Allah Amma nima raina ya biya tun daga nan, dambun nan naki daban ne ai, a gas kina yi ko a mangal?”
    Amma tace.
    “A mangal ne, Babanku kuma kafin ya fita da safe cewa yayi wai yafi son naki wanda kike hadawa da rama… Shine na bawa Adam ya siyo muka saka kar ya dawo ya sake min gori.”
    Amina ta bude bakinta kadan tana dariya.
    “Baya ci sosai fa idan nayi, Amma kin manta har cewa yayi baya son tsaminta…”
    Kafin Amman ta amsa daga cikin wayar Muryar Maryam dake shirin fita daga ɗakin tayi magana da karfi tace.
    “Missing ɗinki yake yi kawai…”
    Amma tace.
    “Ai nima naga alama, don ko da safe da zai fita sai da ya sake tambaya yau din zaku taho kuwa..”
    Kwalla ta cika idanun Amina a take yayin da murmushin ta ya ƙaru.
    “Ni tawa kewar tafi taku Amma, ni kadai na san abinda naji a cikin watannin nan.”
    Ta fadi abinda ya canja akalar hirar tasu a lokaci guda. A lokaci guda da Amma ta gyara wayar a kunnenta sosai kafin ta tambaya.
    “Wannan duk ya wuce yanzu Amina, tunda ga dawowar nan tazo, abinda kawai nake so ki bani tabbaci shine kin tabbata dai babu wata matsala har yanxu ko? Ya gama jin sauki gabaɗaya?”
    Wani abu ya zarce wuyanta a lokaci guda… Yaji sauki? Ma’aruf yaji sauki? Tana da tabbacci?
    Tambayoyin da har take yiwa kanta kenan a kullum wayewar garin Allah tunda ya gaya mata cewa da gaske ɗin yu zasu koma, don ba sai wani ya gaya mata ba ta sani, duk abinda yazo ya faru a gaba, duk abinda yazo ya same shi zata karbi alhakin hakan ne ko da kuwa duniyar gabaɗaya zasu goya mata baya don kare ta.
    Watanni hudu kenan da dawowarsu garin Abuja, bayan watanni biyu na zaman jinyar Ma’aruf a asibiti da kuma faruwar wasu tarin al’amura masu ɗaga hankalin da babu wani a cikinsu da ya taɓa sanin irinsa.
    Ciwon Ma’aruf yayi tasirin da a karon farko likitocin ke zaton cewa ya rasa hankalinsa bakiɗaya, don kusan mutum uku ne suka sa hannu akan cewar Bipolar diorder dake damunsa ta kai mataki na ƙarshe wato ‘Mania’.
    Sai da aka samu banbancin ra’ayi a wajen mutune guda biyu sannan Baffa ya bada umarni aka fita dashi zuwa asibitin da yake ganin likita acan London, da Ishaq da kuma Baba Usman su suka kai shi, don har a lokacin hankalin Baffa ya kasu gidaje da yawa, wajen fuskantar tarin shari’ar da ake yi akan Hajiya Kilishi sakamakon wasu laifukan nata da ake ƙara ganowa a hankali ciki har da aminiyarta da take zarginta da raba ta da ɗan cikinta da tayi tsawon shekaru.
    Zancen ya sake ta da hankalin kowa a sanda suka ji shi… Don yanuwan nata da ƙarfinsu suka zo da kuma tarin hujjojin da suka sa dole aka hada dasu a cikin shari’ar… Wanda bayan hakan ne, likitocin dake kula da Ma’aruf acan suka yi nasu ƙoƙarin wajen dawo dashi cikin hayyacinsa, sai dai da sharadin cewa dole ne ya samu aƙalla watanni uku a wani waje da hankalinsa zai kwanta ba tare da tashin hankali da kuma yawan ganin mutane ba… Wani waje da zai bashi nutsuwar zuciya da kuma kwanciyar hankalin da zai manta da dukkan matsalolin da ya fuskanta yaji sunyi masa nisa har zuwa lokacin da kwakwalwarsa zata daidaita.
    Don haka tun kafin su dawo Ishaq yasa suka kama hayar wannan gidan a cikin garin Abuja, wata kawatacciyar unguwa da kusan tsarinta da komai na kasar turai ne, don tun daga ranar da suka zo Amina ta sani cewa ba kowa ne a duniya yake samun damar rayuwar a irin waɗannan wajajen ba.
    Da farko ta sha wahala wajen fuskantar tarin abubuwa daga sabon Ma’aruf ɗin da a kullum take ganinsa a haka, baya magana baya cin abinci, baya komai sai sallah shima sai idan lokacinta yayi kenan, kuma tsakaninta dashi abu biyu ne kawai zai amsa maganarta da Eh ko A’a, sannan idan zasu kwanta zai rungume ta a jikinsa zuwa safe.
    Baya cewa komai baya bata labari, baya mata ƙorafi, baya tambayar kowa baya tambayar aikinsa, ko Hamida bai taba tambaya ba, ita kaɗai ɗin kawai da ya gani tare dashi ita kadai yake kallo yana binta da eh ko a’a idan tayi masa magana, daga baya har tunani tayi itama din kamar bata da amfani a tare dashi, don haka sai ta samu rana guda ta gwada tafiya daya dakin tayi kwanciyarta don ta gani idan har zai kula bata nan ya neme ta.
    Fatanta kuwa ya karbu don bata ko kai ga yin bacci ba taji motsin bude kofar dakin, da murmushi a bakinta lokacin da ya hawo gadon ya rufe ta a jikinsa ba tare da yace komai ba, ta dago da kanta tana kallonsa ta cikin dan siririn hasken ɗakin dake shigowa daga windo na fitilar waje, idanunsa a lumshe suke yana kallonta dasu kamar a rufe.
    _”I’m sorry BabyDoll…”_
    Muryarsa ta fito a hankali da sautinsa wanda a lokacin idan zata kirga, bai fi cikin hannunta taji shi ba tun bayan zuwansu gidan, ta kalle shi kusa na wucewar minti guda tana auna daɗi da zuciyarta ta shiga kafin a hankali bakinta ya sake talewa da wank murmushin sannan ba tare da ta sake cewa wani abu ba ta kwantar da kanta a saman kirjinsa kawai yana kara rungume ta.
    Kuma tun daga wannan ranar, sai abubuwa suka fara yin sauki, ya zama yana magana daya biyu har ma ya tambaye ta wani abu, idan ta kunna T.v baya kashewa, sannan sau biyu a ranakun da yaga bata jin dadi kuma an kwana biyu likitar dake zuwa duba ta bata ba zo yace mata ta dauki wayarsa ta kira ta kasancewar duk lambobin mutanen da zasu nema idan suna bukatar wani abu a wayar tasa Ishaq ya ajiye lambarsu.
    Lambobin mutum biyu ma kaɗai tafi kira, daga mai canja musu ruwan dispenser sai mai zuwa ya siyo duk kayan abincin da take bukata, kuma a baya yawanci lokacin da zasu zo din, yana jinta dasu a ƙofa ba zai taɓa tasowa ba… Sau ɗaya ya taba ido ya kalli mai yin cefenen da ya taya ta shigo da ledojin kayan da ya siyo ciki… Amma a yanzu shi da kansa yaje bude musu kofa ya karbi duk abinda suka kawo.
    Bayan haka da ta fahimci ya fara sakewa, sai ta fara bashi labarai a hankali a hankali, yan kananan labaran da baza su ja hankalinsa da yawa ba wadanda ke magana akan hakuri da kuma karbar kaddara, ba karara take fito da hakan ba, ko kadan ma bata amfani da kalaman da zasu fito da manufarta, labarin ne kawai zai zo a sigar dashi zai fahimci hakan, kuma da ta kula ya fara tunani na fahimtar abinda take nufi, sai ta kirkiro wani aikin ta tashi ta bashi waje don ya kara fahimtar abinda take nufi ɗin.
    Sannan ta dinga kokarin binsa jam’in sallah, tana gani ya tayar zata yi saurin yin alwala tazo ta bi bayansa…. Tayi tarin abubuwan da ta san ko taya ya ne zasu iya tsayar da hankalinsa waje guda ya samu ya dawo wannan Ma’aruf din da ta sani, wannan Ma’aruf din da tazo ta tarar dashi cikin kyakkyawar rayuwarsa.
    Jinya ce irin tata tayi ta, tayi da jikinta da kuma zuciyarta,tayi dukkan kokarin da zata yi da dabararta da kuma wasu daga cikin shawarwarin Amma har ma da Ishaq wanda a rashin ɗanuwan nasa sai ya zama ita yake kira a kullum yaji cigaban lafiyarsa.
    Har sai da ta kai Baffa da bakinsa watarana da suka yi waya ya bata shawarar cewa ta dinga saka lemon tsami a ruwan ɗumi ta samu yasha kafin ya kwanta, yace mata hakan ba karamin abu bane dake wanke zuciyar ɗan Adam…
    Hajiya Maimuna kuwa tasa Munaya ta rubuto mata tarin addu’o’in wasu kuma tayi recording da muryarta tana tofawa a cikin ruwan shan sa, wani lokacin har ma da kayan da zai saka kafin ya fito daga wanka. Samirah ma ta sha kiran waya ta gaya mata abincin da ta san yana so tun asali wadanda idan anyi ransa ke jin dadi.
    Kowa ya taimaka, kowa ya taimaka da iya abinda zai iya duk kuwa da halin da har yanzu zuciyioyinsu ke ciki, musamman su Samiran ƴaƴan Hajiya Kilishin da ko a idanunsu, baƙo zai shaida damuwar da suke cikinta har yanzu, amma har su Salma dake gudajensu suna kira su ji lafiyarsa.
    Don haka duk da ta sani cewa ba da iya taimakonta kadai suka karaso matakin da Ma’aruf din yake a yanzu ba, matakin da take ganin kusan bashi da maraba da warkewarsa gabaɗaya, duk da haka tana jin zata ɗauki alhakin duk abinda zai biyo baya idan har aka samu wani akasi ga me e da lafiyar tasa.
    Kowa yayi kewarsa a gidan nan, tarin kewar da take ganin kamar shine ruhin gidan nasu gabaɗaya, don irin murnar data ji daga kowa a gidan a ranar da shi da kansa ya dauki waya ya kira su, wani abu ne da mizaninta ya kasa aunawa.
    Tana tsaye daga baya bata ko jin me suke cewa, da amsoshinsa kadai take ayyana tarin murnar da har ƙwalla sai da ta saka ta, sai ta juya masa baya tana sharewa da tafin hannunta yayin da zuciyarta da ma duk wani abu mai hankali a cikin kanta ke ƙara tasbihi ga jalla wata’ala da ya takaita wahalarsa da ma tasu bakiɗaya, don ko daga gidansu Amma tace kowa yayi kwanan farin ciki musamman ma Baba wanda ya matsu ya ga dawowarta.
    Bayan hakan Ma’aruf da kansa ya yanke ranar da zasu koma Kanon bayan tarin abubuwan da suka ƙara gamsar da ita warkewarsa, don a yanzu har da Faruk suna waya game da harkokin kamfaninsu, yana gaya masa iri tsarin sababbin securities dn da Abdurrahim ke sakawa a kowanne bangare na kamfanin ta yadda babu wani mai wayon da ya isa ko yaga kaya ma idan za’a fitar dasu daga kamfanin balle kuma kuɗi.
    A yanzu haka ma kusan sati guda baya yini a gidan yana can fafutukar rufe asibitinsa MMB-6 da cewar zai mayar dashi can hida Kano inda shi da kansa zai dinga jagorantar komai… A yanzu kusan an gama komai ma kokarin samun masu siyan ginin kawai ake yi… Kuma sai ya zama fitar ma ta kara taimaka masa wajen sake warwarewa don ta sani akwai tarin abubuwan da a zaman gidan kadai zasu cigaba da tuno masa da Kilishi da kuma dukkanin abinda ya faru, amma bai taɓa maganarta ba tunda ya farka, ko da Baffa ko kuma da Baba Usman ɗin da suke waya a kullum.
    Sannan bayan tahowarsu Munaya ta gaya mata cewa cikin abinda bai fi sati hudu ba wata guda n canja tsarin gidan bakiɗaya, Baffa ya saka an rushe bangaren Hajiya Kilishi, an haɗe gidan baki ɗaya a waje ɗaya kuma ta kofa guda saboda su Samirah dama dukkanin al’ummar gidan da tabbas ganin ɓangaren nata zai dinga tuna musu da ita a kodayaushe.
    Don ko a lokacin da yayi general meeting tun kafin tahowarsu, ba ga ƴan gidan kadai ba har da sauran yanuwa na da kuma na Hajiya Maimuna akan abubuwan da suka faru, yayi ta jaddada cewa dole ne kowa ya cire ta daga cikin zuciyarta saboda trin laifuka da kuma cutarwar duk da cewa an ɓoye wasu da yawa saboda Inna Danejo dake fama da rikicewar tsufa tun daga wannan daren da al’amarin ya faru.
    A zahiri yanzu rayuwa ta fara komawa daidai, abubuwa suna tafiya kusan a daidai ga kowa don Baffa yana iya bakin kokarinsa wajen ganin ya daidaita rayuwar tasu ta koma kamar da, amma a cikin zuciyoyin kowa Amina ta sani cewa dole akwai wannnan digon bakin ciki da ba zai taba gogewa ba musaman ga su Samirah ƴaƴanta, wanda ko sau daya Baffa bai bari sunje sun ganta a can kurkukun da aka daure ta ba…
    Munaya tace mata wasu daga cikin yanuwansa sunyi kokarin tausar sa akan hakan, amma babu wanda ya san cewa yayi nasa fushin sai a lokacin, don Ishaq ya kira ya zauna a gabansu sannan yace ya zama shaida zai yi shari’a da duk wanda ya ƙara kawo masa magana makamanciyar wannan. Shikenan! Sai zancen ya mutu ko su Samirah basu kara yunkurin hakan ba.
    Gobe itace ranar da Ma’aruf ya yanke shawarar komawarsu, bata sani ba ma idan ya gama da zancen asibitin nan, amma ya tabbatar mata cewar zasu koma gida don tun jiya shi da Ishaq suka gama tsara komai, don haka itama tun a jiyan da kuma yau da safe ta gama shirya dukanin kayansu, akwati guda uku ne sai kuma wata jakar dake ɗauke da yan kanan tarkacenta, ta tattare komai nasu hatta kayan da zasu saka ta fito dasu, na jikinsu idan sun cire ne kawai zata sama musu waje.
    Kuma bata san me yasa ba haka kurum tun jiyan take jin wani iri don haka a yanzu da Amman tayi mata wannan tambayar sai kawai ta sake jin jikinta ya mutu, ta haɗiye yawu a maƙogwaronta kafin ta gyada kanta a hankali.
    “Insha Allah Amma ba abinda zai faru, yaji sauki da gaske, kuma idan mun dawo ɗin ma zai ƙara tafiya can asibitin da ake duba shi kafin ma ya koma aiki insha Allah.”
    Daga cikin wayar, Amma ta yi tata ajiyar zuciyar a hankali.
    “Shikenan, Allah ya kawo ku lafiya, Allah ya ƙara sauki. Maganar da nake son mu yi akan yadda zamanki zai cigaba a gidan nan ne… Na gaya miki Kilishi ba itace matsalarki ta ƙarshe a duniya ba, zama yau da gobe tare da kowa a duniyar nan dole yana bukatar hakuri don watarana ma baka san lokacin da zaka batawa wani ba, kina gani ko sanda kina nan a tsakaninku yanuwa ma kuna samun sabani balle kuma a gidan surukai.
    Don haka dole ne ki cigaba da yin taka tsan-tsan wajen kyautatawa kowannensu da kuma ɗauke kai akan abinda bai shafe ki ba, wadannan abubuwan guda biyu Amina sune abinda mata da yawa suke kuskurensu shi yasa ba ga surukansu kadai ba har a wajen miji suna samun matsala, idan kin dawo zamu sake yin magana insha Allah.”
    Amina ta gyaɗa kanta alamun ta fahimta ta kuma rike kamar dukkan sauran maganganun mahaifiyar tata kafin ta amsa.
    “insha’Allah Amma, insha Allah.”
    “Kice muna gaishe shi, sai goben idan zaku taho kya kira mu.”
    “Toh zai ji insha Allah.”
    Har Amman na shirin katse wayar tayi saurin sake magana.
    “Maryam tana kusa dake? Zan tambaye ta wani abu ne…”
    “A’a bata nan amma ga Adam nan, bari ya kai mata.”
    “Toh Allah ya bamu alkhairi.”
    Amman ta amsa kafin ta mika wayar a hannun Adam dake zaune yana game a wayar Aminu, ya mike da sauri zuwa tsakar gida inda Maryam ɗin ke kitchen tana sake zubawa su Hafsa da suka tsira mata idanu abinci tana faɗin kar su shigar mata daki su bata mata.
    Ta karɓi wayar bayan hakan sannan suka shiga tasu hirar akan wasu ɗinkunan kaya da ta barwa Maryam ɗin ta kai mata kafin tafiyarsu, ɗinkunan da take sa ran su zata yi amfani dasu a bikin Munaya da Ishaq wanda aka saka rana watanni biyu masu zuwa… Watakila lokacin da zata haihu da kwanaki kaɗan. Ko can gidan a yanzu shirye-shiryen kawai da ake yi kenan, shine babban abinda ke dan dauke hankalinsu daga al’amarin da ya faru, musamnan su Samirah da Munsyan ke gaya mata cewa suma sun kara sakewa sosai a yanzu.
    Aminu ya shigo kafin su ƙarasa eayar da Maryam, yana shirin fita zuwa wajen aikinsa da ya cigaba da zuwa sakamakon saukin da kafarsa tayi. ya karɓi wayar daga hannun Maryam suka shiga tasu hirar kamar kodayaushe yana gaya mata cewa ya cika akwati na uku ya buɗe na huɗu da kayan Baby.
    ***
    Daga kan matattakalar benen dake saukowa cikin falon gidan, Ma’aruf ya sauko, kafafunsa na biyo matattakalar a hankali yayin da yanayin hasken falon ke shaida masa yanayin tafiyar da lokaci yayi don har ya kammala shiryawa da komai bai kalli agogo ba tunda wayarsa ma a falon ya barta tun jiya.
    Iskar dake faman kadawa a falon kasancewar bude windows da akayi ta shoga kada shi kotawanne ɓangare yayin da idonsa ya sauka akan Amina dake tsaye daga can wajen kitchen tana zuba fulawa a cikin wani kwano.
    Numfashinsa ya tsaya a kirjinsa a lokaci guda ganin kayan daje jikinta, rigarsa ce… Wata loose T-shirt dinsa da yawanci idan zaiyi ball yake saka ta… Fara ce ƙal, ta tattare dogwayen hannunta zuwa can sama, kanta babu dankwali yayin da girman cikinta ya fito sosai a saman rigar… Kafafunta, wadannan siraran kafafun nata da a yanzu suka kumbura ƙaɗan suna yawo ta kasan dan karamin wandon da ta saka wanda bai kai gwiwa ba.
    Ba wai yau ya fara ganinta da irin wannan shigar ba, kusan kullum ne, amma kusan kullum din sai zuciyarsa ta cika da wani irin abu mara misaltuwar da yake ganin kamar idan ya kira shi da sunan farin ciki kaɗai bai yi masa adalci ba… a lissafinsa itace duniyarsa a yanzu, ita kadai ce wani abu da har cikin ransa yake ganinta a cikin rayuwarsa a matsayin wani abu da yake so har cikin zuciyarsa ba wani abu da ya karba a matsayin maye gurbi ko kuma don babu yadda zai yi ba.
    Yana sonta ta sani, yana sonta saboda kyawawan halayenta, yana sonta saboda kyautatawar ta, sannan yana sonta saboda taimakonta wanda a kullum a kodayaushe yake ƙara ganinsa… Musamman a yanzu da yake ganin wata irin kulawarta wadda duk yadda zuciyarsa ke da tauri a yanzu kai tsaye take wucewa tana taɓowa har can ƙarshe.
    Kuma bai san me yasa ba lokacin da al’amarin ya faru, lokacin da komai ya faru, bai sani ba idan wani a cikin yanuwansa ko ma Hajiya Maimuna sun kalle ta da wani tunani, amma shi bai ko tuna ba sai daga baya, bai tuna ma cewa ta shigo rayuwarsa ne ta hanayar matar da a yanzu bai san a wane irin mizani zuciyarsa ke tunaninta ba. Idan ya kalle ta kawai a kullum kuma a kowanne hali baya tuna komai sai cewa itace waje mafi girman da yake samun nutsuwar zuciya.
    Lokacin da ta juya dauko wani jug din ruwa a gefe, lokacin idonta ya kai kansa, ta kalle shi a lokaci guda da murmushi ta subuce a fuskarta.
    “Wani yasha bacci yau…”
    Ta fada a lokacin da ya karasa saukowa daga kan stairs din, ta cire hannunta daga cikin fulawar ta ware su tana murmushi sannan ta ƙaraso da sauri ta rungume shi, ta rungume shi sosai ta yadda har sai da kafafunta suka ɗaga daga kasa kamar ƴar ƙaramar yarinya.
    “You miss me this much?”
    (Kinyi missing dina har haka?)
    Muryarsa ta fito a hankali dab da kunnenta, sai ta dawo baya a hankali tana sauka akan kafafunta sannan tace.
    “Nayi missing dinka fiye da haka Sugar..”
    Yayi murmushin da fuskarsa tayi mata kyau yana kokarin cije lebbensa.
    “Really? Kamar yaya kenan?”
    “Kamar cikin malala gashin tinkiya…”
    Ta fada tana kama kuncinsa kamar karamin yawo.
    Dariyar da yayi ta jefa kansa zuwa baya.
    “I can’t beleive kina hada ni da tinkiya Babygim..”
    Yadda ya fadi abin ya saka ta dariya itama kafin tace.
    “Kawai fa salon magana ne, ni na isa nace maka haka, you are the most adorable person to me a duniyar nan yanzu Sugar.”
    “Mhmmm, Baki ce masha Allah ba…”
    Ya fada yana daga gira guda. Ta sake yin wata dariyar sosai kafin tace.
    “Dama ana cewa maza Masha Allah ne?”
    “Su ba mutane bane?”
    Sai ta cije nata lebben yanzu har yanzu daya hannunta akan kafadarsa daya kuma tana rike da gefen fuskarsa kafin tace.
    “Idan mazan suna so a gaya musu, su fara fadawa matan tukunna, especially in sun yi kwalliya ba wani dogon turanci ba…”
    “Ni ai ba sai na fada ba Babydoll, saboda ni mijinki ne, nawa hanyoyin daban suke ma bayan wannan dogon turancin.”
    “Really?”
    Ta tambaya tana daga duka girarta biyu bayan murmushin da take yi. Sai kawai ya sake sunkuyo da kansa dab da fuskarta sannan a hankali yace.
    “Ko in nuna miki? Kinga sai mu ƙara da photocopy a ciki kafin printed one din nan ya fito?”
    Ba shiri bakinta ya buɗe sannan idanunta suka zare a lokaci guda. Ta cire hannunta dake gefen fuskarsa ta naushe shi sannan ta juya tana fadin.
    “You’re soooo Bad Ma’aruf Muhammad Bakori!”
    Ta maida hannunta cikin kwanon fulawar daidai lokacin da ya zagaye duka nasa biyu a kugunta yana rungume dan karamin cikin nata da ba zaka yarda ya kai watanni har takwas ba. A kusa da kunnenta sosai ya shiga magana.
    “Zan fita wajen su Khalid ne yace wasu mutane sunyi masa magana zadu je su ga ginin, kinga idan mun daidaita dasu komai zaifi sauki dama ina nan, idan kuma ba haka ba Khalid din shi zai ƙarasa komai bayan na tafi.”
    Sai ta gyada kanta a hankali yayin da ɗaya hannunta ke zuba ruwa a cikin fulawar tana kara cakuda siraran yatsunta a ciki.
    “Zai iya shi kadai? Kuma ka yarda dashi?”
    Ta tambaya, tana cigaba da sbinda take yi,daga bayan nata, nasa udanuna a tsaye akan sbinda take yi ɗin yace.
    “Lawyer ne, abokin Ishaq, kuma gidnsa bashi da nisa da aibitin, saboda haka mai siyan wajen kawai zai samo, jiya muka samu wani kamfani NHC da suka siya duka kayayyakin aikin dake cikin asibitin har sun biya kudin, sannan na gaya miki na gama biyan staffs ɗin duka tun shekaranjiya so kin ga kusan babu abinda ya rage kenan…”
    Daya hannunta ya kara ruwa a cikin fulawar yayin da iskar da ake yi har yanzu ke cigaba da kada su kotawanne ɓangare kamshin damina da kuma sanyinta na cika gidan. Tace.
    “Allah ya taimaka komai ya faru da wuri, Allah yasa hakan ne mafi alkhairi.”
    Addu’ar tayi masa dadin da har sai da yayi murmushi kafin ya amsa.
    “Ameen.”
    Sai kuma fuskarsa ta koma daidai a lokaci guda, ya kusan hade ransa ma kafin yace.
    “Wai meye wannan kike yi?”
    Ta dan juyo da kanta ta kalle shi da murmushi jin muryarsa ta canja.
    “Fanke…”
    Fatar bakinta ta motsa yayin da sautin ya fito a hankali.
    “Fanke?” Ya tambaya cikin rashin fahimta karara.
    “Fanke da na sani na mutuwa? Me za’ayi dashi?”
    Amina ta kyalkyale da dariya ba shiri tana juyar da kanta. Sai kawai ya sake ta sannan ya juyo da ita sosai tana fuskantar sa.
    “Seriously da gaske nake, me zaki yi da fanke? Ba sai anyi mutiwa aje raba shi ranar sadaka ba?”
    “Sugar waya gaya maka? Koyaushe fa anayi… Har yara ana yiwa su je dashi makaranta sannan mutane suna cinsa as breakfast ma, me yasa sai anyi mutuwa za’aci?”
    Yanayin fuskarsa ya nuna alamun ya dan fahimta a lokaci guda, amma duk da haka hannunsa na rike da itan yace.
    “Ke me zaki yi dashi?”
    “Ci zanyi, kawai na tashi ne naji ina sha’awarsa.”
    “Me yasa baki ce in taho miki dashi ba? Me yasa sai kin wahalar da kanki?”
    Ya tambaya a hankali yana cigaba da kallonta… Sai ta karasa matsowa cikin jikinsa ta mayar da hannayenta saman kafadarsa kamar dazu sannan a hankali tace.
    “Saboda nafi son inci wanda nayi da hannuna Sugar, ka daina damun kanka aiki baya wahalar damu, we are strong!” (Muna da karfi.)
    Kalmar ‘Mu’ din da ta furta ta shiga har cikin zuciyar sa a lokaci guda, sai ya sake rike ta a jikinsa yana tallafo ta da duka hannayensa biyu.
    “Jamal is strong Babydoll, don haka insha Allah haka little one dinsa ma zai zama…”
    A lokaci guda kumatunta suka yi murmushin da take yi a kodayaushe ya fadi hakan, don tun daga ranar da suka ga gender ɗin Babyn ya tabbatar mata da sunansa… Jamal.
    Fuskar Kilishi ta gifta a cikin kanta a lokacin maganganun da ta faɗa mata suna haskawa a cikin kanta.
    _”…na san ba zan iya hana Ma’aruf kula ki ba idan har yayi niyya, amma kuma ba zan lazimci wani abu ciki ba don babu shi ko kaɗan a cikin lissafina!”_
    Murmushin da bata shirya masa ba ya kufce mata, a lokacin ta faɗa ne kamar ita ke da iko a komai, kamar ita ke da ƙaddarar su a tafin hannunta, kamar babu abinda ya isa ya giftawa wannan umarnin nata, sai gashi a yanzu tana duniyar, da lafiyarta da komai, amma bata da ikon ko da ganinsu balle har ta san me suke ciki ko kuma tayi gadarar zartar da wani hukuncin…
    Sai ta gyaɗa kanta sau biyu tana cigaba da murmushi kafin muryarta ta fito a hankali tana kallonsa, a hankalin da ko da akwai wani a kusa dasu ba kallai bane yaji abinda tace.
    “Insha Allah.”
    Idanunsa suka cigaba da kallonsa tana nazarin tarin abubuwan dake kara canjawa a hankali a hankali game dashi din. Gashin kansa ya taru sosai sai dai har yanzu bai kai na baya ba, ya taje shi sosai yana ƙyalli, don har yanzu da laushinsa, yadin jikinsa kalar dark blue ya kara fito da hasken da fatarsa ta kara yi a kwanakin sakamakon hutun da ya samu akan rayuwarsa ta baya.
    “Idan kika cigaba da kallo na haka, ba lallai ne in iya fita ba Babydoll….”
    Muryarsa ta fito a hankali yana cigaba da kallonta, sai kawai ta cije lebbenta tana murmushi sannan ta yi ɗage a hankali ta kai fuskarta dab da kunnensa.
    “Kayi zaman ka kawai, idan nayi fanken nan sai mu siyar, kaga may be ma mu samu fiye da kudin asibitin nan… Naga alama ƴan gayu basu san fanke ba.”
    Yayi murmushi sosai yana kallonta.
    “Ki rufa min asiri Babygym, ni da nake neman kudin da zan gina miki irin wannan gidan, naga alama kina son shi da yawa…”
    Idanunta ya zare a lokaci guda…
    “Ni bance ba, ni bance ba Sugar, ka rufa min asiri dan Allah…”
    Yadda ta fada tsakaninta da Allah ya bashi dariya sosai, sai kawai yayi baya da kansa kafin ya sake kallonta sosai.
    “I’m madly in love with you Amina..”
    Ya faɗa yana lumshe idanunwansa. Ta sake yin dage akan kafafunta a hankali tana wasa da yatsunta dake sarke da wuyansa.
    “Madly? Madly dai wanda na sani?”
    Muryarta ta fito kamar wani fiffiken dake fadowa kasa a hankali.
    “Idan baki gane ba Babydoll, zan iya yi miki bayani, kin san babu wanda ya san ƙwarewata anan kamar ke…”
    Ba shiri Amina ta kyalkyale da dariyar da tana yin baya zuwa gefe, hannunta ya dauko wani mug kalar baƙi an rubuta ‘Pa’ a jikinsa ta tsiyayo masa ruwan tea ɗin data haɗa a wani flask sannan ta miƙa masa.
    “Mutane suna can suna jiranka Pa….”
    Da murmushi ya karɓa ya jan kujera a gefensa ya zauna, yana gaya mata wallahi da gaske yaje, zai bata mamaki tunda har bata yarda dashi, yana bayanin tana murmushi tana juyowa tana kallonsa.
    Ƙarar wayarsa ce ta katse shi, yasa hannu a aljihu ya ɗauko ta, nambar Maryam ƙanwarta da ya gani ta tabbatar masa da waye tun kafin ma ya ɗauka.
    “Dadddddyyyy!!”
    Muryar Hamida ta faɗa da ƙarfi daga cikin wayar, ba shiri Amina ta taho da sauri ta karɓa tun kafin ma ya amsa tana tambayarta yadda take, makarantarsu da kuma gaya mata cewa gobe zasu dawo…. Dama a dazun nauyin Amma ne yasa basu gaisa ba, kafin kuma tace Maryam din ta hada ta da ita sai Aminu ya karbi wayar.
    Daga inda Ma’aruf ke tsaye yana kokarin karasa shanye tea ɗin dake hannunsa ya cigaba da kallonta yana murmushi…
    Amina itace rabin rayuwarsa a yanzu ya yarda, itace nutsuwarsa dama dukkan wani fatan samun nasarar sa… Kulawar da yake samu tare da ita, wani abu ne da bashi da inda zai je ya samu idan ba a wajen nata ba.
    Komai muƙaddari ne daga ubangiji ya yarda! lokacin da ya amince da aurenta, yayi ne saboda Jamal, saboda ya san alakarsa da ita a lokacin da yaga sunanta har ma da adireshin ta, sai gashi daga baya ya fahimci cewa wannan sunan na wata Aminan ce daban da itama take a wannan unguwar ta gadon kaya, wata Amina ce daban da suka yi makaranta tare a wajen sauran takardunsa na wajen Hajiya Maimuna da bai san dasu ba sai a lokacin da Amina ta haddasa kusancinsu…
    Allah ya sani bai san tarin alkhairin da zai lissafa da ya samu ta dalilinta ba tun daga lokacin da ta shigo cikin rayuwarsa zuwa yanzu, kamar tana tafiya ne da wani haske a kafafunta dama hannayenta ta yadda duk inda ta taka ko kuma abinda ta taɓa sai ta haskaka shi.
    Ita kaɗai, ita kaɗai ce abinda idan ya tuna cewar ta hanyar Kilishi ya samu, zuciyarsa ke yin sanyi da tarin rangwamen da yake jin cewa zai iya kyale ta da iya hukuncin da take fuskanta anan duniya, amma tabbas ne cewa tsakaninsu da ita wani hukuncin sai a lahira, don ko da giftawar sakan guda baya so ko da fuskarta ne ta gifta a tunaninsa balle kuma wani abu nata.
    Adadin yadda zuciyarsa ta so ta shine adadin tsanar da yayi mata a yanzu, tsanar dake tafiya tare da albarkacin Aminar da ta zama inuwarsa a yanzu, don abinda ya sani shine ba don ita din da yake kallo a gabansa ba, ko zai sake yi sau dubu yana kasawa, ba zai fasa ba zai yi ta kokarin da zai aika ta ne har lahirar da danuwansa ya tafi don ta riga shi zuwa da sakon da yake son ya isa ga danuwansa.
    Amma saboda Amina, saboda ita da kuma sauran tarin yanuwa da iyayensa da yake ganin kokarin da suke yi akansa wajen ganin daidaituwar lafiyarsa…
    Shi yasa a dole yake ta kokarin kai zuciyarsa nesa yana tuna tarin maganganun da kowa ke yi masa wajen ganin yayi hakurin da komai ya daidaita rayuwarsa, sai dai a duk ciki babu abinda yafi rikewa irin kalaman Ishaq da ya gaya masa cewa babu yadda suka iya da Kilishi, babu abinda zasu yi msta da zsiyo daidai da adadin cutar da tayi musu a duniyar nan, dole ne su hakura su kyale ta da iya abinda da Allah ya kadarta a rayuwarta kawai,fon wata shari’ar sai a lahira!
    “Tabbas wata shari’ar sai a lahira…!”
    Bakin sa ya maimaita hakan a yanzu yana kallon Aminan dake dariya a cikin wayar tare da Hamida…
    Shine bai fahimta ba tun asali, Kilishi bata daga cikin mutanen da suka cancanta a rayuwarsa!… Bata cikin su ko kadan.
    Sai kawai ya zaro ɗaya wayarsa ya shiga kiran mutumin da yake son ya hada shi da agency din da zai sayi kujerar makka guda biyu na Amma da kuma Baba (iyayen Amina).
    Fatansa a kodayaushe shine ya faranta ran wannan ƴar yarinyar fiye da yadda take gyara tasa rayuwar!
    *Alhmdlilah.*
    *Ƙarshe.*
    MASU ƁUKATAR A TALLATA MUSU HAJOJINSU ZA SU IYA TUNTUƁARMU TA LAMBOBIN 07045308523 MUN GODE.

    Note
    error: Content is protected !!