Farar Huta 2 – Chapter Twenty
by NadminMASU ƁUKATAR A TALLATA MUSU HAJOJINSU ZA SU IYA TUNTUƁARMU TA LAMBOBIN 07045308523 MUN GODE
“Mami…”
Sabon sunan da Hamida ta raɗawa Amina ya ratso ta cikin hayaniyar kitchen din. Shigowarta kenan bangaren bayan ta gama aikin nata tuwon ta kuma gama waya da Amma, wayar da ta sanya ta farin ciki a lokaci guda, ya kore dukkan fargaba da kuma damuwar da Kilishi ta saka a ranta bayan ta bata maganin nan.
Zuciyarta ta wanku tas da tsarin da Amma ta fitar musu, tsarin da babu shakka duk wayo da kuma hange irin na Kilishi bai isa ya tsallake dabarar tasu ba, don kamar yadda Amman ta fada ne…
_”Na gaya miki takunta zamu bi Amina, da kifi ake kama kifi,kamun da baya ganewa har sai ya ji shi a cikin komar masunci… Idan kika bi irin takun da take bi, to kin riga ki gama tsallake tunaninta har abada._
_Tun kwanaki na gaya miki cewa na fara shiri akan hakan, na gaya miki yarinyar zata makance a idanun Kilishi ne kawai amma ba’a zahiri ba. Don haka tsarin da nayi shine akwai ɗan gidan Baffa Saliyo abokin mmahaifinku na unguwar Sharada, kin gane shi?”_
Kuma a lokacin kwakwalarta bata sha wahala ba wajen hasko mata fuskar saurayin da Amman ke fadi ba, shine Babba a gidan abokin mahaifin nasu kuna kwanan nan ya kammala karatunsa na likita har ma ya samu aiki a asibitin malam Aminu Kano. Don haka ta gyada kanta da sauri tana gaya mata cewa ta gane shi.
_”Shi nasa aka kira min har cikin gidan nan Amina, sati guda da ya wuce, kuma yazo ya same ni da daddare har cikin falon gidan nan… Nayi masa bayanin komai ta sigar da ba zai fahimci cewa matsalar daga ina take ba amma kuma ya fahimci dukkan kudirina, kuma ya gaya min zai taimaka, don haka yanzu duk bayan kwana biyu zai dinga rubuto takardar magunguna daga adibiti na yara da suke shaida ciwon ido, a hankali, a hankali ana yin gaba yana kara rubuta cewa ciwon yana habbaka._
_Maryam zata dinga kawo miki takardun duk bayan wani lokaci kina kai mata da cewar yarinyar ta fara ciwon ido… Rayuwar mace dabara ce Amina kuma Kilishi shaida kawai take nema a yanzu ba zahiri ba Amina, Kilishi tana wani matakin da ba zata saka ido akan al’amura ba yanzu, saboda ko ba’a faɗa ba kin san binciken da suke yi akanta yayi nisa. Don haka a yanzu kamar tana kokarin tattare abubuwa ne don tayi ta gama karasa manufarta kawai._
_Bayan haka kuma, idan kin lura al’adar Kikishi cewar bata da bin diddigi, da ta fahimci abinda take so ya faru shikenan kawai zata gama da wannan babin, na fahimci haka tun daga ranar da ta yi miki alkawarin tafiyar su Aminu India a lokacin da aka kira ta da bayanin Ma’aruf yana asibiti kafin ma ta ganshi.Don haka ki kwantar da hankalinki Amina, komai zai tafi daidai insha Allah.”_
Kuma da wadannan kalaman hankalin nata ya kwanta, don kamar yadda Amman tace ne a yanzu hidimar dake gaban kilishi daban ce ita kanta ta lura, don ko a yanzu ma bata gidan tun dazu ta fita ba tare da kowa ya san ina ta tafi ba, wani abu da ya bawa kowa mamaki kenan, don da wuya ne idan ana hidima irin wannan ta sanya kafarta ta fita, hatta ƴanuwan Hajiya Maimuna da suka zo kowa sai da yayi ta tambayarta ana sa ran dawowarta da wuri amma har yanzu.
Wani abu da a wajen Amina yayi mata daɗi sosai, don a kullum tana son irin wannan tazarar ta dinga faruwa tsakanin Kilishi da kuma farin cikin ahalin gidan.
Sai da ta kammala komai a bangarenta sannan ta taho cikin gidan, inda anan ta tarar har wasu daga cikin ƴanuwan Hajiya Maimuna sun iso ana ta hidimar tarar Abdurrahim ɗin da Ishaq yayi waya yace ya sauka gasu nan a hanya.
Basu yi waya da Ma’aruf ba tun dazu, bai kira ta ba kuma itama bata kara kira ba, don ta fahimci kwana biyu aiki yana yawan yi masa yawa, shi yasa bata so ta zama sanadin katse shi a komai, kamar yadda Amma ta gaya mata ne kamata yayi ta zama nutsuwar da zai dinga hanƙoro a duk lokacin da hankalinsa ke juyowa zuwa gida.
Don haka ko a yanzu ma da aka ce sun taho, bata kira shi ba ko kadan, aiki suke tayi na kokarin haɗa miyar taushen da aka manta da ita kwata-kwata, anyi masar tun rana amma sauran sha’anin su Samirah ya mantar dasu miyar sai a yanzu sannan aka hadu gabadaya ake kokarin gamawa kafin karasowar tasu.
“Mami….”
Hamida ta sake kira sanda ta karaso gabanta da gudu. Amina ta juyo daga yankan alaiyahun da suke yi ita Munaya.
“Su Aunty Sahla sun ce dan Allah in tambayeki su canja min kaya?”
Ta fada muryarta na fitowa kamar haki alamun ta dade tana neman nata cikin mutanen gidan.
“Kaya Hamida? A ina suka sami wasu kayan?”
“Su suka ɗinka a School ɗinsu…!”
Ta faɗa da sauri tana katse ta. Kuma kafin tayi magana Munaya tace.
“Wannan shirmen nasu zasu saka miki Hamida… wannan karkatacciyar rigar da suka dinka?”
Tana fadin haka Amina ta gane kayan da take nufi, don itama har wajenta suka shigo suka nuna mata da murnarsu, rigar bata yi kyau ba sam!
“Wallahi Aunty Munaya tana da kyau… Pink ce fa!”
“Hamida ki bari idan Dadynki yazo sai ki tambaye shi kinji? Zai fi so ki fara tambayarsa tukunna..”
Amina tayi mata wayo ta tsaya kanar bata yarda ba sai kuma ta gyada kanta sannan ta juya da gudu.
“Har yanzu ina mamaki da akace wai yarinyar nan tana da cutar rashin son mutane da yawa, gashi nan yanzu tagane kowa a gidan nan kuma ta saki jikinta.”
Munaya ta fada tana kallo ta ta cikin ymgayaniyar sauran mutanen dake shige da fice a kitchen din du Mama Rabi, sai kawai Amina tayi murmushi tace.
“Bata son ta rabu da ita ne kawai, kin san ɗa da uwa.”
Munaya ta taɓe dan karamin bakinta tana gyara zaman glass dinta tace.
“Ba wani kula fa take yi da ita ba, ba zuwa muke yi ba amma mun sani, atbfirst ma ba’a hannun ƴar aiki Yayan ya samo ta ba? Sai gashi kuma sun dawo da ita da kansu, sannan ko ita yarinyar ba kya ji tana nemansu.”
“Haka ne.” Amina ta fada a hankali idanunta na hasko mata hoton wannan layar, da kuma fuskar matar da aka aiko takanas har cikin gidanta, har yanzu basu sake cewa komai ba, basu sake yin wani abu ba, bata sani ba ko haƙura suka yi ko kuma suna shirya wani sabon shirin ne, zata so idan har ma basu haƙuran ba su cigaba da ɗaga musu ƙafa har zuwa lokacin da abubuwa dake gabanta a yanzu zasu yi sauki, don haka gudun kar Munaya ta cigaba da maganar yasa ta tsokane ta da cewar.
“Ina fata dai kin ajiyewa Yaya Ishaq nasa special abincin?”
Kuma murmushin da Munayan tayi yasa ba shiri ta taya ta itama.
Da misalin ƙarfe tara daidai na daren, motoci guda biyu na Ishaq da kuma Ma’aruf suka shigo gidan, a lokacin sun kammala komai, jiran baƙon kawai ake yi,bakon da sai a yau Amina ta fahimci irin kewarsa da al’ummar gidan suka dade suna yi bakidaya,a da yadda kowa ke harkokinsa ba’a zancensa sai jefi-jefi sai taga kamar basu saba dashi bane ko makamancin hakan, amma yanzu ko zuwan wasu daga cikin yanuwan Hajiya Maimuna kaɗai ya tabbatar mata da matsayinsa a zuciyarsu.
Tana kitchen ita da wasu ƴaƴan Yar Hajiya Maimuna sanda suka shigo gabadayansu bayan sun baro bangaren Baffa inda nan suka fara danganawa dashi. Taji yadda falon Hajiya Maimuna ya ruɗe da hayaniyar murna kala-kala wadda bata ko gane me ake cewa.
Hannunta riƙe da farantin da aka jera kofunan kemo suka fito tare da sauran, kuma a lokaci guda idanunta suka lalubo Abdurrahim din, fari ne, fari ne sosai duk da bai kai Jamal din da take ganin hotonsa a wajen Ma’aruf ba, sannan yana kama da Ma’aruf din sosai, yanayin idanunsu da sumar gashin kansa da shima ya tara, sai murmushi yake yi zaune a kusa da Hajiya Maimuna dake kan kujera yayin da kowa ya yanyame shi da sakon gaisuwarsa.
Ma’aruf na tsaye daga bayansu riƙe da Hamida wadda ta makalkale shi, idonta ya kai kansu sanda Hamidan ke lalubo kunnesa tana rada masa wani abu da ta san ba zai wuce zancen rigar ba, a idanunsa kaɗai ta fuskanci tarin gajiyar da ba sai ya furta mata ba.
Sai kawai tayi masa murmushi ta karaso cikin falon suka gaisa da Abdurrahim din, bata ji muryarsa sosai ba amma taji kamar ya amsa da ‘Lafiya’ a hankali, kuma da yake bai santa ba shikenan abinda tace sannan ta juya kitchen din da niyyar dauko wayarta, a lokacin Hamida ta taho da gudu zuwa gabanta.
“Mami, Daddy yace inje a saka min kayan kuma yace dan Allah shima ki zo ki canja masa kayans…”
Hannunta tasa da sauri ta rufe bakinta don da ƙarfi take maganar sannan ta juyo tana kallon Ma’aruf din da ya juya yana yiwa Ishaq da ya shigo a lokacin magana, ta yaya zai gayawa yarinya wannan maganar?
Hamida bata jira taji me zata ce ba ma ta fita daga hannayenta ta tafi wajensu Sahlan da saƙonta tana murna, a lokacin ne kuma taji muryarsa yana tambayar Surayya da tazo wucewa.
“Ina Mami?”
Tambayar ta fito daidai lokacin da wani al’amari ya faru daga can falon Baffa, inda yake zaune a gaban talabijin ɗin dake ci a gabansa yana kallon labaran NTA na ƙarfe taran dare, a hannunsa guda robar robb ce da yake shafawa a ƙafarsa ta hagu.
Zuciyarsa a cike take da tsananin murnar dawowar Abdurrahim, a kowanne dare da kuma wayewar garin Allah fatansa baya wuce ganin iyalansa sun haɗu waje guda, a kodayaushe yana daga cikin addu’arsa cewar kar Allah ya ɗauki rayuwarsa ba tare da ya ga haduwar iyalansa waje guda ba, duk da cewar ya san akwai wani giɓin da har abada ba zai taɓa cikewa a zuciyarsa da ma ta sauran al’ummar gidan ba… Jamal.
Wayarsa tayi ƙara daga kan kujerar da yake jingine a bayansa, ya miƙa hannunsa ta gefe ya dauko ta, sabuwar lamba ce da b sant ba don haka ya ɗauka yasa a speaker…
Muryar wani dattijo ta fito daga cikin wayar a lokaci guda.
“Barka da dare yallabai… Ina magana ne da Alhaji Muhammad Mansour Bakori?”
“Barkanmu dai, Eh Ni ne Mansour.”
Ya faɗa yana ajiye robar robb ɗin dake hannunsa… Kuma kalaman da suka biyo, kalamai ne da babu shiri suka tsayar da duk wani tunani a cikin kan Baffa.
“Ranka ya daɗe suna na DPO Umar Nasir, matarka Hajiya Kilishi tana nan tare dani!”
***
*Washegari.*
*Ƙarfe shida da rabi na safiya.*
Motar na tafiya ne a wani irin yanayi da Zainab ta ƙasa gane gudu Jawad ke yi ko kuma akasin sa, idanunta na manne da titin dske gabansu yayin da take ji zuciyarta na bugawa a kirjinta da sautin da zata iya rantsewa cewa yana iya jinsa daga inda yake zaune.
Hannnusa ne guda akan sitiyarin motar ya danne shi da ƙarfin dake baiyana a ido, yayin da ƙafafunwansa ke ƙara take motar suna shillawa akan titin da bata san ina zai dangana dasu ba. Ƙarar sautin shigowar kira a wayarsa yafi ƙirgen da zata iya tunawa, bai ɗauka ba, bai kashe kiran ba ko ma wayar gabaɗaya, yi kawai take tana sakewa kamar ƙarar motar agaji,(ambulance).
Ta hadiye rawu a cikin maƙogwaronta a hankali tana sake matse yatsunta a cikin hijabin dake jikinta, wannan dogon hijabin sabo da ya bata, shi ta saka tayi sallar asubahin yau, sallar da tana sallamewa Jawad ya shigo dakin, kuma bai jira komai ba yace ta taso ta biyo shi.
Bata san me yake nufi ba, bata san ina zasu ba don haka ta taso ta biyo shi ɗin zuwa cikin falon da komai yana nan kamar yadda yake a jiya, kayan abincin dake kan dining suna nan har a sannan babu wanda yabi ta kansu, bata ko buɗa su ba tun a jiyan, daga su har ledar magungunan da yace mata taje tasha suna nan a wajensu.
Don babu yadda za’ayi ƙafafunta su iya dauko ta daga inda ya bar ta a jiyan zuwa cikin falon, tasirin maganganun da ya gaya mata kafin ya fita su suka manne ƙafafunta a inda ta tsaya kuma suke ta maimaitawa a cikin kanta, maimaitawar da duk zagayen da tunaninta ke yi ya dawo a waje guda yake tsayawa, waje gudan da har a yanzu da garin Allah ke kokarin wayewa abubuwan da ta gane a ciki basu da yawa, don bayan ma kankantar tasu, ita shaida cewa ko giyar wake aka taru aka sha a garin tunaninta baya hango kasancewarsa.
Aure ba ƙaramin abu bane ta sani, ana yinsa kullum, cikin kowanne sati na duniya, amma duk da haka yana da wani irin girma da kuma darajar da ubangiji ya ɓoye a cikinsa, shi yasa har kullum yake kamar baƙo a zukatan al’umma, idan za’a gama yau a fara wani gobe, na goben zai zo ne da wani sabon farin ciki da kuma doki a zukatan masu yinsa.
Aure abu ne da rayuwar mutum ke tafiya gabadaya akai, rayuwar da zata mamaye farko har zuwa ƙarshe na kwanakin ka a duniya, shi yasa har yanzu bata ga dalilin Jawad na cewar zai aure ta ba don bata ga wani abu da take dashi a duniyar nan da zai iya hada rayuwarsa da tata ba.
Bayan haka ma, ita bata jin cewar tana sonsa, zuciyarta ta riga ta gama tsorata da tarin abubuwa, tun daga rayuwar da ta baro har zuwa wadda take yi a yanzu, sannan shi kansa tsoronsa ya fara dasawa a ranta, tsoron da a yanzu bata san ta yaya zata iya juya shi ya koma wani abu daban ba….
_”Ko ke baki da zaɓi yanzu Zainab, zan aure ki ko baki gama yanke shawara ba, idan yaso daga baya zan koya miki yadda zaki so ni…”_
Ta rufe idanunta a hankali tana tuna sanda suka iso wajen motar tasa yace mata ta shiga, a lokacin ne kafafunta suka tsaya waje guda cak! Ta tsaya daga daidai bayansa tana tambayar ina zasu tafi? Ina zai kaita a wannan safiyar ba tare da Hajiya Mardiyya ta sani ba ko kuma ta bata izini.
Abinda tayi dana sanin tambaya kenan tun daga kirgen wancan lokacin har zuwa yanzu, don yadda ya tsaya a gabanta ya rike hannayenta duka biyu da iya karfin da take tunani nasa ne, ya gaya mata cewar baya son baya son sake jin muryarta kawai tayi dukkan abinda yace, da wani yanayi ne da zata rantse bata taɓa gani a fuskar wani mahaluki ba, don sandan hannayenta duka biyu suna zafi da tasirin riƙon da yayi mata. Shi yasa bata ƙara cewa komai ba har a yanzu da suka yi nisa cikin tafiyar da bata san ina ne ƙarshen ta ba.
Zuciyarta na faman bugawa ne cike da tsoron irin tarin laifin da yake kara mata a wajen Mahaifiyarsa, Hajiya Mardiyyan da tun a jiya ta bata umarnin haɗo kayanta don ta maida ita garinsu, da kuma Deluwa matar da ta kawo ta gidan, don bayan rashin mutunci Dekuwa gar azaba tana yiwa duk yarinyar da ta kai gidan aiki ta gudu…
Tunaninta ya tsaya a lokacin da motar ta tsaya kusan a lokaci guda, kusan a lokacin gudun da tasirin hakan yasa tayoyinta gaba daya suka fitar da wata ƙara da ta cika kunnuwan su da suke ciki ma, kuma kafin Zainab ta sake wani tayi wani tunani ya ɗauki wayarsa da har a lokacin ke ƙara ya jona da wata waya dake jikin motar.
“Jawad, Jawad… Jawad…”
Muryar Aunty Sadiya ta cika speakers ɗin dake cikin motar a take, daga bayanta hayaniya ce mai yawa ke tashi yayin da sautin kukan da babu shakka na Hajiya Mardiyya ne ke barazanar fin muryar tata karfi. A lokaci guda Zainab taji cikinta ya hautsine.
“Jawad kana ji na? Kana ina? Ina ka tafi?”
Tambayar ta shiga kunnen Jawad da sigar rainin hankali, ina ta tafi? Ina suke tunanin zai tafi bayan inda suka gaya masa?
A daren jiya har wajen ƙarfe biyun dare ana case din da yake gani da jin sa tamjar a mafarki, bayan ya shaidawa Alhsji Bashir komai, shi da kansa ya karbi wayar hannunsa, ya kira ƴansandan da shi ya kira ya tsayar daau daga zuwa gidan. Sannan shi da kansa ya kira mijin Aunty Sadiya yace ya kawo ta gidan a lokacin, bayan haka, ya kira dukkan sauran ƴanuwan Hajiya Mardiyyan da suke a garin yace suma yana bukatar ganinsu, kuma cikin abinda bai haura awanni biyu ba dukkaninsu su huɗu suka hallara, mata biyu da yayyensu maza biyu.
Hajiya Mardiyya itace ta karshe a kiran Alhaji Bashir din, alokacin ta kira wayar Jawad dake rile a hannunsa fiye da kirgen mai kirga, don tana ta nemansa a cikin gidan, bangaren Alhaji Bashir ɗin ne kawai bata zo ba don watakila tana tunanin bata da kwarin gwiwar fuskantarsa a wannan lokacin, amma sai gashi kafafun nata sun kawo ta, kuma a lokacin da ta shigo tayi arba dasu, ƴanuwanta har su hudu cikin wannan dare da kuma shi da Alhaji Bashir ɗin dake mata kallon da babu bukatar asarar kalmomi, sai gashi ta samu kwarin gwiwar ƙarasowa har gaban nasu.
Kuma a jiyan yaji komai, yaji dukkan wani bayanin daga bakin ita da kuma Aunty Sadiyan da suka fahimci tabbas dubunsu ta cika zuwa wata dubun.
Sun tunawa da kowa shekarun da Hajiya Mardiyya ta shafe babu haihuwa s gidan alhali dukkan sauran kishiyoyinta na tara ƴaƴa, da kuma yadda ita Aunty Sadiyan ta dinga ziga ta akan shawarwari kala-kala, wadda bata dauki kowacce ba sai ta cewar tayi karyar tana da ciki, ta raini abinta kamar gaske idan lokacin haihuwarsa yayi, zasu samo jaririn da zata dawo dashi daga asibiti bayan sun tafi su biyu ba tare da kowa ba.
Kuma hakan suka yi, don kafin lokacin aka bawa Aunty Sadiyan labarin wata ungozoma acan wani kauye dake irin wannan harkar ta siyar da jarirai idan ta karbi haihuwa don a kaidar aikinta ta idan ta karbi haihuwa yaro bai zo da rai ba, ita ke binnewa, wai ladan aikinta kenan saboda jahilci irin na mutanen wannan ƙauyen a lokacin, don haka idan har ta samu masu nema, to tana basu ranar da zata karbi haihuwa ne su zo, ita kum idan har ta ciro dan, to akwai wani lakani nata da take yiwa jarirai da tun kukan farko basa kara wani, zasu yi ta bacci ne mai tsawo har zuwa wani lokaci ta yadda za’a yarda da ita dewar sun mutu.
Da wannan dabarar take shaidawa nmasu haihuwa cewa dansu ya rasu, da sun ganshi sai a bata gawa ta taho da ita gida, inda daga nan zata samu hanyar da zata yi ta dauko jariri ta kawowa masu bukata su bata kudinta.
Aunty Sadiya tayi bayanin haka ce ta faru dasu, a ranar da suka yi karyar naƙudarta ta tashi a ranar suka ɗauki mota su biyu kawai ita ke tuƙawa suka nufi can wannan ƙauyen da a lokacin ake ce masa Yakura, amma a yanzu ya koma Garun Albasu, anan suka sami matar da babu wani bata lokaci suka bata kudinta ita kuma ta basu yaro, inda murnarsu ta ƙaru ganin namiji ne.
Daga nan suka kama hanya suka dawo da cewar ta haihu kuma har an sallamo ta daga asibiti, kuma babu wanda ya zarge su aka shiga murna da shagalin suna… Kuma tun daga wannan lokacin suka binne wannan abin a tsakaninsu su biyu kawai ta yadda ko sauran ƴanuwansu basu taɓa sani ba sai a yanzu da ƙwaryar da suke riƙe da ita ta faɗi har kasa ta tarwatse.
Yana iya jin muryar Hajiya Mardiyyan a cikin kansa har yanzu, yana jin yadda take magiya da kuma kukan gayawa Alhaji Bashir cewa wallahi sauran ƙannensa mata da ta haifa shekaru biyar bayan shi ƴaƴan su ne na cikinta, ita da ƴaruwarta sunyi garaje ne kawai na tunanin bata haihuwa na tsawon shekaru bakwai kafin lokacin da ta sami cikinta na gaske.
Ya rufe idanunsa a hankali ya buɗe su kafin ya amsawa Aunty Sadiya da abinda take jira.
“Ina hanyar Kaduna…”
“Kaduna?”
Ta tambaya a lokaci guda.
“Inalillahi wainna ilaihir raji’un…. Haba Jawad me yasa zaka kama hanya da sassafen nan? Tun ɗazu muke nemanka, ina zaka tafi? Aƙalla ka saurare mu mana…”
Ina zai tafi? Ta yaya zai cigaba da zama a gidan nan alhali tun a daren jiya labarin komai ya zagaye gidan daga bakin Hajiya Yagana da bashi da tsntamar cewar ta ji dukkan tattaunawar da akayi.
Ta yaya zai kara zama yana kallon idanun kowa ba tare da wani bayani mai gamsarwa da zai iya kare kansa a wajen su ba? Bai ce ba zai dawo ba don ko Alhaji Bashir da yaje yiwa sallama abinda ya gaya masa shine zai dawo bayan ya sami ƴanuwansa, kuma shi bai hana shi ba ko yace masa yayi garaje sai su….?
“Ka yiwa Allah da ma’aikinsa ka dawo Jawad, ka sani a cikinmu babu wanda ta taba cutarka, kuma bamu yi komai don mu cuce ka ba, to me yasa ba zaka saurare mu ba Jawad? Me yasa ko sau ɗaya ba zaka ji daga bakin mahaifiyarka ba… Tunda komai ya fito fili ka tunanin zamu sake ɓoye maka wani abu ne?”
Ya girgiza kansa a hankali kamar tana kallonsa.
“Kar ku damu Aunty Sadiya zan dawo….”
Abinda ya faɗa kenan kawai sannan yatsun hannunsa suka ni kashe kiran, sai dai muryarta ta sake kwararowa kafin hakan.
“Ina wannan yarinyar Jawad? Ina Zainab?”
“Tana tare dani.”
Amsar ta fito cikin tattausan amon muryarsa da tsabar ruɗani da kuma tashin hankalin da yake ciki ya haifar dashi.
Kuma daga shi har Zainab ɗin, suna jin salatin da Aunty Sadiyan ta ruɗe dashi kafin ya kashe wayar.
Ɗib kiran ya katse a kunnen Zainab, yana sake tonawa kanta sautin zuciyarta dake bugawa a ƙirjinta, kuma bata juyo ba, bata juyo ta kalle shi ba, kanta na sunkuye tana kallon yatsunta dake girgizawa akan cinyoyinta, nemanta suke yi ita ta sani, shi tasa ko baccinta na jiya ta cika da mafarkai masu nauyi… Watakila gani suke tana da hannu a duk abinda Jawad ke yi.
Kuma ta sani ko a gaba suka sa ta bata da yadda zata iya yi musu bayanin cewa bata san komai ba, bata san me yake yi ba ko kuma su abinda suke yi, kamar koyaushe a rayuwarta babu wanda ya taba bata zabi a rayuwarta, komai faruwa kawai yake a gaban idanunta yayin da take jin tamkar an rufe bakinta an kuma daure hannayenta, kamar tana tsakiyar wani waje ne da bata da mafita kotawanne ɓangare,kamar tana cikin kwale-kwale ne a tsakiyar teku ta yadda ruwa ya zagaye kowanne bangarenta… Don haka bata da wani zaɓi illa ta zuba ido taga yadda Allah yayi da ita kawai.
Tana ji sanda ƙarar wani kiran ta cika motar, sannan taji sanda muryar wani namiji ta amsa.
“Oga sir..”
Shine abinda ya fara faɗa bayan sallama. Ta gefen idonta taga sanda ya dafe kansa yana yin baya dashi kafin ya amsa.
“Sulaiman ina ga a location dina saura bai fi minti biyar ba na kusa isa zuwa garin, ka tabbata mutumin da zaka hada ni dashi ɗi yana nan a gari?”
Daga cikin wayar Sulaiman din yace.
“Yana nan Yallabai, bai fi minti biyar ba .a da muka yace min ya riga ya fito bakin titi yana jiranka, sunansa Nura, na gaya masa kalar motarka to da ka iso zai gane ka kawai.”
Ya gyaɗa kansa sau biyu yana faɗin.
“Shikenan, nagode.”
Sannan ya kashe wayar. Taji ƙarar sanda ya ajiye ta a gefen dake tsakaninsu kafin abinda bata yi zato ba ya biyo baya…
“Zainab zaki ci wani abu?”
Muryarsa a hankali ta fito,cikin amon dake shaida mata cewa nasa ne, ya dawo daidai ba kamar ɗazu da ta tabbata baya cikin hayyacinsa ba.
Sai kawai ta rufe idanunta a hankali tana jin ɗumin kwalla na kokarin cika su.
“Kina jin yunwa?”
Ya ƙara tambaya a hankali, sai ta girgiza kanta a hankalin itama ba tare da tace komai ba, shiru ya sake ratsa motar na wasu sakanni kafin ya kunna ta su sake hawa kan titin, kuna tafiya yar kadan ta isar dasu cikin wani tsohon gidan mai da ya koma kasuwa kuma maciyar mutanen hanya, wajen da ya hada da tarin kantinan da kusan duk wani abinda matafiyi ke bukata zai samu.
Bai kashe motar ba ya barta a kunne har da mukullin a jiki sannan ya bude ƙofar motar ya fita, Zainab ta bishi da kallo ta cikin mutanen dake wajen, kayan jikinsa wani kalar yadi ne mai ruwan toka, tafiyarsa kadai ta banbanta da tarin mutanen wajen har zuwa sanda ya bacewa ganinta, Idonta ya shiga yiwa cikin gidan man kallon sani amma nan da nan ta ƙaryata kanta, ta dawo da idonta ya dawo kan mukullin motar.
Zuciyarta ta ayyana mata yadda zata koma mazaunin direban ta murda shi, da zarar ta tashi sai tashi sai ta juya kanta ta fita daga wajen, ta komawa dukkan hanyar da suka biyo a baya har zuwa cikin gidansu. Wataƙila idan tayi hakan zata iya wanke kanta a wajen Hajiya Mardiyya da kuma Deluwa, watakila zasu iya yafe laifinta su mayar da ita gida wajen mahaifiyarta komai ya ƙare, komai… Har dashi kenan? Wani bari na zuciyarta ya ayyana mata, kuma rashin sanin amsar yasa ta haɗiye wani abu a maƙogwaronta.
Cikin abinda yake ƙasa da minti goma Jawad ya dawo har a lokacin tana sake-saken a ranta, bata ko ganshi ba sai ji tayi an buɗe ƙofar gefenta, kuma kafin ta dago ya ajiye tarin ledojin hannunsa akan cinyarta sannan ya mayar da kofar ya rufe.
Idonta yabi ledojin da kallo tana jin kanshin kayan abinci kala -kaka da kuma nauyin robobin ruwa dana lemo da suke cikin tasu ledar daban, a cikin wata ƴar karamar leda fara, ta gano magunguna, irin magungunan da ya siyo mata jiya sak wanda suka bari a falon ɓangarensa.
Mamaki ya kamata, tsananin mamakin wani irin mutum ne Jawad da kuma halayensa, sai dai wannan mamakin bai kai koi’ina ba sai a lokacin da suka isa kofar shiga garinsu ‘Garun Albasu’ minti biyar bayan barinsu daga gidan man nan, a lokacin da ta ɗago kanta jin ya rage gudu suna kokarin sauka daga titi, lokacin da ta ɗago da idanunta suka sauka akan kasuwar ƙauyensu ta bakin titi kafin ka dangane da cikin garin, da kuma fuskar ɗanuwanta Nura, (ɗan mijin mahaifiyarta) yana washe baki yana tunkaro motar tasu da saurinsa.
A wannan lokacin abinda taji yayi kama da fadowar zuciyarta a cikin kirjinta, taji kamar ta faɗo ne ta fice ta ƙasan motar, tayoyin baya kuma suka bi ta kanta suka tarwatsa ta, jininta ya fallatsa a koina na jikin motar!
***
A cikin harabar tsakar gidan, mata ne kala-kala da kuma yara dake wasan su, matan na ayyukansu na yau da kullum wanda ya haɗa da girke da kuma surfen hatsi kala-kala, kusan rabinsu na goye ne da ƙananun yara a bayansu yayin da suturarsu kaɗai idan ka kalla, banda gini kasan dake zagaye da tsakar gidan zai shaida maka cewa mutanen karkara ne.
A wannan lokacin ne kuma sallamar wani dattijo ta karaɗe koina a tsakar gidan, sau daya ya furta sallamar amma a lokaci guda yanayin wajen ya canja, yara suka mike a guje suka nufi kasan rumfar dake barandar dakuna suka taru waje daya gabadayansu yayin da matan kowacce ta mike tsaye suna amsawa, yan tsofaffin dake zaune suna aikin busa ne jadai basu mike ba.
Mutumin ya shigo sanye da vabbar rogarsa wadda ta banbanta da yar ciki, hular kansa mai kyau ce wadda dattin dake tattare da ita ya boye hakan.
“Ina Talatu? Talatu, Talatu….!”
Kakkaurar muryar tasa ta fada yana karasowar ciki. Matar dake amsa sunan Talatun tayi saurin sakin itace da ta debobdon kara wutar girkinta tayo gaba tana faɗin.
“Gani Malam..”
Kuma tsaye ya nuna ta yana fadin.
“Wato Talatu rashin mutincin naki bai kai karshe ba dama? Sakin da na dannewa zuciyata ban yi miki wancan karon ba shi kike nema?”
Ba shiri Talatun ta dafe goyon ƴar dake bayanta sakamakon faɗuwar gaban da taji ta ratsa har ta bayanta tana shirin kwance goyon.
“Inalillahi wainna ilaihir raji’un Malam me kuma ya faru? Wallahi Malam vabu abinda na kara yi.”
“Babu abinda kika kara yi? Karya nake yi miki kenan? Ko kuma shi wancan ƙaton Gardin da Nura ɗan gidan Malam Sadi ya rako min shi har majalisa suka zo nema ki dake ƙaryar suke? Dududu kwana nawa kenan da kika shigar min da mutum har ɗakin aurenki? amma ace duk uw*r tarzomar da aka sha baki hankalta ba? Allah wadaran auren jinin Hanne wallahi…!”
Ya fada muryarsa na dagawa, dagawar da tasa sauran matan dake gefe murmusawa suna kallon junansu. Talatu ta sake talkafe goyon bayanta tana girgiza kanta.
“Wallahi Malam, bani da masaniyar komai, ni ban san me suke nema a wajenta ba, ban san ma me yi musu kwatancena ba…”
“Ina zaki sani Talatu? Dama ina zaki sani… Muna zaune a majalisa kawai mota ta faka aka ce wai gidana ake nema, kin kunyata ni a cikin jama’a, ace ina zaune a gida da mata amma wasu maza daga waje suna zuwa nemanta? Wallahi darajar Malam da na karbi aurensa a wajenki kawai kike ci Habiba, amma anyi na farko anyi na biyu, na rantse da kabarin ubana aka sake samun wani ɗan kaza-kazan da zai zo nemanki sai kin bi shi, billahillazi kafar sa kafarki, na gama zaman aure dake…”
Talatu ta gyada kai cikin amincewa da sauri sannan kafafunta suka durkusa har kasa cikin kasar wajen tana neman afuwa. Kuma sai da ya gama cikarsa ya bayse sannan yayi kwafa yace.
“Ɗauko hijabinki, suna soro muje inji me ke tafe dasu.”
Sai ta girgiza kanta, tana kallonsa tace.
“Wallahi Malam ba sai na fita ba, waɗancan mutanen da suka zo sun bar lambar wayarsu suka ce in kira su idan na samu wani labari, to indai suma Hanne suka zo nema zan basu lambar su nemi waɗancan su gaya musu komai, ka yarda dani Malam wallahi bani da wata alaƙa dasu.”
Muryarta na rawa cike da tsoro yayin da yake kallonta idanunsa na haskawa da dimbin bacin rai da kuma fushin da a zuciyarta take kirga adadin kwanakin da zasu wuce kafin ta sake samun fuskarsa.
Muryarsa cike da ba’a, yace.
“Akwai abinda zasu nema ne da ya wuce Hannen? Duk danginku akwai mai jawo muku tsiya ne kamar ita?”
Talatu bata ce komai ba tana tsugunne a gabansa, hannayenta dake tallafe da goyon ƴarta na rawa a ƙasan goyon, kuma bata san lissafin da yake yi ba tsawon wucewar wasu mintuna kafin yace.
“Tashi ki ɗauko lambar, wannan shine na farko da kuma na ƙarshe a lamarin nan na gaya miki Talatu…”
Ba shiri sai ta miƙe tsaye, kuma bata ko damu da karkaɗe kasar da ta ɓata kafafunta ba, ta miƙe da sauri ta nufi ƙofar ɗakinta, kuma cikin abinda bai wuce minti guda ba ta dawo riƙe da wata farar takarda da take a miƙe samɓal, ya fizga tamkar zai yaga sannan ya juya ya nufi hanyar fita.
A ƙofar gidan ya tadda Jawad da kuma Nura dake tsaye suna jiransa, ya juya ya kalli motar da suka bari a can gaban gidan, wannan yarinyar dake ciki har yanzu tana nan, ta juyo tana kallonsu idanunta na na kallonsu a zare, sannan ya kalli tarin yara har da matasan da suka tsaya daga can nesa suna kallo su, don labarin maƙudan kudin da aka bashi ya danna a aljihu bayan ya fara fadan babu mai ganin matarsa ya kusa biye kunnen duk wanda ya sanshi a lokacin.
Ya ja tsaki mai tsawo yana fadin.
“Allah wadaran munafukai…!”
Sannan ya juyo ya sake kallon Jawad ɗin dake a gabansa.
“Yallabai, matata tace bata da wani bayani da zata yi maka don Hanne ta rasu shekaru shida da suka wuce, amma ga wannan lambar, idan ka kira watakila zaka sami wani bayani a wajensu, don suma kamar kai sun zo nemanta kwanaki.”
Idanun Jawad na kallonsa har yaje karshen zancensa, ba haka yaso ba ko kadan, yaso akalla yaga Talatun yaji bayanin komai daga wajenta, tunda sun sha tambaya tare da wannan matashin Nura amma babu wanda ya gane Hannen da suke nema sai da kyar aka samu wanda ya faɗa musu cewa matar ta daɗe da barin garin amma akwai wata Talatu da zata iya basu labarin inda take.
Kamar zai yi magana, amma sai zuciyarsa ta shawarce shi da cewar yabi mutumin a haka, don ya lura idan ya matsa za’a iya samun matsala, yau ya fara nema ba lallai ya samu komai a yau ba dama… Don haka sai kawai ya gyada kansa sannan hannunsa ya karɓi takardar kafin bakinsa ya furta godiyar da bai san ta wace sigar kalamai suka fito ba… Idanunsa suka manne da suna da kuma nambobin dake rubuce a jikin takardar lokacin da mutumin ya juya yana zagin jama’ar dake shirin taruwa a kodar gidan bunun.
Hajiya Salamatu.
080673….
****
Ruwan da ya sauka akan fuskar Awwalu mai tsananin sanyi ne fiye da na farko da Ɗantaro yasa aka watsa masa awanni kaɗan da suka wuce.
Ya buɗe idanunsa cikin tsananin firgita, yana kallon wadanda ke tsaye a gabansa, da farko inuwoyi idanunsa suka fara nuna masa kafin fuskar Ɗantaron dake saitinsa ta fito tar cikin hasken safiyar dake ratsawo cikin fankon ɗakin da aka kawo shi aka kulle tun a daren jiya.
“Ni zaka yiwa shunen ƴan sanda Awwalu? Ni zaka sa in aika yarana gidanka alhali ka aika ƴan sandan can? Ni zaka yaudara Awwalu?”
Ƴan sanda! Kalmar Ƴan sandan ta doka wata irin tsawa a cikin kan Awwalu a lokaci guda tana sa shi wartsakewar da ba shiri.
“Ƴan sanda suka gani a gidan nawa?”
Muryarsa ta fito tare da shakku da kuma tashin hankali da baya neman tabbacinsa, kuma Ɗantaron bsi yi maganar ba sai kawai ya girgiza kansa sannan yayi wa yaransa biyu daje tsaye da bokitai alama da su karasa zuba masa ruwan bokitan dake hannunsu wanda ɗaya na zafi ne ɗaya kuma na sanyi, mai rike da na zafin ne ya fara juye masa tun daga saman kansa sannan na sanyin ya kwara masa shima har ƙasa.
Tasirin zafi da kuma sanyin da suja ratsa jikinsa suka sa dukkanin jijiyoyinsa riƙewa bakiɗaya, ya shiga kokawa da dawowar numfashinsa a kirjinsa kafin ya muryar Ɗantaron ta ratsa kunnensa.
“Kai baka isa ka tona min asiri ba Awwalu, wallahi, wallahi daga yau taka ta kare!”
Kuma ga mamakin Ɗantaro sai kawai Awwalun yayi murmurshi, murmushi mai fadi sannan ya girgiza kansa, don abinda Dantaron bai sani ba shine su duka biyun ne tasu ta ƙare! Tunda ya riga ya jawo shi jikinsa shikenan tasu ta kare gabaɗaya!
MASU ƁUKATAR A TALLATA MUSU HAJOJINSU ZA SU IYA TUNTUƁARMU TA LAMBOBIN 07045308523 MUN GODE
