Farar Huta 2 – Chapter Twelve
by NadminMASU ƁUKATAR A TALLATA MUSU HAJOJINSU ZA SU IYA TUNTUƁARMU TA LAMBOBIN 07045308523 MUN GODE
*Abuja.*
*No. 1146 C west, Maitama.*
A cikin ƙatuwar harabar gidan wadda duk girman wajen ya cika taf da al’umma da koma motaci, baka jin komai sai tarin hayaniya, mata da maza ne fal da lokaci zai dauke ka da yawa wajen ƙirga su ke ta zirga-zirga, kowa sanye da ƙarshen akwatinsa sai ƙyalli kawai kake gani a kowacce kusurwa, musamman ga matan da mafiya kayansu walƙawa kawai suke a cikin fitulun compound ɗin, irin dai kayan da mafi yawan mata ke amfani dasu wajen halartar taron biki na dare, (Dinner).
Taron bikin ƴaƴa biyu mace da namijin da ake gudanarwa a gidan wanda suka kasance ƙannen Jawad din dake tsaye daga barandar ɗakinsa a lokacin yana kallon hayaniyar mutanen dake fita a jerin motocin dake layi, amma duk da haka kamar ba ɗibansu ake yi ba, tunda a cikin tarin ƴanuwansu kaf kowa ya tattaro ya dawo gidan da sunan zama har a gama bikin.
Kananun kaya ne a jikinsa daga wandon har rigar duka farare, kuma gama wayarsa kenan da Haro wanda ke ƙara gaya masa sababbin hanyoyin da ya sake samowa na yadda zasu kama Ma’aruf a hannunsu.
Hannunsa ya koma wajen kira ya sake danna nambar mahaifiyarsa da yake yi a cikin wayar amma har ta sake katsewa ba’a ɗauka ba, karo na shida kenan daga 6uta har ƙannensa biyu babu wanda ya ɗauka, mukullin motarsa da ya bari a ɓangaren nasu yake nema, don shima ba zai zauna ba, nan da minti talatin ya sani kowa ya bar gidan don haka shima yana da inda zai je ba zai zauna ba, dalilin fitowarsa kenan barandar ya tsaya ko zai hango ɗaya daga cikinsu yayi musu magana su kawo masa muƙullin, amma babu alamarsu.
Ya ja tsaki a hankali sannan ya juya ya koma cikin ɗakin, akan gadon ya jefa wayarsa sannan kai tsaye ya nufi kofar dakin, ya fita zuwa koridon dake kaiwa hanyar matatattakala ya sauka zuwa falon ƙasa, a jikin falon daga can ƙarshe akwai wata kofa dake fuskantar babbar kofar da za’a fita zuwa waje, ya buɗe ta ya taka cikin koridon dake bullewa zuwa ɓangaren mahaifiyar tasa, ya buɗe a lokaci guda da hayaniyar wajen ta cika kunnensa.
Allah ya sani ya rasa tunani irin na mahaifiyarsa, a kullum kawai yana ɗora alhakin ɗabi’unta da rashin karatun ta ne, don labari ne da kowa ya haddace shi cewa irin fulanin dajin nan ce mahaifin nasa ya auro ta, idan ba haka ba bai ga dalilin da zai sa itama tayi tata gayyar har kuwa da ƴan kwana ba don ana bikin ƴaƴan kishoyoyinta.
Ya shiga cikin falon inda mutane da yawa suke, suna ta gaishe shi ya amsa sama-sama don kaɗan daga cikinsu kawai ya sani wanda sune manyan, wata yayar mahaifiyar tasa ta tsayar dashi suka yi magana akan aikin da take son ya samowa danta a wajen aikinsu kafin ya shige kai tsaye zuwa ɗakin mahaifiyar tasa.
“Wallahi kinyi kyau, babu wadda ta isa tayi miki kallon raini a cikinsu, babu wadda zata yada miki maganar cewa ba kya fantamawa kamar su.”
Abinda ya fara ji kenan yana fitowa daga bakin wata Aunty Nana kafin hoton mahaifiyar tasa ya shiga idonsa, ta saka wata doguwar riga ta lace da zai rantse da Allah babu wajen da yatsa ɗaya zai zauna ba tare da taɓa tarin dutsunan dake ƙyalli ba, sai walƙawa suke suna haske kota’ina.
Ba shiri ya haɗe ransa a take sanda mutanen ɗakin ke kiran sunansa da korafin tun safe suke nemansa.
“Naje aiki ne.”
Shine amsar da yabi kowanne su dashi bayan gaisuwa.
“Mamah mukullin motata nake nema.”
Ta tambaya kai tsaye sanda ya isa gabanta, sai tayi murmushin da ya nemi karya zuciyarsa a lokaci guda, murmushin da yasa ba shiri duk wannan haɗe ran nasa yabi iska.
“Haba Babana, yanzu ba zaka ce nayi kyau ba…?”
Yasa yatsansa daya ya shafo kan hancinsa, sannan yace.
“Mamah kinyi kyau… Kinyi kyau sosai.”
Sai kuma ya kara da.
“Sai dai na so don ra’ayinki kika yi wannam kwalliyar ba don wani ko kuma wasu ba.”
Murmushin da take bai bar fuskarta ba tace.
“Ka kawo min mata ka gani wanda zanyi don kai bashi da iyaka Babana, har sai ka rufe idonka.”
Murmushin da bai shirya ba ta sake saka shi kafin ya gyaɗa kansa yace.
“Allah ya kaimu, key ɗin motar yana wajenki?”
Daidai lokacin da Zainab ta shigo dakin a lokacin, hannunta dauke da wani katon kwando, yana jin yadda sauran Aunties ɗin nasa na ɗakin suka samu damar korafin jiran bikin nasa da suke yi suna faɗin so yake yi su haɗa shi da ƙannensa su Khairat tukunna, amma hankalinsa baya kansu tun sanda ta shigo dakin, hannunta na ɗauke da wani ƙaton kwondo da ta ciko kayan da bai san na menene ba dasu, idonsa ya bita da kallo sanda taje har can ƙarshen ɗakin ta bude wardrobe tana saka kayan.
“Zainab anyi namu wankin?
Wata ta tambaya a cikin mutanen dakin, sai ta ɗaga kanta da sauri tana murmushi tace.
“Eh suna cikin dryer ban ƙarasa dasu ba, amma yanzu zan kwaso.”
Wata da ya san sunanta Aina’u tace.
“Kafin mu tafi ki kwaso min kayan da kika kai mota ɗazu, na fasa barinsu anan.”
Bata amsa ba wata tace.
“Zainab an karɓo min saƙon kuwa?”
“Yanzu zan karbo Aunty, ban samu lokaci bane tun dazu.”
Sai ta gyaɗa kanta tace.
“Babu komai, ai kina kokari ma, tun safe kike tsaye.”
Daga inda Hajiya Mardiyya ke ƙoƙarin lalubo mukullin motar Jawad ɗin tace.
“In dai Zainab ce ai ba daga nan ba,bata zama sam.”
Duk maganganun da ake yi idanun Jawad na kan yarinyar, yana kallon yadda take saka kayan cikin wardrobe da sauri da kuma yadda hannayenta ke rawa, wani abu ya gifta cikin zuciyarsa da bai san menene ba.
Ta gama saka su tazo wucewa daidai lokacin da Hajiya Mardiyya ke miko masa muƙullin motar, kuma bai ji me take cewa ba kawai ya karɓa sannan yabi bayan ta, suka fita daga ɗakin tare.
Kwandon da ta juye kayan ne a hannunta tana ta ratsawa ta cikin mutanen dake ɗakin har waje, hannayensa duka cikin aljihun wandonsa yana bin bayanta har suka fita wajen, tayi kwana zuwa hanyar inda ɗakunan kwanan su suke,kuma bai tsaida ita ba har suka fara shiga wajen suka bar hayaniyar mutanen nan a baya sannan ya kira sunanta.
“Zainab.”
A lokaci guda ta tsaya cak kafin ta juyo da sauri, idanunta suka zare a lokaci guda da ganinsa, tasirin mamakin ganin nasa ya haska ƙarara a fuskarta kafin ya lura cewa rawar da hannayenta ke yi sun ƙaru. Sai kawai ya taho ya ƙaraso dab da ita ya tsaya. Hasken fitilun wajen ya nuna masa yadda fatar bakinta ta bushe sosai ksmar yadda ya hango.
“Kinci abinci?”
Ya tambaya kai tsaye yana kallon ta, bashi take kallo ba ta sunkuyar da kanta ƙasa kawai, kuma jin tambayar yasa babu shiri ta shiga ɗaga kanta da sauri, ɗaga kan da a cikinsa ya fahimci cewa amsaawa kawai take don ta tsorata amma hakan ba gaskiya bane.
Sai ya ja tsakin da bai shirya masa ba, ƙararsa ta fito ƙarara, sannan yana kallonta ya sake maimaita abinda ya fada.
“Ba wasa nake miki ba, nace kin ci abinci?”
Wucewar sakan daya ,biyu kamar ba zata amsa ba sai kuma ta girgiza kanta a hankali alamun A’a. Ya cije lebbensa yana gyada kai sannan yace.
“Biyo ni.”
Ya fada ba tare da ya matsa ba, ta ɗago ta kalle shi sannan ta girgiza kai har yanzu idanunta na nunawa da tsoro.
“Akwai aikin da zanyi da yawa, su Hajiya suna ta jira na, dan Allah …”
Bata ƙarasa ba saboda tasirin yadda idanunsa ke kallonta, kuma ganin ta dakatar da kanta da kanta yasa shi lumshe idanunsa a hankali sannan ya juya, har a lokacin hannayensa sanye cikin aljihunsa, ya juya ya fara tafiya.
Zainab ta kalli bayansa, yadda ƙaramar rigar ta fito da fadin kafaɗunsa, zuciyarta ta kara nauyi a ƙirjinta, sai kawai ta haɗiye wani abu a makogwaronta sannan ta bi bayan nasa itama.
Ta cikin mutanen nan suka wuce, tana tsayawa nesa dashi kadan duk sanda ya tsaya magana da wasu, kuma kusan sau biyar yana juyowa ya tabbatar idan tana bin nasa har suka ƙarasa ɓangarensa, ya buɗe kofar da mukullin da ya zaro a aljihunsa sannan ya shiga ciki yana barinta a buɗe.
Ta sake yin karfin halin danne zuciyarta kafin ta taka kafafunta ta karasa zuwa ciki, har yanzu tana riƙe da wannan kwandon, hannunta ya saki kofar bayan ta shiga cikiba tare da ta rufe ba, kuma har ta yi taku biyu a ciki taji muryarsa a cikin kanta.
“Koma ki rufe kofar.”
Ta juya gefen da taji muryar, wajen kujerun falon dake gefe, yana kwance akan guda ɗaya three-sitter dake fuskantar Tv ya mike kafafun sa.
Sai ta juya a hankali ta koma, ta tura kofar a hankali har ta rufe, amma kuma sai ta kasa juyowa, ƙafafunta suka tsaya a wajen, hancinta na shaƙar daddaɗan kamshin air freshener da ta fesa da kanta yayin da hannayenta ke rawa riƙe da wannan kwandon.
“Ki ajiye wannan abin ki shigo ki ci abinci “
Ya faɗa ba tare da ya bata damar shawara da zuciyarta ba, sai ta juyo ta sake kallonsa, shima ita yake kallo daga yadda yake kwancen.
“Wallahi akwai abinda zanyi da yawa, suna jirana kuma… kuma Hajiya zata min faɗa, alƙur’an…”
“Me?” Ya katse ta a lokaci guda yana kallonta.
“Me kika ce?”
Ba tare da ta fahimci abinda yake nufi ta sake cewa.
“Alqur’an faɗa zata yi min…” Rantsuwa ta sake fitowa daban da yanayin fuskarta, babubta yadda wani zai ce ma ita ta fada. Sai kawai ya girgiza kansa.
“Kar in sake ji kin fadi wannan rantsuwar. Bana so, kar ki sake faɗa.”
Ta hadiye yawu a makogwaronta sannnan ta gyada kanta a hankali alamun ta ji kuma ta fahimta, shima ya gyada nasa.
“Good, now enter.”
Bata ji me ya faɗa ba amma dai ta san yana nufin ta shigo ne, sai duk da haka ta kasa motsi daga wajen ta tsaya a tsorace kamar wani zaiyi motsi ta juya da gudu ta koma.
Kusan minti guda taba tsaye a haka kafin muryarsa ta sake ratsa kunnenta.
“Zaki yi dana sanin tsaiwa anan, idan na taso.”
Sautin muryar tasa ya fito iri ɗaya dana kwanakin baya, ranar da ya gaya mata cewar idan ta sake ta bayyana wannan sirrin nasa da taji, ba ita zai taɓa ba, mahaifiyarta da ta baro a ƙauye zai sa a lahanta.
Don haka abinda bata gane ba yanzu shine meye manufarsa kuma yanzu akanta?
Wani yawun da bata shirya masa ya wuce a bakinta sanda ta tuno maganar mahaifiyarsa, maganar da tayi sanadin kawo ta cikin wannan ƙullin.
_”Ki saka min ido akansa sosai, shi yasa nake aika ki kuma nake saka ki gyaran ɓangaren sa, duk wani abu da kika gani daban a dakinsa ki kawo min, ko waya yake yi ko kuma yana tare da abokansa ki tsaya ki saurara, dole yana ƙulla wani abu na sani Zainab, don haka idan banji komai daga gare ki ba, matakin da zan ɗauka zai shafi har iyayenki!”_
Allah ya sani a yanzu bata san meye mafitar ta ba, ta san dai kawai ko waye zai fassara halin da take ciki da Gaba kura, baya sayaki.
***
“Ina jinka…”
Tattausar Muryar Ma’aruf ta faɗa a cikin office ɗin, a cikin wayar da yake yi zaune akan teburinsa, hannunsa ɗaya na kan wata ƙatuwar jotter da yake rubutu akai. Daga cikin wayar muryar Yakubu ta cigaba da cewa.
“Na sami former address ɗin sa da komai ance anan gidan ya zauna directly da suka taho daga Kano, amma kuma satinsu uku a gidan suka tashi.
Kuma na fahimci kamar wani abun ne yasa suka tashi don ance min cikin dare suka bar unguwar babu wanda ya sani sai mutumin da suke hayar gidan a hannunsa, to shima jiya munyi kusan 3 hours tare ya rantse min da ubangijinsu cewa bai san inda suka tafi ba, sai dai ya san mai taxi ɗin da ya ɗauke su daga nan unguwar.
To da safen nan munje gidan mutumin amma kuma sai matarsa muka tarar ta, gaya mana cewa wai wasu mutane sun dauke shi haya zai kaisu wani ƙauye a can hanyar Uyo, kuma wai kwana uku zasu yi sannan ya dawo dasu,to da har naui niyyar daukar mai mota naje can sai kuma banga tunda ba dadewa zaiyi ba ai zamu iya jiransa don kwana uku kawai, amma what do you suggest?”
Ma’aruf yayi shiru yana kallon abinda ya rubuta, idanunsa ya haska da nazarin da kwakwalarsa ke yi, sai kawai ya ajiye biron hsnnun nasa sannan ya shafo saman kan hancinsa.
“Kar ka bi shi, ka barshi sai ya dawo din, and idan ya dawo din kayi duk yadda zaka yi ka samu wani bayani daga gare shi, Dan Allah Yakubu ko nawa yake bukata ka bashi kawai ko nawa yace.”
“Banda dai ko nawa Ma’aruf, don ina gaya maka mutanen nan idonsu a buɗe yake game da harkar kudi.”
Ma’aruf ya girgiza kansa.
“Mani da wani choice ne yanzu a harkar nan Yakubu, wani abu ya sake faruwa da idan banyi tackling ɗinsu gabadaya ba ban san ya zan sami kaina ba, saboda haka I’m willing to give everything, wallahi zan iya bada komai nawa idan har zan samu wani gamsashen bayani daga ko waye, so kar ka ja dashi dan Allah.”
“Baka da matsala, zanyi abinda ya dace… Ka tabbata dai kawai zaka biya ni a ƙarshen komai.”
“Ka san bani da matsala.”
“Na sani, shi yasa ma na yarda zanyi maka aikin.”
Da haka ya kashe wayar ba tare da ya sake cewa komai ba.
Ma’aruf ya ajiye wayar shima yana kallon rubutun da yayi a jikin jotter nan, bai san da yaya zai kira wannan bayanin na Yakubu ba, Nasara ko kuma akasin haka? Sai kawai ya koma da baya ya jingina da kujerar sannan ya rufe fuskarsa da duka tafukan hannayensa, fatansa guda ɗaya ne… Nan da kwana uku Yakubu ya iya samo wani kwakwkwaran bayani akan inda zasu sami Mr. Okafor.
“And guess what?!” (Ka canki wani abu!)
Faruq ya faɗa da ƙarfi yana banko ƙofar Office ɗin, sautin muryar tasa yasa shi ɗagowa yana kallonsa.
“License daga wajen ƴan sandan ya ƙaraso.”
“Ka bari dan Allah.” Ya fada yana kokarin tashi tsaye, ya ƙaraso ya miƙo masa takardar hannunsa da nasa murmushin shima.
Ya karɓa a lokaci guda da idonsa ya shiga karanta abinda ke jiki.
“Ishaq ya aiko da nasu license din yau da safe, ɗazu nayi printing dinsa, kaga mun hada komai kenan sai kawai mu fara aiki.”
“And details din mutumin are ready?”
Ya tambaya bayan idanunsa sun bi dukkan rubutun jikin takardar da kallo har karshe,ya kuma tabbatar da dukkan abinda yake nema. Sai dai maimakon Faruq ya bashi amsar abinda ya tambaya sai kawai ya ja kujerar gabansa ya zauna, sannan yace.
“Naga alama hannunka a sake yake game da harkar nan, na dade ina gaya maka cewa ina son motarka, so yaushe zaka bani muƙullinta?”
Ma’aruf ya girgiza kansa sannan ya koma ya zauna shima kafin yace.
“Zan iya bar maka gate ɗin gidana a buɗe da kuma mukullinta a jiki, sai kazo da daddare ka ɗauka.”
“Ɓarawo ka mayar dani kenan…?”
Maimakon ya bashi amsa sai yace.
“Dan Allah ka gaya min Faruq, bani da haƙuri akan wannan harkar ka sani.”
Kuma sanin hakan yasa kai tsaye Faruq din ya ajiye zancen komai a gefe yace.
“Nayi convincing wannan mutumin ba RTL, wanda yaga saurayin da ya karbi kudin,wanda dai yayi mana bayanin kamanninsa, na gaya masa mun sami license ɗin ƴansanda da kuma na kotu, na gaya masa akwai tsaro sosai don haka ya yarda cewa zai bi mu yawon zuwa Prisons din mu nemi mutumin. Kaga babu ruwanmu da ma wani bayanin takarda,ya tabbatar min cewa yana ganinsa zai gane shi.”
Murmushin da ya sauka a fuskar Ma’aruf a lokaci guda, irin murmushin da mutum baya shirya masa ne, irin murmushin dake fitowa tun daga ƙasan zuciya a lokacin da farad daya mutum ya tsinci labarin mai daɗin da bai taɓa lissafinsa ba.
A yanzu tabbas ya yarda cewa zai kirga wadannan bayanai guda biyun da ya samu ne a matsayin nasara, don Allah ya sani har a ƙasan zuciyarsa yake jin cewa watakila sun zo gaɓar da zasu taka matakin nasara a tsawon shekarun da suka ɗauka suna gwagwarmayar da bata da iyaka.
***
*Ƙarfe huɗu da rabi na yamma.*
A cikin ɗakin Munaya, Amina tana tsaye a gaban mudubin ɗakin kare da waya a kunnenta tace.
“Mun shiga cikin gida, ka taho ne?”
Muryarta ta fito a hankali, kuma duk da yaji ta Ma’aruf bai ce komai ba, yana kishingiɗe ne kawai ta baya akan arm chair dake cikin office ɗin Faruq inda suka gama wani aiki.
“Ka taho?”
Ta sake tambaya a hankali, duk da haka baice komai ba.
“Baka ji ba? Mun shiga cikin gida, na ƙulle gidan kuma.”
Ya sake lumshe idanunsa kawai yana jinta, sakan daya, biyu ta wuce sai kawai tace.
“Sugar…”
Ba shiri yayi murmushi a lokaci guda sannan yace.
“Yanzu kike magana Doll, da ban san sa wa kike ba ai.”
Ya jiyo ƙarar murmushin ta a hankali daga cikin wayar.
“Shi yasa ka min shiru?”
Sai ya girgiza kamar tana kallonsa.
“Ki sake fada dan Allah, just say it once.”
Tayi shiru kamar ba zata fada ba sai kuma tace.
“Sugar-Boofy…”
“Ya salam..”
Ya fada a lokaci guda yana dariya.
“Me gashina ya miki kuma?”
“Ba komai,yana maka kyau.”
“Yana min kyau ko yana miki kyau?”
“Duka biyun.” Muryarta ta sake fitowa a hankali tana jiyo hayaniyar dake tashi a can falon data baro.
Sai ya gyaɗa kansa kafin yace.
“So yanzu ki gaya min, kwana nawa kenan da aka saka sunan?”
“Wanne suna?”
“Wanda kike fada.”
Yana jiyo sautin wani murmushin nata kafin tace.
“Biyu, ko?”
Ya gyaɗa kansa.
“Yes, biyu… Kenan ranar Asabar zamu yi suna?”
“Suna kuma?” Tambayar ta fito da mamakin dake nunawa a muryarta.
“Yes, idan an saka suna ba ana yanka rago baysn 7 days ba? Nima zan siyo bawa ranar Asabar mu yanka tare, kinga sunan ya tabbata kenan.”
Sai kawai tayi dariyar dake fitowa mai dadi sannan tace.
“Baka gaya min ba, ka taho din?”
“You miss me that bad?”
Bata amsa ba yace.
“Shi yasa kika kira ni?”
Ta girgiza kanta.
“So nake in gaya maka muna cikin gida ne.”
“Wajen Mami?”
Kai tsaye yayi tambayar da tun ɗazu take dakon jiranta, sai ta girgiza kai tana cije lebbenta kafin tace.
“A’a muna wajen Hajiya.”
“Baku je wajen Mami ba?”
Ta sake wani murmushin jin daɗin nasarar da take fara samu ta wannan ɓangaren, ɗaya daga cikin manya-manyan takun da ta tsara a yanzu shine zata yi amfani da duk lokutan da Kilishi bata nan wajen kokarinta na haɗa kan al’ummar gidan.
Kamar yadda Amma tace ne, kar ta taba bawa Kilishi damar da zata zarge ta don haka ta sani idan har ta fara yawan zuwa wajen Hajiya Maimuna a gabanta, dole zata iya bata wata damar da zata zarge ta da wani abun, amma idan har bata nan, to wannan ce damarta da zata yi komai ba tare da ta bawa ita kanta Kilishin damar ganin laifinta ba, tunda bata da hujjar da zata kafa a gaban kowa game da hakan.
Shi yasa a yanzu ta taho bangaren Hajiyar kuma ta kira har su Samirah ta hanyar dabarar cewa su koya mata wani cin-cin da suka dade suna bata labarinsa… Sannan tayi iya kokarinta da har Hamida ta saki jikinta da Hajiya Maimuna, a yanzu ma ta baro su ne Hajiya Maimunan na kokarin koya mata su alifun ba’un ɗin da tace mata bata san su ba.
Shi yasa ta kira Ma’aruf shima da dabarar da zai sa ya taho nan ɗin, don ta tabbata da kyar ne idan yazo gaishe ta tun bayan warkewarsa. Saboda haka kai tsaye ta girgiza kanta sannnan tace.
“Mami bata nan, mun shiga aka ce bata nan, shi yasa muka zo gaishe da Hajiya.”
Ya gyaɗa kansa kai tsaye alamun gamsuwa da hakan sannan yace.
“Ban taho ba, akwai aikin da zamu karasa da Faruq, ina tunanin sai bayan magriba ma tukunna.”
Itama ta gyaɗa nata kan.
“Allah ya kaimu, Allah ya baku sa’a. Zamu jira ka anan ɗin Insha Allah.”
Ya san jam’in da ta saka yana nufin ita da Hamida ne, don haka ksi tsaye yace.
“Ni nace miki ku jira ni anan? I’m badly missing you Doll, ta yaya zaki hukunta ni da idanun Hajiya.”
Tayi murmushi mai faɗi tana kallon hannunta da yayi buɗu-buɗu da fulawa kafin tace.
“Ba hukunta ka zanyi ba ladan gaishe da ita zan sa ka samu.”
Yayi murmushi a hankali.
“Na sani Allah ya saka da alkhairi, amma da gaske ina missing ɗinki, ki tsara sunan waɗanda zaki kira tun yanzu, last time Amma kaɗai kika yi ta kira…”
“Inalillahi wainna ilaihir raji’un….”
Shine abinda ya fito daga bakin Amina babu shiri kuma ba tare da ta sani ba tana saka ɗaya hannunta ta rufe bakinta don bata san me zata ce ba bayan hakan, Ma’aruf yayi dariya sosai yana rufe idanunsa sannan ya sake cewa.
“Kar ki damu BabyDoll, da mun fara Printing kema zaki fara taya ni wannan hirar.”
A lokaci guda yaji ɗib, wayar ta katse.
***
*Ƙarfe shida da rabi na yamma.*
A cikin duhun magaribar, Hajiya Kilishi ta gyara zaman niƙabin fuskarta tana kallon mutumin dake tsaye a gabanta, ta jinjina kanta a hankali sannan tace.
“Recording muryata yake yi?”
Sadik dake tsaye ya gyaɗa kansa da murmushi yana kallonta.
“Tabbas, da bakinsa ya gaya min cewa yana da Cd’s sun fi guda ashirin da yake nafe muryarki sannan kuma yana dasu a kwamfutocinsa gaba ɗaya, sannan ma ya gaya min duk hanyoyin da zai bi yaci galaba akan ki.”
Murmushin da ya sauka a fuskar Kilishi a lokaci guda, irin murmushin da mutum baya shirya masa ne, irin murmushin dake fitowa tun daga ƙasan zuciya a lokacin da farad daya mutum ya tsinci labarin mai daɗin da bai taɓa lissafinsa ba. Sai kawai ta gyaɗa kanta a hankali tana cigaba da murmurshin sannan tace.
“Aikin ka yana kyau Sadik! Ka cigaba da bibiyarsa ka cigaba da kasancewa amininsa, ai bamu samu komai ba tukunna!”
MASU ƁUKATAR A TALLATA MUSU HAJOJINSU ZA SU IYA TUNTUƁARMU TA LAMBOBIN 07045308523 MUN GODE
