Farar Huta 2 – Chapter Ten
by NadminMASU ƁUKATAR A TALLATA MUSU HAJOJINSU ZA SU IYA TUNTUƁARMU TA LAMBOBIN 07045308523 MUN GODE
A jiya laraba ne mai girma shugaban ƙasa General Sani Abacha ya ƙaddamar da taron karɓar sababbin kayan ayyuka na aikin wutar lantarki a yunƙurinsa na samar da ɗorewar wutar lantarki a faɗin Nijeriya bakiɗaya….”
Rediyon dake yashe a tsakar gidan ke fitar da labaran yayin da mace ɗaya tal don dake tsajar gidan ke tsugunne daga can gefe tana wanke-wanke. Da misalin karfe goma sha boyu ne na rana, ranar kuwa ta hasja a sama kwal alamun lokacin na rani ne. Daga gefe guda na tsakar gidan akwai wutar itace daje ci bal- bal yayin da tukunya ke tafasa akanta.
“Assalamu alaikum.”
Muryar Amma ta wancan lokacin tayi sallama daga bakin kofar tana shigowa, hannunta daya dauke da wata ƴar karamar yarinya mai kama da ita sak! Kuma sautin muryarta da ya fito tare da sallamar, yasa wannan matar juyowa riƙe da kwanon silbar dake hannunta, fuskarta ta haska da tsananin murna da kuma farin cikin ganin nata.
“Maraba lale da Halima, marhaba bikum.”
Amon muryar tata ya fito da labarin kan fuskarta yayin da ta mike da sauri tana kara yi mata sannu da zuwa.
“Shigo, shigo Halima, jiyan nan ai muke zance da Sani nace mun kwana biyu bamu ga juna ba zan sami lokaci inje in gano halin da kuke ciki, ashe kya ce ma kuna tafe.”
“Wallahi Hajiya iya, muna hanya kam.”
Amman ta fada da nata murmushin itama bayan shigarsu dakin.
Hajiya iya ta karbi yarinuar dake hannunta kafin Amman ta zauna kan tabarmar da aka shimfida a saman ledar dakin.
“Anya kuwa ba zan dawo da kishin nan ba, da nace na haƙura muyi zaman salama amma wannan kyan da kike zubawa Aminatu zan yarda kuwa?”
Ta faɗa tana kallon yarinyar data kira Aminar, wadda ke shirin ɓangalewa da dariya kamar ta gane maganar da take mata, sai ta cigaba da cewa.
“Kodayake idanu ne kawai, wannan hancin ba tasowa zaiyi ba.”
Amma tana ta dariya har lokacin da itama Hajiya iyan ta nemi waje ta zauna kan wani kushin dake fuskantar tabarmar riƙe da yarinyar.
Hajiya iya ƙanwar mahaifinta ce, dattijuwa ce mai kirki da kuma sanin ya kamata, bata taɓa haihuwa ba, amma akwai wani ɗan mijinta guda ɗaya Sani da ita ta rike shi tun yana yaro, don haka kusan su ƴanuwanta duka sun san shi, tana yawan zuwa dashi wajensu idan har zata je.
Amma a Nigeria ta tashi tare da sauran ƴanuwanta, amma bayan rasuwar iyayenta ita ta koma Niger yayin da sauran ƴanuwanta biyu suka zauna a wajen yayarta Zahra’u (Tanti) wadda tayi aure a lokacin. Amma da Allah yayi dole bata da rabon zama a Niger ɗin dole aure ya sake dawo da ita Nigeria, kuma aka kawo ta unguwa guda da Hajiya iyan, don haka kusan kodayaushe suna cikin ziyarar juna tunda ita kadai ce ƴaruwar iyayenta mafi kusa.
“Kuna lafiya Halima?”
Amma ta gyaɗa kanta a hankali har yanzu da ragowar murmushin a fuskarta.
“Maigidan naki da nasa ƴan uwan suma duk kalau?”
Ta sake gyada kanta.
“Lafiya lau Hajiya Iya. Alhmdlilah.”
Sai ta gyada kai itama tana sake kallon Aminan dake hannunta.
“Wannan kuma ba sai na tambaye ta ba, daga wannan kumatun nata ma na san kalau take.”
Dukkaninsu suka yi wani murmushin yayin da Amina ta bangale da dariya alamun ta fahimci da ita ake. Kuma karar tafasar tukunyar nan daga waje ya katse Hajiya ita daga maganar da zata yi, ta mike da sauri tana fadin bari tazo, Amma ta karbi Amina yayin da ita kuma ta fita.
A wannan lokacin ne kuma tayi bakuwa, wata kawarta ce mai suna Inna Hajara tazo, a tsakar gidan suka gaisa kafin ta dauro alwalarta sannan ta shigo dakin, suka gaisa da Amman dake shayar da Amina dake kokarin bacci sannan ta tayar da sallarta a gefen tabarmar.
Ta shara-sharan labulen Amina na kallon yadda take kai kawo a tsakar gidan har ta kammala tuka tuwon masararta ta kwashe, tana yi tana kiran suyi mata hakuri.
“Yawwa, na san idan nazo na zauna ne, aikin tsayawa zai yi, amma kinga yanzu ai komai ya kammala sai ci kuma.”
Ta fada bayan ta dawo dakin rike da kwanukan data zubo musu abincin, ta ajiyewa Amina a gefenta tana zaunawa a inda ta tashi, Amina tayi bacci a jikin Amman lokacin, tayi lamo sai numfashi kawai take fitarwa a hankali yayin da bakuwar tata ta idar da sallarta.
Tana jin yadda hirarsu ta cigaba bsyan sun gyara suna cin abincin wanda tun ba’ayi nisa ba Amma ta gane tsaf akan abinda suke maganar don hira ce da ta riga ta zagaye fadin arewa a wannan lokacin kaf, kasancewar labarin wani abu ne da babu wanda ya taɓa jin makamancinsa, wata mata ce da aka kama da laifin hayar wasu mutane da sula je har gida suka kashe ywar mijinta saboda irin takurwar da matar tayi mata.
Ita kanta taji, kuma ko da ta tambayi mijinta ce mata kawai yayi su bar zancen don baya ko son ambatarsa.
“Ai sai jiya aka koma shari’ar, sai jiya suka sake zama.”
Cewar Inna Hajarar tana kai lomar tuwo bakinta kafin ta cigaba.
“Da yake ta kwana biyu a wajen hukumar tana jin matsa shi yasa ba’a je koina ba ta amsa laifinta kuma ta fadi inda ta samo mutanen da ta saka suka yi mata aikin.”
Hajiya iya ta dauko salati tun farko har ƙarshe ta dire sannan tace.
“Su kuwa wadannan mara sa imanin daga ina suke.”
“Wai a Prison tasa aka samo mata su…”
Amsar Inna Hajaran ta fito daidai lokacin da Amma ke shirin shimfide Amina don ta tashi tayi tata sallar itama.
“… Hajiya Ladi ta gaya min haksma suke yi dama, duk mai son ɓoye aikinsa gidan yari yake zuwa yayi cuku-cukun da za’a bashi wanda zasu yi masa, da sunyi sun koma shikenan babu mai sake ganinsu. A sallami iyayen gudansu suma a siyo musu ƴan kayan buƙata shikenan, aikin ka ya rufo kamar yadda na kwance a kabari yake rufe.”
Hajiya iya ta jinjina kanta.
“Ita da tayi rashin sa’a aka kama guda a cikinsu shi yasa komsi ya caɓe mata kenan…”
Maganganun Hajiya iyan, suka zama na ƙarshe da suka taho tun daga wancan lokacin zuwa a yanzu da take tsaye riƙe da wayarta a hannu.
Kwakwalarta ta sake tariyo wannan ranar a cikin kanta tana sake biya kowacce kalma daga bakin Inna Hajara cikin nutsuwar da take jeranta su da kalaman da Amina ta gaya mata a yanzu cewar abinda su Ma’atuf ke nema da sun daina wahalar da kansu abinda suke nema yana wajen da ba zai taba fitowa ba.
So take yi ta haɗa abubuwa guda biyun waje guda sai dai kuma kwakwalarta na ayyano mata tazarar shekarun dake tsakanin zamani biyun da cewar tabbas abubuwa na iya canjawa, amma kuma a lokaci guda sai tunaninta ya cilli kan watarana da yamma lokacin da ta hau adaidaita sahu don zuwa gidan ƴaruwarta Tanti, a cikin adaidaita sahun aka ɗauki wani mutumi da suka shiga hira shi smda ɗan adaidaita sahun kan halin da ƙasa ke ciki a yanzu, kuma ba zata manta ba ya rantse fiye da kirgen da zata iya tunawa cewa fiye da rabi na masifar da ake ciki da sa hannun shuwagabanni.
“… Wai kana ina za’a shiga gidan yari a debo masu laifi duk a basu bindiga ɗan kare, to rabin masu garkuwa da mutanen nan da kuma wadannan ƴan bindigar duk waye ya sansu, wani ya shekara homa a gidan yari za’a dauko shi ya fito yayi wani aikin, da sun ga al’umma sun natsa an fara gano su shikenan sai a maida du inda suka fito, wa ya isa ya gano su a inda ba zasu taba fitowa ba?…”
Kalaman suka kai ƙarshe tare da tabbatarwa da kuma yakinin kowanne abu dake cikin kanta, yaƙinin da take jin sa har ƙasan zuciyarta don haka ba bata sake bata wani lokaci ba hannunta ya sake lalubo nambar Amina a take.
“Idan ya dawo, ki san ta hanyar da zaki gaya masa cewa su nemi mutumin da suke nema har a cikin Prison!”
***
“Ban gane ba, kin ga yarinyar bayan tsawon kwanaki da ɓacewarta, har a gaban alkali an baki ita kuma kice min kin dauke ta kin sake mayar da ita hannunsa? To meye hikimar Rukayya?
Na zata shi kike so, shi kike so ya dawo rayuwarki, kuma Allah ya mallaka miki ƴar da ta dalilinta zaki hillace shi ya dawo gareki, amma sai ki ɗauke ta ki mika masa ita ke ki koma gefe?
Wane irin tunani ne wannan Rukyy? Wane jahilin ne yace miki…”
“Mahaifiyata ce.”
Ksi tsaye Rukayyan ta katse kawarta mai suna Hanan dake wannan zancen ta cikin wayar.
“Kin san ni ba shashasha bace Hanan, tunda kika ga nayi hakan,kin san da dalili,kuma shi ya kamata ki fara tambaya ba ki shiga ƙoƙarin aibata ni ba.”
Ba ganinta take yi ba, amma zata rantse Hanan ɗin ta taɓe baki wani abu da yake al’adarta kafin tace.
“Ni ba aibata ki nake yi ba,amma koma meye shirin naku ina tabbatar miki wannan shirme ne,da kin tambaye ni tun farko da ba haka…”
“Ke na tambaya ai tun farko Hanan…” Ta katse ta muryarta na dagawa.
“Ke na tambaya tun kafin in gama iddar auren Ma’aruf, zuciyata tayi nadama tun a sannan, amma ke kika ce kar in bashi hakuri don in koma Hanan, kuma ke na tambaya kika bani shawarar auren Alhaji Ahmad, kuma ke na tambya lokacin da su Maamah suka hada ni da Jawad, ke kika nuna min cewa in biye masa muyi wannan rayuwar zan manta komai, amma na manta din Hanan? Sannan ke na tambaya kika hada ni da Mary ƴar aikin Hamida… Hanan ki gaya min a cikin tarin wannan shawarwarin naki wanne ne ya juye zuwa alkhairi? Wanne ne ya juye zuwa alkhairin da har yanzu nake mora?”
“Ban gane ba Rukayya, me kike nufi? Me kike nufi dani?”
Muryarta ta fito ne da harzukin dake keto wayar yana dukan kunnen Rukayya.
“Ina nufin ke ba ƙawar arziki bace Hanan, na fahimci babu wani abu mai kyau da ya taba faruwa dani a tsawon zama na dake.”
Kuma daga haka, bata jira komai ba ta katse wayar, ta rike ta a hannunta tana kallon adadin mintinan da suka ɗauka a wayar.
Da dukkan maganganun da ta furta a wayar nan ta kwana a ƙirjinta, dasu ta kwana suna yawo a zuciyarta, don a cikin tarin tunanin dake yawo a cikin kanta ta iya nemo wannan kawai ta jera shi daya bayan daya ta fitar da karshensa, kuma abinda bata gama sani ba shine bayan Hanan, mutane nawa ne kuma bata yi sa’ar kasancewa dasu ba a cikin rayuwarta.
Hannunta ya fita daga bangaren kira na wayar tata, ta shiga wajen sakonni, bayan na banki, sunan Jawad ne a kasa, sakon sa na karshe daya tura mata kafin su yi wannan haduwar.
_I madly love you Barbie, me yasa kike hukunta ni? Pick my call please…_
Haka kurum taji a ranta cewa shirunsa a yanzu yana da nasaba da wani abu, Jawad mai naci ne, mai wani irin rufaffen nacin da baya ji kuma baya gani idan har ya dora ransa akan wani abu, ta san wannan ba tun akanta ba, tun akan aikinsa don hakan shine babban abun da yasa cikin ƴan shekaru kadan matsayinsa ya kere kowa a wajen, to ta yaya don kawai tayi masa wannan bayanin zai haƙura komai ya cigaba da tafiya daidai?
Wayarta tayi kara tun kafin tunaninta ya kai karshe, Mahaifiyarta ce Hajiya Nafisa, ta ɗauka daga haka tasa a speaker.
“Ki sauko kasa, muna magana ne akan wadda zata je gidan.”
Wadda zata je gidan, ba sai Maamahn ta fasa ba, wadda zata je gidan tana nufin gidan Ma’aruf, yarinyar da zata je ta kwance asirin nan, asirin da kamar yadda suka tsara komai a yau ba sai gobe ba aikinsa zai fara, Ma’aruf zai tsani koma wacece yarinyar dake cikin gidan nan a matsayin matarsa, tsanar da a cikin kankanin lokaci zai rabu da ita, don ta riga ta san ko waye Ma’aruf, idan baya son abu baya son sa har cikin ransa kuma babu wanda ya isa a duniyar nan ya canja ra’ayinsa game da hakan hatta Baffa kuwa, shi yasa shi kansa Baffan baya saka baki akan al’amarin wani hukunci da ya yanke.
Sai kawai tayi wani murmushi mai fadi tana hango yadda rayuwa zata maida ita bigiren da ta yarda babu kamarsa duk duniyarta.
Ta yi mu’amala da maza da yawa tun kafin aurenta, amma babu wanda ya kamo kafar Ma’aruf a cikinsu shi yasa ta dage har ta aure shi a sannan, kuma bayan zuciya ta ruɗe ta ta fito, har yanzu bata ga wanda ya kama kafarsa a komai ba… Jawad yana ji da kansa wajen iya kulawa da kuna tarairayar mace, amma ta tabbata zai zubar da dukkan makamansa idan da zata hasko masa kwana ɗaya kawai a rayuwar aurenta da Ma’aruf kafin abubuwa su canja a tsakaninsu.
Wayarta ta sake ƙara, Maamah ce, sai kawai ta sake wani murmushi mai fadi tasa hannunta duka biyu tana gyara dogon gashinta zuwa baya.
Bata san wane irin zama Ma’aruf ke yi da sabuwar matarsa ba, amma koma wane iri ne, yau zata zama rana ta ƙarshe da hakan zai zo ƙarshe.
***
“Meye wannan?”
Ma’aruf ya faɗa a hankali yana laluben gefen fuskar Amina dake tsaye a gabansa, a jikin wardrobe ɗin dakinta ya same ta, tana kokarin samowa Hamida kayan da zata saka sakamakon bata nan jikinta da tayi da hodar ta fasa gabadaya kuma ta zube a jikinta, duk yadda ta kai ga kwashe kayan kwalliyar nan bai hana ɓata kayan nata da take gudu ba.
Dawowarsa kensn daga cikin gida, don can ya fara shiga baysn ya dawo, bata ssn wajen wa yaje ba amma tana tunanin wajen Baffa ne don yau ma yans gida. Ɗazu bayan gama wayarta da Amma, Ssmirah tazo sun shiga sun gaishe shi, har da Hamida da taki zuwa wajensa ta makale a hannunta, wani sbu da ya taba zuciyarta a lokscin yayi mata dadin da kuma yabawa kanta na cewar yarinyar ta fara sabawa da ita.
Kuma sai da numfashinta ya katse a yanzu daya zura hannun nasa gefen fuskarta, tana jin yadda yatsun nasa suka ratsa kunnenta, sanyin jikinsu na bi ta kan fatar ta.
“Ɗan kunne ne, baka sanshi ba?”
Ta fada tana kallon cikin idanunsa hannunta rike da kayan da ta dauko, ya gyada kansa a hankali yana cije lebbensa kafin yace.
“Na sanshi, kawai bana son shi ne.”
“Saboda me?”
“Saboda damuna zai dinga yi.”
Sai da ta dan tsaya tana kallonsa kafin tace.
“Ta yaya zai dame ka?”
Bai ce komai ba ya fara kokrin zare shi a hankali, ya karkato da fuskarsa dab da tata yana kallon ta yadda zai cire kuma bata ce komai ba ta tsaya kawai jiran taga abinda zai yi, ya cire na bangaren dama, sannan ya karkato da kansa daya gefen ya cire na hagun shima, ya hada su a hannunsa sannan ya kamo nata daya a hankali, na hagun da bata rike kayan dasu ba, ya bude tafin hannun ya dora mata su a ciki.
“Please in dai saboda ni kike sawa ki daina, bana son su, takura min zasu yi ‘Cox bayan kafafunki, I like this curve of your body best.”
Numfashinta ya tsaya cak a ƙirjinta yaki fita yaki shigactsawon wasu daƙiƙai, dama kafafunta burge shi suke? Inalillahi! Ai bata taba tunani ba, ko lokacin da ta saka wannan yaluwar rigar sai da tayi ta ayyana yadda yake kallonsu a ranta amma bai ce komai ba, sai yau Allah ya budi bakinsa ya fada kenan.
Sai kawai ta rufe idanunta ta bude sannan tace.
“Insha Allah.”
“Insha Allah me? Baki karasa ba…”
A hankali tana kallonsa tace.
“Me zan karasa?”
“Sunana…”
“Ma’aruf?”
Ya girgiza kansa.
“Wannan na kowa ne, though I like the way kike fadan ‘R’ din sunan, amma na fi so ki samo min wani daban, da ke kadai zaki dinga fada.”
Ta danyi shiru tana cigaba da kallonsa, kwakwalarta na gaya mata cewa sun bar Hamida a can falo amma wani gefen na gaya mata cewa tunda kallo take yi vabu komai.
“Kamar me toh?”
Innocence din cikin muryarta ya fito tar, yayin da idanunta ke cigaba da kallon sa. Sai kawai yayi dariya yana zura hannunsa cikin gashinsa sannan ya girgiza kansa, kuma maimakon ya bata amsa sai kawai ya juyo da ita, tana fuskantar ɗakin, ya tsaya daga bayanta sannan ya sunkuyo da fuskarsa cikin wuyanta, bakinsa daidai kunnenta ya rada a hankali yace.
“Call me the first thing you see…”
(Ki kira ni abu na farko da kika gani.)
Ta cije lebbenta tana murmushi, kuma a hankali idonta ya sauka akan robar sukarin da ta ɗauko ɗazu tayi amfani dashi a wani kayan gyaran fuska da akace mata sai an hada da sukarin.
“Sugar…”
Muryarta ta fito a hankali, sai yayi wani irin murmushi mai sauti a cikin wuyan nata yace.
“Yes! I know I’m that sweet Sunshine.”
Sai kawai ta juya tana nata murmushin itama ta kalle shi, kuma a wannan lokacin ne kwakwalarta ta gaya mata cewa shine damarta na gaya masa sakon da take jin nauyinsa a cikin ƙirjinta.
“Ina so ne in gaya maka wani abu.”
Bakinta ya yanke shawarar fadar abinda ke zuciyarta kai tsaye tun kafin kwakwalarta ta canja tunani.
Sai ya gyada kansa yana kokarin rike ta a cikin hannunsa alamun yana saurarenta, ta haɗiye wani abu a maƙogwaronta a hankali tunaninta na ƙara gaya mata muhimmancin abinda zata fada.
“Ka yarda dani?”
A lokaci guda taga yanayin fuskar sa ya canja, ragowar murmushin na barin kan fuskar tasa, ya zama so serious ɗin da taji zata iya zagin kanta inda har da ba abu mai muhimmanci zata faɗa ba. Ya ƙara gyada kansa sau daya yana kallonta kafin yace.
“With every cell of my body Doll, na yarda dake.”
(Da kowanne kowanne abu dake jikina Doll, na yarda dake.)
Kalaman suka bata jwsrin gwiwar da a lokaci guda ta fara magana.
“Dazu da ka fita ina ta tunanin akan maganar da ka fada min, akan maganar wannan mutumin da kuke nema, nace me yasa baza ku duba har wajajen da ba’a tunani ba kamar irin su Prison, saboda wani lokacin mutane suna wasa da hankali ne kawai su yi abinda suka san ba za’a taba zato ba…”
Ta yi shiru, kamar ta kai ƙarshe kamar kuma akwai sauran abinda zata fada. Shima yayi shiru bai ce komai ba, tsawon wucewar wani lokaci yana kallonta kafin muryarsa ta fito.
“All this while ina ta underestimating dinki ne ashe Doll, naga alama abubuwan da kika sani sunfi karfin tunani na, amma insha Allahu lokaci zai bude min su daya bayan daya.
Abinda kika fada yanzu was amazing, kinyi tunanin da ba ni va har su Faruk wani a cikinmu bai taba yi ba. Tabbas ana amfani da prisoners a irin wannan harkar sosai,mun sani amma Allah bai taba sawa munyi tunanin hakan ba, thank you so much da kika tuna min, Allah ya saka miki da alkhairi Amina kuma Insha Allah a yau zan kira Faruk, kuma daga gobe zamu fara binciken nan, muna da details din yadda siffar mutumin take da komai, so in har a gidan yarin yake, ba zai yi mana wahalar kamawa ba insha Allah.”
Ta gyada kanta tana jin kamar wani abu zai fashe ne a cikin zuciyarta saboda jin dadin yadda ya fahimce ta a cikin kankanin lokaci yayin da shi kuma ya cigaba da kallonta, kuma kafin tayi wani tunani taji ya sunkuyo da fuskarsa dab da tata sannan a hankali yace.
“I want to borrow a kiss right now Doll, don in nuna miki godiyata, amma nayi alƙawarin zan dawo miki dashi Allah.”
Bata san lokacin da ta kyalkyale da dariya ba tana kokarin ture shi, amma sai ya kara rike ta yana fadin.
“Da gaske nake Allah, yanzun nan zan dawo miki dashi, kawai ki ara min.”
Da ƙyar ta samu ta fita daga hannunsa, ta koma falon ta barshi anan yana amsa wayar Ishaq, zuciyarta cike fal da daɗin yadda ta isar da saƙon Amma cikin ƙanƙanin lokaci kuma ta samu fahimtarsa, ta gama da wannan babin insha Allah.
Kilishi ta jirayi abinda zai biyo baya, zata sha mamakin yadda asirinta zai tonu alhali ta san bata budewa kowa sirrinta ba, tunda ko ita ta san bata gaya mata ba, kawai sunyi amfani da kalamanta ne akanta. A yanzu saura abu na gaba da take da yakinin zai fi wannan… Abinda Amma tace ce.
_’…babu abinda zai faru, babu abinda zai sami yarinyar nan, amma kuma a idanun Kilishi komai zai faru, zaki cika mata wannan aikin nata sannan kuma zata kaimu Makkan har da wannan canjin na gida ma!_
Allah ya sani zuciyarta a tsaye take wajen jiran faruwar hakan.
“Zoben Sofia za’a fauko a cikin wannan ramin.”
Hamida ta faɗa tana nuna mata cartoon din da take kallo a cikin Tvn, ta juya ta kalli ramin da take faɗa kafin tayi dariya tana gaya mata cewa rijiya ce ba rami ba.
A daidai wannan lokacin ne kuma taji karar buɗewar Gate alamun sunyi baƙi don ta san da daga cikin gida ne ta baya za’a shigo.
Ta gama canjawa Hamida rigar sanda aka kwankwasa kofar ɗakin alamun koma waye ya karaso.
Don haka tayi saurin ajiye rigar a saman kujera sannan ta nufi wajen ƙofar, hannunta ya buɗe a hankali daidai lokacin da fuskar matar ta shiga idanunta, tana tsaye da dogon hijabi tayin da fuskarta ke dauke da wani faffadan murmushi, kuma kafin kwakwalarta ta fara tunanin inda ta santa, taji muryar Hamida daga bayanta tace.
“Mariya???”
***
“Mun yi magana da mutanen, sunce hodar zata samu zuwa jibi, mutumin da zai kawo jirgi zai biyo don haka ka shirya gobe zaka tafi lagos, don bana son ta ko kwana a hannunsu, kudin dana kashe akanta da yawa, ba zamu yi sske na dage ba.”
Hajiya Kilishi ta faɗa a cikin wayar da take yi. Awwalu ya nisa alamun a kwance yake kafin muryarsa ta fito.
“Daga wace ƙasa ma kika ce za’a kawo?”
“Mexico.” Ta bashi amsa kai tsaye.
“To wai ta yaya ma za’ayi amfani da ita ne.?”
“Ba kai zaka yi ba, me yasa kake tambaya ta?”
“Saboda na lura tunda kika shigo da yarinyar nan cikin al’amarin nan na fara rage sanin wasu abubuwan. Kuma kina ganin kamar ban cancanci hakan ba.”
Sautin muryar tasa ya fito ne da wani irin kauri alamun akwai layin harzuka a ciki. Sai kawai tayi murmushi sannan tace.
“Kar mu fara wannan Awwalu. Ka soke wannan tunanin a cikin ranka, ka kori shaidan daga gefenka. In dai akan wannan hodar ne ka bude kunnenka ka ji.
A cikin kwallin yarinyar za’a saka, a hankali take aiki, ana saka mata yau da gobe zata fara da ciwon ido, ciwon idon ne zai ta ƙaruwa ana kuma cigaba da saka mata a haka har idon ya rufe gabaɗaya ba tare da ko likitoci sun gano dalilin hakan ba.”
Ta kai ƙarshe ba tare da yace komai ba, kuma jin shirun nasa yasa ta ƙara da cewar.
“Idan mun gama da wannan sai kuma mu koma kan ƙafarta, na tabbata lokaci zaiyi mana daidai da sanda zan gama da abinda ke gabana, kaga kenan zan tafi ba tare da na bar kowanne dutse a kife ba.”
“Haka ne, Allah ya bamu sa’a, zan siya ticket ɗin jirgi anjima insha Allah.”
Yadda ya fadi hakan a lokaci guda, kai tsaye, kuma yadda kalmar Allah har sau biyu ta fito a bakin Awwalun yasa ta tsayawa da nata shirun kafin a hankali a furta kalmar ‘Ameen.’ din da bata jin ta kai ƙarshe sanda ya katse wayar.
Wayar ta katse tare da katsewar numfashinta da kuma tsayawar idanunta akan mudubin da taje kallo a gaban ta.
Me Awwalu yake nufi?
Me ke shirin faruwa ne?
Wake shirin girgiza mata tebur ne?
MASU ƁUKATAR A TALLATA MUSU HAJOJINSU ZA SU IYA TUNTUƁARMU TA LAMBOBIN 07045308523 MUN GODE
