Search
You have no alerts.

    MASU ƁUKATAR A TALLATA MUSU HAJOJINSU ZA SU IYA TUNTUƁARMU TA LAMBOBIN 07045308523 MUN GODE

    “Na fahimci har yanzu da saura a harkar nan Kilishi, shi yasa kika ce zuciyarki ta kasa kwanciya… Amma kar ki damu, tunda kin iya da tarin abubuwan da kika shallake a baya waɗannan ma ba zasu yi miki wahala ba, ki cigaba da tsarinki kawai, ina garin nan har sai kaya na sun ƙare, don haka kar kiji komai.”
    Da haka wayar tasu ta ƙare. Hajiya kilishi ta mikie ba tare da ta kula da cewar bata kashe kiran ba ta fita daga dakin, kai tsaye falon ta nufa inda anan take jiyo hayaniyar da bata san dalilinta ba, ilai kuwa isarta ke da wuya ta tarad da su Zahra da Sahla tare da wasu kawayensu da suke makota su biyu suna faman bare kayan decorations daga cikin ledodinsu, kaya ne gasu nan fal-kala, sai faman ɗaga su suke yi suna kokarin ganin ta yadda za’ayi amfani dasu.
    “Duk wadannan abubuwan na meye?”
    Kai tsaye muryarta ta katse su ganin har ta tsaya a falon basu kula da ita ba. Dukkaninsu suka juyo a lokaci guda, ƙawayen nasu suka shiga gaishe ta yayin da Sahla tace.
    “Mami, Ya Samirah ce tace mu fito mata dasu, za’ayi decoration din tarar Ya Abdurrahim ne gobe….”
    “Abdurrahim!
    Sunan yayi amsa kuwwa a cikin kan kilishi a take, kwata-kwata ta manta da lissafin zuwan nasa, tinda suka ui maganar da Baffa bata kara tunawa ba sai yanzu, abubuwan dake saman kanta dama cikinsa suna da yawa, kuma ta riga ta sani cewa yaron ba matsalarta bane a yanzu, ko zai dawo ne da irinsa guda dari ta sani bai isa ya tsaya mata ko a gefen hanya ba balle ya tare mata wani abun.
    Don ma an samu akasi ne, kwakwalarsa taso ta taɓa tun a wancan lokacin, wannan kwakwalar tasa da tun yana karaminsa babu abinda take kange shi daga ganewa.
    Tana tuna wannan ranar, tana tuna ta kamar jiya, lokacin da taje har makarantarsu ta islamiyya a lokacin, ta haɗa baki da maigadin makarantar, idanunta na hango mata yadda hannyensa ke cusa damin kuɗin da ta bashi cikin aljihunsa, da yadda bakinsa ke washewa yana faɗin bata da matsala ya gane yaron da take biɗa, yana bayanin yana kallon idanunta dake boye a bayan niqabin fuskarta, bai ko damu da sanin kamanni ko wani abu nata ba.
    Har ya kawo mata yaron ta ɗauke shi kamar yadda tace a motar da tazo tare da wasu ƴan daba guda biyu da Awwalu ya haɗa ta dasu, don ko Awwalun a wannan lokacin bata yarda ya san abinda take shirin yi ba.
    _”Kar ku kashe shi, so nake kawai ayi min abinda ƙwaƙwalarsa zata taɓu…”_
    Haka ta gayawa mutanen a wancan lokacin, don bata yi niyyar kashe shin ba, kuma haka suka yi mata, don bayan ansha nema hankalin jama’ar gidan dama na malaman sa gabaɗaya ya tashi, an tsince shi ne yashe a cikin wani kango a sume jini na fita ta hancinsa da kuma kunnensa.
    Aphasia.
    Haka likitoci suka kira cutar da ta same shi, sunce gefen kwakwalar sa dake aiki da bangaren magana ne ya sami matsala sakamakon toshewar jini zuwa wajen, farkon rashin lafiyar tasa yana iya magana amma a gutsirtsire, cikin sautin da ba’a ma fahimtar abinda yake cewa duk da cewar da kankantarsa a lokacin.
    Likitoci sun bada shawarar yadda za’a dinga taimaka masa maganar da yadda harshensa zai koma daidai don sun tabbatar da cewar babu wani magani kwakwara game da cutar amma da yake shi yaro ne mai zuciya, tun a lokacin yaƙi bada haɗin kan hakan, ya daina maganar ma gabaɗaya babu yadda ba’ayi ba amma haka ya taso kowa yana kiransa Kurma, don ko makarantar da yake yi a can ƙasar ma ta kurame ce irinsa.
    “Mami fulawa ta kare, kuɗin drawer kuma sun kare su ma…”
    Muryar Samirah da ta fito daga kitchen ta fada a gabanta tana dawo da ita daga tunaninta. Ta juyo ta kalle ta.
    “Sati ɗaya kenan fa dana ajiye kudin nan Samirah,yanzu har kin karar dasu?”
    Da murmushi a fuskarta tace.
    “Wallahi Mami, abubuwan ne wannan week din da yawa, kinga munyi abincin sadakar uku na jikar Mama Rabin nan data rasu, sannan ga wannan shirye-shiryen dawowar Ya Abdurrahim ɗin kuma, surprise party muke haɗa masa tunda ya hana kowa zuwa can..”
    “Amma ni duk ban san da wannan ba.”
    “Mami kwana biyu fa ba kya ko zama a gidan nan, kamar wani abu yana damunki shi yasa kawai muka ƙyale ki…”
    Da murmushi a fuskarta sanda ta faɗi hakan, amma da ta san tasirin da kuma yadda suka shiga cikin kan Hajiya Kilishi da watakila bata yi wannan murmushin ba.
    _…. Kamar wani abu yana damunki shi yasa muka kyale ki…_
    Wannan wajen ya maimaita a cikin kan Hajiya Kilishi fiye da yadda zata iya ƙirgawa a cikin sakannni kawai, ƴarta ce wannan, ƴar da ta haifa a cikinta… Itace take gaya mata cewa sun ƙyale ta saboda tana cikin damuwa, sun ƙyale ta ba tare da sun damu su ji abinda ke damun nata ba a matsayinta na mahaifiyarsu.
    ƙwakwalarta ta tariyo mata wani abu a lokacin, tabbas ba zata iya tuna rana guda da wani a cikin ƴaƴan nata ya taɓa damuwa da damuwarta ba, Ma’aruf ne kawai… Ma’ruf ne kawai ke taɓa nuna damuwarsa akanta idan har wani abu ya same ta, ko a yau ma s gajiye ya dawo yadsa ta fahimta daga muryarsa, smma ssi da ya kira ya gaishe ta ya gsya mata ya gaji ba zsi iya shigowa ba kafin ya shiga gidansa, amma a vikin yan shekarun nan ba zata iya tuna rana guda da ta taɓa ganin wata damuwa mai zurfi daga wajen ƴaƴan nata ba har kuwa waɗanda ta yiwa aure yanzu, su kan dauki lokaci basu kira ta ba sau da yawa sai dai taji su suna waya dasu Samira.
    Wani abu ya wuce daga makogwaronta yana son dasa mata wani abu da ba zsta taba yarda ba, don haka sai kawai ta gyada kanta sannan tace da Samiran dake tsaye tans kallonta.
    “Bari na kawo miki, har da na cefanen wannan watan ma jiya Baffa ya aiko dashi kun fita.”
    “Yawwa Mami, Madallah.”
    Abinda tace kenan kawai sannan ta juya tana gayawa su Zahra abinda zasu yi. Sai itama ta juya tana jin kamar zuciyarta tayi nauyi da abinda ya faru, amma kuma
    kwakwalarta ta cigaba da gaya mata cewa hakan ba komai bane, da zarar lokacin da zata kammala komai yazo, su da kansu zasu gane gatan da ta daɗe tana yi musu, yaushe aka taɓa halittar ƴaƴan da suka juyawa uwarsu baya a duniyar nan? Shaidan ne kawai ke kokarin cin galaba akanta.
    Ta isa cikin dakinta lokacin da idonta ya kai kan wayar da ta bari akan gado, mitunan kiran na da suka yi da Hajiya Salamatu na nunawa akan fuskar wayar har yanzu, mamakin yadda akayi bata kashe ba kuma itama Salamatun bata lura ba ya kamata, sai kawai ta ƙarasa ta ɗauke ta, har zata kashe sai kuma taji wani abu kamar murya na magana don haka ta kara ta a kunnenta kuwa daidai lokacin da ta jiyo muryar Hajiya Salamatun daga can ciki tace.
    _…a idon duniyar nan…!”_
    Mamaki ya gifta a ranta na ma’anar hakan, amma sai wani gefen tunaninta ya bata cewar watakila hirarta ce kawai da wasu mutanen tunda gidan nata baya rabo da jama’a, don haka sai kawai ta kashe kiran ta ajiye wayar akan gadon sannan ta tafi daukowa Samirah kuɗin.
    Da ace dan adam yana da ikon dawo da lokaci baya zuwa sanda yake so, da tabbas Kilishi zata so dawo da wannan ranar kuma wannan lokacin fiye da sau dubu a rayuwarta.
    ***
    *Ƙarfe tara na safiya.*
    Amina ta kunna gas ɗin da ta ɗaura frying pan da mai a cikinsa, idanunta suka tsaya akan man har lokacin da ya fara zafi, yayi zafin yama fara shirin ƙonewa kafin ta farga ta zuba haɗin ƙwan da ta haɗa akai.
    Minti talatin kenan, minti talatin tun bayan dawowarsu daga asibiti, don a ɗazu da asuban nan bayan ta gaya masa abinda take tunani yace ta shirya su fita, ya kira Munaya yace tazo ta dauki Hamida zasu fita.
    Tun gari bai gama haske ba ta shigo ta dauke ta zuwa cikin gidan tana bacci ma bata san me ake yi ba, kuma tana ta tambayar inda zasu je amma bai ce mata komai ba sai da suka tsaya a gaban wani ɗan karamin Private asibiti da a samansa aka rubuta 24hours, (awa ashirin da hudu.).
    A asibitin aka haɗa ta da wata Nurse bayan ya yi musu bayani, kuma minti takatin bayan hakan aka tabbatar musu da abinda suka zo nema cewar da gaske tana da cikin.
    Ta sani, tunda Amma ta gaya mata ta yarda kuma tana ji a jikinta ma, amma a wannan lokacin sai take ji kamar wani sabon labari ne, kamar an tabbatar mata da wani abu ne da a baya yake yawo a iska, kuma tun a cikin asibitin nan ta sani kwatanta irin murnar da ta gani a idanun Ma’aruf, wani abu ne da bata tunanin yana da geji, sai kuma tazo ta tankwaɓe komai a lokaci guda da ta gaya masa cewa bata so zancen ya fita ko’ina tafi son ya barshi a tsakaninsu.
    Bata so ayi wani na ukunsu da zai sani, ta gaya masa tana da dalilinta kuma zai san hakan a gaba, amma bai fahimce ta ba, tayi kokarin ƙara yi masa bayanin amma sai kawai yace ta kyale shi kuma a wannan lokacin da ta kalli idanun nasa ta san babu abinda ya fi dacewa illa ta kyale shin, don ta kasa tantance tsakanin farin ciki da kuma rashin fahimtar tata wanne yafi yawa a cikinsu.
    Ta ƙarasa soya ƙwan gabaɗaya, ta fito da dankalin da ta soya a deep fryer, ta hada komai waje guda tare da kayan shan tea, sannan ta koma ta kwaba fulawa da kwai da butter tayi wani pancake da yayi taushi sosai guda uku.
    A hannunta ta ɗauko woven tray ɗin da ta jera komai akai tana barin flask ɗin ruwan zafin a kitchen din, kafafunta suka fita daga kitche ɗin har zuwa hanyar koridon ɗakunansu, wata doguwar riga ce a jikinta ta atamfa, dinkin jikinta mysi kyau ne don ko ranar da ta fsra saka ts su Samirah sun yaba dinkin sosai, ta daura dankwalin kawai a gaban goshinta, bayan ɗaurin ya tokare da tudun gashinta mai laushi da yake a tsefe ya fito ko tawanne gefe ana ganin sa.
    Fuskarta fayau take, don duk da halin da take ji suna ciki akwai murna kuma a ƙasan ranta fal, godiya ga mahallicinta kawai take mikawa a cikin ranta, tana jin cewa kamar babu wani abu a duniyar nan da zai iya daukar irin farin cikin dake cikin zuciyarta.
    “Assalamu alaikum…”
    Muryarta ta faɗa bayan ta murda kofar dakin nasa, labulayen da iska ke motsawa ta fara gani a idanunta kafin shi, yana zaune daga ƙarshen gadon ɗakin kusa da bedside drawer dake kunne da fitila akanta, hasken fitilar da shi kaɗai ne a cikin ɗakin, kasancewar labulayen windunan sun hana hasken ranar da ya fara fitowa a waje shigowa ciki kuma sauran fitulun dakin duka a kashe suke.
    Faffadar kafadarsa da kuma bayansa su ke kallo ta yayin da kamar kodayaushe hannunsa daya na riƙe da wayar dake kare a kunnensa.
    Taji kamar ya amsa amma bata tabbatar ba don maganar da yake yi ma bata jin ta sosai, kafafunta suka taka a hankali zuwa ciki kuma maimakon ta samu waje ta ajiye tray din hannun nata sai kawai ta tafi gabansa ta tsugunna gabaɗaya da kayan a hannunta, idanunsa suka kalle ta kuma kafin ta gama tantance idan fushi yake yi ko akasin haka, sai kawai ya kamo hannunta guda daya ya riƙe shi a cikin nasa.
    “Zuwa 11 na fito Insha Allah, ina ga muna da two hours kafin lokacin da zanje ɗauko Abdurrahim…”
    Ya fada a cikin wayar da ta san ba da kowa yake yi ba Faruq ne. Idanunta suk cigaba da kallonsa yana sauraren bayanin Faruq ɗin, ba ma sai yace mata ba, tana iya karantar cewa ransa a ɓace yake a cikin idanun nasa da kuma yadda jijiyoyin gefen wuyansa ke fitowa suna motsi su kaɗai, gashin kansa ma wani bayanin ne ƙarara, gabadayansu a hargitse wasu sun durƙusa kamar zasu yi sujjada.
    Sai kawai ta zame farantin daga hannunta ta ajiye shi a ƙasa sannan ta miƙe zuwa gabansa ta zauna akan cinyarsa a hankali, da yatsan hannunta da bai riƙe ba tta shiga shafa gefen wuyansa a hankali kuma tana jin yadda makowagronsa ke tamkewa da taɓawar da take yi, sai kawai ta karya wuyanta ta cusa fuskarsa ta gabaɗaya a cikin nasa wuyan, tana jiyo muryar Faruq ɗin dake bayani tar daga cikin wayar.
    “… Yaron bashi da hankali B, yana gaya min wai baya tunanin nambar ma wani ya taɓa yi mata rijista? Akwai layin da yake amfani babu rijista ne?…”
    Hannunta ya tafi daga wuyan nasa zuwa bayansa kuma a hankalin ta shiga zana masa harafan da ba lallai ta san ya fahimta a lokaci guda ba, don haka ta shiga yi tana ƙara sakewa… SORRY.
    Har a lokacin kanta yana cikin wuyansa, tana jin yadda ko’ina a jikinsa ke amsawa da abinda take yi amna kuma bai ce komai ba, baiyi wani motsi ba ko kuma ya kalle ta tun bayan riƙe hannunta da yayi.
    “Zan kira ka Faruk ina zuwa.”
    Taji ya faɗa a cikin wayar muryarsa na fitowa wani iri, kuma tana jin wayar ta tsinke sai ta ƙarasa da fuskarta daidai kunnensa tace.
    “I’m sorry Sugar, dan Allah kayi hakuri.”
    Muryarta ta fito da sautin da taji da ace dare ne zata iya tayar da hasken taurari su haska masa fuskarta sosai don ya fahimce ta, ta fadi hakan sannan ta janye kanta a hankali zuwa baya tana kallon fuskar tasa, kallonta yake yi kawai babu alamun zai ce wani abun amma duk da haka tana iya jin yadda zuciyarsa ke bugawa kamar tata.
    Komai fushin da zaiyi da ita, bata jin zai karasa har cikin zuciyarsa, ita mai rangwame ce akanta ta sani, sai kawai tasa tafin hannunta duka biyu ta rike kowanne gefen fuskar tasa.
    “Ba fushi nake yi ba, me yasa kike bani hakuri?”
    Ya yanke shawarar fada muryarsa na fitowa da wani irin amo da bai yi nata dadi ba, amon da yasa babu dalili a lokaci guda taji hawaye ya cika idanunta, bai fahimce ta ba har yanzu, bai fahimci dukkan bayanin da tayi masa ba, bata taɓa tunanin kuma zai kasa fahimtar tata irin haka ba.
    Zuciyarta ta matse da tunanin irin fassarar da yayi mata tun kafin ma ta sani, tana jin wani abu na narkewa a cikin jikinta kamar ƙarfen da ake ƙonawa a cikin wuta, wannan yaƙinta ne ta daɗe da gayawa kanta hakan, babu wanda ya san wannan manufar tata a duniya bayan shi, ko Amma bata furtawa ba, shi kaɗai ɗin ne ta san ya zama dole ya sani kuma shi kaɗai take tunanin zai fahimce ta su rufawa junansu wannan asirin duk da bai san komai ba, amma idan har yana yi mata wani tunani na daban nasarar me taci kenan?
    Sai kawai ta girgiza kanta tana cigaba da kallonsa.
    “Da zan iya zan tattaro komai a duniyar nan Sugar, zan tattaro du gabaɗaya in jera a gabanka don su zama shaida cewar ba zan taɓa yin wani abu da na san zai bata ranka ba, so nake kawai ka fahimce ni, ba zaka gane yanzu ba na sani, kuma lokacin da zaka gane ɗin ma na tabata ba sai na sake yi maka bayani ba.
    Roƙon ka kawai nake yanzu ka bani haɗin kanka, bayan shi bana son komai Ma’aruf, kaine inuwata kuma kaine tallafi na, bani da wani mai kare ni a duniyar nan da ya wuce kai, bani da wani da zan dogara dashi a duniyar nan bayan ubangiji da ya wuce kai, kuma ba zan taɓa daina godewa Allah ba da ya kawo min kai cikin rayuwata a lokacin da ban tsara ba kuma ban taba tunani ba, I will always love you in a way that I will never hurt you…”
    A yanzu bata jin wannan kwallar data taru a cikin idonta, wani abu take gani a idanunsa take kuma ji a jikinta kamar kwarin gwiwar da ya sata ƙarasa maganarta.
    “Zamu haifi babyn nan cikin kwanciyar hankali insha Allah Sugar, babu abinda zai faru, ka cire tunanin komai a ranka dan Allah ka yarda dani, kamar yadda kake yarda da Faruq ɗin nan.”
    Sai kawai ya girgiza mata kansa a lokaci guda sannan yace.
    “Kar ki taɓa haɗa kanki dashi Babydoll, matsayinki da nasa daban ne a cikin zuciyata, there’s no way ma da kuka zo kusa.”
    Ya fadi hakan yana matso da ita jikinsa, kusa dashi sosai ta yadda take jin ƙarar bugun zuciyarsu ya haɗe waje guda akan zare guda, sanyi da zafi, mai nauyi da mara shi da kuma siririn da ya yake haɗewa cikin dan’uwansa.
    “Na yarda dake Noor, na yarda I’m just curious ne, abubuwa be suke neman haɗe min haɗe min waje ɗaya matsalar office da kuma…”
    Ya faɗa hannunsa na kokarin lalubo zip din rigarta a hankali, wani abu da yake son wasa dashi a kodayaushe. Sai kawai ta girgiza mata kanta a hankali.
    “Babu ruwan gidan nan da office my Ranger Handsome, ka bani damar da zan sa idan ka dawo wajenmu kaji kamar wata duniya daban ka shigo, kamar mun koma Mars ne mun bar musu duniyarsu da hayaniyarsu.”
    A lokaci guda murmushi ya suɓuce a fuskarsa yana kallonta.
    “Really BabyDoll? Kamar me kenan?”
    Ya tambaya yana ɗaga mata gira ɗaya, sai ta cije lebbenta na ƙasa alamun tunani kafin tace.
    “Zamu zama iyaye nan da watanni masu zuwa…”
    “Alhmdulilah.” Ya katse ta yana gyaɗa kansa.
    Bata tsaya ba ta cigaba.
    “… Kuma yau muka sani, yau aka gaya mana… So let’s celebrate!”
    Ya ƙara gyaɗa kansa murmushinsa na ƙara yawa, yayin da a cikin kanta take godewa Allah ganin yana dawowa yanayinsa na Ma’aruf ɗin ta.
    “We should BabyDoll, me kike so muyi yanzu? I think ina da two hours kafin in fita.”
    Ya fada yana ɗora goshinsa akan nata, hancinsa na taɓa saman nata.
    Ta sake cije leɓɓenta tana kallonsa sannan ta girgiza kai, duka fuskarsu ta girgiza a tare.
    “Yanzu lokaci yayi kaɗan, kayi breakfast ka fita, celebration ɗin zai fi daɗi da daddare.”
    A lokaci guda hannunsa ya tsaya da taɓa zip din rigarta da yake yi, ya janye fuskarsa daga tata yana kallonta sosai, da idanunsa da take jin kamar yana sace ruhinta daga jikinta, har a lokacin da murmurshi a fuskarsa yace.
    “Tabbas zai fi daɗi sosai Babydoll…”
    Ta gyada kanta itama.
    “Zan nemo restaurant hadadde wanda suke da fitulu sosai ‘cox we are going to take pictures na tarihi wanda zasu zauna har tsawon shekar….”
    Bata ƙarasa ba lokacin da Ma’aruf ya kyalkyale da dariya yana ɗora kansa a gefen kafadarta ta dama.
    “Menene? Me ya faru?”
    Ta tambaya tana murmushin da bata san na meye ba yayin da hannunta ke kokarin ɗago da fuskarsa. Tana jin yadda jikinta ke girgizawa da dariyar da yake yi.
    “Na kasa ganewa, wai menene?”
    Ta ƙara faɗa sanda tayi nasarar dago da kan nasa, ya kalle ta sosai yana girgiza kansa kafin yace.
    “Babydoll da kika ce celebration kuma kika ce da daddare, abinda nake hangowa daban…”
    Bata san lokacin da ta ture shi ba tana kiran sunan sa, sunansa gabaɗaya.
    “Ma’aruf Mansour Bakori….. ka dinga tunani irin na mutane a cikin kanka dan Allah.”
    Ta fada tana ƙoƙarin miƙewa, bata je koina ba kuwa ya jawo ta suka koma kan gadon gabaɗaya.
    “Zo ki koya min irin yadda ake yi tunanin mutanen…”
    Abinda ya faɗa bayan hakan ya saka ta kyalkyala dariya tana cusa kanta a cikin wuyansa, abinda ya cigaba da faɗa kuma ya sata faɗin.
    “Inalillahi wainna ilaihir raji’un… Ma’aruf!”
    Dukkaninsu suka kyalkyale da dariya, kuma abinda dukkaninsu basu sani ba shine, za’a ɗauki wata tazara mai tsawo kafin sake faruwar irin wannan ranar a rayuwarsu!
    ****
    *Abuja.*
    *No. 1146 C west, Maitama.*
    Ta san dakin, amma idanunta suna kallonsa ne kamar bata taɓa ganin sa ba, idan ma akace ta ƙirga bata san sau nawa zata kirga adadin data share kuma ta gyara shi ba, shi kaɗai ne a ƙasa bayan falon, kuma tasha tambayar kanta dalilin da yasa aka hada shi har da komai da komai alhali mai wajen baya amfani dashi ko kaɗan.
    Bayan haka kuma zuciyarta tasha hasko mata yadda zata ji daɗin kwanciya akan gadon da yake dakin, don kalar labulayen cikinsa da kuma zanin gadon ɗakin da suke suke dukka kalar yalo, suna faranta zuciyarta haka kawai, tana jin kalar na shiga idanunta da tasirin da take jin kamar tana samun ƴancinta ne a ciki, kamar zata samu wani fiffike da zai miƙar da ita sama ta tsaya da kafafunta irin yadda take fata a kullum.
    Amma yau da take tsaye a cikin dakin rike da ledar kayan dake hannunta bata jin dukkan waɗannan abubuwan, bata jin komai, zuciyarta fayau take kamar fuskarta.
    _”Zainab zaki aure ni?”_
    Sune kalaman dake maimaitawa kawai a cikin kanta, amonsu take ji yana ratsa ko’ina na tunaninta, tana ji kamar shaƙuwar data kwace mata a lokacin zata sake dawowa, don shaƙuwa kawai ta dinga yi yayin da idanunta ke ƙara zarewa akansa, kuma bai sake cewa komai ba sai kawai ya kai hannunsa ya shafa kansa sannan ya juya ya bar wajen.
    Bai sake cewa da ita komai ba har suka gama dukkan abinda za’ayi a asibitin ya karɓo mata magani, binsa kawai take yi tana so ta tsayar da shaƙuwar da ta kasa tafiya, ya barta a mota ya shiga wani waje da ta kula cewa magunguna ake sayarwa, kuma bayan ya dawo ne ya shigo motar ya miko mata robar ruwa har a lokacin bai sake cewa da ita komai ba.
    Tana tuna yadda ta shanye ruwan gabadaya kasancewar ba wani girma ne dashi ba amma har a lokacin shakuwar bata tafi ba, sai kawai taga ya sake miko mata wata robar daga cikin ledar maganin, a lokacin har sun fita daga cikin asibitin sun hau titi. Kuma ga wani mamakinta ba gida suka taho a lokacin kamar yadda ta zata ba, idan zata tuna ma taga sanda suka wuce hanyar gidan suka tafi kai tsaye har wajen aikin sa.
    Wajen da ya ƙara rikita ta, ya kara sawa ta raina kanta ta san cewa ita ba komai bace a duniyar nan, tun daga waje ginin wajen ya daki zuciyarta har suka shiga ciki, don bai bata wani zabi ba yace ta biyo shi, suka tafi har office din wata mata da taji yana kira da Aunty Mary, dattijuwa ce amma kuma arniya, ta saka kayan da basu matse kayion jikinta ba sannan tayi kitson ƙarin gashi.
    Tana da tsananin fara’a da kuma kirki, anan yace ta zauna zai je ya dawo, kuma bayan ya tafi haka tayi ta mata magana duk da ta fahimci ba ganewa take sosai ba, don idan ma zata gane ɗin, taraddadin dake cikin zuciyarta na tunanin Hajiya Mardiyya da nemanta da za’ayi ba zai barta ba, a haka ta zauna cikin tunani da tsoro har sanda wani ma’aikacin wajen ya shigo rike da leda mai dauke da abinci da kuma magungunan da aka siyo.
    _”Hajiya ga shi yace ki ci abincin kuma ki sha magungunan.”_
    Tana tuna fuskar mutumin da ya kira ta da Hajiyar, zata iya rantsewa zai kai sa’an mijin mahaifiyarta da ta baro a gida, amma kamar bai ga kankantar ta ba ko kuma dogon hijabin data zura wanɗanda basa shaida wani abu na Hajiyar da ya kira ta.
    Matar nan da kanta ta gaya mata cewa lokacin sallah yayi, ta buɗe mata banɗakin cikin office ɗin ta shiga tayi alwala sannan bayan ta fito ta shimfida ɗankwalinta akan carpet din wajen tayi sallah, haka ta zauna idanunta na cigaba da zarewa har sanda ya dawo, kuma a lokacin kallonsa kawai tayi taji shakuwar ɗazu ta dawo, haka ta dinga yinta tana kokarin boyewa har suka koma motar kuma ya sake miko mata wani robar ruwan ba tare da yace komai ba, wani abu da duk rikicewarta sai da ya saka ta murmushi a lokacin.
    Sun dawo gidan jikinta na rawa kamar yadda zuciyarta ke yi na tarin abinda ta san zata tarar, abinda ke jiranta wanda kwakwalarta ta kasa hasaso mata shi, amma bai ko bari tayi hanyar wajensu ba yace ta biyo shi bangarensa.
    Kafafunta sai da suka tsaya cak jin hakan yayin da wani shiru ya ratsa ta tana jin yadda komai ya ɗauke a cikin kanta amma bayan yayi gaba ya sake juyowa ya kalle ta da wadannan idanun nasa sai kawai ta kasa cewa komai ta biyo bayan nasa suka shigo har bangarensa, ya buɗe mata kofar wannan dakin ya bata ledar kayan dake hannunta a yanzu yace ta shiga ta shirya.
    Ta shirya. Shiryawar da bata san ma’anarta ba har yanzu, kallon ɗakin kawai take yi kamar a cikinsa zata samo amsoshin da take nema.
    Ta tsugunna a hankali har ƙasa, ta buɗe ledar hannunta ta zaro kayan ciki, wata farar riga ce mai tsawo da kuma laushi, akwai wani dogon wando kakar adon jikinta pink, sannan da hijabi fari tas wanda ta san zai kai mata ne har ƙasa, mamakin inda ya samo kayan ya kamata, Allah ya sani bata san me yake nufi ba, bata gane komai ba har yanzu, so take kawai ya barta ta fita ta samu Hajiya Mardiyya ta gaya mata duk abinda ya faru ta kuma roƙe ta gafara, don ƙwakwalarta na shaida mata cewa itace gatanta ba Jawad da al’amarinsa ba.
    Kusan minti talatin tana zaune a kasan carpet ɗin ɗakin ta jingina bayanta da jikin gadon yayin da kwakwalwarta ke ta faman lissafin wucewar lokaci tana jira yazo ya sallame ta tafi, kuma saboda gajiya da kuma zazzaɓin da bai gama barinta ba har a lokacin, sai ta fara gyangyadi zaune a wajen har zuwa sanda aka kwaknkwasa kofar dakin, sau biyu kawai kafin kofar ta buɗe.
    Idonta ya sauka akansa tana ƙoƙarin wartsakewa, yana tsaye sanye da wata jallabiya baƙa, hasken fatarsa ya ƙara fitowa sosai alamun wanka yayi, yayi shirin da ita bata yi ba.
    Jawad ya tako har ciki yana kallonta, da alama inda ta tsaya bayan ya barta a dakin a wajen ma ta zauna, Babu alamun ta matsa ko’ina, me yasa take so ne ta kara masa matsala bayan tarin abubuwan da yake fuskanta?
    Shi kaɗai ya san yadda ya daurewa kansa yayi aiki a office yau, zai rantse da Allah bai taɓa ganin tsoro a idanun kowacce mace a duniyar nan ba kamar yadda ya gani a nata lokacin da ya tambaye ta idan zata aure shi, shi yasa ko da ya barta a Office din Aunty Mary, sau biyu yana kiranta yaji idan tana nan bata gudu ba, wannan shakuwar kaɗai da ta dinga yi tayi yawo a cikin kansa ta yadda da ƙyar ya goge ta yayi aikin dake gabansa.
    Da gaske yake, da gaske yana ganin zai iya aurenta shi yasa har ya tambaya, don bai taba jin wani abu da ba zai taɓa kasancewa ba sai a lokaci da Mamah ta gaya masa cewar wai aure iyayenta zasu yi mata, ya sani bashi da iko akanta fiye dasu ko ma wani a duniyar nan, amma a lokaci guda yaji cewar babu mahalukin da ya isa yasa hakan ta kasance, babu wanda zai bari yayi nasarar dauke ta daga gabansa, shi yasa a lokaci gudan ya yanke shawarar tambayarta idan har zata aure shi.
    Don a wannan lokacin yana ji kamar idan ta amsa shikenan komai ya tabbata, shikenan ta zama tasa sun kaucewa dukkan wasu abubuwa.
    Burinsa kawai ya cigaba da wayar kowacce safiya yana ganinta a gefensa ko da ba zai iya taɓa ko yatsanta ba, ya riga ya fahimci a yanzu rauninta yake so, shine babban abinda ke jan hankalinsa akanta, wannan rauni da kuma rikicewarta da suke banbanta masa ita da Rukayya, Rukayya mai ji da kanta da kuma taƙamar tsayawa da kafayrta a kodayaushe, komai nata yayi hannun riga da Zainab, shi yasa tun a farko zuciyarsa ta fara tsayawa akanta don yana neman duk wani abu ne da zai sa ya manta da Rukayya a lokacin.
    Da lokaci ya cigaba da tafiya kuma sai yake jin zuciyarsa ta saba da wannan banbancin sabon da baya jin a karo na biyu kuma zai bari ya sake rasa wani abu irin haka a rayuwarsa.
    Tun kafin ya karasa shigowa ɗakin ta miƙe hannayenta na ƙoƙarin fara rawa riƙe da rigar da ta ɗauko a cikin ledar, ya cije lebbensa kaɗan yana daurewa abinda ke ƙoƙarin tasowa daga zuciyarsa.
    “Me yasa baki shirya ba?”
    Ya tambaya kai tsaye yana kallonta, ta girgiza kanta da sauri kafin tace.
    “Ba komai, so nake in koma ɗakinmu dama sai in shirya acan.”
    “You are not going back to that place…”
    Idanunta suka tsaya akansa da kallon rashin gane abinda ya faɗa duk kuwa da yadda take a tsorace, sai ya ɗan kalli gefe alamun mantawa da hakan sannan ya sake juyowa.
    “Anan zaki zauna, ba zaki koma can ba,idan akwai abinda kike bukata a cikin kayanki sai ki saka a dauko miki..”
    Ai tun kafin ya ƙarasa kwalla ta cika idanunta ta shiga girgirza kanta da sauri.
    “Dan Allah kayi hakuri ka barni in tafi, wallahi Hajiya faɗa zata yi min, yau ma tace za’a mai da ni gida kuma…”
    “Babu inda zaki, idan kin warke zan kai ki gidan ki gansu sai mu dawo.”
    Ya fada yana sawa ta tsaya cak tana kallonsa, don hatta kwallar data taru a idanunta bata zubo ba.
    “Ba dawowa zanyi ba idan na…”
    “Dawowa zaki yi, ‘Coz babu inda zaki je ki zauna a duniyar nan da ya wuce nan.”
    Ya faɗi hakan kamar cikin tursasawa don har yanzu a tsaye take cak tana kallonsa, sai kawai ya shafo kansa da duka hannayesa biyu shima yana kallonta, yayi kokarin saita kansa sannan muryarsa ta saje fitowa.
    “Babu abinda zanyi miki Zainab, wallahi babu abinda zanyi miki, baki ga har hijabi na siyo miki ba? I just want to feel you close to me… So nake kawai in dinga jinki a kusa dani. Shi yasa na tambayeki idan zaki aure ni saboda zan je har wajen iyayenki ne in nemi aurenki, babu ruwana idan ma akwai wanda suka tsara zasu baki Zainab, ko shari’a zan iya yi da kowa idan akace za’a hana ni aurenki…”
    Ya faɗa yana kallon yadda take kallonsa har a lokacin, a tsaye kyam amma kuma idanunta na haskawa da dukkan wata ma’anar tsoro na duniya kamar ma bata fahimce shi va, ba sai kawai ya girgiza kansa sannan yace.
    “Ko ke baki da zaɓi yanzu Zainab, zan aure ki ko baki gama yanke shawara ba, idan yaso daga baya zan koya miki yadda zaki so ni.”
    Yana faɗin haka ya juya yayi hanyar kofar dakin, sai dai taku huɗu kawai ya tsayar da kafafunsa kafin ya ƙarasa, ya juyo ya sake kallonta, tana tsaye yadda take har yanzu kamar tana jira ne wani ya taɓa ta ta faɗi, sai ya juyo ya dawo da saurihar gabanta, kuma bai jira komai ba ya janye hijabin kanta zuwa ƙasa, gashin kanta da akayi wa wasu manyan kitso mai suna ‘Doka’ guda uku suka baiyana da jelarsu ƴar gajeriya a baya.
    Sai dai shi ba ta su yake ba ma, hannyensa yasa duka biyu a wuyanta, yatsunsa dukkansu suka zagaye dan siririn wuyan nata har zuwa baya, dumin jikinta ya ratsa zuwa tasa fatar a lokaci guda da ta rufe idanunta gabaɗaya, wannan kwallar da ta taru tana samun damar zubowa.
    Dukkaninsu suka sauke wata nauyayyiyar ajiyar zuciya a tare yayin da Jawad ke kallon fuskarta yana ji kamar ya ƙarasa da tasa ya haɗe goshinsu waje daya, amma ya daurewa kansa ya haɗiye wani abu a kirjinsa sannan muryarsa ta fito, a hankali cikin sautin da baiyi kama da wanda ya gama magana dashi yanzu ba.
    “Maganin ki yana wajen dining, ki ci abinci ki sha, zan je wajen Maamah yanzu zan dawo, kinji?”
    Kuma ga mamakinsa sai kawai ta ɗaga kanta sau ɗaya bata ƙara ba kuma har yanzu idanunta a rufe suke, ya cigaba da kallon fuskarta na tsawon sakanni idonsa na sauka akan siraran leɓɓenta yana jin yadda kwakwalar sa ke kokarin saita kansa daga abinda yake tunani kafin ya zare yatsunsa daga wuyanta a hankali.
    Kuma bai ƙara cewa komai ba ya juya ya nufi hanyar kofa fitar, zuciyarsa na goge hoton ta da na mahaifiyarsa a cikin idonsa, Hajiya Mardiyya… missed call dinta ne a wayarsa kusan goma sha biyar, bayan wayar da suka yi sau hudu yana gaya mata inda suke da kuma sanda zasu dawo, yanzu ma ya tabbata bata ji shigowar motarsa bane da tuni ya ganta tazo.
    “Jawad dan ub*nka a matsayin me ka dauki yarinyar nan ka kaita har wajen aikin ka?”
    Haka take gaya masa lokacin da yace mata suna office tare.
    Bata taba zaginsa ba, zai rantse bai ma taɓa jin kalmar zagi a bakinta ba, sunansa kadai akan shafe watanni bata furta ba, a kullum kuma a gaban kowa shi baban ta ne, amma yau da girman sunan da take ji da komai ta haɗa ta zage gabadaya.
    Ya hadiye wani abu a maƙogwaronsa lokacin da ya fita zuwa waje gabadaya, haka kawai yake jin kamar ko ita bata isa ta shiga tsakaninsa da yarinyar nan ba.
    Yana isa ɓangaren nata kannenta ya fara tararwa tare da wasu cousins dinsu sun zo gidan, sun haɗu akan wani katon tray da suka dafa wata tarin indomie da kifi a ciki, kowacce ta tattare kayanta sun baje suna ci ga wasu manyan-manyan jugs na zoɓo a gabansu.
    Gaisuwarsu ta amsa a cikin kansa cikin amo ɗaya na siririyar murya, kuma bayan ya amsa bai jira komai ba kafafunsa suka karasa zuwa hanyar koridon da zai tarar da dakin mahaifiyar tasa.
    Kofar a buɗe take, ya tura ta a hankali ya shiga ciki da sallamar da ta tsaya iya maƙoshinsa, sai dai idonsa bai gane masa kowa ba alamun bata ciki, kuma har ya juya zai koma lokacin da kunnensa ya jiyo masa muryarta daga cikin banɗakin ɗakin wanda kofarsa bata rufu sosai ba.
    “Yanzu duk ba wannan ba Aunty Sadiya, mu fuskanci maganar nan, ina jin kamar zan iya komai don in gyara abubuwa su koma daidai, ba zan yi wahalar banza ba tsawon shekarun nan Aunty Sadiya, na kaɗe idan har Jawad ko waninsa ya san cewar ba ni na haife shi ba….!”
    MASU ƁUKATAR A TALLATA MUSU HAJOJINSU ZA SU IYA TUNTUƁARMU TA LAMBOBIN 07045308523 MUN GODE

    Note
    error: Content is protected !!