Farar Huta 2 – Chapter Fourteen
by NadminMASU ƁUKATAR A TALLATA MUSU HAJOJINSU ZA SU IYA TUNTUƁARMU TA LAMBOBIN 07045308523 MUN GODE
Ƙafafunsa suka shigo cikin tangameman falon a hankali, kai tsaye ya shiga wuce tarin wajajen dake cikin falon har zuwa inda ya san zai sami mahaifin nasa, yana bi ta kan tausasan carpet ɗin dake wajen kala-kala har ya karasa wajen a daidai lokacin da idonsa ya shaida masa mutanen dake zaune bayan mahaifin nasa.
Mahaifiyarsa, matar mahaifinsa ta biyu mai suna Yagana, sai kuma shugaban ma’aikatan gidan Joshua, yana kallon yadda kayan Hajiya Yaganan ke ƙyalli tare da na mshaifiyarsa a cikin fitulun wajen kamar masu shirin tafiya fadar shugaban ƙasa.
Ya karasa da sallama sanda mahaifin nasa ya sauke jaridar dake fuskarsa sannan shirun da suka yi dukkaninsu ya tafi tare da amsawar sallamar daga mahaifinsa da kuma mahaifiyarsa su kaɗai yayin da Hajiya Yaganan ta shiga jefo masa hararar da sau ɗaya ya gani ya ɗauke kansa.
“Barka da Safiya Abba.”
Ya gaishe da mahaifin nasa yana zama kusa da Joshua.
“Yawwa mun tashi lafiya?”
Amon muryar mahaifin nasa ya fito babu yabo kuma babu fallasa.
“Lafiya kalau Alhmdlilah.” Ya amsa kafin mahaifin nasa ya sake cewa.
“Ai ban san kana gari ba ma har akayi bikin ƙannenka, sai yau da na tashi da ƙorafin ka da aka kawo min.”
Kafin ya amsa muryar Hajiya Yagana ta cika falon da cewar.
“Ƙorafi? Ai ba ƙorafi bane Daddyn su Amal, laifi ne yayi kuma shi kansa ya san da hakan.”
Ta kira sunansa tana kebanta shi da ƴaƴan ta saboda Hajiya Mardiyyan dake zaune. Kuma maimakon mahaifin nasu yayi maganar katse shin da tayi a zancensa, sai kawai yace da Jawad ɗin.
“Me yasa ka korar mata ƴan aiki har mutum uku Jawad?”
Jawad ya gyara zamansa yana fuskantar inda zancen ya dosa kafin yace.
“Ni ban san ƴan aikinta bane, laifi suka yi min nace da Joshua ya kore su, kuma ko a karkashin wa suke aiki a gidan nan haka zan ce.”
Alhaji Bashir ya gyaɗa kansa alamun ya fahimta.
“Laifin me suka yi?”
Kai tsaye ya sake cewa.
“Wata yarinya suka ƙonawa kayan sawarta gabadaya, sunanta Zainab.”
Amsar ta fito da zare idon da Hajiya Mardiyya tayi a lokaci guda tana kallonsa da kuma kallon haushi dana takaicin da Hajiya Yagana ke jifansa dashi.
“Ita wannan yarinyar a ina take da har kake yanke wannan hukuncin saboda ita?”
Kai tsaye ba tare da wata shakka ba Jawad ya sake bada amsa, idanunsa na kallon adon carpet din dake gabansa, yace.
“Anan gidan take, ƴar aikin Maamah ce.”
Wannan karon ba matan kaɗai ba, hatta Alhaji Bashir din da kuma Joshuan dake zaune a gefensa sai da mamaki ya haska a fuskokinsu.
“Zainab Jawad? Zainab din dake wajena?”
Da alama Hajiya Mardiyyan dake tambaya bata shiryawa hakan ba, sai dai kafin ya bata amsa mahaifin nasa ya kawo tasa tambayar shima.
“Meye tsakaninka da ita kenan?”
Jawad ya girgiza kansa.
“Babu komai, I just like seeing her around me.” ( Babu komai, kawai ina jin dadin ganinta a kusa dani ne.)
Ba wai sabon abu bane, duka wanda ke zaune a wajen hatta Joshua daya ɗebi shekaru a gidan, ya san hali irin na Jawad, halin kafiya, jajircewa, naci da kuma rashin boye ra’ayinsa akan abu, halin da tun a baya ya jawo rashin jituwa tsakaninsa da mahaifin nasa don ra’ayinsu ya banbanta sam kan gudanar da harkar mulkin da yake yi wanda ya faro tun daga matakin Chairman. Sannan kuma halinsa wanda ya dace da aikin da yake yi a office wanda ya jawo har ya samu babban muƙami a ƙananun shekaru.
Don haka babu wani ja in ja, Alhaji Bashir din ya sake gyada kansa alamun ya fahimta sannan yace.
“Bayan haka babu wani abu?”
Kalmar wani abun a dunƙule ta fito, ɗauke da tarin ma’anonin da kowa a wajen ya fahimce su, Jawad ya haɗiye wani abu da bai san sunansa ba a maƙogwaronsa, a wannan muhallin amsar sa mai tsafta ce ya sani, amma a wancan ɓoyayyen al’amarin na Ruƙayya, zai iya faɗar amsar da zata sanya kowa sallallami a wajen nan, amsar da zai tozarta mahaifiyarsa ta mafi munin hanyar da ba zata taɓa tsammani ba, wannan shine kadai rauninsa, shine kaɗai rauninsa a duniya ya sani, kuma bai san ma ta yadda zai fuskanci hakan ba.
Wannan karon idanunsa na kan mahaifiyarsa dake kallonsa da tarin wasu abubuwa da ba zai iya fassara su ba yace.
“Babu wani abu Abba, babu komai tsakani na da ita.”
Alhaji Bashir ya sake gyaɗa kansa kafin yayi magana.
“Daga kai har yayyenka da ƙannenka babu wanda nake takurawa a rayuwarsa kun sani, abu ɗaya ne kawai ba zan taɓa lamunta ba shine hoto mara kyan da har zai iya taɓa siyasa ta, saboda haka ina son labarin nan ya cigaba da kasancewa a yadda ka faɗe shi yanzu Jawad.
Yarinya aiki take yi a gidan nan, kar ka shiga hakkinta, kuma kar ka shiga hakki na da naka na neman wani abu da ya ɗara haka a tsakaninku, ko mai kyau ko kuma akasin sa. Ba zan lamunta ba wallahi!”
Shiru ya ratsa ɗakin sabidya yadda muryar Alhaji Bashir ɗin ta fito cikin ɗagawa da kuma hasala, wani abu da idan har ba a fagen siyasar tasa da yake ji da ita ba, da wuya ne kaga ɓacin ransa irin haka, tsarinsa guda daya ne, yace a cikin iyalansa kowa yana da yanci da kuma damar yin abinda yake so, abu daya ne kawai ba zai taba lamunta ba, idan har al’amarinka zai shafi siyasar sa komai kankantarsa kuwa, balle kuma a yanzu da kujerar tasa ke girgidi kowa ya sani.
Sai dai duk wannan ba shi ya dami Jawad a wannan lokacin ba, ba shine abinda kwakwalarsa ke biyawa ba, kalamansa ne, kalaman mahaifin nasa na ƙarshe masu dauke da ma’anar da ya kasa fahimta balle har ya ajiye su a gefe ya fuskanci ma’anar kallon da mahaifiyarsa ke masa a lokacin.
_… kar ka shiga hakki na da naka na neman wani abu da ya ɗara haka a tsakaninku, komai kyau ko kuma akasin sa…”_
***
Ƙofar falon ta buɗe, ta buɗe a lokacin da Jawad ke magana cikin wayar dake kare a kunnensa, dawowarsa kenan daga ɓangaren mahaifin nasa ya shiga ansa kira daga wani shugabansa na wajen aiki da yake can babban branch dinsu na Lagos. Kuma bai ɗago ya kalli kofar ba don ya riga ya san waye mai shigowar har ta ƙaraso ciki, kamar kodayaushe hannunta ɗauke da tray din kayan abincin da ya zama dolenta wajen kawowa.
“I’ll see to it on Monday sir.”
Cewar Jawad bayan ya fahimci dukkan abinda mutumin ke faɗa ta cikin da wayar.
“Okay, so thank you for your time Mr. Kuliya.”
“Thank you too sir.”
“You are welcome.”
Cewar mutumin kafin wayar tasu tazo ƙarshe, Jawad ya ajiye ta a gefensa sannan ya dago yana kallon Zainab fin dake tsaye daga wajen Dining ɗin bayan ta ajiye kayan abincin, bai sani ba idan kyau tayi ko kuma akasin hakan, kawai dai ta ca’nja, don tana sanye ne da ɗaya daga cikin bunbula-bunbulan dogwayen rigunan da ya bawa wani direba a gidan yaje ya siyo mata jiya, wanda sai bayan ya siyo din sannan yaga wautarsa na bawa namiji ya siyo, don in banda yawo ba abinda take yi a cikin kayan, Khairat zai kira ya bata wani kudin ya san zata siyo wanda zasu yi mata daidai.
“Ina wuni.”
Ganin yadda yake kallonta ya sa ta furta gaisuwar da ta san ba amsawa zaiyi ba don bai taɓa ba, amma kuma wannan bai sa ta fasa ba a kullum itama, sai kawai yayi ajiyar zuciya a hankali sannan yace.
“Ga wata jaka nan akan table din dauko ta ki zo.”
Ta juya ta kalli jakar daga can gaban inda ta ajiye kwanukan, ta mika hannunta ta dauko ta sannan ta taho, ta karaso cikin falon a hankali har zuwa gabansa.
“Zauna.” Ya faɗa kai tsaye bayan ya karɓa, kuma ta riga ta san me yake nufi don haka bata yi wani musu ba ta sami waje a daidai gaban nasa ta zauna.
“Maamah ta ganki kafin ki taho?”
Ya tambaya yana kallonta, sai ta girgiza kanta a hankali.
“A’ah, tun dazu ta tafi ɓangaren Alhaji bata dawo ba.”
“Wani ya sake miki wani abu a cikin gidan?”
Ta sake girgiza kanta a hankali tana kallon ƙasa.
Ya cije lebbensa kaɗan sannan ya buɗe jakar ya dauko wani bandeji da kuma wasu kwalabe har da plaster, kuma bai sake cewa komai ba kawai ta ga ya sauko daidai gabanta shima, sannan yasa hannunsa kai tsaye ya janye ƙasan rigarta kadan, kumburarriyar ƙafarta da taji ciwo lokacin da plate din tangaran din nan ya fashe akanta ta fito fili.
“Just stay still.” Ya fada a hankali ba tare da ya damu da ta gane ko bata gane ba.
Zuciyar Zainab ta buga a ƙirjinta, mamaki ya riƙe ta a yadda take a zaune, sannan tsoro ya mamaye koina a ƙirjinta, hannayenta suka shiga rawa, amma sai dukkan hakan ya tafi da saukar ruwan wani abu cikin ciwon nata, zafinsa ya ratsa har ƙasan ruhinta ta yadda ba shiri ta runtse idanunta da dukkan karfin da zata iya tana jin yadda yake kokarin bajewa a ko’ina na jikinta amma duk da haka bata motsa daga yadda take ba har ya gama.
Ya ɗaga kafar tata a hankali ya naɗe ta da bandeji bayan ya saka plaster sannan ya tattara sauran kayan ya mayar cikin jakar da ya bari akan kujera sannan ya juyo ya sake kallonta, itama shi take kallo yanzu, manyan idanunta sun buɗe sosai akan fuskarta, kuma yanayin yadda yake zaune yayi kusa da ita sosai amma duk da haka bata yi ƙoƙarin matsawa ba kallonsa kawai take yi da tarin wasu abubuwa fal da bata san ma’anarsu ba a cikin kanta.
“Ni kike yiwa wannan kallon?”
Muryarsa ta fito a hankali shima yana kallonta, kuma muryar ta fito kamar ya daeo da ita cikin hayyacinta don babu shiri ta miƙe a lokaci guda jikinta ya hau rawarsa, sannan tayi hanyar wajen Dining inda ta san aikinta na gaba shine zuba abincinsa.
Sai kawai yayi murmushi a hankali sannan ya miƙe tsaye shima yana nufar inda ya ajiye wayarsa kafin yabi bayanta.
**
A cikin dakin Hajiya Mardiyya tayi wulli da dankwalin kanta akan gadon ɗakin yayin da jikinta ke rawa tana rike da wayar hannunta kafin tace.
“Ki taimaka min Aunty Sadiya kizo gidan nan yau, tsoro na Allah tsoro na Annabi sce wannan yarinyar tana da alaƙa dashi.”
Daga cikin wayar yayarta mai suna Sadiyar tace.
“Baki da hankali ai Mardi, na daɗe ina gaya miki har yanzu baki da wayo balle hangen nesa idan banda haka, me yasa zaki dauki yarinyar nan aiki? Tun farko da kika ji ance daga Garun Albasu take me yasa zaki rike ta har ki sakar mata kamar yadda nazo na tarar kina yi?
Garun Albasu ƙauye ne, mutanen cikinsa ba wani yawa ne dasu ba, idan har ma yarinyar nan ta kasance ƴaruwarsa wani abun mamaki ne?”
Hajiya Mardiyya na faman girgirza kanta tace.
“Ba zai yiwu ba, ba zai taba kasancewa ba, dan Allah Aunty Sadiya kizo mu zauna akan zancen nan…!”
***
*Kano.*
*Bakori Enterprises.*
*10:30am.*
“Ina Faruk ɗin yake?”
Yakubu ya tambaya ta cikin screen ɗin computer dake gaban Ma’aruf wanda suke video call ta jiki, Ma’aruf ya girgiza kansa kafin yace.
“Baya nan, ya tafi wani aiki ne.”
Yakubu ya gyaɗa kansa yana cije leɓe.
“I wish yana nan, da na nuna masa proof na kokwanton da yake yi akan aikina.”
Ma’ruf ya gyaɗa kansa kusan sau biyar a jere.
“Ya sani Yakubu, ai munyi maganar dashi tun sanda ka kira ni, let’s just get straight to the point dan Allah, ina yake?”
“Ka kwantar da hankalin ka yanzu zasu shigo dashi, bana garaje a aikina ka sani,ko so kake yi yazo a sigar da ba zaka sami wata amsa ba?”
Ma’aruf ya haɗe tafukan hannayensa biyu akan fuskarsa sannan ya fitar da iska ta bakinsa, kusan awa guda kenan da Yakubun ya kira shi cewa zai haɗa shi da Mr. Okaforn ya tambaye shi duk abinda yake so ta wayar video call kafin su yanke hukuncin abinda zasu yi dashi.
Kuma tun a lokacin suke magana da Yakubun ta wayar ba tare da ya ga Mr. Okaforn ba don kamar yadda Yakubun yace ne yana hannun wadanda zasu lallasa shi ta hanyar da ba zaiyi taurin kai ba.
Tunani kawai yake a cikin kansa na yadda zasu sami karin bayanin da zai kai su ga ko waye wannan Awwalun da ya faɗa, kuma ko a ina yake, don a yanzu haka har an fitar masa da list din duk wani ma’aikaci dake karkarshin kamfanin nasu mai suna Awwalu, da wadanda suka yi aiki suka bar wajen har da ma wadanda applying kawai suka taba yi ba’a dauke su ba tukunna.
Ance idan rakuminka ya bata ka duba har cikin tulu, a yanzu ya koyi buɗe idanunsa sosai wajen nema, maganar da Amina ta fada masa na cewar su nemi mutumin nan har a cikin prison ta bude tarin wasu abubuwa da yawa a cikin kansa, ta sa shi ya daɗa fahimtar cewa bai kamata yayi limiting nemansa a iya wani waje guda ba, watakila tun farko abinda yasa suke ta zagaye suna dawowa kenan… Da wannan tunanin yake ƙara godewa ubangiji a kodayaushe da ya azurta shi da mace kamar Amina a cikin rayuwarsa.
Ƙofar dake bayan Yakubu a cikin videon ta buɗe a lokacin, wasu mutane biyu suka shigo, dogwayen jikinsu kawai ya gani kafin Yakubun ya juya yaga mutumin da suke rike dashi.
Kuma ba don ya tabbatar da cewar Mr. Okaforn da suke jira ne za’a shigo dashi ba, zai rantse ba shi bane wannsn saboda fuskarsa ta kumbura gabaɗaya, idanunsa sun shige a fuskar tasa sannan hancinsa da bakinsa na fitar da jini. A lokaci guda ya shiga girgiza kansa yana kallon Yakubun.
“This is not what I ask of him Yakubu, ( ba abinda nace kuyi masa ba kenan) mutumin nan yana da iyali…”
“Just ask your questions.”
( Kawai kayi tambayoyin ka.)
Cewar Yakubun yana katse shi, daidai lokacin da mutanen nan biyu suka ajiye Mr. Okaforn a gaban camerar sannan suka juya suka fita.
Ma’aruf ya haɗiye wani abu a maƙogwaronsa yana girgiza kansa sanda Mr. Okaforn ya shiga magiya yana haɗe hannayensa biyu cikin kuka. Sai kawai yayi karfin halin saita muryarsa sannan ya shiga magana da turanci.
“Komai zai koma daidai idan har ka bamu hadin kai akan dukkan abinda muka tambaye ka, ba zan bari su sake taɓa ka ba, za’a maida kai gida cikin iyalanka lafiya, hatta ƴarka Mary zan yafe mata laifin da tayi min akan ƴata, kuma ba zamu sake tuntubarka bayan nan, zaka cigaba da rayuwarka cikin kwanciyar hankali idan har ka fada min dukkan abinda ka sani Mr. Okafor.”
Kuma bai bashi damar da zai tsaiwaita godiyar da ya fara ba yace.
“Ina jinka.”
Babu musu balle tirjiya Mr. Okafor ya gyada kansa da sauri alamun zaiyi hakan kafin muryarsa dake cike da kuka ta fara magana cikin nasa yaren na Pidgin English.
“Kamar yadda ka sani Yallabai ni mai shara da goge goge ne a kamfaninka,to watannin baya da suka wuce, sai wani abokin aikina mai suna Sani ya same ni da labarin cewa ya samo mana hanyar da zamu yi kuɗi mu daina wannan bautar, ya gaya min cewa akwai wani mutumi mai suna Isa, bayarbe ne amma kuma musulmi, yana harkar computer hacking da duk wani abu da ya shafi harkar technology na yanzu.
Rana ɗaya yazo yace min wai wasu mutane sun same shi da rokon cewa zasu bashi miliyan daya idan har ya shiga ofishinka ya samu wasu nambobi a cikin computerka, to shi bai san harkar komai na computer ba shine yazo ya same ni yace zai bani rabin kudin dubu dari biyar idan har na taya shi aikin, ya gaya min sau ɗaya cewar sunan mutumin da ya saka su aikin shi da Isa Awwalu amma bayan nan bai kara gaya min komai akansa ba.
Kuma sai a ranar da nake da aikin gyaran ofishin naka ne sannan muka yi waya da daya mutumin mai suna Isa, shi ya kwatanta min inda zan shiga a computer taka in kwafo wasu security numbers wanda sune na account din kamfanin, kuma na sami sa’a har naje na samo nambobin ba’a kama ni ba.
Kuma Sani ya gaya min cewa da wannan nambobin suka yi amfani akayi hacking account number kamfanin har aka turo muku da alert din ƙarya alhali kuɗin sun tafi ne zuwa wani account daban, kuma sunyi haka ne ta hanyar da ko banki baza su gane balle idan kun je ku sami wata gamsashshiyar amsa daga gare su.
Bayan mun gama aikin da sati ɗaya sai shi abokin aikin nawa ya kawo min kuɗi dubu dari kawai yace min wai shima basu bashi yadda suka fada ba, amma idan sun bashin zai ciko min. Daga nan bai ƙara yi min mgna har tsawon lokaci kuma na tuntube shi amma yaki saurarata.
Ni kuma hakan sai nayi kokarin ɗaukan matakin da zan tsorata su su bani kudina, shi yasa naje na sami sbokin aikin ka Yallabai Faruk na gaya masa cewa ina da masaniyar abinda ya faru, nayi recording hirar mu a wayata sannan naje na sami abokin aikin nawa Sani da niyyar in nuna masa hakan.
Sai dai ina zuwa gidansa na tarar ya mutu har ana jana’izarsa. Sai na tsorata na dawo gida, bayan kwana biyu sai Isa ya kira ni da cewar inyi hankali watakila wadanda suka kashe Sani suna da alaka da wadanda suka samu aikin nan, a wannan ranar ne kai kuma kazo gidana Yallabai, sai dai bamu samu munyi magana ba ka dauki wannan yarinyar ka tafi.
A washegari kuma na tsinci labarin mutuwar Isa shima, shi yasa ba shiri na haɗa iyalaina muka gudo nan garin ranka ta daɗe, kuma nayi maka rantsuwa da kabarin babana tun daga wancan lokacin ban ƙara jin wani bayani daga kowa ba ranka ya daɗe.”
Mr. Okafor ya kai ƙarshe a lokacin da Ma’aruf da kuma Yakubun suka cigaba da kallonsa, kallon da Ma’aruf ke yi masa daban ne, kallonsa yake yana kuma saurarensa da dukkan wani abu mai hankali dake jikinsa, kwakwalarsa na fahimtar kowacce kalma dake taruwa tana fitar da jimla guda a bayanin nasa, kuma bayan ya kai ƙarshe, abu na farko da ya fara yi shine jawo wayarsa. Hannayensa suka lalubo nambar Martha a lokaci guda.
“Ki duba min a kananun ma’aikatan dake aiki akwai wani Sani da ya mutu kwanakin baya?”
“Okay sir.” Ta amsa da sauri fahimtar cewa shima saurin yake yi a cikin muryarsa, kuma daga inda yake zaune yana jin karar keyboard din computer ta da take dannawa, cikin abinda bai fi rabin minti ba tace.
“Akwai yallabai, sunansa Sani Madugu, wani danuwansa ne yayi reporting mutuwarsa wata hudu da suka wuce, kuma har an bawa iyalinsa garatutinsa wancan watan.”
“Thank you.”
Kawai ya faɗa sannan ya ajiye wayar, idonsa ya sake dawowa kan Yakubu da kuma Mr. Okaforn dake jiran abinda zai ce ta cikin computer, zai so kwarai yace a sake shi ya tafi ga iyalansa amma ba zai iya ba, bayani kawai suka samu daga wajensa babu wata shaida ko kuma kwakwaran bayanin da zai kaisu ga wani abu har yanzu, don haka sakinsa zai zama tamkar saki na dafe ne wanda ba zai fara hakan ba.
Saboda haka yayi ajiyar zuciya mai nauyi kamar ta cikinta ne zai fitar da tarin abubuwan da yake jin nauyinsu a cikin kansa sannan yace.
“A cigaba da rike shi Yakubu, amma kar ku sake taba shi…”
“Sir pleeeease, pleeese sirrrr, abeg naaaa, help me sirrrr pleaseeeeee…..”
Magiyar Mr. Okaforn ta sake cika oficce din a lokaci guda kafin Yakubu ya daga murya ya kira mutanen nan, kuma suka shigo a lokaci guda suka ɗauke shi suka sake fita dashi yana ta magiyar yana rokon Ma’aruf.
“Kar ka damu, duka iyalan nasa ma suna nan tare damu, zan cigaba da rike su har lokacin da kace, ‘Cox ina da wani aiki da zsn yi anan garin ma.”
Ma’aruf ya gyaɗa kansa.
“Nagode sosai Yakubu it’s a pleasure to work with you. Zan sake turo maka da wasu kudin insha Allah to keep things going.”
Yakubu ya gyada kansa shima sau biyu a jere sannan kiran ya katse. Ya katse a lokaci guda da saƙon Amina ya shigo wayar Ma’aruf dake gefe, ya dauko ta ya duba, abinda ta rubuta dan guntu ne.
“Sugar, zanje kitso dan Allah…”
Yana gama karantawa wani saƙon nata ya kara shigowa akai.
“Ba nisa…”
“Kusa da gidansu Fatima ne…”
Gidansu Fatima, wannan kawar tata da yake yawan ji tana faɗa, dazu tare suka fito ya sauke ta s gidansu tare da Hamida kafin ya tajo office, shima ya shiga ciki sun gaisa da kowa, don saura kwana biyu kawai tafiyar mahaifinta da kuma kaninta Aminu zuwa India, har da kansa ya yiwa Mami godiya da yaji labarin cewa ita ta ɗauki nauyin tafiyar, ƴanuwanta ne ya sani amma haka kurum sai yaji kamar saboda shi tayi hakan, shi yasa shima a yanzu da yaje yayi musu irin tata kyautatawar wanda da kyar suka karɓa, abinda basu sani ba shine, zuciyarsa na gaya masa cewa zaiyi tarin abinda yafi haka ma indai akan Amina ne.
Saboda haka kafin wani saƙon ya sake shigowa ya shiga typing amsar sa da take jira.
“Ki tabbatar an rubuta sunana a jikin kitson nan Doll.”
Sakon ya tafi a lokaci guda tare da shigowar kiran Faruk, don haka ya fasa cigaba da rubuta abinda yayi niyya ya ɗauka.
Muryar Faruk ɗin ta fito a lokaci guda da ya kara wayar a kunnensa.
“Muna High Prison, mun sami mutumin nan B, yana ganinsa ya gane shi, yanzu haka ma ya fadi duk wadanda suka saka shi ya fita daga Prison din suma an tafi za’a fito dasu don dukkaninsu ma’aikatan wajen ne.”
“Alhmdlilah, Alhmdlilah, Alhmdlilah….”
Itace kalmar dake fitowa daga bakin Ma’aruf tunda yaji abinda Faruk ɗin ya faɗa na farko. Ya miƙe tsaye a lokaci guda ya fito daga kujerarsa ya dawo tsakiyar office din hannunsa a cikin gashin kansa yayin da zuciyarsa ta kasa tsaida kanta waje guda a tsakanin murnar wannan nasarar da kuma taraddadin abinda yake shirin tambaya.
“Ya gaya maka wani abu Faruk? Any clue na su waye mutanen da suka sa shi aikin kafin yaje ya karbi kudin?”
Ya tambaya muryarsa a tsaye kyam!
A can bangaren,Faruk ya girgiza kansa yana kallon hayaniyar dake faruwa a gabansa wadda ma’aikatan Prison ɗin suka tayar na Cewar baza’a tafi da ogansu ba kasancewar har da sa hannunsa al’amarin,tarin ƴan sandan da suka zo dasu na ta ƙoƙari wajen hana su haurowa inda su suke tsaye ana shirin fito da mutumin, sai ya girgiza kansa a hankali sannan yace.
“Ko waye Awwalu ya shiga uku Ma’aruf, don gayen yace min mutum daya ya gani da ya saka shi aikin, shi ya bashi wallet dinka da wayoyinka ya kuma fada masa duk abinda zaiyi, kuma yace sunansa Awwwalu.”
“Awwalu.” Ma’aruf ya furta ba tare da ya san ya fada ba.
“Awwalu.” Ya sake faɗa a hankali.
****
“Awwalu.”
Hajiya Kilishi ta faɗa tana kallon Aminiyarta Hajiya Salamatu.
“Ni Awwalu zai yaudara ya mayar mara hankali Salamatu? Wai har ni Awwalu yake kokarin cin amana a harkar nan?”
Ta sake faɗa amon muryarta na fitowa cike da takaici. Suna zaune a cikin falon gidan Hajiya Salamatun ne,inda bayan su kaya ne fal na sabbabin atamfofi da kuma lesuna tsibiri-tsibiri an zube su kamar banza kasancewar dawowar Hajiya Salamatun kenan daga ƙasar da take yo siyayyar kaduwancinta.
Hajiya Salamatu ta girgiza kanta.
“Wannan ai ba komai bane Kilishi, ki duba fa ki ga yadda kike cin amanar wadannan mutanen dake tare dake, to har dan abokin aikin ki wanda kullum yake ganin abinda kike yi ya kwaikwayi hakan sai kiji wani zafi? Kamata yayi ace daman kin dayde da shirya masa.
Kilishi dake kallonta tace.
“Maganganunki sunyi zafi Salamatu, amma haka ne, tabbas abinda kika faɗa haka yake, wannan ba komai bane don Awwalu ya nemi ya bauɗe, daɗin shine na daɗe ina shirya masa dama, kuma a tunaninsa ya koyi irin taku na yana shirya hanyarsa bai san cewa sawun giwa ya take na rakumi ba kuma ko a gidan giya akwai babba, sannan sama tayi wa yaro nisa sai dai ya ɗaga kai yayi kallo.”
“Wannan haka yake, nice ta farko da zan fara yi miki wannan yabon bayan ke Kilishi, yanzu ki gaya min a ina kuka tsaya tare dashi.”
Kilishi ta kurbi lemon hannunta tana kallon Salamatu ta cikin gikashin kofin, kuma bata ajiye ba sai da ta shanye shi tas sannan tace.
“Tun daga ranar da ya kawo min hodar nan daga lagos bai sake ce min komai ba nima kuma ban kira shi ba, dukkan abinda yake ciki ina jinsa ne ta hanyar wannan Sadik din dana tura ya zama abokinsa a kwanakin baya, saboda haka na riga na daɗe da gama shirya masa, yanzu jira kawai nake yi ya nunawa Sadik inda ya tara Cd’s din da yake ɗaukar muryarta, ya riga ya ganoinda computers din suke, da mun samu Cd’s din, zan sa ya ƙona komai ne gabaɗaya sannan inje in fuskance shi.
Zan gaya masa dukkan shirinsa da na san yana yi da kuma yadda akayi na kama shi, kafin in aiwatar da nufi na akansa.”
“Me zaki yi masa?”
Kai tsaye Salsmatun ta tambaya tana wulli da wani leshi dake kan cinyarta zuwa cikin kayan dake baje a dakin.
“Haukata shi zanyi Salamatu, ba zan kashe shi ba, Haukata Awwalu zanyi ta yadda zai kare rayuwarsa yana biyan bashin cutar da yaso yayi min.”
Salamatu ta gyada kanta tana taɓe baki kafin tace.
“Shi kuma Sadik din fa?”
Kilishi tayi shiru tana nazari kafin tace.
“Sadik irin mutanen da basu da ra’ayin kansu ne Salamatu, kuma daga Ghana yake kin sani saboda haka wani kaso kawai zan bashi ya koma kasar su, da ya koma ya cigaba da shaye-shayensa shikenan bani da wata matsala dashi na sani.”
Salamatu ta gyada kanta tana murmushi sannan ta sake cewa.”
“Victoria Island dai na can na jiranki Kilishi, kafin ki kammala komai na tabbata an gama gine-ginen nan.”
Girgiza kanta kawai Kilishi tayi kafin tace.
“Bar wannan zancen tukunna yanzu Salamatu, jikina ya bani cewar Ma’aruf ya dage akan binciken kamfanin nan nasu, bai ce dani komai ba amma na fahimci hakan ne kawai, shi yasa na tsayar da komai nake son inyi in gama da Awwalu akan kari.
Tunda kin san indai har sun sami mutanen nan duk abinda zasu samo zai kaisu ne kawai ga Awwalun tunda shi kadai suka sani, kin ga idan na kammala abinda zanyi dashi kafin su nemo shi, zasu je su same shi ne a haukace, haukan da ba zai taɓa warkewa ba. Daga nan sai in dawo in fuskanci batun yarinyar nan da kuma Baffa, yadda zan tsara mutuwarsa a ranar da kudi na gaba zasu shigo kamfanin.”
Dariyar da Hajiya Salamatu ta kyalkyale da ita tana debo wani zagi wata iriyar dariya ce da babu shiri Kilishin ta shiga taya ta itama, muryoyinsu suka karaɗe falon cikin wani irin amo mai ɗauke da tsananin nishadi da kuma taƙama, taƙamar da a cikinta Kilishin ke jin kanta zuwa wani mataki da take jin cewa bata da takwara a duniyar nan.
Abinda bata sani ba shine, alƙalami ya riga ya bushe akan wata ƙadddara da zata wanzu cikin kwanakin da take lissafawa kanta da wani labari da yasha banban da wasiƙar da zuciyarta ke biya mata!
Kuma zaren labarin ya fara ne a daidai wannan lokacin kuma a cikin wannan dakin!
MASU ƁUKATAR A TALLATA MUSU HAJOJINSU ZA SU IYA TUNTUƁARMU TA LAMBOBIN 07045308523 MUN GODE
