Search
You have no alerts.

    MASU ƁUKATAR A TALLATA MUSU HAJOJINSU ZA SU IYA TUNTUƁARMU TA LAMBOBIN 07045308523 MUN GODE

    Lokacin da aka shigo da gawar, lokacin da gidan ya sake hargitsewa da tarin jana’ar dake da ta shigowa da kuma masu kuka da salatin da muryarsu ke ɗagawa, lokacin Hajiya Maimuna ta bude fuskar gawar danta da aka shimfude a falon Baffa, hannunta ya rike zanin atamfarta da aka nannaɗo shi a jiki, danshin jinin dake jikin atamfar ya a ratsawa har tsakiyar kanta, a lokacin ne kuma abinda ya faru tsakaninta dashi jiya ya dawo cikin kanta.
    “Mimi…
    Muryarsa lokacin da ya shigo cikin gidan ta ratsa kunnuwanta a jiyan. Tun da yayi sallama da Ladi ta bude masa ƙofar yake kwala kiran har ya shigo gidan, a lokacin tana kitchen, ta jiyo shi tana ta amsawa ama shi bai jiyo ta ba gashi babu kowa a gidan, don safiya ce dukkan yammatan gidan sun tafi makaranta, don haka tana jinsa sai da ya zagaye kusan kowanne daki a gidan yana kiran sunanta a yadda shi kadai yake gaya mata wato Mimi, kafin ya dangana da kitchen din.
    Kuma shirun da tayi bayan ya buɗe kofar kitchen ɗin ya saka ta juyowa daga tukin tuwon da take yi. Ya tsaye riƙe da hannun ƙofar kawai yana kallonta, ta manta rabon da ta ganshi da manyan kaya, kullum cikin kananun kaya yake sune shigarsa a kodayaushe, don shekara wajen biyar ya shafe a Cairo yana karatu don haka dasu ya saba.
    Amma yanzu da ya dawo gida kuma ya karbi aikin kamfanin Bakori wani abu da yake burinsa kuma mafarkinsa tun yana yaro, sai ya zama dole manyan kayan su zasu zama kayansa.
    Jamal yafi kowa kyau a gidan, hakan wani abu ne da ba sai an lissafa ba, tun daga kan yayanta har zuwa na Kilishi babu wanda yake ko kama dashi, tun yana yaro mutane da yawa na cewa ma ba ita ta haife shi ba duk da cewar itama fara ce, amma baya kama da ita kuma baya kama da kowa banda hancinsa da wasu suka ce yana shige da na Baffa don na Baffan ma dogo ne kamar nasan, akwai lokacin da yana shekara bakwai har sai da jama’a suka sa mata kokonto a ranta game dashi itama ta shiga tunanin ko anyi mata canjansa a asibiti ne sai da Baffa ya dakatar da ita tukunna.
    “Raina yana ta tashi har nayi zaton ko bakya gidan ne, muryarsa mai zurfi ta fada yana kllonta,.
    “Allah ya sawwake maka, ta ina rai yake tashi Jamal?”
    Ta faɗa tana dariya kafin ta juya.
    Ya karaso ciki ya tsaya a kusa da ita yana kallon tukunyar dake jan gas din da take tuka tuwon da ita.
    “Mimi kice min wannan miyar waken ce?”
    Ya tambaya sanin cewar ta gaya masa tana da miyar tun jiya.
    “Itace dai yanzu zan dauko ta daga freezer, kawai tashi nayi yau ina sha’awar tuwon.”
    “Alhamdlilah.” Ya fada yana zura hannunsa cikin gashin kansa.
    “Dama banci komai ba wallahi, ina tashi naga wai yaran nan dankali aka soya musu.”
    Shi baya son duk wadannan kayan cimar na zamani, abu kadan yake ci a cikinsu yafi son abincin gargajiya duk kuwa da zamansa a kasar waje, bama shi kadai ba kusan duka yayanta haka suke, har Ma’aruf idan bata manta ba.
    A lokacin ne ya zaro wasu kudi daga cikin aljihunsa ya ajiye a gabanta, gaban flask din da ta gama kwashe tuwon a ciki, kuma ganin yawan kudin shi ya tsayar da ita cak daga karasa abinda taje yi.
    “Baffa ne yace in kawo miki.”
    Ya fada da sautin muryarsa da ya canja a yanzu, tana iya tuna yadda wani irin daci ya mamaye kirjinta a lokaci guda kafin ta yi kokarin ture hakan, hannunta ya kai kudin tana fadin “Allah ya saka da alkhairi’, amma sai Jamal yasa nasa ya dafe nata kafin ta dauka.
    “Kudin cefane ne ko?” Ya tambaya, muryarsa na shaida irin bacin ran dake cikinta, bata amsa ba ya cigaba.
    “Tunda Baffa ya bani kudin nan bake binsa da kallo, baice min komai ba amma na fahimci baya miki magana tun last week, kuma na tambaye shi amma bai bani amsa ba, bana son inyi komai akan zargi Mimi, ki gaya min abinda nake tunani haka ne?”
    “Jamal…” Ta fada tana kallonsa.
    “Dan Allah.” Yayi saurin katse ta.
    “Ki gaya min gaskiya, ki san gyarawa zanyi, kin san ba zanyi abinda bai dace ba.”
    Wucewar wasu sakanni kafin ta gyaɗa kanta a hankali tana cigaba da kallonsa.
    “Akan zancen zuwa hutun su Munaya ne a Abuja, yace bai yarda ba kuma suna son zuwa, shine nayi masa maganar cewa ta kanaya suje din, amma sai bai fahimta ba, sai laifin ya dawo kaina, yace sun fara girma sun fara raina maganganunsa ni kuma ina biye musu.”
    Ya kalle ta tsawon waucewar wasu mintuna kafin ya zura hannunsa cikin gashin kansa.
    “Kiyi hakuri Mimi, insha Allah duk irin wadannan abubuwwan sun kusa zuwa karshe, na sha gaya miki akwai sa hannun wani a irin wadannan abubuwan dake faruwa tsakaninki da Baffa amma nq kusa gyara komai a gidan nan da yardar Allah, rayuwarmu ba zata cigaba da tafiya a haka ba.”
    Sai ta girgiza kanta.
    “Nima na sha gaya msaka cewa ka daina irin wannan tunanin Jamal, ka daina saka zargi a zuciyarka, wannan matsala ce dake faruwa a kowanne irin aure ba wai wani abu ba, duk sanda kayi naka zaka fahimta kaima. Amma babu ruwan kowa a wannan al’amarin, kana gani dai ko Kilishi da muke kishoyoyi bata da matsalar komai to waye kuma zai saka mu a gaba? Akan me?”
    Ya zura hannunsa daya cikin gashin kansa.
    “Matsalar kenan Mimi, ba kya bari zuciyarki ta bude abinda yake kasan zuciyar mutane, shi yasa ba kya yarda dani a kodayaushe, amma insha Allah kwanan nan zan nuna miki wani abu da zaki san ba zargi nake yi ba Mimi, so nake kawai in tabbatar in dai ina raye komai ya kusa zuwa karshe insha Allahu.”
    Haka ya fada a lokacin, amma ita kallo sa kawai take yi tana son gaya masa cewa a wannan lokacin ba wannan ne fatanta ba, ba wannan ne buri ta ba, burinta bai wuce cewa yayi kokarin jawoata Ma’aruf zuwa kusa da ita ba, tana fatan hakan daga yadda take ganin alakarsu na tafiya, fon tun a wancan lokacin maganganun ƴ ƴanuwanta dun fara zama a zuciyarta, musamman a lokacin da Ma’aruf din ya kammala karatun secondry dinsa, tana ganin ma’anar kowacce kalma da suka sha fada mata game da alaƙarta da ɗan nata.
    Sai gashi kwata-kwata awannin da hakan ya faru basu karfin na kwana guda ba, yace in dai
    Ina raye… Kamar wani abu a lokacin na gaya masa cewar zai iya rasa ran nasa da wuri.
    Tana jin kukan su Shukra da sauran jama’ar gidan daga wajen falon, tana jin tashin kukan kowanne a cikinsu yayin da mazan dake wurin ke ƙoƙarin basu baki, don an hana kowa shigowa a wannan lokacin, Baffa yace babu wanda zai ga gawar a wannan yanayin sai an shirya shi tukunna, itama ta shigo ne don ita mahaifiyarsa ce, babu wanda zai iya kallon idonta yace ba zata ganshi ba.
    Idanunta na kallon gawar da tayi kaca-kaca da jini, kirjinsa ya dagargaje, ance bishiyar da suka daka shi ta soke don a saitinsa take, kuma har a yanzu ma akwai wasu kananun itacenta da suka hade da jikinsa da aka kasa cire su, jini yana malalowa a hankali har yanzu daga jikin gawar yana jika kayanta a lokacin, don tana tsugunne a gabansa, sanye da wani tsadadden leshinta da tayi shirin zuwa biki dashi a ranar.
    Tana jin yadda danshin jinin nan ke jiƙa kayanta, yana gaya mata cewa jinin Jamal ne, ɗanta guda na farko a duniya, ɗan dake mutukar sonta fiye da komai a duniya, ɗan da tun yana karaminsa zuciyarta ke cin buri akansa, wannan kyakkyawan Jamal ɗin da kowa ke yabawa, kyakkyawan ɗan da take alfahari dashi a kowacce, a yanzu vabu wannan kyan, babu kamanninsa ma ko kadan, dogon hancinsa ne kawai ake iya ganewa a cikin kumburar da fuskarsa tayi ba. A cikin kunnenta muryarsa kawai take ji yana ce mata…
    _Zafi nake jin Mimi, ko’ina a jikina ciwo yake yi…_
    Haka yake ce mata duk lokacin da bashi da lafiya a makaranta idan suka yi waya.
    “Limamin ya iso.”
    Taji wani a cikin mazan dake bayanta yana faɗa, sannan taji muryar Baba Usman yana cewa.
    “An kira waya yanzu, ance an shiga da Ma’aruf din tiyata, likitocin sun ce anyi sa’a babu internal bleeding.”
    Sannan taji wani a cikin mutanen na tambayar su waye a wajensa.
    “Mami ta tafi tun dazu.”
    Amsar da ta fito daga bakin wani, itace a amsar da tun a wannan lokacin ta bawa Hajiya Maimuna wani tabbaci na cewar shikenan tayi biyu babu…. babu Jamal ɗin kuma babu Ma’aruf din! Don bata jin bayan addu’a tana da wani sauran fata a duniyar nan na dawowar Ma’aruf wajenta.
    ***
    *Present Day.*
    Tun da Munaya ta shigo tace da Hajiya Maimuna wai Ma’aruf ne ke zaune a falo yana jiranta hannayenta ke rawa wajen shiryawa, karfe goma sha ɗaya na safiya a lokacin sai kallon agogo take tana karawa.
    A tarin shekarun da lissafinta ba zai iya ta tancewa ba, ta manta yaushe rabon da ta sanya idanunta a cikin na Ma’aruf din a wannan lokacin, iyakarta dashi bayan tsawon wasu kwanaki ne da zai shigo ya gaishe ta kawai, zuciyarta ta daɗe da haƙura dashi game da wasu abubuwa da ta san cewar hakan ne ya kamata, ta dade da ɗaga kasan ruhinta ta binne dukkan wasu al’amuransa, shi yasa har a yanzu dukkan maganganun ƴanuwanta game da hakan basa damunta sosai.
    Sai dai duk da dauriyarta, ta sani cewa bata isa ta canja cewar ita uwa ce ba, bata isa ta daure wannan kewar da zuciyarta ke ciki shekara da shekaru game dashi ba. Basu saba ba, ɗawainiyarsa kaɗan ta sani, abinda take gayawa kanta kenan a kullum wajen tausar kanta, amma ta sani cewar babu wani abu a duniyar nan da zai yi daidai da dawainiyar rainon cikinsa da kuma haihuwar sa da tayi, shi yasa har abada a duniya uwa ɗaya ce, kuma babu girman wani abu da ya isa ya canja matsayinta.
    A zaune a falon kuwa ta same shi baysn ta fito, hannunsa rike da wani dan karamin kwano mai kyau, yayin da idonsa ke manne da Tvn dake nuna tashar CNN.
    Ya juyo ya kalle ta daidai lokacin da ta karaso hannunta yana danna buttun ɗin tsayawa jikin keken tayar.
    “Barka da safiya.”
    Muryarsa ta gaishe ta ba tare da wata inkiya ba kamar yadda yake yi kullum, kuma a wannan lokacin dai taji hakan bai dame ta ba kamar yadda take ji a baya, ganinsa kadai a wannan lokacin ma ya isa ya mamaye dukkan tarin abubuwan da take lissafawa a kansa.
    “Barkanmu dai, kun tashi lafiya?”
    Ta amsa farin cikin dake zuciyarta na nunawa akan fuskarta.
    “Lafiya kalau, ya ƙarfin jiki?”
    “Alhamdulilhi mun gode Allah.”
    Har yanzu idanunsa na ƙasa bai dago ya kalle ta ba, kuma tayi zaton iya abinda zaice kenan kamar yadda suka saba a kodayaushe, amma sai kawai taga ya dago ya kalle ta sannan yace.
    “Kwanaki Baffa yace mun Abdurrahim ya kusa dawowa ko?”
    Ba shiri ta daga kanta da murmushi.
    “Eh, nan da sati biyu insha Allah.”
    “Ashe har ya tsayar da rana, the last time da muka yi magana yace mun bai saka rana ba tukunna.”
    Mamaki ya shiga cinye ta a yadda take zaune, amma sai ta daure tace
    “Yanzu ya kammala komai ai, don ma baya son taro ne amma ni da nayi niyyar wasu suje masa convocation din.”
    Sai ya gyada kansa.
    “Haka yace mun nima, har Ishaq ma ya tambaye shi amma sai yace masa wai ba wani abu za’ayi ba.”
    Ta sake yin murmushi.
    “Rigimarsa tafi shi ai, nace masa ko kewar mu baya yi.”
    Shima murmushin yayi ba tare da ya sake magana ba, yana tausayin kannin nasa ya sani, duk sanda suke magana ta hanyar text idan ya tuna cewar ba zai taba iya kiransa ba yana jin wani iri a ransa. Wani iri kamar yadda yake ji a yanzu da yake zaune gaban mahaifiyar tasa yana hira da ita, hirar da ba zai iya tara shekarun da aka rufa kafin ta iya tuna lokaci na karshe da suka zauna irin haka ba.
    Kai tsaye yaji wani ɓangare na zuciyarsa ya shiga godewa Amina da tayi sanadin zuwan nasa, don yadda ta kalli idanunsa ta roƙe shi da Allah ya san ba zai taba iya kin ce mata A’a ba.
    Kuma a wannan lokacin ba kallon Hajiya Maimunan yake yi ba amma sai jikinsa ya bashi cewa robar dake hannunsa take kallo, kuma yaji shigowar sako a cikin wayar dake aljihunsa, ya san Faruq ne, shi yake jiransa don haduwarsu da Yakubu (mutumin da zasu tura nemo musu Mr. Okafor.)
    Don haka sai yayi saurin tasowa ya miko mata robar dake hannun nasa.
    “Wai zogale ne na bayan gidan ta tsinko ta dafa shine tace in kawo miki Munaya tace mata kina so.”
    Yadda shiru ke ratsawa waje a lokaci guda ya kashe ƙarar komai haka Hajiya Maimuna taji a cikin kanta lokacin da ta karbi robar, kalaman suka shiga cikin kanta amma suka tsaya cak! Ta riga ta fahimci wa yaje nufi da itan ba sai ya fassara ba, amma hakan wani abu ne da bata taba tunanin faruwarsa a cikin lissafinta ba.
    Ta kalli robar ta sake kallonta, ba wani abu ne mai yawa ba, amma wannan lokacin tana jin kamar nauyin zogalen nan daje ciki yafi girman dukkan wata kadara da take shi, kwalla ta cika ramin idanunta a lokaci guda, don haka bata ɗago ba sai kawai ta daga kanta a hankali.
    “Nagode sosai, Allah ya saka da alkhairi Ma’aruf, Allah ya ƙara haɗa kanku, Allah ya baku zaman lafiya, ya kade dukkan sharrin da zai shiga tsakaninku, Allah ya baku zuri’a dayyiba.”
    Mami tasha yi masa addu’a, kala-kala ma, har da wadanda idan ta fada zai kara kallontasau biyu kafin ya amsa, amma Allah ya sani ya dade baiji addu’ar da ta shiga har cikin zuciyarsa ta tabo wani abu da bai san da zamansa ba irin wannan. Kalaman Mami daban ne da irin wadannan, yawanci addu’arta tana tsayawa akansa ne kadai babu wani a gefe da ya shafe shi, don haka tmya sani tun bayan lokacin daurin aure sa da Baffa da kuma Baba Usman suka yi musu makamanciyar wannan addu’ar, zai lissafa wannan a karo na biyu da yaji irin wannan addu’ar daga bakin wani.
    Makogwaronsa ya bushe a lokaci guda, amma yayi kokarin hadiyr wani abu a hankali kafin ya amsa sannan ya tsugunnna yana yi mata sallama, bai kara iya kallonta ba itama kuma baya jin ta sake kallon nasa, don wataƙila suna raba abu iri ɗaya ne a zuciyarsu daga shi har itan.
    Kuma karo na farko a wannan ranar bayan ya shiga wajen Hajiya Kilishi yaji haka kurum baya son dadewa don ransa bai gana daidaita ba har a lokacin, yaji hirar da take yi masa ba fahimta yake yi sosai ba, don haka yayi mata sallama ya fito, sai dai kafin ya bar cikin dakinsai da yayi mata wata tambaya dake yawo a cikin kansa tun bayan lokacin sa Amina ta bashi robar zogalen nan.
    “Mami kina son zogale kuwa?”
    Ta kalle shi kamar tana son gano wani abun kafin tayi murmushi tace.
    “Haba ka manta ne Mai gaskiya, amma bana son zogale tun asali.”
    Sai ya gyaɗa kansa kawai sannan ya ƙara yi mata sallama.
    _”Dan Allah zaka miƙawa Hajiya wannan? Zogale ne na bayan gidan nan tsinko na dafa, Munaya tace min Hajiya tana so, amma Mami ita bai dame ta ba.”_
    Haka ta gaya masa lokacin da ta tsaya a gabansa rike da robar tana ta juya ta a hannunta. Wani abu ne ya faru smdashi bai gama gabe masa ba har yanzu, ya san dai kawai ba laifi suka yiwa Mamin ba amma kuma duk da haka yana jin wani iri.
    Ya zaro wayarsa ya duba bayan ya shiga mota, sakon da ya shigo dazu ba daga Faruk bane, daga mutane kamfanin RTL ne da suka yi dasu akan cewar gobe zasu je shi da wasu daga cikin board trustees ɗinsu su karbo kudin da suka siya dilolin kaya a hannunsu, haka kurum wanna karon ya yanke shawar cewa baza su karbi kudi ta account ba gwara su karbi cash kawai, tunda an cuce su wancan karon kuma har yanzu basu gama da gano matsalar ba.
    Sakon yana bayani ne kan wajen da zasu hadun da kuma lokaci da sauran abubuwa, ya kashe wayar ya tada motar daidai lokacin da kiran Faruk ke shigowa, ya san ya riga shi isa wajen kenan kuma yanzu zai dame shi, don haka ya danna motar ya nufi hanyar titi daidai lokacin da idonsa ya kai kan robar zobo mai sanyin da Amina ta ajiye masa daga kasan dashboard din motar wajen da akayi musamman don ajiye roba dama.
    Babu shiri wani murmushi ya subuce a bakinsa, yana da plan dama tarin tsaruka na ydda zai saita rayuwarsa tare da yarinyar nan, don tabbas ya gama yarda cewa ita din alkhairi ce a rayuwarsa, kuma mafi dadin abin shine ya same ta ne a lokacin da ba nema yake ba.
    Wani abu da alokacin bai sani ba shine kwance a cikin zobon nan, sinadirin kwayoyin maganin Hajiya Kilishi ne ke yawo tun daga sama har kasa.
    ****
    *Abuja.*
    *No. 1146 C west, Maitama.*
    A cikin ƙaton falon, baka jin komai sai ƙarar A.cn dake hurawa ta kowanne bangare na falon, akwai manya-manyan royal chairs set uku da aka rarraba falon zuwa waje uku dasu. Jawad yana zaune daga kujerun gefe masu kalar ruwan madara, gajeran wando ne a jikinsa kuma wata t-shirt kalar ruwan kasa, a gabansa wani tebur ne da aka cima da kayan abincin safiya, hannunsa na rike da kofin mug yana kuɓar shayin ciki yayin da mahaifiyarsa dake gefe Hajiya Mardiyya ke kallonsa tana sake maimaita maganganun da ba jinsu yake yi ba.
    “Yanzu Babana ko don wadannan makiran matan mahaifin naka ba zaka saurare ni ko sau daya a rayuwarka ba? Kana ganin irin banbancin da ake nuna mana a gidan nan, kuma da nayi magana sai kace dani ba zaka yi ba babu kyau, bayan shi kansa mahaifin naku ai ya san abinda su Suraj din ke yi, kawai bai damu bane kuma yana sane yake barinsu. Kowa na diban kason sa amma kai so kake mu mu tashi a tutar babu? Ba don ma Perm Sec. ya shiga zancen mahaifin naku ba kai ka sani da yanzu bama kan wannan kujerar.
    Wallahi idan na shiga lissafo maka kadarorin da matan nan suka tara yanzu zaka rike baki Jawad, amma ni gida uku fa kawai nake dashi har yanzu, ba don nayi fafutuka ta ma ba da bana jin ina da ko daya ai, kai kuwa banda motarka bana jin ka tara wani abu, karfi da yaji ka maida mu talakawa alhali muna iyo a cikin kudi Jawad?”
    Ya lumshe idanunsa a hankali lokacin da ta kai karshe sannan ya juyo ya kalle ta.
    “Mamah amsata ba zata canja ba kema kin sani,abinda nake gaya miki kullum shi zan kara gaya miki a yanzu, ba zan saci kudin mahaifina ba ba zan dauki abinda ba nawa ba, shi yasa nake aiki kin sani, su sauran matan nasa da yayansu ke zuwa su debo musu ai basu suka saka su a gaba suka roke su ba, kowa ganin damarsa ce tasa shi yin hakan, don haka me yasa ni zaki takura min, ba ga su Khairat nan ba? ( Kannensa mata biyu) Ki koya musu wata hanyar da zasu samo miki mana, ai ba maza ne kadai suka iya samowa ba.”
    Ya ajiye kofin hannunsa sannan ya mike tsaye, sannan yace
    “Zanyi bako anjima, Dan Allah Mamah ki sa ayi mana abinci, wadannan duk basu yi min ba.”
    Ya fada yana nufin tarin cimar dake kan teburin daya tsallake, kuma bai jira abinda zata ce ba yayi gaba, ya zaro wayarsa ya kira Haron da suka yi akan lallai ya shigo Abujan don ta nan ne zasu hau jirgi zuwa Kano, ya gaya masa shi ba zai yi tafiyar mota ba.
    Kuma awa guda bayan hakan sai gashi ya iso, suka zauna daga falon kasa na ɓangarensu yayin da Haron ke ta mita akan tason shi da yayi babu shiri.
    “Kaifa kake bukatar abin nan J, amma ni ka takurawa na taho rana tsaka, ina ga dole mu maida harkar nan ma taciniki don na fahimci ni zan sha wuya a banza.”
    “Ko nawa ne ka san zan biya ka, I never regret anything indai akan Rukayya ne ka sani.”
    Haron ya kalle shi lokacin da ya tsiyaya wani lemo mai sanyi a daya daga cikin tambulan ɗin da aka kawo musu sannan yace.
    “Shi yasa ni kuma nake iya kokarina don inga na ciro ka daga wannan masifar, Haba ka kalli fa inda kake rayuwa, ni ban ma san kun canja wannan gidan ba, amma ka kallafa ranka akan wannan shashashar yarinyar, in the first place ni ban san ma me yasa zaka neme ta ba idan har ka san aurenta zaka yi.”
    Jawad ya gyada kansa alamun ya fahimta yana kallonsa sannan yace.
    “Ina ga duk mun wuce wannan stage din Haro, mun karaso wajen da kace zaka taimake ni, ni kuma nake jiran inji ta hanyar da zaka taimake ni din.”
    Cike da takaici Haron yana kallonsa kafin ya buɗe briefcase din da yazo da ita a gefensa sannan ya zaro wasu hotuna guda uku ya miko masa, ba tare da bata lokaci ba kuwa Hawad yasa hannu ya karba.
    Hotunan mutum daya ne a mabanbantan llokuta har guda uku, na farko kamar ranar daurin aure ne, don a cikin jama’a yake sanye kuma da kaya masu babbar riga, na biyu kamar hoton wajen aiki ne, yana sanye da suit da kuma sumar gashinsa wadda aka gyara cikin wani style mai kyau, sai na karshe a bakin titi ne yana waya, hoton yayi kama da cewar a boye aka dauke shi sosai.
    Kuma ba sai Haron ya sake yi masa bayani ba, ya riga ya fahimci waye tun da wuri, don idan zai iya tunawa ma ya tabacganinsa sau daya a wani taron harkar kasuwanci da ya halarta shekara guda baya, idonsa ya manne akan fuskar sa yana son ya gano banbancin dake tsakaninsa dashi, wannan banbancin da yasa Rukayya ta juya masa baya, banbancin da yasa ta rufe idanunta akan tarin kyautatawar da yayi wa rayuwarta ta kasa ganin kokarinsa, ko ma rabewar da zuciyarsa ke yi a lokacin da take gaya masa cewa bata dauke shi komai ba face abin wasa kawai, abin wasanta!
    “Na gama samun duk wani background information akan gayen, ashe har aure ma ya sake yi…”
    “What?”
    A lokaci guda ya katse Haron da ke kokarin fara bayaninsa. Fuskarsa na kallonsa da tsananin mamakin da ya kasa tantance daga ina yake fitowa yana shiga jikinsa.
    “Yes, ya sake aure ƴan kwanakin bayan nan, amma naji ance kamar bashi matar kawai akayi don tare akayi auren dana sauran yanuwansa.”
    Sai kawai ya gyada kansa a hankali ba tare da ya san me zai ce ba, hakan yasa Haron ya cigaba da maganarsa.
    “Ka san ni bana sanya a al’amarina, so na samu labari ance min zai hadu da wasu mutane gobe, na samu details ɗin da komai daga bangarensu, so kawai zamu yi masa aiki ne a lokacin.”
    Jawad ya dago ya kalle shi.”
    “Aiki? Wane irin aiki?”
    “Plan dina shine mu kama shi for now, kar ka tambaye ni me zai faru bayan nan, mu fara gama wannan din tukunna.”
    Jawad ya kalle shi tsawo sakanni biyu.
    “Ba zan tambaye ka ba, amma ka sani cewa I wont sign for any shit, idan har kashe shi ne plan dinka…”
    “Wa yake maganar kisa anan J? biyu babu muka ce zamu sa yarinyar nan tayi, you want to make her pay ko ba haka ba? Then we are just going to make her pay kamar yadda kake so, ka yadda dani kawai.”
    Jawad ya sake kallonsa na wani lokaci kafin ya gyaɗa kansa.
    “To meye plan din?”
    “Ba ma zamu bari ya isa wajen mutanen da zai hadu dasu ba, kafin ya isa za’a tare shi kawai sannan a juyo da motar, yaran da nasa sun nemo titin da komai har ma da daidai wajen da zasu tsaida shi din, shi yasa nace maka dole mu bar Abuja yau.”
    Jawad ya gyada kansa alamun ya fahimta.
    “Idan har babu zancen kisa a al’amarin nan, I think hakan yayi daidai.”
    Haro ya girgiza kansa.
    “Wannan gayen ba irin mutanen da za’a kashe su maganar ta wuce kamar iska bane J, daga shi har mahaifinsa suna da tarin connections din da ban san iyakarsu ba, don haka wasa kawai zamu yi dashi mu cimma manufarmu.”
    Kalaman ƙarshe suka tafi kai tsaye cikin zuciyar Jawad suka yi masauki.
    Wasa kawai zasu yi dashi, wasa… Ya cije lebbensa na kasa yana sake maimaita kalmar a ransa. Yanzu yake ji cewa da gaske Haro ya dauko hanyar cimma manufarsu, tunda har zsi bashi damar da zai nunawa Rukayya cewa mutumin da take wa kallon duniyarta, take wulankanta shi akansa shima bai fi karfin ya zama abin wasan a wajen sa ba.
    Yana jin Haron na kokarin yi musu booking jirgin da zai tashi zuwa Kano lojacin da ya miƙe don zuwa dakinsa ya fara shiri, a lokacin ne kuma yaci karo da ita, wannan yarinyar, wannan yarinyar da ya ƙi jinin ganinta, 6ar aikin mahaifiyarsa, tana tsaye daga koridon dake jikin falon haunnuta rike da wani katon faranti da ta shako kayan abinci dasu, kuma ba sai tace komai ba, rawar da hannayenta keyi tare da kwanukan abincin shine abinda kai tsaye ya shaida masa cewa tsaf taji dukkanin shirinsu!
    ***
    Karo na ba adadi Amina ta kalli agogon dakin, zuciyarta ta kara yin nauyi a kirjinta, rawar hannayenta ya karu, amma sai tayi saurin danne hakan ta hanyar daukan wani ƙaton mangwaro dake gabanta.
    A bangaren Inna Danejo suke wadda bayan fitar Ma’aruf Samirah tazo ta gaya mata isowarta don haka ta ƙulle gidan suka taho tare, inda ta tadda dukkan sauran jama’ar gidan kowa yazo don saukarta.
    Kuma ba’a dade ba aka shiga hayaniyar rabon tsaraba kamar yadda ta fahimci ana yi duk sanda Inna Danejon tayi tafiya ta dawo, su Msma Rabi dama wasu da bata san su waye ba sun zo ana ta faman kwance tsaraba kala-kala, Samirah ce ke gaya mata cewa in dai Inna Danejo taje Bakori to ba gidan kadai ba, tun daga farkon layinsu har karshe kowanne gida sai an kai masa tsarabarsu, abubuwa ne kala-kala har da wanda ita bata taba gani ba ma sai faman rarrabawa ake yi bisa umarnin da Inns Danejon ke bayarwa.
    Kusan ita dasu Mama Rabi ne ma ke ta aikin don Samirah ita nata na amfanin gida kawai take ta warewa, tana yi suna fadansu ita da Inna Danejon akan cewar tana diban komai da yawa, Munaya kuma tsince-tsincen duk abinda ta san zata iya ci take yayin da Surayya ke ta aikin danna wayarta taje ta nanike a jikin Inna Danejon dake ta nan-nan da ita, wanda sai a lokacin Amina take jin wai sunan maman Inna Danejon aka saka mata, shi yasa duk gidan tafi shiri da ita akan kowa.
    A lokacin ne kuma Samirah ke gaya mata cewar gobe Amaren da akayi bikinsu tare zasu zo, don haka duk tarin taraddadin dake zuciyarta, sai taji itama tana murna da zuwan nasu, don aƙalla koyaushe tana jin hirarsu kala-kala a bakin su Samiran.
    Ta cakuda hannayenta duka biyu waje daya lokacin da Mama Rabi ta karbi aikin da take yi tace taje ta huta, Inna Danejonnkuma ta miko mata wata damammiyar fura mai gardi a cikin roba tana yi mata nata sannun itama, kuma duk da yadda take murmushi akan fuskarta hakan bai ƙarasa har cikin zuciyarta ba, don bai isa ya kore halin da zuciyarta ke ciki ba.
    Ta samowa kanta mafita ta sani sai dai duk da hakan mafitar bata canja daga umarnin Amma ba don ba zata taɓa iya kin bin maganganunta ba, itace gatanta ta sani kamar yadda ta san maganganunta sune fitilar da zasuvgitar da ita daga duhunnda taje ciki, don haka a dole ta tsamo kanta daga rudanin zuciyarta ta yanke hukuncin aiwatar da umarnin Amma tare kuma da samawa kanta mafitar da take ganin zata jefi tsuntsu biyu ne da dutse daya.
    Zata yi abinda Amma tace, zata aikata umarnin Kilishi ta hanyar samun gaskiya da kuma yardarta, sannan zata yi jinyar Ma’aruf ta hanyar da hakan zai ƙara shaƙuwa tsakaninsu, a yanzu zuciyarta ta riga ta karɓe shi da dukkan iyawarta, don haka zata ajiye komai a gefe ta gyara rayuwarsu kamar yadda ya roƙe ta, kamar yadda yake so… Idan tayi hakan ta san zata samu sauƙi a zuciyarta na ganin laifi da kuma rashin kyautawarta.
    Hannayenta suka kara rawa lokacin da ta tuno yadda suka kasance dazu da safe, dama abinda ya rada a kunnenta kafin ya fita bayan tambaya karbi robar zogalen nan.
    _You are really making me insane, and I like it…_
    Tana iya tuna yadda wasu abubuwa ke harbawa a cikin kanta wannan lokacin, dama yadda jikinta ya dinga rawa a cikin hanayensa kafin ya janye ta a hankali yana gaya mata cewar zai fita a cikin kunnuenta.
    Sai dab da magariba sosai sannan komai ya natsa, suka gama haɗa kan tsarabar nan tsaf, sannan ta samu tayi sallah, har kowa ya tafi sai ita kadai a bangaren Inna Danejon, don bata san me zata koma bangarensu a wannan lokacin tayi ita kadai ba, jira take amma bata san ma abinda take jira din ba, dawowar Ma’aruf ko kuma akasin sa??
    Kuma da misalin karfe bakwai da rabi daidai, sai dukkan wani tunaninta dama kokwanton ta yazo kan gaɓa, sannan fatanta dama duk wani tsarinta ya tafi daidai lokacin da kiran Hajiya Kilishi ya riske ta.
    Mama Rabi ce ta shigo ta gaya mata sakon, kuma bayan hakan bata ce komai ba don haka Inna Danejon ma bata yi wani tunanin komai tayi mata sallama ta fito tare da tata katywar ledar kayan tsarabar.
    A harabar gidan ta hango Mamin, tana tsaye a jikin motar ta kirar Camry yayin da Malam Sani direba ke ciki ya kunna motar, hasken gitulun danjojinta na haskawa ta kowanne gefe, tafiya kawai take yi har suka karasa tare da Mama Rabin dake fadin.
    “Hajiya ashe har kin fito.”
    Kuma Mamin bata amsa ba, sai ta kalli kayan hannun Aminan kawai sannan tace da Mama Rabin ta karba ta tafi dasu.
    Kwatanta yadda zuciyar Amina ke bugawa a kirjinta wannan lokacin wani abu ne da ba zai bayyanu ba, don kafafunta ma bata jinsu a jikinta kwata-kwata, yayin da jikinta yayi shafal kamar fallen takarda.
    “Amina…”
    Hajiya Kilishin ta kira ta cikin sautin muryarta da ya fito tar a shirun harabar compound din.
    Bata amsa ba don bata san me zata ce ba, tana kallonta ne kawai da dukkan taraddadin dake yawo akanta, kuma ga mamakinta kawai sai taga tayi wani irin murmushi mai fadi da ya tabo har cikin idanunta kafin ta fadi abinda ya tsayar da duk wani hargitsin kanta cak!
    “Ma’aruf yana asibiti, yanzu Ishaq ya kira ni yake shaida min!”
    Maganganun suka fito tar cikin muryarta, kuma bata jira komai ba sai ta miko mata wata takarda da sai a yanzu ta kula da ita a hannunta.
    “Ga nawa albishir din Amina, kamar yadda kema kika bani naki.”
    Bata san tsawon sakanni nawa ne suka wuce kafin ta ita sa hannu ta karbi takardar amna idonta da kwakwalwar ta basa gane ko meye a jiki balle har ta kai ga fahimta, kuma abinda Mamin ta gane kenan saboda haka tace.
    “Appointment ne na wani asibiti a Indiya, za’a kai Aminu a gyara masa kafafunsa, na biya komai, saura shi da mai raka shi su fara fafutukar visa.”
    Ta fadi hakan sannan ta yi shiru tana kallon yadda hannun Aminan ke rawa tare da takardar, sai kawai ta sake wani murmushin sannan tace.
    “Me na gaya miki ne Amina? Komai mai sauki ne umarni na kawai zaki bi, shikenan sai in mayar miki da duniyarki kamar aljanna.”
    Abinda bata sani ba shine a wannan lokacin Amina ba jinta take yi ba, kwata-kwata bata saurarar abinda take fada take yi ba, maganganun Amma mahaifiyarta ne kawai ke yawo akanta.
    _”… A tafin hannunki zaki dora Kilishi Amina, a tafin hannunki zaki dinga juya ta ba tare da ta sani ba, duk abinda kike so har ma da wanda baki roka ba zata yi, da kanta zaki sa tayi ta haƙa ramin binne kanta har sai yayi zurfin da zai rufe ta!”_
    ***
    _Me ya faru da Ma’aruf?_
    _Kun fahimci cewa mun fara wasa da hankalin Kilishi?_
    _Kun fahimci kudirin Amina?_
    _Kun fahimci inda rayuwarsu ke shirin kaimu?_
    _Me zai faru game da tsarin su Jawad?_
    _Me ke shirin faruwa da Zainab? ( Ƴar aikin gidan su Jawad.)_
    _Allah yasa baku manta da Hameda da kuma mamanta Rukayya ba… Suna nan tafe._
    MASU ƁUKATAR A TALLATA MUSU HAJOJINSU ZA SU IYA TUNTUƁARMU TA LAMBOBIN 07045308523 MUN GODE

    Note
    error: Content is protected !!