Duniya ta – Chapter Two
by NadminWai me ya sa mutane ba sa son talaka ne? Har bahaushe ma kan ce wai “talaka ba aboki ba, ko kun shirya ranar biki kwa bata” Irin tunane tunanen da Hindatu ke yi kenen a wata safiyar Laraba. Ta san an ce wai Laraba ranar sa’a ce, to amma sai ta yi wa wannan Larabar taken ranar bakin ciki, ranar ban haushi.
Matsalarta a yanzu bata wuce biyu ba;ta tashi ba ta maganin komai sai naira hamsin! kuma ta wayi gari jinjirinta wanda yayi kwana 40 a duniya yana fama da zazzabi da mura, ciwon da ya kamata ta kai shi asibiti. ‘Ya’yanta biyu Abba da Asiya su suka tsira mata ido suna ma ta kallon gasasshen balangu don yunwar da ke azalzalarsu.
Abba dan shekara shida shi ne mai wayo cikinsu ya ce
“Mama, in yi gudu in je in siyo kosan”?
ta yi sauri ta kawar da idon ta daga kan sa, tausayi yake ba ta. Hamsin din dai ita ta ci wa buri tayi kudin mota ta kai jinjirinta asibitin Murtala tunda ba a biyan kudin kati, idan ya so in aka rubuta magani ta karba a wajen Danladi mai kemis na unguwarsu baga baya ta biya shi a hankali. To amma ya za ayi ta bar yara da yunwa?
Da wannan tunanin da zaro kudin ta ba shi ta ce “yi maza ka je wajen karama ka siyo kosan ashirin ka ce ma ta in ji ni..kar fa ka tsaya wasa” ya fice a guje kafin ta karasa. Ya dawo ya bata canjin suka hau kan dan tsurut din kosan suka cinye har da lashe lashen takarda. Ba ta bi ta kan su ba ta saba jinjirinta a baya agogon bango ya nuna karfe takwas na safe cif.
Ta dauki jinjirin da ta sawa suna muhammadu ba don ta yanka ma sa ragon suna ba ta saba a baya,jikinsa zafi rau! ta tarkato ragowar yaran suka yiwo waje. Ta rufo kofar gami da saqalo ta da wani kara ba don tsoron kar barawo ya shiga ya ma ta sata ba sai don cika ala’da. Ta zunkuda goyon bayanta da ke mutsu mutsu ta ce da Abba ta na nuna makotansu
” ku shiga gidan malam wajen Iyami ku ce nace ku zauna a wurinta zan je asibiti na dawo” ba ta bar gurin ba sai da ta ga shigar su.
Ta fara kissawa ranta irin tazarar da ke tsakanin unguwarsu hausawa da asibitin Murtala, sai ta yanke wata shawara. Za ta sabi tafiyar kafa zuwa dangi daga nan ta roki dan acaba ya dauketa zuwa asibiti a naira talatin, a dawowa kuma ta biya gidan mahaifiyarta da ke Kofar Wambai ta samu kudin mota. Da wannan shawarar ta fara tafiya. Gari ne na damina dan haka tsilli tsilin mutane ne akan titi saboda ruwan da aka maka da daddare. A cikin wannan tafiyar ne ta tafi dogon tunani.
*************************
Ita yar asalin haifaffiyar kano ce a wata unguwa da ake kira Kofar Wambai. Mahaifinta ya rasu tun tana karama inda mahifiyarta Hajiya Uwani mai zuciyar nema ta cigaba da kula da su har zuwa lokacin da hindatun ta kamala diplomarta a Health Technology da ke kano. Abubuwa sun fara cabewa ne lokacin da mahaifiyar ta su ta gamu da cutar ciwon ido ta “glaucoma” har ya zamana ta daina gani.
Fadi nan tashi nan Hindatu ta fara neman aiki da dan kwalin diplomarta amma abu ya ci tura. To bata san wani a sama ba,ba ta kuma san wani wanda ya san wani ba don haka maganar neman aiki ta rushe.
Abubakar wanda aka fi sani da Habu yana cikin masu neman aurenta kuma shi ya fi kwanta mata a rai. Soyayya aka yi irinta bugawa a jarida wacce in ba kai ba sai rijiya.
Habu ba mai kudi ba ne,rufin asiri gare shi yana aiki a wani kamfanin robobi da ke sharada a matsayin mataimakin manaja kuma yakan taimakawa su Hindatu. Aka yi biki aka kare aka kai amarya dakinta. Wani abu da ya fara daure ma ta kai bai wuce yanda zamantakewar ta da Habu take neman sauya zani ba. Shi din da ta sani a samartaka mai wasa da dariya sai ya zamana idan ta ji dariyarsa to kallon ball yake inda yan club din su suka yi sa’ar buga kwallo cikin ragar abokanan hamayyarsu.
Auren bai fi wata shida ba gabadaya zaman ya isheta. Dan taimakawa mahaifiyarta da yake ma duk ya watsar suka koma gidan jiya. Dama shi iyayena sun rasu a wajen kawunsa ya tashi,to su ma nan sai ya dade kafin ya je.
Sa’annan Hindatu ta fahimci abu guda daya, samun da yake yi yanzu ya karu wanda hakan ya sa masa girman kai . Ita tai ta san ba ta ji a wajensa ko wajen wani cewar an masa karin girma ba amma yanayin kashe kudinsa ya bala’in wuce na da. Ya sayi motarsa “volvo” ba dan ya isa saya ba yake buga abarsa yana shanawa a gari hindatu ba ta isa ta ce uffan ba!
Lokacin da ta haifi Abba kuwa ranar suna yaron irin shagalin da aka sha aka ci mutuncin nera sai da jikinta yayi sanyi. Ta lura yanayin abokansa yanzu duk wadanda suka fi karfinsa ne ta yanda in ta lura da motocinsu da siturunsu. Abin tambaya anan shi ne ina Habu ya samu kudaden da yake facaka da su wanda daga gani sun fi karfin albashinsa?
Ranar dai ta kasa hakuri ta tambaye shi ya yi mata mugun kallo ya ce cikin gatsali
“fashi da makami nake”
ya mayar da kan sa kan akwatin talabijin. Ba ta daddara ba
ta ce ” wannan rayuwar da ka daukar mana ba fa za ta kaimu koina ba. Ko ba ka gayamin inda kake samun kudi ba na san da haram a ciki ina ji maka tsoro ranar da zata tashi da mu”.
“Ta tashi da ke dai uwar mugun fata”!
Ya fada yana kumfar baki,sanna ya nunota da dan ali
“ke na ga fa kwanan nan kina kawomin raini. Idan hawainiyarki ba ta kiyayi rama ta ba to ungulu za tayi saurin komawa gidanta na tsamiya. To ma ina ruwanki da al’amarina? Biyayyar da aka ce ki yi kenen? Kina tuhumar mijinki..a irin haka shi ya sa mata ku ka yi yawa a wutar jahannama!”
Jikinta yayi sanyi ta ce
” Daga shawara? Gyara kayanka ai ba ya zama sauke mu raba. Ka ari wadansu halaye ka ratayawa kan ka. Duk me ba ka shawara wallahi ba masoyinka ba ne,ka nemi masoyinka tun wuri!”
Ya zuba ma ta ido kamar wanda zai mayar ma ta..sai kuma ya buga shaddarsa mai sitati ya shuri takalmansa ya kara gaba. Wannan kenen.
Ba ayi sati da wannan maganar ba rigima ta tashi asiri ya tonu inda aka kama Habu dumu dumu da satar kudin kamfani hade da manajan kamfanin. Masu kamfani ba sani ba sabo suka miqa su gaban kuliya manta sabo. ‘Yar motar da Habun ke fafa da ita aka sayar aka hada da gidan da suke ciki na gado, Hindatu ta hada da gadonta da ‘yan kujerunta aka hada aka kwato shi da kyar!
Ragowar kudin hannunta ne ta kama musu hayar wani dan tsurut din gida mai ciki da falo da ‘yar rumfa ta kuma ja jari tana yan kulle kulle na su gishiri,maggi da sauransu. Ya zo ya koma ba ko sisi,ba aikin yi sai buga buga duk abunda ya ganganda ya samo ya kawo ma ta ta hada da na ta a rufa asiri.
Aka cigaba da gurgura rayuwar a haka tana samun ciniki sosai har ta sayi gadonta na fameka a wajen wata dillaliya a unguwar ta kuma sayi shimfidediyar tabarma ta shimfida a falo. Ta dauki Naira dubu biyu ta bawa Habu ta ce ya kafa tireda a kofar gidan ko sa dan dunga rage wani abun. Da ya karbi kudin washegari sai ganinsa tayi da katuwar rediyo mai manya manyan sifiku ya zo ya kima mata a falo,ya zuba mata manyan batira yana sauraren labaran duniya. Har ma ya kan ce
” Au har mutum zai iya zama bai ji labarin abinda duniya ke ciki ba? Idan mutum fa ya saki jiki a haka a haka arzikinsa zai zo ya wuce bai sani ba!”
Ido bai fara raina fata ba sai da shekara ta zagayo mai gida ya fara batun kudin haya har ma ya bayarda notis Habu ya dubi Hindatu ya ce
” kam bala’i wallahi tallahi talaucin nan ya isheni. Wai kasar nan ina za ta da mu ne? kullum cikin babu muke.
Muna nema kamar ba ma yi gwamnati ta bi dukiya ta handame mu talakawa an bar mu da hamma. Kyaun kasar nan a rushe wani abu wai shi gwamnati,a raba kudin kasar gabadaya kowa ya dau kason sa in ya so kowa tashi ta fisshe shi.”
Duk wannan maganar da yake yi Hindatu na talgen tuwo bata juya ba mamaki ya gama mamaye ma ta zuciya tana jinjina maganganunsa. Ai gwamnatin kowa tana farawa ne daga kan sa shi yanzu gwamnatin ya shiga har ya samu ya handame dukiyar kamfani? Shi ya fara yiwa kan sa fada mana. Ba irinsa irinsa ba ne a gwamnatin suke handame dukiyar kasa? Lallai laifi tudu. Ta share korafinsa don ta san tana magana cibi zai zama qari ta ce
“to yanzu ya za ayi game da kudin hayar?”
Ya watsa hannayensa a iska ya ce
“yo ni me kuwa zan yi? Kur’anin Allah da naira ashirin na tashi,shekaruna kike so na cire na biya kudin hayar da su?”
A sanyaye ta ce
“wai da tunani na ko zaka je gurin kawunka” ya ja tsaki ya ce
” kawun da nayi wata bakwai rabon da ko gaishe shi na je?ai ina tsammanin idan bai kira ubana na kabari ya zaga ba to kuwa ba zai dauki kwandalarsa ya bani ba”
Ya cigaba da sauraren rediyonsa yana shan iskar karkashin bishiyar dalbejiya. Da sauke tuwonta ta sabi mayafi ta tafi gidan Hanne uwar adashe bayan dogon roko ta samu aka bata daukan watan. Da dan cinikinta na cikin gida ta hada aka biya kudin hayar wannan shekarar. Wannan ta wuce.
Hindatu ta kuma dagewa da sana’arta har ma ta soma yin lamurje da kunun zaki ana siyo ma ta kankara a zoo road tana dorawa tunda ba ta da firji. Akwai wani Mai kudi a unguwarsu ta je ta roki matarsa da ta taimaka ta sa baki wajen maigidan a bawa Habu aikin shara da ban ruwan fulawa sai ake biyansa wata wata.Aikin ya samu cikon ikon Allah shi ma ya karba ya yarda zai yi. Idan ya dawo maganganunsa ba sa wuce
” kin kuwa san tazara tsakanin mai kudi da talaka kamar tazara ce dake tsakanin sammai da kassai? Ai ma su abun suna shanawa! Dan arzikin namu sun hada sun tura bankunansu na kasashen waje daga su sai matansu da ‘ya’yansu. Mai kudi bai san zafi ba saboda yana cikin “ac” bai san sanyi ba saboda yana cikin “heater”. Ke idan kasar ta ishe su sai su kwashi iyalansu su tafi ingila ko amurka ko saudiyya. Su je su roki Allah ya yafe masa zunubansu. Shin wai ba kya ganin kamar sun fi kusanci da Allah? Kamar dan su aka halicci duniyar? Kamar za su ri ga mu shiga aljanna??
Ta yi sauri ta ce
” Auzubillahi.. wai so ka ke kayi sabo? Ai babu wani makusanci da Allah sai wanda ya fi bauta ma sa. Wai ya ka ke nema ka yarda imaninka?”
Jikinsa yayi sanyi ya ce
“kuma fa haka ne ,banbancin kawai daular. Don ke kan ki kin san kudi su ne jin dadin rayuwa su ne kumbar susa wanda ba shi da su ya zama sorry! Dubi dazu dazun nan Hajiya ta miko min ragowar abincin Alhaji wallahi da na bude kwanon miyar kin ga nama zuqu zuqu? Na rantse miki da Allah yadda kika san yana aurar da diya wai a haka ci yayi ya rage”
Hindatu ta kwashe da dariya shi ma kuma ya biye ma ta suka yi tare har yana karawa da
“wallahi”
Ta ce ” kuma shi ne ka kasa ragomin”?
Yayi ma ta hararar wasa ta nuni da yau yana cikin nishadi ya ce
“Inaa… ai anan na sude na lashe ban bar ko dan kankani ba don kar ma ‘yan wanke wanke su samu sudi”
Canje canje sun fara aukuwa ne bayan ta haifi ‘yar ta Asiya da shekara daya lokacin ne Alhaji ya kori Habu daga aiki saboda rashin bawa aikin muhimmanci. A kuma lokacin ne hindatu ta zo ma sa da wani zance da yayi wa laqabi da zancen banza marar dadin sauraro , wai tana dauke da ciki. Cikin da ya zo ma ta da masifar laulayin da ko sana’ar ta bata iya yi. Cikin jikinta na da wata bakwai ta wayi gari da wani mummunan alamari na ban mamaki na an nemi Habu ko sama ko kasa an rasa. Aka shiga cigiyarsa gidajen rediyo da unguwanni amma ba labari.
Hankalinta ya fi raja’a akan ‘yan mafiya ne suka sace shi ,amma kuma ba ta karyata tunaninta ba sai da aka yi kwana bakwai da batansa.
Daidai matsatsin yaloluwar katifarta da gadonta ta tsinci wata takarda mai jimla biyu. Ga abunda ta kunsa
“Ni Habu na saki matata Hindatu saki daya,domin bazan iya jure zama da ita a halin talauci ba. Kar da ta neme ni don baza ta ganni ba.”
Yan hanjinta ta ji sun murda dan cikinta kamar zai hudo ya fito. Sai ta ji kamar numfashinta zai dauke hawaye wani na riga wani a fuskarta, yaya Habu zai mata haka? Wani abun ban haushin ma ko maganar ‘ya’yansa bai yi ba balle cikin da ya bar ta da shi. Wato ma wai ka da ta neme shi kamar bai bar ta da wani nauyi ba.
Ta cigaba da jujjuya takardar a hannunta tana maimaita ” Habu Allah ya isa ..Allah ya ma ka abunda ka min..”
*******************************
Ruwan da aka fara kamar da bakin kwarya shi ya katse wa hindatu dogon tunaninta. Cike da tsananin mamaki ta tsaya cak don har ga Allah bata lura da hadari ba. Jinjirinta ya fara tsala kuka na fitar hayyaci yana mimmikewa nan ta shiga diriricewa tana neman wajen fakewa.
Ta fara gudu tana hange hange har sai da ruwa ya taba su sa’annnan ta samu wani wajen rubabben rumfar langa langa ta fake. Hakoranta suka cigaba da kaduwar sanyi kaf…kaf tana mai dana sanin fitowarta a wannan bahaguwar larabar.
Sai da aka yi kusan minti talatin sannan ruwan ya tsagaita, muhammadu yayi shiru a lokacin tsammaninta ya samu bacci. Tsiraran motoci da babura da wasu a kafa sun soma wucewa bisa titi don gudanar da uzurirrikansu. Har yanzu ba ta kai Dangi ba kawai sai ta tsallaka gefen titi da niyyar ta roki dan achaba da ya taimaka ya kai ta asibitin murtala a naira talatin.
Can sai ta hangi wani daure da hankicif shudi a kan sa ta sa hannu ta tare shi ya tsaya hade da fadin
” Hajiya ina za ki”?
Ta fito da talatin din da ke jikinta ta karyar da murya ta ce
” Dan Allah bawan Allah ka taimake ni yanda Allah ya taimake ka, yaro na ne ba shi da lafiya ka taimaka ka kai ni bakin asibiti a naira talatin. Dan son ma’aiki”
Dan achaban baki wuluk mai faffadan lebe da katon hancin da ya mamaye kusan rabin fuskarsa ya kura ma ta kwala kwalan idanuwansa masu kama da jan gauta ba tare da ya ba ta amsa ba har tayi zaton taimakonta zai yi. Amma me? Sai ta ga ya sa kafarsa ya burga babur din bayan ya jeho ma ta wata murdaddiyar tambaya
” Yo Hajiya mashin din na uwarki ne?!”
Ya cilla kan titi ya bar ta anan. Duk wannan abun da suke yi akan idon wani dan achaba da ya tsaya a gaban mai tireda ya sayi sigari. Ya cigaba da kallonta bayan ya dora sigarin akan lebensa ya cinna ma ta wuta. Gangarowa yayi gabanta ya kalle ta bayan ya zuki hayaki mai yawa ya fesar akan fuskarta. Wani abu mai kama da ashar ya zo ma ta iya wuya kafin ta furta ta ji ya ce
“kawo talatin din”
Cikin rawar jiki ta mika ma sa ta dane kan babur din ya cilla da ita bisa titi har asibitin murtala.
Tana isa ta wuce miltara babu cikowar mutane saboda ruwan saman da aka yi sai ta samu benci ta zauna ta kama layi. Ta tamabayi ta kusa da ita
“ya na ga layin baya motsi”?
matar ta ce
” tun dazu muke jira wai kati ya kare sai an kawo..to jiran ya zama na gawon shanu”
Ta ja dan karamin tsaki tana mai cigaba da ba wa wani dan yaro awarar da ke hannunta. Hindatu tayi shiru ta san ba yadda za tayi sai dai ta jira.
Wata mata mai dauke da farin bokiti cike da alala kullin leda ta zo wucewa ta na cewa
” alala alala ashirin ashirin”
Sai ta ji cikinta ya bada kululu ta bi alalar da ido ga ta lubu lubu , jajir daga gani ta sha manja. Ta hadiyi yawu makwat tana mai tuna rabonta da cin alala irin wannan. Mai alalar har ta bace wa idonta tana binta da kallo kamar ta kwata. Daga bisani ta kau da ido ranta a bace da ta tuna ba ta maganin ko ficika.
Ta yanke shawarar komawa gidansu tun da zaman na ta bana kare ba ne,dama a gajeran tunaninta ta dauka Habu ba nisa yayi ba zai waiwaye su. Hakan ya sa ta share ta zauna zaman jiransa ya dawo duk da zunden da mutane ke ma ta.
Aka kawo katin ta karba har aka zo kan ta a layi ta shiga dakin likita. Wata nas na zaune a gefensa , ta gaishe shi ya amsa ba tare da ya dago ya kalle ta ba. Daga bisani ya karbi katinta ya dago kan sa ya ce
” menene matsalar?”
Tayi ma sa bayani ya ce ta miko yaron. Ta kunto shi a kunshin zanin goyo mai damshi ya karba a daidai lokacin yayi sauri ya dago ya kalleta jin yaron sakab sannan a jike ya ce
“yaya na ji shi a jike??
Ta ce a sanyaye
“Ruwan sama likita,ruwa ne ya dake mu”
Likita ya maida kallonsa kan jinjiri muhammadu a wani yanayi da ya sa hindatu shan jinin jikinta. Ya shimfidar da shi akan gado yana ta dudduba shi da kayan aiki. Cikin kasa da minti daya ya juyo ya ce ma ta
“Hajiya ai ya rasu”!
Duniyar Hjndatu ta fara juyawa da ita jikinta na kyarma..me take ji haka? Ba ta iya cewa komai ba karbar gawar jinjirin kawai ta yi ta fice a guje. Sai ta kankame jiririnta tana gudu, tayi gudu tayi gudu amma fa ba ta san takamaimai inda tayi ba. Haka mutane suka dinga binta da kallon mahaukaciya sabon kamu.
Lokacin da Allah ya taimaka ta isa gida har an idar da sallar laasar. Malam mai almajirai makocinsu mai taimakonsu har ya sa an baza tabarmi na karatun yamma. Ta fado gabansa cikin gigita ta zube ma sa ta fashe da kuka cewa yake
” lafiya? Hindatu lafiya? Shiga cikin gida gani nan zuwa”
Ta kasa ce masa komai saboda kuka sai kawai ta miko ma sa gawar ta dora ma sa, kamar numfashinta zai dauke ta ce
“Ya rasu malam”. A jikina ruwan sama ya taba shi aka zare mishi rai ba tare da na lura ba. Ina ma ni aka dauke na je lahirar da ta fiye mini duniya! Malam akwai wasu mutane wanda ba a halicce su dan su ji dadi a duniya ba,wadanda duniya bata karbe su ba..ina ga ina cikinsu malam! Malam ya mike tsaye a cikin tashin hankali ya ce
“Auzubillahi..wannan kalamai ne na wadanda suka fitar da rahama daga ubangiji, na wadanda suka bata ne, ke kuma ba batacciya ba ce”
Ta ce “
Ina ma na tashi a cikin batattun watakila da na san menene dadin duniya”!
Malam ya lura sumbatu take don haka ya karashe zancen da
“garin yaya wannan kaddara ta auku”
Yana mai nuni da gawar. Ta nisa tana jinjina kai zuciyarta cike da kissa ma ta abubuwa ta ce
“Rashin kumbar susa..Allah ya tsinewa rashin kumbar susa”!
MASU ƁUKATAR A TALLATA MUSU HAJOJINSU ZA SU IYA TUNTUƁARMU TA LAMBOBIN 07045308523 MUN GODE
