Search
You have no alerts.

    MASU ƁUKATAR A TALLATA MUSU HAJOJINSU ZA SU IYA TUNTUƁARMU TA LAMBOBIN 07045308523 MUN GODE

    Ashe tsakanina da ke wani alamari ne mai ban mamaki? Ashe tsakanina da ke ‘yanuwantaka ce? Ashe tsakanina da ke soyayya ce? Me ya sa abubuwa ba sa zuwa a daidai lokacin da ya kamata su zo? Me ya sa su kan zo a kurarren lokaci? Me ya sa????
    Almustapha Iliyaso Tillaberi

    ( you may need a tissue paper, this is going to be a tough ride. Going on a break i have exams to write. Do not conclude until you have read the last chapter, the last sentence, the last word. Few chapters to go inshallah)

    Hajiya Hadiza ke tafiya akan titin zoo road da ke kano. Tana hanyar zuwa wani biki diyar kawarta na nunawa sa’a. Nakasasshen mijinta ta bar shi a gida ko bi ta kan sa ba ta yi ba. Warin da ya isheta ne ma ya sa ta sa aka maida shi baskwata don ba zata iya ba.

    Kiri kiri abokiyar zamanta Khulsumou da ke Niamey ta ki zuwa sai faman aiken malamai ta ke. To ita ina za ta iya? Ta godewa Allah Almustapha dan ta shi ke kan komai da ina za ta sa kanta?

    Ta san in dai ta khulsumou ne da ta wawure komai ta gudu ta bar ta da salallami.

    A zuciyarta ta kagu maigidan na ta ya cika ko ta rabu da alakakai. Dama ai kowa ya debo da zafi bakinsa ya ke kaiwa. Ita ta aike shi ya zalunci jama’a ga shi nan abu ya dawo kan sa zai shafe su. Inaa…ba da ita ba.

    Wannan gidan bikin da zata je ta za ta hadu da matar mataimakin shugaban kasa dalilin ma da ya sa ta ci burin bikin kenen. Sun yi ajandar cewa za su hadu su tattauna kan batun ‘ya’yansu. Akwai diyarta Ramlat da take yiwa Almustapha hange. Ta san sun dace yanayin arzikin gidajensu ya dace da juna.

    Idan ta biyewa Almustapha ta san ba zai tsaya yayi zabe yadda ya dace ba. Gwara ta zaba ma sa wacce ta dace da shi yadda sunansa zai kara daguwa a idon duniya.

    Wani abun ma shi ne ba ta ma san inda dan na ta yake ba ko wani hali ma yake ciki. Kwana 2 ma ba suyi waya ba. Dama haka halinta yake in dai ba wai tana bukatar kudi ba ko wani abu da wuya ta neme shi don a ganinta kar ta katse ma muhimman aiyuka.

    Za ta neme shi da zaran ta gama da gidan bikin nan, dole ne ma ta neme shi. Tunaninta kenen.

    Dama zaune take a bayan mota gefen mai zaman banza direba na jan ta. Da yake ma’abociyar karatun jaridu ce sai ta ce bari ta sayi jaridu akan juction. Ta siya aka ba su hannu suka wuce. Wani abu daya tak ne ya sa ma ta luguden zuciyarta. Labarin farko da ta gani a shafin jaridar daily news da kuma Nigerian ne ya girgiza ta. Ga abunda ta gani

    Wani kara tayi ta ce

    ” Whattttttttt!!!”
    “Karya ne wallahi! Sharri za a yiwa da na! Karya ne!”

    Wani irin gumi ne ya fara tsattsafo ma ta ta koina. Ta shiga rudani. Amma wani sashe na zuciyarta na raya ma ta sharrin abokanan hamayya ne. To yaushe ma Almustaphan ta yayi aure? Yaron da aure ma baya gabansa.

    Wani sashe na zuciyarta na so na yarda wani sashe ya hane ta. Ai daga gani ma kazafi ne, an ga danta mai karancin shekaru ya faso gari ana ma sa bakin ciki.

    Ba shiri ta nemi wayarta tana ta gwada wayarsa. In dai an yi ne don a bata masa suna sai ta sa an tabbatar an kama su. Duk irin kiran da take wayar a kashe. Kanta ya kara daurewa.

    Daidai lokacin ta iso gidan bikin. Tayi sauri ta kama kanta ta mayar da nutsuwarta. Wannan ne damar da take da ita wajen ganin ta hadu da Hajiya murjanatu su kulla alaka. Ka da ta bari damar ta wuce akan wani zancen shafa labari shuni.

    Tana gamawa da gidan bikin za ta san yadda za ta yi a kama gidan jaridun nan. Yanzu haka ma labarin bai bazu ba. Za ta sa dan na ta ya je gidan radio da talabijin ya musanta ya wanke kansa tun kafin masoyansa su juya masa baya. Lokacin siyasa ya matso bata son abinda zai taba sunan danta.

    Kawai sai Hajiya Hadiza ta biris ta yi kamar bata ga jarida ba. Ta shiga gidan biki cikin taqama da izza. Amma zuciyarta fargaba ce da bacin rai. Tunaninta kawai ina Almustapha ya shiga, don tana so tayi magana da shi da gaggawa ta ji wacce a ciki.

    Abun farko da ya sa jikinta ya fara yin sanyi bai wuce yadda uwar bikin Hajiya Hanne mai gwal ta karbe ta ba. A yadda suka saba kwata kwata sai ta ga ba wannan.

    Yadda aka nuna ta a wajen matar mataimakin shugaban kasa ma bai mata ba, don ganin ai kamata yayi a ce su ne gaba gaba. Ba su san wacece ita ba?

    Kawai sai tayi gaban kan ta. Ta fara shiga ana damawa da ita. Ta lura da gani ganin da wasu ke ma ta amma ta dauki hakan hassada kawai.

    Ba tayi kasa a gwiwa ba ta fara shigarwa Hajiya murjanatu batun da ke ranta. Ba ayi wata wata ba ta daka ma ta wata mahaukaciyar tsawa da ya bar Hajiya Hadiza cikin matsanancin mamaki. Ta ce

    ” Kina da hankali kuwa Hajiya Hadiza?! Ko kan ki ba daya ba? Ramlat din za a dauka a bawa sakaran dan ki manemin mata! Dan ta’adda! Ke idan kina cin kasa ki kiyayi ta shuri!”

    Wani irin abu ne ya daki kirjinta ba da wasa ba. Kafin ta ce wani abu Hajiya murjanatu ta wurgo ma ta wata jarida

    ” kin dauka mu mahaukata ne? Ko bamu san abinda duniya ke ciki ba? Lokacin da dan ki ya sha sarka, kya gane annabi ya faku”

    Cikin gigita Hajiya Hadiza ke cewa

    ” karya ne Hajiya! Wannan aikin makiya ne”

    Hajiya Murjanatu ta watsa mata banzan kallo ta ce

    ” Abin da ake bugawa a jaridu da gidajen talabijin shi ne karya?”

    Kawai sai ta dauki remote ta kunna tv da tai tashar da take bukata ta ce , wanna ma karya ne?

    Wani irin juyowa Hajiya Hadiza tayi ta kurawa Tv din kallo cikin matsanancin tashin hankali ta ji yawu ya kafe ma ta kaf ganin abunda take kallo

    Ta kuma canja tashar talabijin din ta ce “wannan fa shi ma karya ne?”

    ” lahaula wala kuwwata la haula wala kuwwata”

    Su ne kalaman da Hajiya Hadiza ta samu furtawa cikin dimuwa. Wani irin abu take ji a kirjinta, wani irin faduwar gaba.

    Rokon Allah take so tayi ta rasa takamaimai me zata roka saboda rudani. Kawai sai ta zari jakarta da mayafi ta fita bazar bazar kamar mahaukaciya sabon kamu.

    Wayarta ta dauko tana ta rusa masa kira amm bata shiga. Daga karshe ta tuna wani private layinsa na etisalat ta gwada kira ko za a dace. Tana fara bugu ta ji gabanta na bugawa wayar har zata tsinke ta ji an dauka. Cikin sauri ta ce

    ” Almustapha!! Me ke faruwa ne? Menene yake faruwa? Wasu irin munanan labarai nake ji?”

    A wata irin murya a kasalance ya ce

    ” Mummy…! Mummy ina police station… Mummy ki taya ni addua!”

    Tun da take da Almustapha bai taba yi mata magana a irin wannan muryar ta nuna sarewa ba. Sai ta ji wani abu ya daki kirjinta, ta ji wani yarr a jikinta.

    Almustaphan ta! Gudan jininta! Shi ke nan guda daya tilo gurinta.

    Akwai matsala, akwai babbar matsala.

    Kawai sai ta tsugunna a wajen ta fashe da kuka cewa take

    ” Innalillahi..wa innailairrajiun”

    MASU ƁUKATAR A TALLATA MUSU HAJOJINSU ZA SU IYA TUNTUƁARMU TA LAMBOBIN 07045308523 MUN GODE

    Note
    error: Content is protected !!