Duniya ta – Chapter Three
by NadminMASU ƁUKATAR A TALLATA MUSU HAJOJINSU ZA SU IYA TUNTUƁARMU TA LAMBOBIN 07045308523 MUN GODE
Ina aka je? Ina za a dawo?
Saudi Arabia
“Hajiyya goro”? Balaraben ya tambayi wata mata da ke fitowa daga harabar “airport” din Jidda a cikin gurbatacciyar hausarsa. Matar ta girgiza kai tayi gaba cike da takaicin goronta da aka kwace a wajen screening . Ranta ya cigaba da raya ma ta dama a gida Najeriya ne, ta bada cin hanci ta wuce da shi ta ci kazamar riba.
Wannan abun da ya faru akan idon Lubabatu wacce ta sha bakar abaya da nikabi baka hango komai sai fararen idanuwanta. Can ta hango wata mata lukuta ta fito da sassarfa tana tafiya da kyar kamar kwai ya fashe ma ta a ciki. Luba tayi sauri ta mike ta cafki hannun matar ta ce
“Salam ya ukhti..Hajiyya barka da zuwa barka da zuwa na ga alama akwai goro ko?”
Hajiyar ta kalli Luba da mamakin yadda ta gane yayin da takari maza da mata suka yanyame ta da rokon ta siyar musu. Amma sai ta ki, ta tsayar da Luba akan dalilin ita ta fara taryo ta. Suka sauke goron ta na mai bawa Luba labari
” Ai duk cikin ‘yanuwana ni kadai na samu na ketaro da shi yau sa’ar a kaina take. Abokanan tafiyata an kwace musu har da masu kwarya goma! Amma kin ganni nan sai da na haye da kwarya takwas!”
Luba tace ” Mashallah mashallah”
Sa’annan ta daga baki ta kwalawa Hajiya ‘yar Sakkwato kira ita kuma tayi ma ta alama da hannu cewar ta na zuwa. Suka yi ciniki ta biya ta kwashi goronta tayi gaba suka hade da Hajiya ‘yar Sakkwato tana murmushin mugunta ta ce
” ai halin na ma ta ,na ga sabuwar hajiya ce ko kan lisafin riyal din ba ta sani ba”
Suka kwashe da dariya. Hajiya Yar Sakkwato ta ce
“Kwanda da kin kai ma ta haka. Duka nawa an ka saida huhun goro ga kano? Amma dan Allah ya bisshe su ga sa’a sunka hawo da shi ,sai su lumka mishi kudi su saida shi da tsada bayan mu abun kai baka kawai munka bida” .
Luba ta gyara nikab dinta tayi murmushi ta ce
” Kin ko samu kin sayi man bilicin din kin san fa kwanan nan shi ke kawo kudi.”
Hajiyar ta saka hannu a ledar hannunta ta nuna ma ta ta kara da cewa
” har atanhwa ta jikka bibbiyu ni ssiya sai mu siyarta ga uwani mai tuwo na ji tana bida”
Suka rankaya za su fita Luba tayi sauri ta ce ” au ki tsaya mu duba ko an kawo maggi star kin san fa yanzu zuwan ‘yan umara ne, su in ba su ji maggin nan zai! a abinci ba babu magana”. Da kayan da suka siya daga hannun matafiya ‘yan Najeriya suka koma Makkah. Nan da nan fa sai kasuwa ta bude, suka raba goron nan bari bari suna siyarwa larabawan nan mayun goro su kuma suna rububi.
Idan da mai karatu zai ga inda su Luba ke kwana a unguwar Sharu mansur da Sharu sittin sai abun ya bashi mamaki. Anan za ka ga mai siyar da tuwo, waina, shinkafa har da danginsu gyada da aya. Dakin kwanansu Luba wani tsukakken daki ne a can saman bene su goma sha uku ne a dakin kowa akan ‘yar yaloluwar katifarsa. Daukacin jama’ar wannan daki ba sa dauke da takardar shaidar zama ta dan kasa igama, a takaice dai bakin haure ne.
Luba da Hajiya kan yi tuwo,suna kuma sayar da kayan sare saren da suka samo daga ‘yan Najeriya. Sa’annan Luba kan dauki kayan yara da dan kananan siturunsu masu saukin kudi ta kulle a zani ta kai bakin “Harem” .Duk inda suka ga askar to fa sai su fyalla a guje ita da ire irenta , don idan aka kama ka yanzun nan ka sha zaman” sijjin”daga nan sai kasarka ta gado.
Idan lokacin Ummara da Hajji ya wuce sukan yi aiki a gidajen larabawa kamar su wanke wanke, shara, raino da sauransu. Wadannan aiyukan da bakaken fata kan yiwa larabawa shi ke sawa suke musu kallon kaskanci a ganinsu kowani bakar fata matsiyaci ne, boyi boyi ne. Don haka kyara ta dalilin banbancin launin fata (racism) yayi yawa yayin da aka samu rangwame na rashin sanin darajar kai a wajen bakaken.
Wani abu da Luba kan yi wanda ma fi yawan ‘yan kano to jidda ke yi shi ne karuwanci. Hakan zai iya zama tsakanin bakaken fata mazauna can ko kuma mazan larabawa. Hakan ba karamin kudi yake kawo musu ba domin kuwa mazan larabawa ba su kyashin fitar da ko nawa ne idan har bukatarsu zata biya.
Luba ta kalli Hajiya a wani dare da suke shirin kwanciya ta ce
” wai ko hajiya don munafirci kin san ‘yar Gombe fara lekawa tayi wajen Balaraben nan mai gwal na Jidda wanda ki kai min hanya? Shegiya tsinanniya! kin san kuwa cewa Hajiya Zulai kawarki ita ce ta ma ta hanya dan ta ga yana barin kudi? Duk sai sun ci ubansu ‘ya’yan matsiyata, ‘ya’yan bakin ciki!” Ta dauko ashar ta maka!
Hajiya tayi salati ta sanar da ubangiji cike da mamaki ta ce “wacce Hajiya Zulai kinka nihi? Wagga da na yiwa hanya ta zo garin ga tana tsumma gaba tsumma baya? Hal ita ce akan gama baki da ita ai mana zalumci?”
Luba ta tsuke baki kamar irin yanda yara kan yi, yanayin halayyarta kenen. Ta saki bakin a hankali sannan ta ja karamin tsaki. Ba ta tanka Hajiyar ba illa ma ta shiga warware gashin kanta wanda ya zubo har gadon baya ta sa mataji ta soma taza.
Hajiya Yar Sokoto ta lalace wajen
duban Luba da irin nata kyawun sai kace barbarar yanyawa. Wasu irin idanuwa gareta manya manya farare da ta da take iya yin wani kallo da su ta kafe mutum kamar tocila. Bakin kwayar idonta da gashin girarta kan rikita yawa yawan maza da suka kauce hanya a irin hilata da jan hankali irin na ta. Yanayin jikinta daidai yake da yanda mazan da ke kara kaina akanta ke bukata. Tana da kowacce irin halitta da mace ke bukata a kira ta da mace ta kuma amsa da babbar murya.
Tana da tsayi daidai ita da kibar da bata wuce misali ba sai dai me? Duk cikar halittar Luba dafi ce ga wanda bai san ta ba, zinariya ce ga wanda ke cikin duhun jaraba haka guba ce ga wanda ya sake ya rabe ta.
Hajiya yar sokoto tayi firgigit ta dawo daga duniyar tunaninta lokacin da Luba ta daka mata duka a cinya. Ta ce “Hajiya yaya dai?” Hajiyar ta janyo kwananta da kubz da yar miyar dankali ta ce
” To ke me ma yaka damunki? Su fa larabawan ga irinki sun ka hi so har wani manemi za ki qi yi? Ni fa shekarata ishirin kasar ga , wallahi ki tsumayi aikin hajjin ga mai zawwa Alhazawan da na ka gama ki da su..K’ ..kya yi mamaki”
Budar bakin Luba sai cewa tayi
” Kutumar! Hajiya rainawa kan ki hankali ina ce bara ma haka kika ce da ni amma da aka kawo yara kanana kasuwarki ta bude da su ban ko ji duriyarki ba! Ke ma kika samo naki abokin harkar Alhaji mai goro ko kwana gida ba ki yi”
Hajiya ta kule matuka da kalaman Luba. Dama ita matsalarta kenen shegiyar fitsara da tantiriyar rashin kunya.idan ban da don tana samun kudi ta hanyarta ba da tuni ta yarda kwallon mangwaro ta huta da kuda. A kule ta ce
” Luba ni ki ka dannawa ashariya?
Luba ta ce ” yo Hajiya ni…ni…karya nayi? tsofai tsofai da ke wai har kin san dadin maza?” ta yi sakaka da baki cikin tsabar rashin mutunci.
A fusace Hajiya ta ce
” Tun kahin a haihi uwalki na san maza!kin ji ni ko? Ganin kin zo Saudiyya kin waye na ‘yan shekaru hal kin ka isa ki mini ragaita? Sa’ilin da kike kudin cizonki har na bisshe ki ga daudar dakin uwalki ba ki ki min ragaita ba! Sai yanzu da kin ka hwara kama kudi bisa hannunki shi ne za ki tasamma zagina?”
Luba ta gintse dariyarta ganin ran Hajiya ya baci. Ita ta san cewa Hajiyar na cutarta tana mata wayonsu na tsofaffin kilaki don haka ta dade mata a makogwaro. Ranta na raya mata Hajiya ita ta yiwa yar Gombe hanya wajen balaraben nan don hadama amma ta ke nema ta ninke ta baibai.
Amma sai ta tuna cewa ba yanzu ne lokacin da ya kamata a bata ba , da sauran lokaci. Sai ta share ta shiga bawa Hajiyar hakuri. A ranar ta kwanta da burirrika iri iri a ranta.
**************************
Ga duk wanda ya kwana ya tashi a unguwar Birget ya san Luba a zamaninta. Gidansu wani tsukakken gida ne mai mata hudu da ‘ya’yan da ko mai gidan farat daya ba zai ce ga yawansu ba.
Duk macen da mahaifinsu ya aura ya saki sai ta dangwarar da ‘ya’yan ta kara gaba ba don akwai takamaimai wanda zai iya daga ido ya kalle su da rahma ba. Haka zai ta gararamba duk inda ya wuce matar uba tana bin sa da alkaba’i
“shege tsinanne dan gidan ta maqwalle mai gani har hanji” ,
“gantalalle da micin ido irin na uwarsa”
Wadannan kalaman su ne ruwan dare akan ‘ya’yan tsakar gida. Kazar gidan ta fi dan da ke yawo a tsakar gida daraja domin kuwa ita watakila a watsa ma ta hatsi ko don ta girma a ci moriyarta.
A tsawon zaman Luba a gidansu bata taba ganin mahaifinta ya shigo da leda da sunan cefane ba sai lokaci daya tak!wato idan ya yiwo sabuwar amarya. A ranar da ta zo a ranar ne za a gwangwajeta da dankwaleliyar gasasshiyar kaza daga nan kuma sai ga ji dif! Kamar an dauke ruwan sama sai kuma zuwan wata amaryar!
Baban na su an fi saninsa da “Baban yara” kuma talaka ne tilis bai ajiye ba bai ba wa wani ajiya ba bai kuma damu da hakan ba. Mutane na mamakin yadda aka yi mata ke amincewa su aure shi ,har ma wai suka yi hasashen cewa yana da wata laya ta farin jini da babu macen da ta isa ta musa ma sa. Yar sana’ar ta sa ba ta wuce sayar da danginsu tumatir, tattasai da attaruhu amma aure aurensa ko tattabara albarka.
Idan ka ga an dora tukunya a gidan to uwar kowa ce ta nema ta baiwa ‘ya’yanta su kuma ‘ya’yan tsakar gida idan an ci a sude su samu na lasa.
Wani iri zama ake yi a gidan irin na marina , zaman ban san ka ba..kowa tashi ta fisshe shi. Kowa burinsa ya nema ya samu ya hana danuwansa. Ga tsananin kishi tsakanin matan kowacce so take a ce ita da ‘ya’yanta sun fi.
Mahaifyar Luba ita ce ta biyu kuma ita da uwargidan a yanzu su ke da zaunannen gurbi a gidan. Hakan ne dalilin da yasa suka zama dadaddun abokanan hamayya. Dukanninsu suna da yara maza da mata.
Iya Asabe uwargida tana da ‘ya’yanta bakwai wanda akwai biyu mata wadanda suke kusan sa’anin Lubar.
Iya tamadi mahaifiyar Luba ‘ya’yanta maza uku da autarta Luba.
Ragowar gurbin na mata biyu wanda akan iya canja su a kowane lokaci na da ‘ya’ya barkatai wanda kirga su ma tsatsar rashin aikin yi ne. A zuciyar Iya tamadi ba komai sai tsanani kwadayi, kullum Allah Allah take wani ya kawo abunsa ta lashe ko da kuwa yayan cikinta ne. Halin da ya sa kenen ‘ya”yanta maza suka guje ta ba ma sa son shigowa gidan saboda jarabar bani bani. Ita a son ran ta , ta fi iya asabe komai dangane da abun duniya. ‘Ya’ya mazan data kwallafawa rai suka ki tsinana mata komai ,kawai sai ta kafa murhu take suyar kosai safe da yamma.
Iya asabe na ganin haka sai ta nunawa iya tamadi ranar haihuwar ‘ya’ya mata. Sai take yin alawoyin yara take dora musu talla.
A tun tasowar Luba ta saba da rayuwa irin ta kashin dankali na sama ya danne na kasa, da kuma kowa tashi ta fisshe shi. Sai ta taso a yarinya yar kanta ba mai fada ma ta ta ji. Da fari ta takura wa uwar ta sa ta a makarantar firamare ta gwamnati da ke unguwarsu saboda kawai ta banbanta da sauran yan gidansu da take kira ‘yan kauye. Luba ta fi ganin karatu a matsayin hanyar bunkasa da birgewa ba wai wata hanyar samun ilmi ba.
Da fari uwar ta ki ta ce zata kashe mata jari. To amma da yake Luba uwar naci ce kuma auta shalelen Iya Tamadi sai ta yarda amma da sharadin daga nan ba cigaba. Da ta gama firamare lokacin tana da shekara goma sha biyar sai ta ci common entrance ta kuma dage ita fa sai ta je sakandare.
Iya tamadi ta hau ta fado kasa ta ce ba da jarin kosan ta ba karya da ciwo mari da zafi. Luba uwar giggiwa da tsaurin ido sai cewa tayi
” yo ni ma sana’ata zan kafa na huta da wulakancinki. Ranta min dubu biyu billahillazi kafin karshen sati zan maido miki kudinki”
Iya tamadi ta mika ma ta kudin ta hada da rantsuwar sati na zagayowa idan bata maido da kudin ba ,za ta siyar da atamfarta mai tambarin gidan Sarki da saurayin ita Lubar ya saya ma ta ta ci sallah. Luba ta ce
“eh na ji”.
Washegari kuwa ta yi cefenenta ta ta dafa shinkafa da taliya tayi miya da naman saniya. Ta sa yaro ya siyo ma ta salak da tumatir ta yanka siri siri ta saka a farin bokiti mai suna fallasa. Kayan abincinta ta kwasa ta dora a kai ta fice abunta ba tare da ta ce wa kowa ga inda ta je ba.
Da yammaci lis ana shirin kiran sallar magariba sai ga ta da fararen bokiti komai ya kare. Iya tamadi ta rike haba cike da mamaki ta ce
” ke…auta! Ba dai wai har ya kare ba?”
Sai ta yi wa uwar kallon galala na ina ruwanki ta ce
” yo ku dai ku zuba min ido ba kowa ya ki ya taimake ni ba? Ai kuwa ni zan taimaki kaina”
Iya tamadi ta cigaba da cewa ba tare da ta damu da kallon banza ko maganar da tayi ba
” Auta kenen. Ke dai da yake kina da tagomashin arziki dole ki ce haka. Mata nawa ke saida shinkafa da taliya a bakin kasuwa kuma suke bandaron kayarsu? ke..ni ko dai juye aka miki?”
Luba ta kada kanta ta tafi bakin rijiya ba tare da ta bawa uwar ansa ba ta janyo ruwan wanka. Ta shiga bandaki ta sallo wankanta. Bayan sallar isha’i ta ci kwalliyarta cas ta baza turare .Iya tamadi tana ta yashe baki ganin diyar ta ta tamkar zinariya. Ta sa kai ta fice abunta ba tare da ta cewa kowa kanzil ba. Kullum haka Luba kan yi karshen sati na zuwa kuwa ta lalo dubu biyu cas ta mikawa iya tamadi ,ragowar kudin dumus a hannunta riba ce ta fara kokarin turawa a ‘yar pos. Iya tamadi ta ce
” Haba haba auta..ai ido guba..ai kya dan lasa min irin wanna uban kudi haka?”
Luba ta ce ” Tabdijam! Dubu biyun ma na ga da kyar kika ranta min, da ace ban samu riba ba da yanzu kin daga min hankali kin ce na ba ki abarki. Kin ga wannan kudin? To kudin kayan makaranta ne zan sai abuna da ‘yan littafai Alkur’ani sai nayi bokon nan in ga uwar meye a cikinta da masu zuwa suke daga mana kai!”
Iya Tamadi ta fara zazzaro ido ta ce
” Au ke yanzu wannan uban kudin asararsa za kiyi a karatun boko? Ni ca nake ma taro za ki fara tunda dai kin san halin ubanki ko cokalin shan shayi bai siya miki in aurenki ya tashi. Ni ce dai komai kuma so nake na yankawa su Hafsi da Rahila sakwaninki. Kin ga wannan fita tallar da suke billahillazi samari kashe musu kudi suke. Karkashin gadonsu kuwa kamar kantin kalau kalau. So ki ke yi mu ji kunya?”
Luba kuwa sai buga cinya tayi ta gatsina baki ta ce
” yo ke iyannan ina ruwanki? Su sayi kasuwar kwari su hada da ta bakin asibiti. Ke ba kya ganinsu ne wai ‘yan kauye ba wani aji yanzun haka har wani saurayin kirki ne zai aure su? Daga mai tireda sai mai gurasa me na sama ya ci ballantana na kasa ya dangwala? Ni fa dan boko zan aura mai aikin ofis ko so kike yanda kika kare nima na kare? ”
Cikin tsananin sauri Iya tamadi ta buga a’uziyya ta ce
” Allah ya kiyashe ki auren irin ubanku. Haihuwar guzuma ‘ya kwance uwa kwance” sai ta kama haba ” ni na rasa wani tsautsayi ya kai ni auren ubanku ba ci ba sha auren matsiyaci” ta karashe da watsa hannaye a iska cikin saduda ta ce ” rabon haihuwarku ne auta in ba don haka ba ai na fi karfin ubanku!”
Luba ta ce ” A to. Ki bari ni dai nayi bokon nan na goge. Miji kuwa sai na zaba na darje ban yin auren wahala Alkur’an!Idan banda abunki ma ke ba da kudinki za a je bokon nan ba, ba kuma na uban wani ba me zai dame ki?”
Iya tamadi ta ce “Ai fa..to ban dari biyar auta ladan ganin ido”
Luba ta zaro ‘yan dari biyar biyu ta mika ma ta sabbi kar, ta yi saurin karba kamar ta kifa don d’oki.
” Duk cikin ‘ya’yana ba mai kaunata irinki auta, daga gani ke za ki fitar da ni cikin kangin talauci. In banda abunki ma wlh da mun hada jari” inji Iya tamadi.
Luba ta kwashe da dariya ta ce ” ka ji iyannan ta ji zancen kudi. Ban ki ba dai tunda yanzun zan shiga makaranta sai kike min girkin da safe, ni idan na dawo da rana sai in fita talla. Idan ya so duk abunda aka samu sai na ke ware miki ladan ki. Amma fa ni miya ta ba ajino kadai nake sa ma ta ba, ina saka dunkule kin ji dai na gaya miki”.
Iya tamadi ba musu ta ce ta yarda.
Litinin na zagayowa Luba ta shiga makaranta abunta ba tare da kowa ya damu da ya aka yi take zuwa ba. Idan ta dawo kuma sai ta dauki abincin tallarta tayi gaba. Sau dayawa har takan kai bayan ishai ba ta dawo ba. Babu wani abu da ya damu iya tamadi illa dai kawai idan ta dawo komin dare za a ja lissafi.
Abu kamar wasa abincin Luba ya bunkasa har ta kai tana yin doya, wake har da kajin gidan gona. Tana kama kudi sosai kuma ita din ‘yar jin dadi da son kwalliya ce. Idan ka gan ta ba zaka ce daga cikin gidansu ta fito ba. Cimar ta ma daban ce a gidan. Idan suna shiri da iya tamadi ta sammata idan ba sa yi ta cinye kayanta. Sai dai ka ji Iyar na cewa
“um’um..uhmm auta..ido guba!”
Samari ‘yan sha’awa suka yi wa Luba caa tamkar ita kadai ce mace budurwa a layin su. Sau dayawa idan ta dauki tallar abincinta kafin ta kai inda take siyarwa wani yake mata juye. Dan Luba ta wanki saurayi ko ya taba ta ya bata abun duniya ba komai ba ne. Ita dai a rayuwarta ta tsani talauci kuma ta rantse ba zata rayu a cikinsa ba ko da kuwa zata yi yawo tsirara.
Tayi matsanancin sabawa da maza a karancin shekaru irin na ta. Kafin ta shekara sha takwas ta kara cika, ta fara shafe shafe tana walwali sai kuma ta iya taku, tana kuma zuwa makaranta tana dan tsintar turanci.
A wata ranar asabar ba makaranta Luba ta dora wa almajirai kayan abincinta tinkis tinkis har zuwa kofar shagon Olu inda take da tebur. Duk cikin kasuwar ba mai iya ajiye tebur a gaban shagonsa sai Luba. Olu wani bayerabe ne da ke da shagon siyar da kayan masarufi. Katoton shago ne da shi wanda babu abunda baya siyarwa, hakannan kuma mayen Luba ne.
Luba tana yiwa Olu kyau, tana ba shi sha’awa idan ya gan ta jikinsa har bari yake. Hakan ne ma ya sa ya barta take kasa abinci a kofar shagonsa kuma duk ranar da tayi bandaro yakan siye duka ya rabar don kar ta dau asara. Luba nayi da Olu cikin samarinta ba wai don yana birgeta ko da da kwayar zarra ba ,sai don kudin da take samu a hannunsa da kuma kayan da take dauka a shagon gaba gadi ba tare da ta biya ba.
A rayuwar Luba bata san so ba, kuma ba wanda ya isa ta so shi sai dai ta so abun hannunsa. Sai dai kuma Luba na da kyauta, abun hannunta baya rufe ma ta ido.
Da isowarta ta fara jera kayanta akan tebur a tsaftace. Ta sha atamfarta mai tauraro da kuma gyalenta mai suna “rakani gantali” dan karamin bakinta ya dau jambaki tana taunar cingam kas kas. Ya fito daga shago sanye da wandonsa “three quater” da “vest” hannunsa daya a cikin aljihu dayan kuma ya kama hannun ta yana matsawa ya ce
” Haba Lulu na, ka zo kuma shi ne ba zaka ce min ka zo ba? ”
ta dalla masa harara cike da cike da jin haushi ta warce hannunta ta ce
” eh..ai dama yanzu zaka iya zuwa ka min dadin baki ni kuwa na riga na dawo daga takiyarka tunda dai har zaka iya nunamin iyakata akan dubu biyar”
Olu a rude ya ce ” haba haba now..dont say that..luluna you know now..market dis day..e..no sabi good woo..ehn. But ba na gaya maka ka zo monday ba, monday..monday if ka zo..i go get money..i go carry five thousand give you. Wetin be five thousand self..mami water like you i go even give you six thousand ..oh my lulu” ya fadi bayan ya rungumota yana kokarin saka hannunsa a rigarta.
Ai kuwa ta wancakalar da shi sannan ta murguda masa baki ta ce
” kan uba! Mayar ni wawiya, ‘yariska rainon tasha ma! Kai kudinka ne kudi ni jikina ba jiki ba ne? Ai wallahi ba ma zan bar gurin nan ba sai ka bani ko ka zata ban san kana kula halira ba? Mai kawo danwake, rainawa kan ka hankali”
Olu yayi tsuru tsuru har ga Allah baya son bacin ranta domin ya jarrabi kan sa da shaawarta kuma har yau ta ki ta bashi hadin kai sai yawo da hankali take masa tana lashe kudinsa. Tsakaninta da shi bai wuce ta bar shi ya taba wani sassa na jikinta ba daga nan kuma sai ta doje. Tunani sa na gaya masa watakila isassun kudin ne baya ba ta,shi ya sa yake ta barinsu.
“Haba lulu” ya fadi yana shafa gefen fuskarta ba tare da ya nuna jin haushi ba ya zaro dubu uku ya ce
” ka gani ba, daga wannan ba ni da komai sai an yi kasuwa yau”
Cikin azama ta warce ta cusa a kirjinta ta ce
” ai kuwa na raba ka da su”
Anan ne fuskarsa ta dan canja ya ce
” ka dan ba ni guda daya mana lulu ko sigari na sha”
ta bude ‘yar pos din ta, ta zaro murtala ta danka ma sa ta ce
” in dai sigari ce ishirin ma ta ishe ka”
Kamar abun magani sai yayi kus. Daga karshe ya ce ” to ka zo mu je ciki mana lulu, 2days ba ka yi da ni” . Ta share shi kamar ba ta ji ba ta cigaba da harkar sayar da abincinta.
Shekaru suka ja yayin da tantirancin luba ke karuwa amma ko yaya takan je makarantar ta. Lokacin rubuta jarabawar kammala sakandare ta kawo kai ana bukatar naira dubu gima sha biyar. Dama ita kudi ba sa zama a hannunta sayi banza sayi wofi. Hankalinta ya tashi . Ta bi shawarar zuciyarta ta rankaya wajen Olu wanda suka dade ba sa tare. Ta wassafo ma sa bayani ya galla ma ta harara ya ce
” Ka bani abunda zan baka kudi ne? Chegen yaro mai yaudalan tsiya”
Ta ce kai dai ka kawo ka gani mana ” ya ce
” In dai zaka bani kan ka sai na baka mana”
Ciniki ya fada. Olu yayi abunda ya ga dama da Luba a shagonsa ya lalo kudinta ya bata ya ce
” kana ta min yanga ashe ma ba ni ne farko ba”
Ta linke kudinta ta cusa a bakin zani ta kada ma sa idanu ta ce
” shege, dan akuya dan kasa da wutar jahannama!” Ta ranta ana kare.
Da sakamakon jarabawarsu ya fito ta ci credit bakwai da pass biyu duk da dai duk jarabawar kusan satar amsa ce. Ta ci “maths” ta ci “English”don haka take doka tsalle ta ce da iya tamadi
” na ci jarabawata da a ce son samu ne da har jamia za ni”
Iya tamadi ta auna ma ta mugun kallo ta ce ” gaskia auta ba ki da hankali. Kina lissafa bana shekarunki ashirin da daya kuwa? Ba za kiyi tunanin aure ba? Ga su hafsi nan sun fitar da mazaje so kike ayi mana dariya ace kin yi kwantai?”
Luba tayi dariya mai isarta ta ce
” yo ka ji iyannan wallahi. Na gaya miki ki daina hada ni da wasu kucakai can su hafsi..ai wannan har mazaje ne suka fitar? Ni fa har yanzu babu wanda ya kwanta min”
Iya ta ce ” uwar ruwan ido, ina wanda ya zo ranar har ya bani kudi? dan gayu mai sabon babur..billahillazi kar ki wuce shi”
Luba ta kada baki ta ce
” tun yaushe na ba shi jan kati . Ke kin ga ni fa makarantar aikin koya jinya ma za ni, in zama nas”
haushi ya kama Iya ta ce a fusace
” to ke da ubanki!!Dan jiya a tsakar gida ya ce Alhajin kyalli zai bawa ke.”
Luba ta wani ja da baya cikin gatsina ta ce
” ka ji baban nan da kankanba. Bai san ci na ba balle sha na sai lokacin aure na ne ya san zai bawa Alhajin kyalli? Kuma na gayawa Alhajin kan sa tun farko kar ya nemi babana don wadanda suka fi shi ma sun ganni sun bari. Iya ta ce
” gane min hanya wai makaho ya so tsegumi. Ai shi babanku wani iri ne wallahi. Ai kuwa shekaran jiya na gan shi da sabuwar shadda wacce Alhajin ya gwangwaje shi da ita. Ke dadin ki ma Alhajin akwai nera, ko banza kya ci”
Haushi ya rufe luba ta ce
” to in kin hadu da baban namu kawai ki gaya ma sa kar ya soma don ba lallai sha’anin yayi dadi ba”
Daga fadar haka ta ja lallausan bargonta tayi kwanciyarta abunta.
Luba na ganin abu kamar wasa aure dai yake nema ya tabbata da Alhajin kyalli. Gidan shi a bayan layinsu yake yana da mata uku da ‘ya’ya ashirin da bakwai ,da yawansu sun girme ta. Ya dade yana makahon son ta amma tayi kememe ta ki. A cewarta wai ya cika gajarta da baki kamar shuni, hakoransa jage jage saboda tsabar cin goro sannan leben baki sidik saboda tsabar zukar sigari.
Aka dunga tafka rigima, iya tamadi da take bayanta ta samfe saboda Alhaji yayi mata ruwan kudi. Wata zuciyar ta ce da ita ta gudu amma sai take ganin asarar hakan tunda ba ta da isasshen kudi a hannunta ,wahalar banza kawai za tayi.
Wata zuciyar ta ce ta kale su su aura ma ta Alhajin da kan sa zai sako ta. Zuciyarta ta kissa ma ta , ta lallaba kamar ta yarda ta , ta samu ta warci abunda zaga warta a gidan ta ware tunda ko banza ya fi gidansu.
Alhaji yayi barin nerar da ya dade bai yi ba a wannan biki. Bangarenta daban komai ya siya ya saka ma ta. Da bikin kuwa kowa ya sha gorin iya tamadi, auta tayi goshi mutan gida ta hana su sakat da sakin maganganu .
Abinda ba ta sani ba shi ne baya fa ta haihu domin a daren farkon Alhaji da Luba ya diro daga kan gado tulun cikinsa na rinjayarsa ya narko wani ashar tun na zamanin maguzawa ya aikawa Luba ya ce
” dama ke yar iska ce? Yawon titi ki ka gama shi ne za a lullube ni a bani ragowar bakin kwalbati?”
Luba na daga kwance ko motsawa bata yi ba hankali kwance tayi sakaka da baki abinda ya zame ma ta dabi’a ta ce
“haba? “
cikin tsananin rainin hankali ta kara da
” ni fa ba na son sharri irin na tsofaffin najadu”.
Ya ware ‘yan yatsunsa duka goman ya aika ma ta da daquwa ya ce
” ubanki shi ne zai miki sharri ba ni ba! Ni zaku ninke a baibai? Ke da matsiyacin ubanki ku lullube ku cuce ni. To ai kuwa cikin daren nan ba sai gobe da safe ba za ki koma inda kika fito”.
Tayi zumbur ta tashi ta ce
” A’a Alhaji..zagi ubana in ka so amma kar ka sake ka hada da ni don baka cikin ‘yan kayana”.
Ya bude baki cikin tsananin mamakin yarinyar da tsaurin idon. ta ya ce
” ke ni ki ke gayawa haka? To na haifi kamarki”
tayi caraf ta ce
” tsohon banza ka san ka haifi kamata ka aure ni? Kuma don zalunci ka zo zaka bini da sharri ni dana san budurwa sabuwa fil na zo a leda?” Sai ta fashe da kuka.
Takaicinta ya kama Alhaji ya shaka sosai kawai sai ya ware ‘yatsunsa ya tsinka ma ta mari! bai kuwa mayar da hannu ba Luba ta damki murfin mai ros din ta da aka ma ta jere ta wurgi Alhaji ta kuma same shi a daidai tsakiyar goshi ji ka ke ..kwam! Sai ga jini na malala.
Cikin azama irin ta maza Alhaji ya ziro hannu ya shako ta ‘yar tazugensa da bai kulle ba ta tade shi ya fadi rikica!
Luba ta tsallake shi ta shiga bandaki ta kulle abunta bayan ta bar shi jina jina. Ya daure ya mike hannu rike da goshi yana aunowa ita da iyayenta zagi kwando kwando.Har ya gaji don kan sa ya nufi sashen sa don samowa kai taimakon gaggawa,da niyyar gobe iyayen luba ko da tsumburbura suke tsafi ba abunda zai hana ya daure su.
Bai kuwa kwanta ranar ba sai da ya rubuta ma ta saki uku ras!
Alhaji bai yi awa da fita ba luba ta zari karamar akwatinta ta cusa tsadaddun kaya da Alhaji ya saya ma ta da kudaden da yayi ta barnatar ma ta , ta sulale ta gudu abunta. Ba ta je ko’ina ba sai gidan Ilu -Ilu wani dadden saurayinta dan kano to legas
Shago gare shi na sayar da atamfofi na legas a kasuwar kwari don haka garin legas ba bakonsa ba ne. Tun kafin luba tayi aure ya dunga zugata su gudu zuwa legas ta ki saboda rashin isasshen kudi. Yanzu da ta je wurinsa dama zani ce ta tadda mu je mu kawai sai suka tafi abunsu.
A can gida kuwa neman duniya an yi ba a gan ta ba, Alhaji bayi wata wata ba ya daure Baban yara. Rigima ta ki ci ta ki cinyewa Iya tamadi tayi kuka har ta gode Allah. Da kyar manyan unguwa suka sa baki aka saki Baban yara damma fa Alhaji ya dage sai an biyashi komai.
A Ikko luba ta kara gogewa da wayewa sai ta ga ashe ma ba komai take yi a kano ba? Ilu ilu bai yi wani zurfin karatun boko ba amma dan gaye ne daidai da zamaninsa, don haka duk wani club club na casu sai da ya kutsa da Luba. Wani daki ne suke zaune a unguwar obalande na wani abokin ilu ilun da ya tafi aiki makurdi suke sheke ayarsu.
A tunanin ilu ilu da shi kadai luba ke ta’ammali amma a rashin saninsa ta riga ta hango wadanda suka fi shi komai! A cikinsu babu gwaninta irin wani Dpo na wata police station da ke unguwarsu. A lokuta da dama idan ilu ilun ba ya nan yakan dauketa su je “bar beach” inda kan luba ya fara fasuwa. Duk yawonta iyakacinta kano sai a legas ta lura ashe iskanci suna ya tara?
Ta ga mata na yawo daga su sai “pant” da “bra” . Kan luba ya daure, ashe ita bata waye ba? Ashe ita yar kauye ce? Ashe ana irin wannan rayuwar a gida Najeriya amma ta nade kan ta a garin Kano kamar kifin rijiya. Son duniya da jin dadinta suka rinka dibanta ta ji ina ma ta cinye rayuwarta a garin legas. Dpo ya bala’in shagwaba ta ya dunga kashe ma ta kudi kamar ba gobe.
Watansu hudu cur da zuwa legas Luba ta fita fit a ran Ilu ilu. Shi lokacin ma hangen wata yarinya Bianca yake. Bai yi kasa a gwiwa ba ya tunkari Luba kan sa tsaye da batun ta bar masa daki dan zai kawo sabuwar yarinyarsa. Kan Luba ya kulle ta tsaya tana yiwa ilu ilu kallon tsananin mamaki . Idan ita ba ta ce za ta rabu da shi ba, har shi ne zai koreta saboda wata basamudiya can!
Ta karewa dakin kallo ta ga yawancin abubuwan ciki ma ita ta saya da kudinta. Yana gama fadin abinda zai fada ya wuce bandakin tsakar gida yana fito ya fara wanka. Takaici ya kule ta har ta raya ma ranta za ta nunawa Ilu ilu ta fi shi bariki. Ta tattara abun da take so ta sa a yar jaka da kudadenta. Kawai sai ta cinnawa dakin wuta ta gudu abunta. Ba ta zarce koina ba sai gidan hutawar DPO.
Da kyar Ilu ilu ya sha da taimakon makwabta da suka kawo caffa har wutar nan aka samu ta mutu. Hakan ne ya sa ya baza mutanensa neman Luba ko a ita ko a shi. A rashin saninsa Luba na boye cikin gidan shakatawar DPO tana sha’aninta. Washegari kuwa ya sai ma ta tikitin jirgi zuwa kano yace idan bincike ya lafa zai biyo baya.
Gaban Luba ba ko dar ta shiga unguwarsu ta Birget ta kuma nufi hanyar gidansu da matsattsen siket din ta da daurinta mai tocila. Baban yara ya hau kanta yake jibga kamar an aiko shi ya ce sai dai ta bar ma sa gida, Luba ko gezau.
Da kyar aka kwace ta ta shiga dakin uwarta ta yi mata gashin ruwan zafi. Washegari ta danka wa yayanta Iro wasu ‘yan kudade a cikin wanda DPO ya sallameta da su ta ce ya siyo wa Baban yara yadudduka da takalmi sau ciki. Ba ta tsaya anan ba ta bayar aka siyo kayan abinci kala kala aka rabawa kowa. Tun ana jin daga muryar baban yara sai kuma aka ji tsit!
Iya Tamadi tun tana korafin ta tozartata da ta ga irin kudaden da ta zo da su kuma take kashewa yan gida sai tayi kus, kar ta ja zancen ya zamana ba rabonta.
Duk yawan kudi idan dai ba kara nemansu ake ba to zasu kare, haka ce ta faru ga Luba. Anan sai ta fara tunanin mafita ta ga dai wannan zama haka ba zai fissheta ba.
Kwatsam rannan sai ga Hajiya ‘yar sakkwato wata aminiyar iya tamadi da suka yi ‘yanmatantaka tare. Hajiyar ta dade a Saudiyya don tun lokacin da aka ma ta auren fari ta kaso auren ta gudu can. Ta kawo ziyara gida Najeriya ne sai ta biyo gidan iya tamadi a sada zumunta.
Daga zuwanta kuwa tayi ido biyu da Luba ta ce
” Tamadi shin ina kin ka samo wagga budurwa tsaleliya?”
Iya tamadi tayi dan murmushi ta ce
“Diyarki ce fa Lubabatu” .
Hajiyar tayi salati ta sanar da Ubangiji ta ce
” Luba ce tayi girma hakan ga? Hala ba ta kai ga aure ba?
Iya Tamadi ta kwashe labari kaf ta gaya ma ta. Ita kuwa Hajiya ta ji wani sanyi a ranta, hanyar neman kudi ta samu. Ta ce
“Ke mi ya kai ga damunki? Ai diya mace ita ajjari. Ki ban ita kawai mu tahi Saudiyya. Wallahi idan Allah ya bissheta ga sa’a kya sha mamakin arzikin da zata yo ga can”
Iya Tamadi ta riki baki ta ce
“Saudiyya? Mu ina muka ga arzikin zuwa can muna fama da kan mu?”
Hajiyar ta murmusa ta ce
” Ke dai bammin wuka da nama hannuna ,ai ni yaruwa ni dauke ki. Lubabatu diya ta ta. Ke dai bari a ji ta bakinta in ta yadda sai mu tahi ayi ma ta fasfo da biza. Zuwa sati biyu sai in sayi tikiti mu tahi”.
Da aka tuntubi Luba da zancen dama zani ce ta tarda mu je mu, ta ce ta amince. Shi kuwa Baban yara ji yake Luba ta zame ma sa nauyi, tana jawo ma sa zagi a unguwa sai ya ji kamar ya rabu da kaya. Haka kwanaki suka cika aka gama shirye shirye Luba ta daga sai Saudiyya.
MASU ƁUKATAR A TALLATA MUSU HAJOJINSU ZA SU IYA TUNTUƁARMU TA LAMBOBIN 07045308523 MUN GODE
