Search
You have no alerts.

    MASU ƁUKATAR A TALLATA MUSU HAJOJINSU ZA SU IYA TUNTUƁARMU TA LAMBOBIN 07045308523 MUN GODE

    Harabar cikin club din na Luoisiana babu haske idan ka cire jajaye da korayen fitilu masu kawowa da daukewa wanda aka fi sani da “disco light”. Kowa harkar gabansa yake yi.
    Masu rawa nayi, masu shan taba ko wiwi , masu kwankwadar giya kowa na aikatawa daidai da halayyarsa.

    Wasu kuma da suka daukin hakan karancin cinyewa suna zaune a VIP a wasu kalar kujeru masu hade da tebura, suna hirarrakin da ya shafesu tare da shan abunda yayi daidai da raayinsu.

    A wata ‘yar kusurwa kadan da babu mutane wata mace ce a zaune ita kadai. Kallo daya za kayi ma ta ka san wayayyiya ce a bariki. Ta sa wata riga mai kama da ta bebin roba iya gwiwa, gashin izgar dokinta ya ziro har kafadunta.

    Ba ta cewa kowa kanzil ba wadanda suka tanka fa ma sun gaji sun tafi. Ba ta da wani aiki sai zukar taba don har ta kusa tashi da kwali daya a a tsawon zamanta.

    Ta kuma jan tsaki a karo na ashirin ba daya, a rayuwarta ta tsani jira sai dai a jira ta shi ya ta ta kagu. Ta jefar da kwanson tabar da ta shanye ta janyo wani karan ta kyasta,zuka daya tayi ta ji an janye daga hannunta.

    Cikin tsanannin mamakin son ganin wanda ya isa ta dago kai tayi ido biyu da wani rusheshen mutum mai uban tumbi. Ya saka wani burgujejen wando tiri kwata da wata katuwar riga, ya dora hular inyamurai a ka.

    Ya zuki tabar ya fesar ma ta a fuska kana ya ce

    ” Baby girl sunana tobacco kin ga kuma ban miki adalci ba a ce ina raye na bar ki ke kadai kina tayar da hadari a gizagizai”

    Ta dan nisa ta jingina da kujerar da take zaune ta zuba masa ido. Yana murza hannayensa ya ce

    ” Gaskiya ana sanyi a garin nan anya ma kina jin sanyin nan kuwa?”

    Bata kula ba sai ma tace da shi

    ” yaya aka yi ka gane ni?”

    Yayi wani guntun murmushi ya ce

    ” kina sanye da fuskar ‘yan wasan karta”

    Ta yamutsa fuska don bata gane ba ya ce

    ” poker face”

    Ta gyada kai, ta gaji so take a wuce gurin. Shi kuma sai taga ya daga hannu ya yafito sabis na club din ya fada masa irin kalar giyar da yake so ya kawo masa aka kawo. Ta ga an rubuta blue crystal ba ta taba ganin irinta ba, ta basar wannan ba damuwarta ba ce.

    Ya zuba a tambulan ya kwankwada sau daya, watakila wannan ne maganin sanyin da yake bukata. Maganar shi ce ta katse ma ta tunani da ta ji ya ce a tsaurare

    “Ina sakona?”

    Tayi masa kallon tsaf, sannan ta zuge jakarta ta zaro wani nadi a takarda a farar takarda. Ba ta mika ma sa ba sai ta ajiye akan tebur. Ya sa hannu a aljihu ya jawo wata siririyar ambulan ruwan kasa ya ajiye a daidai saitin da ta aje sakon nasa.

    Ta sa hannu zata dauki ambulan din ya kai hannu ga danne ya ce

    ” not so fast..baby girl..not so fast”

    A tare suka janye hannu. Sai ya dauki wannan farar takarda ya bude ya kai hancinsa kamar mai shakar hodar iblis. Ya dandana da bakinsa ya jinjina kai ya ce

    ” komai yayi kyau”

    Ya zira a aljihu ya mike. Ya dauki kwalbar giyarsa da bai karasa ba yayi gaba abunsa ba tare da ya waiwayeta ba.

    Ta dauki ambulan din. Kaurinta ya sa ta san ba kudi ne dan kadan ba. Ta jefa a jaka. Bai fi minti biyar da fita ba ta janyo waya kirar samsung ta danna wata namba, a ringin na uku aka dauka. Ta ce

    ” ya taho”

    Ta goge kiran hade da kashe wayar gabadaya ta jefa ta a wani kwandon shara. Sa’annan ta cigaba da kada kafafuwanta.

    Fitar tobacco ke da wuya ya shiga motarsa ya dauki wata barauniyar hanya da sai wanda yayi wa Abuja sani bana wasa ba. Bai tsaya a koina ba don ya san tsayuwar bata kamace shi ba kuma hanyar akwai karancin checkpoint.

    Yayi hanyar fita daf da Nyanya aka tsayar da shi a wani checkpoint da ya ji bai aminta da shi ba. Dan gajeren dansandan mai lubu lubun kumatu ya haske tobacco da tocila ya ce

    “Oga daga ina?”

    Tobacco ya kara mazewa kokari yake kar giyar da ya sha ta dauke shi ya tapka kuskuren da zai jawo ma sa asarar nairori. Ya ce

    ” daga cikin gari”

    Dansandan ya cigaba da dallare masa idanu ya ce

    ” At this time of the night? Its already past 2am”

    Tobacco zai bada hakuri ba don ya so ba sai don uzurin da ke gabansa. Dan sanda ya dallaro kwalbar giyar da tobacco ya taho da ita.

    ” kana tuki da daddare sannan kana drinking. Ba ka san cewa wannan biyun manyan offense ba ne? Za kayi bayani a station”

    Nan tobacco ya dago bakin zaren bai tabbatar da hakan ba sai daya dauki gudar dubu daya ha mannawa dansandan a hannu ya ki karba. Sai ma ya kara da cewar

    ” you are under arrest for late driving, drinking while driving and bribery!yanzu zamu wuce da kai station”

    Tobacco ya gane shune ta masa wannan karamar yar iskar, za kuwa ta gane bata da wayo. Kafin dansanda ya kira abokin aikinsa su shigo motarsa su tafi tare yayi wuf ya dauki wayarsa ya danna speed dial 1. Ringing daya tak tayi aka daga a daya bangaren. Ya ce

    ” Get her!”

    Bayan fitar tobacco ne tayi odar giya katamar kwalba daya bata tashi daga gurin ba sai da ta kwankwade. Ta fara jin ga kamar a sararin samaniya take. Ta dauki jakarta ta fara tafiya kamar mai tatata zuwa hanyar fita.

    Wani ya zo ya cakume ta yace

    ” hey make i carry u go home?”

    Ta wancakalar da shi tana ji yana aiko ma ta da zagi har da “ashawo”. Wani tsaki ta ja da ta tuna sai ta tsaya taren mai tasi. Wata zuciyar ta ce mata ta tsayar da lift kawai wanda uwarsa ta laance ma sa kawai ya dauketa.

    Tana fitowa kamar jiranta ake wata mota baka kirin mai tinted glass ta sha gabanta, wani shirgege mai kyalle a fuska ya damke ta. Za tayi ihu ya toshe bakinta ya watsa ta cikin motar kamar kayan wanki. Suka figa kamar zasu tashi sama.

    *******************************
    ” Hello….baby girl”

    Wata kakkaurar murya marar murmushin imani ta ce da ita. Hakan ya fara sawa ta dawo cikin hankalinta saboda ta kwana bata san inda kanta yake ba.

    Ta bude fuskarta a hankali har sukai tangararau suka sauka akan faskaceciyar fuskar tobacco. Ya sakar mata wani murmushi wanda kana gani ka san ka kade har hanjinka. Fuskarta ta nuna mamaki cikinta ya bada kululu ya ce

    ” kin yi mamakin gani na ko? Bayan an hada baki da ke an min cunen yansanda ko? Alhalin na fitar muku da hakkinku ba tare da ragin ko kwandala ba!

    Ya nuna kan sa da danyatsa rai a bace ya ce

    ” Ni tobacco na fi karfin kowane dansanda don a tafin hannuna suke. Ko awa daya ban yi ba na fito saboda mu ne garin nan. Ko da yake ba zama nayi anan don in karanto miki labaran kasa ba”

    Ya shako mata wuya kamar ba zai bar ta da rai ba ya xe

    ” who do you work for?

    Ba ta taba jin kamshin mutuwa ba irin na ranar. Ya wancakalar da ita ya sa kafa ya shure ta. Ya dunga kwallo da ita har sai da ta sume.

    ” wannan daga gani za tayi taurin kai” ya ce da wani shirgege kamarsa ” watsa mata ruwan sanyibta farfado”

    Watsa mata ruwan sanyin da aka yi yasa ta dawo daga duniyar cankacakare, ita bata rayu ba ita bata mutu ba. Bata taba shan duka irin na yau ba. Lallai ta yarda bariki alalar gero don kuwa yau ta kwabe ma ta.

    A cikin wannan taraddadin ta dubi tobacco a marairaice ta ce

    ” Na tuba, na bi Allah na bi ka. Ka rufa min asiri’

    A fusace ya ce

    ” Ba ki bi ubanki ba kika fito yawon duniya sai ni za ki bi!! Zancen banza kawai..stupid..idiot fuck you!

    A daga ta sama cancakat ya ce

    ” Ina miki tambayar karshe, wa ya turo ki wa kike yiwa aiki?”

    Bata ba shi amsa ba. Kawai sai ya sake ta ta fadi rikica.

    Ya ce a kai ta wani daki. Mai tsaron dakin ya dube ta yace oga ya baki awanni ki bayyana wanda kike yiwa aiki..if not..yau za ai bako a lahira!

    Ta karewa jangin dakin kallo ta ji fuskarta ta ma ta nauyi wanda ta san ba zai wuce dukan shan gishirin da tobacco ya mata ba. Daga nan a karo na farko na rayuwarta ta fara jin fargaba. Fargaban barin duniya ba tare da ta tsinana wani abu kwakkwara ba.

    Daga baya ta samu arzikin wani abinci a wani yasasshen kwano ta ci don kar yunwa tayi ajalinta. Tobacco ya shigo wannan karin ma sanye da burgujejen wando da riga sai ya dora hula mai malafa. Ta gane hakan dai kamar shigarsa kenen. Ya tsugunna a gabanta ya dafa kafadunta ya ce

    ” Baby girl..are you ready to talk?”

    Hawaye ne suka fara zuba mata kamar ruwan fanfo. Wani takaicinta ya kama shi. Shi za a nuna wa taurin kai? Ya fito da pistol ya dana mata a makogoro. Kawai sai ta saki fitsari saboda tsoro.

    ” you have 2 hours ki bayyana kan ki da wadanda suka turo ki. Idan ba haka ba sai na sa bindigar nan na tarwatsa miki kwakwalwa. Su inna da baba da suka tsine miki sun huta nemanki! Tick..tock..” ya fita abunsa

    Wani tunani ya zo mata. Da alama fa anan za a kasheta a yar da mushenta. Ta yi ta tsinewa son kudinta da ya kawo ta halaka. Ta yanke hukuncin fada za tayi kawai. Wata zuciyar ta ce ma ta ko kin fada ko baki fada ba kashe ki zai yi.

    Awa biyu ta kusa cika wani tsamurmuri ya shigo yana mata nuni da lokaci ya kusa. Ta ce

    ” ka ce da shi ya zo zan yi magana”

    Ya shigo rai a bace ya ce

    ” ina saurarenki”

    Zata tsaya kame kame ya tsinka mata mari. Zai kara ma ta kenen suka ji wani kara kamar tashin bomb. Saboda tsananin firgita bata son lokacin da ta fyalla a guje ba ta fada wani bayan drum. Wani ya shigo a firgice ya ce

    “Oga we are raided..an zagaye mu”

    Ba su bi ta kan ta ba suka fita a guje. Bata jiyo komai sai karan bindigogi. Can bayan kamar minti talatin sai ta ji dif! Kamar daga sama ta ji aka doko kofar inda take ta ji an fara tafi taf taf. Wata murya ta ce

    ” fito matsoraciya Luba, kin ci kudinki”

    Ya fara kwantsama dariya hahaha. Ta fito tayi ido biyu da “Roller” anan ta tuna abunda ya faru wata daya daya wuce.

    *****************************

    Wani maneminta ne a kano da ya fara koya mata shan tabar wiwi ana ce masa Rabs. Dan yaro ne marar mafadi kamarta watarana suna aikin shaye shayensu yace ma ta.

    ” wani oga na ne ya ce na nema masa yarinya ta ajiyewa a gaban mota ba wacce ta fadomin a rai sai ke.”

    Ta daga kai ta kalle shi idonta luhu luhu ta ce

    ” Ni? Kai ko kishina ba ka yi?

    Ya yamutsa fuska yace

    ” Ke dalla malama ana maganar samun kudi wa ke ta kishi? Uwata ta ce ke?”
    Ta share shi ta san ya fara tafiya kan ba daya ba. Ya karasa da

    ” bari in rabu da ke idan kin ji jakar ta miki sakwa sakwa kya neme ni”

    Ba a wani dade ba ta neme shi kuwa ya dauketa ya kaita Abuja ya hada ta da Roller. Wani daniskan dan cinikin kwaya ne da ya kasa kamuwa. Ya shiga kashewa Luba kudi har ta ji ina ma tun farko a Abuja take. Dama haka ‘yan Abuja suke holewa?

    A wajen yawon shakatawarsu ne rananan ya ce ma ta

    ” Ni kuwa akwai wani aiki dana ke so ki min”

    Ta ce “ina saurarenka”

    ” Ina da wani abojin hamayya da a ke kira tobacco. Ko da yake gaskiya da aminina ne neman kudi ya sa muka yi baram baram. Harkar tamu dai duk ta kwaya ce.

    A hankali tobacco ya zame ya fara production a karan kan sa. Yana fitar da wasu kwayoyin da shi ya hada da kuma syrup na shi na kan sa, ba karamar riba yake ci ba. Ya siye jami’an tsaro ya siye gwamnati.

    Abinda har yanzu kowa bai sani ba shi ne ina ne tobacco ya gina empire din sa, plant din sa inda yake production yake kuma boye makudan kudade da yake tarawa. Don ba banki yake kaiwa ba gudun kar a kama shi.”

    Luba ta katse shi ta ce

    ” Ni ban gane ba. Ta ina labarin nan ya shafeni?”

    Yayi gajeran murmushi ya ce

    ” ina ga dai baki cika wata tara a cikin gyatumarki ba ko? Na ga kina da garaje”

    ” Barin ciki na tayi” tace da shi a kufule ” ka ga karewar garaje kenen”

    Ya cigaba ba tare da ya tanka ta ba

    ” A halin da ake ciki yanzu Tobacco yana kan production din wani syrup na maye wanda in har aka sake ya shigo kasuwa to kashina ya bushe. Don mahaukacin kudin da tobacco zai yi zai iya sawa a kama ni a manta da labarina.

    Abu daya kacal yake bukata. Wata hoda ce da ake kiranta DZT ba zan gaya miki ainihin sunanta ba saboda tsaro.

    DZT ba a shigowa da ita saboda an sanya matakan tsaro masu tsanani. Idan har zai samu hodar nan ko da 5g ce to zai iya producing wannan syrup din iya adadin da tashi daya zai zama biloniya. Maganar da nake miki yanzu ni ina da DZT”

    Ta kalle shi baki a washe ta ce

    ” To ai matsala ta kare sai kayi amfani da shi ka hada maganin kayi mahaukacin kudi”

    Ya girgiza kai a hankali ya ce

    ” Luba DZT kawai gareni bani da formular din wannan syrup ban san da me da me ake hada shi ba. Kin ga DZT ba shi da amfani kenen.” Ta ce

    ” To kai da can menene dubararka”

    Ya ce

    ” Ke ce zaki kaiwa tobacco DZT”

    Ta kware da lemon da take sha ta ce “ni? Kai menene ribarka idan ka dauka ka ba shi? Ina ce abokin hamayyarka ne”

    Ya ce

    ” An zo gurin. Ai shigo shigo ba zurfi za muyi ma sa. Mu kira shi mu ce muna da DzT tunda nema yake ruwa a jallo. A tsadance sai ki dauka ki kai ma sa. Daga nan sai muyi ma sa cunen yansanda. Na san ba zai fi awa ba zai fito kuma daga nan zai sa a kama ki. Mu kuma duk abunda ku ke muna da ido.

    Idan ya sa aka daukeki ba shi da inda zai kai ki sai hideout din sa. Zai bi duk wata hanya don ki fada ma sa wanda ya turo ki. Kiyi kokari kar kiyi breaking. Mu kuma dama mun tura dan leken asiri, shi zai fada mana hanyar da kuka bi wacce za mu bi ku. Zamu gano hideout din. Sai mu mamaye shi.

    Mu sace duk wasu takardu. Da formular da kudade. Ke kuma mu fito da ke. Wato dai za ki zame mana “bait ne”. Irin tsutsar nan da ake sawa a jikin qugiya a kama kifi..hahahaha”

    ” kafin nan su kuma sun saka kaina gabas sun yanka sun zuba jinina a kokuna sun shanye. Kai kuma sai ka zo ka ceceni ko? ” Ta fada tana kalonsa a sakarce

    Ya ce

    ” komai akan timing za a yi. Ke dai kar ki sake kiyi breaking.”

    Ta dauki jakarta tana mai cewa

    ” waziri aku na saurari magana jarinka tun daga na daya har na uku. Lokacin tafiyata yayi” ta fara tafiya tana barin harabar gurin. Ya ce

    ” Ko da magana jarin tawa tana dauke da zunzurutun kudi har Naira miliyan 2?”

    Ta juyo ta dawo ta zauna a kujera ta ce

    ” Ina jin ka Roller, kamar kana bani labari”

    Ya ce

    ” ki yi fata Allah ya rufa miki asiri irin rufin da yayi wa dogo mai gyada”

    ” Sama ‘ya’ya kasa ‘ya’ya ” ta ce da shi

    ********************************

    Ta dawo daga tunaninta bayan ta yi ido biyu da Roller da yake tafa mata. Ta ce

    ” Duk ba wannan ba ina ladan aikina zan ware? Tun kafin ‘yansanda su zo su karasa ni”

    Ya kyalkyace da dariya ya ce

    ” Ba ki fi ni sauri ba. Kudinki ai a akawun din ki suka kwana saboda raahin tabbas din rayuwarki. Kin ga gyatumi ya samu abun juyawa ko da kin sheka barzaku”

    Ta angaje shi ta wuce. Ya cillo mata mukullin mota da damin dari biyu ta cafe. Ya ce a tsaurare

    ” Ki bar gari. Kar ki ce ban gaya miki ba. Idan komai ya lafa zan zo in karbi motata.” Ya duba agogon hannunsa ya ce

    ” karfe 6 na hamma yanzu..Run don zaki dade baki ganni ba”

    Cikin sauri suka nufi motar ta mata key ta leko ta taga ta ce

    ” Ina tobacco din?”

    Yace

    ” Kanin uwarki ne?!! Yayi ta kan sa keme kiyi ta kan ki”

    Da haka ta bi su a baya suka fitar da ita kan titi. Sai yanzu ta amince babu wanda zai gano hideout din tobacco saboda tsananin kasurgumin dajin da ya je ya boye.

    Ta hau kan titi ta dauki hanyar titin da zai kai ta kaduna tana fyalla gudu. Lallai ta yarda dare daya Allah kan yi bature. Yau ga ta da zunzurutun kudi har naira miliyan 2 cas! Lallai su Hindu da Rukky za su sha labarai. Ta san cikin daya biyu ko ta riga su isa ko su riga ta. Ta san ma zasu riga ta.
    MASU ƁUKATAR A TALLATA MUSU HAJOJINSU ZA SU IYA TUNTUƁARMU TA LAMBOBIN 07045308523 MUN GODE

    Note
    error: Content is protected !!