Duniya ta – Chapter Nineteen
by NadminMASU ƁUKATAR A TALLATA MUSU HAJOJINSU ZA SU IYA TUNTUƁARMU TA LAMBOBIN 07045308523 MUN GODE
Kwance yake akan wani katafaren gado da aka lullube da wani lallausan zanin gado. Ji yake kamar yana bacci kamar idonsa biyu. Irin baccin nan da ka kan yi idan damuwa ta yi maka yawa, gabanka na faduwa fat fat.
Kafin wani lokaci ya ji kamar yana kasa numfashi. Sai a lokacin ya lura ashe wuta ke cin dakin.
Wani abun ban al’ajabi uku ne ya sa shi cikin dimuwa.
Na farko baya ganin hasken hutar illa tsananin zafin da yake ji. Na biyu wani DUHU ne ya mamaye shi ba ya ko iya ganin tafin hannayensa. Na uku ya kasa tashi ya gudu daga wannan duhun da ke mamayarsa.
Wannan wani irin al’amari ne?
Kamar babu iska…
Kamar ba ya numfashi…
Kamar baya gani..
Sai gata ta bayyana a cikin duhun, siffarta ce kawai kuma don ita ma bata tare da haske. Ta mika hannu kamar zata taimake shi. Amma sai duhun ya mamaye da ita!
Shin yaushe haske zai bayyana? Abinda yake tambayar zuciyarsa kenen.
Almustapha ya tashi firgigit daga wannan mummunan mafarki ya jike da zufa sharkaf! Har yanzu ya kasa daina jin zafin nan, duhun nan ya matukar ba shi tsoro. Me ke faruwa wai?
Wacce ya gani a duhu tare da shi, ko a mafarki sai ya gane surarta RUKKY ce!To me ya kawo ta irin halin da yake ciki?
Watakila hakan na da dalili na yarda ya sa ta a rai a ‘yan kwanakin nan. Ya wayi gari yana matsananciyar kaunarta! Kaunar da bai taba zaton ana yiwa karuwa ba!
Yarinyar ta shigar masa rai ta zauna daram dam. Har yakan ji son kamar wani abu ne da aka halicce shi da shi. Ya lura ita ma ta kamu da son sa da kuma tsananin kishinsa.
Dalilin kenen da ko da wasa bai bari zancen aurensa na sirri da Rebecca ya kai gurinta ba. Zata haukace ne kawai a idonta yake kallon kishinsa da take.
To wai a haka za su kare rayuwa? Wai yaushe zai ‘yanta kan shi daga irin wannan rayuwar ta rashin tabbas? Lokaci yayi da zai san abinda yake ciki, shekaru ja suke, kwanaki tafiya suke. Da ya tuna mutuwa sai tsikar jikinsa ta tashi yarr.
Shin ba sharri mahaifinsa ya kulla ba har ya sa yanzu ya fada wannan rayuwar. Shi ba matacce ba shi ba rayayye ba? Kowa ya guje shi harta matansa. Idan ba don shi Almustapha ba yana ga da yanzu ya rube ya lalace sabida wari da rashin kula.
Wani abu ke daure masa kai shi ne, a kullum ya je wajensa a cikin sarkakken harshensa ya kan ce da shi
” Al..mus…tapha…duhu! Duhu shi..mmamaye ni!”
Kamar baya gani amma idanuwansa a bude suke. Haske ya kaurace masa duniya ta juya masa baya. Shin ko shi ne duhun?
Da sauri ya tashi ya dauro alwala ya fara jero sallolin nafilar da ya manta rabonsa da su. Ya san laifuffukansa dayawa, ga shi nan kullum sai tsunduma kan sa yake cikin sabuwar matsala.
Ko da ya je ofis a ranar tunanin bai bar zuciyarsa ba. Al’amarin Rebecca ya daure masa kai. Ya tuna ranar da yayi ido biyu da dansa, sai da ya ji kwalla ta tarar masa. Kamar an tsaga kara.
Shin wannan bai zame masa izina ba? A ce duk zamansa da tsohuwar matarsa khairiyya bai taba samun da ba sai akan karuwa? Wai shin ana yiwa Allah wayo?
Sai ya ji yana so ya kaunaci yaron amma idan ya tuna wai shi ya haifi shege sai gabadaya ransa ya dagule. Kiri kiri ta hana a taho da shi aka bar shi ahannun mai kula da shi acan kadunan wai ita takamar kar ya cutar da shi. Shi ma dai ya ga fa’idar barinsa don hakan ma ba karamin taimakawa zai yi ba wajen adana sirrinsa.
Me zai faru idan mummynsa ta ji? Ita mai mutane mai kawaye na zarra? Ai ya gama jawo mata abun kunya cikin mutanenta. Hakan sai ya zame ma ta abun gori. Balle kuma jama’ar duniya!
Baya son zancen nan ya bullo, dalilin kenen da yake lallaba Rebacca kafin tarzomar siyasa ta kwanta ya dauki mataki a kanta.
A halin da ake ciki tana zaune ne a gidansa tayi kane kane. Ta kuma uzzura masa da cewar ko yaya ne sai ya kira aminansa makusanta ko da guda 5 ne an yi wata dinner ta nuna aurensu. Wai ta san halin musulmai sarai, idan ba shaidu aka ajiye ba yanzu wani abu ka iya faruwa a ce ita ba matarsa ba ce.
Zancen da ya kawo cece ku ce tsakaninsu. Daga karshe ya amince ba wai don komai ba sai dan a lallaba a wuce wurin. Ya matukar gajiya da matar amma da sannu zata gane ko shi wanene.
Wannan yarinyar Rukky dole ne su zauna su san abinda suke ciki.
Watakila ya kamata su shiryu su daina zaman haram
Watakila ya ce tayi istibra’i ta koma gaban iyayenta
Watakila ma ya bata jari yana ga hakan kamar zai tserar da ita cigaba da irin wannan rayuwa
Watakila ya aureta!wa ya sani??
Watakila shi ma ya tuba!
Da alama irin duhun da ke neman mamaye mahaifinsa ne ya doso shi. Ba zai yi karshe irin na mahaifinsa ba ya tabbatarwa kan sa.
Kafin wani mugun abu ya faru da rayuwarsa zai tuba. Bari tarzomar siyasa ta kwanta.
Iya yanayin tunaninsa kenen, hangensa da hasashensa bai wuce na yana da cikakken lokaci ba.
Haka mutanen duniya suke kamar Almustapha!
Sukan kididdigi rayuwarsu tamkar su suka tsara ta.
Sukan hangi tuba a wani abun da ka zo musu da sauki, da ka zo musu a lokacin da suka so.
Mai karatu shin ko ka san illar lokaci?
Shin ko ka san adadin kwanakin da suka rage maka a duniya?
Shin ko ka tuba?
*********************************
Yara ne guda biyu dukanninsu ba zasu wuce shekara 13 ba. Suna zaune ne a kan benci a wani filin kwallo da ake horar da yara. Dan farin mai suna fahad ya cigaba da daura takalminsa na ball idanuwansa taf da kwalla da kyar yake daura takalmin ma. Daga gani yana cikin tashin hankali.
Abokin nasa Abba ya dafa shi ya ce
” wai me ya sa kullum za ka tafi sai kayi ta kuka?”
Maimakon yaron ya ba shi amsa sai ma ya fashe da kuka. Abinda ya tayar da hankalin Abban shi ma kwalla ta taran masa yana lallashin abokin sa. Daga karshe fahad din ya samu ya ce
” Mamanmu ce fa ta tafi ta bar mu. Kullum idan muka koma gida bata nan. An dade sosai kullum bata nan.Ta ce wai babanmu ne ya kore ta”
Wani tausayi ne ya mamaye zuciyar Abba. Da ya tuna yanda yake kuka shi ma lokacin da mamansa za ta tafi sa’ilin da suke gidan Hajiya uwani. Kwata kwata baya so mamansa ta tafi, ya fi son lokacin da take zama da su shi da kanwarsa Asiya.
Sai ranar nan ta zo ta tafi da su. Suka je wani gida mai kyau. Sai ya koma ba sa kwana da yunwa, suna zuwa sabuwar makarantarsu kuma suna da kayan wasa kala kala. Sai yake ta murna shikenen zasu zauna da mamansu yanda suka saba. To amma sai dai me?
Sai yayi kwana da kwanki bai ga mamansu ba. Asali ma wataran tana cikin gidan da suke amma ba sa ganinta. Sai dai yana ta ganin wasu suna zuwa masu manyan motoci kuma mamansu tana ta musu dariya.
Ranar da ya ga wani da mamansa sun fita ya zata cewa babansa ne. To amma mamansu ta ce babansu ya mutu kuma idan an mutu ba za a dawo ba. To shi waye???
Yana son mamansa sosai. To amma akwai wani abu da yake ji game da mamansa da ba zai iya gayawa kowa ba.
Yakan ji a gidan kakarsa hajiya uwani tana cewa wai mamansa bata da kirki. Wai kudinta na haram ne. Su Anti safara sun ce wai mamansa yar iska ce. Yan unguwarsu suna kiran mamansa wani suna..ko me? Ya manta.
Sai ya ji ya fara jin kamar baya son mamansa. To me yasa yaje jin haka? Me yasa?
Da ya tuna yanda yake ji idan mamansa bata dawo gida ba sai yaji tausayin abokin sa fahad ya lullube shi. Sai ya ce da shi
” kayi hakuri. Ka dunga yin addua wataran zata dawo. Ni ma babana da mamanmu tace ya mutu ina masa addua”.
Fahad ya share hawayensa. Ya ce
” ka san me? mamana ta ce wai wata ce ta raba mu da babanmu. Ita ce ta sa babanmu ya kore ta. Wai sunanta karuwa!”
Sai da gaban Abban ya fadi. Shin ba wannan sunan ne ya ji ana gayawa mamansa ba? Amma ta ce wai karya ne ba sunanta ba ne. Amma daga ji ya san ba abu ne mai kyau ba. Sai yayi shiru yana tunani har fahad ya ce masa
” To kai me yasa ba ka san komawa gida, sai ka wuto nan bayan ba koyan kwallon ka ke yi ba?”
Abba yayi shiru sannan ya ce
” Kawai gidan baya mun dadi ne. Saboda kullum mamana bata nan”
Sai fahad din ya ce masa
” kai ka ma ji dadi ai ko bata nan tana dawowa, in ta dawo zaka ganta”
Abba ya kalle shi a mamakince ya ce
” wa ya gaya maka? Wataran a wajen aikinsu take kwana ai! Iya ce ke kula da mu. Rabe ya kai mu makaranta”
Fahad din yayi shiru yana tunani sannan yace
” Au har kwana mamanku take a aiki? Ko likita ce? Mamansu abokina Ridwan ma likita ce tana kwana a asibiti”
Shiru Abba yayi. Bai san me zai ce ba. Shi dai ya san mamansa ba likita ba ce don bata allura. Amma..?
Sai kawai ya bawa fahad ansa da
” Ban sani ba wallahi”
Sai suka mike gabadaya. Zasu zauna a teburan da ke gaban wajen. Anan ne idan aka zo daukanka za ka gani. Suna tafiya a hankali fahad ya ce
” Babanmu ne zai zo daukana yanzu ko zaka zo mu ajiyeka a gida? Amma fa tare suke zuwa da wannan mai suna karuwan data kori mamanmu. Babanmu yanzu baya son mu kamar da. Da nace matar babanmu ce sai mamanmu tace wai bata auri babanmu ba. Ka san me mamana ta ce? Wai wataran sai ta kashe wannan me suna karuwan! “
Wani irin abu Abba ya ji marar dadi. Shi ma sai ya ji ya tsani matar yana kuma tausaya mamansu fahad. Sai kawai ya ce
” Ba komai Allah zai saka wa mamanku”
Suka zauna a bakin gate din gurin. A lokacin motar baban Fahad ta iso gurin. Ya ce
“Ga babana nan ma ya iso ka zo mu sauke ka”
Suka doshi motar. Zaune yake a motar da wata mace tsaleliya a gaba. Sun iso motar kenen, juyowar da za ta yi Hindu tayi ido biyu da Abba dan ta. A firgice ya ce
” Mama”!!!
**********************************
” Ahap! Wa billahillazi Rukky tunda uwata tayi kuskuren satalo ni duniya ban taba ganin kifin rijiya kamar ki ba” cewar ‘yar modu ” yo mace har mace da ke ,son kowa bakinciki da haushin wanda bai samu ba, abun hassadar wanda kika subucewa amma namiji dan babarsa ya miki haka! Kwarankwatsa dubu sukari ko ni mace ‘yaruwarki lalacewa nake a kallonki ballantana namiji dan hau!sarkin zalama ba! Namiji kenen. Ga abu a hannunka kana hangen na wani! Manta alherin jiya ba , ai sai maza mutanen mu!”
Rukky ce zauna akan kujera mai cin mutum uku. Ta kishingida da wata rigar bacci a jikinta , zuwan yar madu bai sa ta tashi ba ko ta canja daga yanda take. Hira ma suke yi ta aminan juna. Bata da wata masaniya cewar yar modu ne ya kaiwa luba labarinta. Ta dai san kawai yanzu kowa ya san Almustapha na ta ne. Ko ma ya ta same shi wannan ba damuwarta ba ne.
Kawai dai yanzu harkar gabanta take yi tunda dai su Luba da Hindu dai ko lamarinta ba sa shiga. Bai dame ta ba, ita dai idan aka barta da Almustaphan ta to komai daidai kenen.
Jin ranta take fes bata da wata damuwa. Sai take jin kamar duniya ta ma ta kadan ta sha shagalinta. Dama haka duniya ke da dadi? Mutum ya yi abunda yake so a sanda yake so? Ya taka uban kowa! Ga ta ga masoyinta mai zai dame ta? A halin da take ciki ne yar modu ya kawo mata ziyara har gida suna yar hirarsu sai taji zancensa ya karkata wani waje.
Ta zunkuda kafadarta kadan cikin nuna halin ko in kula ta ce
” Au yau kuma ware ranar ka yi ka zagi maza? To kuwa baka zo a daidai ba don ni nan na dauke su ‘yan goyo da zani”
Ya kalle ta galala sai ya kwashe da dariya yana tafa hannu ya ce
” Ahayye nanaye..yau na ga abunda ya isheni. Ana ga annabi kina rintse ido. Yaki ya taso ina ruwanmu da kura? Shi wanda kika goya da turmin zanin kwarankwatsa dubu ya hankada ki rijiya kafa dubu! Ahayye nanaye..Ana tsiya tsiya a bariki..to kinji!”
Sai ta dan tashi ta zaune. Ta san zancen duniya yana bakin ‘yar modu kuma baya kawo zancen karya. To amma ya sa ta a tunani. Ta ce
” wai me ke faruwa ne? Sai wani lauya zance ka ke. Ka fito sak ka fadi kawai abinda ke ranka. Wani abu ne ya faru da Almustaphan?”
Ya ce
” Yaki dai bai kare ba a legas, rikici ake zuuuuqar! Mutane sai mutuwa suke”
Wani tsaki ta ja ta ce
” yo ai ta kashewa mana! Indai ba uwata aka kashe ba ina ruwana”
Yayi sauri ya ce
” Ta kwarankwatsa dubu wannan karin uwar ta ki ma bata tsira ba!”
Ta kalle shi a fusace ta ce
” Ka san me kake cewa kuwa? “
Ya ce
” Yo ba fa sallah nake ba ballantana ki ce nayi rafkanuwa. Jarida ce da ni mai tsada. Iya kudinki iya adadin inpomeshan din da zai marabci kunnuwanki”
Hannu ta sa a wata jakarta nan kusa da ita ta zaro kudi yayi caraf ya amshe. Sannan ya gyara zama ya ce
” Masoyinki Almustapha autan maza, wanda kika goya da turmin zani kwananansa biyar cif da angoncewa. An ce wai ya auri wata arniyar saman dutse”
Wani abu ne Rukky ta ji ya tafi da ita kamar guguwa. Ta ji gabanta ya fadi ras! Cikin wani irin tsananin gigita ta ke kallon ‘Yar modu ta ce
” karya ne! Karya ka ke! Almustapha ba zai taba min haka ba. Ka san irin son da ke tsakaninmu kuwa? To ko aure zai yi ni kadai zai iya aura!”
Ya kalleta galala ya ce
” Au Allah? Au Allah hurul aini cikomakon matan duk duniya! To ko da yaqutu aka sassaka ki ya samfe ya auri wata ba ke ba. Yo da ma bariki ai ta gaji haka. Ka warce a warce maka. To in banda abinki Sukari ba a yin ‘yar warce warce ke kya same shi?”
Bakaken maganganun yar modu ba su dame ta ba, labarin da aka gaya mata ya fi komai daga ma ta hankali. Ji tayi kamar zata haukace, bata taba tunanin tana da kishi ba sai yau. Almustpha ya auri wata ba ita ba? To ina zata saka kanta? Ai sai mutanen gari da makiyanta irinsu luba ma suyi mata dariya. Ji take kamar ta mutu don bakin ciki!
Kawai sai ta ji kuka ya zo ma ta, abun da ta dade bata yi ba. Ta kalli yar modu a gigice ta ce
” Almustapha nawa ne, nawa ne ni kadai! Duk wacce tace zata shiga hurumin nan ta sha mamaki! Wallahi yar modu bazan iya barwa kowa shi ba! Da sannu za su sha mamaki na!”
Ta yi sauri ta wawuri wayarta da alama kiransa za tayi ‘yar modu ya sa hannu ya warce. Ya ce
” ke wawiya. Idan za a kaiwa makiya farmaki a ba a sanar musu. Dirar mikiya ake yi a tarwatsa komai”
Ta kalle shicikin rudu ta ce
” To ni yanzu ya zan yi? Ka san yadda raina ke suya kuwa?”
Ya ce
” shirunki. Ai ni haka nake idan mutum ya mun 10 to bi zatil rasulullahi sai na masa ashirin. Na ji a wata majiya anjima kadan za suyi wani dan taron cin abinci. To kawai bayyana za ki yi kamar mahadi mai karshen zamani ki tarwatsa komai! Ita kuwa annamimiyar ki mata billen Allah tsine uwar mai karya! Kayan sarki ai ba na ‘yan gari ba ne. To kin ji!”
Ta ce
” Ai kuwa ka kawo shawara. Shi ma munafikin da bai gaya min ba ya sha mamaki na. Kowa ya ci tuwo da ni miya ya sha. Na rantse da Allah zan iya yin komai akan gayen nan!”
” shirunki sukari..ai ba kiyi farin banza ba.” Ya sa hannu yana zaro wasu kwalaben syrup da tabar wiwi yana cewa
” Ki sha ki sha kiyi mankas! Sannan ki tunkari abokanan gabarki. Yadda in kika je sai ki zagi uwar kowa! Yo uwarki ce? Yo ko uwar mutum kika zaga yaushe hakan zai dame ki, yaushe ma kika san kin yi? Yo me aka yi da maza inji karya??
Almustapha na zaune a kujerar wani wajen cin abinci mai suna peacock. Kusa da shi Rebecca ce sai wasu abokanansa guda 4. Iya wadanda ya ga zai iya kira kenen.
Komai na rayuwwarsa yanzu taka tsantsan yake yi da shi. Ran sa a jagule yake komai na duniya ba ya masa dadi yin sa yake akan dole. Rebecca nema take ta zame masa kashi a wuya kuma ya rasa yanda zai yi.
Zuciyarsa ta gaya masa ya jure yayi hakuri na dan lokaci daga baya ya dauki mataki.
Abincin da aka kawo a gurin ma bai iya ci ba, rabonsa da ya ci cikakken abinci ma ya manta. Tun kwana biyu da suka wuce ya ke ganin misdcalls na Rukky amma ya gagara dauka. Ya rasa me zai ce, ya san har yanzu ba ta ji ba. Baya so ta ji har ayi a gama, burinsa kenen.
Ko da Rukky ta bayyana a gabansu kamar mahaukacin kare , kan ta kamar ba daya ba saboda kayan mayen da ta sha. Gaban Almustapha ya bada daam! Duk inda hankalinsa yake ya tashi!
Ta kalle shi ta ce
” Ba don kai na zo ba bakin munafiki saboda na san ba yin kan ka ba ne. Amma daga lokacin dana dauki mataki akan ta zaka dawo hayyacinka.
Ta juya ga rebecca da ke mata kallon mamaki ta ce
” Ke! Kida….huma..arniyar kan titi. Ki kama kan ki Almustapha nawa ne ni daya. Kin taba ganin anyi sarki biyu a masarauta daya! Da kika rabe shi ba ki tambayi waccece sukari ba? Dakalin majina ce ni a hau ni a zame na hau mutum na zauna daram! Fitarki daga rayuwar Almustapha tamkar fitarki ne daga cikin uwarki! Shin za ki taba komawa?”
Sai fa yan guri suka zama yan kallo abinda ke kara tayar da hankalin Almustapha kenen. Abin sirri ya koma abin tsiya?
Wohoho ina wuta Rebecca ta jefa Rukky. Kallonta take kawai cikin tsananin mamaki. Karamar yarinya irin haka har ita zata tare ta ta gaya mata maganganun banza kamar haka!
Rebecca ke kallon Rukky da mamaki ta ce
” And who the hell are you? Kin san kina wasa da wuta kuwa? Kin san wacece ni?”
Ke din banza! Arniyar ka..n du..tse! Yar gabar bakin teku! Ub..an ku.turu yayi kankani Alqur..an!
Almustpha da wadannan abokanan na sa ne sukai nufin shiga tsakani. Sai ‘yar modu da ke neman janye Rukky wai zata daki Rebecca.
Rebecca ba tayi wata wata ba ta cakumi Rukky tayi katantanwa da ita ta wurga kan wasu tebura masu tangaraye suka fardi tar…tsa..tsa!
Abun da ya daki zuciyar Almustapha ba da wasa ba.
Kafin ya ankara Rukky ta dauki wata fasasshiyar kwalba anan ta doshi Rebecca da ita tana cewa
” Ni ki ka wurgar?..to ..daga yau..uwarki ma in taga kayana bata taba ba ballantana ke! Yau sai Na Kashe ki! Zan kasheki! Sai naga uban da ya tsaya miki! Ta nufo ta da fasasshiyar kwalbar zata caka mata.
Wani irin wawan juyi Almustapha yayi ya cakumi Rukky a wuya ya shaketa. Ya kura mata kwayar idonsa ciki tashin hankali yake cewa
” Kina da hankali kuwa! Kina da hankali! Kin san me kike yi kuwa!”
Wannan abun ne ya sa tayi sanyi lakwas. Ya cigaba da kallonta a idonta yana ganin wasu irin abubuwa da ya kasa tantancewa. Sai ya ji wani tausayinta ya mamaye shi, wani irin tausayi da bai taba jin shi akan kowa ba. Ko hakan na da nasaba da mafarkin da yayi?
A idonta ya ga wani abu da take kokarin lullubewa.
Akwai wani abu, dole akwai
” Lahaula wala kuwwata ni jikar A’i!” Cewar yar modu ” yau an bani an lalace. Karamar magana ta zama babba. Ke Rukky zo mu bar gurin nan tun kafin ki jawo mana alakakai”
Abokanan hudu su ne suka janye Rebecca. Almustapha da yar modu suka fita da Rukky.
Abinda ya konawa Rebecca rai kenen. Kiri kiri ya nuna Rukky yake so. Lallai da sake, za su sha mamakinta.
Manaja din restaurant din yace su tattara su fitar masa ko kuma yanzu ya kira ‘yan sanda.
Ko da suka je mota Al Mustapha bankawa Rukky balai yake na irin halin da ta nuna a ciki. Sai daga baya kuma ya lallashe ta da ta je gida ta saurare shi.
Kuka kawai take, ji take kamar zuciyarta zata tarwatse. Komai na rayuwarta ya dunga dawo mata kamar a majigi. Yanda ta rasa kowa. Yanzu ma haka zata rasa Almustapha.
Ta dauka haduwarta da Almustpha zai sa ta tuba, zai sa ta fita daga rayuwar karuwanci amma sai ga shi hakan na nema ya subuce ma ta.( ta manta don Allah ake tuba)
A hankali ya cigaba da kallonta tana kuka sai ya dafa kanta ya ce
” I’m sorry, i’m so sorry. Ya kamata ni da ke mu gane wannan rayuwar ba rayuwa ba ce. Ya kamata ki koma gida hakannan. Ya kamata mu san abun yi tun kafin lokaci ya kure mana.
Lokaci na da illa babba, yakan tarwatsa mafarkai ne. DUHUn da ke rayuwarmu ya kamata ya yaye. Kina ga kamar yaushe haske zai bayyana?
Sai ta kara fashewa da kuka. Ta koma gida? Ina ne gida?. Ta san ma yaudarar ta yake. Kamar irin yadda take yaudarar kanta. Da me za a yi da ita? Dattin kazantar zina? Ragowar maza barkatai!
A hankali ta ce da shi
” In..a …ne gida? zuciyata ita kadai ce gidan da zan iya kira nawa!”
Da haka suka rabu yana kallonta a mamakince.
Sai daga baya ya gane dama ba su rabu ba! Dama ya hana ta tafiya! Da wata kila sun samu daddadan labarin adarwa. Watakila da rayuwa tayi kyau.
To amma antaba gujewa rubutacciyar Kaddara?
*********************************
Ko da ta je gida ba ta kara komai ba in banda banke banken kayan mayenta. So take ta manta da komai ta manta da kowa. Sai ta amince cewar babu abinda zai mantar da ita fiye da shaye shaye.
Kowa baya son ta. Ita abun gudu ce. Ba za ta samu farin ciki ba.
Washegari ne ta ga an aiko mata da wani text kamar haka
” I am sorry” Almustapha
Sai ta duba da kyau sai taga kamar sabuwar lamba. Wato canja layinsa yayi kenen. Dama wadancan layukan ko ka kira ma bata shiga. Haka yake da canje canjen layuka kamar marar gaskiya. Ko da yake ai marar gaskiyar ne ta ayyana a ranta.
Sai taji ranta ya ma ta sanyi ashe dai bai manta da ita ba. Dama ta san Almustapha masoyinta ne. Wannan arniyar ce take son raba su, ta ga ma kamar asiri ta masa. Da sannu zata dawo da abunta hannunta.
Sai ta kira sabuwar number ta sa gama ta ringing amma ba a dauka ba. Tana ajiye wayar ne wani sakon ya shigo
” Mu dunga communicating ta sakon text kawai saboda kar Rebecca ta zargi wani abu”
Wani uban tsaki ta doka ta wurgar da wayar. Cikin takaicinsa ta ce
” sakarai matsoracin namiji kawai. Akan mace duk ya bi ya susuce. An ba shi ya sha a ruwa” ta cigaba da harkokin shaye shayenta.
Sai ya zamana har dare tana amsar sakonnin Almustapha da ke nuna yadda yake kewarta. Sai ta daina amsa shi saboda haushinsa da ya cika mata rai. Kira ba zai iya amsawa ba saboda yana tsoron matarsa amma a boye ya cika ta da sakonni. Kai namiji! Sai a bar shi. Wasu ta ba shi amsa wasu ta share shi kawai.
Washe gari da safe ne maigadinta ya shigo mata da sakon wasu jajayen furanni ya ce an ce a bata.
Ta karba roses ne, tana mutuwar son su. A jiki akwai wata ‘yar takarda an rubuta
” with love, from Almustapha”
Nan da nan ta ji ranta yayi fes. Ashe dai da gaske yake. Ita har ga Allah ta dauka yaudara ce kawai irinta maza. Wata zuciyar ta raya mata ko dai ta je ofis din sa? Da ta tuna abun da ya faru jiya sai ta fasa.
Ta tura masa da sakon godiya shi kuma ya bata amsa da kada ta damu. Ya dora da cewar zata ji shi nan ba da dadewa ba.
Ko ma dai yaya ne ta ji dadi. Sai ta fara dokin ranar da za su dawo kamar da. Ko da yake ya fa ce su bar irin wannan rayuwar. Ita ma kwanakin nan ji takeyi komai ya fice a ranta. Tana ga kamar lokaci yayi da zata gayawa Almustapha wacece ita. In ya so daga nan sai ya kwato mata dukiyarta daga wajen iliyasou Tillaberi. Daga nan sai su yi aurensu. Shikenen ta huta da wannan rayuwar marar tabbas. Tunaninta kenen
Da misalin karfe 7 na dare sai ta yanke hukuncin zuwa wani club watakila ma ta biya wa kawarta Reza su je tare. Tana ga kamar hakan zai dan sanyaya mata zuciyar.
Text ne ya shigo wayarta
” Mu hadu a gidana da karfe 8, akwai muhimmiyar maganar da za muyi”
Kawai sai ta daka wani uban tsalle. Duk yadda take tunanin abun ma ashe bai kai nan ba. Ta san ma nunawa Rebecca zai yi ita ba tsaran ta ba ce. Ahap!
Sai ta rushe zuwanta club da biyawa kawarta Reza. Ta shiga ta gyara kwalliyarta yanda kallo daya zai mata ya gigice. Ta dauki yar jakarta da bata rabuwa da kayan shaye shaye tayi gaba zuciyarta fes!
Ta shiga motarta tana bin wata waka turanci ta michael jackson mai suna thriller wacce a ka sa a gidan radio din da take saurare.
Ko da ta isa gidan 8 ta gota da ‘yan mintuna. Kallo daya maigadin ya ma ta ya gane ta don ba bakuwarsa ba ce. Gida ne da ya zama gidan zuwanta. Kwanan nan ne ma bai cika ganinta ba.
Ta wuce ciki ta faka motarta. Kai tsaye kamar gidan ubanta ta shige ciki jin ta take a sama. Jin ta take daidai da kowa.
Falonsa na sama ta wuce ta cigaba da trying layinsa amma ba a dauka. Ta yi masa text da cewa ta iso. Ta samu guri ta zauna. Ko ina hakimar ta ke? Oho wannan ruwanta don ba gurinta ta zo ba.
Ta fi minti talatin a zaune ba Almustapha tana ta kiran layinsa ba ansa. Ba ko tsoro ta fada dakunansa da ba bakin zuwanta ba ne tana duba shi amma baya nan. Sai ta fada kicin anan ta tarar da kuku. Ya san ta sarai suka gaisa. Ta ce
” ina ogan ka ne wai? “
Ya ce
” oga ai bai dade da fita ba”
Sai abun ya bata mamaki to ko ya gaji da jiranta ne ya fita? To amma me yasa ba ya daukan wayarta?
Ta ce
” To madam fa?”
Ya ce
” Madam de inside, for her part”
Kawai tsaki ta buga ta fice.
Gidan nasa da ma wani tafkeken gida ne me sassa daban daban. Shi yasa ma ta shigo gaba gadi saboda ta san sai ta shigo ta fita ma basu hadu da Rebecca ba.
Da ta jira ta ga bai dawo ba, kawai cikin fushi ta fice. Tana ganin wannan ma ai wulakanci ne. Amma zai san da ita ya ke. Ko dai ya fasa son ta ne? Ita ta ma yi zaton ma zancen auren zai ma ta, daga nan ya ce ma ta ya rabu da Rebecca.
Kawai sai ta ji wata kwalla ta tarar ma ta a ido. Ta tsani rainin hankali.
Sai ta wuce motarta a fusace ta shiga ta fice daga gidan. Maigadin na ma ta Allah kiyaye ko kallonsa ba tayi ba ta fice a guje. Idonta har rufewa yake don bacin rai.
Sai ta kama kan ta tana kuka.
Ba shiri ta ciro wata tabar wiwi ta fara zuqa ko ta ji saukin yadda take ji.
Ta yi tafiya kamar ta minti 15 aka tsayar da ita a wani checkpoint da ba ta yi tsammani ba.
Abinda ya sa tayi sauri ta kashe wiwin kenen sai dai kuma har yanzu qaurinta ya mamaye motar. Ta tsaya tana kokarin kama kan ta. Ba karamin aikinsu ba ne yanzu ta kare a cell.
Baqi dogon dan sandan ya leko ta tagarta qaurin wiwi ya dake shi ya ce
” wai wai madam kaurin menene haka? Park well park well”
Ta gangara bakin titi ta paka motar tana jan uban tsaki. Ya kalle ta tsaf ya gane ta sha wani abu ya ce
” madam ina drivers license? Ina takardun motarki?”
A lokacin daya abokin aikin na sa ya karaso. Kaurin da ya ji shi ma a motar ne ya sa ya ce
” ke zamu je station da ke wato ku ne bata gari ko? Kuna shaye shayenku kuna tuki. Sai kun je kun doke wani a zo a ce tsautsayi ne.”
Sai a lokacin ta dan dirice don bata da ko daya. Ya ce ta fito daga motar. Sai a lokacin suka ga shigar jikinta babu marabarta kadan da tsirara. Takaicin ta ya kara kama su. Dayan ya ce ma ta
” you be ashawo ko? Lallai yau kin gamu da gamonki. A cell za ki kwana!”
Bata kawo komai ba don ta san kudi su ne kare magana. Tayi sauri ta zaro ‘yan dubu dubu a jakar da nufin ta basu toshiyar hanci jakar ta fadi ragowar kwalaben syrup syrup da ke cikin jakar da sauran wiwi suka tarwatse a kasa.
Na farkon ne ya ce
” ka gani ko? Ka ga irinta ko? Shi yasa a ka samu wannan patrol din kwannan nan. Saboda yan iskan gari. Ashe ma yar maye ce. Ba drivers licence , ba takardun mota sai kwalaben shaye ahaye a motarki. Wallahi ko waye ubanki yau sai ki je bayan kanta!”
Dama a qule yake, kawai sai ya samu wacce zai saukewa ya dunga zuba bala’i.
Suka ce sai sun caje motar suka fara haska cikin motar ita kuma tayi firi firi da ido ta ji zancen cell. Sai yanzu take bakin cikin fitowarta a wannan dare.
” Madam bude boot! Bude boot!”
Ya buga motar bam!
“Yanzu haka ma dealer ce ke, ‘ya’yan masu kudin nan menene ba za a gani a wajenku ba. Duk zamu iya da ku..yau yau din nan kya gayawa aya zakinta”
Ta saka hannunta na karkarwa ta bude ta wajen mazaunin direba. Na farkon ya haska da tocila.
Akwai tayar mota a ciki sai kuma wani himilin abu an nannade kamar kayan wanki
Na biyun ya ce
” menene wannan? ” a fusace. Jikinsa na raya masa makamai ne, dama kasar na cikin tarzoma, ire irensu ke safarar makamai suna basaja. A haka a haka ake janyo balai a kasa.
Bai jira amsarta ba ya zunguri abun da bakin bindiga ya rikito yana me yaye mayanin.
Abu daya ne tal ya faru ya sa suka ja baya a tsorace cikin wani karaji!
Bayyanar wata shirgegiyar gawa!
” what the hell”!!
Ihun da yasa ta leko boot din motar a firgice ita ma ta leka.
Sai tayi ido biyu da abinda ya sa numfashinta yake neman daukewa.
Shirgegiyar gawar Rebecca ce a boot din motar jini na malala ta wuyanta kamar an yanka rago.
Sai ta daskare a tsaya
Tunaninta ya tsaya cak
Ta nemi yawun bakinta ta rasa
Ta nemi numfashinta ta rasa
Ta gane abu daya. DUHUn rayuwarta ne ya danno. An mata gadar zare ta fada!
Yanzu ta gane. Shiri ne!
Ba da Mustapha take magana ba, makiyanta ne!
Su ne suka yi mata gadar zare ta rufta da ita.
Bata tantance halin da take ciki ba sai da ta ji dansandan ya auna mata hancin bindiga ya na cewa
” You are under arrest”!!
” You are under arrest”!!
” For murder”!!
A kwayar idonta sai ta ga kamar momodou yana kuka!!
**********************************
Sakarai bata da wayo
Na gano abun mamaki ta audu mai roko, an yi haihuwa a garinsu, ana ta gayyar barka
Uwargida ta tashi, ta debi ruwa sai taje ta rangada wanka sai ta dauro leshi
Daya kuma sai taje ta dauro supa
Sai ta kusa da su ta je dauro joji
Kuma ga yal gwaggwaronsu ga murjani
Kuma sannan ga agogo ga takalma
Sakarai bata da wayo
Oh..yaya ni na bi ku?
Yaya ina gyautan nan da kike cincin in sassabe shi in bi ku…
Karan da wayarta ke yi ne ya katse ta daga rawar da take takawa ta wakar barmani coge. Nishadi take ji, Shi yasa ta ware wakar mutuniyar tata a sipikun dakinta tana cashewa.
Ta rage karan wakar ta dauki wayar cikin murmushi tana sauraren abinda na daya bangaren zai ce. Ya ce
” An gama”
Ta murmusa ta ce
” Haka ake so, ka bace bat kamar walkiya. Zan neme ka”
Ya ce
” Aiki yayi kyau, komai ya tafi kamar yadda ake so”
Cikin izza ta ce
” Da sauran kyaun aiki. Da sannu jaridar gobe za ta samar musu da labarin da zai tarwatsa tunaninsu!
Kwatankwacin yadda suka tarwatsa nawa!
Mosoyiyar tasa na cinnawa karnuka!
Gobe Almustapha zai gane dukiya da suna kayan aro ne da duniya ta ba shi, shin ko ya zai ji idan ta buqaci ya maido mata kayanta????
Da sannu zasu gane ni Luba
Kududdufin barkono ce iya kacin mace gwiwa!
Icen kabari ce ni ban fito ba ban koma ba!
Farar kaya nake me hankali ba zai taka!
Jar tsakuwa nake ko an daka ba a casa ba!
Haka tafiyar take, dauke da illar lokaci…
Wasu buririkan mafarkai ne…
Wasu burirrikan ba sa kaiwa gaci, ruwa tafiya yake da su!
MASU ƁUKATAR A TALLATA MUSU HAJOJINSU ZA SU IYA TUNTUƁARMU TA LAMBOBIN 07045308523 MUN GODE
