Duniya ta – Chapter Nine
by NadminMASU ƁUKATAR A TALLATA MUSU HAJOJINSU ZA SU IYA TUNTUƁARMU TA LAMBOBIN 07045308523 MUN GODE
Sabo da maza jari ne!
Kaduna, Nigeria
Bayan shekara biyar
Alhaji Balala-Cinye-du ya duba tsadadden agogonsa na hannu ya ga karfe 10 cif cif na safe, ya ja dan karamin tsaki ganin cewar ya makara. “Bidding” garesu na motoci kuma karfe goma ne daidai ga shi har goman ta masa a daki. Ya dauki hularsa mai taken minista baka ya dora akan Farar shaddarsa mai babbar riga. kallo daya za ka yi wa shaddar kyaunta ya fallasa tsadarta. Sai ya saka takalma rufaffu sau ciki.
Ya tsaya yana kallon kan sa a gaban mudubin dogon yaro kamar wata ‘yar budurwa mai tashen budurci. Baki ne mai matsakaicin tsawo gwani na saka fiskar gizago musamman idan mutum ba dankwali ya daura akansa ba.
Dan kasuwa mai samu fiye da daidai misali amma iyalansa ba su wadatu daga hakan ba. Ya gama shirinsa tsaf ya rufa da fesa turare da yake mutum ne mai son gayu na birgewa. Shekarunsa ba zasu wuce 45 ba amma idan ka gan shi ba za ka ce ya kai 40 ba.
Ya dauki “brief case” da ke dauke da farare bugun Abuja ya rike ta kyam sannan ya kulle kofar sashinsa ya jefa mukulli a aljihu. Ya tako taf taf kamar wani ingarman doki ya shigo sashen iyalinsa cikin takama da izza.
Kallo daya zaka yiwa matar ka zata ‘yar aikin gidan ce idan ka karewa yanayinta kallo. Wata kodaddiyar cheras ne a jikinta da ta sha wanki da takalmanta silifas dan madina tana aikace aikace a tsakar gidan. Gida ne yalwatacce ginin zamani sai dai kana zuwa za ka gane babu kulawa.
Duk irin tarin dukiyarsa matarsa Lantana rura gawayi take don tayi girki. Ya karaso gurinta da niyyar ya bata kudin cefanen ranar kawai sai wani almajiri mai zakin murya ya katse shi
Maula ta sidi maula ta balarabe, maula
Muna bara a bamu domin annabi, maula
Kowa ya bamu ya baiwa annabi,
maula
Alhaji Balala ya daka wata mahaukaciyar tsawa ya ce
” wani dan iskan yaro ne anan? Don iyayenka kar ka kara zuwa mun gida tunda bana ubanka ba ne!Shi ma uban naka ai ya san da yunwar ya turo ka almajiranci. Wai tukunna ma Lantana ba na ce a dunga garkame gate din nan ba saboda shigowar sakarkarun yaranan?”
Ya cigaba da sababi Lantana kuma ta cigaba da kujiba kujibar aikinta ba ta ko bi ta kan sa ba. Sai ma tana hura gawayinta ta soma rera wata waka
Wayyo wayyo habiba yardamalmala
Dan Allah zo gareni yardamalmala
Alhaji ya kule. Ya lura da take taken Lantana kwanan nan sai ya ce
“Wai Lantana ba magana nake miki ba kika mayar da ni mahaukaci. Tukunna ma bana hana wake waken nan na wasan hausa ba?”
Cikin halin ko in kula ta ce
” O’o ni ba kayan kallo ba ina zan kalli wasan hausa? A bakin yara na ke ji idan sun je makwabta kallo sun jiyo”
Wani haushi ya turnuke shi ya ce
” Au don lalacewar tarbiyya har yaran nawa kike bari su shiga makota kallon wasan hausa? Kina da hankali kuwa Lantana?”
Ta watso ma sa wani kallo wanda bata taba yi ba har sai da Alhaji ya ji ba dadi. Kan sa ya daure? Wai me ke faruwa ne? Wa ke zuga Lantana? Abinda yake gudu fa yana neman ya faru dalilin kenen da duk aure aurensa bai taba auro ‘yar jami’a ba.
Me akai akai ‘yar jami’a fitsararrun yaran mata da kan su ya gama wayewa da ‘yanci, yaya za ayi su lankwasu? Komai kana yi tana jin daidai take da kai. Ya fi ganewa mai karancin wayewa komai aka gaya ma ta ko bata so ta yi.
Amma mamakin Alhaji bai kai kololuwa ba sai da ta mayar ma sa da
” Yaya za a yi in yi hankali kadangarun barikinka su ma suyi hankali? Ai abun sai yayi mana yawa”
Da a ce Alhaji mai sabon dukan mace ne babu abunda zai hana yau ya yiwa Lantana lilis. To amma ba wai dukan ne bai taba yi ba, muhallin dukan ne babu. Duk cikin aure aurensa shida Lantana ta cikon bakwai babu wacce ta taba zama sama da shekara biyu saboda jarabar maqonsa da neman mata. Duk cikin matan ba wacce bata haihu ba kuma haka lantana ta hada da na ta guda biyar ta killace.
To ma a ajiye wannan a gefe ba Shin ba shekarar bara ba ne da ya fallawa lantana mari mahaifiyarsa Iya ta ce idan ya kara zata tsine ma sa? Ta fara da jero gore gore na halaccin da lta lantanar ta ma sa wanda matan da ya aura har shida suka gaza. Da ya tuna irin cin mutuncin da mahaifiyarsa ta masa akan lantana sai ya ji duk ba dadi.
Ba ya hada Iya da komai, ta je ta ci albarkacin Iya. Kuma da gaske idan lantana ta tafi ‘yayan nan sama da goma ina zai je ya ajiye su? Amma zai yi maganinta a cikin ruwan sanyi da shi take zancen.
Ya share ta ya zura hannu a cikin aljihun rigarsa na hagu yana lalube kamar zai dauko abun kirki ya zaro wata cikwikwiyayyiyar N200. Dama haka yake yi kudinsa ma su dan daraja a aljihun cikin wandonsa yake adanawa. Kafin ya bata N200 ne wani dan yaro ba zai gaza shekara 5 ba ya fito da kofin koko a hannu ya zo wajen uwar ya ce
” Ummanmu ban koshi ba”
Ta dauki wani fulas a gefenta daga gani rabonta ne ta juye ma sa. Sai a lokacin ya lura da uban ya gaishe shi. Alhajin ya ce
” Sadiq ya baka je makaranta ba?
Yaron ya ce
” Baba ai tun jiya dayawa dayawa aka kore mu wai bamu biya kudin makaranta ba”
Alhaji ga dago ya kalli lantana fuskarta kamar hadarin da ya hadu ya ki saukar da ruwa ya ce
” yanzu lantana don rashin mutunci a kori yara daga makaranta kwana da kwanaki ki kasa gayamin?”
Ta daga hannu tana cewa
” Dakata dakata Alhaji idan dai don dora ruwan talgen tuwon nan ne da ka ajiyeni sai in sauke in wuce inda na fi wayo! Kai ba ka san cewa lokaci biyan kudin makarantar yara yayi ba? Bar mun su a haka, ai a gida suke kwana”
Alhaji ya san shagube take ma sa da shi take. Idan banda jiya kwana uku kenen bai kwana a gida ba bai kuma bar kudin cefane ba. Ba dai Lantana Iya zata je ta gayawa ba?
Ya dake ya ce
” Idan jikinki yana miki ciwo zan lallasa ki. To idan na zauna a gidan talgen tuwon zan juya miki? To..to..to shikenen ma!sai ki bani aron zaninki in tafi kofar gida in ke toye toye kin ga nayi daudun da kyau kenen!!”
Da kyar yake fitar da numfashi saboda bacin rai na son zuciya ya cigaba
” Ana zuga ki ko? Kin kwana kin hantse da fitsara da rashin mutumci. Idan kin fasa ba kya kaunar gyatumarki!! Iya ta daure miki gindi ko? Zamu gani ni da ita wake aurenki!”
Kawai sai ya mayar da N200 sa aljihu ba zai bayar ba. Rashin kunyar tayi ta kudinta. Ita ma ranta a harzuke da alamun rashin tsoro ta ce
” Mu je zuwa! Kai ne dai zaka iya lallabowa da daddare ni kuma na iya rufa maka asiri a lokacin da kadangarun barikinka sukai maka bankada! Bi za til rasulillahi sai Allah ya saka min. Mai kuntaccen tazuge kawai!”
Alhaji ya lura lantana so take ta dora masa jakar hatsi kaji suyi ta caccaka sai ya fice kawai cikin tsananin bacin rai. Yana jiyo fashewarta da kuka ya buga tsaki yana jin takaicin halin mata. Mace..mace ba tayi ba mace akwai rashin godiyar Allah. Idan ka bata taku daya to wallahi sai ta hau goma sha daya. Balle idan ta gan ta ita kadai..inaa…ai kyaun mace ka yi ma ta kishiya daga nan zata hankalta. Ya na ga dai aure zai kara.
Amma ba anan take ba shi ba shi da ra’ayin tara mata saboda daukar nauyi. Yanzu mace kana aurota ba ka huce gajiyar hidimar aure ba sai tace ciki. Ka ci da ita ka ci da danta. Ga abun kamar gasa su yi ta haihuwa kamar ‘ya’yan zomaye. Yau abinci gobe rashin lafiya kana ta fitar da kudi.
Ya kuma buga uban tsaki auren nan ba ma shawara ba ce a yanzu sai dai zai san matakan da zai bi yayi maganin lantana.
Ya isa kan dalleliyar motarsa kirar marsandi ta yayi, ya hau ya cilla kan titi. Ya san ya gama makara abunda yake gudu kenen. Ya tsani a rayuwarsa wani ya riga shi isa inda samu yake. Ya fi so ya mallaki komai shi kadai, shi yasa ma ake masa lakani da “cinye-du”.
” Mai kuntaccen tazuge kawai”
Har ga hau kan titin Govenor road maganar lantana bata gogu daga ransa ba. To ma wai ina ruwan lantana da sabgarsa ta mata? Har zata sa ma sa ido ita ta ga zata iya wahal da kan ta. Saboda ya rage bacin rai sai ya tuno da faifan sidin dan kwairo da ya siya a danja jiya. Sai ya kunna ya na bin wakarsa ta sarkin muri takaicin Lantana yana ficewa daga ransa. Ya fara gyada kai in da yake cewa
Alhaji musa dan kwairo, ga babbar riga ya baka
Ga kufta kuma ga alkyabba, ga rawani kuma ga jar hulla
Har da agogo da takalmansu
Mu biyu sai ya bamu wan tauzan
Yaran dan kwairo goma sha uku
Kowa riga da tu hadred nera
An kayi total an ka hada
Kudin kwairo dana yara
Ya zama faif tauzan da sis hadred nera
A lokacin ne danja ta tsayar da su sai kuma a bayansa wata karamar mota kirar starlet ta kwararo a guje ba ta lura da tsayawar danja ba ta dokawa Alhaji mota. Alhaji ya fito jiki sa yana rawa kamar mazari saboda tsananin bacin rai. Mutane ‘yan ganin kwaf suka fara dafifi a gaban motar sa su ji yanda aka yi. Sai kunfar baki yake yana zage zage. Sai cewa yake
” Yau zan ga uban da ya tsaya maka a garin nan in ji ko da shi aka taru aka hadu aka shinfida kasar kaduna.”
Wani abu da ya fi bawa Alhajin haushi shi ne duk wannan hargitsa ballin da babatu da ake yi mazaunin motar wacce ke rufe ruf da tint bai ko motsa ba balle yayi alamun fitowa.
Ya kara duban agogon hannunsa sha daya saura abinda ya sa wani mululu ya zo masa makogwaro ya tokare. Ya yanke shawarar ya je wajen motar ya bude ya fizgo mutumin ya sharara ma sa marin gobe- ba -zaka-kara-ba.
Abu daya ne tal ya tsayar da shi bude hancin motar da aka yi hade da bayyanar wata zukekiyar mace mai haske kamar watan sallah. Ba wai yanayin Kyawunta ne kadai ya dada shi da kasa ba, aa ya ga kyawawan mata fiye da adadin shekarunsa a doran kasa. Sai dai me? Yanayin shigarta ne ya rikita shi har ya ji ya nemi kululun nan na makogwaronsa ya rasa.
Lallai ya yarda wani kaya sai amale. Da ta fito ma tsayawa tayi cak tana kallon dandazon mutanen kamar ‘yan taron sinima daidai.
Wata riga ce marar hannu a jikinta da ta wuce cibiyarta da dakika daya sai wani dogon wando “jegens” mai lafewa a jikin mutum kamar tare aka halicce su. Gashin kan ta an yi kari dana doki an kitse ya sauka har yana tabo kugunta. Ta dauki wani bakin gilashi da yake nuna iya adadin rashin mutuncin da zata iya dokawa ta kwama a fuska. Nan take Alhaji Balala ya raya a ransa cewa wannan safiyar litinin din ta sa ce.
Babu kunya balle jin nauyin idanuwa kusan hamsin da suka mamaye ta ta tako kamar tana tausayin kasa ta karaso inda yake ta ce
” Yallabai barka da war haka”
Alhaji ya hadiye yawu mukut! Ya saki wani murmushi da yake yiwa masu dankwali in dai ba matansa ba ne ya ce
” Barka da war haka dai masu gari”
Tayi far da ido ta ce
” Sai wannan tsautsayi ya afku, an yi shi kan kuskure Alhaji sai dai ayi hakuri…je suis desole yallabai”
Anan Alhaji ya gani abu biyu, faransa ce kuma rabonsa ce don haka sai ya karo mizanin fara’arsa ya ce
” yanmata wannan ai ba matsala ba ce, asali ma ni ya kamata na baki hakuri ta dalilina har fitilar motarki ta fice ni kuwa kwarzane ne kawai. Bari ma ki gani yanzu zan kira bakanike na ya wuce da motar ta ki. Wannan ai ba abun damuwa ba ne”
Ya jawo wayar zai danna kira sai a fusace ya dubi mutanen nan da suke musu kallon kwaf ya ce
” Kai jama’a menene haka wai? Kun zo kun min dafifi a kai..to..to..ko marhaba sinima ce ni..zancen banza zancen wofi”
Haka aka watse ana masa dariya wai reshe ya juye da mujiya har wani shakiyyi ya ce
” Alhaji mayar da wukar, ji da dankwalin!”
Bai kula ba ya danna waya ya kira bakanike ba a wani jima ba ya karaso. Ya ce ta bada motar ta kwaso tarkacenta duka bakaniken ya wuce da motar.
Ta dubi Alhaji cikin farin ciki ta ce
” Godiya nake yallabai vous remercie dama haka mutanen kaduna ke da karamci?”
Alhaji ya fashe da dariya ganin ta fadi gasassa ya dauki akwatinta yace
” Mu tafi ko? Zan kai ki duk inda kike da muradi”
Ta murmusa ta ce
” nous pauvons aller”
( za mu iya tafiya)
Alhaji ya jinginar da batun bidding suka shiga mota. Wannan karin ya kashe wakar dan kwairo ya kunna Radio kaduna sannan ya dube ta a tsanake ya ce
“Har yanzu ban san sunan gimbiyar ba”
” Mahfuza” tace da shi
Ya ce
“Lallai sunan ya dace da ke. Me ya shigo da ke garin gwamnan namu?”
Ta ce
” wallahi daga Abuja nake na zo wani aiki ne zan je masauki”
Ya tambayi masaukin ta gaya ma sa Haraba hotel. Bai yi wata wata ba ya zarce.
Alhaji ya cake naira dubu arbain kudin kwana biyu kamar yadda tace za ta yi suka hau sama hawa na biyu daki mai namba 24. Ya kira”room servive” ya ce ta fadi duk abunda take son ci, ta fada aka kawo. Suka ci suka yi nak!
A ranar yini suka yi suna sheke ayarsu ba tare da Alhaji ya tuna iyalen da ya bari a gida ba cefane ba. Da daddare Alhaji bai fita ba sai daya kulleta ta baya ya tafi da mukullin. Ya san halin irinsu sarai yanzu sai ta tafi abinta ta bar shi bayan bai gama barje kudinsa ba.
Ya je yayi ‘yan harkokinsa daga karshe ya tsaya a wajen me nama ya siyo gasasshen nama da robobin lemo hade da kayan bukatu kala kala. Bai wuce koina ba sai haraba hotel. Yau ma bazai kwana a gida ba, ya gayawa kan sa hakan.
Ya sa mukulli ha bude kofa ya tarar da ita a inda ya barta yashe a kan gado tana kallon tv. Banbancin kawai yanzu ta sheka wanka ta yi ado da wasu kaya masu daukar hankali. Nan Alhaji ya dada rikicewa shi dai yarinyar nan ta shiga ransa baya jin zai iya barinta ta tafi a kwana biyun nan. Wayo zai yi ma ta ya lallaba ta yi masa sati har ya fanshe kudinsa.
Dama sun yi waya da bakanikensa da ya bawa motarsa gyara ya ce wannan motar ai tana bukatar gyara sosai don komanta ya kwarkwance. To sai yayi amfani da hakan ya ce wai zai canja mata motar ma idan ta kara masa kwanaki.
Sai da ta kara kwanaki biyu ta yini sannan ta dubi Alhaji a cikin fari da ido ta ce
” Alhaji wai yaya ne? Ka san fa aiki na zo amma ka kafa ka tsare. Sai dai ka kulle ni a daki ka fita ka je ka dawo dan aikin da na zo yi ma na gagara lekawa”
Ya kwashe da dariya rayuwa na gara masa yanda yake so. Ya ce
” To wa zai gan ki ya bar ki haka kawai kamar wani sakarai? Ni da nake ta son ki min sati ma!”
Ta kalle shi kasa kasa a ranta tana rayawa wani irin tsohon kwar tu kwar ne wannan? Amma a shagwabe sai ta ce
” A’a ni dai gaskiya Alhaji abunda da fa ya kawo ni kenen ba a yi haka ba”
Ya taso matsowa inda take ya rungumota ya ce
” haba haba gimbiyata kwantar da hankalinki. Ni da kai na gobe zan dauke ki na kai ki kiyi alamuranki. Amma fa da sharadin sai kin min sati.”
Ya jawo brief case din sa ya kirgo ‘yan dubu dubu guda hamsin ya danka ma ta a hannunta ya ce
” Kin ga idan mun fita sai ki tsaya kiyi shopping ko?
A haka dai har ya lallabata ta amince.
Da safe ya shirya zai fita ya yi wasu harkoki sannan ya dan leka gidansa. Tana magagin bacci ya ma ta sallama da cewar zai dawo su fita. Ya kulle dakin ya tafi da dan mukullin.
A gurguje ya je gidan nasa ya bada N200 kudin cefane. Lantana ta yi ma sa korafin yaro ya tashi da ciwon ido da kyar ya kara N100 wai a sayi ampikilos a kemis a balle a barbada masa a idon. Bai tsaya jin wani dogon bayani ba ya fice.
Ya wuce wani wajen sayar da motoci da suka saba harka tare ya duba wata ‘yar madaidaiciyar “thankyou daddy” ya taya. Watakila ya rike yarinyar nan wata 6 in ya so ya dalle ta da wannan mota. Tunaninsa kenen.
Daga nan ya wuce Haraba hotel in da ya fi wayo. Ya shiga daidai reception kamar daga sama ya ji wata zazzakar murya ta ce
” Ranka shi dade Alhaji Balala, dama ashe rai kan ga rai?”
Ya waiwayo a hankali yana mamakin cafkar sunansa da aka yi. A zaune a kujerar reception din ya ga wata bakar yarinya sanye da atamfa ruwan dorawa. Tayi dinkin riga da siket sun matseta tsam! Hakannan wuyan rigar ya sauko yana bayyana rabin kirjinta. Tana karkada kafa tana taunar cingam kas kas. Ta hadu ba karya
Har ga Allah bai gane ta ba bai kuma taba ganinta ba amma kuma ai da kunya kyakkyawar budurwa ta ambaci sunanka ka gwasale ta. Ya karaso har inda take da gaske so yake ya gano ta. Tayi galala da baki ta ce
” Alhaji kar dai ka ce da ni baka gane ni ba”
Ya ce
” Mutum har zai iya manta kyakkyawar fuska kamar ta ki?”
Ta tsare shi da idanuwa da alamun nuna jin zafi ta ce
” wallahi Alhaji baka gane ni ba. Amma nayi mamaki. Ai shikenen ni dana damu da ka ai ga shi ai na rike fuskarka”
Ta mike da alamun da ke nuna tafiya za tayi. Ya jawo ta ya zaunar cikin kaskantar da kai ya ce
” Haba ranki shi dade fushin ba wuya ne? Kin san ni mutum ne mai harkalla shi yasa wasu abubuwan suke subuce min”
Nan dai yayi ta lallashinta yana kwantar da kai don har ga Allah yarinyar ta mugun tafiya da imaninsa. Cikin yauki da rangwada ta ce
“Ai ka san farida ko? ‘Yar mutan jimeta. Ko ita ma ka manta ta?
Kwarai ya san farida. Wata tsohuwar yarinyarsa ce da yayi yayinta kamar hauka ta kara cewa ” to ni kawar ta ce mun hadu da kai ba sau daya ba kuma na rike fuskarka tunda na damu. Yanzu haka sunana ma sai na gaya maka kai kuwa farat daya na fadi naka. Alhaji ya kwantar da kai yana dariya dariya yana cewa
” afuwan..afuwan da girman kujerarki. Idan an tuna min ai ba alifi ba ne”
Ta dago hannunta ta mika masa ta ce
” A nawa?”
Babu tantama ya zira hannunsa a aljihu ya zaro naira dubu goma cas ya dora ma ta. Ta ce
” To ka ci gari, sunana Tani”
Nan suka kacame da hira kamar sun saba. Daga baya sai ta mike ta yi wata irin doguwar mika Alhaji ya kura ma ta ido kamar tsohin maye ta ce
” Zama guri daya tsautsayi in ji kifi bari ka ga in shiga daga ciki dawowa ta kenen na rashe a nan.”
Alhaji ga mike cikin azarbabi ba wai ya manta da yarinyar nan mahfuza ba ne da ya bari a daki to amma idan wannan ta subuce ma sa fa? Shi dama can haka halinsa yake hadamamme ne anan ya samu sunansa cinye-du. Don haka sai ya kalleta ya ce
” Haba tauraruwa ka da ki ce mini ba kya bukatar rakiya”
” Ban ce da kai ba”
Ta ba shi amsa. Daga nan suka qarke a hawa na uku daki mai namba 38.
Lokacin da Alhaji ya samu ya kubuta daga tarkon Tani karfe biyu daidai na rana. Bai so ba amma ba yadda ya iya ne ga shi ya bar mahfuza a daki ya san har ta gaji da jira. Sai ya damkawa Tani damin kudi a hannunta kafin su rabu da cewar zai je ya dawo. A ransa yana mamakin irin wayonsa yanda yayi dubarar darje yanmata har biyu a lokaci daya.
Nan da nan sai ya wuce daki mai lamba 24 yana taraddadin yanda zasu
Kare da mahfuza don ya san yayi laifi. Kafin ya karasa wani sabis ya taho da keken tura abinci suka ci karo har ya barar da kwanuka. Wata miya ta tsallarwa Alhaji akan tsadadden takalminsa. Ya dunga banka masifa kamar zai tayar da otal din. Wai ba su waye da aikinsu ba. Sabis din yayi ta ba shi hakuri har ya goge masa Alhaji bai daina bala’i ba. Ya buga tsaki ya wuce.
Ya sa mukulli ya bude dakin mahfuza bai gan ta a kan gadon ba, bai kawo komai ba don ya ji karan ruwa a bandaki. So yake ta fito ya samu ya dan dauraye jikinsa.
Ya cire hularsa ya kishingida akan gadon yana jiran ta fito. Tunaninsa yana ta shawagi akan irin zaryar da zai yi a dakunan biyu yau ranar ta sa ce.
Shiru shiru bata fito ba har ya gaji ya kwankwasa, ya kara kwankwasawa ya ji shiru. Sai ya tura sai dai me? Wayam!
Gabansa ya yanke ya fadi. Ah ko ga gaji da jiransa ne ta tafi wajen aikin da ya kawo ta? Amma sai ya tuna cewa ya kulle kofar ya tafi da mukullin. To ta ina ta fita? Sai a lokacin ya kula ba jakarta. Yayi sauri ya bude wardrobe nan ma ba akwatinta.
Tsoro tsoro ya fara shigarsa da tunanin ko aljana ya dauko? Ya fita daga dakin da sauri ya tafi reception yana tambayar ko matar da ke daki mai namba 24 tayi “checking out”. Suka ba shi amsa da a’a domin ma ai mukullin dakin yana hannunsu. Kan sa ya kara daurewa.
Sai ya kasa gasgatawa ya koma dakin yana bankade bankaden neman ta kamar allura. Ya gaji don kan sa, ya hada gumi sharkaf ya baro dakin. Tunaninsa ko garin kwashe kwashensa ya dauko aljana gwara yayi sauri ya bar hotel din. Daga nan wucewa zai yi wajen Malam yunusa yayi ma sa rubutun kariya ya sha.
Ya zira hannu aljihunsa don ya lalubo mukullin motarsa kafin ya karasa inda ya ajiyeta sai mukulli yace daukeni inda ka ajiye. Nan ya shiga waswasi watakila garin bankade bankadensa ya yar a dakin don haka sai ya koma kamar zai tashi sama.
Nana ma yayi iya dubansa bai gani ba. Sai a lokacin ya tuno ashe fa ya je sheke aya dakin yarinyar nan Tani, ta yiwu anan ya yar. Kamar mahaukaci haka ya bazama daki mai namba 38.
Ya kwankwasa ba da wani jimawa ba aka bude amma sai yayi ido biyu da “room service”. A hanzarce ya tambaya ina wacce ke dakin. Sabis ya ce
” Ai ba ta fi minti talatin da checking out ba, shi ne ma na karbi mukulli nake gyara dakin”
Kan Alhaji Balala ya shiga dimuwa. Shin ba yanzu yanzu ya rabu da yarinyar ba ne? Me yasa daga Tani har Mahfuza ya neme su ya rasa?
Ya kawar da wannan a ransa shi ta mukullin motarsa yake ma. Ya samu ya bar hotel din nan don ya ji komai ya gundire shi.
Yayi wa sabis din takaitaccen bayani suka shiga suka duba dan mukullin amma babu ko alamunsa. Alhaji ya gaji iya gajiya wani sashe na ransa yana raya ma sa watakila ya yar da mukullin a daidai inda ya paka motar.
Ya sauka ya tafi inda ya paka motar sai dai me? Babu mota ko sama ko kasa kamar an yi ruwa an dauke.
Wata irin rikicewa ta ziyarci kwakwalwar Alhaji, har sai da ya zagaye wajen paka motoci sau uku kamar mahaukaci babu alamun mota. Danqari!
Wanann alamari ya daure ma sa kai wai mota a cikin randa. Wani irin duhu yake gani yana neman kayar da shi, akwai wani rikitaccen alamarin da ya kasa warwarewa.
A lokacin ya danna waya ba don yana cikin cikakken hankalinsa ba ya kira Alhaji Shitu amininsa tun na rai da rai. Halayyar neme neme ta Alhaji Balala ya sa aminin sa ya ja baya da shi duk da dai suna tare. Bai tsaya dogon bayani ba ya ce su hadu a Haraba Hotel.
Ya karasa reception ya tada ballin a kira masa manaja do yau sai an fito ma sa da motarsa. Kafin Alhaji shitu ya karaso rigima ta kacame a hotel, Alhaji yana ta kumfar baki har ya kira yan sanda biyu. Alhaji shitu ya iso aka mayar da yanda aka yi.
Manaja ya rufe ido yace su ba su san da batan mota ba kuma ba zasu biya ba saboda a wajen pakin sun rubuta
” vehicles are parked at owners risk”
Cewa duk wanda fa ya aje motar to hakkin motar a kan sa yake. Rigima ta tsaurara har Alhaji Shitu ya samu ya janye Alhaji Balala da cewar yansanda zasu cigaba da bincike. Ya fice da shi a motarsa yana sharfa gumi.
Yau wata irin rana ce birkitacciya marar dadin tunawa. Alhaji Shitu ya bude hancin robar ruwa ya mika ma sa ya kwankwada kana ya ce masa
” wai tun farko ma me motarka ta ke yi a otal? Tabbas akwai abunda kake boyemin”
Babu wata kwana kwana Alhaji Balala ya zayyane masa tun daga farko har karshe. Alhaji Shitu ya ci birki ya faka a gefen titi saboda tsanananin mamaki. Ya daki sitiyarinsa ya ce
“Ka gani ko? Ka gani ko Balala na sha gaya maka irin tayuwar nan ba rayuwa ba ce. Babu inda zata ajiyeka sai a tashar asara. Na gaya maka na gaya maka ka kasa ganewa. You were played! Wannan alamarin duk shiri ne..gadar zare ce aka shirya maka bayan an yi watanni da karantarka. Hasbunallahu wa niimal wakeel!
” kamar ya shiri?” Ya tambaya
Alhaji Shitu ya nisa kan ya ce
” Saurareni da kyau. Wadannan mata guda biyu sun san ka ba tun yau ba sun karance ka sun kuma gano halayyarka ta cinye du. Don haka sai suka sa ka a matsayin target.
Da farko wannan motar da aka zo aka buga maka sai da aka tabbatar bata da mamora tsohon gwangwani ce. Ba tsautsayi ba ne da sane tayi ta san in dai ka gan ta sai ka dauke ta. Daga nan wasan ya fara.
Tani ita ma ta san ka, bakinsu daya da ta farko. Ta yi abunda tayi ne don ta janye hankalinka ita mahfuza ta gudu. Ita tani ita ta dauke maka mukullin mota Allah ya sa ma mukullin motar kadai ta dauke. Kafin daga dakin Tani mai lamba 38 zuwa dakin mahfuza mai lamba 24 Tani za ta gudu ta zure maka mota. Shi yasa a shirin nasu kuka ci karo da sabis don ya kara bata maka lokaci kafin ka isa dakin mahfuza.
Da ka shiga ta bar famfo a kunne don ka zata tana bandaki wannan ma duk wata dubara ce ta kara siyan lokaci. Amma asali shi ne ta dade da fita daga dakin. Tani zai iya zama ita ta fice da motar ko kuma mahfuza ta dade da jiranta a waje ta bata mukullin motar ko kuma su duka biyun. Wannan safa da marwar da kayi ta neman dan mukulli da mahfuza ya isa a gudu da kowacce irin mota.
Alhaji Balala ya nisa a cikin daurewar kai ya ce
” To ya aka yi mahfuza ta fito daga dakin bayan kullum sai na kulle ta kafin na fito?”
Alhaji shitu yayi murmushi kafin ya ce
“Wai shin Balala ka manta da bariki ne shin ba kai ne a cikinta ba? Ka manta cewar komai in dai da kudi kare magana ne. Za ka sa a yi maka shi ko menene sabida cin amana ba komai ba ne in dai da kudi. Ai wannan hotel din da ka gani tabbas akwai wata mas’ala.
La’alla yanmatan biyu bakinsu daya da manaja sun siye shi. Ko kuma suna da wasu ma’aikatan hotel din da suka siye. Za ta yiwu mai aiki a reception da kuma sabis sabis. Dukkaninsu za su iya samu access zuwa ga spare key na kowani daki. Ai ina ga abu mai sauki ne wanda aka hada baki da shi musamman room sabis ya dauki mukulli ya je ya bude ta ba tare da kowa yayi la’akari ba. Idan dai har zasu ba shi cin hanci. Ina fatan ka fahince ni?”
Ya fahinta din sai dai ya gaza gasgatawa har za ayi mishi wayo irin haka cikin fusata ya ce
” To in dai kuwa haka ne yanmatan nan sai na nemo su na kai su kotu. Sai na nunawa yarinya ni Alhaji Balala kowa ya ci tuwo da ni miya ya sha. Har otal din ma sai na sa an rufe shi, na tona musu asiri!”
Huci yake yi, yana tsananin cikin tashin hankali. Motarsa ta yayi akalla ta kusa miliyan 3.
Alhaji Shitu yayi murmushin takaici.
Ya ce
“Calm down abokina. Duk abunda za kayi ina so kayi tunani kafin ka aikata kar balli ya tashi da kai. Su wadannan yanmata ina za ka gan su? Ina tabbatar maka ba yan gari ba ne. Yanzu haka ma sunayen da suka gaya maka duk na karya ne.
Wata hujja gareka akan otal bayan kai ka kawo kan ka? Sai uwa uba ta ina zaka fara shariar nan? Labari ya ba za duniya ka dauki matan banza sun damfare ka abu ya je har kunnen iya, matarka , ‘yayanka, masoyanka da makiyanka. Ta ina aka hau ta ina za a sauko?
Wani irin gumi Alhaji Balala ke sharewa kamar ba gobe. Ambatar Iya a lamarin ya sa ya ji zuciyarsa kanar za ta fashe. Idan Iya ta ji sai ta yi ma sa tsinuwa ta har abada! Da a ce shi mai saurin kuka ne babu abinda zai hana shi zubda hawaye.
Sai a lokacin ya tuna da wani abu. Wannan tsohuwar motar tata a gurin bakanike. Wata kila ya rage asara. Ya kira shi, bakaniken ya ce
” Alhaji wata mota fa? Motar da ka aiko tun safe aka karba har ma aka bada kudin gyaran in ji ka….”
Alhajin ya katse wayar ba tare da ya ji karshen wannan kayan takaici ba. Ya bude baki kenen zai labartawa Alhaji Shitu yanda aka yi. Sai ya ji wayoyinsa biyu suna fitar da qara rraki barkatai na shigowar sakonni.
Cikin sauri ya bude ya gamu da rikicewa da ta ninka ta dazu sau goma sha tara. Bankuna uku yake amfani da UTA , Charity da UD. Kowanne a ciki yana aika masa alert na zarar makudan kudade.
Cikin azama ya zaro wallet din shi in da atm cards din sa suke, wayam!
Cikin kaduwa ya dubi Alhaji Shitu wanda ya riga ya hano abunda ake ciki ya ce
” kudina suke kwashemin! Na shiga uku!…kudi na Shitu!
Shi ma Alhaji Shitu cikin rudewa yake cewa
” kira Manaja yi sauri. Aikin hackers ne…yi maza maza”
Ya rude ya ma rasa wanne zai fara kira har ya samu ya danna kiran na UD. Bai ma san inda hankalinsa yake ba kawai ji yayi yana cewa
” Stop the transaction!! Stop the transaction!
Alhaji Shitu ya dafe kai, ya san lamarin sai du’a’i. Alamarin sai gyaran Allah!
*********************************
Wani irin gudu take fyallawa a motar kamar zata tashi sama duhu ne yake fara mamaye garin. Can ta gangara daga bakin titi ta sauka wata hanya da babu kwalta. Tayi tafiya ba da yawa ba har ta isa wani yasasahen kango. Unguwar babu mutane sosai sai babura da keke napep da ke wucewa tsilli tsilli. Kamar dai wata hanya ce ta “short cut”
Wayarta ta danna ta kira ta wani mai suna Osi, ya daga ta ce
” gani na iso” ta katse
Ba ayi cikakken minti biyu ba ya bayyana dan tsamurmuri da shi sanye da singileti da dogon wando jins. Hannunsa yana dauke da tabar wiwi yana zuka kamar zai tashi huhunsa daga aiki.
Ya fara tafa hannayensa yana zagaye motar cikin farin ciki ya ce
” Beb komai yayi na yaba da kokarinki” ya kwashe da wata mahaukaciyar dariya.
Ta katse shi da cewar
” Dakata Osi ba wannan ya kawo ni ba. Sallame ni in tafi akan hanya nake”
Ya wani kai mata cafka yana cewa
” haba beb wai ke kan maganar kudi ba kya sassauci? Ni da ke ai mun zama daya”
Ta ce
” Na ji na ji Osi, sallame ni”
Yayi wani matsiyacin murmushi ya daga waya ya kira wani ya ce
” fito da jakar nan”
Wani dan saurayi da bai wuce ahekara 20 baya fito da wata yar jaka irinta ‘yan makaranta ya mika ma ta. Ta zuge jakar sannan ga kirga kudin da ido rafa ce ta dubu daidai har guda goma sha biyu. Ta dago a fusace ta ce
” miliyan daya da dubu dari biyu? A wannan dankareriyar motar da kuma kudin account na Alhaji. Ita motar a karan kan ta ta yi miliyan 3. Ka ji tsoron Allah Osi!”
” Ka ji ‘yar banten uba! Dalla malama kar ki mana e ya ne. Ke tsoron Allah ne yasa kika sato motar? Wannan kudi dana baki a dunqule fa ni ke da risk ke kin ware abinki. Yanzu yanzu zan dauki motar a kara canja ma ta plate number a kuma yi mata feshi. Suk dare sai na bar garin nan. Kika san tsautsayin da zai iya ritsawa da ni? Ke ai ta fado miki gasassa ne kawai!”
Wani bakin ciki ya tsaya ma ta a makogoro shi yasa ta tsani aiki da Osi saboda son kan sa amma ba komai. Saboda tuwon gobe ake wanke tukunya. Ta karba tayi gaba kadan ta tare me napep. Ba ta fi minti 2 da tafiya ba Osi ya dauki waya ya kira, aka dauka. Ya ce
” Bi ta ka sumar da ita ka karbo min kudina”
Aka amsa da
” Ok”
Suna karya kwana da mai napep ta sauka ta fyalla a guje bayan wata himilin bola ta kwanta ruf da ciki. A gaba idonta wani ya zo ya wuce a guje ya taddo mai napep, ya leka nemanta bai gan ta ba. Ya kai masa naushi yana tambayarsa ina take ya gaya masa ta sauka a baya. Ya bazama nemanta yana haska tocila domin duhu ya sauka. Daga baya ya koma hanyar da ya fito yana nema.
Ai tana ganin ya juya ta fyalla cikin tsurkukin bolar nan da gudu kamar ranta zai fita. Ba ta nisa ba sai da tazo bakin titi. Kamar a tare wata bakar mota kirar toyota ta ci wawan birki a gabanta. Ta bude ta shiga, matukiyar motar ta take totur ta danna a guje kamar tashin duniya. Mai tukin ta ce
” Damn it! You stink!”
Bata kula ta ba ta dauko waya ta danna nambar Osi yana dagawa ta kundumo masa ashariya ta ce
” haduwarmu ba za tayi kyau ba!”
Yayi wata bahaguwar dariya ya ce
” kin sha wannan karin, amma ki tsumaye ni”
Ta kashe wayar bayan ta danna masa wani zagin.
DIreban motar ba ta daina sharara gudu ba har ta iso fly over, ta dauke kan motar zuwa titin Zariya. Sai da ta dan yi tafiya mai nisa sannan Hindu ta juyo ta kalli Rukky ta ce
” Sukari, yaya an dace?”
Ita ma ta kalle ta tana jinjina ma ta kai ta ce
” An dace, sosai ma an dace”
MASU ƁUKATAR A TALLATA MUSU HAJOJINSU ZA SU IYA TUNTUƁARMU TA LAMBOBIN 07045308523 MUN GODE
