Duniya ta – Chapter Fourteen
by NadminMASU ƁUKATAR A TALLATA MUSU HAJOJINSU ZA SU IYA TUNTUƁARMU TA LAMBOBIN 07045308523 MUN GODE
Luba ce ke zuba wannan zance a gaban Hindu , Rukky da ‘yar modu. Zaune suke a falon Hajiya Kububuwa ana taya Hindu kwashe kayanta za ta koma sabon gida. To amma aikin na su bai je ko’ina ba saboda abun almarar da Luba ta shigo masu da shi. Bin ta kawai suke da kallo saboda tsananin mamaki. Ta ce
” Sai ina ganin kamar ba ni ba ce. Kun ga Almustapha kuwa Wow..mashallah..mashallah. Ban taba haduwa da mutumin da na ji ina son shi farat daya kamar shi ba! Ai kwana biyun nan da ba ku ganni ba ina gidansa. Kun ga gidan? Aljannar duniya!Dole ne yau na wuce wajen Iyannan na gaya mata yau fa na samu mijin aure! Don bazan juri na ga Almustapha da wata ba! Almustapha…ya rouhi..ya habibii qalbee!”
Rukky ta taso ta zunguri Luba ta ce
” Wai mafarki ki ke ko idonki biyu? Ko dai wani abu kika sha ya gaya miki karya? Na ji har kina batun aure”
Luba ta ce
” Garau nake ras! Ai daga nan wajen Iyannan zan je kawai ta fara shiri”
Rukky buga tsaki tayi ta koma ta zauna ta ce
” A duniyar nan dai luba, a yanzu ban ga son da za a yi masa marmarin aure ba!
Ta koma ta zauna.
Luba ta yi mata kallon sakaka. Sannan ta taso ta zungureta ta ce
” Sukari kin san wanene wannan mutumin kuwa!Uban gidan Idi maina ne fa. Ai irin wannan ba ka dangwali arziki ka bar shi ba! Ka bar shi ka je ina? Ai gwara ka samu gurbi ka dawwama anan daga ‘ya’yanka har jikoki sun huta da jaje! Me aka yi da maza in ji karya!Idi Maina ma mene ba a samu a jikinsa ba ballantana ubangidansa.”
Rukky ta ja dan karamin tsaki ta ce
” Ai ko wanene tsakanina da shi mu rabu a hanyar da mu ka hadu. Kurunkus!”
Sai a lokacin Hindu ta saka baki ta ce
” This is surprising yau da bakinki Luba kike ambatar aure? Gaskiya zan so in ga wannan mutumin dan na san ya isa! Isar tasa ma ta isa!”
Luba ta miko mata hannu suka kashe.
Sai a lokacin ‘ yar modu ya tashi yana rawa yana rera wata waka
” Ayyaraye daure jure
Zaman gidan wani tilas ne
Zaman gidan wani sai hakuri
Ai ba da kan ki aka fara ba
Ai da da kan ki aka fara ne
Da kin yi kuka kin koshi
Hindu ce ta taso ta biye masa suke taka rawa. Wai su a dole aure ya zo har ya tabbata.’Yar modu ya karkace baki ya rangwada guda suka tafa da Hindatu ya ce
” Wannan abu yana min siga! Muna jin aure a makwabta yau bana dai tamu za mu kai. Kuma dama ai abun na Allah ne budurwa da jika. Da haka da haka mu ma za a zo kan mu , ba mu fidda rai ba Alquran! Eh ai muna gayawa Azza wa jallah. Kawata lubancy ni zan miki babbar kawa. Billahillazi rabon cingan daga nan har kawayenki na kwatano. Abu namu maganin a kwabe mu! Ahayye Allah na dawo!”
Hindu ce ta tunkude shi ta ce
” Babbar kawa ki ke ko ni? Ji shisshigi da kwala kai a faranti”
Yar modu ya kama baki ya ce
” Yau naga abun da ya isheni ni jikar A’i. Wannan da da ke aka shimfida duniyar da ba kya bari mu karaso ba! Yo kin zama mahandamiya. Ki ci nan ki ci can dangin makwadaita! Don kawai kin ji nace ni ce babbar kawa shi ne kike tada jijiyar wuya? Kai Hindu amma kin yi faduwar bakar tasa! Kyangarann!”
Suka kwashe da dariya suka kara tafawa.
Luba ta ce tana fari da ido
” shirun ka nawan..ai ni kadai na san matsayin da zan baka. Ka manta kai ka fara kaimu la mirage. Ai da bazarka nake rawa!”
“Idan kima kara sa ni a cikin jinsin da ba nawa ba..babu abunda zai yana in yi tsallen alkafira nayi kuli kulin kubra da ke!” Cewar ‘yar modu
“Laaaa..yar modu wulakaci” luba ta fada tana masa kallon kasa kasa
Hindu ce ta ce
” Look guys..ku fa kun cika yarinta dayawa. Ke Luba wai ya ma aka yi kika san aure yake so. Kin san fa halin mutanen mu”
Ta harari Hindu da wasa ta ce
” Ai yanzu ba sai namiji na son aure ba ake aurensa. Yanzu ke ce zaki so auren sai ki bi dare ki bi rana kuma dole aure ya dauru! Zauna nan Hindu idan a tsaye kika kwana ni a tafiye na kwan! Wai kin ga gidan mutumin? Gari guda kamar wata masarauta. Da sannu zan zama sarauniya a masarautarka ya Nouri Mustapha! Kin san kuma shi ma fa na ga yana ra’ayina! Wallahil azeem faduwa ce ta zo daidai da zama!”
“Da kyau mutuniyar” ‘yar modu ya bata hannu suka kashe.
Duk abinda suke yi Rukky ta zuba musu ido bata ce komai ba.
Luba ta fara tattara wata jakarta ta hannu tana mikewa ta ce
” Bari ku ga. Ba a bori da sanyin jiki. Bari na je wajen Iyannan. Ina ga nayi wata 3 rabo na da gidan sai aike”
Hindu ta yi sauri ta ce
” Au ba zaki raka mu wankan sabon gida ba?”
Gaba tayi ta ce
” Hindu kiyi ta kan ki in yi ta kai na”
Wata motar ta kirar corolla ta shiga tana tukawa tana tuno abubuwan da suka faru kwana biyu da suka wuce.
Duk yadda take tunanin masoyin na ta da arzikinsa ya wuce nan. Ta tuno irin baja bajan da ta samu a gidansa da makudan dalolin amurkan da ya cika ta da su kafin ta baro gidan.
To yanzu da take a matar waje kenen ballantana ta shiga daga ciki! irin shagalin da za a yi a wajen bikinta abun sai wanda ya gani. Dole ne ta rarrabawa malamanta kudi su sa shi a gaba! Ina ba zai yiwu ba alewa ta zo hannun yaro sannan ya bar ta ta fadi kasa! Inaa…
Gidansu na nan a yadda yake sai dakin Iya Tamadi da ya banbanta da na kowa. An sake masa ginin bulo an yi fenti an sa mata sabbin kaya. Shi kuwa baban yara da aka ce za a mishi gyara cewa yayi ba ya so a bashi kudinsa a hannu.
Ba ta yi sallama ba don yanzu ita ta fi karfin sallama idan za ta shiga gidan. Sannan uwar gulma Iya Asabe za ta kafa ta da habaici. An ya kuwa ba zata sa a batar da matar nan ba? Tunaninta kenen.
Rashin sallamar tata bai sa ta kasa yin ido biyu da Iya Asabe ba daga shigowarta. Ta watsa mata harara ta ‘ba ki isa ba’ ta wuce dakin uwarta. Tana jiyo Iya Asabe na cewa
” Ah fulanin tashi yau an bayyana kenen”
Iya tamadi na zaune tana tsintar wake tana kallon wani shiri a talabijin Luba ta shigo.
“Lale lale maraba da auta”
Cewar iyannan fuskarta fal faraa . Ko banza ta san yau ranar samu ce. Luba zata zauna ta ce
” Auta kar ki zauna anan. Ga wata dadduma can dauko ki shimfida ai ta fi laushi”
Maimakon ma ta ji tayin da ake ma ta sai ta fasa zaman kasan ta fada kan kujera. Ta buga wani uban tsaki ta ce
” Gaskiya ina da mahassada. Amma …k’ “
Iyan ta kalle ta ta ce
” Au na san ba zai wuce Asabe ba. Ai ita Asabe wannan shigar da take ganin kina shigowa da ita ta alfarma da wannan dankareriyar motar su ke ruda ta. Bar ta! ‘Yar matsiyata har ubanta ya mutu da tsohon bashi akansa! Baruma ce fa ai anan tsiya ta kare!
Dalilin kenen da ko ‘yan unguwa nake gaya musu ba ki nan kina saudiya. Aiki ya kai ki.Yo ba sai sun gan ki ba ballantana suyi gulma? shegu iyayen sa’ido!”
Luba bata kula ba. Tunaninta yana gurin sun yi za su hadu da Al Mustapha yau da dare. Irin shigar bajintar da ya kamata ta yi. Ta dago kai da murmushi ta kalli iyannan ta ce
” Iyannan ai sai ki fara shiri. Bana dai adduarki ta kusa karbuwa. Na samu miji abinda ya rage mu samo kan sa ayi aure. Miji dai na wuce sa’a akwai shi!”
Iyannan ta karkace baki ta rangada guda tana habaice habaice ta ce
“Da kyau! Auta ta..auta ikon Allah. Masu miki bakin ciki sa sha kuka. Allah ya kaimu..ni jikar mutum hudu ina zan saka mutane na? Ko wani dakin za ki tayar mun?” Ta karasa tana dube duben girman dakin
Tsaki Luba tayi ta ce
” ke iyannan baki gajiya da bani bani. Yo idan na samu na aure shi ai gidan kan ki zan gina miki. wannan ma ai karamin al’amari ne”
Ta washe baki ranta kal. Gwara dai Luba tayi auren a daina saka ta a waka. Ana yiwa diyarta bakin ciki an ga kudi sun zauna ma ta.
Luba ta lalo wasu kudade ta mikawa Iya ta karba tana rawar jiki ta ce da ita
” So nake ki sa malamanki su fara min aiki. Yanda duk ta inda aka bullo masa da maganar aure ba zai ki ba! Ai maganin shege karan maguzawa!”
Iya Tamadi ta ce
“Ai kuwa dai..kin yi farar dubara. Mazan yanzu sai da haka. Da zafi zafi akan daki karfe. Daga wannan maganar can zan wuce”
Luba tayi murmushi ta ce
” Da kyau Iyanan..shi yasa nake son ki. Ke kadai ki ke iya rufamin asiri”
Daga nan ta hau motarta ta wuce. Ta danna wata wakar nancy ajram tana saurare tana bi. Ranta kal! Duniya sabuwa. Duniyarta da Al Mustapha.
******************************
Sabon gidan Hindatu wadatacce ne mai sassa guda biyu. Na farkon shigowa nan ta bari a matsayin sashenta da zata dunga cin karenta ba babbaka.
Na daga ciki kuma anan ta ajiye yaranta. Ta dauko wata tsohuwa mai kula da su da mai gadi ta ajiye a gidan.
Sai a yanzu take jin hankalinta ya kwanta yaranta za su samu kulawa kuma ko banza ta huta da fadan Hajiya uwani. Yaushe ma a rayuwa zaka bari a kankameka a takureka kana da ‘yancin kan ka?
Sai dai akwai wadansu canje canje da ta gani game da Abba da yasa jikinta yin sanyi. Tun farko ta san Abba tunaninsa da maganganunsa sun fi karfin shekarunsa to amma tana mamakin irin kallon da yaron ke jeho mata.
Yawa yawan lokuta idan ta kawo musu sabon abu sai Asiya take tsalle tana murna sai ta ga Abba bai ko nuna a fuska ba. Daga baya ma ta lura ko abubuwan bai cika tabawa ba.
Jikinta ya fara yin sanyi ko zigar da ake masa a makota ya fara dauka da irin maganganun aibatawa da ake jifanta a unguwa da su. Shi ne tayi shawarar dauke su gabadaya ta kawo su gidanta. Ta sa akai musu kofa ta baya inda za suke shiga da fita yanda ba zasu takurata ba.
Ta gayawa kan ta za ta dunga taka tsan tsan da shigowar abokanan iskancinta ko don idon yaron.
Ranar da suka tare Hindu ta shigo da su cike da doki. Asiya na ta tsallen murna musamman da aka nuna mata dakinta mai dauke da kaloli daban daban. Amma Abba bai ce kamai ba. Hindu ga dafa shi ta ce
” Yaya dai yaro na, ko kalar fentin dakin naka bai maka ba a canja wani? Ka san fa duk don ku nake yi”
Ya dago ya kalle ta a tsanake, cikin kwayar idonta ya kalla. Ta ji wata irin faduwar gaba da bata taba jin irinta ba. Sai ta ji wani irin tsoron yaron ya tsirgar mata. Abba ya mata kwarjini dayawa. Meye haka?
Ya ce
” Ni mama, mecece sana’arki?”
Kallonsa take amma bata samu ansar da zata ba shi ba. Ba dai lokaci yayi ba? Ba dai illar lokaci zai yi halinsa ba???
Tafe suke akan titi Luba ce da Rukky a cikin motar Lubar. Luba ke tukawa a hankali sanyin ac na dukansu sai karan sautin cikin radiyo dake fitowa na wata wakar Nancy ajram.
Luba ta sa hannu ta kara volume mutuniyar ta ce kamar ‘yan tashar radiyon sun sani suka sakata. Ta ci gaba da bi tana jinjina kai kwanan nan nishadi take ji. Ta cigaba da cewa Rukky
” Sukari ba zaki gane ba, ke fa ba ki taba fadawa so ba. Labaransa ki ke ji a cikin littafan hikaya. To yaushe zaki adar?!”
Murmushi Rukky tayi. Bata bukatar bayani. Ita ta san ba ita bace ta da. Rayuwarta ta da a shafe take ba a tuno ta bama a saka ta a lissafi. Ta yarda bata san so ba, wannan shi ya fi ma ta komai sauki!
Ta dubi Luba a karkace ta ce
” Ai kuwa dai sai ku masoya. Ko ku ne laila da majnun?”
Dariga luba ke yi irin dariyar nan ta nishadi ta ce
” Sukari kenen. Ke fa kin dau maganata a sha- sha -gare ko?”
Murmushi Rukky tayi. Luba ta dora da bayan fuskarta ta dan canja
” Amma kin san me? Shi sai na ga baya doki na kamar yanda nake dokinsa. Kamar ma mace bata dame shi ba. Shi dai komai aikinsa. To amma idan ya dauke ni irin karuwar da ake dauka a aje a manta da babinta to da sauransa! Allah sukari zan iya yin komai akan na samu gayen nan. Hmn…k’ “
Rukky ta ce
” Ai naga alama. Ki sani dai karuwa bata zurfafa so. Dan na ga kin zira kai dayawa. Kar ya zo ya miki abinda zaki haukace. Ko da yake yanzun ma a haukace ki ke!”
Luba ta daka mata duka ta ce
” ke ma ai don baki gan shi ba ne shi yasa kike cewa na haukace. Amma…au..au..kin ga karfe biyu ma na rana bari mu je ofis din sa mu gaisa. Daga nan sai ki kallo min shi za ki gane me nake nufi”
Ta juya kan motar ta koma baya hanyar ofis din Almustapha.
Rukky ce ta fara fadace fadace ta ce
” Haba Luba mu da muke da AP ki bari a dawowa ma je”
Luba bata kula ta ba. Ganin haka sai tayi shiru tana gunagunai ta na cewa
” Ai fa mun shiga uku”
Harabar ma’aikatar babu mutane sosai. Yawa yawansu sun yi sallah sun koma ofishoshinsu. Rukky ta cigaba da kallon wuri cikin mamaki. Ah lallai dole Luba ta rude kyau da tsarin wajen ya baci.
Bata ga laifin Luba ba, ai kowa ya samu rana dole yayi shanya. Ita ma da zata samu wani ya taya ai da ciniki ya fada.Tinkis tinkis take bin ta a baya har suka hau lifter zuwa ofis din sa. Sakatariya dama ta san luba don haka kawai sai suka shiga.
Wata irin shiga ce a jikinsu wanda ba marabarta da tsirara sun sa wani coge mai tsini da ke bayyana kowane takunsu.
Yana danne danne akan kamfutar da ke gabansa. Aiki ya sha masa kai. Ya ji shigowar Luban ya daga kai yayi mata murmushi da alamar nuna su karaso. Suka karaso Luba ta ce
” Habibii ga aminiya ta nan na kawo ta ta kwashi gaisuwa.”
Kallo daya ya dago yayi mata suka gaisa ya dauke kai zuwan kan abinda yake kallo.
Yanda yayi matan bai musu dadi ba musamman Luban da take gani ya yabantata a bisa yanda take kambama shi a gaban kawayenta.
Ita kuma Rukky sai ta tabe baki bata wani damu ba idan tayi la’akari da tangamemen ofis din sa na masu fada a ji. Kuma Luba ta ce shi ne mamallakin ma’aikatar gabadaya. To dama masu kudi suna da wata dabi’a banda izza da girman kai ne?
Cikin halin ko in kula ta ce da Luba zata sauka mota ta jira ta don ta dan ba su waje su tattauna, tayi musu sallama tayi takunta kwas kwas ta fice.
Taku goma sha biyar tayi kafin ta fita ya kirga a ran sa. Me yasa ya kirga ya tambayi kan sa. Me ya sa?
Ko abin daga zuciya ne??????
#Maitafiya
13. Abin sirri ne
Abinda ke cikin zuciya ai sirri ne!
Kano, Nigeria
Iliyasou Tillaberi ke zaune a daya daka cikin kujerun ofishin Al Mustapha na I and A group of companies. Kallo daya za kai masa ka gane ya sha jinya jikinsa ya nuna matsananciyar rama. A hannunsa wata sanda ce da yake dan dogarawa irin ta masu kudi.
Al Mustapha ke zaune yana fuskantar sa. Ya riga ya sanar kar kowa ya shigo ofishin suna ganawa da mahaifinsa. Bayanai yake yi masa akan wasu kamfanoni da suke son siya su mayar da su masaka. Uban na saurarensa har ya gama ya ce
“Komi hwa yana yin kyau aikinka yana kyau. Ita dukiya ba a barinta ya wannan, juyata ake ta hayayyafa hal ‘ya’ya da jikoki. Tilas idan kana so hwa ka girma kayi kasaita ka buwaya sai ka zamne na kasanka ka dakusal da su ya zamana ba a kallon kowa sai kai! Yanzun wannan da danuwanka da ran shi tare za kuyi komai. Allah kyauta makwancin shi”
Almustapha bai ce komai ba ya tabo masa abinda ke masa ciwo a zuci. Kuma bai ga dalilin da yasa zai jajanta ba bayan shi ya jawo. Wani irin abu yake ji kan uban da ya kasa fassarawa. Sai ya gwammace kawai yayi shiru.
Uban ya tsaya yana duban dan yana kallon yanayin fuskarsa ya ce
” Diba yadda cuta ke neman halakani yarona…kamata yayi ka zubal da komi ya wuce. Rayuwace fa gaba gareka ga tarin dukiya nan ubanka ya nema maka. Mi zai dame ka?”
Ya kalli uban kamar yanda zai kalli sa’ansa ya ce
” Ina gaya maka hakkin Ahmadou ba lallai ya barmu ba. A nemo yarinyar nan. Abba na roke ka a nemo yarinyar nan”
Wani irin kallo uban ke masa na tsananin mamaki. Ya rasa wannan irin bala’i da me zai ji ne wai? Shi duk ‘ya’yansa maza da yake alfahari da su ba su da magana sai ta wannan yarinya?
Babu abinda ke damunsa irin mafarkan da yake da Ahmadou. Ya kan gan shi yana masa fushi yana tunkuda shi cikin wani rami. Babu ranar da zata wuce da bai yi shigen irin wannan mafarkin ba. Abinda ya hana lafiyarsa daidaita kenen. Ya sa damuwa da fargaba a ransa jinin sa sai kara hauhawa yake.
Ya tuna irin shigen ficen da yayi na jawowa Ahmadou masifu na karayar dukiya da sanadin mutuwarsa. To amma kamar Ahmadou din ya bar wata halitta da take neman fito na fito da shi. A dalilin hakan ya rasa dan sa yanzu kuma Almustapha na masa zancen banza. Ya dake irin na mazan jiya ya ce cikin nuna alamar gargadi
” Idan har kana kamnal muyi shiri da kai to ka tsaya inda nicce maka. Idan ka ce za ka shiga wannan magana kuwa..ma gamu!”
Da haka ya kokarta ya tashi, tashi irin na jikin tsufa. Almustapha ya taimaka masa. Ya raka shi zuwa waje gurin zungureriyar motarsa ya bude masa mazaunin mai zaman banza ya zauna. Ya dago ya kalle shi a tsanake ya ce
” Na tuna. Ka je gidan abokina Abbassodor Mukhtar, mun tattauna mun yi za ka je ka ga diyal wajen shi ku zanta. Ya kamata a ce yanzu wannan ka ajje mata hakanan. Kai da ka ke dulmiya kan ka cikin halkokin siyasa ya kamata ka ajje mace don a kalle ka da mutumci. Kal mutane su ga hakan a matsayin gazawa.
Duniya ita ake yiwa bauta gwamma ka moreta lokacin da kake da rai. Ranar da ka zamo babu wani ne zai maye gulbinka.”
Gyada kai kawai yayi. Wasu maganganun sun shiga zuciyarsa sun zauna, ya fara hangen duniya a wani waje mai dogon zamani da zai isheka ka cika burirrikan ka. Suka yi sallama shi kuma ya dawo ofis.
Ya cigaba da juyawa akan kujerarsa tunani sun masa yawa amma akwai wani abu da ke damunsa a zuciya. Ya kasa manta fuskar wannan yarinyar da ya gani da Luba.
Shi mutum ne mai tsananin taste din yanmata. Farkon ganinsa da Luba ya ga ta masa zata cike wani gurbi a wajensa to amma kallo daya yayi wa kawar ya ji yana so ya kara kallonta. Yanayin idanuwanta ne suna masa wani irin kamanceceniya.
Bai damu da fadan da zai haddasa tsakaninsu ba karuwa wani daraja ne da ita da za a duba a ki abu don ita? Mai kudi kuma yana da haramiya ne balle shamaki?
Dadin duniya kenen ka mallaki abu a lokacin da ka ke son mallaka ya kuma zo maka a yanda ka ke so. Yarinyar nan ta masa! Ai kawai yar da luba zai yi ya dauketa duk da ya ga Luban ta zarma dayawa. Amma shi gaskiya yanzu ba ya jinta kwata kwata a rai.
Ya dauko wayarsa ya kira wani mutuminsa da yayi wa maganar yarinyar jiya. Kara daya biyu suka gaisa. Ya ce
” ya ya bashari…ka gano gidan da yarinyar take kuwa?”
Ya ce
“Eh yallabai…amma gidansu daya ne da Lubar”
Yayi shiru, da zai ce ” so what” sai yayi tunanin kar ita Luban ta bata mai show. Sai ya ce
” Ka ce mata kawai ka samo mata bako, zan je gidan daga nan zan karba”
Ya ba shi amsa da
” Ok oga”
Ya kashe wayar yana cewa
“Good, very good”
Ba shi da matsala ta wannan bangaren. Sai dai ran shi na raya mishi ya kamata ya rage neman matan nan ko dan harkar siyasa kar wani ya shammace shi ya dau hotunansa. To ko yayi aure ne? Ya tuno tayin mahaifinsa ya ja tsaki, bazai je ba.
Ran sa ya raya masa
To ko yarinyar…?
Ya buga wani uban tsaki yana jin haushin zuciyarsa. Duk duniya ya rasa wacce zai aura sai karuwa? Karuwar titi da maza suka gama jagwalgwalawa! Ai tsakanin ka da karuwa kayi abinda za kayi ka watsar da ita!
Da daddare kawai zai karasa wajen wannan yarinyar..me sunanta ma? Oho!
Zai neme ta ko na sati daya ne ya ji ko abinda yake ji akanta zai ragu. Ya san ” infatuation” ne da sannu zai neme shi ya rasa.
Da sannu zai nemi yarinya mai hankali ya aura, cikakkiyar mace.
Da irin wannan tunanin ya tashi daga ofis.
Abinda Almustapha ya manta shi ne
Rayuwa tana zuwa maka ne a yanda ka dauketa, ba zaka taba girbar abinda ba ka shuka ba! Idan hairan hairan…idan sharran sharran!
*********************************
” Ka san illar shaye shaye kuwa? Tabdijam!Da ka san irin illar da yake yiwa rayuwarka, to..to…tamkar ka je ka rungumi transifoma ne ana ruwan sama da daddare! Kai ma ka san ubanka zaka ci ko?”
Cewar Iliya bakanike. Zaune suke akan benci da shi da wasu maza guda biyu sababbin daukan aiki a wani gidan mai na Total. Magana yake yana sakace da wani dan tsinke bayan wata mai abinci ta kawo masa shinkafa da wake ya siya. Da kyar ya sayi naman goma ya dora akai ga shi don jaraba naman ya zame masa kajaga.
” Naman kirki ma ba za a sa a wa mutum ba da kudinsa, sai an hada masa da jijiya” ya fadi yana wurgar da tsinken.
Wani a gefensa fuskarsa duk cin zanzana ya ce
” Ai oga ka gane ko? Rayuwar ce sai da haka ka gane ai..abubuwan duniya sun yi wa mutum eh..ya..ne…dole shi ma ya dan dunga afawa..yana..wullawa ko don ya ji garau. Ka gane ai.. idan ba a yi ana hawa gajimare..sai ka ga abubuwan ba sa tafiya….su na yiwa mutum eh..ya ne..”
“Eh…eh ..eh wallashi oga” Cewar wani tsamurmuri a gefen da tabar wiwi ta zuke shi tas!
Kallon takaici Iliya ya musu ya ce
“Matsalar ku ku baku da hankali. Ina wani wali da ya zo dazu ka gan shi ai..mai farkakken wando nan nan ya roke ni abinci na ce a zuba masa na hamsin. Kwarankwatsa dubu da anan yake aiki, Oganmu ne amma da ya kafa shaye shaye ka gan sa nan kamar tuburan mahaukaci! Tun yaushe aka kore shi baya komai yanzu sai yawo da roke roke.
Wai ya ma za a yi mutum ya zama sakarai makiyin kan sa. Wadanda kuka taso tare ka ga suna samun cigaba a rayuwarsu ana damawa da su amma kai sakaran banza! Ko ta kai ba a yi ka kafa zuke zuke. Ka kashe rayuwarka ka kashe ta ‘ya’yanka da sauran dangi. Ka zo a gyara zaka koma a alakoro. Ka je lahira walakiri ya suburbude ka!”
Duk wannan hirar da suke yi Rukky ta kasa kunne tana jin su. Ita ma zaune take a wani benci nesa da su kadan tana jiyo su. Wata jar atamfa ce a jikinta da aka yiwa dinkin doguwar riga. Ta daura dankwalinta daidai da zamani amma bata yafa komai ba.
Mai ta zo sha sai ta bayar da motar a mata service tunda ta ga ba wani dadewa ake ba. Suka bata benci ta zauna tana danne dannen waya amma kunnenta na kan su Iliya.
” Iya kano kawai idan ka duba adadin benelin din da ake kwankwada! Kai! Lamarin ya baci. Wallahi wani ana ce masa Raf a makotanmu taba kadai sai da ta dagargaza masa huhu a haka ya mutu..yo Allah na tuba kanwar uwarsa ce?”
” Ah..Allah oga har da laifin gwamnati ma..ai gwamnati bata yi ba oga..Allah ya tsine ma ta!….inaaa..ta bar mu ba ko sisi” cewar mai cin zanzanar nan
Wata muguwar harara Iliya ya watsa masa ya mike yana cewa
“Tun da gwamnatin ita ta halicceka ba..wawa kawai. Gwara ka hankalta ka gyara rayuwarka kafin lokaci ya kure maka.”
MASU ƁUKATAR A TALLATA MUSU HAJOJINSU ZA SU IYA TUNTUƁARMU TA LAMBOBIN 07045308523 MUN GODE
