Search
You have no alerts.

    MASU ƁUKATAR A TALLATA MUSU HAJOJINSU ZA SU IYA TUNTUƁARMU TA LAMBOBIN 07045308523 MUN GODE
    So ai ruwan zuma ne, idan ka sha ka ba masoyi!

    Niamey, Niger Republic

    Rokaiyatou ta cigaba da kallon hanya yayin da take wasan kasa a kofar gidansu ta ga ta inda Momodou zai bullo ta ruga. Can ta ji an kwalla ma ta kira “Rokaiyatou”! daga kan da za ta yi sai ta hange shi ba ta yi wata wata ba ta fyalla gida a guje. Yarinya ce da ba za ta wuce shekara 8 ba jikinta ku san duk tsummokara. Ba ta yi wata wata ba ta fada bayan babarta ta kwakumeta ta ce

    ” Momma, frère Momodou shiddawo ya tardoni ina wasan kasa”

    Uwar ta tunkude ta daga jikinta cikin hausarta ta zallar kananci ta ce

    “Ke kaleni, ku je can ku karata”

    Momodou ya shigo da riga “long sleeve” fara da shudin wando bayan sa goye da jaka irin ta yan makaranta, ya sa safa da kambos. Ya nufi bayan Momma ya janyota da kunne ya murda ya ce

    “Mi na gani kina yi waje?”

    Ta na ta jan kunnen kokarin yakicewa shi kuma ya kalli momma kamar me neman bayani ta dago daga tsintar shinkafar da take ta ce

    ” Rokaiyatou, K’…ai kadan ka gani..kamar mai aljanu..ai duka kawai zaka ma ta sai ta ji a jikinta”

    Ya kura ma ta ido hawaye kwance male male a fuskarta, gashinta mai tsawo da yawa ya cukurkude ga kasa kamar an yi yaki. Kafafuwanta butu butu kamar tayi hakan rijiya. Sai kuma ya ji tausayinta ya kama shi da ga rigar jikinta yar yaloluwa da yawan wanki ya sa ta kode ta jeme. Abubuwa dayawa suka cigaba da yawo a kansa duk da karancin shekarunsa dan yanzu ma yake aji shida yana neman gama makaranta.

    Ya janyota suka zauna akan tabarma yana kakkabe ma ta gashi ya ce

    ” kin yi abinci dai ko?”

    Yana so ya ji ko ta ci abinci.
    Ta girgiza kai ta ce

    ” yanzu dai Momma za ta dahwa”

    Ya juya ya kalli shinkafar da ake tsinta ‘yar kut a faranti wacce ya san bai wuce a ci ta da mai ba. Ya bude jakarsa mai dauke da yar ” cooler” na abinci ta yan makaranta , dankali ne ko tabawa bai yi ba ya sa a gabanta. Ta fara ci da budu budun hannayenta ba tare da yace ta je ta wanko ba, ya cigaba da kallonta. Momma ta dube su tayi murmushi ta ce

    “Kai dai baka son cin abincinka, sai dai ka kawo wa kanwarka”

    Murmushi yayi. Sai ya sa hannu ya zaro biskit da wani dan lemo ya ce

    “Wannan kuma sai kinyi wanka, ba ki son wanka ko?”

    Ba ta kula ba cin abinci kawai take. Ya kalli. Momma ya ce

    ” Ina ruwan da za tayi wanka?”
    Ya kama haba tace

    ” Au har wani ruwan wanka zan ke ajiye ma ta? To sau nawa zan ajiye”?

    Murmushi kawai yayi ya nannade hannun rigarsa ya doshi inda rijiya take. Ya jefa guga ya fara jan ruwa har ya cika wani dan karamin bokiti. Sai ya yafito yarinyar da hannu ya ce

    ” je ki dauko sabillo”

    Ta shiga daki ta dauko ya ce ta tsugunna ya fara wanke wannan kan na ta dikin dikin har sai da ya fita tas. Ya kalli Momma ya ce

    ” Dan Allah Momma ki kai ta bayi ki ma ta wanka”

    Ta yi murmushi ta mike tana cewa

    “Tou momodou na Rokaiyatou ai idan ban taso ba ba zaka kaleni ba”

    Ta zo ta karbe shi. Ya dauki jakar makarantarsa tana kallo ya zaro kudi ya cusa a karkashin farantin shinkafar nan yayi tafiyarsa ba tare da ya waiwayo ba. Ta gyada kai a hankali a cikin ran ta tana tunanin irin kaunar da momodou ke yi mu su sai ta raya a ranta ko dan Rukaiyatou jininsa ce? Ta kawar da wannan tana mai la’akari da cewar duk ‘yan gidan ma ai yanuwanta ne to amma wa ta ishi kallo? Momma ta cigaba da dirzar Rokaiyatou da sabulu ta na mai ayyanawa a ranta , ko ya rayuwa za ta yiwu ba Momodou?

    Washegari da safe Rukaiyatou na tsaye a kofar kangon gidansu tana hangen wani tsararren bene mai bakin gate tana so ta ga fitowar frère. Gida ne tangameme wanda kallo daya za ka masa ka san an zubar da dukiya. Can aka bude tangamemen gate din motar da take kai yan makaranta ta fito. Tun daga nan ya fara kwalla ma sa kira tana daga ma sa hannu. Da ma ya san tana tsaye domin al’adarta ce yin hakan. Yana isowa zasu wuce shi ma ya daga ma ta hannu suna ta dariya.

    ***********************
    Iliyasou Tillaberi mahaifin Momodou yayane ga Ahmadou Tillaberi mahaifin Rukaiyatou. Wadanan yanuwa suna zaune ne a garin Niamey suna gudanar da kasuwancinsu. Tafi tafi sai suka bude kamfanin hadin gwiwa na sarrafa shinkafa , taliya, flour da mafi yawancin nau’in abinci. Kasuwancunsu ya bunkasa tsakanin Nigeria, Niger, togo , Mali , cameroon da senegal. Daga baya suka kafa babban kamfani da reshensa biyu Nigeria da Niger. Aka sa wa wannan kamfani suna I and A and sons.

    Maganar irin tarin kudi da kadarori da suka mallaka wani abu ne da mai karatu zai sha mamaki. Kasuwanci ya karbe su , su ma kuma suna dagewa game da bunkasar arzikinsu. Iyayensu duka sun rasu sai baffaninsu da ke Tillaberi, wani karamin gari a yankin Niger.

    Iliyasou wani irin murdadden mutum ne mai bakar zuciya. Ya fara da auren uwar Mommodou anan Niamey wata zabarmiya me suna Hajiya Khulsomou. Ta haifa masa ‘ya’ya biyar mata sai namiji daya wato Momodou. Sai kuma Allah ya jarabce shi da son wannan yaro.

    Daga baya yayi aure a Nigeria da wata mai suna Hajiya Hadiza bakanuwa ce ya usul ta haifa masa da guda daya tal Al Mustapha. Wani irin tsananin kishi ke tsakanin wadannan mata biyu har ya zamana daya ba ta zuwa kasar da daya take. Amma me? Wani irin zumunci ke tsakanin Mustapha da Momodou da suke ku san sakwannin juna. Sun shaqu ta inda takanas daya kan bar kasar sa ya ziyarci daya duk da halin da iyayensu mata kan nuna na tsanar hakan.

    Ahmadou Tillaberi kafin ya hadu da mahaifiyar Rukaiyatou mai suna Ramlatu ‘yar kano yana da matan aure guda uku. Suk cikin matansa ba wacce ta taba ko batan wata. A matsayinsa na attajiri mai tarin dukiya zai so wataran in ya fadi ya zamo yana da magaji. To amma ya zai yi?

    Wannan rashin haihuwa na Ahmadou yana yiwa Iliyasou dadi a rai duk tunaninsa bai wuce yau in ba ran kaninsa to komai ya zama na sa. Ana cikin hakan kwatsam rannan kasuwancinsu ya kai su kano duba wani sabon kanfani a lokacin. To anan ne fa ya ga wata kawar Hajiya Hadiza matar yayansa mai suna Ramlatu ya makale ma ta. Ba yanda Iliyasou bai yi ba akan ba ya so amma ya jajirce sai ya aureta.

    A sanin Iliyasou Ahmadou neman haihuwa yake, shi kuma ba ya fatan hakan dalilin da ya sa ya tsani auren kenen. A bangaren Ramlatu kuwa dama marainiya ce a hannun yayanta take, ta kafe ta tsare ta ce sai Ahmadou yayanta ya rantse ba zai ba wa wanda ba dan kasa ba. Aka dunga tafka rigima daga karshe yayan ya ce in dai ta yi auren nan to ba shi ba ita, ta ce ta amince. Aka yi aure Ahmadou ya tafi da amaryarsa Niamey.

    Tun Momma na amarya babu wani dan gidanta da ya wuce Momodou. Yaron na kaunarta ita ma haka. Hakan na kona ran Hajiya khulsomou a ganinta an zaqewa danta ga kuma karin abun kawar kishiyarta. Sai wata gaba ta kullu, sai gore gore na rashin haihuwa ganin cewa har a lokacin ita ma bata samu ciki ba. Ganin an yi shekaru Ramlatu ba ta samu ciki ba sai hankalin iliyasou ya kwanta su kuma kishiyoyinta suka hau ta da habaici. An auro ta daga Nigeria dan ta nuna musu iya haihuwa ashe duk kamwar ja ce.

    Lokacin da Ramlatu ta samu ciki har ya fara fitowa sai fa hankalin kowa ya girgiza, sai aka fara kallon kallo. Ahmadou kamar zai yi hauka don murna. Nan fa kaunarta ta kara azalzakar zuciyarsa aka shiga tattalin ciki ana ririta shi. Sai kuma wani abun al’ajabi ya faru.

    Al’amuran dukiya na Ahmadou suka fara ja baya. Duk a abunda ya taba sai ha zamo asara. Nan da nan fa yayansa da matansa suka fara nuna Ramlatu da cewar ita ke da farar kafa kuma wai zata haifa musu bala’i. Da aka haifi yarinya sai abubuwan suka kara tabarbarewa amma me? Shi bai wani damu ba farincikinsa kawai ya samu abun kauna Rukaiyatou. Ya so Rukaiyatou irin son da ake yiwa da guda daya tilo da yayi jinkirin zuwa. Sai matansa suka fara ganin haukarsu ta zama da shi ba abun duniya ba da ba jika..me zai zaunar da su? Sai suka watse abunsu suka bar shi da Ramlatu.

    To amma yawa yawan kudadensa suna hannun Iliyasou na kanfanunnukan hadin gwiwa da suka bude. Zaman iliyasou babba sai ya zamana ya fi karfi akan dukiyar don haka sai ya tuntube shi da batun kudinsa. Sai ya nuna ma sa cewar ba fa zai iya fitar da komai ya sa a hannunsa ba hakan kamar ganganci ne yayi hakuri zai cigaba da juya musu. Ahmadou mutum ne mai hakuri sai ya jure hakan ya cigaba da juya dan abunda ke hannunsa.

    Tun haihuwar Rukaiyatou Momodou ya kalli Momma ya ce

    ” shikenen kin haihwa min mata, ni ina kamnar ta! ”

    tayi dariya ta ce

    “Allah Momodou? To inshallahu in ta girma kai ne mijin”

    Sai ya kama tsalle irin na yara har ya tafi da gudu ya gayawa babarsa . Ita kuma ta ce a fusace

    ” Ba ka amren mayya, ita ta lashe dukiyar Ubanta!”

    Kamar abun almara, Rukaiyatou na da shekara biyu Ahmadou Tillaberi ya yanke jiki ya fadi a bayi ko shurawa bai yi ba. Ai tun daga nan sai fa nuni ya koma kan su, lallai Ramlatu da diyar ta sun tabbata mayu masu lashe dukiya da kurwa. Daga nan sai rayuwa ta musu kunci. Iliyasou ya rantse da cewar Ramlatu ce ta jefe shi da asiri ya fadi ya mutu don ta gudu da ragowar dukiyarsa, don haka sai ya hau kan dukiyar Ahmadou ya danne babu ma batun rabon gado. Da kyar aka samu ya basu wani kangon gida anan kusa da shi wancan tsararren gidan na su ya siyar ya ce shi zai rikewa marainiya dukiyarta.

    Momma tayi kuka ta gode Allah ganin yadda aka musu fin karfi ita da diyarta. To amma ina zata je? Wa zata gayawa? Babu. Yayanta da take da shi ma sun riga sun raba hanya, tun da tayi aure bai taba neman ta ba. Sai kawai tayi zamanta a wannan gidan take dinkin fata na takalmi da jaka take kaiwa kasuwa suke cin abinci.

    Iliyasou ya watsar da su ya ma manta da wasu iyalan Ahmadou. Baffaninsu sun sa baki ya samu ko diyar ce ya kula da ita amma ya shashantar da batun. Wani irin mulki na zallar zalunci yake gwada musu da asalin fin karfi.

    Momodou yaro ne amma ya taso da tsanar wannan dabi’a ta mahaifinsa yana matukar jin takaicin hakan. Mahaifin ya kwallafa rai akan sa a matsayinsa na babban dan sa namiji hakan ya sa tun yana karami ya fara dora shi akan harkar kasuwanci. Shi kuma sai ya taso da kauna da tausayi na wadan nan bayin Allah ta yanda duk abunda ya samu to nasu ne.

    A shekarun girman Rukaiyatou ta taso ba ta shaku da kowa ba sama da yayanta frère, wannan shakuwar da ko iliyasou Tillaberi ya gaza rabawa. Al’adarta ce kullum ta tsaya a hanya ta ma sa bye bye idan za shi makaranta ba don ita tana zuwa ba.

    Ganin hakan ne yau ya ga bai gan ta ba sai ya shiga gidan don a zatonsa ko ba lafiya ba. Da shigarsa ya tarda ta tana wasan ruwa, shigowarsa tayi fatali da ruwan ta ruga daki. Momma ta fito daga wajen wani kewayayyen langa langa inda take tukin tuwo tana share hannayenta a jikin kodadden zaninta. Tayi murmushi ta ce

    “Mutuniyarka ta gudu ko”?

    Ya mayar ma ta da murmushin sannan ya ce bayan sun gaisa

    “Na ji ta shiru bana ganinta a waje, nayi zaton ko bata da lahiya ne, lahiyarta lahiya?”

    Ta kwalla mata kira, ta zo tana rabe rabe. Ya zaunar da ita kan tabarma ya ce
    ” Me ya hwaru ba na ganinki waje da sahe?”
    Cikin kasa kasa da murya ta ce

    ” Ba kowa yana zawwa L’ècole amma ban da ni ba”

    Yayi shiru kamar mai nazari sai can ya ce
    ” kina son zuwa L’ècole ko?”

    Ta gyada kai. Ya ce

    ” Ba ina zuwa ina koya miki ba har kin ka iya karatu ba?” Ta ce

    ” Ai naka ba irin na L’ècole ba ne, ba a sa kayan L’ècole” ya ce

    ” To shikenen kamnata, in dai ina raye sai kin je kin ji ko?

    Ta fara tsalle. Ya fito da wasu yan kudi a hannu ya manna mata yana dariya.

    Duk abinda suke Momma na kallonsu. Ya mike zai tafi ta kira shi cikin damuwa ta ce
    ” Kana dan makaranta ka ke wa wani alkawarin sa shi a makaranta?”
    Ya sosa keya yace

    ” jiya ne fa muka gama gwajinmu na karshe sai jiran sakamako kawai”
    Ta ce

    ” Alhamdulillahi, dana ya girma. Amma ina fatan ba mahaifinka zaka gayawa ba, ka san bana son kuna samun matsala akan Rukaiyatou”

    Shiru yayi na wasu dakiku sannan ya ce
    “Kar fa ki sa komai a ran ki Momma na san yanda za a yi na samu kudi. Ba ki san yanzun haka Abba ya bude min shago a Grand Marchè ba? Nan zan ke zuwa kafin sakamakon gwajin mu ya fito. Babana ke da alhakin kula da ita kuma ya ki. Wallahi idan ki ka ga ban kula da Rokaiyatou ba, to ba yadda naka iyawa”.

    Kwallar cikin idon Momma ta tsiyayyo. Yau ta ga bakar tukunya mai fidda farin tuwo!

    Kawar da kai yayi..ya fita da sauri. Ta cigaba da kuka a hankali ranta ya kasa ayyana ma ta irin kaunar da momodou ke musu. A hankali ta ce

    “Ba mu da tamkar ka Momodou, ba mu da!”

    Abu kamar wasa sai Rukaiyatou ta fara zuwa makaranta. Abinda ba su sani ba shi ne shagon da aka budewa wa Momodou to duk ribar ranar a karatun Rukaiyatou yake karewa. A lokacin shekarunsa ba za su wuce ashirin ba, amma zurfin tunaninsa da hankalinsa ya fi na dan shekara talatin. Hakan ne ma yasa uban ya dada jan sa a jiki da nuna ma sa harkokin kasuwanci dan ya ji a ran sa shi zai gaje shi.

    Daga nan ya shiga Universite Abdou Moumouni de Niamey ya fara karanta harkar kasuwanci kamar yanda mahaifinsa ya ke so. Lokacin da ya gama a sannan ne Rukaiyatou ta gama ta gama karatun primary da aka sa ta daga aji uku har ta fara zuwa wata makarantar sakandare ta yanmata je ka ka dawo.

    A mafarkin Rukaiyatou ba ta da kamar Momodou kuma shi zata aura idan sun girma. Kuma shi zai sa ta a universete tayi karatun aikin jarida. A lokacin ne kuma Iliyasou Tillaberi ya ke son aika Momoudou kasar faransa domin ya je yayi digiri na biyu a harkar kasuwanci. Wannan wani tsari ne da bai so saboda tunanin wa zai bar wa su Rukaiyatou?
    Dan haka sai ya fara zamewa batun

    A irin haka ne ya shiga gida wajen mahaifiyarsa Hajiya Khulsomou ta kira shi ta ce

    ” Yo kai bakka kishin kan ka ko? Ba zaka tahi karatun kirki ba ka tsaya anan kamar marar gata. Ka hi son ubanka ya dora sobanka Mustapha ko?”
    Har yau ya kasa gane irin kishin da babarsa take da Mustapha. Ba ma haka ba kowa a duniya abokin kishi ne a wurin mahaifiyarsa. Ba a gari daya ba , ba kasa daya ba amma ta uzzura ma ranta. Ga shi ita Hajiya hadiza ba ta ma cika nuna masa tsangwama ba. Kai tsaye a faransan sa ba wata rufa rufa ya ce

    ” Ai na hwadi miki, ban iya tahia na kyale Rukaiyatou”

    Ta kalle shi a tsanake, maganar da ya fada ta taba ta ba dan kadan ba don haka sai ta kalle shi ta ce a tsaurare

    ” Idan ma son ta ka ke, ba ka amrenta..in ni da ubanka muna da rai baka aurenta!”

    Wani abu ne ya ji ya gifta ta gabansa mai tsananin duhu saboda bacin rai. Duk duniya bai ga mai hana ma sa aurenta ba, abinda ya ayyana a ran sa kenen.

    Da daren ranar ne yana zaune a gaban Momma tana dinkin takalmi da taimakon fitilar aci bal bal. Suna hira kamar yadda suka saba, Rukaiyatou na kishingida can gefe akan tabarma. Yanzu ta fara zama yar budurwa ta rage halayenta na kiriniya ta ce

    “Frere ka ci tuwo in zubo maka? Ni na dahwa”
    Sai ya fara dariya ya ce

    ” yanzun yar dul da ke anan har kin iya dahwa tuwo”?

    Ta ce
    ” Ai na dan iya saboda Momma ta ce kana son tuwo in mun yi amre sai in dunga tuka maka ko?”

    Ya rasa wannan hali na ta na rashin jin kunya ga Momma a zaune. Ya yi sauri ya ce

    ” Ni na ce miki zan amre ki”?

    Ta dago kai cike da mamaki har ga Allah ta ce

    “Ba Momma ta ce Kai a mijina ba? Wai tun ina zanin goyi ta ba ka ni?”

    Haushi ya sa Momma ta mako ta ta na cewa

    ” uwar surutu”

    Cikin basarwa ya ce dauko takardunki na Lecole mu gani ko kina kokari. Ta dauko ya duba ya gyara ma ta wasu abubuwan. Yayi shirin tafiya Momma ta ce

    ” zo nan in tambayeka”

    ” ya ba ka tafi ba”?
    Ya ce

    “In tafi? Rukaiyatou fa? Wa ke gareta”?

    Ta nisa a hankali ta ajiye dinkin takalmi ta kalle shi a hasken fitilar aci bal bal ta ce

    ” A kan ta sai ka fasa karatu? Ai muna hannun Allah ko? baka yarda da ikon Allah ba? Da ba dan ikonsa ba da taimakon ka zamu kai yanzu? Ka je kayi karatunka ka ji”

    Shiru yayi, ba mai yawan magana ba ne. Abinda ba ta sani ba shi ne shi ya san babansa na son tura shi faransa ne dan yayi nesa da su. Ya san tsarin uban ,ya gaya ma sa ya je ya karo karatu a can sannan nan ya zame ma sa ido akan wani karamin kamfani da yake son budewa a can. Har wani tsawon lokaci hakan zai dauka? Amma kuma shi kan sa ya san ba shi da zabi.

    Sai yayi murmushi har ya taba rashin kunyar ya ce

    “Bari na je na dawo ko Momma? Kafin nan na yi kudi sai na zo na amri kamnata” iyaka gaskiyarsa kenen bai kuma iya boyewa ba. Momma kamar wata abokiyar shawara ya maida ita tun tasowarsa.

    Ta tsaya tana duban yaron, har yanzu da yarinta a jikinsa amma duk tsarinsa na su ne. Tayi ma sa kallon nutsuwa ta ce

    “Rukaiyatou dai! Rukaiyatou dai! Akwai wani shirinka na duniya da babu ita? Wanene ya ce sai kayi kudi zaka aureta?” Ta girgiza ma sa kai tana ma sa kallo irin na uwa sannan ta ce
    “Ko ba ka da ko dala ni zan baka Rukaiyatou”!!

    “Momodou ka tafi kamar yau ne zaka je ka dawo” cewar Momma

    Ya gyada kai a hankali. Ya yiwa Rukaiyatou inkiya da ta biyo shi daga gani wani abun zai ba ta. Ta bi shi a baya. Momma ta kare musu kallo tayi murmushi ta ce

    “So, ruwan zuma”
    MASU ƁUKATAR A TALLATA MUSU HAJOJINSU ZA SU IYA TUNTUƁARMU TA LAMBOBIN 07045308523 MUN GODE

    Note
    error: Content is protected !!