Search
You have no alerts.

    MASU ƁUKATAR A TALLATA MUSU HAJOJINSU ZA SU IYA TUNTUƁARMU TA LAMBOBIN 07045308523 MUN GODE
    So ai ruwan zuma ne, idan ka sha ka ba masoyi!

    Niamey, Niger Republic

    Rokaiyatou ta cigaba da kallon hanya yayin da take wasan kasa a kofar gidansu ta ga ta inda Momodou zai bullo ta ruga. Can ta ji an kwalla ma ta kira “Rokaiyatou”! daga kan da za ta yi sai ta hange shi ba ta yi wata wata ba ta fyalla gida a guje. Yarinya ce da ba za ta wuce shekara 8 ba jikinta ku san duk tsummokara. Ba ta yi wata wata ba ta fada bayan babarta ta kwakumeta ta ce

    ” Momma, frère Momodou shiddawo ya tardoni ina wasan kasa”

    Uwar ta tunkude ta daga jikinta cikin hausarta ta zallar kananci ta ce

    “Ke kaleni, ku je can ku karata”

    Momodou ya shigo da riga “long sleeve” fara da shudin wando bayan sa goye da jaka irin ta yan makaranta, ya sa safa da kambos. Ya nufi bayan Momma ya janyota da kunne ya murda ya ce

    “Mi na gani kina yi waje?”

    Ta na ta jan kunnen kokarin yakicewa shi kuma ya kalli momma kamar me neman bayani ta dago daga tsintar shinkafar da take ta ce

    ” Rokaiyatou, K’…ai kadan ka gani..kamar mai aljanu..ai duka kawai zaka ma ta sai ta ji a jikinta”

    Ya kura ma ta ido hawaye kwance male male a fuskarta, gashinta mai tsawo da yawa ya cukurkude ga kasa kamar an yi yaki. Kafafuwanta butu butu kamar tayi hakan rijiya. Sai kuma ya ji tausayinta ya kama shi da ga rigar jikinta yar yaloluwa da yawan wanki ya sa ta kode ta jeme. Abubuwa dayawa suka cigaba da yawo a kansa duk da karancin shekarunsa dan yanzu ma yake aji shida yana neman gama makaranta.

    Ya janyota suka zauna akan tabarma yana kakkabe ma ta gashi ya ce

    ” kin yi abinci dai ko?”

    Yana so ya ji ko ta ci abinci.
    Ta girgiza kai ta ce

    ” yanzu dai Momma za ta dahwa”

    Ya juya ya kalli shinkafar da ake tsinta ‘yar kut a faranti wacce ya san bai wuce a ci ta da mai ba. Ya bude jakarsa mai dauke da yar ” cooler” na abinci ta yan makaranta , dankali ne ko tabawa bai yi ba ya sa a gabanta. Ta fara ci da budu budun hannayenta ba tare da yace ta je ta wanko ba, ya cigaba da kallonta. Momma ta dube su tayi murmushi ta ce

    “Kai dai baka son cin abincinka, sai dai ka kawo wa kanwarka”

    Murmushi yayi. Sai ya sa hannu ya zaro biskit da wani dan lemo ya ce

    “Wannan kuma sai kinyi wanka, ba ki son wanka ko?”

    Ba ta kula ba cin abinci kawai take. Ya kalli. Momma ya ce

    ” Ina ruwan da za tayi wanka?”
    Ya kama haba tace

    ” Au har wani ruwan wanka zan ke ajiye ma ta? To sau nawa zan ajiye”?

    Murmushi kawai yayi ya nannade hannun rigarsa ya doshi inda rijiya take. Ya jefa guga ya fara jan ruwa har ya cika wani dan karamin bokiti. Sai ya yafito yarinyar da hannu ya ce

    ” je ki dauko sabillo”

    Ta shiga daki ta dauko ya ce ta tsugunna ya fara wanke wannan kan na ta dikin dikin har sai da ya fita tas. Ya kalli Momma ya ce

    ” Dan Allah Momma ki kai ta bayi ki ma ta wanka”

    Ta yi murmushi ta mike tana cewa

    “Tou momodou na Rokaiyatou ai idan ban taso ba ba zaka kaleni ba”

    Ta zo ta karbe shi. Ya dauki jakar makarantarsa tana kallo ya zaro kudi ya cusa a karkashin farantin shinkafar nan yayi tafiyarsa ba tare da ya waiwayo ba. Ta gyada kai a hankali a cikin ran ta tana tunanin irin kaunar da momodou ke yi mu su sai ta raya a ranta ko dan Rukaiyatou jininsa ce? Ta kawar da wannan tana mai la’akari da cewar duk ‘yan gidan ma ai yanuwanta ne to amma wa ta ishi kallo? Momma ta cigaba da dirzar Rokaiyatou da sabulu ta na mai ayyanawa a ranta , ko ya rayuwa za ta yiwu ba Momodou?

    Washegari da safe Rukaiyatou na tsaye a kofar kangon gidansu tana hangen wani tsararren bene mai bakin gate tana so ta ga fitowar frère. Gida ne tangameme wanda kallo daya za ka masa ka san an zubar da dukiya. Can aka bude tangamemen gate din motar da take kai yan makaranta ta fito. Tun daga nan ya fara kwalla ma sa kira tana daga ma sa hannu. Da ma ya san tana tsaye domin al’adarta ce yin hakan. Yana isowa zasu wuce shi ma ya daga ma ta hannu suna ta dariya.

    ***********************
    Iliyasou Tillaberi mahaifin Momodou yayane ga Ahmadou Tillaberi mahaifin Rukaiyatou. Wadanan yanuwa suna zaune ne a garin Niamey suna gudanar da kasuwancinsu. Tafi tafi sai suka bude kamfanin hadin gwiwa na sarrafa shinkafa , taliya, flour da mafi yawancin nau’in abinci. Kasuwancunsu ya bunkasa tsakanin Nigeria, Niger, togo , Mali , cameroon da senegal. Daga baya suka kafa babban kamfani da reshensa biyu Nigeria da Niger. Aka sa wa wannan kamfani suna I and A and sons.

    Maganar irin tarin kudi da kadarori da suka mallaka wani abu ne da mai karatu zai sha mamaki. Kasuwanci ya karbe su , su ma kuma suna dagewa game da bunkasar arzikinsu. Iyayensu duka sun rasu sai baffaninsu da ke Tillaberi, wani karamin gari a yankin Niger.

    Iliyasou wani irin murdadden mutum ne mai bakar zuciya. Ya fara da auren uwar Mommodou anan Niamey wata zabarmiya me suna Hajiya Khulsomou. Ta haifa masa ‘ya’ya biyar mata sai namiji daya wato Momodou. Sai kuma Allah ya jarabce shi da son wannan yaro.

    Daga baya yayi aure a Nigeria da wata mai suna Hajiya Hadiza bakanuwa ce ya usul ta haifa masa da guda daya tal Al Mustapha. Wani irin tsananin kishi ke tsakanin wadannan mata biyu har ya zamana daya ba ta zuwa kasar da daya take. Amma me? Wani irin zumunci ke tsakanin Mustapha da Momodou da suke ku san sakwannin juna. Sun shaqu ta inda takanas daya kan bar kasar sa ya ziyarci daya duk da halin da iyayensu mata kan nuna na tsanar hakan.

    Ahmadou Tillaberi kafin ya hadu da mahaifiyar Rukaiyatou mai suna Ramlatu ‘yar kano yana da matan aure guda uku. Suk cikin matansa ba wacce ta taba ko batan wata. A matsayinsa na attajiri mai tarin dukiya zai so wataran in ya fadi ya zamo yana da magaji. To amma ya zai yi?

    Wannan rashin haihuwa na Ahmadou yana yiwa Iliyasou dadi a rai duk tunaninsa bai wuce yau in ba ran kaninsa to komai ya zama na sa. Ana cikin hakan kwatsam rannan kasuwancinsu ya kai su kano duba wani sabon kanfani a lokacin. To anan ne fa ya ga wata kawar Hajiya Hadiza matar yayansa mai suna Ramlatu ya makale ma ta. Ba yanda Iliyasou bai yi ba akan ba ya so amma ya jajirce sai ya aureta.

    A sanin Iliyasou Ahmadou neman haihuwa yake, shi kuma ba ya fatan hakan dalilin da ya sa ya tsani auren kenen. A bangaren Ramlatu kuwa dama marainiya ce a hannun yayanta take, ta kafe ta tsare ta ce sai Ahmadou yayanta ya rantse ba zai ba wa wanda ba dan kasa ba. Aka dunga tafka rigima daga karshe yayan ya ce in dai ta yi auren nan to ba shi ba ita, ta ce ta amince. Aka yi aure Ahmadou ya tafi da amaryarsa Niamey.

    Tun Momma na amarya babu wani dan gidanta da ya wuce Momodou. Yaron na kaunarta ita ma haka. Hakan na kona ran Hajiya khulsomou a ganinta an zaqewa danta ga kuma karin abun kawar kishiyarta. Sai wata gaba ta kullu, sai gore gore na rashin haihuwa ganin cewa har a lokacin ita ma bata samu ciki ba. Ganin an yi shekaru Ramlatu ba ta samu ciki ba sai hankalin iliyasou ya kwanta su kuma kishiyoyinta suka hau ta da habaici. An auro ta daga Nigeria dan ta nuna musu iya haihuwa ashe duk kamwar ja ce.

    Lokacin da Ramlatu ta samu ciki har ya fara fitowa sai fa hankalin kowa ya girgiza, sai aka fara kallon kallo. Ahmadou kamar zai yi hauka don murna. Nan fa kaunarta ta kara azalzakar zuciyarsa aka shiga tattalin ciki ana ririta shi. Sai kuma wani abun al’ajabi ya faru.

    Al’amuran dukiya na Ahmadou suka fara ja baya. Duk a abunda ya taba sai ha zamo asara. Nan da nan fa yayansa da matansa suka fara nuna Ramlatu da cewar ita ke da farar kafa kuma wai zata haifa musu bala’i. Da aka haifi yarinya sai abubuwan suka kara tabarbarewa amma me? Shi bai wani damu ba farincikinsa kawai ya samu abun kauna Rukaiyatou. Ya so Rukaiyatou irin son da ake yiwa da guda daya tilo da yayi jinkirin zuwa. Sai matansa suka fara ganin haukarsu ta zama da shi ba abun duniya ba da ba jika..me zai zaunar da su? Sai suka watse abunsu suka bar shi da Ramlatu.

    To amma yawa yawan kudadensa suna hannun Iliyasou na kanfanunnukan hadin gwiwa da suka bude. Zaman iliyasou babba sai ya zamana ya fi karfi akan dukiyar don haka sai ya tuntube shi da batun kudinsa. Sai ya nuna ma sa cewar ba fa zai iya fitar da komai ya sa a hannunsa ba hakan kamar ganganci ne yayi hakuri zai cigaba da juya musu. Ahmadou mutum ne mai hakuri sai ya jure hakan ya cigaba da juya dan abunda ke hannunsa.

    Tun haihuwar Rukaiyatou Momodou ya kalli Momma ya ce

    ” shikenen kin haihwa min mata, ni ina kamnar ta! ”

    tayi dariya ta ce

    “Allah Momodou? To inshallahu in ta girma kai ne mijin”

    Sai ya kama tsalle irin na yara har ya tafi da gudu ya gayawa babarsa . Ita kuma ta ce a fusace

    ” Ba ka amren mayya, ita ta lashe dukiyar Ubanta!”

    Kamar abun almara, Rukaiyatou na da shekara biyu Ahmadou Tillaberi ya yanke jiki ya fadi a bayi ko shurawa bai yi ba. Ai tun daga nan sai fa nuni ya koma kan su, lallai Ramlatu da diyar ta sun tabbata mayu masu lashe dukiya da kurwa. Daga nan sai rayuwa ta musu kunci. Iliyasou ya rantse da cewar Ramlatu ce ta jefe shi da asiri ya fadi ya mutu don ta gudu da ragowar dukiyarsa, don haka sai ya hau kan dukiyar Ahmadou ya danne babu ma batun rabon gado. Da kyar aka samu ya basu wani kangon gida anan kusa da shi wancan tsararren gidan na su ya siyar ya ce shi zai rikewa marainiya dukiyarta.

    Momma tayi kuka ta gode Allah ganin yadda aka musu fin karfi ita da diyarta. To amma ina zata je? Wa zata gayawa? Babu. Yayanta da take da shi ma sun riga sun raba hanya, tun da tayi aure bai taba neman ta ba. Sai kawai tayi zamanta a wannan gidan take dinkin fata na takalmi da jaka take kaiwa kasuwa suke cin abinci.

    Iliyasou ya watsar da su ya ma manta da wasu iyalan Ahmadou. Baffaninsu sun sa baki ya samu ko diyar ce ya kula da ita amma ya shashantar da batun. Wani irin mulki na zallar zalunci yake gwada musu da asalin fin karfi.

    Momodou yaro ne amma ya taso da tsanar wannan dabi’a ta mahaifinsa yana matukar jin takaicin hakan. Mahaifin ya kwallafa rai akan sa a matsayinsa na babban dan sa namiji hakan ya sa tun yana karami ya fara dora shi akan harkar kasuwanci. Shi kuma sai ya taso da kauna da tausayi na wadan nan bayin Allah ta yanda duk abunda ya samu to nasu ne.

    A shekarun girman Rukaiyatou ta taso ba ta shaku da kowa ba sama da yayanta frère, wannan shakuwar da ko iliyasou Tillaberi ya gaza rabawa. Al’adarta ce kullum ta tsaya a hanya ta ma sa bye bye idan za shi makaranta ba don ita tana zuwa ba.

    Ganin hakan ne yau ya ga bai gan ta ba sai ya shiga gidan don a zatonsa ko ba lafiya ba. Da shigarsa ya tarda ta tana wasan ruwa, shigowarsa tayi fatali da ruwan ta ruga daki. Momma ta fito daga wajen wani kewayayyen langa langa inda take tukin tuwo tana share hannayenta a jikin kodadden zaninta. Tayi murmushi ta ce

    “Mutuniyarka ta gudu ko”?

    Ya mayar ma ta da murmushin sannan ya ce bayan sun gaisa

    “Na ji ta shiru bana ganinta a waje, nayi zaton ko bata da lahiya ne, lahiyarta lahiya?”

    Ta kwalla mata kira, ta zo tana rabe rabe. Ya zaunar da ita kan tabarma ya ce
    ” Me ya hwaru ba na ganinki waje da sahe?”
    Cikin kasa kasa da murya ta ce

    ” Ba kowa yana zawwa L’ècole amma ban da ni ba”

    Yayi shiru kamar mai nazari sai can ya ce
    ” kina son zuwa L’ècole ko?”

    Ta gyada kai. Ya ce

    ” Ba ina zuwa ina koya miki ba har kin ka iya karatu ba?” Ta ce

    ” Ai naka ba irin na L’ècole ba ne, ba a sa kayan L’ècole” ya ce

    ” To shikenen kamnata, in dai ina raye sai kin je kin ji ko?

    Ta fara tsalle. Ya fito da wasu yan kudi a hannu ya manna mata yana dariya.

    Duk abinda suke Momma na kallonsu. Ya mike zai tafi ta kira shi cikin damuwa ta ce
    ” Kana dan makaranta ka ke wa wani alkawarin sa shi a makaranta?”
    Ya sosa keya yace

    ” jiya ne fa muka gama gwajinmu na karshe sai jiran sakamako kawai”
    Ta ce

    ” Alhamdulillahi, dana ya girma. Amma ina fatan ba mahaifinka zaka gayawa ba, ka san bana son kuna samun matsala akan Rukaiyatou”

    Shiru yayi na wasu dakiku sannan ya ce
    “Kar fa ki sa komai a ran ki Momma na san yanda za a yi na samu kudi. Ba ki san yanzun haka Abba ya bude min shago a Grand Marchè ba? Nan zan ke zuwa kafin sakamakon gwajin mu ya fito. Babana ke da alhakin kula da ita kuma ya ki. Wallahi idan ki ka ga ban kula da Rokaiyatou ba, to ba yadda naka iyawa”.

    Kwallar cikin idon Momma ta tsiyayyo. Yau ta ga bakar tukunya mai fidda farin tuwo!

    Kawar da kai yayi..ya fita da sauri. Ta cigaba da kuka a hankali ranta ya kasa ayyana ma ta irin kaunar da momodou ke musu. A hankali ta ce

    “Ba mu da tamkar ka Momodou, ba mu da!”

    Abu kamar wasa sai Rukaiyatou ta fara zuwa makaranta. Abinda ba su sani ba shi ne shagon da aka budewa wa Momodou to duk ribar ranar a karatun Rukaiyatou yake karewa. A lokacin shekarunsa ba za su wuce ashirin ba, amma zurfin tunaninsa da hankalinsa ya fi na dan shekara talatin. Hakan ne ma yasa uban ya dada jan sa a jiki da nuna ma sa harkokin kasuwanci dan ya ji a ran sa shi zai gaje shi.

    Daga nan ya shiga Universite Abdou Moumouni de Niamey ya fara karanta harkar kasuwanci kamar yanda mahaifinsa ya ke so. Lokacin da ya gama a sannan ne Rukaiyatou ta gama ta gama karatun primary da aka sa ta daga aji uku har ta fara zuwa wata makarantar sakandare ta yanmata je ka ka dawo.

    A mafarkin Rukaiyatou ba ta da kamar Momodou kuma shi zata aura idan sun girma. Kuma shi zai sa ta a universete tayi karatun aikin jarida. A lokacin ne kuma Iliyasou Tillaberi ya ke son aika Momoudou kasar faransa domin ya je yayi digiri na biyu a harkar kasuwanci. Wannan wani tsari ne da bai so saboda tunanin wa zai bar wa su Rukaiyatou?
    Dan haka sai ya fara zamewa batun

    A irin haka ne ya shiga gida wajen mahaifiyarsa Hajiya Khulsomou ta kira shi ta ce

    ” Yo kai bakka kishin kan ka ko? Ba zaka tahi karatun kirki ba ka tsaya anan kamar marar gata. Ka hi son ubanka ya dora sobanka Mustapha ko?”
    Har yau ya kasa gane irin kishin da babarsa take da Mustapha. Ba ma haka ba kowa a duniya abokin kishi ne a wurin mahaifiyarsa. Ba a gari daya ba , ba kasa daya ba amma ta uzzura ma ranta. Ga shi ita Hajiya hadiza ba ta ma cika nuna masa tsangwama ba. Kai tsaye a faransan sa ba wata rufa rufa ya ce

    ” Ai na hwadi miki, ban iya tahia na kyale Rukaiyatou”

    Ta kalle shi a tsanake, maganar da ya fada ta taba ta ba dan kadan ba don haka sai ta kalle shi ta ce a tsaurare

    ” Idan ma son ta ka ke, ba ka amrenta..in ni da ubanka muna da rai baka aurenta!”

    Wani abu ne ya ji ya gifta ta gabansa mai tsananin duhu saboda bacin rai. Duk duniya bai ga mai hana ma sa aurenta ba, abinda ya ayyana a ran sa kenen.

    Da daren ranar ne yana zaune a gaban Momma tana dinkin takalmi da taimakon fitilar aci bal bal. Suna hira kamar yadda suka saba, Rukaiyatou na kishingida can gefe akan tabarma. Yanzu ta fara zama yar budurwa ta rage halayenta na kiriniya ta ce

    “Frere ka ci tuwo in zubo maka? Ni na dahwa”
    Sai ya fara dariya ya ce

    ” yanzun yar dul da ke anan har kin iya dahwa tuwo”?

    Ta ce
    ” Ai na dan iya saboda Momma ta ce kana son tuwo in mun yi amre sai in dunga tuka maka ko?”

    Ya rasa wannan hali na ta na rashin jin kunya ga Momma a zaune. Ya yi sauri ya ce

    ” Ni na ce miki zan amre ki”?

    Ta dago kai cike da mamaki har ga Allah ta ce

    “Ba Momma ta ce Kai a mijina ba? Wai tun ina zanin goyi ta ba ka ni?”

    Haushi ya sa Momma ta mako ta ta na cewa

    ” uwar surutu”

    Cikin basarwa ya ce dauko takardunki na Lecole mu gani ko kina kokari. Ta dauko ya duba ya gyara ma ta wasu abubuwan. Yayi shirin tafiya Momma ta ce

    ” zo nan in tambayeka”

    ” ya ba ka tafi ba”?
    Ya ce

    “In tafi? Rukaiyatou fa? Wa ke gareta”?

    Ta nisa a hankali ta ajiye dinkin takalmi ta kalle shi a hasken fitilar aci bal bal ta ce

    ” A kan ta sai ka fasa karatu? Ai muna hannun Allah ko? baka yarda da ikon Allah ba? Da ba dan ikonsa ba da taimakon ka zamu kai yanzu? Ka je kayi karatunka ka ji”

    Shiru yayi, ba mai yawan magana ba ne. Abinda ba ta sani ba shi ne shi ya san babansa na son tura shi faransa ne dan yayi nesa da su. Ya san tsarin uban ,ya gaya ma sa ya je ya karo karatu a can sannan nan ya zame ma sa ido akan wani karamin kamfani da yake son budewa a can. Har wani tsawon lokaci hakan zai dauka? Amma kuma shi kan sa ya san ba shi da zabi.

    Sai yayi murmushi har ya taba rashin kunyar ya ce

    “Bari na je na dawo ko Momma? Kafin nan na yi kudi sai na zo na amri kamnata” iyaka gaskiyarsa kenen bai kuma iya boyewa ba. Momma kamar wata abokiyar shawara ya maida ita tun tasowarsa.

    Ta tsaya tana duban yaron, har yanzu da yarinta a jikinsa amma duk tsarinsa na su ne. Tayi ma sa kallon nutsuwa ta ce

    “Rukaiyatou dai! Rukaiyatou dai! Akwai wani shirinka na duniya da babu ita? Wanene ya ce sai kayi kudi zaka aureta?” Ta girgiza ma sa kai tana ma sa kallo irin na uwa sannan ta ce
    “Ko ba ka da ko dala ni zan baka Rukaiyatou”!!

    “Momodou ka tafi kamar yau ne zaka je ka dawo” cewar Momma

    Ya gyada kai a hankali. Ya yiwa Rukaiyatou inkiya da ta biyo shi daga gani wani abun zai ba ta. Ta bi shi a baya. Momma ta kare musu kallo tayi murmushi ta ce

    “So, ruwan zuma”

    4. Ina mafita

    Ina mafita? A lokacin da babu mafita!

    Kano, Nigeria

    Washegarin rasuwar Muhammadu Hindatu ta tattara na ta ya na ta ta koma gidansu, ‘Yanuwa da abokan arziki suka yi ta zuwa ma ta gaisuwa.
    Ta kudurce a ranta cewar idan fa bata nemi mafita ba to da daya da daya sai ta nemi ‘ya’yanta ta hange su a hannun mutuwa.

    To zaman gidan ma jiya i yau. Makauniyar uwarta na nan yadda take da kannenta gudu uku mata, sai ita cikon ta hudu da ‘ya’yanta biyu cikon biyar da shida wanda suka samu mazauni a dan tsukakken dakin mutum biyu. Maza yanzu ba sa son zawarcin mace mai ‘ya’ya in dai ba dukiya aka bar musu ba, don haka daga mutum ya zo daya, biyu sai ta ji dif.

    Wani abu da ya fi daure ma ta kai da kuma ba ta haushi bai wuce gani ganin da kannen nata ke ma ta ba suna ma kallon wacce ta zo ta takura musu. Wani mugun raini ne ya shiga tsakaninsu kamar wacce kan ta aka fara zawarci. ‘Ya’yanta sai suka zama ganguna sai dai ka ji tim! An kai musu duka ba gaira ba dalili.

    Lokacin da tana gidan Habu tana ‘yar sana’arta ba ta taba zuwa gida ba tare da ta ruko musu dan wani abu ba don haka anti sama anti kasa. Amma yanzu da suka gama gano ba ta da wata mamora sai kawai aka guntule antin aka yar a juji ake kiranta Hindatunta sak.

    Ranar wata Alhamis ana kiran sallar La’asar Hindatu na alwala a bakin rijiya, kanwarta mai suna safara na zaune a bakin kofar daki tana cin taliya da manja. Can kamar an koro Abba ya shigo a guje da gare-garensa daga kofar gida. Sai ya tsaya cak a gaban Safara ya kura ma ta ido saboda yunwar da ke addabarsa . Ta kai lomarta ta hudu kenen ta ankara da shi ta ko galla ma sa harara ta ce

    ” Uhun..ya na ga kana kallona kamar ni na kori ubanka?”

    Hindatu ta dago kai daga alwalar da take tana so ta gane abunda yayi zafi har safara ta jefi Abba da magana irin wannan. Ya kalle ta bayan yayi narai narai da ido ya ce ” Anti Safara yunwa nake ji in zo in ci?” Bai karasa ba ta ce a fusace

    ” Ca akai maka ta ubanka ce?! Ku ji ni da tsinannen yaro” ta mika hannu ta rankwashe shi.
    Hindatu kamar ta share amma sai ta tuna anyi haka ya fi a kirga. Sai ta ce

    ” Safara kan abinci ne kike zagi har da rankwashi? Ba dan ki ba ne”
    Safara tayi caraf ta ce

    ” kut, ku ji Hinden nan. Yaro ba tarbiyya ba za a koya ma sa ba? Ko kuwa tambayar da na masa ce laifi? To karya na yi? Na ubansa ne?”

    “Da sauki tunda ubansa ya taba kawowa har kin ci kin goge baki” cewar Hindatu saboda ranta ya fara baci. Cikin rashin kunya Safara ta ce

    ” Kin ga Hinde, ba ni na kar zomon ba ratayar ma ba a bani ba. Kan Abba ne kike nema ki gayamin magana ko ni na ce ubansa ya gudu ya bar ki ba ci ba sha? Kawai kin zo gida kin cushe mana guri ke da ‘ya’yanki gayyar kwarkwata gayyar kudin cizo!”

    Hindatu ta katse alwalar da take ta iso inda da Safara take ta nuna mata dan yatsa ta ce

    “Kar gigin tashen balagarki ya kai ki ki zageni don kin yi kadan kin yi tsararo. Gwara ni na auru ke ki gayamin karen da ya zo ya shinshina takalminki a tsawon zamaninki!”

    Toh fa! Wannan magana sai ga harzuka safara har ta dangwarar da kwanon taliyarta ta mike daidai da tsawon Hindatu ta ce

    “Na rantse Hinde da aure irin na ki billahillazi gwara na mutu ba mashinshini…auren wahala..auren bakin ciki!”

    Ai kafin ka ce me Hindatu ta fizgo ta an fara dambe kamar wasu dadaddun abokanen hamayya. Abba ne ya tafi da gudu ya je ya kira uwar ta fito tana dogara sandarta. Ta daidaici inda take jin rubdugun damben ta kwada sandarta ta na cewa

    ” Ba ku isa ku saka min hawan jini ba don ba ni kadai na tara ‘ya’ya mata ba a layin nan”. Suka rabu aka mayar da yanda aka yi ,budar bakin uwar sai ta ce

    “Um..um Hinde na fa fara gajiya da ke. Kafin ki dawo gidan nan salin alin muke zamanmu amma tunda kika zo fadan yau daban na gobe daban. Duk dai kan ‘ya’ya? Ni na ce , wai nan din gidan ubansu ne?”

    Wani abu ya taso ya daki Hindatu a zuciya ta ce
    ” Hajiya dan Abba ya ce zai ci abinci laifi ne? Yana da inda ya fi nan?”

    ” Oho miki!” Ta fada da karfi, ba ya da dangin uba ne ko daga sama ya fado? Maza maza ki tattara su ki maida su dangin tsinannen ubansu don bazan iya ciyar da ke na ci da ‘ya’yanki ba. Don ban da ma kulafuci da rashin zuciya irin ta ki ubansu ya gudu ya bar ki amma kina nane da su. Sakarya kawai!”

    Tana gama fadan ta dogara ta shige dakinta tana mita.

    Hawaye ne suka biyo idonta sai tayi sauri ta shige daki. Anan ma ta tarar da maryama kanwarta ta shuro ma ta kayanta ta tura su wani loko, ta ma shinfide katifa a gurin tana sharar baccin rana. Sai kawai tayi zaune kan tantagaryar simunti jin da tayi kan ta ya dau caji na wucin gadi. Ba ta taba tsammanin haka ba daga babarta to amma ko don yau da gobe? Dan yanzu a kalla tayi wata tara a gida ba kas ba as. Yaranta da ake ma ta gori ina za ta kai su? Yaya za tayi? Ina mafita?

    Abba ya zo ya jingina da kafadunta yana share ma ta hawaye ya ce

    ” Mama ki daina kuka. Anti safara ce ta dake ki ko? Nima idan na girma zan siyi bindiga na harbeta!”
    Tayi sauri ta daki bakinsa ta ce

    ” Ba a fadan haka ka ji ko?”
    Ya gyada kan sa sannan ya ce

    “Mama wai ina babanmu? In ji Anti safara wai ya gudu”
    Ta tsura ma sa ido sannan ta janyo shi ta dora akan cinyarta a ranta tana juya abunda zata fada ma sa ta ce

    ” Abba ba ka san babanka ya rasu ba?”
    Yayi narai narai da ido ya ce
    ” To mama yaushe zai dawo?”
    Tayi murmushin karfin hali ta shafa kan sa ta ce

    ” wanda ya mutu ba ya dawowa Abba”

    A ranar Hindatu ta sa zuciyarta ta kashe Habu!!

    Kwanaki suka cigaba da ja a haka ba wani canji babu isasshen abinci, ba sutura, yaranta ko makaranta ba sa zuwa. A wata ranar litinin a cikin irin ranakun da tayi Allah wadai da su ta dauki wata atamfarta hitarget da ta fara kodau ta sa. Ta ja hannun diyarta Asiya ta shiga makwabta kitso. Dowowarta gida ta tarar har an yi abinci an raba kanwarta sadiya ita ce da wannan aikin. Ta samu kujera yar tsugunne ta zauna tana yiwa Hajiya uwani sannu da gida.
    Hajiyar ta ce

    “Kin yi sauri, har an gama kitson?”

    Ta ce
    “Eh, ai babu layi”

    Sannan ta juya kan sadiya da ke gugar kayanta ta ce

    ” Sadiya miko min abinci na, yunwa kamar za ta karasa ni”

    Sadiya ta dago kai ta ce

    “Au dama ba ki ci ba ki ka fita?”
    Hindatu ta kalle ta a tsanake ta ce

    ” kamar yaya? Lokacin da na fita kin gama ne?”

    ” Cab! Ai kuwa rabawa nayi ba ke wallahi, ai na zata kin ci” cewar sadiya.

    Wani abu ya zo ma ta wuya ya tokare, wai sadiya kanwar kanwar bayanta ke neman raina ma ta hankali. Babbarsu na zaune amma ba ta ce komai ba, dama ta san ba zata tanka ba.Ta hadiye bacin ranta ta shiga daki ta dauko wata atamfarta da take boyo tun barka muhammadunta ta kama Asiya suka fita.

    A bayan layinsu akwai gidan wata mata da sukai mutunci a tun zamanin tana budurwa ana kiranta hannatu. Hannatu gogaggiyar ‘yar kasuwa ce da ba ta rabuwa da mutane. Takan siya kaya irinsu atamfofi da lesina kuma takan siyar. Har ma akan yi gulmarta da cewar wai har ma kayan sata takan siya. Tun farko abunda ya dan kawo raunin kawancensu shi ne hannatu na da wayewa ta kin karawa idonta idon kudi ba magana. A lokacin sai Hindatu tayi tunanin ta kai ma ta atamfar nan ta siya ita kuma ta kashe larura da kudin.

    Shigar Hindatun ke da wuya ta hango ta a zaune a tsakar gida an shimfida katuwar dadduma da kwanukan abinci akai. Sai dai kuma ba ita kadai ba ce kamar yadda ta yi tsammani akwai wata mace zaune a irin kujerar roba nan fara da kwanon abinci a hannunta.

    Dukkaninsu auna karkashin bishiyar umbrella da ke tsakar gidan suna shan iska. Hannatu ta kama haba da alamun mamaki ta ce

    ” Wa na ke gani? Amma dai batan kai kika yi?”

    Hindatu tayi murmushi a kunyace ta ce
    ” ba batan kai ba ne da kafata na zo”

    Hannatu ta tabe baki ta ce

    ” Watanninki nawa a unguwar nan amma ko leke? Gaskiya ba ki da kirki”

    Hindatu ta bata hakuri a wasance. Sai hannatu ta ce
    ” To ga kawata ba ku gaisa ba”

    Hindatu ta waiwayo sai ta ji gabanta ya fadi. Zaune akan kujerar wata mace ce hamashakiya daure da wani leshi mai ruwan bula da ratsin fari fari. Daga ganinta ba fara ba amma ta yi wankan mai me tsada! Yan yatsunta tayi ado da zobunan gwal biyu, kan ta ba kallabi sai gashin dokin da aka kara ma ta ya sakko har gadon bayanta. Ba wata kyakkyawa ba ce sai dai daga gani kudi da gayu sun samu mazauni ba shakka. Duka duka ba zata haura shekarun hindatun ba a kallon da tayi ma ta, don haka sai ta jj wani abu ya darsu a ranta, ina ma ita ce ga juyawa talauci baya yanda bakuwar nan ta yi.

    Suka gaisa faran faran da ita har hindatu tayi mamaki don ba ta zaci ire irensu da kallon irinta da fuska a sake ba. Matar ta janyo Asiya jikinta ta fara ba ta abincin da take ci wanan abu ya taba ta, dama an ce mai da wawa.

    Nan take matar nan ta gama burgeta, ga kudi ga mutunci. Aka yi ma ta tayin abinci, ba ta yi fulako ba ta zauna ta nada anan kuma sai aka bude babin hira. Labari ta shiga ba su tiryan riryan tun daga gudun Habu har yau da aka ma ta rowar abinci. Anan ne bakuwar ta dubi Hindatu ta ce

    ” kin ga wannan duniyar? Idan ki ka biye ma ta ba ki tashi tsaye ba kina ji kina gani za ki koma abun tausayi.. ai ni tunda na ganewa duniya na sha maganin zama a cikinta.” Sai hindatu ta ji ta birgeta.
    Anan ne hannatu ta ce

    ” Wannan kawata ce Nusaiba amma Nusy muke ce ma ta. Tare mu kayi makaranta ita ma ta taba aure ta fito. In dai kika bi shawarata wallahi za ki ga haske, ba ke babu jaje”

    Hindatu tayi murmushi ta ce

    “Allah sarki”

    Bakuwar mai suna Nusy ta dubi Hi datu ta ce

    ” Ai kin ce kin yi diploma ko?”
    Ta caraf ta cafe

    ” kwarai kwarai, tabbas nayi diploma a school of technology”

    Sai ta fito da wayarta hindatu ta bita da kallo sanin waya sai wane da wane, ta lallatsa ta kara a kunne. A cikin wata irin murya da hindatu baga san mace na iya mallakarta ba ta ji Nusy ta na amsa wani da ake kira da yallabai. Mamaki ya cika ta wai dama idan ana waya da namiji har wata kwarkwasa ake? Da taga wai ba ganinsa ake ba.

    Ta watsar da wannan tunanin, ita fa ba ‘yar gayu ba ce irinsu Nusy da suka goge da duniya, har me za ta adar? Can ta ji ta ce
    ” Ina mutuminka kuwa honourable?” Ba ta ji ansar da ya ba ta ba sai ta ji ta ce
    ” honourable na ka mana kana da wanda ya fi shi ne?” Sai kuma ta kyalkyace da dariya ta ce ” o’o o ‘o wannan karamar kwangila ce ma percentage din ba yawa ,na samo. Ba na ji yana cigiyar mai yiwa yara lesson ba? To ka ce ma sa ina da kawa idan zai taimaka ya sakaya ta” Sai ta ji ta kuma kwashewa da dariya a nishadance ta ce

    ” a’a babu sim , ba ta hau network ba”

    Daga baya sai suka yi sallama ba tare da ta ji wata matsaya ba. Ta juyo ta kalli hindatu ta ce

    ” ki kwantar da hankalinki suna ma tare da wanda nake nema. Lesson ne nake so na samo miki na yaransa ko banza ai kya rage zafi kafin a samu mafita ko?”

    A lokacin ta hada ido da hannatu sakai murmushi ba tare da hindatu ta lura ba. Tayi ta faman zuba godiya. Nusy ta ce ba komai. Har ma ta ce ta kwatanta ma ta gidansu in ya so duk abunda ake ciki za ta gaya ma ta. Hindatu ta kwatanta.

    Hindatu tayi ta kirgen kwanaki ko za ta ji da ga Nusy kwatsam ranar sai ga ta. Yau kuma wata tsaleliyar atamfa ce a jikinta wacce aka gutsittsira aka ma ta dinkin fan darinki tsirara. Hindatu ta lalace a kallon gayu irin na ta in ka kalle ta kamar zinariya caa cas gwanin sha’awa a idon Hindatu. Sai dai a ranta tana mamakin shanawar Nusy da tunanin wata irin sana’a take haka mai kawo kudi. Ta share wannan tunanin ganin ba wani abu ba ne da ya shafe ta . Daga nan Nusy ta ce ta zo su je ta nuna mata gidan da za ta yi aikin lesson domin an dace an samu aiki. Murna kamar za ta kashe hindatu!

    Ba ta tsinke da al’amarin Nusy ba sai da ta ga sun doshi wata tsaleliyar mota. To sai fa ta fara jin dari dari a ranta tana jin cewar Nusy din ta fi karfinta. Ta jingina kan ta a hankali tana shakar sanyin ac da kamshin air freshner din da ke manne a motar. Ta dunga rayawa a ranta, ina ma ta ta ce tana murza ta aka titi.. ai da ba karamin morewa rayuwa ta yi ba.

    Hindatu ba ta ankara ba ta gan su a gaban wani tangameme gida wanda ya isa a ma sa lakabi da huce haushin duniya. Nusy ta kalleta ta ce

    ” Nan ne gidan honourable. Nayi magana da shi mun zartar za ki dunga zuwa kina yiwa yaransa na primary lesson na maths da english a wata za dunga biyanki dubu goma. Ya kika gani? Ya miki?”

    Cikin tsananin farinciki ta ce ” dubu goma fa kika ce? Anya kin ji da kyau? Ba ga masu NCE ma da ke koyarwa a firamare ba sa daukan hakan a wannan zamanin”

    Nusy ta kyalkyace da dariya har da buga sitiyari ta ce

    ” ke hindatu kin san wanenne honourable kuwa? Kin san mahaukatan kudaden da ya mallaka?Yayi shekara takwas yana dan majalisa banda manya manyan kamfanonin da ya mallaka. Kuma fa ta hanya ta ki ka biyo, aminin yallabai di na ne kut da kut, don haka ko dan ni zai iya miki fin haka. Ke dai ki bi yanda na ce billahillazi halin da ki ke ciki sai dai ya zama labari.

    Hindatu ta jinjina kai hankalinta yayi mugun kwantawa da Nusy. Ba ta gudun talakawa don haka ta yarda mai kaunarta ce. Ta fara yarda shawarwarinta abun bi ne don ga shi har ta fara ganin haske. Nusy ta maida hindatu gida ta ajiye suka yi sallama.

    Bayan rabuwar ta su ne ta daga waya ta kira yallabai suna ta dariyar Hindatu.

    Ta ce ” ina sane na bi da ita a haka ai sabuwar hannu ce. Kai yanzu idan na fito baro baro na gaya ma ta ai ba za ta yarda ba. A bar ta ta fara lesson din, daga nan ai shi ya san abun yi”

    Ba a wani dade ba Hindatu ta fara aiki a gidan honourable, ba ta san sunan shi ba ba kuma ta damu da ta sani ba. Bai fi sau biyu ta hadu da matar gidan ba huldarta tsankaninta da yaran ne. Da karshen wata ya zo wani mai kula da harkokin gidan ya zo ya ba ta albashinta dubu goma cas! duk da rabin wata ta ci. Murna kamar ta yi me. A satin ta yiwa yaranta rijista a wata makarantar kusa da su. Har ta dan fara murmurewa, wannan muguwar kamar ta tsananin yunwa ta fara barinta. Har abada hindatu ba zata manta da Nusy ba, tana daya daga cikin mutane masu abun hannunsu da ba su kyamaci talaka ba. Daga nan sai kawancensu ya koma na kut da kut.

    A yawancin labaran mutanen duniya akwai wata kebantacciyar rana da za su iya ma ta lakabi da ‘azal’ to wannan rana ba ta wuce ranar da ta yi ido biyu da honourable A B Kankiya ba! Shigowa yayi har inda suke lesson, kallo daya tayi ma sa shekarunsa ba za su wuce hamsin ba amma jin dadin rayuwa ya boye. Jallabiya ya sa fara ya aske kan sa amma hakan bai hana nuna tsilli tsillin furfurar da ke barazanar mamaye kan ba.

    Honourable AB Kankiya ya kurawa Hindatu ido yana jinjinawa Nusy da iya aiki da sanin irin kalar macen da ta dacewa sha’awarsa. A karo na barkatai ya ji ya kuma kamuwa da wata irin jaraba da ya kwana biyu bai ji ta ba. A sakwan goma sha biyar ya nakalci halittarta irin nakaltar da ko ita ba ta yiwa kan ta ba!

    Baka ce don ko da can Hindatu ba ta yarda da shafe shafen zamani ba. Komai na fuskarta kadaran kadahan ne ba zaka ce da ita kyakkyawa ko mummuna ba. Sai dai wani abu da ita kan ta ba ta sani ba shi ne kyawunta jiki yake don a cikin mata kafin a samu mai kyaun kirarta za a dade. Tsawonta madaidaici ne hakannan da ya kalli idanuwanta sai take tuna ma sa zamanin da yayi wata budurwa ‘yar kasar ethiopia jamaima, idanuwanta kamar mai jin bacci. Karshen magana sai ya hango wata wushirya a hakoranta abinda yake matukar birge shi a mace, nan fa sai kan sa ya dau caji!

    Ya matso kusa da ita yana mai mika hannu a turance ya ce

    “Nice to meet you”

    Sai ta ji banbarakwai namiji da suna hajara. Ita fa bata saba da irin wannan wayewar ba don haka sai ta noke ta gaishe shi da fatar baki a matsayinsa na wanda ya ceto rayuwarta daga haula. Yayi murmushi, ya riga ya gane ba ‘yar hannu ba ce, da sauranta . Su kayi gaisuwa irinta al’ada ya fice.

    Bayan kwana uku da faruwar hakan Hindatu ta taso daga aikinta tana neman tare dan acaba da misalin karfe 5 na yamma. Ba ta wani dade ba sai ga wata mota rantsetsiya baka wuluk gilasanta masu duhu ta tsaya a gabanta. Ta dan ja da baya a tsorace. A hankali aka saukar da gilas na bangaren mai zaman banza sai idonta suka kallo ma ta ubangidanta yana doka ma ta murmushin rashin dalili.

    Suka gaisa ya ce

    ” malama Hindatu ya na ganki a tsaye anan?”

    Ta ce

    ” yallabai ina neman abun hawa ne zan wuce gida”

    Ya ce

    ” Au to in dai haka ne shigo mana na kai ki, nima zan fita ne zan yi wani dan uzuri.”

    Sai ta ji gabanta ya fadi har shi ma ya lura da hakan, ta dan ja da baya ta ce

    ” Aa ba komai zan ma hau achaba na gode”

    Honourable ya dan gintse fuska nuna alamun rashin jin dadi ya ce

    ” Haba, haba ai ko ba kya aiki a gidana ke kawar Nusy ce don na rage miki hanya ba wani abun ba ne.”

    Ta dan yi jim, in ta ce bata shakkar honourable tayi karya. To amma kuma fa tana tsoron kar ya ga kamar ta yi ma sa raini a matsayinsa na babban mutum kar a je hakan ya sa ta rasa aikinta. Duk da hakan ta ce

    “Wallahi nagode, ba wani nisa gareni ba”

    Ko bai ji me ta ce ba ko kuma ya ji ya share ne kawai don bude motar yayi da nuna alamun ta shigo kawai. Cikin dan jinjinawa ta shiga lintsimemeiyar motar, direba ya ja suka bace daga unguwar.

    A hankali ta dunga yiwa direban kwatance har bakin lungunsu. Ta dan kaikaici ido ta dubi honourable sai ta lura unguwar yake karewa kallo a tsanake kamar mai kirga adadin bolar da kwatocin da suka zagaye gurin. Ya dan kalle ta da murmushin da ya zame ma sa jiki ya ce

    “To ina ne gidan naku?”

    Jiki a sanyaye ta daga dan alinta na nuna wani gida a farkon layi mai kofar karfe da tayi tsatsa. Ta fito a hankali daga motar a ranta tana sake sake ya miko ma ta kudi dauri guda ‘yan hamsin hamsin. A cikin wata murya da take nuna hakan ba komai ba ne ya ce
    “To malama Hindatu ga wannan kya dan rage wani abun ko?”

    Hindatu ba yarinya ba ce. Idan ta ce wadannan halayen da yake nunawa ba su daure ma ta kai ba tayi karya. Don haka tayin farko ta ce

    ” A’a nagode da ka kawo ni gida ma yayi”

    Ya ce

    “Shin malama Hindatu ko kina tsoro na ne? Naga kina dari dari kamar zan cinye namanki danye. Wai ko dai Nusy ba ta miki bayanin ya muke ba ne?” Ya karashe yana dariya dariya. Ambatar Nusy sai ta mika wuya. Sai kuma ranta ya fara tariyo mata irin larurin da zata kashe da wannan kudi. Kawai sai ta karba ta soke wani sashe na zuciyarta na gaya mata watakila yau dai ranar juma’arta ce.

    Me zai faru? Sai rage ma ta hanya da kyautar bazata ya zame wa honourable wata al’ada kamar cin tuwon dare. Ranar sai ta wuce gidan Nusy ta labarta ma ta abunda ke faruwa. Sai ta nuna mata hakan ai ba komai ba ne in dai ta dubi yanayin arzikinsa. Sai ta nuna mata watakila ma zawarcinta ya ke son yi idan aka dace sai tayi aurenta ta huta.

    To dama Hindatu nema take sai kuma masoyiyar zuciyarta ta cigaba da raya ma ta Allah ne maji rokon bawa ya aiko ma ta tsuntsu daga sama gasasshe, shin mai zai hana ta sa hannu biyu ta karbe?

    Da wasa wasa ta gane dai mutumin son ta yake, manufar son wannan ne bata waye da shi ba. Mu’amalarta da shi ba karamin dago tattalin arzikinta yayi ba. Har abun ya zamana cewar wata baya karewa ba tare da ya juye kayan abinci da kudi a gidansu ba. Ba ayi tsawon wata biyu ba ta ji ya tsaya ma ta a rai yayi kane kane. Aka fara soyayya ta ban mamaki!

    Wani abun mamaki shi ne ba ta taba ji yayi maganar aure ba ko me ya sa? Ga shi ta saki jiki da shi abu kadan sai kamo ta ko ya rungumo ta abinda ba ta saba ba amma kuma ta kasa hana shi. Ba don komai ba sai don tana tsoro kar komai ya tarwatse. Sai karin abun Nusy na kara zugata har takan ma ta nuni da cewar ko fa bai aureta ba to ta lashi banza. Ya kuwa za a yi ta bar banza ta wuce daga baya ta zo tana da na sani? Mafarin tunaninta kenen kuma mafarin tarwatsewar rayuwarta!

    A wata rana ya dauketa a mota ya kai ta wani wajen shakatawa da ake yayi a lokacin mai suna see sweet. A ranar ya dalle ta da sabuwar waya wacce ko baza gari ba tayi ba. Kan hindatu ya fashe yau ga ta da waya wanda sai a hannun wane da wane. Gaskiya yallabai na ji da ita!

    Tunaninta ya katse ne a lokacin da ya ce yana bukatar ta ma sa rakiya zuwa Abuja suyi kwana biyu rak a hotel din Nicon Hilton don wani aiki da zai kai shi. Sai ta kwalalo ido a birkice ta ce

    ” yallabai wai ka zata ni karuwa ce?”

    Ya gintse fuska kamar ba shi ne ma’abocin fara’ar nan ba ya ce

    ” A tsammanina ina da matsayi a wurinki da kowacce irin bukata za ta samu gurbi to ashe ma ba haka ba ne. Ashe ni haukan banza ma nake ba so na ki ke ba”

    Jikinta yayi sanyi ta ce

    ” kayi hakuri, gaskiya bazan iya ba. Don Allah ka bar maganar nan”
    Ya kalle ta da wani irin duba mai wuyar fahimta ye ce

    ” Au hakane? Ashe da gaske ne da aka ce yawa yawan mata mayaudara ne. So kawai suka sani a baki, amma a zuciyarsu akasin hakan ne. Nagode da kika nunamin haka hindatu”.

    Har ta koma gida kalamansa suna ma ta yawo a rai. Rabuwa suka yi baram baram ta ce ta hakura da shi tunda tsarin rayuwarsu bai zama daya ba. Sai ba ta doshi wajen aikinta ba, to me za ta je tayi?

    Abubuwa suka fara ja baya ta ga da gaske dai nema take ta koma rayuwarta ta baya. Tana cikin tsammanin warrabuka sai ta ga bari ta je gidan Nusy don tun bayan rabuwarsu da honourable ta daina daga wayarta. Ta kalle ta shekeke ta ce

    ” Arziki na bin ki kina gudu. To menene don ya bukaci ki masa kwana biyu? gutsirarki zai yi?

    Ba tun yau ba Hindatu ta gane Nusy cikakkiyar yar tsalle tsalle ce, a gidan kanta take zaune wanda wani maneminta yayi mata kyautarsa sukutum! sai dai taimakon da tayi ma ta ya sa ta kasa rabuwa da ita.
    Ba ta ce komai ba har ta bar gidan tana tunani. Ta iso gida rai a bace sai kuma me? Kofar gidan ta gani a cike makil an yi cirko cirko, abinda ya zo ranta kawai babarsu ce rai yayi halinsa.

    To amma sai ta dauke wannan tunanin daga ranta bayan ta hange ta a bakin rijiya da sauran mutane ana ta zabga salati. A kidime ta karaso dan ta tantance wannan alamari. A cikin jimla da ba ta wuce biyu ba kanwarta sadiya ke labarta ma ta wai Abba ne safara ta ba shi guga ya debo ruwa sai ya tsunduma rijiya! Amma a halin da ake ciki wani dan unguwar da ya iya ruwa ya shiga ciki ya tsamo shi.!

    Wani irin zaman ‘yan bori ta yi ta dora hannu aka ta na rusa ihun mutuwa. Wai sai yaushe mutuwa za ta daina yi ma ta wafci daidai? Ta ga hakan ba zai ma ta ba kawai sai ta cakumo safara tana ma ta dukan shan gishiri! Duk yanda aka so a raba wannan mugun fadan bai rabu ba sai da aka tsamo Abba ranga ranga. Wani tsoho ne ya ce

    “Yaron nan bai mutu ba, ayi sauri a kai shi asibiti”

    A ka dunga dannawa cikinsa ruwa na fita har ya ja wani irin dogon numfashi. Nan take ya sume. Nan aka dauke shi sai asibiti don karaya ma biyu ce a jikinsa.

    A wannan dare barci bai ko ziyarci gurbin idonta ba tana tsaye a harabar asibiti tana jiran sakamako. Sakamakon bai yi mata dadi ba ba kuma wai don Abba ya rasu ba sai don ana bukatar zunzurutun kudi har naira dubu dari da ashirin na gado da aikin da za a masa.

    Wani jiri ta ji yana dibarta tana jin kan ta a gajimare. Sai ta daidaici wani dan benci tana kukan mutuwa. Wai me yasa mutuwa bata da alkawari ne? Tana ce a bayanta ta suri muhammadunta shi ne yanzu za ta sure mata Abba? Hankalinta bai kara tashi ba sai da tayi ido biyu da dan na ta yana wani irn kukan ban tausayi ya ce

    ” Mama ni ma mutuwa zan yi irin babana? Ba zan dawo ba?”

    Daga wannan kalaman na Abba Hindatu ta san dayan biyu. Ko gangar jikinta ko lafiyar Abba!

    Gidan Nusy ta wuce ita kadai gareta ta labarta ma ta yanda ake ciki. Ta ce
    ” Ya salam Hindatu..ga shi kin zo bani da kudi. Yau da Naira dubu na tashi kacal!” Fuskarta dauke da damuwa.

    Hindatu ga fashe da kuka tana rokonta irin rokon nan na rashin madogara Nusy ta rungume ta ta ce

    “Kuka ba zai yi magani ba ina ga kamar muna da mafita”

    Hindatu tayi sauri ta ce
    ” ya kike ganin za a yi?”
    Ta ce
    ” Honourable kadai zai iya fidda ke. Kin ga masoyinki ne ke ce dai kika ki shi”

    Tayi shiru
    Nusy ta ja tsaki
    ” Ai kin ga irin matsalarki kenen. Ga yanda za a yi sai a bar yaro ya mutu? Ba ga waya ba mu daga mu kira shi na san zai taimaka.”

    Wata zuciyar ta ce wa Hindatu a kul, dayar na gaya mata faretin da mutuwa take a kusa da Abba. Ta ce ta amince. Aka kira shi Nusy ta masa bayani. Akayi rashin sa’a ba ya gari. Amma ya ce a ba Hindatu wayar. Ya ce
    ” Hindah wannan fa ba wani abun damuwa ba ne in dai kina tare da ni to baki da matsala. Ki kwantar da hankalinki kin ji baby na. Gobe karfe 11 zan iso kano inshallahi za ayi settling komai, zai samu lafiya kin ji Hindah na?” Ya karashe a wata yaudararriyar murya ta wadanda suka goge da duniya.

    Washegari kuwa bai saba alkawari ba yana dira ya dauketa suka wuce asibiti. Kafin ka ce me har an shiga da Abba dakin tiyata. Wani irin kwanciyar hankali ya mamaye Hindatu sai ta ji kamar Abba ya warke. Tayi ta zubawa honourable godiya. Ya kamo hannunta yana murzawa ahankali ya ce

    ” Hindah, ai ni ne da godiya” ya daga ma ta gira

    Ta zame hannunta a hankali ta jingina kai a jikin bango, ba ta ce komai ba.

    Aka fito da Abba aiki yayi kyau. Sai jiran warkewa kawai. Bayan kamar sati da aikin honourable ya zo Hindatu na zaune a kujerar roba kusa da gadon Abba shi kuma ya samu bacci. Ya kura ma ta idanu kamar tsohon maye ya ce

    ” kina ta min yanmatanci ko? Wai..me yasa mata duk girmansu sai sun ja aji? Yau ma ba za a mun rakiyar ba ne?”
    Tayi shiru kamar ba zata ce komai ba sai kuma ta ce a kasalance

    “Idan kuma yaron ya tashi fa?”
    Ya kalleta shi ma a kasalance ya ce

    ” wannan din shi ma duk yanmatancin ne”?

    Murmushi yayi yana karkada yan mukulli ya kara da

    ” ina jiranki a mota”

    Ya wuce abin shi.

    Wata nurse ta bawa amanar Abba da cewar za ta je ta dawo. Ta fita kamar kwai ya fashe ma ta a ciki.

    Da ya dauki Hindatu a mota bai zarce koina ba sai Hamdala guest inn. Ya kama daki mai lamba 9. A cikin kalaman kwantar da hankali da alkawurra da dama ya samu ya cika burinsa a kan ta!

    *****************************

    Tana zaune a kujerar gaban mudubi tayi tagumi ba kuka take ba, zuciyarta ta kangare. Mamakin kan ta take, wai yau itace a hotel da wani kato ta kwana da shi?! Shin wai shikenen ta maida kan ta karuwa? Ashe karuwanci ba wuya gareshi ba fadawa cikinsa farat daya ne? Ta ayyana a ranta, tayi ne don ceto ran Abba daga yau ba zata sake ba. Sai dai abinda Hindatu ba ta sani ba shi ne, wannan ne mafarin aukuwar duk wasu al’amura da zasu gabata!

    Ya fito daga bandaki daure da tawul a kugunsa. Ya cigaba da share kan sa da dan karamin yana mai kurawa hindatu ido zuciyarsa na raya masa abubuwa da dama. Ya san Nusy ta san irin kalar matansa amma fa duk da haka ya sha mamaki! Shi ya sa Nusy ta dage da cewar ya nace ba banza ba , ai kuwa kamashonta daban ne. A tsarinsa macen waje duk haduwarta da ya kwana daya da ita to zai aje ta sai wata kuma. Amma alamarin yau yana ba shi mamaki yanda yake jin hindatu a ran sa.

    In bai yi karya ba zai iya cewa duk matan da yake mu’amala da su bai taba haduwa da kamar hindatu ba. Da a tsarinsa zai jefar da ita yau kowa ya kama gabansa amma sai ya ji bai iyawa , Hindah din shi daban ce!

    Ya matso har inda take, a zare hannunta daga tagumi ya ce

    ” Haba Hindah, menene matsalar? Bai kamata kike damun kan ki ba. Ko kina so a canja ma sa asibiti?”

    Haka dai yayi ta bi da ita har ta ware. Ya zaro wata brief case ya ciro damin kudi ya zira ma ta a hannu ya hada da na sa ya matse gam.

    “Ga wannan” yace da ita “ki dan kula da kan ki don zan yi wata ‘yar tafiya zuwa japan gobe amma sati daya zan yi. Hope ba matsala? ” ta girgiza kai. A ranta tana ayyanawa ita da shi har abada. A rashin saninta shedan din da ke yawo a zuciyarta ya wuce duk yanda take tsammaninsa.

    Dawowar da yayi ba su kare a koina ba sai a wani sabon hotel mai suna kings and queens, suka makance a cikin duhun jaraba. Ba ta iya ce ma sa a’a domin shi ma ba ya gajiya da share ma ta hawaye da abun duniya. A gidansu babu wanda ya damu da alamarinta in dai ta samu na kula da yaranta ba ta bar musu dawainiya ba to ba su da damuwa. Hindatu ba ta tsinci rayuwarta a koina ba sai a matsayin farkar honourable AB kankiya!

    Sun fi wata shida suna ta’asarsu son ran su sai ta yanke hukuncin bari ta tuntube shi da batun aure. To da yake dama harkar bariki shirme ce shi a lokacin bama a kan ta hankalisa ya ke ba. Don haka da tayi masa zancen aure sai ya kalle ta galala don shi tunda yake a duniya ma bai taba kawowa ransa aurenta ba. Ba kunya ya gintse fuska ya ce

    ” Haba Hindah, auren lafiya ana zaune kalau? Da me na rage ki da shi har kike hangen aurena zai sa ki same shi? Ka da ki katse mana jin dadin rayuwarmu mana a daidai lokacin da muke cin ganiyarta”

    Ya rungumo ta tamkar wata jinjirar da yake so ya maidata cikinsa yana ajiye wani dalili daya tal a ransa da ya hana yayi mata barin makauniya. Ta zame jikinta a hanakali a sanyaye, in dai ita ba sakarya ba ce ta san yaudarar kan ta kawai ta ke game da A.B kankiya. Ta san holewarsa kawai yake yi da ita amma me? Ita fa mijin aure take nema ashararancin ya isa haka!

    Da dai ya ga tana neman botsare ma sa sai ya ji ran sa ya fara baci har ta kai shi ga cewa

    ” Ku fa ‘ya’yan talakawa ‘yan taka haye ne! Da kun ga mutum da abun hannunsa zai huce lalurarsa da ku sai ku ce sai ya aure ku. An gaya miki na fito bariki neman aure ne? In je in nemi diyar mutunci mana idan auren zan yi!”

    Ba tayi kuka ba, ta wuce kuka da dadewa. Amma wannan wani irin cin fuska ne? Shin wai ba shi ke nemanta da lallami ba ta amince da shi ? Lallai an ci moriyar ganga za a yada korenta.

    Kamar kullum idan ta shiga damuwa gidan Nusy ta wuce ta labarta mata yadda suka yi. Nusy ta lailayo wani ashar!ta kyalkyace da dariya. Ta dubi Hindatu a sakarce ta ce

    ” Tun da nake a duniya ban taba ganin marar wayo irinki ba. Kin kasa fitowa daga akurkinki duniya ta san ki. Me aka yi akai Honourable me ki ka samu a duniya har da zaki maida kan ki baiwar wani ta hanyar aure? Me auren Habu ya kare ki da shi da kike marmarin kara wani? Ai hindatu yanzu ganiyar rayuwarki ta sako kai. Ki ajiye honourable kamar yanda za ki ajiye zanin daurawarki ki canja da mafificinsa! A duniyar nema shi ba komai ba ne! Da za ki bini a sannu ki hankalta da alamarin da zan zo miki da shi, to da ke da talauci sai dai kiji a labaran duniya!

    Tayi shiru maganarta na samun gurbi a tata zuciyar. Ta dubi yadda rayuwarta ta canja a dan kankanin lokaci da ta samu kulawar naira. Maganar gaskiya ta fita cikin kunci da takura daga ita har yaranta. Ta yarda da maganar Nusy. Sai ta fara jin za ta iya komai saboda kudi!

    Nusy ta ce

    ” Idan har kin amince kuma kina so kiyi fice, to akwai wata kungiya…….”

    Kun ji masomin labarin Hindatu.
    MASU ƁUKATAR A TALLATA MUSU HAJOJINSU ZA SU IYA TUNTUƁARMU TA LAMBOBIN 07045308523 MUN GODE

    Note
    error: Content is protected !!