Search
You have no alerts.

    MASU ƁUKATAR A TALLATA MUSU HAJOJINSU ZA SU IYA TUNTUƁARMU TA LAMBOBIN 07045308523 MUN GODE
    Ahayye..yau ana shagalin duniya a gidan nan” cewar ‘yar Modu ” gaskiya ku din nan an yi ‘yan kwal uba! Kamar lokacin da uwarku take da cikinku ta zagi ubanta! Wannan balbalcewa haka.

    Ko da yake zaman duniya ai ta gaji haka..in dai da ranka ai dole sai kayi motsi. Rayuwa idan ba ka daga ‘yar kwalbar nan kana dan zuke zuken nan ya kwakwalwarka za tayi kiliya? Ai sai dai bakin cikin duniya ya yasarka a gindin kwalbati irin yadda ya yada uwata da tayo cikina a kwararo. Billahillazi bata mike ba sai da ta sankato ni! Ahayye Allah raba mu da takaicin duniya…cas!

    Rukky ce ta kalle shi tana dariya

    ” Dama ‘yar maduwaye kai shege ne? Katakatan uba! Haba dole tambadewar tayi yawa ka ce tsotso kayi a nono..hahaha” ta kwashe da dariyar ban haushi

    Yayi sakaka da baki

    ” Yo ke uwar taki da tayi cikinki ta hanyar halas alfahari tayi da ke? Ku ji ni da karamar ‘yar iska. Me kika fasa?kwanan gida ko sane? Ko kuwa idan kun hallara a gaban Allah ana gobe kiyama za ta nuna ki a cikinmu ta hada ubangiji ya jefa ki jahannama? A billahillazi Rukky yanda na san zan mutu haka na san sai mun dandani wuta! Duniya gidan dadi! Allah kar ka kashe mu bamu tuba ba…ahayye nanaye! Gargadi na karshe kar ki kara sani a jinsin da ba nawa ba..To kin ji!”

    Hindu tayi caraf ta ce

    ” Amma ‘yar moduwaye an yi dan tselan uwa Rukky ka ke cewa za ta shiga jahannama? To kai gida Allah zai gina maka a aljanna? Akwai abunda ma ya kai daudu zunubi?”

    Maimakon ya kula ta sai ya dauko karan tabarsa ya kunna ya fara zuka ya ce

    ” ke Hindu shi zunubi yana da kankani yana da mai yawa ne? Yo Allah na tuba ko da sata a ka bar ku ai sai dai ku hango mu a karshen siradi mun tsallaka mun bar ku. Ai wuyarta kan ka mutu kayi taubatan nasuha cikakkiyar tuba kenen. Ka kuma shaidawa Allah ba zaka koma i zuwa wannan aikin zunubin ba. Yo ke ‘yar nan ba ki je islamiyya ba? Dan ahalarin nan ma ba ki haddace ba?”

    Hindu ta zuba masa ido da mamaki ta ce

    ” Ta ce wai kai anan din nan har islamiyya ka je? Amma a bige da daudu? Wanda ya sani ya take shi Allah ya fi hukuntawa!”

    Ya kalleta yayi sakkaka da baki karan taba na reto a lebensa ya ce

    ” Allah jikar Alaramma wacce aka yi cikinta aka haife akan dandamalin masallaci! Aka yiwa uwarta wankan jego da ruwan alwala! To duk yadda aka kai ga tofe ki da kul’a’u zai idan ba ki shuka khairan ba ba ki tadda shi gaba! Ehe kin ji na gaya miki.

    To ‘yar ni din nan da kika raina izifina 20 cif! Hadda kuwa tun daga alhamdu abunda yayi izza sama’u zuwa kulu hiya babu wacce ban iya ba! Kin ga kuwa ina da na sallah wacce muke dan jejjefa ta haka kar abun yayi mana yawa. Babun badiluhu..mu ba tsinana abun arziki ba mu ba mu zauna a musuliluncin ba. Kin ganni nan Alquran Hajiya nike don bara biyu da ta wuce na je aikin hajji na sauke farali..ai aljanna ta mai rabo ce! Ahayye…cas!”

    Hindu ta karkace kai ta rangada guda ‘yar Modu ya bata hannu suka kashe. Ran su tas suna ganin duniya ba a bakin komai ba.

    Duk wannan shagalin da ake a Gidan Hajiya Kububuwa ne a wani tangamemen falo kuma ba su kadai ba ne a ciki. A can gefe kowa shagalinsa yake..yawa yawansu wasan karta suke. Wasu suna gefe suna shaye shaye.

    In da su Hindu ke zaune su hudu ne. Hindu, Rukky , Luba sai ‘yar Modu. Duk wannan hirar da suke ita Luba bata sa baki ba. Ba ta da wani aiki sai zukar wiwi dama gwanace amma tana saurarensu tsaf. A lokacin ne ta ga Rukky jikinta yayi sanyi da maganar da ‘yar Modu ya dankara ma ta. Kawai sai ta tashi ta nufi inda take ta cusa ma ta tabar wiwi a baki ta ce

    ” wayyo Allah na sukari…ai tunani ba naki ba ne! Kin ga duk duniya babu abunda ke yakice tunani irin wannan abar. Ki sha ta ki more ki ji kamar yau aka nada ki sarauniya..ki ji duniyarki fes! Yi ma ta zuka daya tak sukari..wataran idan kika kamata ba kya barta ba!”

    ‘Yar Modu ne ya sa baki ya ce

    ” wallahi! Ai idan zaka sha giya ka sha ta dubu! Kowa ya tuba don wuya ba lada! Duk wanda bai fasa ba ni ‘ yar moduwaye na ce tsinannne dan gaba da kasan wuta!! Yarinya ki sha wanda bai sha ba ya bar dadin duniya…ahayye..nanaye..yau ana shagali!!”

    Rukky ta kafa kai ta zuka sau daya.

    Luba ta ce

    ” wannan ai ba zuka ba ce. Ja za kiyi sosai ta shiga hanjinki da huhunki ta koro miki tarin matsaloli. Gobe idan an ce ga damuwa ko hanyar inda kike ba ta bi ba. Ja sukari..ma za ja”

    Rukky ta kama ta ja da kyau..wani tari ya sarkafe ta ta fara malelekuwa a kasa tana surutan banza. ‘Yar Modu da Luba na mata daria. ‘Yar Modu ya ce

    ” Da kyau ‘yar gidana ai da koyo akan iya. Ai abun ban haushi bai wuce na ganni a layin ‘yan wuta ba ke ba, ina zan sa kai na? In je in shiga uku ga miji barawo ga kishiya mayya!”

    Hindatu ce ta buga tsaki ta gyara zama ta cigaba da danna waya. Chatting suke da wani maneminta tana so ta lallaba shi ta wanke shi tas! Wani tunanin kuma yana kan yaranta tana tuna dadewarta bata je dubo su ba amma dai aiken kudinta baya yankewa. Ta fara tunanin ta sayi gida na ta na kan ta ta kwaso yaranta abunta ta ajiye masu kula da su. Budar bakin ta ta ce

    ” Allah ya kiyaye. Ni duk iskancina wallahi bazan yi shaye shaye ba. Da me zan ji? Ko na tuba kaina ya kwarkwance..iya shege ya iya shege amma shaye shaye har abada! “

    ‘Yar Modu ne ya karkace kai ya rangada guda. Ya ce

    ” An ki cin biri an ci dila…da sannu dai! Ai masomin hauka soshe soshe”

    ****************************

    Yanzu Hindatu tsarin da kika daukarwa rayuwarki hanya ce mai bullewa? Yanzu wannan rayuwa ce da ya kamata ‘ya’yanki su taso su gan ki a ciki? Kin girma amma kina cin kasa? Gaskiya kin yi karkon kifi daga ruwa kin koma wuta!”

    Hindu ta daga kai ta kalli makauniyar mahaifiyarta ranta a cushe, gabadaya ranta ya gama baci. A nata hangen ai yanzu ta wuce nan, a wani zauna ana mata fada kamar karamar yarinya. Da can babu ce tasa take jurewa yanzu kuwa ba ta ga abunda ta tarewa wani ba.

    Zaune take akan wata kujera ‘yar tsugunno sanye da wani ubansun leshi mai ruwan shashanbali. Bata ko yafa mayafi ba ta turo daurinta gaba daidai da zamani. Ta na danna wata tsadaddiyar waya a hannunta hade da tauna cingam kas kas.

    Hindu na kallon duniya wani fage na ‘yancin kai. Ranta na raya mata ta isa don rayuwa ma yanzu ta fara. Ta kalli uwar ta ce

    ” wai Hajiyarmu me nayi? Babu dama in shigo gidan nan sai ki ta min fada. Na san ba zai wuce zantukan mutane ba, su yanzu mutane da kike ganinsu fatansu a kullum su bata ka ko sukai suka. Bakin ciki ake mun an ga Allah ga daukaka ni alhalin da can an ga na zama liability. Wannan aikin dana samu ne fa yake tsonewa mutane ido”

    Hajiya Uwani ta kama baki cike da mamaki ta ce

    ” Hindatu ni ce me miki bakin cikin?” Sai ta fashe da kuka

    Hindu ta ce

    ” Aah Hajiya ke ma kin san ba da ke nake ba da ‘yan gulma nake irinsu Safara. Ba tayi aure ba ba a huta ba tayi aure ba a huta ba. Su suke zuwa suke kawo miki zancena. Na ga duk wani abu da ake bukata daga ku har yara ina kawowa. To na samu aiki sai na bar aiki na zo na tsugunna muna zaman warrabbuka? Haba i cant “

    Hajiya tayi shiru yanzu hindatu tsoro take ba ta ce

    ” Aiki dai aiki dai wannan wani irin aiki ne na shekara da shekaru da kamar ke kwanan gida ya gagare ki? To shikenen ya maganar aure? Yanzu dai autarku ce kadai a gabana sai ke da kika fi karfina. Aure dai shi ne mutuncin diya mace”

    Budar bakin Hindu sai cewa tayi

    ” Na farkon dana yi Hajiya da me ya qare ni? Ai da muguwar rawa gwamma kin tashi”

    Kafin Hajiya ta ce komai sai Abba da Asiya suka yi sallama suka shigo. Suna ganin mahaifiyar su sai suka rugo da gudu suka rungume ta.

    Ta kankame su a jikinta tana jin wani irin nishadi na tsirga mata. Yinifom ne a jikinsu amma sai taga sun zame mata abun kallo sun yi fes da su. Da yanzu sun mutu ko kuma suna cikin ha’ula’i saboda zafin talauci, abinda zuciyarta ke gaya mata kenen.

    Abba ya kara tsawo yayi wayo ya kai shekara goma sha daya. Ya kura ma ta ido har ta tsargu ya ce

    ” Mama na dauka ke ma kin mutu ne kamar babanmu. Muna kwana dayawa bamu gan ki ba. Kar ki tafi ki bar mu kin ji mama”

    Sai taji kwalla ta tarar ma ta. Ta kankame su a jikinta kamar zata maishe su cikinta. A lokacin ne Abba ya fadi wata magana da ta nemi ta tarwatsa.ma ta kwakwalwa. Ya ce

    ” Mama wai menene karuwa?”

    Ai bata san lokacin da ta fizge shi daga jikinta ba ta wancakalar da shi a gurin . Wani irin kallo take ma sa na tsananin mamaki. Cikin zafin rai ta ce

    ” Abba a gidan uban wa ka ji wannan kalmar!”

    Shi ma jikinsa yayi sanyi ganin yadda uwar tayi. A marairaice ya ce

    ” Mama zagi ne ko? Ba ni ne na fada ba. Su munkaila ne ‘ya’yan gidan Hajiya Mari suke fada. Idan muka je makarantar allo ta Malam dogo sai su ce wai ba zasu zauna a kusa da ni ba ko baza su sammin alewarsu ba wai inji mamansu ni dan gidan karuwa ne!!”

    Wani abu ya soki ran Hindu ba da wasa ba wai duk yadda take tunanin tana boye rayuwarta daga kan idon wadanda suka san ta ashe abun ba haka bane? Har ma wai an fara yiwa yaranta gori? Ah lallai yau mai raba ta da Hajiya Mari sai Allah. Kawai sai ta tashi a fusace za ta fice. Hajiya Uwani ta gane fita za tayi ta ce

    ” Zo nan! Dawo nan sakarya ana mata hannunka mai sanda idanunta sun rufe! Dawo ki zauna”

    Ta dawo sai huci take na bacin rai. Yaran sun kura mata ido suna kallon uwar ta su kamar bakuwa. Ta ce

    ” Hajiya wai ba ki ji yanda ake zagi na ba? Wai ‘yan unguwar nan me suke so da ni ne? Habu ya gudu ya bar ni akaita yamadidi da ni yanzu na samu na dogara da kai na abun kuma ya zama kazafi. This is nonsense!”

    Uwar ta ce a sanyaye

    ” Hindatu, kin ga rayuwa ? Ba a mata shigar sauri! Kin ga duniya? To budurwar wawa ce duk wanda ya daka ta tata to zai sha kuka! Kin girma ba sai an zauna ana gaya miki daidai da ba daidai ba sai dai ke ki gayawa wani.

    Yanda kika dau rayuwa wasu dayawa sun dauke ta fiye da ke sun kuma ajiye ta a lokacin da basu shirya ba. Ni dai kin ga karfina ya kare abunda zan muku na yi. Wanda na gaza Allah ya sani ba don son raina ba ne sai dai bazan iya ba. Ki kama kan ki kiyi aure Hindatu lokaci bai kure miki ba.

    Hindatu idan ni ce sanadin jefa ki a wannan rayuwa..ki yafe min..ki yafe min hindatu”

    Kawai sai ta fashe da kuka. Maimakon ta ji ma me take fada sai ya kara kulewa. Matsalarta da Hajiyarsu kenen abu kadan ta saka a gaba tayi kuka. Tana ce ita ma haka tayi kukan? Wa ya cece ta?

    Tayi aure to wa zata aura? Tayi tsaki a hankali kwata kwata maganganun ma basu shigeta ba. Tayi nisa ba ta jin kira. Ta ce

    ” Ni dai Hajiya ba ki min komai ba ni ban ce kin min wani abu ba. Kawai dai zancena na karya da ake kawo miki ki hau ki zauna nake rokonki dan Allah ki daina. In don yara ne ma kawai zan zo na kwashe su akwai wani shiri da nake yi. Maganar aure ki sani a addua Allah ya fito min da nagari”

    Uwar bata sake magana ba, abun ya sha mata kai.

    Hindun ta kalli Abba ta ce

    ” kar in kara jin wannan kalmar a bakinka. Karya suke maka ka ji ko?”

    Yaron ya gyada kai ahankali. Ta ce tana murmushi don su saki jiki

    ” ku zo ku ga abubuwan dana siyo muku na kayan wasa kala kala. Abba kai har da kwallo Asiya ke kuma har da ‘yar bebi”

    Abinka da yara sai suka fara tsalle suna murna. Siyayya ce tayi musu baja baja. Ta kira kanwarta maryam da take kula mata da su ta bata na ta da na uwar. Hajiya uwani dai bata kara cewa komai ba a zuciyarta ta ji kamar ta ce ta kwashe kayan bata so. Amma sai taji kamar tsoron Hindatun ma take ji. A ranta ta raya Allah ya shiryeta idan mai shiryuwa ce.

    Tana gama abunda za tayi ta tashi tayi tafiyarta bayan ta yiwa yaran alkawarin dawowa nan ba da dadewa ba. Ta isa gurin motarta ‘yar madaidaiciya kirar corolla ta bar unguwar. Tunane tunane ke dawo mata rai na ganin yanda aka sa mata ido, ko ina ruwansu oho?

    Tana da appointment da wani Alhaji Bala wani tsohon ministan gwamnatin da ta shude. Sun yi da shi zasu hadu a wani joint ta san yau ranar arzikinta ce.

    Ita komai take yi tana yi ne don yaranta zuciyarta ta raya mata hakan. Kuma kafin su Abba da Asiya su girma za tayi sauri ta tuba ta tara abunda ta tara sai kawai ta bude kasuwanci. Tana son yaranta tana kaunarsu. Ba ta dalilin Abba ba ne don ta ceto ransa ta fada wannan harkar? Da irin wannan tunane tunanen ta tuka motarta ta bar unguwar.

    Ina ma Hindu ta san cewa Abba zai kyamace ta! Irin kyamatar da tayi wa talauci! Ina ma ta san zai yi fatan dama ace bata haife shi ba! Ina ma ta hakura! Ina ma lokaci bai yi halinsa ba!

    Lokaci sakarai ne, ya kan tafi ba tare da ya waiwayo ba, ya kan tafi da burirrika ya kan tafi da imani. Ina ma ana dawo da hannun agogo baya..kaico!!

    *********************************

    Aminan uku Hindu, Rukky da Luba ma fi yawancin abunda za suyi tare suke yi. Amma babu wanda ya san ainihin cikakken labarin danuwansa. Sukan yi hirarrakin duniyarsu su kuma yi zantukan samarinsu da hanyoyin da zasu bi don su wanke su.

    A wannan shekarar suke shawarar barin gidan Hajiya Kububuwa ba don wani abu ba sai don cewar su ma sun giga sun bunkasa. Hindu na da sha’awar ta ware gidanta daban don ta kwaso yaranta da me kula da su. Suk wasu harkokinta na iskanci za ta yi su a waje don ba ta son yaran su gane ko ita wacece. Kafin su kara girma su mallaki hankalin kan su zata watsar da wannan sanaar ta tuba. Tunaninta kenen.

    Kowacce a cikinsu tana da mabanbancin halaye.

    Hindu ita ce me dan hankali kuma ta fi su kaifin tunani. Yawa yawan dubarirrukansu Hindu ke tsarawa da yake ta fi su zurfin ilmi. Hakannan duk cikinsu ta fi su magana da son jan mutum a jiki da kuma rashin tu’ammali da kayan maye. Tana son yawan saka turanci a maganganunta.

    Ko taba sigari ba ta sha bata da wani buri irin yaranta su girma cikin gata da jin dadi. Ita kuma ta yi rayuwa cikin baja baja da annashuwa, watakila ma gaba idan ta tuba har tayi aure.

    Luba dama yar gararamba ce. A duniyarta bata taba wasu cikakkun kawaye ba sai a yanzu, kuma hakan yana mata dadi. Ashe dama ba duka kawaye ba ne maciya amana? Don gaskiya hankalinta ya kwanta da Hindu da kuma Rukky.

    Duk cikinsu ta fi kowa shaye shaye ba abunda ba ta sha. Ta sha giya, taba wiwi roci babu wanda Luba ta bari. Tana yawan saka larabci kadan kadan a maganganunta.Hakannan ta fi son kudi da abun duniya. Ta fi su kaifin wayo da son kai. Luba ta fi gane komai a duniya a ce ta fi wani kuma nata ne ita kadai.

    Ta fi su gogewa a barikanci da sani yanda ake tafiyar da maza. Bata da wani buri irin ta girma ta buwaya ta zama gawurtacviyar yar siyasa ta wawashe kudin gwamnati.

    Ma fi kankantar shekaru a cikinsu ita ce Rukky. Ba ta da yawan magana ba ta da yawan fada. Duk cikinsu babu wacce samari ke kaiwa caffa kyawunta yake ruda su irin Rukky. Ta gwanace da hilatar da namiji da kwakular kudi. Tana yawan saka faransanci a maganganunta.

    Sannan tana da kwanta kwanta maciji sari ka noke a fuska kamar mutuniyar arziki a zuci kuwa ita ta san tuggun da take kullawa. Duk duniya bata da wani buri irin ta girma ta bunkasa ta kai wa makiyinta hari. Da hakan take kwana take tashi.

    A cikin kwanakin nan ma da Luba ta koya mata shan wiwi bata da aiki sai ta samu guri tana zuqa Kamar Allah ya aiko ta. Sai ta ji ranta fes! Tunaninikanta sun tafi.

    A wata ranar lahadi da misalin karfe shida na yamma ‘yar modu ya fado musu daki suna baccin asara. Ya fara yayewa kowacce bargo ya na cewa

    ” kai ku ji min sakalci. Lallai na yarda mata suna suka tara. Yo ai duk inda mace me zaman kanta ta isa da kanta duk inda 6 tayi ta shiga ta tsala wanka lokacin neman kudi yayi. Wallahi ni ‘yar moduwaye tun da uwata ta sallo ni duniya ban taba gani tabararru irinku ba!”

    Hindu ce tace

    ” Look ‘yar Modu ya zaka fado mana daki haka kawai ba wani neman excuse? “

    “Eskis din uwaki!” Ya ce da Hindu yana aiko mata dakuwa ” ka ji almura kamar gidan ubanta! Yo ni ai ko dakin uwaki na fada ba eskis! Menene banbancina da ita?”

    Babu wacce ta kara kula shi don idan da sabo sun saba da halinsa. Kawai sai ya fada bandaki ya tara ruwa ya fito ya ce

    ” Ni fa akan aikina nake don ko sojojin da aka aika dajin sambisa ba zasu nuna min aiki ba..ehe! Kowacce yar iska ta shiga ta sallo wanka yau bamu da wajen zuwa sai La Mirage.

    Wani hadadden gurin ‘yan caca ne na kasaitattun masu kudi. An ce duk karuwar da ba ta je La mirage ta baza hajjarta ba, ta kasa an samu mai saye da tsoka to ta cika mai bakin jini! Ni kuwa na kara da tsinanniya ce da aka kade uwarta dauke da cikinta da bakar mota da daddare!!ahayye..ras!”

    Ai jin samuwa ce sai suka tashi zumbur suka fara shiri. Kowaccensu tayi irin tata shigar da ta fito da irin na ta kyawun.

    ‘Yar modu cikakken kawali ne da yake aiki da Hajiya Kububuwa sama da shekara 10. Babu wani wanda ya girma ya gagara da iskanci da ‘yar modu bai san shi ba. Duk wata kulla kulla ta gidan Hajiya da shi ake yi. Duk wata mai son a hada ta da wani gawurtacce to sai ta bi ta yar modu don ta samu abunda take so.

    La Mirage wani katon wuri ne na holewa na wadanda suka ci suka ta da kai da nera. Babu abunda aka gwanance a wannan gurin sai caca. Duk wani rikakken dan caca da ya giga ya gagara to za ka same shi a la mirage.

    Tun da suka je ba abunda ake sai sharholiya. Wani fitaccen mawakin kasar Ghana aka gayyato yana wasa a gurin. Dama haka suke idan sun yi nishadi sai su gayyato manyan mawaka daga kasashen duniya su zo suyi wasa. Maganar shan giya da sauran kayan maye kuwa ba a magana. Wani abun ban haushi shi ne yawa yawan mazan gurin masu iyalai ne da suka mayar da nan wajen badala.

    Duk cikin yanmatan kowacce ta kama saurayinta. Wani balaraben kasar lebanon shi ya makalewa Rukky ita kuma Hindu wani Alhaji Tanimu mutumin jahar katsina. Luba na tsaye da nata manemin wani matashin yaro da ake kira Zayyad.

    Irin lalatattun yaran masu kudi din nan ne da ba sa jin kwaba. Mahaifinsa babban attajiri ne ya sangarta shi yaron ke yin yadda ya so. Ba shi da aiki sai caca da shaye shaye babu mai ce masa don me.

    A kan tebur din su ne yau ake dabdala ake buga wasan karta kamar ba gobe. Mutum zai iya shiga da mota la miraj ya fito daya shi sai kayan jikinsa saboda an cinye su a caca! To daren yau ana buga wani wasa ne tsakanin matsahin yaro zayyad da wani mutum magidanci Idi Maina.

    Ihu kawai ke tashi kowa da magoya bayansa. Wani abun mamaki Idi Maina ya yiwa zayyad kankat. Tun daga motar da ya zo da ita har agogon hannunsa sai da ya ciwo su. Za a tashi wasa zayyad ya ce bai yarda ba a buga wasan karshe. Idi Maina ya ce ya ji amma akwai sharadi. Ya ce masa ya fada a ji.

    Idi Maina ya dago ya karewa Luba da ke tsaye akan zayyad kallo, hannunta rike da tambulan tana kurbar lemo a hankali ya ce

    ” wannan yarinyar taka za ka bar mun..in dai na kayar da kai to ni zan tafi da ita”

    Cikin zafin rai zayyad ya ce ya ji! Ya ma fizgo ta ya kawo ta tsakiyar fili gani yake kamar abun ba zai yiwu ba. Ita kuma Luba sai dariya take ganin ai yau ta isa har mazan fama na fada akanta. Ba a tashi wannan wasan ba sai da Idi Maina ya ciwo Luba a CACA!!

    Idi Maina a ranar ya zamewa Luba wani tsani…tsanin da yayi sanadin da ta fada wani tarko. Tarko irin na so.. bai ban mamaki!

    Soyayyar da ta zo da alakakai da yayi sanadiyyar tarwatsewar amintar kawayen guda uku. Shin wannan wata irin soyayya ce?????

    MASU ƁUKATAR A TALLATA MUSU HAJOJINSU ZA SU IYA TUNTUƁARMU TA LAMBOBIN 07045308523 MUN GODE me karatu menene ra’ayinka game da labarin nan? A tunaninka ina ya dosa? Me zai faru?

    Note
    error: Content is protected !!