Search
You have no alerts.

    MASU ƁUKATAR A TALLATA MUSU HAJOJINSU ZA SU IYA TUNTUƁARMU TA LAMBOBIN 07045308523 MUN GODE

    Shekaru kadan da suka wuce

    Harabar La mirage cike take da manyan motoci na masu fada a ji, wadanda shedan ya buga musu ganga suke taka rawa. Ranar ta kama asabar yawan yawan ma’aikata da suke Abuja da kaduna sun shigo hutun karshen sati. Mafi yawansu kan rashe a wannan waje domin nishadi, suna taba dan shaye shaye da caca.

    Wannan karin wani mawakin Hausa suka dauka mai suna “dan mudubi”. Sukan yi hakan idan sun so nishadi ko su dauko masu garaya suna wake su kan su na fasuwa.

    A ranar dai waken dan mudubi bai wuce kan Almustapha ba. Almustapha bai fasa yi masa ruwan nera ba kamar bai san ciwonta ba!. Ran dan mudubi fes! Har yakan ce

    Ka ga Mustapha gwani na gwanaye!

    Yaro da kudi abokin tafiyar manya

    Mai takalmin karfe kowa ka taka ya taku
    M
    usty nera ka je las vegas sun buga sun kyale!

    Wanan abu kan fasa kan Almustapha, sai ya dunga jin kamar shi kadai ne ya gawurta duniyar! Aka dunga cika masa kofi da gulder yana sha yana barin nera!

    Akwai wani da ake kira Hafeez kamala. Wani matashin yaro ne mai irin zubin Almustapha. Shi ma gwanin caca ne ba karya kuma wannan kirari na dan mudubi yana sosa masa rai. Yaushe Almustaphan ya shigo bariki har da zai nuna musu ya isa? Karamin yaro dan haure asalinsa ma ba dan najeriya ba! Ya za a zo garinsu a fi su da rawa sa’annan a bi su tsinannen duka?! Ina ba za ta yiwu ba!

    Almustapha ya cigaba da cika tambulansa da giya yana durka ma cikinsa, yau nishadi yake ji! Wani abu da bai cika yi ba, buguwa da giya. Na kusa kusa da shi mazigansa da suke kiran kansu masoyansa sa suna kara ingiza shi nuna masa duniya fa ba komai ba ce.

    Ana cikin wannan shagalin ne da Hafeez kamala fa ya lura Almustapha ya yi tatul sai yayi challeging din sa da caca. Ba ai wata wata ba aka share fili ana shirin ganin wannan wasa tsakanin gwanaye biyu. Kowa yana da magoya bayansa ‘yan shaida. Ba a komai sai iface iface da kumburawa mutum kai.

    Sai a lokacin Hafeez kamala yace

    ” idan ka cika kai gwani ne na gwanaye. Yaro ne kai abokin tafiyar manya. Ga dan mukullin mota ta. Sabuwa ce dal! Zuwan shekaran jiya. Benz ce da za ta kai kimanin naira miliyan ashirin. A yau na sata a tsakiyar fili idan a yau kai ka ci cacar nan na ba ka ita!”

    Ya dauko mukulli ya aje bisa tebur

    Waje ya dau ihu da sowa Almustapha yana murmushin takaici. Kamar shi har za ayi challenging irin haka? A la mirage babu gwani kamarsa! Zai nunawa Hafeez Kamala ya ci ubansa ya dama a caca!”

    Ya ce

    ” Na ka wasa ne. Me aka yi aka yi motar miliyan 20? A gurinka take kudi. Sabon kamfaninmu da zamu bude da zai doke kowani kamfani na sayarda kayan masarufi a Arewacin Najeriya gabadaya shi zan aza bisa tebur! In ka isa kai gawurtacce ne sai ka nuna a daren yau!Idan ka ci ni ka dauka na baka halak!”

    Yawa yawan mutanen gurin sun ga wautar Almustapha to amma su fa ‘yan abi yarima a sha kida ne. Sun san giyar kudi ke rudarsa, Idan ba don haka ba wa zai yi wannan gangancin?

    Hafeez kamala ya ce a fusace

    ” karya kake ba zaka iya ba! Idan za ka iya dauko takardun a aje bisa tebur idan ka haihu cikin uwarka”

    To wannan abu ya fusata shi har ya bazama dauko takardun da ke compartment na motarsa. A ranar ya karbo su daga inda ya bada a ajiya a banki, mahaifinsa zai saka hannu à wani waje. Sai akai rashin sa’a wannan muhawara ta ritsa da su.

    Ganin abunda Almustapha ke yi kamar ba cikin hankalinsa dan nuna izza da isa ya sa sadiq abokinsa rike shi. Yayi nufin hana shi don ya san al’amari na giya to amma sai Almustaphan ya ki. Wai hakan zai iya nuna gazawarsa.

    Ihu da sowa bai mutu ba a harabar la mirage kowa idonsa na kan abunda ake yi. Aka fara buga wasan karta tsakanin Almustapha da Hafeez kamala.

    Wasu lokutan ba kullum ake kasa kaya a sayar ba, duk yanda mutum ya so sai yayi bandaro. To hakan ce ta faru domin kuwa babu wani tsimi babu dubara Hafeez Kamala ya cinye wannan caca!Bai yi wata wata ba ya wawashe takardun nan muhimmai ya bar Almustapha da mutanensa a zaune cikin madaukakin mamaki!

    Wannan al’amari ya girgiza la mirage har ta kai fada ya balle. Almustapha yana cikin dimuwa da tashin hankali. A tarihin la mirage bai taba rasa caca ba. Bai taba zaton Hafeez zai ci ba, ko kusa tunanin shi bai ba shi hakan ba. Da ya san zai ci ko da wasa ba zai fidda takardun nan ba domin hakan wasa da rai ne!

    Da kyar abokinsa sadiq ya janye shi ya kai shi mota. Dole abokin ya tuka ya kai shi gida. Ya kale shi da cewar zai garzayo ofis gobe su tattauna mafita.

    A ranar Almustapha bai rintsa ba. Abubuwa biyu ke damunsa a rai. Da farko wannan kamfanin da shi za suyi suna. Ya mahaifinsa zai ji idan ya ji wannan ta’asar da ya tafka?

    Na biyu a lokacin suka bude sabuwar jamiyyarsu, tayi fice tana tashe. Magana daya zata fito yanzu sun shiga uku da ‘yan adawa. A bi shi da yamadidi. Watakila har wadanda suke ganin mutuncin shi su daina.

    Duk abunda yake yi a boye yake yi. Almustapha mai son a ga shi mai tsantsani ne, mai tsoron Allah. Da hakan ya kan janyo manyan manyan mutane su so shi. Su so muamala da shi.

    Wani irin hali gare shi na musa a fuska firauna a zuci. Za ka gan shi gaba akan sahu, shi ne taron kwamitin masallaci, gobe shi ne babba a taron musabaqa. Gobe bayarda da tallafi ga daliban makarantun islamiyya.

    Bai cika son a san shi ciki da bai ba, yawa yawan dalilan da suka sa ya rabu da matarsa khairiyya. Yanzu idan zance ya fito kan ya nuna irin wannan ganganci da wani ido zai kalli mutane? Ya san ko giyar wake Hafeez ya sha bai dawo da takardun nan. Bai isa ya yiwa hafeez cune a sace takardun nan ba domin kuwa shi ma gwaskan kan sa ne! Dan duniya ne da ya dade a bariki. Abu kadan Almustapha zai yi Hafeez ya juyo kan sa, ya kuma san ba zai ji ta dadi ba! Don haka menene mafita?

    Dole ya san yadda zai yi ya dawo da takardun nan a karamin lokaci? Dole ne!

    Da wannan ya kwana a ran sa.

    **********************************

    “Almustapha ya kamata fa ka gane” cewar sadiq” lalashin Hafeez ko yi masa fito na fito ba zai sa ya dawo da takardun nan ba. Wannan abu an yi shi ne specifically don a ci mutuncin ka. Ban ma yarda da wasan nan ba akwai wani magudi a ciki. Shin ko kana tunanin hada shi da hukuma?”

    Wani irin numfashi Almustapha ya saki. Ya sa hannu ya loosing necktie din sa da yake jin kamar ya shake shi. Komai ya dagule masa a kwana 2 kacal! Me ye haka?

    Hukuma? To ya cewa hukuma me? Ai kamar ya daga hannu ya caka ma ka sa wuka kenen. Makiyansa su ji suyi masa dariya. Bayan shi a karan kan sa ya san a sha cin makudan kudade da kadarori a la mirage. Ba a taba cinye shi a caca ba sai a ranar.

    Ai ko dan cikinka ka saka a caca a la mirage ka fadi to ya cinyu! Balle takardun kamfani. Dama ai caca ta gaji haka ko ka ci ko a cinye ka.

    Abun da yake tunanin ba komai ba ne ya zo ya tsaya masa a makoshi. Ba irin lallamin da bai aika an yi ma hafeez ba to amma abu ya gagara. Ya masa alkawarin kudade masu dama a madadin takardun amma ya ki. To shi yanzu ya zai yi?

    Kwanaki sai matsowa suke da mahaifinsa zai shigo da Niamey domin za a kaddamar da kamfani. Da me zai ji wai.

    Ya kalli sadiq a tsanake. Abokinsa ne tun lokacin da daura alkawari da bariki. Ko banza sadiq idon gari ne kuma idonsa ne a wajaje da dama. Abokin sirrinsa ne domin kuwa yana matukar taimaka masa a harkokin lullube fuskarsa. Ya ce

    ” Sadiq kai na ya daure. Allah kwanakin nan ko runtsawa bana yi. Ni kawai ka bani shawara menene kake ganin za a yi?”

    Sadiq ya nisa shi ma a kwana biyun nan ba kanta. Can kamar mai tunani sannan ya dubi Almustapha ya ce

    ” Amma ka san an ce idan gabas ta ki sai a koma yamma. Ba ka gani kamar ya kamata mu aje komai a gefe mu hada shi da malamai. Malamai masu aiki irin na hatsabibanci. Aiki irin na tsubbu! Su rufe masa baki su rufe masa gani ya dawo da takardun nan ko ya ki ko ya so!”

    Kallin galala Almustapha ke yiwa Sadiq. A rayuwarsa iskancin sa ya iskancinsa amma bai taba shiga harka ta irin dube duben nan ba. Ma fi yawan lokuta ma bai yarda da su ba. Gani yake wani ne kawai yunwa ta ishe shi ya baza buzunsa yake yin damfara.

    Ya ce

    ” Kai sadiq wadannan yan damfara ne kawai! Me za su iya mana banda su karbi kudaden mu su ware? Ka sake shawara”

    Dariya sadiq yayi ya ce

    ” yallabai kenen. Ai idan baka san gari ba to ka nemi dan jagora! Da gaske malamai na damfara , to amma wannan kankat ne! Dalili kuwa lokacin da mahaifinmu ya rasu ka san ya bar mata da yara dayawa. To an ta yin hatsaniya wajen rabon gado.

    Mahaifiyarmu da take mowarsa akwai takardun gidajensa da filaye dayawa a gurinta. Magada suka yi mata caa ta fito da su ita kuma bata ga dalilin hakan ba. Wallahi da ta ga sun sako ta gaba ba shiri ta dauke ni muka je wajen wannan malamin aka rufe bakinsu. Har jini sai da aka zubar!Ka san Allah? Yau shekara goma kenen da rasuwar wallahi har yau! Ba wanda ya kara daga maganar filayen nan!”

    Wani irin shock ne ya shigi Almustapha har ya kurawa sadiq ido. Karara ya gane gaskiyarsa yake fadi. Bai yi mamaki ba amma abun ya tsorata shi. Wani sashe na zuciyarsa na raya masa ya je wani na hana shi. Ya ce

    ” Sadiq anya hakan kuwa ba babban zunubi ba ne? Ga hakkin mutane da kuka danne ga kuma shirka?”

    Sadiq ya dan jingina da kujerar da yake zaune yana murmushi ya ce

    ” Lallai mutumina ba duniyar kake nema ba. Ai me neman duniya baya tone tone. Duk wadanan manyan mutanen da ka ke gani attajirai da manyan masu kudi a tunaninka haka sunka zauna? Wa billahillazi sai da tsaro! Ko ba ka nemi kayan yaki ba ai ka nemi na kariya.

    Kuma waye ya gaya maka shirka ne? Ba fa boka ba ne. Ba a daji yake ba a gidansa yake a zaune.Kawai dai yana da ilimin Almatsutsai da taurari. Da su yake amfani ya taimaki mutane su biya bukatarsu. To..to idan banda abunka ma Allah ai gafurur rahimu ne. Idan ka gama al’amarunka na biyan bukata ba kawai sai ka roke shi gafara ba! Ka tuba, wallahi yafe maka zai yi.”

    Sai zuciyar Almustapha mai tsananin son biyan bukata ta ga ai hakan ne! Kuma ga shi shi bama hakkin wani zai danne ba hakkinsa ma zai kwato. Me ye a ciki? Shi ba jini zai zubar ba
    Kuma inshallahu zai tuba.

    Da wannan suka shiga mota suka tafi wani yanki na kauyen Rano ba su tsaya ba sai a kofar soron malamin nan.

    Tsoho ne amma ba tukuf ba. Ya shaida sadiq domin kuwa yana yawan ziyartarsa shi da mahaifiyarsa. Babu wani bata lokaci suka yi masa bayani. Ya yi ‘yan zane zanensa a kan kasa ya dago ya kalle su yace

    ” Za a yi aiki, ba kuma wani abu ne mai wahala ba. Da kan sa zai dauko takardun ya dawo da su, kuma ba zai kara tada zancen ba, ba zai taba bari a masa zancen ba kuma ba zai kara saurarar duk wanda ya masa zancen ba!”

    Almustapha ya ji ran sa fes! Anya ba zai dawo wajen mutumin nan akan alamuransa na siyasa ba? So yake ya kafa kansa watakil shekaru kamar goma masu zuwa sai ka ga ya zama gwamna!

    Ya ci gaba da kallon tsohon yayin da tsohon ya cigaba da bayani kamar haka

    ” kafin hakan ta faru sai ka nemi tauraruwarka. Sai kayi mu’amala da tauraruwarka na kwana daya tal! Daga nan ba zaka kara waiwayenta ba. Yadda baka waiwayeta ba haka hafeez zai dawo maka da takardun nan ba zai waiwayeka ba. Ba a so ka kara haduwa da ita daga wannan rana, idan kuwa har hakan ta faru duk abinda ya biyo baya kayi kuka da kan ka!”

    Sai da gaban Almustapha ya fadi. Sai ya ji kamar abun ya fara fice masa a kai. Kamar tsafi. Me ya kawo shi ne wai? Sai a ranar ya fara jin ya tsani caca da duk wani abu da ya dangance ta don ga shi bata kare shi da komai ba sai wahala.

    To amma ya zai yi? Idan bai bi shawarar malamin nan ba wata shawara zai bi? Ko da wasa ba zai iya bar wa hafeez takardun nan ba inaa..da sake.

    Yayi gyaran murya ya ce

    ” Ina fatan dai ba za a zubar da jini ba?”

    Tsohon yayi jim sannan ya ce

    ” Ni dai ban ga zub da jini ba, kuma ta bangare na bazan saka zubar da jini ba. Sai dai kuma abunda ke boye a gaba wanda kai zaka iya fi na sani”

    Wata magana yake masa kamar zaurance. Amma sai ya share. Ya ce

    ” to ita mecece tauraruwar tawa”

    Tsoho ya ce

    ” Mace ce..kuma ta zo a Ahlul kitabi”!

    AlMustapha ya ji gabansa yana wani irin lugude na tsoro amma ya kasa hana zuciyarsa abunda take so. Ya ce

    ” To a ina zan gan ta? Ya zan gane ta?”

    Tsoho ya ce

    ” Ba a garin nan take ba..tana wani gari a kudancin kaduna. Zan fasalta maka inda zaka je. Tana siffofi kamar haka:

    Bata da yawan hasken fata amma ba za a saka ta a bakake ba,doguwa tana da ingarman jiki, tana da idanuwa masu kama da na kyanwa. Tana yawan saka bakaken tufafi. Ahlul kitabi ce mabiya addinin kiristanci. Tana zaman kanta ne a wannan gari kuma shahararriya ce, tana zaune a wani sanannen gidan mata da ke garin. Idan ka cigaba da ziyartar wannan gidan matan zata wuce za ka ganta za kuma ka san ita ce. Zaka neme ta na kwana daya ba za kuma ka waiwayeta ba. Ba za ayi sati ba zaka zo ka bani labarin dawo da takardun nan.”

    Tsafi ne! Siddabaru ne! Shirka ce!

    Abinda ke yawo a ran Almustapha kenen. Kawai sai ya ji ba zai iya ba ya tashi ya bar tsohon nan a gurin. Sadiq na kwala masa kira bai waiwayo ba. Kawai wani huci mai zafi yake fitarwa daga bakinsa.

    ” Bana so in zama haka, bana so in so duniya har haka!”

    So yake ya ceci imaninsa amma kamar abun ya gagara. Wataran yakan yi tunanin halayensa ya ga ya kamata fa ya daina wani abun domin lokaci fa tafiya yake kuma mutuwa bata sauraren uzuri. Amma sai ya ji ya kasa.

    Har ya koma gida yana tunanin mafita, ya san Sadiq yayi fushi da shi. To amma ya zai yi?

    A ranar ya gane ashe ba shi da abokin shawara ko da kuwa uwarsa ce mahaifiya? Ashe shi kadai ne? Ina ma Momodou na nan ko zai yarda? Wata shawara zai iya ba shi? Yawan yawan mutanensa ya san suna tare da shi ne dan dukiya da daukakar da Allah ya ba shi. A yau ina masoyi na gaskiya?

    Ran sa bai dagule ba sai da ya samu kira daga mahaifinsa a wannan dare da yasa shi yanke hukuncin da bai shirya ba. Ya gaya masa nan da kwanaki zai karaso shi da mutanensa. Ya cigaba da masa jawabin cewa sun samu investors da yawa da suke burin saka hannun jarinsu a wanan kamfani. Yana yiwa Almustapha albishir da cewar sun kusa kafa record bama a yankin su Niger da chadi da makusantan kasashe ba, har ma a Najeriya gabadaya.

    Yadda mahaifinsa ke magana da dandazon da ya san za a tara ya sa ya yanke hukuncin bin maganar malamin nan.

    Ya daga waya ya kira sadiq, a bugu na uku ya dauka muryarsa ba walwala. Almustapha ya ce

    ” ka shirya gobe mu dau damarar tafiyar nan, zamu je neman tauraruwar nan”

    ***********************************

    Ko da suka je kaduna garin da tsohon nan yayi magana ba su wani sha wahalar gane gidan matan da ya ambata ba. Wani gida ne na masu zaman kan su daga garuruwa daban daban suka taru suke aikata abunda ran su ya so.

    Babu kalar kabila ko addinin da babu a gidan. A gaban gidan wani wajen sayar da abinci ne mamallakin magajiyar gidan mai suna REBECCA.

    Rebecca ba ta da asalin da wani zai labarta. Yawa yawan mutane na hasashen wai ‘yar bendel ce. Wasu kuma sukan ce yaren tivi ce da ke can jahar benue. Kawai dai ganinta aka yi ta zo garin da makudan kudade ta bude wannan gida. Ba zata haura shekara 35 da biyar ba amma shahararta da hatsabibancinta ya wuce karamin tunani. Tana jin yare sama da guda bakwai.

    Wata kawarta bayan sun yi baram baram ta ce wai Rebecca mijinta ta kashe ta gudo da kudin ta bude wannan gidan. Ko da zancen ya fito bai damu rebecca ba , haka take abun kunya na duniya ba su cika damunta ba. Ita dai kawai ta samu kudi tayi facaka ta more.

    An yi rikicin duniya akan rufe gidan nan , hukuma tayi iya yin ta amma abu ya faskara. To mafi yawan manyan mutane da suke rike da mukamai suna da karuwai a gidan. Dalilin da yasa kenen hukuncin rufe gidan ya ki tasiri.

    Tana da mutane iya mutane babu kuma kalar zunnubin da ba a aikatawa a gidan na ta. Don haka ba kananan kudade take caska ba. Ta kuma bude wani katin gidan abinci a gaban wajen inda ake zuwa siya daga wurare da dama.

    Mace ce da bata cika son yin kwalliya ba. Mafi yawan kayanta bakake ne kuma tana dauke da cross a wuyanta. Ga wanda bai san ta ba babu abunda zai hana ya ce mai zafin rike addinin kiristanci ce. To amma inaa..ko coci kafarta bata taba takawa ba. Yanayin ra’ayinta ne kawai.

    Almustapha da sadiq suka sauka a wani hotel da ba shi da nisa da wannan gidan matan. Ba su da aiki sai su share guri a kofar hotel din su zauna, su je zagayen gari su dawo.

    A kwana na uku ne Almustapha ya gaji ya dubi Sadiq ya ce

    ” kai ni fa na gaji. An taba gane mutumin da ba a taba gani ba? Kwananmu uku a gari ba wani bayani? Anya mutumin nan ba damfararmu yake ba?”

    Sadiq ya ce

    ” To idan banda abunka mutumin da yace sai aiki ya ci zamu biya saboda tsabar sanin aikinsa. Muyi hakurin yau mu gani. Kai yallabai kamar ba ka san ita biyan bukata sai an cije an dage ba”

    Da jin haka sai Almustapha yayi shiru. Yana ta tunane tunanen yawan aikin da ya bari a kano. Ga kiran da mahaifinsa ke ruga masa na nemansa da gaggawa. Sadiq ne ba bada shawarar su shiga gidan abincin nan su ci ko sa rage lokaci.

    Shigarsu yayi daidai da fitowar Rebecca, suka kusa yin karo ita da Almustapha. Kallo daya ya mata gabansa ya yanke ya fadi dan tsoro sai da ya ji jikinsa na karkarwa. Bata da wani banbanci da yanda dan tsohon nan ya fasalta masa. Danqari!

    Har ya zauna ya kasa dauke idonsa akanta haka ita ma. Shi don tsananin mamaki ita kuma dan tsananin kyawunsa da take gani. Gaskiya ya mata a ganin farko ta san ya mata. Sai abunda ya turewa buzu nadi.

    Duk abinda suka ci a ranar ta hana su biya kudin. Sai shisshigewa Almustapha take. Ta yi masa masauki a kawataccen dakinta na alfarma. Kowa fa manufarsa a rai. Ita ta so da kaunarsa shi kuma na biyan bukatarsa.

    Asubar fari Almustapha ya sulale ya gudu daga dakin Rebecca ba wai don wani abu ba kawai gani yake ya tsani gari da duk abinda yake cikinsa. Tun da ya aikata abunda ya kawo shi, to me ya rage? Kawai sai yayi komawarsa kano ba tare da ya waiwayeta ba kamar yadda tsohon nan ya fada ba kuma tare da ya bar wani abu da zata iya tunawa da shi ba. Bai kawo komai zai biyo baya ba bai taba kawo wa ba.

    Tafiyar Almustapha wani abu ne da Rebecca ta daukake shi ba nan kusa ba. Tun da take a rayuwarta bata taba jin son wani kamar shi ba. Ya zai yi mata haka? Duk yanda take tunanin zata neme shi tayi cigiyarsa tayi amma ba ko labari. Tayi kuka kamar ranta zai fita. Ta nisantar da kan ta daga kowani maneminta saboda tsabar kewarsa.

    Daga baya ta hakura. Amma me? Bai yi wata biyu da tafiya ba ta gane tana dauke ta juna biyu. Ba sai ta bincika ba ta san babu tantama na masoyinta ne. Har zata zubar wata zuciyarta ta ce mata ta bar shi kawai, me ya fi da ya wuce ta ajiye dan masoyinta ta dunga kallonsa kullum? Ba ta dai gama tantancewa ko ta bari ba sai da wani abu ya faru.

    Wata kawarta ce Reema ta shigo da wata mujalla ta ‘yan wasan polo da aka yi a kaduna na wannan shekarar. A ciki ne ta ga hoton Almustapha a kasan a rubuta.

    ” Shahararren matashin attajiri kuma dan siyasa nan da ake masa taken ” yaro abokin tafiyar manya” mai suna Almustapha a wajen kallon wasan polo da aka yi a wannan shekarar”

    Ba tayi wata wata ba ta karbi mujallar ta rungume. Ashe ma sananne ne! Ah ai ita ke da jari. Babu abunda zai hana illa ta ajiye cikinta ta haifo abunta. Samo Almustapha ashe ma ba abu ne mai wuya ba! Ashe sunansa kenen! Wayyo masoyinta Almustapha.

    Ai da cikinta bata da wata danuwa. Za ta ajiye ranar da zata tunkare shi kuma dole ya saurare ta! Dole ne ya zamo nata. Dole ya aureta. Domin kuwa tana dauke da gudan jininsa.

    Ba za tayi garaje ba, a sannu zata bi don ta cimma buri.

    Da ciki ya isa haihuwa ta haifo santaleln danta mai kama da ubansa sak! Abunda ya fi burge Rebecca kenen. Babu abinda ya bari na ubansa har idanun. Ba tayi wata wata ba ta laka masa suna AL MUSTAPHA. Ai kyaun da , ya gaji ubansa. Zata fara kirga lokaci da Almustapha zai hadu da gudan jininsa. Tana bibiyar labaransa tana bibiyar takunsa ba tare da ya sani ba.

    Lokacin da ta ga abubuwansa sun kankama, siyasa ta zo ya kara bunkasa. Yaronta na yawo koina kamanninsa da ubansa na fitowa baro baro. Ta shirya tsaf ta tunkari garin kano, domin lokaci yayi. Lokaci yayi da Almustapha zai zamo nata, ita daya. Dole ne ya aureta ko ta shiga kafafen yada labarai da na sada zumunta ta bata shi! Ta bata shi a daidai lokacin da baya bukatar tozarci!

    Ta san komai nasa , bata kuma sha wahala ba ta bayyana a ofis din sa. Za ta sanar masa da wani albishir wani daddaden albishir na samuwar gudan jininsa Al mustapha.

    ***** *****

    Ko bayan da Almustpha ya koma kano bayan rabuwarsu da Rebacca bai kara tuna ta ba. Me zai yi da ita shi da aka ce kar ya waiwayeta.

    Wani abun da ya bashi tsananin mamaki shi ne ba ayi kwana uku da dawowarsa ba sai ga Hafeez kamala ya kawo masa takardun kamfanin nan har ofis.

    Ko bayan tafiyar Hafeez din sai ya kama kan sa yana dariya wata irin dariya ta mutanen da suka samu duniya, ta zo musu a tafin hannu.

    Sai ya kama kan sa yana yiwa kan sa kirari da

    ” Sai ni Almustapha, mai takalmin karfe..kowa na taka..ya taku!!”

    Abinda Almustapha bai sani ba shi ne

    Duniya tana zuwa maka ne a yadda ka dauke ta

    Ba zaka taba girbar abunda baka shuka ba

    Sannan, shi sharri kare ne

    Mai shi yakan bi!

    *********************************

    A YAU

    ” our baby is home”

    Kalaman Rebecca da suka bakunci kunnen Almustapha suka tarwatsa masa zuciyarsa kenen.

    Bai yi wata wata ba ya wancakalar da ita daga jikinsa ya na auna mata mummunan kallo. Ya ce a fusace

    ” What the hell are you doing in my office? Kar ki zo ki min iskacinku karuwai anan. You better behave yourself ko yanzu na saka security su waje da ke!”

    Kallon shi take yi kamar tababbe sa’annan ta fashe da dariya. Ta san za a yi haka, fiye da haka ma ta san za a yi. To amma me? Ta shirya. Irin shirin da bai zata ba.

    Ta ce

    ” look young man. Ba zai yiwu akan karya na taho daga nesa na ce kana da yaro ba. Ka kwantar da hankalinka da sannu zaka gane bayani na.”

    Ta fito da wayarta ta nuna masa hoton da ha mamaye fuskar wayar ta ce

    ” Ga shi nan..ka kalle shi da kyau ka ce you havent seen a part of you in his eyes! Yana nan na rada masa sunanka. Kyaun da ya gaji ubansa!”

    Kawai sai ta fashe da dariya

    Ya ga hoton, ya kuma gane abu daya. Yaron nan ko ba dan sa ba ne jininsa ne. Don har sai da ya ji tsikar jikinsa ya tashi yarrr. Me ye haka? Me yasa balai yake danno sa ne?

    Ta ce

    ” ko baka yarda ba za mu iya zuwa ayi muku Dna test bani da damuwa akan hakan. Fata na dai ka yarda ka gane yaronka ne”

    Wani abu ya hadiye mukut don tsananin bakin ciki. Ya aka yi yarinyar nan ta shammace shi haka? Da ya san zata iya masa haka babu abunda zai hana ya sa a batar da ita. Shi zata batawa wasa.? Wasa a daidai lokacin da yake daf da cimma burinsa.

    “What do you want?”

    Tambayar da yayi mata kenen kai tsaye

    Ta ce

    ” Ka aureni. Idan baka amince ba a shirye nake da na yayata ka na bata maka suna. Jaridar da zata fito a watan gobe bai wuce wacce ke dauke da sunanka ba da cewar ka min fyade! Har yayi sanadin da na samu ciki! Yaron nan dan ka ne ba ko tantama. Yaya kake ganin abokanan hamayyarka zasu dauki zancen nan? Ya ya ka ke ganin mutanen da za su zabi jamiyyarku saboda kai za su ji? Wadanda suke ganin mutuncinka fa?

    Kai bari na gaya maka sai na kai ka kotu akan fyade. Sai nayi dragging sunanka in the mud! Kafin a gane gaskiya sunanka ya ri ga ya baci. Yaron dai yana gurina idan kana so muyi magana ga number na nan. Tick…tock”

    Ta fice ta bar shi a tsaye yana share zufa cikin tsananin bacin rai.

    Almustapha bai yi wata wata ba ya aikawa sadiq waya yana masa neman gaggawa. Haka ya zo ya zauna suka yi jugub jugub suna neman mafita. Sadiq ya ce

    ” yanzu haka sharrinsu ne fa na karuwai. Har yaushe a kwana daya zata ce wai an bar ta da ciki. Kayi watsi da zancenta kawai. Kuma ai zaka iya musuntawa. Tunda bata da wata kwakkwarar shaida”

    Almustapha ya daki tebur din sa ya ce

    ” Baka gane ba sadiq, wannan matar ta dade tana shirinta. Ta riga ta kwana da makaman yakinta. Wannan yaron zan yi DNA test, amman fa jikina yana bani nawa ne. Ka san kuwa duk inda yaro ya zamo nawa dole ni ne a kasa. Ya zan yi idan a daidai wannan lokacin duniya ta ji ina da dan shege??”

    Murmushi sadiq yayi yana mikewa tsaye ya ce

    ” Mutumina wannan fa ba abun damuwa ba ne. To mene a ciki idan ka aureta? Sai kayi auren a sirrance. Kwana nawa ne an yi zabe an kare. Tarzoma ta kwanta. Ka zake ta ta kama gabanta. Ka ga kayi mata lumbu lumbu kenen wutar kaikayi. Duk inda ka aureta ka saki wa zai kama wani zancen fyade? Wa sai damu da wani shege. Ina ganin hakan shi zai sa ka tsira da mutuncinka”.

    Shi ma tsaye ya mike shawarar bata masa ba. Ya aureta yace ya auri wa? Kilaki ma kilaki irin Rebecca?

    Amma me? Sai ya ji kamar yana son ganin dan. Ya kalli idon yaron a hoto sai ya ga kamar ya kura ma sa ido.

    Ya sunkuyar da kan sa. Sadiq ya ci gaba da nuna masa auren nan fa shi ne dubara. A haka suka rabu.

    Wani abu da Almustapha bai sani ba shi ne makiyansa suna tare da shi. Wadanda ya yarda da su , su suke masa gadar zare su suke neman ganin bayansa.

    Sadiq da Rebecca bakinsu daya! Ita yake yiwa aiki. Babu wani shiri na rebecca da ba ta qulla hade da sadiq ba. Shi ke kawo mata labarin Almustapha. Shi ya gaya mata daidai lokacin da ya kamata ta shigo cikin rayuwarsa ta tarwatsa ta!

    Ya gaya mata zai ziga shi ya masa gadar zare har sai ya aureta, kuma da sannu za ta gano musu abinda Almustapha ya mallaka a hankali tana sato musu.

    Haka suka je aka yi test tabbas da nasa ne. Sadiq ne ya nemo malamai da shaidu kalilan aka daura wannan aure.

    Daurin auren da ya jawo aka fara yiwa matafiyan dauki dai dai!

    Tafiyar ta koma ta mutum biyar

    Almustapha
    Rebecca
    Rukky
    Hindu
    Luba

    Ba ayi mako guda ba, Aka kashe daya!

    Daya ya taka sawun barawo ya kare a gidan yari!

    Biyu suka qarke da sida!

    Daya saura shekaru goma cif.. ya sheqa barzahu!

    Tafiyar tana dauke ne da ban al’ajabi…irin ban al’ajabin da shallake tunanin mai tunani!

    MASU ƁUKATAR A TALLATA MUSU HAJOJINSU ZA SU IYA TUNTUƁARMU TA LAMBOBIN 07045308523 MUN GODE

    Note
    error: Content is protected !!