Search
You have no alerts.
    The Den of Novels
    Chapter Index

    ~TRUE LIFE STORY~

    *PAID BOOK*

    *AYSHA A BAGUDO*

    *MASU ƁUKATAR A TALLATA MUSU HAJOJINSU ZA SU IYA TUNTUƁARMU TA LAMBOBIN 07045308523 MUN GODE*

    …A matukar firgice ta farka daga nannauyen baccinta tana zaro idanuwa dafe da gefen fuskarta inda taji saukar mari “are you mad what are you doing ? ” yayi maganar a fusace yana zaro mata kyawawan idanunshi , take jikinta ya ɗauki rawa “uban wa yace kiyi changeover ?”

    “inna lillahi wa inna ilaihi rajiun ta shiga furtawa a zuciyarta tana maimaitawa kafin a hankali ta yunkura ta mike tsaye tana duban inda yake tsaye kikam hannunsa rike da yar saman suit d’insa, Kana kallonta zaka gane irin tashin hankalin da take ciki a lokacin, dan gabadaya fuskarta cike take da matsanancin tsoronsa , babu abinda take ganewa a tun sanda ta buɗe idanunta akanshi baya ga fuskarsa da kayan dake sanye ajikinsa ..”

    Take Jikinta ya sake ɗaukar rawa sakamakon irin kallon iskan da yake jifanta dashi , yayinda zuciyarta ke dokawa da matsanancin karfin gaske , da sauri ta durkushe a gabansa tare da haɗe hannuwanta duka “dan girman Allah kayi hakuri nasan nayi kuskure , karka dakeni nayi maka alkawarin bazan sake ba “..
    ya zuba mata kyawawan idanunshi kawai yana kallonta “kayi hakuri nasan cutar da kai na sakaka cikin damuwa nasan wannan kadai zai …….”
    “Shiiiii……..” ya d’aura yatsansa ɗaya akan lip’s d’insa ” karki sake na sake jin sound d’inki anan “kin jawowa kanki dan babu ruwana da wani banzar hakurinki dan sai jikinki ya gaya miki ya ajiye rigar hannunsa a kan kujera ya soma ƙoƙarin sunce belt din jikinsa ” shegiya har da wani cewa kar dakeki gaki yar gwal ko ?” zaki yadda zanyi dake gobe idan nace ga yadda nake son tsarin gidana haka zaki bi ,tana ganin ya kusan gama sunce belt din kugunsa ta kwasa aguje ta haye sama tana ihu dan tasan mai kwatarta a hannunsa sai Allah bayanta ya biyo taku uku yayi ya samu nasarar hard’e kafarta ɗaya ta fadi akan step , yasa kafarsa ya take mata kafafu ya shiga zuba mata belt tana ihun Kiran sunan iyayenta “wayyo Allah na shiga uku wallahi bazan sake ba ! bazan sake ba!! kayi hakuri bazan sake ba karka kasheni dan girman Allah ka maidani gida wallahi na hakura da aurenka jin haka yasa ya sake daddagewa ya lafta mata belt a tsakiyar bayanta wani gigitaccen qara ta saki tana dafe gadon bayanta tare da furta wallahi zan bi umarninka bazan sake ba “….

    “kima sake an faɗa miki wannan aliyu irin wanda kika sani ,wanda kika raina , wannan Aliyu ya wuce da tunanin dakikiya sakariya irinki , yana magana yana lafta mata belt tana ihu tana tarewa da hannunta sai daya lilis sannan ya barta yana haki ” Useless girl Kawai , idan kika sake min irin wannan ganganci zaki ga aikin ganganci dan daidai sisin kwabo bazan raga miki ..”

    yayi kwallo da kafafunta ya nufi d’akinsa ya buɗe ya shiga ya soma balballe botiran gaban rigarsa ya cire ya saura daga shi sai dogon wando da farin singlet ya rike kugunsa yana fifita da hannunsa kafin daga baya ya ɗauki remut ya kunna ac d’akin , karasa cire kayansa yayi ya shiga bayi yayi wanka ya fito ya sauya wasu kayan ligth blue jeans da riga dark blue ya fito yana takowa a hankali kamshin daddad’an turarensa na tashi, rakube ya ganta a gefen kujera ta mike kafafunta tana kallon jikinta daya shashin belt abinda tafi tsana kenan duka sam bata qaunar ganin shashin bulala ajikinta bare belt .

    “ki ɗauke min waɗan nan banzayen kafafun naki masu kama dana aljanu ,da sauri ta janye kafafunta jikinta na rawa “na ɗauke ” ta fada bakinta na rawa .
    “karki ɗauke kiga yadda zanyi kwallo dake , ya samu guri ya zauna akan kujera ,yana zama ana murd’a handle din kofar parlou’n tare da turo kofar ,nasir ne ya shigo tare da matarsa , d’agowa yayi ya kalli kofar , gani nasir ya gyara zama , yayinda matar nasir data shigo karshe ta maida kofar ta rufe ta k’arasa shigowa bakinta dauke da sallama .

    Fuskar nasir ɗauke da murmushi ya mikawa Aliyu hannu shima ya mika masa hannu suka gaisa “har kun karaso ?” nima ban ɗauka zamu karaso da wuri haka ba nasir ya kai bakinsa kunne Aliyu yayi masa rad’a yatsina fuska Aliyu yayi tare da cewa” Madam ki zauna mana kin tsaya tayi murmushi “ina yini uncle aliyu an dawo lafiya ya ka baro mutanen gida ?”

    “alhamdullahi kowa yana lafiya a tare suka zauna bayan kamar second biyu tace “ina amarya ayi min kiranta na ganta dan wannan zuwan nata ne sam hankalinta bai ga kisna dake ruku’be ba , shi kuwa aliyu wata uwar harara ya sakar mata yana cewa “,ke baki iya gaisuwa bane kina wani kallon mutane da wasu idanunki can ?”
    “am sorry , sannuku da zuwa Ina yinku ?” ta faɗa muryarta na rawa a hankali Aliyu yaja tsaki daga nasir har matarsa safiyya da ido suka bi kisna dashi ,shi kuma Aliyu yayi kwafa yana girgiza kai dan bai so suka isketa a parlou’n ba ,ɓacin ran abinda tayi masa yasa ya manta da batun zuwansu , mikewa Safiyya tayi ta k’arasa inda take zaune , ta durkusa a gabanta tana sake binta da kallo, gaba-daya sumar kanta ta hargitse fuskata kwance da ruwan hawaye sha’be Sha’be , ga jikinta duk ya tashi da alamun duka taci .
    ta kamo hannuta ta mikar daita tsaye ta nufi gun doguwar kujerar daita tana cewa “uncle aliyu … “
    shiru yayi mata kamar ba dashi take ba , ya shareta “mai ya samu kisna haka duk jikinta yayi rudu rudu kar dai laifi tayi maka ka mata duka irin haka ta fad’i haka ne saboda hirarsu data ji suna yi da mijinta “zan taho daita amman bazan d’aga mata kafa daidai dana second ɗaya ba kurkusre kaɗan duka ne da izaya kala dabam dabam”
    ” ita kuwa kisna shiru tayi qirjinta na dukan uku uku a hankali ta d’ago kanta shima ya d’ago kyawawan idanunsa idanunsu ya tsarke cikin juna ido cikin ido suke kallon juna , itace tayi saurin janye idanunta cikin nashi “haba uncle aliyu duk abinda kisna zata maka bai dace ka mata irin wannan dukan ba kalli jikinta fa tayi maganar kamar zata yi kuka tana nuna masa hannun kisna ,” ko karen gidanka banyi expecting zaka iya yiwa irin wannan hukuncin ba bare kisna da take da matsayi biyu a gurinka matakar kuma yar’uwarka , gaskiya banji dadi ba “.

    sake waigowa Aliyu yayi ya kalli kisna a daidai lokacin data sake d’ago kanta , kura masa ido tayi na zuwa wani lokaci sannan ta mike ta soma tafiya , da kyar take d’aga kafafunta ta shiga bayi tayi wanka tayi alwala dan la’asar ta kusa gashi ko azahar bata yi ba bayan tayi sallah kwanciya tayi akan gado ta lullu’be jikinta saboda zazzabin da jikinta ya ɗauka, gabad’aya hankalin Safiyya ya tashi zaman parlou’n ya gundireta kamar ta mike ta bi bayan kisna daki take ji , amman ta kasa, dan bata son yiwa rayuwarsa shishigi “

    “Uncle aliyu …..”
    Safiya ta sake kiran sunansa ,a natse ya d’ago yana kallonta batare da yace komai ba “dan girman Allah uncle aliyu zan nemi alfarma agurinka , karka sake dukan kisna zai fi kyau kayi mata wani punishment dabam idan tayi maka laifi ,amman tsarin duka sam bai yi ba ga macen aurenka “.
    “Dan baki san halin wannan makirar yarinyar bane shiyasa kike tausaya mata ,ki tambayi mijinki shi ai yasan komai wannan yarinyar da kike gani matsala ce arayuwa ta ,ta haifar min da matsaloli bila’adadi “.
    Safiyya ta kalli mijinta domin jin ƙarin bayani ganin yaki cewa komai ta sauke ajiyar zuciya “kina kallona dan kiji wani abu ,ba sai kinji komai ba , friend ka ƙara hakuri idan baka manta abinda ya faru a baya ba bazaka taɓa samun kwanciyar hankali ba, rayuwa duk yadda Allah ya rubuta babu wanda ya isa ya canza rayuwarku kaddara ce , a hankali ya dinga masa nasiha mai ratsa jiki sai kusan shida na yamma suka bar gidan zuciyar Safiyya cunkushe da bakinciki duk abinda mijinta ya faɗa bata dauki komai ba , ita dai tasan Aliyu ya taho da diyar mutane ne ɗan kawai ya cutar daita “.a mota tsokano maganar ta dinga yi dan nasir ya faɗa mata abinda ya faru tsakanin kisna da Aliyu amman yaki ,dan baya son tasan komai dangane da rayuwar Aliyu , ganin haka ta kudurta a ranta zata dawo musamman domin taji komai abakin kisna”

    Ranar haka kisna ta kasance da zazzaɓi , ko falon bata sake fitowa ba , ya shigo d’akin kallo ɗaya yayi mata ya fahimci zazzaɓi ne ke d’awainiyya daita “kin shigo daki dan bakin munafurci kin boye ,to ki buɗe kunnuwanki da kyau , duk abinda kika san nawa ne acikin gidan karki yi ganganci ta’bawa idan ba haka ba wallahi wallahi ……”
    qarar wayarsa ce ta katseshi ya ɗauka ya juya ya fita daga d’akin kunneshi manne da wayar har ya fita bata san ya fita ba wani sabon tashin hankali da faduwar gaba da wani irin tsoronsa ne suka d’arsu a zuciyarta “yanzu irin rayuwar da zata yi kenan “?
    “a she Aliyu bai san darajan dan adam ba kamar yadda tai tsammanin ? ” mutumin da kullum take wa kallon yafi kowani ɗan adam kirki da nagarta a duniya shine yau yake kokarin kasheta da ranta ta share hawayen daya wanke mata fuska ta tashi ta soma haɗa kayanta a jaka tana cikin zubawa cikin jakarta ya shigo sai da gabanta yayi wani mumnunar faduwa da ganinsa , da sauri tayi jefa da kayan da yake hannunta sakamakon kallon da yayi mata ta matsa baya da sauri “kashina ya bushe ta furta hakan a kasan ranta ” cikin matsananci mamaki yake kallonta “a kwana biyu kacal har ta gaji dashi ya furta a ransa dariyar mugunta na kokarin subuce masa yayi saurin had’iyewa yana watsa mata harara, tausayin kanta ya ka mata “a kwana biyu kacal har kin gaji da aliyunki kin soma nemanwa kanki mafuta ba ?”

    “haba yarinya har yaushe daren yayi? “ai yanzu aka fara buga wasan ,ina irin naki wasan yake ?”yayi magana yana tsareta da idanushi tare da tsuke ƙaramin bakinsa “Okay a she fa yanzu son Aliyu ake baza’a iya aikata komai ba , amman zan so ki fito da salon iskanci da kika iya kala kala sai mu buga wasan mugani cikin ni dake waye zai yi nasara “.

    “babu abinda zanyi har kullum hakuri zan cigaba da baka saboda nasan …… ” yi min shiru munafukar Allah kawai hakurin ubanki zaki cigada da bani ? tayi saurin girgiza masa kai jikinta na rawa wallahi kika sake bude wannan rubabben bakin naki da zumar bani hakuri sai Kin dawo ball a gidan nan , dan na dinga kwallo da kanki kenan har sai kin mutu ..”Tsit tayi tare da sunkuyar da kanta kasa tana sauke numfashi ,”mai mugun hali kawai ya fada yana fad’awa saman gadon ya talla’be kanshi da hannunwansa duka ya runtse idanunshi gam yana jan dogon tsaki …”

    Tun daga rana bata sake samun canji rayuwa daga Aliyu ba, tsananin yafi na wanda take ciki , kuskure kaɗan duka da zagi ga azabar yunwar da yake mata, sai ya fita tun safe ya barta babu abinci , sai idan ta roki mai gadi ya taimaka mata dashi a rana sau daya take cin abinci , kafin kace me ta zabge tayi wata ƙatuwar rama sai dogon hanci da wuya ,a qalla sai datayi sati biyu a kasar , sannan wata ranar lahadi yace ta shirya dan shiga kasuwa shima darajan nasir taci if not haka zai barta tayi rayuwar yunwa daga karshe ta mutu ya huta ..

    yana zaune cikin motarsa kiran beaz 330 hannuwansa akan stearing , ganinsa cikin mota ya hana escout dinsa harama biyosa dan duk sanda yayi haka baya nufin yana da bukatar rakiyarsu , ta fito jikinta sanye cikin doguwar riga marun colour har kasa mai zanen fulawa milk colour tun daga wuyar rigar har zuwa shashin dukiyar fulaninta ,rigar tayi mata kyau sosai ,kafafunta sanye cikin flat shoe masu matukar kyau , babu kwalliya a fuskarta sai powder data dan shafa, ta shafawa lip’s d’inta Whit lipstick
    duk da ta rame sai dai hakan bai hana kyawun da Allah yayi mata fitowa ba ,ta fito haraban gidan tana taku a natse kamar koda yaushe ta bude murfin mota ta shiga cikin dari dari ta zauna batare da ta sa seatbelt ba , ya murza stearing din motar , take mai gadi ya bude musu makeken get din gidan suka fita .

    a hankali motar ke gudu akan titi ta ɗan juyo inda yake ta kallesa yayi kyau sosai , komai nashi irin nasu aryan ne babu abinda suka bari nasa , ya ɗan juyo ya kalleta ya ɗauke idanunshi yana jan tsaki “mayya kawai ji yadda ta kurawa mutu ido kamar zata cinye mutu ,burki yaja aiko gabad’aya ta gigice ta zubo jikinsa dole yasa ya tsaya ba dan ya shiryawa hakan ba yana kallonta , a fusace yace “kina hauka ne ,ki sanya seatbelt mana “am sorry ta fada tare da janyo seatbelt ta sanya tana kallon wani bangare “komai yayi kyau yake masa zan cigaba da hakuri da kai nasan wata rana zaka sauko ka soni ?”
    Duk wani abun bukata a gida bangaren abinci babu wanda bai siyo ba sai daya cika bayan Boot d’insa sannan suka ɗauki hanyar dawowa gida , akan hanyarsu tace “ina bukatar waya da sabon layi ina son nayi waya da mummy “.
    banza yayi mata cikin haka taga wani guri da’ake siyar da waya da layin waya tace “yauwa dan Allah ka tsaya ka siya min , ya tsayar da motar kamar abun arziki yana gama tsayar da motar ya sauke mata yatsunsa biyar a fuskarta “shiga hankalinki baki isa kisani yin abinda banyi niyya ba, duk abinda kika ga nayi na gadama ne wawiya mara kamun kai kawai , kina wani hauka kamar tinkiya , ke din da bakowa bace , ba matsayi gareki a zuciyata ba ,dake da jaka daya kuke agurina , ya kai hannunsa ya murza stearing ya cigaba da tuki har suka karaso gida kuka take kamar wacce akace uwarta da ubanta sun mutu yana gama daidai tsayuwar motarsa ya bude boot ya fito ya shige ciki abunsa ya barta ..

    yana zaune a parlou’n ta shigo fuskarta tayi jajur kwayar idanunta sunyi luhu luhu sun kod’e har ta kusan gifta shi ya hard’e kafarta tayi kasa luuuuuuuu zata faɗo jikinsa , bai san yadda akayi ya tarota ba aikuwa hannuwansa duka suka sauka akan dukiyar fulaninta wani irin shock yaji a gabad’aya jikinsa , idanuwanta ta tsura masa tana kallonsa a tsorace , hakan yasa yayi saurin cire hannunsa “ya’akayi hannuna ya kai jikinki “?
    yayi maganar cikin ɓacin rai zuciyarsa na wani iri zafi ,mikewa tsaye yayi jikinsa na rawa yana mata wani irin kaskantacce kallo mai razana duk wanda aka yiwa shi “ba tambayarki nayi ba kika min shiru” ya’akayi hanuna ya kai wannan banzar jikin naki “wallahi ban bansani ba nasan dai san zaka taimaka min ne hakan ta faru “

    “meye shi hakan ya faru yanzu ? tayi saurin girgiza masa kai idanunta na ciccikowa da ruwan hawaye ta samu guri zata zauna” uban wa zai kwaso miki kayan ?” ta kalleshi da sauri hawaye na zubo mata . “oh kina tunanin ni ne zan shigo miki da kayan bayan naje nayi wahala na siyo da kudina ?”
    “bance ka shigo dashi ba amman dan Allah ka bawa mai gadi umarni ya shigo dashi jikina ciwo yake “ubanki da ciwon jiki dan Allah malama tashi kije ki kwaso ,” sai na maidake kaskantacciyar baiwa a gidan nan , duk wata babbudewa da cikar iskar da kike takama dashi sai na sauke miki shi ,ya zira hannunsa cikin aljihun wandonsa ya zaro wayarsa ya soma danne danne …. ….”

    Juyawa tayi jiki a matukar sanyaye ta koma haraban gidan ta k’arasa bayan motar ta buɗe ta soma fito da caton din monster fury energy, lamunsa ne yana bala’in son shi ya kusan carton goma , ta fito dashi ta kai kitchen ta dawo ta ɗauki carton din ruwa shima guda goma ,sai kayayyakin amfani shikafa manja mangyada da dai sauransu , gabad’aya ta haɗa gumi tana cikin aikin Safiyya ta shigo gidan da sauri ta karaso gareta , ta dafa kafad’unta a tsorace ta juyo ganin Safiyya ta sauke naunauyen ajiyar zuciya tana fad’ad’a fuskarta da murmushi “
    a she kice ?” ta gyada mata kai “,abinda zaki saka mai gadi ya shigar miki dashi shine kike yi da kanki ,”kai ai babu komai zan iya ai ne shiyasa “zaki iya ko wannan mugun mijin naki ya sakaki , kalli idanunki kamar ma duka yayi miki , kai bama kamar bane marinki yayi ko? “
    “Karki damu dani plz mu shiga ciki ta ɗauki wani kwali guda biyu muje ko “bari na tayaki safiya ta ɗauki wani kwali tare suka shiga parlou’n basu iske Aliyu ba ya hau sama tare suka kwashe kaya sannan ta tayata ajiye komai a mazauninsa ,suna aikin Safiyya na zargin Aliyu”Allah yana sama yana kallon abinda Aliyu yake miki shi zai kwatar miki hakinki ,kuma inshallahu nan ba dadewa ba sai ya girbi abinda ya shuka ,mugu azalumi kawai ,kisna tayi dariya tace ayya Safiyya ki daina fadar haka babu abinda zai sameshi inshallahu , mijina mutumin kirki ne wallahi wannan abinda ya faru a tsakaninmu ki ɗauka qaddarata ce haka , tayi tsaki “lallai yanzu har wani yabonsa kike ? “To ai bashi da laifi wallahi, bana ganin laifinsa hasalima zuciyata sake qaunarsa take “tab gaskiya zuciyarki bata miki adalci ba ” ……

    Har kusan shida Aliyu bai sauko ba, tare da Safiyya suka da dafa soyayyiyar taliya wacce taji salad garbage da carote da soyayyen nama kaza sai dataci sannan tayi mata sallama ta wuce.

    bayan safiyya ta wuce ya sauko yana mika haɗe da salati ,ko kallon inda take bai yi ba , ya zauna ya dauki remut ya kunna tv ya janyo jakarsa ya fito da computer d’insa ya kunna ya soma duba sakonnin mutanen dake kaunarsa wasu yayi maida martani wasu kuma ya wuce , ganin haka yasa ta mike ta shiga kitchen ta dauko kular data zuba masa abincinsa , ta daura a tire da ruwa da fury ta dauko ta fito , ta ajiye akan table din da computer dinsa ke kai.

    ya d’ago kyawawan idanunshi ya zuba mata yana kallonta, murumushi tayi masa mai narkar da zuciya tamkar ba ita ce ta gama cin azaba a hannunsa ba dumple d’inta ya lotsa hakan yasa ta ƙara kyau “kaci abinci sannan ka cigaba da aikin “baza’a ci ba , ki ɗauke abincinki yanzu kafin nayi miki rashin mutunci “dan Allah ni da kaci idan ka gama ci sai ka min rashin mutunci ,kalli yadda ka rame kaima, kaki kwantar da hankalinka kaci abinci mai nauyi kullum daga cake sai snaks ….”

    Ai ko gama rufe bakinta bata yi ba taji gabad’aya kular abinci ajikinta , a firgice take kallonsa tana kakkabe abincin , duk jikinta ya baci da taliya cigaba kakkabe jikinta tai Allah yasa abinci ya ɗan sanyi “bana bukatar komai daga gareki ke ce mayar abinci gashin nan kiyita fama , duk ranar da kika sake min tayi abinciki da bai dadi ,dan nasa ba iyawa kika yi ba , yawon gantali bai bari an tsaya an koya ba , sai na kasheki da duka stupid Kawai mai kama da siffar maciji “…

    “duk yawon gantalina dai da darajata ka ……..”
    Saurin katse maganarta tayi ta kwasa aguje saboda ƙoƙarin mikewa da yayi “da ki tsaya mana kiga yadda zanyi dake ƙaramar mara kunya ? “Kuma wallahi ki dawo ki gyara gurin nan minti goma kacal na baki ,ya dauki computersa ya fita zuwa haraban gidan ya buɗe motarsa ya shiga ya cigaba da aikinsa ….

    Bayan ta gama aikin gyara garin daya abinci ya ‘bata d’aki ta koma tayi wanka ta sako wata doguwar riga milk colour kusan yanayinsu daya data safe data saka sai dai ita wannan mai karamin hannu ce ,kuma shara shara dan kana iya hango jikinta bata d’aure gashin kanta ba tabarshi ya zubo gadon bayanta ta koma parlou’n ta tsurawa tv ido wanda a zahiri ba kallon take ba hankalinta na gareshi ,
    bai shigo parlou’n ba sai bayan isha’i , ɗauke kanshi yayi ya hayewarsa sama ,yau ma bacci suka yi kamar yadda suka saba, tana kan gado yana kan kujera yayinda baccin nata ya kasance rabi da rabi tana yi tana buɗe idanunta akan shi ,shi kuwa tsakaninaa da Allah yake sharar baccinsa sai tayi kamar ta sauko ta kwanta ajikinsa sai zuciyarta ta gargadeta a haka har bacci bawon yayi awon gaba daita..”

    *****
    Washegari

    Tsaye yake a gaban dress mirrow ,jikinsa sanye da rigar wanka yayinda hannunsa ke rike da towel , ya cire rigar wanka ya goge sumar kanshi da fuskarshi yabi jikinsa da lotion sannan ya feshe jikinsa da turaruka masu sanyi kanshi ya tsuke cikin suit baki masu matukar da tsada , ya da’ura agogon dimond a tsintsiyar hannunsa ,ya dauki culmb ya gyara sumar kanshi ,yana ƙoƙarin ɗaukar briefcase dinsa ta shigo d’akin tana rausaya wanda ya zame mata jiki dan idan basaninta kayi tun asali ba ,zaka ɗauka yanga take ,wata hadaddiyar riga ce har kasa ajikinta rigar tayi matukar yi mata kyau sosai kamar dan ita akayi , abunka ga farar mace sai rigar ta haskakata sai kamshi take zubawa ” fuskarta ɗauke da murmushi tace amincin Allah ya tabbata a gareka mijina barka da Safiyya ,ina ta sauri nazo na shiryaka shine har ka shirya ko ? ” ta fad’i hakan tana kallonsa tabe baki yayi yana jan dogon tsaki yana tare da d’aga mata hannu yana mata gargadi sannan ya maida hankalinsa ga kofo ta kai hannu zata amshi briefcase din hannunsa “bana bukatar hauka plz yabi gefenta zai wuce , tabi bayansa da kallo “kaɗan kadan dai tunda ka sauke ra’ayin barin wutan lantarki a kunne ka siyo kayan abinci yau gashi ka manta baka kulle kofa ba wata rana zaka canza tana cikin zance zuci ya dawo d’akin , gyaran murya taji har ta tsorata “, dauki abinda zaki ɗauka zan kulle d’akina …..”

    Domin bukatar karanta novel dina kyauta a sauke manhajar Aysha a bagudo ta hanyar shiga wannan link din dake kasa* 👇🏻
    https://play.google.com/store/apps/details?id=aysha.a.bagudo.all.books.pro

    Mmn sudaus
    💗💗💗💗💗💗
    CUTAR DA KAI
    💖💖💖💖
    💗💗💗💗💗💗

    ~TRUE LIFE STORY~

    Note
    error: Content is protected !!