Search
You have no alerts.
    The Den of Novels
    Chapter Index

    *PAID BOOK*

    *AYSHA A BAGUDO*

    *MASU ƁUKATAR A TALLATA MUSU HAJOJINSU ZA SU IYA TUNTUƁARMU TA LAMBOBIN 07045308523 MUN GODE*

    Yayi saurin toshe mata baki da hannunsa yana zaro mata ido “kina hauka ne salon kisa yara su farka su ɗauka wani mugun abu nake miki “? Wani irin harbawa zuciyarta tayi a sanda ta jita kwance a saman faffad’an qirjinsa dake kwance da laulausan gashi , hannunsa ta cire tare da marairaice murya kamar zatayi kuka tace “to ai kaine kasani ihun”.yaja tsaki yana furzar da iska mai zafi “zaki iya yin komai dan ki kusanta kanki dani ya fada yana harararta haɗe da zareta a jikinsa dan kusancin da suka samu ya soma canza yanayinsa zuwa wanda baya so a tsakaninsu , mikewa tayi tana d’aga kafafuwanta da kyar, madadin ta kwanta sai ta fita a d’akin taje tayiwa mumy sai da safe bata jima ba ta dawo ta nufi gurin shimfid’anta ta kwanta taja bargo ta lullu’be rabin jikinta ta zuba masa narkakkun idanunta tana jin kamar ta fixgoshi jikinta su kwanta tare .”

    a natse ya maida idanunsa kan aikinsa yana yi yana hamma da zarar taga zai kallo inda take sai tayi saurin runtse idanunta , ta ɗan bude idonta daya taga ya mike ya dauki plet din data shigo masa dashi ya ajiye akan table ya koma ya zauna yana aiki yana ci tun tana jiran taga tashinsa a aiki har bacci yayi nasarar d’aukarta , misalin karfe biyu na dare ta farka taga yayi bacci ga system dinsa a bude ta mike tsam ta isa inda yake ta rufe masa system din tare da ajiyewa akan table ta kamoshi ta kwantar dashi akan kujerar sosai dan kar jikinsa yayi ciwo , tana kokarin zare hannunta ya farka idanunshi akanta “me kike ƙoƙarin yi ?

    “Uhmmm ammmmm babu komai naga kayi bacci ne shine nayi tunanin “kika yi tunanin me “?yayi mata tambayar cikin tsananin ɓacin rai “Wai ke dan Allah mai yasa baki da kai sai na daukar kaya bance kar hannunki ko wani sashi na jikinki ya gogi nawa ba “? Muryarta a sanyaye tace “Kayi hakuri inshallahu na daina “Kina da bala’i shishigi da takura wallahi ,ki daina ‘bata lokacinki akan Aliyu , yana gama fadar haka ya soma ƙoƙarin mike wa tsaye ” dan Allah malama ki bani hanya na wuce ya karasa maganar yana harararta da sauri ta matsa ta bashi hanya tana kallon bayansa .”

    Cike da jarumta tace “ko bata lokacin nayi akanka ya Aliyu daidai ne bare ni nasan ba batawa kaina lokaci nake ba,dan na kasance tare da kai zanyi duk abinda ya dace ,kuma nasan yadda nake mutuwar sonka kaima kana mutuwar sona kawai kana takura zuciyarka ne bisa wani dalili naka bancin haka da an ga haukan soyayya a gurinka ………..”

    cak ya tsaya ya kasa cigaba da d’aga kafafunsa “ya Aliyu i love you more than word’s a hankali ya juyo da idanunshi dake cike da mayen bacci ya tsura mata yaji kamar ya ɗauketa da mahaukacin mari tsabar takaicin abinda tace a natse yayi taku biyu ya tsaya a gabanta har lokacin kwayan idanunshi na kanta , gabanta ne ya shiga dokawa da sauri da sauri saboda tsoro da fargaban abinda zai aikata mata “kinsan wani abu ? tayi saurin girgiza masa kai zuciyarta na wani irin tsalle “wallahi wannan abun kunya kike aikatawa kanki kar ma ki bari wani kunnen yaji wannan kalmar a bakinki “babu komai barni na cigaba da aikata abun kunya nifa a halin yanzu bana fahimtar komai sai yadda nake sonka “.wani dogon tsaki yaja tare da juyawa ya hau saman gado ya kwanta kusa da yaransa ya janyo bargon data lullubesu dashi ya rufe rabin jikinsa ta zauna akan kujerar daya tashi ta zuba tagumi tana cigaba da kallonsa ,ta rasa yadda zatayi da rayuwarta ,bata san me Aliyu yake son tayi masa ba duk abinda tayi bata burgeshi ,komai tayi masa daga hantara sai zagi da harara “ya Allah ka duba halin da nake ciki kasa mijina ya fahimceni “zaman me kike ki tashi kije kiyi alwala ki kaiwa Allah kukanki mana wankakkiyar zuciyarta ta sanar daita zumbur ta mike ta shiga bayi ta d’auro alwala tazo tayi raka goma da wutiri byn ta sallame ta zauna tana addu’a akan Allah ya karkato mata da hankalin mijinta Ta dade zaune tana kaiwa Allah kukanta sannan ta mike ta nad’e sallaya dan lokacin sallar asuba da saura madadin ta koma ta kwanta a kasa sai ta koma dayan bangaren da yaran ke kwance ta kwanta suka sa yaran a tsakiya ita da Aliyu ,ta kashe wutar dakin ta kunna mara haske ta kai hannuta tana shafa kan areef dake kusa daita a hankali bacci yayi awon gaba daita ….”

    Kiran sallahr karshe ne ya tada ita ta bude idanunta a hankali tana mika haɗe da sallati ta kunna wutar dakin ta tsura masa ido yana kwance sai faman sauke numfashi yake , yayinda hannunsa daya ke rungume da yaransa matsowa tayi ta kai hannunta ta shafa gefen fuskarshi tana lumshe ido fuskarta dauke da murmushin jin dadi ,duk da yana kinta amman baya kin ya’yan data haifa masa wannan kadai ma wani alfarma ce daga Allah, a kullum bazata daina godiya ga Allah da aunty Zainab ba bancin ita data hanata cire cikinsu a wancan lokaci daya yanzu matsaloli sun mamaye rayuwarta ,saukowa tayi ta shiga bayi ta dauro alwala ta fito ta gabatar da sallah ,a natse take yin komai dan karsu aryan farka su tashi babansu ..”

    Karfe bakwai saura ta shiga Kitchen dan hada musu break fast, tana kitchen tana aiki ta jiyo motsin saukowarsu suna wasa da magana da juna daman kuma haka suke suna son wasa akan step ko akan karfen step su hau suna lilo a hankali ta liko tace “maza ku koma dakin mumy ku kwanta , gabad’ayasu suka tsaya suna kallonta suna mata dariya “bazaku koma ba tayi maganar tana kokarin fitowa suka kwasa a guje suna dariya “areef ga momy na zuwa zo mu gudu.” tayi saurin dafe qirjinta “kubi a hankali dan Allah karku fadi ,ta biyosu sama ta shiga dakin mumy taga basa ciki dan haka ta nufi dakinsu ta iske su kwance a bayan Aliyu suna faman kyalkyale dariya.”

    tayi saurin kama bakinta tare da daukar areef ta sauko dashi aryan na ganin haka ya makalkale Aliyu yana dariya “zo nan aryan ku kwanta anan karku tashi papa daga bacci yayi aiki jiya ya gaji sosai yana bukatar bacci juyi duniya tayi da dabaru dan su koma bacci amman suka ki dole ta koma dasu kasa ta cigaba da hada breakfast sun so su makale mata a kitchen taki yarda tace su tsaya a parloun dan suna da mugun wasa sosai ,a parlou’n ma tana aiki tana lekosu ..”

    Basu dade da barin dakin ba Aliyu ya tashi dan duk abinda suke yana jinsu , sallah yayi ya koma karfe tara daidai ta kammala da komai ta shirya dining table ta kamo hannun yaranta suka nufi dakin momy anan tayi musu wanka ta shiryasu cikin wasu had’ad’d’un kaya sabbin riga light green da wando blue black “aryan ya kalleta yana murmushi yace momy I love this clothes are you the one brought it for us or grandma “?
    “No it’s grandma brought it say thanks to her ya washe baki yana kallon mumy dake zaune tana bare tafarnuwa yace “thanks you grandma kisna ta karasa shiryarsa yazo ya tsuguna a gaban mumy yana surutu irin nasu na yara tare da ƙoƙarin ɗaukar tafarnuwa,mumy tayi saurin rike masa hannu tana cewa “uhmmm aryan ,kisna ta kamo areef yayinda aryan ya haye saman gado ya rungume mumy ta bayanta ” I love you so much grandma tayi murmushin jin dadi “love more my boy tana tsananin qaunarsu akan sauran jikokinta ,amman tasan hakan bai rasa nasaba da kasancewarsu ya’yan Aliyu da kisna ba ..”

    Aryan ya mike ya tsaya a tsakiyar katifa ya kalli areef yana murmushi yace “mommy kayan sunfi min kyau akan areef ko ? aiko take areef ya sa kuka , kisna ta rungumoshi rabu dashi world best kaima sun maka kyau sosai kamar dan kai akayisu sai da ta gama dasu sannan ta nufi d’akinta , koda ta shiga Aliyu baya dakin jin motsin saukar ruwa yasa ta fahimci wanka yake dan haka ta soma gyara dakin ta feshe ko’ina da turare yana fitowa ta fada bathorrom tayi wanka ta fito ta tsaya gaban madubi tana goge jikinta da karamin towel ita cinyarta yayinda rabin dukiyar Fulaninta suka bayyana , wani irin duba yayi mata sama da kasa sannan ya ɗauke idanunshi akanta ya soma daura agogo a tsintsiyar hannunsa.
    Muryarsa a tsarke yace “karki sake fitowa daga ke sai towel idan ina guri”.wani kalar juyowa tayi tana masa wani irin kallo mai cike da takaici da mamaki wanda kaɗan ya rage towel din jikinta ya subuce tayi saurin kamoshi gam ta rike , iya towel ma yayi complain ina ga jikinta ya bayyana ai sai dai taji saukan duka ko mari da fada mata bakaken maganganu”.

    “hope kinji abinda nace bana son ganinki d’aure da towel idan ina guri bana son karuwanci dan kin wani tsareni da ido kina kallona kamar mayya idan kuma bazaki yi abinda nace bane na sani “.saurin girgiza masa kai tayi tare da cewa “zanyi .”
    ya sa kai ya fita zuwa dakin mommy ita kuma ta gaugauta goge jikinta ta sanya kaya ta fito ta shiga dakin mommy ta zauna kusa dashi akan kujera ,areef na zaune akan ciyarsa yayinda aryan ke tsaye a bayansa yana ƙoƙarin hawa wuyansa mommy ta Kallesu sun burgeta sosai ,sun dace da junansu , bata taɓa ganin halittar da suka dace da juna ba kamar Aliyu da kisna ko dan kamar da suke da juna ne batasani ba ,a ranta ta dinga masu addu’ar akan Allah ya zaunar dasu lafiya ,kisna ta dubeta “mommy abinci fa yayi ready “to kisna sannu da ƙoƙari Allah yayiwa rayuwa albarka amman gaskiya kinyi sauri kammalawa , haka ake so bari na fito.
    “Ki bari a kawo miki nan mana ba sai kin sha wahalar saukowa ba saboda kafafunki inji cewar Aliyu, “haka ne amman dai muje kasan gabad’aya zai fi ya dauki areef ya sabashi a kafad’ansa aryan na rike a hannunsa suka fito . “

    Mommy ce ta soma yin gaba sannan suka biyota a baya kisna na kokarin jerawa dashi ya dakatar daita muryarsa can kasa ta yadda mommy bazataji ba “karki sake ki jera dani bana bukata “.aryan najin abinda yace yayi saurin saki hannunsa ya rike na kisna muryarta a sanyaye tace “Okya babu matsala idan da hali ka kira su ya Samir a waya suzo suyi break fast banza yayi mata kamar bai ji abinda tace ba ,Suna saukowa parloun Samir da aunty zee suka shigo aunty zee ta karasa gaban mommy ta durkusa har kasa cike da girmamawa “mommy Ina kwana kin tashi lafiya”?

    Mumy tayi murmushi tace “Lafiya lau zainab ya kika tashi ya gajiya? “alhamdulillahi mommy ta fada tana mike wa tsaye tare da mikawa kisna hannu “ya’akayi autar momy kinyi kyau fa sosai “na gode aunty zee Ina kwana suka gaisa cike da kulawa, Aliyu ya mikawa Samir hannu suka gaisa ya dauki aryan ya daga shi sama “wooooowwww my dad you look so beautiful ,aryan ya wangale masa baki yana kyalkyale dariya dan yana son yaji an ce masa yayi kyau ,zama sukayi akan dinning kisna tayi saving dinsu tare ajiyewa kowanensu plet a gabansa da ruwan tea Mai kauri sannan ta zubawa Aliyu nashi ta zagayo inda yake ta ajiye masa ,
    ta zauna a kusa dashi ji yayi kamar ya tashi ya canza gurin zama amman babu dama gashi yana jin idanun mumy ajikinsa , spoon ya dauka ya dinga feeding din yaransa batare daya ci abincin ba sai daga karshe ya curbi tea kadan …”

    Bayan sun gana break suka dawo kan kujera nan hira ta barke mommy tace kisna ta d’auko babba jakar dake ƙarƙashin step wanda suka zo dashi tsaraban kisna ne acikin makil ,kisna ta mike ta janyo jakar ta bude had’ad’d’un kaya ta gani atamfofi da lace duk a dinke kusan kala goma ta soma d’agawa daya bayan daya tana murmushin jin dadi duk wannan kayan nawa ne mumy ? “Naki ne ke kadai mamana “.

    kisna ta daga wani lace guda biyu wanda akalla kudinsu zai kai dubu dari dari tace” kai mommy wannan lace din sun min kyau sosai wallahi duk sunfi shiga raina murmushi mumy tayi “tana tuna yadda aka yi ta samu kayan Alhaji realwan ne ya siyo mata a wata tafiyar da yayi zuwa kasar hollond ” ya kika ga kayan nan uwar marayu da yake haka yake kiranta dashi ? “gaskiya sunyi kyau sosai dady ,”shiyasa na siyo miki dan nasan zasu miki kyau ,ta sake kallon kaya sosai “gaskiya sunyi kyau amman zasu fi yiwa kisna kyau akaina kuma zata so kalarsa gaskiya ita ma zanbawasu sun shiga cikin tsarabanta “what na siyo miki abu kice wata kisna wacece haka “? yayi maganar yana bata rai .”Mutun ce ita zanbawa kuma bana son ka sake cewa komai ni ka siyowa ni kuma na bawa diyata shikenan ” shiru yayi bai sake cewa komai ba har ta bar dakin..”

    “Momy na gode sosai me dady ya bayar ki kawo min “bai bayar da komai ba ya ce idan zan dawo ki faɗa min abinda kike bukata idan na koma na faɗa masa zai aiko miki ta fadi haka dan ta kwantar mata da hankali amman a zahiri cewa yayi bai da abinda zai bada a kawo mata dan har yanzu bai gama yarda daita ba .
    “okay mumy zanyi tunani ta kwashe kayan ta kai su d’akinta ta jera cikin wardrobe ta dawo suka ci-gaba da hira har rana tayi suka shiga Kitchen tare da aunty zee ,”me zamu dafa ne kisna “?

    Kisna ta rausayar da kwayar idanunta sannan tace “mu dafa predrice da coslow saboda ya Aliyu zai so . …”
    “Lallai kisna kina shagwa’ba muradi dayawa fa shiyasa gashi nan yayi bulbu ke kuma duk kin zuke sam na lura mumy bata ji dadin ganinki haka ba “ajiyar zuciya kisna ta sauke da karfi tace ” wallahi kamar kinsani dan har sai da tayi magana amman na fada mata babu komai “Allah yasa babu din to ko ciki gareki ne ?Kisna tayi murmushi har dumple d’inta na lobawa tace “kai aunty zee ciki fa …”?
    “Kai aunty ko gaskiya tunda nasan muradi shapshuter ne nan da nan yayi ajiya a mararki dariya suka kwashe dashi gbdy sannan suka fara aikinsu suna tsaka da aiki Samir ya shigo kitchen hannunsa rike da farar leda aunty zee ta kalleshi tace “me muka samu ne ranka ya dade ? Cikin jin dadi ya gyara tsayuwarsa yana cewa “Kayan dadin da gimbiyar muradi ta kawowa mumy ne shine na dauko leda daya na kawo muku “Gabadaya kisna ta maida hankalinta da natsuwarta kan Samir qirjinta na wani irin dokawa da matsanancin karfin gaske ” wace irin mata ce wannan wato sai data sake dawowa gidan nan ? Bata gama tunani ba ta sake jin muryar ya Samir “yarinyar nan fa tana mutuwar son Aliyu kinga yadda take wa mumy kamar zata yi mata sujjada dan ladabi abun ya burgeni sosai shiyasa nace mata idan akwai ta aure a gidansu ta gaugauta sanar min ya karasa maganar yana nuna aunty zee da baki alamun tsokanar , take aunty zee ta sakar masa hararan wasa ya shigo cikin kitchen din sosai ya ajiye laidar hannunsa ya tsaya a bayan aunty zee Kamar zai shige jikinta “gimbiya Ki amince min mana na sake shiga daga ciki kamar yadda dan’uwana zai yi ?
    shiru dukkaninsu sukayi kafin daga bisani tace “ai zuciyarka bazata iya son Abu biyu ba bare soyayya , shi kansa d’anuwan naka zuciyarsa mace daya take so ya dai ki yarda da hakan ne amman nasan da sannu zai fahimci haka idan lokaci yayi..”

    numfashi Samir ya sauke ya ɗan saci kallon kisna dake aikinta ganin kamar bata damu da maganar ba yace “muje ku gaisa da ita ko ? ya fada yana barin kitchen din ,aunty zee ta kalli kisna “muje ko “
    ” gaskiya bazani ko’ina ba kije kawai duk yadda kisna taso kin zuwa amman aunty zee tace dole sai sun suje , a durkushe suka isketa a gaban mumy kanta a kasa tana rike da hannu aryan tana kokarin kamo hannun areef yaki yarda daita daman kuma shi muguwar kiyuwa garesa baya yarda da kowa sai yan gidansu …
    Nawal na ganinsu ta sake fad’ad’a fuskarta da murmushi ta maida hankalinta sosai a kan aunty zee tace “aunty zee sannuku da zuwa kun zo lafiya ya kuka baro mutanen gida ?
    “Alhamdulillah aunty zee ta amsa mata atakaice ,nawal ta ɗan saci kallon kisna wacce gabad’aya yanayinta ya sauya sam bazaka ce ta taɓa dariya ba ,yanayin fuskarta yasa gaban nawal ya dinga faduwa amman ta sanyawa jikinta jarumta tace maman twins ina wuni ?
    Sai da kisna ta gama shan kamshinta dan har nawal da Aliyu sun fidda rai zata amsa suka ji sautin zazzakar muryarta “lafiya ” atakaice .
    shiru dukkaninsu sukayi ,daga kisna har nawal babu wacce numfashinta bai fita da matsanancin sauri ,wani irin kishin Aliyu ne ya mamaye zuciyar kisna ,duk da a yanzu tafi kowa maraba da shigowar nawal gidanta a matsayin kishiya ta huta da wasu daga cikin iskanci Aliyu amman wani lokaci sai taji kamar ta kashe nawal din akan tsananin kishin mijinta dan Allah ne kaɗai yasan irin ciwo da rad’ad’in da take ji a zuciyarta a duk sanda ta tuna da aurensu , sai dai tana kokarin danne kishinta saboda bata son zubarwa Kanta da mutunci a idanun nawal din da Kuma idanun duniya dan ta lura da tsoronta dake tattare da zuciyar nawal din kuma tasan hakan bai rasa nasaba da kashedin data mata a wancan ranar ba , ita kuwa nawal gbdy jinta tayi duk a takure a gurin , mikewa tayi cikin sanyi jiki tayiwa mumy sallama ta wuce zuciyarta cike da matsanancin tsoron kisna , Aliyu ya so bita sai dai kunyar mumy yasa ya kasa Binta suka ci-gaba da hira da mumy da zumar anjima zashi gurinta ,yayinda kisna da aunty zee suka koma kitchen ..

    “Kinji wani sabon salo kiran sallah da husir wai aunty zee a bakin guzuma abun ma babu dadin ji aunty zee ta karashe maganar tana kwashewa da dariya “ai naga yadda kika shaka dan gaisuwar ma da kyar kika amsa kisna ta fada tana dariyar mugunta “ba dole na bata rai ba mata ta girmeni nesa ba kusa ba amman ta bige da ce min wani aunty kinji kuwa yadda raina ya ɓaci ,dan wallahi ko shi ya Aliyu a girme zata iya girmansa idan kuwa bata girmesa ba zasuyi daidai daita amman tsabar iyayi wai aunty zee ta fadi tana jan tsaki “ke kuwa meye abun jin haushi bayan gindin zama take nema sgurinki “
    “Ai kuwa idan dai agurina zata samu bazata taba samu ba sai dai gaisuwar fatan baki ,kisna tace “to ai shima aunty data kiraki dashi ba wani abu bane fa normal ne yanzu da wanda ka girma da wanda ya girmeka duk zaku iya kiran junanku da aunty Kawai dai ke baki son girma ne shiyasa kikaji haushi “,gaskiya bana son gara ma idan nasan na girmeka ina iya hakurin wannan amnan ita datayi kanwa ta biyu ko uku dani ta wani ce min aunty …” Dariya suka yi suka ci-gaba hirarsu suna aiki batare da sun bi ta kan laidar da Samir ya kawo musu ba ..”

    ******”

    Tunda su mommy suka zo wasu abubuwa suka ragu kasancewar basa zama a gidan kullum sai sun fita yawo har da kukan murna kisna tayi saboda tun zuwanta kasar sau daya ta fita zuwa kasuwa sai gashi yanzu kullum sai sun fita , sai dai duk daren duniya sai Aliyu yasan yadda yayi ya bata mata rai har ya kai ta ga yin kuka , satinsu mommy uku a kasar suka fara shirin komawa Nigeria ita da yara ban da aunty zee zata zauna tare da mijinta duk abinda ya dace mommy tayi tsaraba dashi Aliyu ya siya mata Ana jibi jirginsu zai daga tace zata shiga kasuwa ta duba ta gani ko akwai abinda zata bukata dan haka washegari ta shirya da misalin karfe biyu na rana direban Aliyu ya bar gidan ita.”

    Aliyu da samir da nasir na zaune a haraban gidan akan fararen kujeru suna tautaunawa akan business da buga wasa dan wani sati zasu wuce spain domin buga wasa yayinda safiyya da aunty zee da kisna suke dakin mommy zaune akan gado suna kimtsa mata kayanta aryan da areef suna wasa a kasan tayis da kayan wasa, can aryan ya fita daga dakin ya tsaya abakin kofa kasancewar safiyya data shigo dakin bata rufe ba, mikowa areef hannu yayi alamun suje parlou’n kasa babu mutsu areef ya mika masa hannu suka fice daga dakin da kayan wasansu .

    Suna saka da hira kisna taji gabanta yayi wan irin mumnunar faduwa sakamakon tunowa datayi ta daura ruwan zafi kafin ta hawo sama qara ta saki tare da durowa daga saman gadon ta sauko da sauri “lafiya kisna “?Safiyya ta tambayeta cikin tsananin tashin hankali “wallahi ruwan zafi na daura tun dazu na manta sai yanzu na tuna tayi maganar tana karasa barin dakin da sauri ,tana taka step taji qara areef da gudu ta karasa saukowa jikinta na wani irin rawa kamar mazari ,ganinsa jikin hot plet jikinsa na rawa yasa ta saki qara ta fito da gudu dan ta kashe wutan gidan gbdy sai dai rudewar datayi yasa ta kasa hada kujera , ta dawo zata rungumeshi ajikinta adaidai lokacin da safiyya da aunty zee suka shigo kitchen sakamakon ihunta da suka jiyo safiyya tayi sauri riketa cikin tashin hankali tana furta ” inna lillahi wa inna ilaihi raji’un Samir da nasir ne suka shigo atare ban da Aliyu dake amsa wayar wani abokin harkallarsa hankalin samir a matukar tashe ya kai hannu ya kashe meter gidan gbdy yana kashe meter arif ya zube kasa a sume kisna ta fixge jikinta ta karasa rungumeshi tana kuka da kiran ta shiga uku..”

    samir ya dawo kitchen din da hanzari ya amshe areef a hannuta yana tambayarta yadda abun ya kasance ta biyosa tana yi masa bayani tana kuka ,Gaba-daya Samir ya gigice ya rasa inda zai nufa dashi kawai ya nufi sama dashi gabad’aya suka biyo bayansa hankalinsu a matukar tashe kofar dakin mommy dake bude ya shiga ya kwantar da yaron yana kiran sunansa tare da taɓa kumatunsa cikin tashin hankali “areef! areef!! dukkaninsu babu abinda suke faɗa sai sunan areef bude idanunka.
    aunty zee tace “areef my boy open your eye’, amman Shiru …
    kisna data karasa shigowa dakin ta tsaya daga bakin kofa ta kasa k’arasowa inda suke hannuwanta duka dafe da qirjinta dake wani irin mahaukacin buguwa da karfi ,jira kawai taji abinda zasu ce mata ya mutu ko yana raye ….

    a guje Aliyu ya shigo dakin sakamakon faɗa masa da nasir yayi yana k’arasowa bai san sanda ya matsar da samir gefe ba ya cicccibi d’ansa ya rungume ajikinsa yana kiran sunansa “areef !arerf !! aunty zee ta d’auko ruwan roba dake ajiye ta mikawa Samir sannan ta amshi yaron daga hannun Aliyu ta kwantar dashi ta amshi ruwa ta shafa masa a fuska ya ɗan sauke ajiyar zuciya da kyar yana ƙoƙarin bude idanunsa amman ya kasa Samir ya fita da gudu tunawa da yayi idan mutun ya samu shock na electric ruwan gishiri ake fara bashi ko cikkaken second biyu bai yi ba ya dawo dakin ya mikawa aunty zee ruwan rige rige safiyya da aunty zee sukayi gurin amsa ruwan aunty zee ce tayi nasarar amsar ruwan ta bashi ya sha tana kiran sunansa “areef plz my dear open your eyes say something to aunty zee …”

    ” Nasir Kira doctor plz inji cewar Samir , Nasir ya mike ya fita da sauri, gaba-daya sun rude sun gigice , a mutukar fusace aliyu yace ” wai ya’akayi wannan accident din ya faru dashi “?Cikin rawar jiki samir ya sheida masa kamar yadda kisna ta fada masa ta daura ruwan zafi ta manta amman tana tunanin areef yayi wasa da ruwa kafin ya taɓa hot plet din , saurin dafe goshinsa yayi yana furta “ya Salam yaji kamar ya kamota ya rufeta da dukan mutuwa ,
    jin yadda suke kiran sunan areef har lokacin ta sadaukarwa ranta cewar ta rasa d’anta wasu zafafan hawaye suka soma turereniyar zubowa daga idanunta ta sake makalewa a jikin bango tana furta kalmar data ji ta fito daga bakin aunty zee wato “inna lillahi wa inna ilaihi rajiun, shi kawai take furtawa tana maimaitawa cikin haka nasir ya shigo tare da doctor rike da briefcase a hannunsa gabad’aya suka matsa suka bashi guri ya cire abun awon daga wuyansa ya auna shi yaga yana numfashi sai dai ba sosai ba Aliyu ya daga kafafunsa daga inda yake tsaye ya fuskanci inda kisna take tsaye “kuka munafurcin me kike wa mutane bayan sakacinki ne duk ya janyo zan rasa d’ana “? Gabanta ya shiga dokawa da karfi ta
    Hannuwanta duka ta haɗe guri daya alamun yayi mata afuwa “ki daina nuna kamar kin damu da halin da areef yake ciki kowa yasan baki damu dasu ba saboda tsanar da kike min yayi maganar a fusace yana nuna qirjinsa …”

    “Aliyu dan Allah ka natsu areef zai dawo daidai bai kamata kayi bleming d’inta ba kasan bazata bari wani abu ya samesa da ganga ba inji cewar nasir .. “furzar da iska mai zafi yayi haɗe da rike kugunsa da hannunsa daya “bata sona komai zata iya yi dan ta dakushe farincikina bayan waɗan nan yaran sune rayuwata, sune dangina ,sune komai nawa ya karasa maganar cikin tsananin fushi yana nunata da yatsansa “wannan muguwar babu abinda bazata iya yi akaina ba tun da bata sona …”…

    Doctor ya kai hannu yana ƙoƙarin bude idanun areef “open your eyes da kyar yaron ya iya dan bude idanunshi da taimakon doctor , haka ma bakinsa ya buɗe ya duba sannan yace “karku damu zai dawo daidai Aliyu yace doctor “kana ganin zai rayu ? “Zai rayu sai dai jikinsa yayi week sosai saboda shock din daya samu me kuka bashi kafin na karaso ?” An bashi ruwan gishiri suka hada baki gurin fadar haka “Yes wannan abu ne mai kyau, abinda ake son abawa duk wanda ya samu shock daga wutar lantarki kenan garin yaya ma karamin yaro kamar wannan akayi careles dashi haka “?”Wannan mahaukaciyar uwar tashi ce tayi sakacin dashi yanzu kalli abinda ya faru dashi bancin yana da sauran yawanci rai da ba abinda za’a fada kenan ba “gaskiya ta dinga kula dashi idan ba haka ba zata iya rasa shi wata rana ,yanzu dai ku bar shi ya huta zuwa wani lokaci duk suka fito daga dakin suka bar aunty zee tana shafa masa kai …..”

    Nasir ya dubi Aliyu yace “muradi abinda kayi sam bai dace ba ban ji dadin abinda ka faɗa a daki ba , tun bakasan da zaman yaran nan ba ita ke kula da yaranta dan me zaka yi bleming d’inta without any reason for god sake”dan Allah karka faɗa min babu dadi kulawar banza kulawar wofi ,wacce irin kulawa ce wannan da har za’a yi careless da rayuwar yaro ? idan har tana kulawa dasu bazata bari abinda ya faru yanzu ya faru dashi ba “.”karfa ɓacin rai ya sa ka furta sabo itafa yar adam ce “ai komai za’a fada akanta ba yarda zaka yi ba kana bayanta “.

    “ba haka bane wallahi nasan tayi kuskure tunda tasan yaran suna gidan kuma suna da kiriniyya bai kamata ta barsu a parloun kasa su kadai ba alhalin kofar Kitchen a bude yake sannan kuma bata gurin sai dai ya zamu yi da qaddara “? “Allah ya qaddara haka dole sai hakan ya faru babu tsumi babu dabara kisna ta matso kusa dashi saboda ganin yadda ɓacin ransa ya fito fili muryarta na rawa tace “dan Allah kayi hakuri wallahi ba da ganga nayi ba ai jin maganarta yayi kamar garwashin wuta a zuciyarsa ya juyo a fusace yana dakatar daita da hannunsa ” baki da abinda zaki kare kanki agurina bare wani hakurinki din banza ,me zanyi da hakuri ?
    ” kima san wani abu wallahi bazan barki haka ba sai na hukataki bisa gangancin da ki ka min akan yarona ……”

    zaro ido waje tayi hawayen dake makale a cikin kwarnin idanunta suka gangaro ya kai hannu zai cafki wuyanta nasir yayi saurin rike masa hannu “haba aliyu meye haka kake kokarin yi “? ya fixge hannunsa da nasir ya rike yana damko tsintsiyar hannunta yayi hanyar waje daita tana biye dashi tana kuka tana kallon bayansa jikinta na wani irin rawa gabad’aya suka biyosa har Samir daya zuba masa ido suna masa magana yayi musu banza bai kula kowa ba sannan bai tsaya a ko’ina ba sai a haraban gidan yana gama k’arasowa yayi cilli da hannunta ta tafi luuuuuuuu zata fadi “ki bar min gidana sannan ki fita a rayuwata bana bukatarki ,Aliyu baya bukatarki arayuwarsa”shiru tayi tana kallonsa zuciyarta na dokawa da karfi kamar zai fasa qirjinta ya fito waje ,”bana sonki bana bukatarki arayuwata da ki kashe min ya’ya gara tun wuri na zareki acikin rayuwarta ya karashe maganar jijiyoyin kansa na mikewa alamun ya kai kololuwa gurin ɓacin rai “.

    ” Aliyu dan girman Allah ka tsaya ka dawo hankalinka idan rai ya ɓaci hankali ke dawo dashi abinda kake yi sam bai dace ba haniyarsu ta fito da aunt zee haraban gidansu “kasan Allah bazan saurari duk abinda zaku faɗa min akan wannan ba kawai ta bar rayuwata kafin nima ta kasheni dan babu imani a zuciyarta “no aliyu wannan ba daidai bane aunty zee ta fada tana kallon samir dake tsaye rungume da hannuwansa duka a qirji ya bala’i tsurawa Aliyu ido yana kallonsa yana mamakinsa yana jin wani irin d’aci acikin ransa wanda bai taba tunanin zai ji akan Aliyu ba mutumin da suka taso tare, gurin baccinsu daya komai nasu tare sutura iri daya suke sakawa hatta karatu iri daya suka yi babu abinda ya bambamta su sai karfin zuciya cikin fushi aunty zee tace “ka tsaya kana kallanmu ka masa magana mana nasan idan ka masa magana zai fahimka akan tamu maganar “numfashi ya sauke yayi mata alamar tayi shiru tare da cewa “bana bukatar ki sake cewa komai…”

    “Na tsaneki fiyye da tsanar da kika min , duk kalamanki basa shiga zuciyata bare su samu matsuguni sannan karki sawa ranki ni Aliyu zan dawo na soki a wannan duniyar never hakan ba zai taɓa faruwa ba ,bani da lokacin da zan fahimci kowa daga cikinku akan wannan yarinyar ya nuna kisna kinga zamanki acikin gidan bashi da wani amfani dan dake da babu duk daya ne agurin Aliyu gara ki kama gabanki .”
    Cike da tsananin tashin hankali tace “dan Allah ka tsaya ka fahimceni ta kai hannuta zata kamosa ya buge mata hannu da sauri “don’t don’t ever touch me ,karki ga na dawo dake cikin rayuwata ki ɗauka ko tsoro ne a’a hallaci na duba if not ke da Aliyu har abada dan ko alahira bana qaunar na hadu dake ,wallahi akan wannan gangancin da kika min zan iya sakinki …….”

    kanta ne ya soma juyawa saboda jin kalmar daya fito daga bakinsa take ta soma ganin juya jikinta ya kama rawa sosai fiyye da d’azu gabad’aya tsayuwa ya gagareta jikinta ya kasa ɗaukar kafafunta ta soma yin kasa zata fadi aunty zee tai saurin matsowa kusa daita ta rikota jikinta tana girgiza mata kai “aunty zee kina jin abinda yake faɗa akan ya’yan da ni kadai nasan irin azabar dana sha akansu , nasan nayi masa kuskure amman ya kamata zuwa yanzu ya yafe min ko da yake na fuskantarshi so yake ya koreni ya rabani da ya’yana suyi rayuwa tare da wata “exactly abinda nake nufi kenan kuma na gode da kika fahimci haka saboda bani da abinda zanyi dake , jin haka yasa ta sanyawa jikinta jarumta ta mike bisa kafafunta da suke rawa ta goge hawayen idanunta “to ya kake tunanin zan iya rayuwa babu ya’yana”? “Ka barni na rayu tare da yarana karka nisantani dasu , dan Allah kayi hakuri bazan sake ba nasan nayi kuskure bazaka sake kamani da makamancin irin wannan laifin ba, kayi hakuri nayi kuskure bazan sake ba “. tana kuka tana rokonsa …”

    “baki da hankali ki rike hakurinki dan babu abinda zanyi dashi rayuwa dake ne dai bai zai me min dole sai nayi ba dan haka ki kama kanki da kyau dan at any time zan iya rabuwa dake wallahi coz you are nothing to me ya karasa maganar yana huci kamar zakin daya ga abincinsa ya rasa har zai juya ,ya tsinkayi muryarta cikin kuka “yadda baka damu dani ba nima bazan sake damuwa da kai ba ……”

    “daya fiyye miki Kinga kin hutar da bakar zuciyarki son Wanda baya sonki yana gama fadar haka ya juya ya shige gidan , kuka take sosai kamar ranta zai fita haka aryan shima kuka yake yana rike da hannunta duk ta fita haiyacinta da kyar aunty zee da safiyya suka kamota suka shigo daita suna rarrashinta “har sai yaushe Aliyu zai ga farina aunty zee “?
    “Na kaskantar da kaina na bashi hakuri yaki hakura ,na bishi na bishi yaki saukowa me zan masa aunty zee ki faɗa min abinda zanyi masa ya huce “? ta karasa maganar tana sake rushewa da wani sabon kuka “aunty zee ko hakura zanyi dashi ne na hutawa rayuwa tunda baya sona ya furta min ni dashi ya furta agabanku “wani irin tsana ce haka ? aunty zee ta girgiza mata kai” maganar hakura dashi ma bata taso ba ” kai aunty zee wallahi na hakura da Aliyu koda kuwa shine karshen namiji a duniya zan barshi ta mike cikin rawar jiki ta hau sama tana taka step biyu biyu aunty zee ta biyo bayanta da sauri tana kiran sunanta …..”

    Mmn sudais
    💗💗💗💗💗💗
    CUTAR DA KAI
    💖💖💖💖
    💗💗💗💗💗💗

    Note
    error: Content is protected !!