Cutar Da Kai – Chapter Sixteen
by Aysha A Bagudo~TRUE LIFE STORY~
*PAID BOOK*
*AYSHA A BAGUDO*
…..Gabanta ne yayi mummunar fad’uwa ganin yana ƙoƙarin sunce belt , hankalinta yayi matukar tashi taji kamar ta bashi hakuri sai dai tayi tunanin ta tsaya taga iya gudun ruwansa dukan zai yi haka daga ita sai pent ? har ya gama sunce belt ya nade a yatsun hannunsa idanunta na kanshi ta maseefar kura masa idanuwanta cikin tsananin tsoro da tashin hankali mai tattare da faduwar gaba , zuciyarta ban da rawa da tsinkewa babu abinda take , cikin wani irin matsefaffen tsanarta ya d’aga hannunsa zai labta mata belt tayi saurin rike belt din da hannunta tana kallon cikin kwayar idanunsa shima kallonta yayi yana ciza lip’s dinsa ,Kafin daga bisani ya soma kokarin fixgewa ta sake rikewa gam da hannuwanta duka hawayen dake makale a kwarnin idanunta na kokarin zubowa “ki saki belt din nan tun raina bai kara ɓaci ba “to wai me nayi maka ne saboda Allah ? “Okay tambayata ma kike yi dan kin rainawa kanki hankali ? ” Kai dai a rayuwarka baka son ganina cikin kwanciyar hankali idan baka gannin cikin halin damuwa ba baka jin dadi ?”
“Eh bana jin dadi nafi son ganinki cikin ukuba tamkar baiwa saboda babu wata halitta dana tsana a rayuwata kamarki ya fada mata haka cikin tsananin fushi duk yadda ta kai da daurewa dan kar hawayenta su zubo sai da suka samu nasarar zubowa bisa kuncinta “very good haka nake so ganin ya furta murmushin farinciki na bayyana akan fuskarshi “ina son ganinsu kuma bana gajiya da ganinsu burina na cigaba da ganinsu har karshen rayuwata ,”ke da zaki dinga zubar dasu a kullum wallahi da Kinga yadda farincikina zai karu a gidan nan “saboda kai mugu ne mai muguwar zuciya ba ? ta faɗa acikin zuciyarta , yayinda zufa ke tsatsafo mata ta ko’ina a sansar a jikinta tana addu’ar Allah ya kwaceta a hannunsa , tasan babu wanda zai kawo mata dauki sai ubanginta “ki saki belt dina kafin nasa kafa na taka miki wuya yayi maganar a zuciya ko gama rufe bakinsa bai yi ba wayarsa dake yashe a kasa ta soma ƙara ya waiga bayansa a hankali yana kallon screen din wayar ganin haka yasa kisna sakin belt din tayi wata irin durowa daga saman gado zata fita daga d’akin babu kaya a daidai lokacin da yake kokarin maida fuskarshi gareta aiko taku daya yayi ya fixgota da karfi sai gata a jikinsa ya matseta soaai tare da belt , numfashinta ne ya soma barazanar daukewa saboda muguwar matsar da yayi mata da kyar take iya fitarwa ta saki kara mai sauti tana kokarin kwatar kanta daga garesa ya sake matseta gam dan yaga iyakacin karfinta “ke har kin isa na rikeki ki kwace ?” Har yanzu da saurinki , ke bama za ki taba kaiwa ba ,” guda nawa kike maza ma sun kasa dani bare ke ? idan kuma kina da karfin zuciyar kwacewa ki gwada kunjinki mugani yana magana yana sake matseta “wayyo bazan iya ba ta furta muryarta can kasa ko shi dake manne daita bazai ce yaji abinda tace ba , ganin jikinta ya mutu murus babu wani sauran karfi ajikinta duk ta gama mutsu mutsunta bata samu nasara ba ta hakura , ya dan sausauta rikon da yayi mata yana lumshe idanunshi ya sa kafarsa ɗaya ya d’aga wayar yayi sama daita tamkar kwallo ya cafke da hannunsa daya ya duba mai kiransa sannan ya zauna a bakin gado tare daita manne ajikinsa batare daya bin kiran ba ..”
hannunsa ɗaya yasa ya juyo da fuskarta garesa suna fuskantar juna ya balain kura mata kyawawan idanunshi masu matukar fitgita duk wanda ya kalli cikinsu sannan ya kamo lip’s dinsa na kasa yana cizawa da karfi yana cigaba da kallo tamkar ranar ya fara ganinta kuma har lokacin iskancin data masa yana dawo masa cikin kwakwaluwarsa ” wallahi wallahi baka isa ka mareni ba ya Aliyu ,” ka daina marina anan duniya sai dai a wata, yana kallo hawaye na zubowa daga idanunta kamar an bude fanfo “kalleta kamar jarumar gaske amman da zarar tazo hannu sai ta dawo abar tausayi ..” ya furta a kasan ranshi ”
a hankali ya shiga matso da fuskarshi daidai nata da zumar yi mata kissing din wasa dan babu niyyar yin na gaske a cikin zuciyarsa kawai so yake ya tsokanota ya barta cikin tashin hankali tunda yasan halinta jarababbiya ce, sai dai abun mamaki gani yayi tayi saurin kawar da fuskarta gefe tana sauke wahalallalen numfashi ,cikin tsananin tashin hankali ya sake tsura mata idanunshi kamar ranar ya soma ganinta , kusan minti shabiyar ya ɗauka yana kallonta fuskantarshi ɗauke da matsanancin mamakinta sam bai yi expecting haka daga gareta ba , ya ɗauka zata nuna maitarta a fili ne kamar sauran lokuta , ransa ne yayi bala’in baci , kisna ta kunno muradi sosai domin kuwa take zuciyarsa tazo wuya ta soma tuttukin bakinciki tare da tunanin azabar da zai gana mata “.
runtse idanunta tayi gam ta nuna bata son kallon fuskarshi bare ya samu damar wulakantata , hawaye ya sake zubowa kan kuncinta , hakan ya sake tunzura zuciyarsa , hannunsa ya Kai bayan keyarta ya damka da karfin gaske jikinsa na wani irin rawa ya saita fuskarta daidai nashi a zahiri ake iya hango ɓacin ransa , jijiyon kanshi sun yi rudu rudu ya fuskanceta yana busa mata hucin numfashinsa sannan ya bude bakinsa ya kira sunanta cikin tsananin tashin hankali “kisna Ni………… ” Sai kuma yayi shiru ya kasa magana ya cafki bakinta yana furzar da iska mai zafi ,idan yace abinda tayi masa bai ji haushi ba yayiwa kanshi karya har shi zata kawar fuska ? “Wacece ita shi da mata ke rububunshi yana sharesu “ina bazai taba daukar wulakaci daga gareta ba dole ne ya hukuntata daidai da abinda ta aikata masa, ya lumshe idanunshi zuciyarsa na tafarfasa kamar an daura garwashin wuta a samanta ..”
Duk da abinda Kisna tafi bukata kenan daga garesa suyi musayar yawu baki da baki amman sai taki nuna tana bukata ta haɗe hakoranta guri daya taki bashi dama , yayi saurin toshe mata hanci da hancinsa , take numfashi ya soma kokarin tsayawa babu shiri ta bude bakinta a gigice tana shaƙar nnumfashinsa gabadaya ta sadaukar da kanta garesa dan babu wani karfi daya saura ajikinta , haka ya dinga sarrafa harshensa cikin bakinta batare da yayi niyyar aiwatar da hakan ba, shi daya so hukuntata sai gashi ya buge da fitar da sanyayyen numfashi tare da jin wani mugun feeling’s dinta na taso masa a gaba-daya ilahirin jikinsa , sai daya gaji dan kanshi sannan ya zare bakinsa ya matseta sosai a gefen jikinsa yana sauke ajiyar zuciya da karfi yana jin wani iri a sansar jikinsa .
gabadaya yanayinsa ya sauya , duk wani gashi dake kwance ajikinsa babu Wanda bai Mike ba , ji yake muddin bai hada da murza nipples dinta ba wani mummunar abu zai samu zuciyarsa ,a hankali ya soma murzawa sai dai take zuciyarsa tayi saurin hankalta dashi idan yayi mata yadda zataji dadi zai fadi warwarsssss a gabanta gara ko zai yi yayi mata da zafi kuma ta tsigar horo…”
” da karfi ya damki kan nipples dinta yana murzawa da karfi yana sauke ajiyar zuciya , ya Kai bakinsa cikin kunnenta ya zira harshensa wani iri yrrrrrrrrrr taji ilahirin jikinta kamar anjona jikinta da shocking , ya sake matseta gam yana hura mata iskan bakinsa “duk kin gama iskancinki kizo hannu , ko zaki iya maimaita kalmar iskancin da kika fada min d’azu ? ya karasa maganar yana sake zira harshenta cikin kunneta take tsigar jikinta suka mike ta sake dawowa abar tausayi ,
Tayi shiru ta kasa cewa masa komai dan ji take dama kasheta yayi akan yadda yake murza kan nipples dinta da karfi dan har gara tafiyar harshensa cikin kunneta tana jin wani abu akan akan murza nipples dinta da yake .”
“a she iskancinaki da cika bakinki na karya ne babu abinda zaki iya yi , Aliyu yafi karfinki ya karasa maganar yana matsa kan nipples da karfi , ta saki wata razananniyar kara hawaye na zubo mata so yake tayi magana a lokacin ko yaya ne domin tabbatar da zata sake kallon kwayar idanunsa ta fada masa son ranta ko kuwa ta shiga hankalinta ?
“Ya zamo karo na karshe da zakiyi sa’insa dani ,ya zamo karo na karshe da zan fada ki fada domin baki isa ba , dama rayuwarki ta dameni zan iya daukar nauyin haka sai akayi sa’ar rayuwarki bata gabana dan haka baki isa kiyi abinda kike so ba kuma ni ba sakaran namiji bane,” kinfi kowa kin san da haka ,dole ki cigaba da bin tsarin da nake so, tun da na fahimci baki canza halinki ba , ki sanyawa ranki halin Aliyu na nan fiyye da saninki a fusace yake magana cikin haka wayarsa ta sake ɗauka ƙara ya furzar da iska mai zafi sannan ya dauki wayar yana cigaba da murza kan nipples dinta yana magana a hankali cikin sanyayiyyar muryarsa data dawo kamar ta dan maye ” naji dan Allah malam banason takura yanzu zan fito ba sai ka hawo ba kalmarsa ta karshe kenan da yayi yana jan dogon tsaki addu’ar take a lokacin ya saketa kuma ya bar dakin koma ya bar gidan gaba-daya zuciyarta ta huta da muguntarsa dan muradi yasan ta kan mugunta bai bar dakin ba a lokacin Sai da ya gama jagwalgwalata son ransa sannan ya barta ya mike zuciyarsa na matukar zafi “karki ɗauka kin sha banza , baki sha banza ba dan sai na horaki kafin na bar kasar nan gobe idan aka ce ki sake furta min kalmar zakiyi yawo tsirara bazaki yi ba “. Allah Allah ta dinga yi ya fita tana ganin fitarsa ta mike da sauri ta janyo rigarta ta saka tana yiwa Allah Godiya daya kuftar daita daga hannunsa da bai fita sai yadda hali yayi dan har ta fara hango yadda fatan jikinta zai yi, bata tsaya bata lokaci ba ta fice daga dakin ta shige dakin mumy ta kulle kanta ciki dan baza zauna ya dawo ya jibgeta a karon banza ba ..”
Yana saukowa kasa Samir da sauran abokansa suka kalleshi ganin yadda ya sauko a hargitse idanunshi gaba-daya sun canza kala daga fari zuwa kore kuma sai faman ciccin magani yake yasa samir yace “me ka tsaya yi ne bayan kasan akwai inda zamu ana can ana jiranmu ” muradi ya tsare shi da idanunshi yana fitar da numfashi yace “wannan wace irin tambaya ce ? ya tambayesa a zafafe ” maida wukar abun bai kai na fada ba muje ya nuna masa kofar fita dan yasan halinsa sai yayi zuciya akan dan wannan tambayar , cikin abonkansa akwai mutun daya wanda bai cika jin tsoron muradi ba yace “ta ya zaka ma magidanci kamarsa wannan tambayar ai ya tsaya ragewa kansa zafi ne ,”kaga duk yadda tafiyar ta kasance daidai ne ko abokina ? yayi maganar yana dariya yana duban muradi suma sauran abokan biyu dariya suka yi banda rohon da yaji ranshi ya ɓaci dan tsab ya fahimci abinda jocub yake nufi kallonsu muradi yayi daya bayan daya har rohon daya lura da yadda yayi akan maganar , fuskarsa dake daure tamau yasa dariyarsu ta soma tsayawa ,gashi dai sa’ansu ne a shekaru amman suna mugun jin tsorosa saboda yana da wani irin kwarjini kuma duk inda ya ratsa cikin mutane sai kaga ana shakkarsa kuma hakan baya hana mutane sonshi da rububin mu’amala dashi ga shi da farinjin mata, babu kasar da zasu shiga mata basu nuna suna tsananin son shi ba a tarihi ma babu macen daya furta wa kalmar so sai dai a furta masa ,mace daya ce tayi galaba akanshi itace nawal itama itace ta soma furta masa tana son shi …”…
Ganin sun rage sautin dariyarsu yasa Samir dafa kafadansa “am sorry dan’uwa na katse maka hanzari ko yayi maganar yana dage masa gira sa daya alamun zolaya , muryarsa can kasa yace”kar muyi haka da Samir yayi gaba , Samir ya biyosa yana cigaba da cewa “wai kana nufin har yanzu baka shiga daga ciki? tsayawa muradi yayi a lokacin daya fito haraban gidan ya watsa wa Samir wani rikitaccen kallo cikin yanayin maganarsa dake fita a hankali yace “zuciyaka dake wannan tunani ta daina ni babu ruwana da mata “babu ruwanka da mata kake kokarin kara wani aure na biyu kai dai wallahi anyi mugu mai cutar da kansa amman ….” katse maganar yayi alokacin daya abokan tafiyarsu sun fito , suka shiga mota gabadaya suka bar gidan , a motar ma zama yayi gidan baya yana kallon gefen titi tunani abinda ya faru yanzu a tsakaninsa da kisna ke dawo masa wani murmushin gefen baki ya bayyana akan fuskarshi “kalmar zata fita tsirara ta dame shi sai dai tafi kowace kalma bashi dariya Samir dake gefensa ya kalleshi ya girgiza kai ya rasa meke damun dan’uwansa wani lokaci kaganshi cikin farinciki wani lokaci kuma tamkar wanda azarailu ya kawowa sakon mutuwa har suka karasa inda zasu fuskarshi babu yabo babu fallasa ,har yaje ya dawo abun na yawo a brain dinsa kalmar ta kasa bace masa …..”
bai isketa a parloun ba ya ajiye laidar daya shigo daita ya haura sama ya shiga dakin baccinsu nan ma bai ganta ba ,ita kuwa tun da taji motsin shigowarsa ta rasa natsuwarta gabanta ya dinga faduwa yana tsinkewa kar yace zai balla dakin mumy ya shigo ta sauke numfashi ta shige bayi ta kulle.”
ya cire kayan jikinsa ya shiga wanka bai wani dade ba ya fito sanye da boxer da farar singlet ya sauko kasa ya zauna akan dining table ya bude kulolin dake kai yaga wayam babu komai hasali ma babu alamun anyi girki yaja tsaki yana furta “aikin banza dama wani damuwa nayi da abinciki bare kiyiwa mutane salo , ladar daya shigo daita ya janyo ya bude ya soma cin gasashiyar kaza wacce taji kayan hadi bayan ya gama ya koma sama , a daren ya hada kayansa da kanshi cikin qaramar jaka dake dauke da zanen kwallo da tambarin sunan club dinsu , bawasu kaya ya diba ba saboda kowani kasa da yake buga wasa yana wadatattun kaya wanda ba tsiya yake ba kamfani ke bashi .”
har 11 :00 ta buga bai runtsa ba sannan bai ga shigowar kisna ba bai damu ba yayi kwanciyarsa bayan yayi waya da mumy da dady kafin bacci ya daukeshi wayar nawal ce ta shigo ya ɗauka ya duba da kamar bazai amsa ba sai kuma ya ɗauka saboda ba lallai ne ta sameshi a waya ba idan ya tafi , har bacci ya daukesa nawal na zuba masa surutu akan yadda take son shi jin shiru baya magana ta katsen kiran itama ta kwanta dan ta fahimci yayi bacci , karfe hudu daidai ya farka yana mika haɗe da salati ya fada bayi domin yin wanka tare da dauro alwala ya fito ya shiya cikin hadadden sult ya daura agogon dioman a tsintsiyar hannunsa tare da fesa turare a jikinsa da bayan kunnensa ya rataya jakarsa ya fito daga dakin har ya wuce dakin mumy ya dawo da baya da baya ya tsaya a bakin kofar saboda zuciyarsa ta tabbatar masa da kisna na ciki , yasa kafarsa ɗaya ya buga kofar da karfi kamar zai balla …..”ya Allah ta furta tana farkawa daga baccinta tare da kamkame jikinta guri daya a hankali ta fara karanto addu’ar neman tsari daga bala’in sa , a zafafe yace “ki bude kofa “.
“nayi maka me ? ta fada cikin karfin hali ,nifa banason tashin hankali da sanyi safiyar nan , tafiya zakayi ka tafi Allah ya tsare ya bada Sa’a “ko baki min addu’a ba zan yi nasara tunda uwata tayi min kuma wallahi kin taimaki kanki da kika boye kanki da jikinki ya gaya miki “tun da kana jin karfi ai sai ka balla kofar ka shigo ka kasheni ta fada masa a tsorace “da kyau ai ina son haka ki jira dawowata sai dai idan ban iske ki a gidan ba amman wallahi sai na …. ƙarar sautin wayarsa ce ta katse shi ya ciro yana duba screen din wayar tare da manna wayar a kunneshi ya barin kofar dakin …”
Ba ita ta fito daga d’akin ba sai da taji sautin muryar aunty zee ta dawo da natsuwarta jikinta “ya naganki a firgice ? Numfashi ta sauke tace “nida ya Aliyu ne tun jiya dana shiga dakin nan na kulle kaina sai yanzu na fito ke ina ganin kwaso kayana ma zanyi na dawo nan wallahi bazan iya da balainsa b “me kuma ya faru da zaki raba daki da mijinki ke da kike cikin sharadi ? A hankali ta fara zayyanowa aunty zee duk abinda ya faro ,aiko ta dinga dariya har da rike ciki “wallahi kisna baki da kirki amman kuma kin yi daidai gara da kika masa haka “ai ina ganin zan fara nuna masa ajina na nan bai je ko’ina ba dan sakar masa da nake yasa gabadaya ya rainani wai har da cewa sai dai bai dawo ya sameni a gidan nan ba kamar wata yarsa ke wallahi na ma fasa dawowa dakin nan a can zan cigaba da zama ya dawo ayi burouban da za’a yi …”
“ke ban son cika baki kiyi kokari dai komai ya daidai tunda dan rainin hankalin ya fara shan baki ina ganin ya Kusan zuwa hannu “tab wannan mai shegen taurin kan abinda ma shan bakin yana sha yana cika yana batsewa kamar nace dole ya sha “kai ya Aliyu sai a hankali zuciya kamar da karfe aka ginata yana magana cike da izza da nuna mutun ba kowa bane mutun kamar dan gidan saurata koda yake a duk jirgi ɗaya ya kwaso ku ke dashi “a’a wallahi muna da bambanci kisna ta fada da sauri nan dai cigaba da magana akan muradi …”
Karfe daya suka tashi suka shiga kitchen kasancewar kayan abinci a bangaren kisna yake jollof rice suka dafa anan suka wuni suna hira wanda rabin hirar duk ta muradi ce tsawon kwanakin uku suna zaune a bangaren kisna ranar da su muradi zasu buga wasa kuwa kisna manta komai tayi ta tare agaban tv , muradi kawai take kallo sanye da wonda da riga dark blue Wanda aka rubuta muradi a bayansa yayi maseefar kyau sai ya saje da fararen fata , sai kwace kwallo yake a kafar abokan karawarsu yana bugawa yadda ransa ke yaso ,idan aka dauke fuskarshi kisna taji wani mugun haushi , idan aka haskoshi ta dinga murmushin kenan tamkar wacce aka yiwa bushara da gidan aljanna duk aunty zee na lura daita tayi murmushin tana dafata “muradi fa ya tafi da rabin rayuwarki autar mumy ” bata kalli inda aunty zee ke zaune ba ta maida mata amsa da “ba rabin rayuwata ya wuce dashi ba gabadaya rayuwata ya tafi dashi shi yasa na kasa ciresa araina ,sai dai duk da haka bazan sake daukar wulakaci daga garesa ba wallahi duk yayi min sai na rama saurin mikewa tayi haɗe yin tsalle cikin jin dadi sakamakon muradi ya wulla kwallo cikin raga ba ita dake tsallen murar ba hatta abokansa murna suke gabadayansu suka rungumeshi , bayan wani lokaci aka cigaba da wasa sun dauki tsawon lokaci suna fafatawa babu wanda yayi nasara sosai muradi yake kokarin jefa kwallo cikin raga wani abokin buga wasansu messi na tauyesa babu zato yasa masa kafa tare da dukan qirjinsa take muradi yayi kasa rike da qirjinsa kisna ta dafe kirjinta da duka hannuwanta taji kamar qirjinta aka taba gabadayan zuciyarta ta jagule kamar ta dora hannu aka ta sa kuka ganin an rufesa har reaf .
ta fashe da kuka tana kamo hannu zeey cikin nata tare da tsine wa wanda ya hardeshi take aka sake hasko yadda abun ya kasance tabbas mugunta abokin wasansa yayi masa, reaf dake tsakiya ya janyo mesi gefe yana bashi warning tare da yi masa magana kasa kasa “ka daina buga wasa haka sai kayi lossing tun ba’a je ko’ina ba ko da yake na lura ka sakawa muradi ido da yawa, cikin tsananin jin haushin maganarsa messi ya soma magana yana daga murya reaf ya juya ya barshi ya karasa gurin muradi dan tuni likitansu ya karaso da wata karamar akwati ya tsugunna a gabansa ya soma duba lafiyar ,muradi dake kwance ya damki sumar kanshi dake kwance luf luf gwanin ban sha’awa da hannunsa daya, yayinda dayan hannun ke dafe da qirjinsa ya runtse idanuwansu kisna kamar ta fasa tv ta shiga dan dawowa tayi gaban tv ta zauna tana kuka , cikin kankanin lokaci aka masa abinda ya dace ya dawo daidai aka ce ya fita a canza wani a madadinsa amman yaki dan haka aka sake komawa wasa dashi , har kusan sau uku ana bawa messi warning akan muradi dan zuwa yake yayi atttakig dinsa har sai da aka bashi yellow card, hankalinsa bai dawo jikinsa ba sai da aka ciresa gabad’aya aka bashi read card , ranar cikin sa’a team dinsu muradi suka lashe su 3-0 .
washegari ma aka sake hadasu da wasu team din still suka cinye har aka je final still dai sune suka cinye
Ranar cike da fara’a kisna ta yini daga karshe ta shige daki tayi kwamciyarta zuciyarta na tunanin muskilin mijinta …
Satinsu biyu suka soma shirin dawo wa kasar cairo ,Samir yayiwa aunty zee tsaraba sosai yayinda muradi yayi fuska duk da yaga abubuwan da zasu dace da kisna amman yaki siya ,ganin haka yasa Samir daukar mata yana zolayarsa , misalin takwas saura na dare tana kwance a falo ta runtse idanunta sai dai ba bacci take ba ta dukufa ne gurin nazari da tunani , sam bata ji motsin shigowarsa ba ,yayinda shi kuma yayi tsaye akanta yana kare mata kallo da kallon falon komai tsaf tsaf very neat kamar yadda yake bukata ga kamshin airfreshner na tashi gauyare dana turarenta ita kanta a tsaftace take tayi kyau sosai cikin doguwar riga kamar an tsinkareta ta motsa haɗe da bude idanunta taga mutun tsaye a gabanta wani irin mummunar faduwar gaba taji sai dai bata nuna masa ba tayi masa kallon sama da kasa tace “sannu da zuwa ta dauke kanta akanshi ya ajiye jakar hannusa yana cigaba da kallonta cike da takaicinta “wato ma dan samun dama taci ta koshi ta hau bacci ganin yadda yake kallonta kuma bata manta da yadda suka rabu dashi ba ta mike tsam tana kokarin bawa kafarta iska sautin muryarsa taji “tunda nake ban taba ganin wawiyar yarinya irinki ba…..”
da hanzari ta tsaya tana dubansa da idanuwanta da suka kada zai sake magana ta katseshi ta hanyar daga masa hannu “enough muradi ya kamata zuwa yanzu kana sanin irin maganar da zaka dinga fada min, karka manta nifa ba yarka bace matakar ce ita kuma mata ba kowace magana zaa dinga fada mata ba, ka lura ka hankalta kuma gane kisna tafi ƙarfin wannan tozarci dan haka kayi ka dawo taitayinka , idan ba haka nan kusa zaka tantance tsakanin aya da tsakuwa taja tsaki tana sakar masa harara tayi gaba abinta tana rausaya abinda yafi tsana kenan a rayuwarsa ayi masa tsaki a wuce shi ji yake kamar ya mutu ya gwamaci shi yayi da ayi masa , biyota yayi cikin zafin nama aiko ta kara sauri sai dai akan step ya cafkota ya damki naman cikinta zuciyarta ta soma sarewa da lamarinsa daga dawowarsa abin nasa yafi karfinta hawaye suka gangaro mata “wannan wace irin tsana ce haka” ?
Da kyar ta fixge jikinta tana masa harararsa da yi masa Allah ya isa ta shige dakin mumy tun kafin ta saka key ya banko dakin ya ɗauketa da mari “bayan tsaki har da Allah ya isa ni sa’anki ne dukan tsiya mata ,sai da yayi mata lilis sannan ya samu guri akan kujera ya kallonta tana kuka “muddin zai fada ta fada bazai raga mata ba ya dinga gallazawa rayuwarta kenan har sai ta shiga hankalinta” zaki yiwa mutane shiru ko sai na an kawo min kyankyasai ?tana jin haka tayi shiru ta daina zubar da hawaye sai shesheka “shima sheshekan kuka bana son jinsa dan kin cika min kunne kuma na sake jin kin kirani da muradi sai zubar miki da haƙora wawiya kawai “. tashi tayi gbdy ta shige bayi , tunda ya dawo bata sake bari sun hadu dashi ba ,shima bai fiyye zama a gida ba kullum sai ya fita acikin kwananki harkoki sun masa yawa training da office saboda zasu sake fita German buga wasa yadda ya fita tsabgarta haka itama ta sharesa babu mai shiga tsabgar wani sai ya wuce ta wuce ..”
*********
da wani yammaci da misalin karfe hudu tana zaune akan doguwar kujerar hannunta rike da waya tana magana da mommy yayinda idanunta ke lumshe ,kamshi turarensa ne yasa ta bude idanunta suka sauka akan shi yana saukowa daga mattatakala sanye da gajeren wando baki da karamar riga fara irin ta yan kwallon hannusa rike da kwallo yana bugawa har ya sauko daga step ya fita zuwa wajen idanunta na kanshi , sake lumshe kyawawan idanunta tayi” Aliyu ba dai kyau ba komai kyau yake masa cigaba da waya sukayi da mommy daga karshe ta hadata dasu areef ..
Shi kuwa aliyu kai tsaye field din gidan ya nufa inda Samir ke jiransa shima sanye cikin irin kayan dake jikinsa tun kafin ya karaso zee ta hura husir tana karfafawa mijinta gwiwa “karka yarda ya cinyeka kamar sauran lokuta “Kima daina bata bakinki yarinya dan kamar na cinyesa na gama idan dai wannan mijin naki ne da bashi da momora sai aiki cin tsiya Samir yayi dariya yana tafa hannu yace ” sharesa baby duk ya gama cika bakinsa daga karshe Allah ya bani Sa’a akanshi ba”. Aliyu ya saki kwallo aunty zee ta sake hura husir suka fara wasa da kwallo..”
Ganin har kusan minti goma suna fafatawa a tsakaninsu kuma har lokacin babu wanda yayi nasara cinye d’an’uwansa, sai dariya take ita kadai, idan taga Aliyu zai cinye mijinta da sauri zata sa ihu kamar zatayi kuka haɗe da daura hannuwanta saman kanta ,idan kuma mijinta ke kokarin cinye Aliyu sai tayi ta bashi kwarin gwiwa tana kiran “Samir !Samir !!Samir !!!
Haka nan tayi tunanin taje ta fito da kisna itama tayi kallo koda aunty zee ta shiga parloun ta isketa zaune ta tallafe gwiwar hannuta da filo data daura a saman cinyarta ta tallafe kumatunta da tafukan hannuwanta tana tunanin mijinta da auren da zai yi “kisna stop overthinking “me ke damunki mai yasa kike wannan dogon tunanin”? “Idan kika kashe kanki da tunanin ya Aliyu babu ruwansa ya’yanki zakiyiwa hasara “.
Taja numfashi ta fesar tana sauke naunauyen ajiyar zuciya sannan ta kalleta “tunanin auren ya Aliyu nake aunty bansan ya komawar rayuwata zata koma ba idan nawal ta shigo gidan nan wallahi har na fara tausayin kaina saboda ba karamin so yake wa yarinyar ba “Mai nawal ta fiki ilimi kyau ko nasaba ko kudi da zaki shiga damuwa akan shigowarta “?”Ki bani amsar tambayoyina numfashi ta sake saukewa ta tsurawa yar’uwata kuma matar yayanta uwa guda uba guda ido sannan ta girgiza mata kai “bata fini ko daya ba sai da munanan kalamansa gareni yana sani jin kamar tafi ni komai tunda ita yana sonta ”
“Ciwon rashin sonki shine babbar matsala da zai kawowa rayuwarki shamaki sai dai kisani kowa ne dan adam akwai ciwo acikin rayuwarsa kawo kunnenki kiji wani abu kisna ta mika mata kunnenta murmushi ne ya subuce mata “babu abinda ban masa ba aunty har takai ta kawo ma daidai towel baya son ganina dashi hatta kwanciya guri daya baya yi dani duk abinda nasan zanyi dan na janyosa gareni nayi amman yaki ni gara kawai ayi ayi auren na cigaba da zaman biyayyar da naki yiwa iyayena a tun farko”.
“Ai duk kece kika cutar da kanki kisna “uhmmm ta sauke numfashi karki tuna min abinda ya faru aunty wallahi nasani shiyasa wani lokacin idan yayi min wani abu konaji haushinsa sai na dawo na huce “Kinga share tunaninsa da tunanin aurensa taso muje muyi kallon kwallo ta kamo hannunta suka fito zuwa filin kwallo .”
Tun kafin su karaso kisna ta hango Aliyu da Samir sun hada gumi da sauri ta juya” ina kuma zaki ? inji cewar aunty zee “ruwa zan dauko musu ko cikakken minti biyar batayi ba ta dawo hannuta rike da roban ruwa guda biyu da kananan towel ta mikawa aunty zee daya sannan suka karaso gurin a daidai lokacin da Samir ke kokarin cinye Aliyu yayi saurin kwance kwallon da ƙafarsa Aunty zee ta dauki husir ta hura tana murmushi “to ku huta haka dan da alamun babu wanda yaci suka tsaya suna fidda numfashi rike da kugu, aunty zeey ta karasa kusa da mijinta ta shiga goge masa fuska zuwa wuyansa …”
Hakan yasa kisna cikin sanyi jiki ta karasa kusa da Aliyu ta kai hannu daidai kunnesa zata goge masa fuskarsa dake tsiysyar gumi ya juyo ya watsa mata idanunsa masu matukar kyau da haske take gabanta ya shiga dokawa duk ta daburce taji kamar ta saki towel din ta falla da gudu . hannu ya kai ya amshi towel din hannunta idanunshi na kanta ya soma goge fuskarsa bayan ya gama ya mika mata , ita kuma ta mika masa roban ruwa saɓanin aunty zee da a baki ta bawa ya Samir ya sha.
tun daya d’aura bakinsa akan goran ruwan bai sauke ba sai daya sha rabi sannan ya mika mata sauran suka ci-gaba da buga kwallo yayinda su kuma suka samu guri suka zauna a gefe akan fararen kujeru suna Kallonsu a hankali kisna ta tsurawa mijinta ido tana kallon yadda yake sarrafa kwallo kamar dan shi Allah ya haliccesa duk wani siffar karfi dake jikinsa ta gama bayyana burinsa kawai ya cinye Samir cikin sauki , yadda surar jikinsa take cike da karfi haka yake da mazakunta, karfi garesa kamar doki , sautin muryar aunty zee da ya karade gurin ya dawo da kisna daga duniyar tunani” Samir isa goal ta rungumeshi ajikinta tana murna “Allah yayi yau Samir ya cinye ya Aliyu ….”
Aliyu dake tsaye rike da kugunsa da hannunwansa duka yaja dogon tsaki yana kallon kisna dake dafe da goshinta tana kallonsa dan sam bata ji dadin cinyesa da Samir yayi ba shi da yake bugawa wasa kasa da kasa kuma ya cinye har yanzu da yake kan ganiyar buga kwallo babu kasar datayi nasarar cinyesa sai wannan karon da Samir ya lashe aunty zee ta sake hura husir “baby ka kara masa daya dan Allah “aliyu ya haɗe rai bazan yi ba ,a tunda kika dad’d’ako min wannan nasan bazan yi nasara ba ya juya fuuuuuu a zuciye ya soma tafiya Kisna tayi saurin d’agowa tare da dafe kirjinta idanunta suka cicciko da ruwan hawaye “ke dan Allah meye abun kuka “? “Ki barta hawayen ne suka mata yawa inji ya Samir take ta maida kukanta tana sauke numfashi tare da tsuke karamin bakinta tana shesheka sannan ta mike ,tare suka jero suka fito daga filin kwallo suna fitowa haraban gidan ya fito sanye da riga pink da gajeren wando iya gwiwar ya nufi gurin motarsa escort d’insa na ganinsa suka taso yayi saurin daga musu hannu take suka kame ya danna mukulin mota haɗe da bude murfin ya shiga mai gadi ya bude masa ya fita a guje ..
Ganin yadda ya fige motar da gudun maseefa Yasa kisna fashewa da wani kukan mai cin ranta , hankalinta yayi matukar tashi tsoro tattare da fargaba ne sukayi nasarar lullube ilahirin jikinta, abubuwan da yake mata sun fara isarta amman ta rasa yadda za’tayi dashi ita meye laifinta ita tace samir ya cinyesa ko me”? takaicin haka yasa ta durkushe bisa gwiwowinta ta kife kanta bisa cinyoyinta tana sake risgar kuka mai cin rai da suma zuciyar ma’abocin sauraro har aunty zee zata mata magana Samir ya dakatar daita “ki tashi ki shiga ciki kin dai san halin zuciyarsa ba karamin aikinsa bane ya dawo ya sameki agurin nan ya kara miki da duka , yana gama fadar haka ya ja hannun aunty zee sukayi bangarensu ..”
A hankali ta mike ta shiga part d’inta tana goge hawaye kai tsaye kitchen ta shiga ranar ma bai ci abincinta ba haka bai yarda ta kusanci inda yake ba dan har gargadi yayi ma tare da rantsuwa “wallahil azim idan na farka na jiki ajikina ko kusa dani sai na miki abinda har ki mutu bazaki manta dani ba tasan shi tasan halinsa shiyasa tana kammala abubuwanta ta kama kanta ta kwanta akan kujera..”
********
Bayan wata uku
Duk wani abinda za’a bukata na kayan auren nawal Aliyu yayi ya sakarwa aunty zee kudi masu yawa domin hada kayan lefe koda ta tambayeshi na kisna cewa yayi bazai mata ba har zatace bazata haɗa masa ba sai taga rashin dacewar hakan , duk abinda ya kama tun daga kan dogayen rigunan da takalma da jakakkuna turaruka anan egypt ta siya ,ta tura kudin atamfofi da lesina da wasu abubuwan daza’a bukata negeria tunda can za’a tura kayan lefen dan amarya ma tuni tana Nigeria safy tazo ganin kayan lefe tayi mamakin bata ga na kisna ba, ba tayi kwaron baki ba ta tambaya aunty zee “ina kayan kisna na fadar kishiya .. “?shiru sukahi mata gabadaya dan rasa abinda zasu faɗa mata “tambayarku nake kun min shiru ina kayan kisna ko ita bazai mata komai ba “?Kisna dake kwance tana tunani ta yunkura ta mike zaune “bai min ba kuma ban damu ba saboda har yanzu ina da tarin kayan da ban yi amfani dashi ba “gaskiya wannan ba adalci bane ke kuma ba hujja bane dan kina da kayan da zakiyi amfani dasu ,yau ace Aliyu bashi da kudin da zai siya muku ku biyu ne sai ki ɗauki hakuri amman yana da ninkisu da ko mata dari zai aura a rana daya zai iya hada musu kayan lefe, gaskiya aunty zee ban ji dadi ba ya kuna kallon yadda Aliyu ke wulakanta kisna amman ku kasa ɗaukar mataki akanshi sai ma wani lalla’bashi kuke sai ya kasheta kuce zakuyi kuka ” idanun kisna ya cika da hawaye , aunty zee ta sauke numfashi tana cewa “safy kenan bazaki fahimta ba, lallashinsa shine mafi alkhairi idan aka yi wani abu na ɓacin rai idan dady ji zai iya janyo gagarumar matsala wannan auren iyayenmu na murna dashi fiyye da kowani aure babu yadda zamuyi duk yadda ya tsara lamarin gidansa haka zata hakura ..”
“Hakuri hakuri hakuri kullum shi ke kashe mata ko saka su kamuwa da wata mummunar cuta safy ta fada cikin ɓacin rai “karki manta hakuri shine jigon rayuwar duniya Allah yace kuyi hakuri lallai ni ina tare da masu hakuri ,hakurin shi karan kanshi aikin lada ne ba kuma kowa allah yake bawa baiwar hakuri ba inji cewar aunty zee.
“Haka ne Allah ya qara mana hakuri sai dai na dade dasanin kisan na cikin damuwa dan Allah ko zaki iya faɗa min abinda tahi masa har yasa yayi mata irin wannan muguwar tsanar “?
Shiru parloun ya ɗauka babu wanda ya sake furta komai “,ko kuwa ban kai matsayin da zamu iya sanin sirrin juna bane “?Kisna ta kalli aunty zee fuskarta dauke da damuwa safy ta kamo hannu kisna “dan Allah ki daukeni tamkar yaruwarki ina son sani abinda kika wa aliyu da har ya rikeki a zuciyarsa ya kasa hakuri ya kasa manta komai “?”Shiru still tayi ta kasa magana hawaye na kokarin zubo mata bata jin zata iya fadawa wani tahirinta da abinda yasa Aliyu yake mata wulakanci daya ga dama .”
“Ni da zuciya daya nake zaune da mutum kuma Allah ya sakamun jin damuwarki a ciki raina , bana zama da mutum don in yaudareshi ko qin fada mishi damuwata, abu daya na dauka cewan mutunci ya hadaka da mutum tou kuyi zaman haka. Mutunci na kawo yarda da juna wani zubin tana bada amana ma, kuma amana babban amincewa da mutum kesa aba mutum , kuma baya zama me kar6an amana alhalin bashi da kamala, dattaku, girmama na gaba, girmama na qasa, gaskia da haquri da halin mutane , Ina zaune dake tsakanin da Allah ba wai dan mazajenmu na matsayin aminai ba, amma wariyar da kike ta nunamun yau ya qureni wacce ni a wajenki? Shasha? Ko kuwa sakariya wanda zaki dinga 6ata lokaci daita ? Ko kuwa banza kike kallona? Ko mara illimi? Ko mara tunani? Ko mara sanin ya kamata? Ko kuwa yarinya qarama wacce bata san komai ba? Ko wacce bata san meye rayuwa ba? Duk abin da kike nunamin yana kunshe da wannan sannan rashin daukata yadda na daukeki yasa bazaki fadamun ba saboda kila bazan fada miki kiji ba ko bazan baki shawarar da ta dace ba ko kuma zan fallasa sirrinki ga wasu saboda kina mun kallon wawiya wacce bata san me take ba.
“A yau na yarda zaman da muke bashi da anfani kuma zaman da muke bana amana bane in dai bazamu ji damuwar juna ba ,mu bawa juna sharawa ba zaman munafurci ne.
“,Wallahi idan na tambayeki damuwarki kika ki fadamun bakisan zafin da nakeji ba amma sai in barki sbd kar in daga miki hankali ko takura miki, babu komai sabon sanayya game da rayuwa dama nasan irinta ,kuma bazan daina aminta da aminta dake ba , kuma bazan daina jin zafin ciwon dake damunki ba a kan Aliyu nagode sosai da yadda kika nunamun matsayina da kuma yadda kike zaune dani na rashin yarda , na hakura da son jin komai dan ko kin bude bakinki qarshe bai wuce kice “bazan gane abinda ya hadaki da mijinki ba ” Nagode sosai wlh tunda ta soma magana kisna take kukan zuci dana zahiri safy ta mike tsaye ta dauki jakarta ta rataya zata wuce kisna tayi saurin riko hannunta cikin zafin nama tana kallon aunty zee hawaye na gangaro mata..”
“alamar tayi magana aunty zee tayi mata dan haka a hankali tace ” kiyi hakuri ki zauna safy ba wai naki fada miki labarina ba ne dan ina tunanin wani abu ko zaki fallasawa wani illa bana son Tina abubuwan da suka faru dani sannan asalina ni mai zurfin ciki ce bana fadawa kowa damuwata idan ba mutun ne da kanshi ya fuskanci haka ba safy ta zauna tana kallonta cike da tausayawa ” safy abinda ya faru dani ciwo ne dake cin zuciya ,ni kaina na kasa yafewa kaina abinda nayi bare ya Aliyu ,damuwa kuwa muddin Aliyu bai sauko daga dokin nakin daya hau ba haka zan kare rayuwata cikin damuwa da garari tunda nasan dan ra’ayin kanshi bazai sakeni ba sai dai idan iyayena ne suka bashi umarni “safy Kowane dan adam akwai ciwon da Allah ke daura masa wani gurgu wani makaho wani kurma da sauran ciwuka da dama amman ni Allah da ya tashi sai ya jarabeni da ciwon kaunar wani halittan mutun a sheakaru goma sha biyar data gabata a lokacin ina jss one …….”
waiwaye ……..
Mmn sudais
💗💗💗💗💗💗
CUTAR DA KAI
💖💖💖💖
💗💗💗💗💗💗