Cutar Da Kai – Chapter Six
by Aysha A Bagudo~TRUE LIFE STORY~
*PAID BOOK*
*AYSHA A BAGUDO*
*MASU ƁUKATAR A TALLATA MUSU HAJOJINSU ZA SU IYA TUNTUƁARMU TA LAMBOBIN 07045308523 MUN GODE*
“Tunda nasir da matarsa suka bar gidan ta bashi magani ya sha ta kwantar da kanshi akan cinyarta ta d’aura hannunta ɗaya a qirjinshi tana shafawa a hankali zuwa fuskarsa tana yi masa sannu tana jin kamar ta cire masa ciwon ta dawo dashi kanta , idanunshi ya runtse gam yana sauke numfashi sama sama batare daya amsa mata ba “
“wani iri ya dinga ji a gaba-daya sansar jikinsa a lokacin daya tsinci laulausan tafin hannunta a saman qirjinshi tana shafawa ga kamshin turaren jikinta dake gauraye dana parlou’n duk sun buwayi hancinsa , itama hakan ce ta kasance gareta kamshinsa ya buwayi hancinta ji take tamkar su kasance haka har abada , sake runtse idanunsa yayi sosai har bacci mai nauyi yayi nasarar d’aukarsa a cikin mintunan da ba su wuce goma ba, ya d’aura laulausan hannunsa a saman nata yana sauke numfashi a hankali .
kyawawan idanunta ta zuba masa tana kare masa kallo tsab wani irin yanayin ta dinga ji a jikinta, da kyar take janyo numfashi tana fesarwa , dayan hannunta ta kai gefen wuyansa ta shafa har lokacin jikinsa da sauran hucin zafi ,kanta ta rankwafo kaɗan daidai fuskarshi tayi shiru tana shaƙar numfashinsa ,abinda ta tsani shakarsa ada shine yanzu ya zama muradin ranta , ko iya shaƙar numfashinsa kaɗai ya bata dama ya isheta k’arasa sauran rayuwarta da tai saura a duniya .
” a hankali take addu’ar akan Allah ya sausauto mata da zuciyarsa tare da fatan samun soyayyarsa koda bai kai wanda take masa ba , kusan minti talatin tana zaune tana kallonsa yana sharar bacci da alamun kamar akwai maganin bacci acikin magungunan daya sha dan ko daga hannunsa bai iya wa , sosai suke musaya numfashi juna batare daya sani ba , mutuwar da jikinta yayi ne yasa ta sake kusanta kanta dashi har lip’s dinsu na had’uwa da juna ,
tsawon lokaci ta ɗauka tana zaune tana kallonsa tana shaƙar
numfashinsa tana jin kamar ta kamo lip’s d’insa ta tsotsa ko kaɗan ne ,dan tana kwadayin sake jinsu cikin bakinta sai dai tsoro da tsananin fargaban abinda zai faru idan ya bude idanunshi ya kamata ya hanata aiwatarwa.”
da kyar ta daidaita natsuwarta cikin sanyi jiki ta zare jikinta ta d’aura kanshi akan pillow ta hau sama ta d’auko bargo mai taushi ta lullu’beshi sannan ta koma d’aki ta shiga bayi ta tsalla wanka haɗe da alwala ta fito ta goge jikinta ta buɗe wordrobe ta ɗauki wasu kayan ta canza tayi sallah ta sake gyara ko’ina a d’akinta ta d’auko turaren da take amfani dashi ajikinta ta feshe ko’ina , duk inda tasan yana kwanciya a cikin dakin sai data fesa turarenta har cikin bayi, ko’ina ya ɗauki kamshi turare sannan ta ajiye kwalban turaren ta sake dawowa parloun.”
A gabansa ta tsaya tana kallon yadda yake sauke numfashi yayinda a hankali zuciyarta ke bugawa tamkar zata fasa qirjinta ta fito waje ta ɗauke idanunta akanshi sakamakon wayarsa dake ringin cikin sanyi jikin nan nata ta kai hannu ta ɗauki wayar tana dubawa sunan Samir ta gani yana yawo akan screen ɗin wayar da sauri ta d’auka “hello ya samir barka da warhaka” ?
“Yes my lovely sweet sister ya kike ya mai jiki fatan ya samu sauki”?
“Alhamdulillah ya samu sauki gashi nan yana bacci ,”jikin dai nashi da sauki sosai ko”? “da sauki yaya mummy ta amshi wayar “kisna ya jikin d’ana “? kisna ta kwa’be fuska kamar zatai kuka “mummy ai ni fushi nake dake tunda na sauka a kasar nan baki kira kin nemi ba kullum sai dai kiyi waya da muradi “kinga sarkin shagwa’ba ajiye batun fushi nan muyi maganar jikin d’ana , ya jikin dana ? “ya ji sauki doctor yazo ya dubasa Kuma yace da zarar ya tashi a bacci zai sake samun sauki yanzu haka bacci yake” “okay naji dadi sosai dan nasan wannan mayatattacen ciwon kan nashi zai iya kai shi ga kwanciya asibiti Allah dai ya bashi lafiya ,ya dai zaman naku fatan dai babu wata matsala babu damuwa “?”Yes my sweet mummy babu damuwar komai , muna zaune lafiya dashi ,d’anki yana matukar bani kulawar data dace , baya son ganin ɓacin raina ,duk abinda nake so shi yake min ina jin dadin zama dashi sosai ,ko’ina zashi idan ba gurin aiki ba tare muke zuwa ,tare muke zuwa tsiyaya , babu abinda zance miki mummy sai godiya Allah ya qara nisan kwana na gode bisa ƙoƙarinki gareni, hakika samun uwa irinki a waannan duniyar tamu da kamar wuya ta karasa maganar tana sauke numfashi da ajiyar zuciya a tare “.
dariya mumuy tayi tace “iye lallai kin zama yar gatan haka muradi yake ji dake ni ina can cikin damuwar yanayin zamanku , duk da nasan zaki samu kulawa fiyye da haka daga garesa,” muradi yaron kirki ne ya fita dabam acikin mutane. ” “a saninki da tunaninki ba amman wannan dan naki mugu a duniya babu kamarsa tayi maganar a kasan zuciyarta tana jan numfashi da kyar .
“hello kisna kina jina “?
Numfashi ta sauke da karfi tace “ina jinki mummy , maganarki haka ne samun mai kyawun hali irin nasa da wuya ta fada tana dariya.
“ki zauna lafiya da mijinki kiyi masa biyayya kiyi masa duk abinda kika san zai faranta masa, yanzu muna wani zamani ne da ake lalla’ba maza bare miji irin naki mai tsananin tsada da samun irinsa da wahala, shiyasa kikaga bana son ki bar karkashinsa, dan Allah ki zauna lafiya da mijinki , ki rike shi amana sannan ki rike sirrin gidanki nasan kina da zurfin ciki ki ƙara akan wanda nasanki dashi muma inshallahu zuwa karshen wata ko sabon wata zamu shigo Cairo”.
wata irin qara ta saki na farinciki tare da furta “dan Allah mummy nah ?”inshallahu kuwa “kai amman mummy naji dadin wannan maganar sosai kamar ance ta d’ago idanunta inda yake kwance taga idanunshi fesa akanta ya bala’in haɗe rai tamkar wanda aka aikowa da sakon mutuwa tunda ta soma wayar ya bude mayatattun idanunshi akanta rungume da hannyensa a qirji yana kallonta, duk maganarta babu wanda bai yi nasarar shiga kunne shi ba ,haka nan ya tsinci kanshi da jin dadin abinda ta fad’awa mummy ko babu komai ta rufe wani sirri dake tsakaninsu “lallai kisna ta canza irin canzawar da’ake so, ina ma zai iya daya bata wani gurbi a cikin zuciyarsa kamar yadda ta bukuta sai dai ba zai iya ba dan shi yanzu burinsa bai wuce ya auri nawal ba saboda zamansa haka without having sex ya soma damunsa , kuma nawal itace matar data fi dacewa da rayuwarsa duk da bai tsananin sonta amman haka zai aureta “.
Idanunshi dake tsaye kyam akanta yasa gaba-daya ta rud’e , ta gigice a matukar tsorace tayiwa mummy sallama ta katse kiran ta mike tsaye jikinta na rawa ta k’arasa inda yake kwance ta ajiye wayar a inda ta ɗauka taja ta tsaya gabanta na faduwa da matsanancin karfi “ka….kayi hakuri dan Allah mummy ce ta kira kana bacci shine na ɗauka tana gaisheka ” ta karasa maganar a matukar tsorace .”
ɗauke kanshi yayi batare da ya ce komai ba yana ƙoƙarin mikewa tsaye , tayi saurin rikoshi ta karasa mikar dashi tsaye ta sanya hannuta daya a kugunsa sannan ta zagaye hannunta ɗaya a wuyansa wani irin shock suka ji a tare , a hankali
suka fara takawa suka nufi hanyar sama akan step taji ya dafa kafad’anta sosai ɗan ya samu damar takawa ta tsaya cak tare da waigowa a tsorace suka haɗa ido fuskarsa babu walwala ya d’age mata girarsa ɗaya alamun tambayar kallon mai take masa ? kawar da idannunta tayi da sauri ,yayinda shi kuma ya daga ƙafarsa ɗaya da kyar wani sanyin dadi taji yana ratsata kamar wata wawiya ta dinga daga kafafunta har suka shiga daki , kai tsaye bayi ta nufa dashi saboda tasan bai yi Sallar magrib ba ga isha’i ta karato ta taimaka masa yayi alwala suka fito ta kaishi gurin sallah “ka zauna kayi sallah a zaune saboda jikinki babu kwari”.
banza yayi mata ya tsaya bisa kafafunsa ya soma tada ikama ita kuma ta koma falon kasa ta gyara ko’ina ta shiga Kitchen ta wanke plet din da suka yi amfani dashi ,ta goge ko’ina dan tasan halinsa da rashin son kazanta sannan ta dawo parlou’n ta tattara kan magungunsa ta dawo sama wanda zuwa lokacin har sallar isha’i yayi yana ƙoƙarin tashi ta shigo d’akin ta karaso da sauri ta taimaka masa ta kwantar dashi akan gado tana yi masa sannu “sallar isha’i tayi ta dawo gefen gadon ta zauna tana sake jin tausayin kanta dan batasan ranar da zata fita daga cikin wannan kangin damuwar ba, ganin sai faman mika yake yana juyi alamun jikinsa yayi masa tsami , ya juya a hankali ya kife yayi ruf da ciki ,hakan yasa ta hau gadon sosai, hannunta na tsananin rawa ta kai bayansa ta fara shafawa a hankali jin bai yi magana ba , yasa ta canza salo zuwa massaging a natse ta dinga mammatsa masa sansar jiki tun daga bayan wuyansa da tsakiyar bayan kanshi har zuwa kasa gurin gwiwowinsa zuwa kafafunsa da tafin ƙafarsa “ya salam ya furta a kasan ransa dan sakonta yaje masa inda bai yi expecting ba , jin reaction din jikinsa ya fara sauyawa yayinda zuciyarsa ta fara bugawa da tsalle na kaiwa kololuwar sha’awa , cikin dakakkiyar muryarsa yace “stop……”
ya fada tare da sauke wani wahalallen numfashi.”ka bari nayi maka massagin zaka ji dadin jikinka ya juyo a zuciye cikin rashin sani gaba-daya ya zubo jikinta sai gashi a saman ruwan cikinta ita kuma tana kasan shi hannunta duka a saman qirjinsa daidai kan nipple’s d’insa , ya tsura mata idanunshi tare da haɗe rai , a tsorace ta cire hannuwanta ajikinsa ta zuba masa ido tana kallonsa , ya lumshe idanunsa yana furzar da iska mai zafi daga bakinsa kusan minti goma suna kallon juna tare da shaƙar numfashin juna batare da yayi magana ba, ya
kai hannu ya ɗauki pillow yayi cilli dashi kasa ya lalubo bargo ya jefar sannan ya gyara kwanciyarsa ya lullube jikinsa tun tana ganin motsinsa har bacci yayi awon gaba dashi ta lalla’ba ta d’auko bargo da pillow ta kwanta a dayan gefen , ta lullu’be jikinta ta runtse idanunta itama bata ɗauki dogon lokaci ba bacci ya ɗauketa ..
Washegari
A hankali ya soma buɗe idanunshi kawai ya jishi ajikinta da sauri ya k’arasa buɗe idanunshi yaji ƙafarsa akan kafafunta ya kanainayeta yayinda hannunsa daya ke saman kirjinta daidai dukiyar fulaninta da sauri ya cire hannunsa da ƙafarsa ya mike tare da matsawa baya ,yaji kamar ya sakar mata mari dan bakinciki ,” shiyasa fa baya son su kwanta guri daya waya sani ma ko yayi wasanin da jikinta “?
“Oh my goodness yarinyar nan tana son damun rayuwata saukowa yayi ya shiga yayi alwala yazo yayi Sallah ya koma kan doguwar kujera ya kwanta bata tashi ba sai gurin tara wanda wayarsa ce ta tasheta a bacci, ya kasa tashi ya ɗauki wayar har ta katse wani kiran ya shigo ta sauko ta dauki wayar ta mika masa ta shige bayi “hello my love aka faɗa daga can bangaren da kyar ya iya bude bakinsa yace “nawal ya kike “?
” Sorry na tasheka a bacci ko ya karfin jikin “?”Naji sauki ya za’a yi nazo na ganka ina son ganinka plz naga yanayin jikinka “
“Karki damu zaki gani dan nima ina son ganinki akwai abinda nake son muyi magana akai yana cikin maganar kisna ta fito daga bayi gabanta ne ya shiga faduwa da karfi ko ba’a faɗa mata ba tasan da wacce yake magana “?”Karki damu zaki ganni nima ina son ganinki ta sake maimaitawa kanta na kanta kalmar , ta dawo kusa dashi ta durkusa bisa gwiwowinta tana kallonsa kasancewarta agurin bai sa ya katse kiran ba sai ma cigaba da wayarsa da yayi daga karshe yace” me too tasan duk yadda akayi kalmar i love You aka furta masa idanunta yayi raurau da hawaye “dan Allah kace ka yafe min laifin dana maka sannan ka sake bani dama Ina sonka Aliyu mai yasa bazaka soni ba “?
“Bani da ra’ayin sonki , ko yin wata muamula dake ,ki rayu dani cikin wannan rayuwar ko ki rabu dani ki auri wanda zuciyarki ta kafu akan soyayyarsa tun farko ba damuwata bace , wannan da kika ji muna waya daita sunanta nawal nasan kina da labarinta itace matar da zan aura sai ki shirya zama daita idan fa zaki iya idan bazaki iya kofar gidan Aliyu a bude take “. yana gama fadar haka ya juya mata baya ta mike tsaye hawaye ya gangarowa daga idanunta kafafunta take d’agawa a hankali tamkar bata da laka ajiki “nawal ta furta sunan a fili dan Allah karki shigo rayuwarmu nida mijina yanzu ma yaya aka kare ,nasan idan kin shigo ko kallona bazai ba , har ta hau kan step zance zuci take ta shiga Kitchen ta soma kwabin fulawa dan yi masa samosa haka ta dinga aikin tana zance zuci tana hawaye tamkar wata mahaukaciya sabuwar kamu ,hawayen idanunta yaki tsayawa bayan ta gama samosa ta dibo arish ta bere ta soya da kwai sannan ta d’aura ruwan zafi .”
Tana tsaye a kitchen ya sauko parloun kasa fitowarsa kenan daga bayi jikinsa sanye da gajeren wando baki da farin singlet ,wuyansa rataye da farin towel yana goge fuskarsa zuwa wuyansa , yayinda kafafunsa ke sanye da bakin silifas yana tafiya yana goge jikinsa , kai tsaye kofar Kitchen ya nufa dan ɗaukar fury har ya kawo bakin kofa yaji sautin qarar dayan wayarsa dake ajiye a parlour tun jiya ,ya juyo ya dawo ya ɗauki wayar ya manna a kunnen “hello Samir ya garin”? ” da fatan komai lafiya ko ? lafiyata qalau na gaya maka fever ne kawai kuma anyi maganinta kaine aji farko fa ,daga can bangaren dady ya amshi wayar suka gaisa ya masa ya jiki “dan zazzaɓi ne kawai fa dady me yasa zai faɗa maka dan kawai ya tadda maka hankali “to ya saukin jikin “?”Yanzu lafiyata qalau inshallahu ma gobe zan fita zuwa office “okay naji dadin abinda kace ba damuwa za’a yi komai yadda ya dace samir ma zai shigo karshen wata tare da mummynku dole ayi tafiyar dashi gashi Samir din yace zaku je buga wasa spain ko “.?
“Eh haka ne dady “.
“to shikenan Allah yayi jagora idan kun dawo sai kuje hollond da Austaraliya ayi abinda ya dace “to shikenan dady sai anjima ya katse kiran ya shiga Kitchen kamshi ne ya bugi hancinsa ya zagayeta ya buɗe fridge ya ɗauki abinda ya shigo dashi ya fita ..”
shadaya da rabi na safe ta gama komai har da break fast ta gyara gidan ta hau sama tayi wanka dan zuwa lokacin tuni ya sauya kaya zuwa na gado wato kanana kaya zuwa wando da riga duk blue Black , tun ganiyar kuruciya bata sake ganinsa da manya kaya ba ,sai ranar daurin aurensu ,kuma tun daga lokacin bata sake ganinsa dashi ba, daga suit sai wondo da riga”.
wardrobe ta bude inda ta jera kayanta ta tsaya tana karewa kayan kallo ta dauki doguwar riga ja wanda aka tsaga bangaren kafarta ɗaya har zuwa cinyarta hannun riga daya dan tsiriri ne yayinda d’ayan hannun ya zamanto dogo ta taje gashinta ta fakashi a tsikiyar kanta tasa ribbon ta kama ta fito ta zuba masa chips da soyayyen kwai da tea Mai kauri ta kawo masa inda yake zaune yana danne danne a system ta ajiye “kayi break kasha magani ” gyaran murya kawai yayi ya cigaba da abinda yake ta juya zata bar gurin “ummmmm ummmmm ummmmm yayi sound din Kamar Waka ta juyo da sauri tana murmushi “kana magana ne “?
Ya d’ago ya bar abinda yake haɗe da tsura mata idanunshi “tana da damuwa a rayuwarta , daman haka take shi bai sani ba , shi da yake daukarta mai mugun girman kai da taurin kai da rashin son shiga lamarin mutane, a she abun ba haka bane shegen rawar kai ne daita kamar farar kura da surutun tsiya , yatsun hannunta ta kamo ta soma wasa dashi tana kallonsa , kawar da kanshi yayi yana jan tsaki bai gama takaicinta ba yaji ta soma waka har da dan rawa ..,”
“Omo walai if them pont gun to my head say make I deny you I go tell them say lallai Ni be lie.
“I fit spen all of my money on you (oh ho)
“Speed a couple million you (yeah yeah )
“Give you loving tell you say e don do (yeye)
Special type of felling that I feel when am with …….
” Enough dan Allah Malama bana son hauka anan ya fada a tsawace yana watsa mata kallon banza ” shiru tayi tana dubansa kamar ruwa ya cinyeta ganin ya hassale tace “kayi hakuri dan…… ” jeki dan Allah banason hayaniya kin wani cika min kunne da banzar waka da wata muraryarki gangarin da bata dadin sauraro ,tsimi tsimi ta bar gun tana tabe baki ,yace ” mahaukaciya kawai ji yadda take faman wangale baki kamar wata shasha ya yaja tsaki tare da maida kanshi a kan computer..
Tunda ta koma sama ta kwanta lamo tana tunanin rayuwa bata sake yunkurin saukowa kasa ba , sai misalin karfe huɗu na yamma , shima gabanta taji yana ta faman faduwa da bugawa ,ta sauko a natse take daga kafafunta , aiko idanunta suka ci karo da mugun abu ,dan kuwa wata matashiyar mace ta gani zaune a gefen mijinta ,sanye cikin doguwar riga blue black wacce aka yiwa aiki da zare milk colour a gaban rigar da hannun rigar , ta nad’e kanta da mayafi milk colour ,haka kafafunta sanye da takalmi blue black da ratsin milk colour , shekarunta zasu zarta nata a haihuwa, tana rike da yatsun hannun Aliyu cikin nata tana murzawa tare da yi masa sannu .
a hankali ta dinga takowa jiri na dibanta har ta karasa saukowa “Allah sarki my love sannu kaji Allah ya baka lafiya kaga da muyi aure bazan taba barinka kai kadai ba ,dole ina tare da kai a cikin wannan yanayin , kusan abinda tafi furta masa kenan ,yayinda kisna ke binsu da wani irin kallon mamaki “a gidan aurenta wannan film din ke faruwa ?” Take zuciyarta ta dinga tuttukin tana zafi da ciwo taji kamar taje ta rufeta da duka har sai taga bata mosti, sai dai sanin cewa bata da wani power agurinsa yasa ta d’auke Kanta akansu ta nufi kofar shiga kitchen zuciyarta na wani irin tsalle da rad’ad’i , tana gama shiga ta danne lip’s d’inta na kasa da hakorinta da karfi tamkar zata fasa lebanta “ya Allah me ya kamata nayi yanzu “?”Na ɗauki mataki akanta ne ko kuwa na hakura na kama girmana ?”Ki hakura ki kama girmanki kisna idan abu mai kyau tayi miki da sannu zata ga sakamako, idan ma akasin haka ne shima zata girbi abinda tayi tunda itama macece “mai yasa kika zo gidana ?” Ta sake furtawa a fili
“Mai yasa bazaki bari har sai kin kasance mata a garesa ba ?”
“Mai yasa na sauko? ” da nayi zamana a sama da ban haɗu da wannan tashin hankalin ba , cikin sheshekar kuka take waɗan zantuttukan “mai yasa Aliyu ?kasan ina tsananin sonka dole zanji babu dadi a raina idan naganka tare da wata “. “mai yasa ka bata dama zuwa inda kake alhalin kasan kana da mata ?”Mai yasa zaka min haka Aliyu ?”Why! why!! why !!!do you this to me Aliyu ?”.
“A cikin soyayyar da nake maka har yanzu ban bayyana maka rabi daga ciki ba, ka tausaya min kar zuciyata ta tarwatse akanka ” na fita sonka da bukatarka , zan sadaukar maka da dukkanin farincikina , ka yarda dani dan Allah ka bani dama akwai sauran lokaci da zan gyara zamantakewar mu ,Aliyu duk abinda nayi maka ba yin kaina bane , zugar aunty afra ne gashi tasa na dasa kiyayyata acikin zuciyarka tun daga zamanin kuruciyata har zuwa auremu ,plz forgive me and forget what I did to you ,nasan kayi tsananin fushi dani ne shiyasa baka shayin aikata mummunar abu gareni ,sai dai bazan iya ɗaukar zuwan wannan matar gurinka ba ,I will be able to handle this situation tana cikin wannan halin ya shigo kamar an jihosa bataji motsin shigowarsa ba sai tsayuwarsa a gabanta taji yana huci tamkar mayunwacin zaki”uban me kike yi ?
“Ko baki ga anyi bakuwa bane da zaki wani tsaya batawa kanki lokaci ki kawo mata wani abu ta sha “.
Tayi saurin gyada masa kai tana goge hawayen dake kwance akan kuncinta “da kyau kuka ba ?”. ya fada yana kai hannunsa ya dago ha’barta Yana kallon cikin kwayar idanunta tayi saurin girgiza masa kai alamun “a’a “.
“uban meye wannan idan ba hawaye ba da zaki ƙaryatani ?”Shine amman kayi hakuri bazan sake ba ta fada muryarta na rawa ya ingiza ta baya da iyakacin karfinsa tayi taga zata faɗa tayi saurin rike Kitchen cabinet ta tsaya bisa kafafunta tana sauke numfashi da kyar “haka nake so kullum nayita ganin zubarsu har zuwa sanda zuciyarki zata buga ki mutu ……”.Ya karasa maganar yana sakar mata tsadadden
murmushinsa ,”minti a shirin na baki ki shirya mata abinda zata ci yayi baya kaɗan yana kallon falon “my nawal mai zaki ci ?”…..
Mmn Sudais
💗💗💗💗💗💗
CUTAR DA KAI
💖💖💖💖
💗💗💗💗💗💗
~TRUE LIFE STORY~