Cutar Da Kai – Chapter Seven
by Aysha A Bagudo*PAID BOOK*
*AYSHA A BAGUDO*
*MASU ƁUKATAR A TALLATA MUSU HAJOJINSU ZA SU IYA TUNTUƁARMU TA LAMBOBIN 07045308523 MUN GODE*
Tambayar da yayiwa nawal yasa ta mike tsaye cike da yauki da rausaya ta soma takowa zuwa bakin kofar Kitchen din ,ta tsaya a gabansa tare da rungume hannuwanta duka a saman qirjinta ta tsura masa idanunta tana kare masa kallo ,ganinta tsaye a gabansa yasa kisna juyawa da sauri tana danne kukan dake shirin kufce mata dan babban abun kunya ne gareta ta bar nawal taga hawayenta ko damuwarta “me zaki ci a dafa miki my nawal ?”. sautin muryarsa ta doki dodon kunnen kisna ,take zuciyarta ta cigaba da dokawar da take a tun sanda ya shigo kitchen din , cike da sihirtaccen kaunar da nawal take wa Aliyu ta sake matsowa jikinsa tamkar zata shige masa ta kai hannunta ɗaya ta shafi gefen fuskarshi cikin shaukin son shi tare da jin dadin kulawarsa gareta “tabbas Aliyu na matukar sonta tunda har zai iya mata irin wannan karramawar a gidansa”.
“i love You so much my love ta faɗa tana kashe masa idonta ɗaya “I love you too my nawal ki faɗa min abinda kike son ci “?nawal ta saki murmushin jin dadi tace “my love karka takura min kanka da auntyna banason wahalar da…..”
Aliyu bai barta ta k’arasa maganarta ba ya katse mata hanzari “nasan halinki da rashin son cin abinci just tell me what you … ..”
itama saurin katse shi tayi ta hanyar sakala hannunta cikin tafin hannunsa ta soma masa tafiyar tsutsa yayinda idanunta ke kanshi ta soma tafiya da baya da baya dashi , tana masa magana a shagwa’be .
“Cikina akoshe yake my love if not da zan so naci wani abu a gidanka kodan na sake faranta maka “. wani irin yanayi na zallar sha’awa ya tsinci kanshi ciki gabad’aya tsigar jikinsa ta mike gabadaya mazantakarsa ta motsa abunka ga lafiyayyen namiji ya sausauta muryarsa sosai kana yace”ok my nawal ” .
a sukwane kisna ta juyo idanunta ya sauka a cikin na nawal sakamakon fuskarta na kallon kofar Kitchen , murmushin gefen baki kisna ta sakar mata tana mai danne abinda taji ya sauka a tsokar dake makale da qirjinta ,itama nawal din murmushin barikanci ta sakarwa kisna tana sake shigewa Aliyu kamar zata ratsa gangar jikinsa .
“Yau naga abinda yafi karfina , anya kuwa rayuwata zata d’aure a gidan nan idan wannan yarinyar ta shigo ? ta yiwa kanta tamvayar haɗe da kawar da fuskarta hawayen bakinciki na gangaro mata .”inna lillahi wa inna ilaihi rajiun kawai ta shiga furtawa tana maimatawa domin neman sausauci daga gurin Allah …”
Nawal ta zaunar da Aliyu sannan ta zauna suna fuskantar juna ta matso da fuskarta sosai suna shaƙar numfashin juna bai an kara ba yaji saukan lip’s d’inta akan lip’s d’insa tana yawo dashi a daidai lokacin da kisna ta sake juyowa gabanta yayi wani irin mummunar fad’uwa ,ta dinga jin kamar zuciyarta zata kama da wuta, Gabadaya yanayinta ya sauya , numfashi ma da kyar take janyowa tana fitarwa zuciyarta na wani irin tuttukin bakincikin , ta ɗauki wuka tana kallonsu “naje na tsoka mata wukar nan a kahon zuciya na kashe shegiya na huta .”No no karki yi haka wannan ai haukan kishi ne ,”to bari na d’aura ruwan zafi nayi mata wanka dashi ta soma ƙoƙarin kunna gas “kai shima wannan ba mafuta bane gara ki nemo abinda zaki mata cikin sauki ki korata ta sake maida idanunta akansu zuciyarta na wani irin zafi da ciwo .”
Aliyu na shirin kawar da fuskarshi yaji ta cafki bakinsa ta soma tsatsa kamar ta samu sweet , kisna tayi saurin runtse idanunta tare da yin kasa dafe da kirjinta dake tafarfasa tamkar an daura mata wuta , Aliyu ya kasa hana nawal aiwatar da abinda take so akanshi saboda feeling din da yake ji yana ratsa sansar jikinsa , batare daya ce mata uffan ba ta cigaba da sha bakinsa tana sauke numfashi dan wani irin sanyin dadi taji yana ratsata da kai wa kwalkwaluwarta sako na musamman ,wannan shine karo na farko da suka fara musanyawar yawu a tsakaninsu kuma kowanensu yaji sauyi na dabam ajikinsa shiru yayi ya cigaba da amsar sakon nawal bisa ra’ayinsa guda biyu na farko ragewa kanshi feeling , na biyu kuma dan ya sake tarwatsa zuciyar kisna tasan yana da martaba da darajan da za’a so shi……”
sai data tsotsi bakinsa sosai kafin daga baya ta saki tana sauke numfashi , shi kuwa komawa yayi ya jingina bayansa da kujera yana fidda numfashi “na matsu sosai my love , burina bai wuce mu kasance ma’aurata ba , yayi mata shiru yana lumshe mata ido dan shi kadai yasan yanayin daya tsinci kanshi a lokacin da take tsotsan bakinsa a hankali ya bude idanunshi akanta ya lura gabad’aya yanayinta ya sauya da gani da za’a wuce shan baki bazata hana ba ,shima ya kai zuciyarsa nesa ne bancin haka da yaso ya murza dukiyar fulaninta a tare suka sauke numfashi suna kallon juna yayinda kisna Ke kai sosai har da shesheka zuciyarta na zafi “mai yasa bazai soni ba ,bayan ina da duk abinda yake so …?”Dan Allah ya Aliyu ka tausaya min wallahi zan kasance maka yadda kake so ,zan baka farinciki da kwantar maka da hankali ,zan kula da kai ,zan baka rayuwata hatta numfashina zan iya sadaukar maka dashi ka tausaya min ta karashe maganar tana wani irin kuka mai ban tausayi “.
bayan kamar minti biyar kisna ta goge hawayen dake kwance akan kuncinta ta fito a natse tamkar bata tare da wani damuwa hannunta rike da jug ɗauke da ruwan sanyi ta ajiye a gaban nawal batare data kalli inda take ba hatta aliyun bata kalleshi ba ,ta juya a hankali tana taku tamkar kazar da kwai ya fashewa a ciki ta haye saman d’akinsu , zariya ta shiga yi a cikin d’akinta tana zance zuci kanta kamar zai tsage gida biyu tsabar bakinciki, kwakwaluwarta ta shiga cajin da tunanin neman mafuta ,dan dole tasan abunyi tun lokaci bai mure mata , idan ta bari wannan yar iskar matar nayi mata karuwanci a gida tun yanzu shinkenan zata rainata kuma kashinta ya bushe , tana tsaye ya shigo d’akin kallo ɗaya yayi mata ya dauke kanshi aranshi yace “wahallaliyar banza kawai baki ga komai sai nayi nasanadin da zuciyarki ta buga ya soma cire kayan jikinsa ya ɗauki towel ya taraya a wuyansa da alamun wanka zai shiga ,take ta sauke wani wahalallen numfashi , wani dadi ya lullu’beta ta samu damar da zata fattakar wannan yar iskar mata a gidanta ,yana gama shiga bayi ta fito daga d’akin ta kulle kofar ta bar key ajikin ta dawo parlou’n kasa inda nawal take zaune , wani irin mugun kallo mai haɗe da harara ta sakar nawal dake zaune kafarta ɗaya akan ɗaya tana girgizawa tana sake karewa falon kallo , gabanta ne yayi mummunar fad’uwa da ganin irin kallon da kisna tai mata , a hankali ta motsa bakinta “sannu da …….”.Kisna tayi saurin katse mata hanzari ta hanyar d’aga mata hannu “sannun uwarki da ubanki zaki min amman dai ke anyi tsohuwar kilaki tsohuwar yar tasha ,jaka shasha ballagaza da bata san ciwon da darajan kanta ba , yanzu har rashin kamun kanki ya kai ki kwaso waɗan nan tsilla tsillan kafafun naki kamar na jemage ki zo gidan saurayi ? nawal ta cika da tsananin mamakin kisna ta buɗe baki zatai magana kisna ta sake d’aga mata hannu “dakata malama bana bukatar jin komai daga bakinki ,idan ki kayi ganganci bude wannan dan iskan bakin naki sai na lahira yafiki jin dadi dan sai zubar miki da haƙora , maza maza second biyu kacal na baki ki tashi ki bar min gidana kafin na tura miki wannan abun a gidan kashinki dakikiya mai fuskar alade ta nunata da sekundireba ………..
“an gama yawon tazubar da karuwanci an rasa mashin shini shine za’a lekewa mijina ,na sake ganin waɗan kafafun naki masu kama dana jemage sai na lalata miki rayuwa , ai wallahi Allah ya taimakeki da kinci abincin gidana da kin tabbatarwa kanki mutuwa, domin guba zaki ci oya out ta kai hannu ta janyo wuyan rigarta ta soma tafiya daita bata tsaya a ko’ina ba sai a haraban gidan ta saida ita a jikin motarta “to be your first and last warning da zaki tako zuwa gidana a matsayinki na karuwa ,ki tabbatar da aure ne zai kawoki gidan nan ba karuwanci ba ta karasa maganar tana buga mata sikundireban hannuta a baki .
nawal ta saki ƙara mai sauti tare da rike bakinta cikin azaban zafi ta juya ta buɗe motarta ta shiga ta zauna zata maida murfin motar ta rufe ,kisna ta rike “bance karki faɗa masa ba ki faɗa masa dan girman Allah kiga yadda zanyi dake , wallahi sai kinga kudi kince kashi ne shashar tumakiya sannan kuma zaki iya cigaba da zuwa gidan bazan ce karki zo .”cikin rawar jiki nawal ta bar gidan tana zubar da hawaye “
kisna na ganin tafiyar motarta ta saki murmushin jin dadi “kadan kika gani wawiya ta juya da sauri taje ta buɗe kofar ta dawo parlou’n kasa ta zauna tana kallon tv qirjinta na bugawa da karfi a natse ya sauko falon yaga wayam babu nawal babu alamun , yace” ke ina yarinyar nan “?.
“Wacece haka ? Ta tambayesa tana hura hanci “Banason iskanci nasan kinsa wacce nake nufi yayi maganar a zafafe yana tsareta da idanunshi “to ni ina zansan inda take tayi maganar a shagwa’be mutumin dake zaman kansa har a tambayi inda yaje “wacece ke zaman kanta ? yayi maganar yana ƙoƙarin damkar makoshinta ta goce haɗe da mikewa tsaye tayi nesa dashi kirjinta na bugawa …”Wallahi ki kiyayeni idan ba haka ba zan bata miki rai “to ni me na maka kodan ban da gata shi yasa kake min abinda kaga dama ? Ko Zaman daduro muke da kai ya dace ka gayyato budurwarka gidan nan har ma ku zauna kuna iskanci alhalin ga matarka sunanh a gidan ?
“Da wa kike wannan Maganar ya kara taku biyu zai cafkota ta buge hannunsa ta zura aguje “ni ka kyaleni karka dokeni bata tsaya a ko’ina ba sai a karshen step tana haki tana hura masa hanci …”
“Zaki sani ne kuma zan kamaki cikin ruwan sanyi , zaki san baki da kunya dan wallahi sai na fasa bakin rashin kunya, kuma ki bari na kira nawal naji tace kin mata wani abu sai kin gane baki da wayo kamewa tayi guri daya ta rungume hannuwanta tana kallonsa tana fargaba, tasan idan nawal ta fada masa abinda tayi mata sai ya mata dukan mutuwa dan haka ta tsaya jira ya kirata taji yadda abun zai kaya ,idan taga dukan zai yi ta shige daki ta kulle ta barshi yayi kwanan falo ..”
Tana kallonsa ya dauki wayarsa yana ƙoƙarin neman layin nawal kiran cochi dinsu ya shigo ya zauna yana amsa wayar ” hello Mrs birsat kwana biyu bamuyi waya ba, ya kake ya kwana biyu ?”. “yanzu kake nufi to shikenna ka dan bani lokaci zan kiraka back …”ya katse kiran yana neman na Samir…
Bayan sun gama waya da Samir ya sake kiran mr birsat yayi masa bayani komai a natse sannan ya soma neman nawal ,tana ɗauka yaji gabad’aya muryata ta sauya “me yasa kika wuce bayan nace ki jirani ?
“Kayi hakuri dan Allah na samu kiran gaugauwa ne “akwai kiran gaugauwan daya fi dokata mahimmanci? ” kin fa san banason saba doka “kayi hakuri bazan sake ba yayi shiru yana kallon kisna dake tsaye tana kallonsa can yace “me yasa muryarki ya sauka kamar ma kuka kika yi ?”No babu komai fa wallahi mura ce ke son kamani Kuma nasha magani “ke dai ki faɗa min gaskiya idan akwai wani abu “babu komai ta fada a takaice tana danne kukanta duk yadda Aliyu yayi daita ta fada masa abinda ke damunta taki saboda taji tsoron gargadin kisna ..
******
Kwance yake akan gado hannunsa rungumeta da pillow yayinda idanunshi ke kallon celling d’akin, sosai yayi zurfi cikin tunani wayarsa ce ta ɗauki qara ya kai hannunsa ya lalubo wayar yana dubawa sunan daya gani yasa ya ɗan mike ya jingina bayansa da abun gado “assalamu alaikum “
“Wa’alaiki salam mummuy anyini lafiya “lafiya ya jikin naka jiya samir yake faɗa min baka da lafiya ? Cikin kwantar da murya yace “jiki alhamdulillah mumy naji sauki sosai “Allah ya qara sauki ka kular min da kanka fa ,ya amsa mata da “inshallahu mamana ya mutanen gidan ? “Duk muna lafiya ina ita kisna take ya d’ago ya kalli inda take kwance akan doguwar kujera idanunta na kallonsa, tun sanda daya ambaci sunan mummuy tayi shiru tana sauraronsa tana jin kamar tazo ta fixge wayar a hannunsa ta sake jin muryar mahaifiyarta .”
muryarsa a raunane yace” tayi bacci “okay inshallahu gobe zan kira ka haɗani daita su aryan sun damu suna ina son magana daita “okay suna kusa ne yanzu ko sunyi bacci “?
“Ai tun takwas sukayi baccin dole ,ya gyara zamansa sosai yana son jin dalilin baccin “mai ya samesu mumy “? yayi maganar hankalinsa a matukar tashe ” kasansu da kiriniya d’azu ne suna wasa a parlour daf da magariba sukai karo da juna , aryan ya fasa baki shi kuma areef goshi ,sai da muka dangana da asibiti shine fa muna dawowa sukai bacci ,amman tun jiya suke nacin kisna har d’azu da suka dawo daga makaranta , na faɗa musu muyi magana da mamansu shine suka samin kuka ……”
saurin runtse idanunshi yayi “kenan sun fi son mamansu dashi ?”ta yaya bazasu sota ba bayan sun rayu daita sama da shekara uku zuciyarsa ta faɗa masa haka “daita suka saba duka wata nawa kayi tare dasu ka barosu?”. numfasawa yayi sannan ya buɗe idanunsa akanta tana kallonsa ya katse kiran batare daya bata sun yi waya da mahaifiyarta ba ya ajiye wayar akan bedside ya koma ya kwanta ruf da ciki tare da rufe rabin jikinsa da bargo yana tunanin rayuwarsa ..”
“A cikin kwana ɗaya da yayi rashin lafiya zaka fahimci yadda ciwon yaci jikinsa baya wani cin abinci sosai sai kisna ta matsa masa sannan yaci” Kwanaki shadaya kenan da samun saukinsa wanda yayi daidai da sauran sati biyu mummuy da Samir da matarsa zainab da aryan areef su sauka a kasar sai dai har zuwa wannan lokacin suna gidan jiya ita da Aliyu babu wani cigaba da’aka samu a zamantakewar rayuwarsu , duk abinda kisna tasan zata yi domin ta karkato da hankalinsa garesa tayi ,amman yaki sakin jiki daita , yana dai iyakacin ƙoƙarin kyautata mata ta bangaren bata abincin barin wuta a kunne daina kulle gida da daidai sauransu ,
bangaren aurattaya ,hira a tsakaninsu wannan ma ba’a maganarsa, mari kuwa sai dai idan bata masa kuskure ba ,kuskure kaɗan zata yi masa yanzu ne zai ɗauketa da mahaukacin mari ,zamansu babu wani sha’awa tamkar ba ma’aurata ba, duk da ita kam tana iyakacin bakin kokarinta na ganin wani abu ya shiga tsakaninsu amman shi sai ya hauta da bala’i da zagi ,sai dai duk inda yake tana makale dashi wani lokacin ta rungumeshi ajikinta ta manna masa kiss a wuya ko d’aura hannunta akan jijiyarsa idan zai hauta da bala’i ta marairaice ta nuna bata sani bane , duk sanda ta rungumeshi kuwa haka zai zareta ajikinsa tare da nuna kyama da nuna mata ta fita hanyarsa “dan shi a yanzu bashi da lokacinta ,damarta ta rigada ta wuce kuma har abada bazata dawo ba yanzu ma yana zaune daita ne kawai saboda darajan iyayen .”
Sanye yake cikin black jeans with white t shirt kwantaccen sumar kanshi dake kwance har bayan wuyansa ya sha gyara sai sheki yake, hannunsa daure da agogon dimond sannan rike da wasu file ya kalli kisna dake sanye cikin abaya mai sharara sai dai acikin abayar wasu had’ad’d’un kananan kaya ne wondo da riga wanda a zahiri ake iya ganin kayan dake sanye ajikinta , ta nade kanta da mayafin kayan tamkar yadda indiyawan Pakistan suke yi , fuskan nata tar kamar wacce take shafa mata madara , wuya da azabar da Aliyu ke ganamata sam basu nuna ba, sai dai ta zabge ta rame sosai amman hakan bai sa tayi muni ba.”
Ganin yana ƙoƙarin barin d’akin ta sha gabansa da sauri tana fuskantar shi hancinsa ya shaki kamshin turarenta saurin lumshe ido yayi na second biyu sannan ya bud’esu tar akanta “nima za… zani gidan nasir wata uwar harara ya watsa mata sannan yace “daman nasan sai kinyi min shishigi tunda ke uwar yan neman gindin zama ce da cusa kai babu kwarjini ya fada yana jan tsaki tare da tsareta da kyawawan idanunsa , shiru tayi tana mamakinsa ita da duk abinda zatayi sai ya gwaleta duk wannan maganar da suke idanunta na kan jijiyarsa yayinda yanayinta ke sauyawa sake motsoshi tayi sosai kamar zata shige jikinsa kirjinta na dukan uku uku on-expecting yaji ta kai hannunta daidai saitin jijiyarsa dake kwance wani irin ɗauke numfashi yayi da sauri yana kallonta take tsigar jikinsa ya tashi ya dinga jin wani iri a Gabadaya ilahirin jikinsa mai kama da shocking , murmushi ta sakar masa mai narkar da zuciya tace “kana bukatar matarka Aliyu mai yasa zaka tauye kanka “? Cike da zafin rai ya buge mata hannu ya juya da sauri tayi saurin riko laulausan tafin hannunsa ya juyo a fusace “Are You mad “?. Ta fada yana zaro mata ido ,
ta kashe masa idonta ɗaya idan dai akanka ne tuni na amshi certificate , ta karasa maganar tana rungumeshi ajikinta ta fara shafasa numfashi ya sauke da karfin gaske ya zareta a jikinsa ya bar da’kin yana jan tsaki “aikin banza kawai duk abinda zakiyi a banza .
tana jinsa ta kwashe da dariya “kana so kana cutar kanka ,tun daya fita bai dawo gidan ba sai kwanciyar bacci , lokacin tana kwance akan gado ta haɗe pillows gabad’aya ta d’aura kanta akai haka bargon lullu’ba ta hadesu duka ta lullu’be gashi jikinta babu komai sai wata yar yololuwar rigar bacci iya gwiwa mai shara shara kai tsaye agogon hannunsa ya soma cirewa ya da’ura a gaban mirrow sannan ya soma balbale botiran gaban rigarsa ya cire ya zame wondonsa ya zauna akan kujera ya k’arasa zarewa ya shiga bathoroom ya soma wanka tana jin motsin shigowarsa ta share ta ci-gaba da baccin karyanta bayan kamar minti goma ya fito ya goge jikinsa ya sauya wasu kaya ya kira nawal suka sha hirarsu duk tana jinsa zuciyarta kamar ta kama da wuta , amman ta kudurta aranta zatayi hakuri ita yanzu har Allah Allah take ya aurota ma a wuce gurin sai daya gama abinda yake hankalinsa ya koma kanta ,a ransa ya furta matsala wallahi wannan yarinyar matsefa ce arayuwata ,k’arasowa yayi inda take kwance”ke..! Ke!! Shiru yaji ya kai hannunsa ya dafe goshinsa yana tunanin yadda zai ɗauki pillow da bargo kusan minti biyar yana tunanin abun yi kafin daga baya ya kai hannunsa daga saman kanta inda tayi double din pillow ya fara ja a hankali batare daya bari hannunsa ya taɓa jikinta ba , daman abinda baya so kenan jikinsa ya haɗu da nata , murmushi tayi ta sake danne pillow sosai da kanta ya ciza lip’s d’insa da karfi yana kokarin zaro pillow tayi wani juyi har bargon jikinta ya zame kayan baccin dake sanye a jikinta suka bayyana fuskanta na kallon nasa tana sauke numfashi a hankali, cak ya bar abinda yake ya tsura mata ido yana kallonta babu abinda baya gani ajikinta, tun daga kan dukiyar fulaninta dake tsaye cak tamkar ba’a taɓa sarrafasu ba har zuwa lafaffen cikinta wani wahalallen miyo ya had’iye haɗe da lumshe idanunsa .
sake gyara kwanciya tayi ta matso jikinsa sosai nan rigar tayi sama kaɗan cibiyar ta ta bayyana “,inna lillahi ya furta a fili tare da saurin runtse idaunshi yana k’arasa zare pillow ya ajiye kasa yana sauke numfashi .wata irin mika tayi tare da juya masa baya nan take bombom d’inta suka bayyana makale da wani siririn pent Wanda shi da babu duk ɗaya , a hankali ya ɗan bude idanunsa daya “subhanallahi ya furta qirjinsa na wani bugawa da matsanancin karfi ya dauko pillow daya ciro ya kare bombom d’inta yana sauke numfashi da ajiyar zuciya a tare a hankali ya soma jan bargo yayinda ita kuma ta rigada ta rike bargon gam yana ja madadin bargon ya dinga dawowa garesa sai itace ke dawo masa kafin ya ankare ta zubo jikinsa gabad’aya tare da d’aura hannuta daya a kan qirjinshi daidai nipple d’insa tana cigaba da baccinta na karya .runtse ido yayi yana ƙoƙarin zare hannuta daga qirjinsa ya fado jikinta gbdy jin tudun dukiyar fulaninta yasa jikinsa ya kama rawa tamkar mazari , shigewa jikinsa tai tana zagaye hannunwanta duka ajikinsa a firgice ya kalli fuskarta muryarsa a kausashe yace “ke ke …..!!! yana marin fuskarta da sauri ta cire hannunta tana dafe goshinta “aikin banza kawai ace mutun ko baccin arziki bai iya ba saboda rashin natsuwa”. yayi maganar yana jan bargo da karfi ya k’arasa kan kujera ya ajiye pillow Yana ƙoƙarin kwanciya yaji sautin muryarta “kai me ya kawoka inda nake da har ka kwanto jikina da zaka wani Kirani da kalmar rashin natsuwa “?
Wata irin zabura yayi ya dawo gareta yana girgiza kai sannan yace “lallai to me kike expecting zanyi da wannan jikin naki? ” yayi maganar a fusace yana huci tamkar mayunwacin zaki , tayi shiru jikinta na daukar rawa “sauko nan sai naji dalilin da yasa kika faɗa min wannan maganar “ganin zata ‘bata masa lokaci yayi gaggawa fincikota daga kan gadon ya sauko daita sauran kaɗan kirjinsu ta haɗe yayi saurin ja baya yana furzar da iska , eye’s dinsu suka haɗu cikin juna take zuciyarsu yai mummunar baguwa a tare “ance miki ni maye ne irinki ? “ko jikinki zinari ne da har zan kwadaitu dashi bare ki samu damar faɗa min magana “?
A hankali ta soma ja da baya saboda ganin jijiyoyin kansa sun mike kar ya ɗauketa da mari dan gashi zuciyarsa tazo wuya tasan kaɗan da aikinsa ya narkar mata mugun duka ko mari , ganin ya kara taku ta juya da sauri zata gudu aiko bai tsaya wata wata ba ya sa mata kafa sai gata ta fadi kasa dummmmmm wata irin razananniyar kara ta saki tare da kokarin mikewa ,ya sake saka mata kafa cikin tsantsar ɓacin rai “yar iska kawai mai muguwar zuciya kuma na rantse da Allah idan kika sake faɗa min makamancin maganar da kika faɗa min yanzu sai na miki azaban da ba’a taba miki irinta ba ya k’arasa maganar yana murje mata kafa, ita ba faduwar datayi kasa ko take mata kafarta yafi damunta ba kamar mugayen kalamansa, a tarihi babu wani mahalukin daya taɓa faɗa mata irin kalamansa rarrafawa tayi ta koma kan gado ta rakube jikinta tana kuka mai cin raina .
Shima Kwanciya yayi bugun zuciyarsa na karuwa sai dai bai damu da abinda yayi mata ba ,hasalima ko ajiinsa lalubo wayarsa ma yayi yashiga danne danne har bacci ya daukeshi ita kuwa kasa runtsawa tayi yadda taga rana haka taga dare har gari ya waye zuciyarta cunkushe take da bakincinsa ,Itace ta rigashi tashi kasancewar bata samu isasshen bacci kai tsaye bayi ta shiga tayi alwala ta fito ta dauki zani ta daura a saman rigar jikinta , ta sanya hijab ta tada sallah bayan ta idar ma bata koma ba zama tayi tana lazimi da kaiwa Allah kukanta har sai da gari ya waye ta waiga inda yake kwance a lullu’be so take ta tashesa saboda ya makara sallah amman tana jin tsoron tashinsa ,mikewa tayi ta sauko kasa domin haɗa masa break fast bayan ta gama ta shirya dining table dawo dakin domin tayi wanka ta sauya kaya wanda zuwa lokacin tuni ya tashi yai sallah yana zaune akan kujerar kushin ya da’ura kafarsa daya a kan daya yana girgizawa tare da yin shiru yana tunani , har ta gama abinda take bai daga kai ya kalleta ba, ta tsaya nesa da kaɗan dashi tana kallonsa taba son ganinsa cikin damuwa barin kuma ace itace silar damuwar dan tunaninta ko abinda ya faru jiya yake tunawa .
dan dawo dashi cikin walwalarsa yasa ta kaskantar da kanta da muryarta tace “kayi wanka kayi breakfast ina jiranka “bana ci a gidan nawal zan ci”? yayi mata maganar muryarsa a dake da kuma zumar ya ‘bata rai ai kuwa yayi nasara dan wani abu taji ya tsaya mata akahon zuciyarta mai kama da dalma ,kusan sai da kafafunta suka gaza d’aukarta Allah yasa a kusa da jikin bango take dan haka ta tsaya da kyar qirjinta na bugawa da karfi ..
a qalla ta ɗauki sama da minti talatin bayan tayi masa tayin abinci ya fada a gidan nawal zai ci batare daya damu da halin da zata shiga ba ,
wani lokacin gabadaya yanayinsa sauyawa yake kamar hawainiya .
tayi shiru tana kallonsa zuciyarta na mata wani irin zafi ,tunda take baa ta’ba mata cin fuska irin Wanda yake mata ba, sai dai ta danne zuciyarta ta nuna kamar abun bai dameni ba ya kalleta yaga kamar bata damu ba dan babu alamun damuwa a tattare daita shiru yai yana nazarin abinda zai sake mata da zai d’aga mata hankali .”
tana kallonsa ya tashi ya bude wardrobe d’insa ya dauki kayan da yake son sakawa ya dawo hannusa rike da iron da Kaya wando da riga duk bakake ya soma kokarin jona iron a wuta “jiki a sanyaye ta karaso inda yake tsaye a daidai lokacin daya Kai hannusa ya taɓa kasan iron din, yaji ko ya dauki zafi “kana jina ko kawo kayan na goge maka kayan da zaka saka kaje gurin nawal din ai bana kishi daita hasalima ma nafika son ayi auren ,yayi shiru kwakwaluwarsa na sake maimata masa abinda yace ” kawo ta sake magana a marairaice a matukar tsawace yace “bana so ko dole ne ?
“Dole mana gani bana aikin komai ai ni yafi dacewa nayi maka komai ta Kai hannu ta janyo kayan gabanta zata d’auki iron yayi sauri rike tsintsiyar hannunta “banaso nace da ke kike min da zaki wani ce na kawo ?ya fadi haka tare da wurgi da hannunta ya soma guga .
Ta sake matsoshi ya kalleta a wulakance bata damu ba tace “Da dabam yanzu dabam da baka da mata kusa da kai yanxu Kuma kana da ita to me zai sa kayi guga da kanka ? “duk fa yadda kake son zareni cikin rayuwarka dole ka hakura ka barni tunda ba iya rabuwa zakayi dani ba.”
Cak ya bar abinda yake ya waigo inda take tsaye kusa dashi a matukar firgice ya tsura mata ido yana kallonta itama idanunta ta tsura masa tana kallon cikin kwayar idanunsa tana jin zuciyarta na harbawa da sauri “Dan girman Allah banace ki fita rayuwata ba kiyi naki nayi nawa ba “? “Kace sai dai bazan iya ba dole ina na kasance da rayuwarka har zuwa sanda zan daina numfashi “ki daina shiga tsabgata , bari na fada Miki abinda baki sani ba kawai kina zaune a gidan nan just for nothing dan haka ki daina shiga rayuwata ” abu na biyu ni aliyu bana bukatar duk wani taimako ko kyautatawa daga gareki , dan bazaki taba samun cigaba a zuciyarta Aliyu ba muddin rai haka zaki kare rayuwarki a gidan nan baki da wani amfani agurina “.
wani irin yanayin mai wuyar misaltuwa ta tsinci kanta ciki take yanayita ya sauya zuciyarta ta dinga bugawa da sauri tana mata zafi ,Aliyu na jin dadin cin mutuncinta , wannan shine karo na sau babu adadin dayake tozartata yana faɗa mata duk abinda ya fito daga bakinsa hawayen dake makale a kwayar idanunta ne suka samu nasarar zubowa, kusan minti goma zuciyarta na wata duniyar da jin rad’ad’i da zafin zantuttukansa , yayinda shi Kuma ya cigaba da gugansa hankali kwance tamkar bai san da wata halitta a kusa dashi ba hasalima dadi yaji saboda fahimtar da yayi ya bata mata rai “.
Muryarta cike da kuka ta soma magana “duk da nasan kana yin haka ne dan ka kasheni da bakincikika amman zan cigaba da yi maka komai har sanda bakincikika zai kasheni ka huta ,zan maka komai koda kuwa bazakayi appreciate dinsa ba “kawo nayi maka gugan ta sake Kai hannu zata amsa iron din tana kuka , ɗauke iron din yayi da sauri yana mata wani mugun kallo mai cike da gargadi “kiyi duk abinda zakiyi a gidan nan babu ruwana amman idan yazo kaina karki yi saboda bana bukata,dan zukatanmu bazasu taba kasancewa tare ba kamar yadda kike tunani “. ya cigaba da abinda yake
Matsoshi tayi sosai hawaye na cigaba da gangaro mata ” babu ruwana da duk wani abinda zaka ce, zan tabbatar dana sauki hakkinka dake kaina ba wai kafi karfina bane kawai Ina kyaleka ne sabida abinda nayi maka amman ya kamata nayi abinda zai sa ka shiga hankalinka “komai zan maka sai ka gwaleni ,kaki ka bani dama na gyara kuskurena na baya , bansan me ye matsalarka ba “….
Kallon inda take yayi yace “da kyau yar hannu an zo gurin ai nasan zaki kasa jurewa ,sai dai matsalarki shine baki iya komai ba, sannan bakisan daidai ko akasinsa ba, komai kina yinsa ne tamkar na mahaukata .
zaro duka idanunta tai da sauri tana kallonsa hawaye na sake gangaro mata “yes ki daina wani zaro ido kamar am miki karya halinki na fada ,komai na dabbanci kike yi idan kin manta na tuna miki , shiyasa nake Allah Allah nawal ta shigo gidana dan ke daita akwai bambamci mai yawa, nawal ta fiki komai idan ma kyau kike takama dashi ta fiki ,haka idan ilimi ne tafiki phd gareta ke fa ?”Yayi mata tambayar yana cigaba da guga “just digre gareki amman Kika damu rayuwarki, bazaki taba kamo kafar nawal dina a komai ba ,dan haka na rokeki ki daina bata min lokaci kina batawa kanki,sannan matakin da zaki ɗauka wanda zai sa na shiga hankalina ina jiranshi karki canza ra’ayiki fa …… “.
tayi sororo tsaye gabadaya jikinta yayi sanyi da kyar take janyo numfashi tana fesarwa ta juya a hankali kanta na jujjuya mata da kyar ta dinga daga kafafunta “jina nan ……”ya fadi haka yana kallon bayanta ta tsaya cak batare data juyowa ba ” abokan aikina zasu zo anjima da yamma dan Allah ki yi wani Abu wanda zai nuna masu cewar ke din mahaukaciya ce kiga yadda zanyi dake stupid Kawai mai siffar aljanu “.
Tafiya ta cigaba yi har ta fita daga dakin hawaye na gangaro mata “,ya Allah ta furta cikin tsananin tashin hankali ” yanxu haka rayuwata zata cigaba da kasancewa “? ina zan shiga acikin gidan taji sanyi arana dan har wani duhu duhu take gani ,rasa inda zata shiga yasa ta fada bayi ta zauna aciki ta dinga risgar kuka kamar ranta zai fita yayinda kwakwaluwarta ke sake tariyo mata magangunsa masu kuna da ciwo ” wani hanya zan bi yanzu kafin ya kasheni ..”?
Mmn Sudais
💗💗💗💗💗💗
CUTAR DA KAI
💖💖💖💖
💗💗💗💗💗💗
~TRUE LIFE STORY~