Search
You have no alerts.
    The Den of Novels
    Chapter Index

    ~TRUE LIFE STORY~

    *PAID BOOK*

    *AYSHA A BAGUDO*

    *MASU ƁUKATAR A TALLATA MUSU HAJOJINSU ZA SU IYA TUNTUƁARMU TA LAMBOBIN 07045308523 MUN GODE*
    bismillahirrahmanirrahim

    ….Wani irin kyarma jikin mumy yake batare da sun fahimci haka ba saboda idanuwansu daya rufe, sai faman ya’bawa juna bak’ar magana suke cikin kunar rai ,
    A matukar fusace Aliyu ya katsewa kisna hanzarin “na fiki son rabuwa dake mumy nima na amince da tsarinta mu rabu kawai kowa ya huta , dan Allah mommy ki sanyawa zuciyarki salama kiyi hakuri ki bari mu bar rayuwar juna mu cigaba da zumuncinmu shima idan zai yiwu idan kuma bazai yiwu ba kowa ya kama kansa ya fada yana furzar da iska mai zafi daga bakinsa , wannan maganar data sake dokan kunnuwan mumy yasa taji wani mummunar faduwar gaba ya sake ziyartar jikinta , qirjin mumy ya dinga baguwa da tsananin karfi , duk wani tashin hankalin da take kokarin dannewa acikin zuciyarta sai daya fito fili saboda babu abinda ta tsana a rayuwarta kamar taji maganar rabuwa a bakin Aliyu dan na kisna mai sauki ne tunda sakin ba a hannunta yake ba ….”

    Aliyu ne ya fara lura da yadda jikin mumy ke karkarwa kamar mazari yayi saurin rikota cikin tsansnin tashin hankali yana kiran sunanta “mumy !mumy!!! dan girman Allah mumy ki kwantar da hankalinki “.a hankali ta kai hannu ta dafe daidai qirjinta da taji yana mata wani irin zafi da bugawa ” Please Karki min haka wallahi bana son na rasaki bana son wani abu ya sameki a dalilin rabuwata da kisna idanunta suka fara rufewa sakamakon kalmar rabuwar daya sake maimaitawa “mumy Please ki tamaineni ki bude idanuki me kike so ayi yanzu ? ” duk abinda kike so a shirye nake zan miki matukar zai sakaki farinciki cikin tsananin tashin hankali kisna take furta mata haka kafin daga baya Aliyu ya kwantar daita akan katifa ya mike cikin sauri gaba-daya ya rud’e ya gigice hawaye sun cika masa kwarnin idanunshi tamkar ba wannan Aliyu mai karkarfar zuciya ba ya fita daga d’akin , itama kisna hankalinta yayi matukar tashi dan kusan tafi shi shiga tashin hankali, take ta fara data sani maganarta da bata furta kalmar su rabu da mumy bata shiga damuwa ba ,wani sabon hawayen ne yazo idanunta ya fara zuba akan kuncinta tamkar an bude fanfo , a hankali ta fara rera kuka mai ban tausayi ,ta sake riƙe hannun mumy dake cikin nata gam yayinda hawayenta yaki tsayawa sai faman kuka take da kiran kalmar “na shiga uku cikin tsananin tashin hankali “mumy na tuba bazan sake ba, bazan sake furta kalmar rabuwa da ya Aliyu ba tunda bakya son rabuwarmu , ” ki taimakeni dan Allah karki mutu ki barni a gurinki kawai nake samun farinciki da kwanciyar hankali idan kika mutu kika barni rayuwa zata min muni, sosai take kuka tana rike da hannun mumy itama mumy ta rike hannunta gam hawaye na gangaro mata … …..”

    Zuciyar Aliyu na matukar zafi ya dawo d’akin hannunsa rike da goran ruwa bai tsaya tsiyaya ruwan a cikin cup ba ,ya ɓalle murfin goran da karfi wani zafi yaji ya ratsa tafin hannunsa inda yaji ciwo sai dai bai tsaya kallon tafin hannunsa ba ,ya soma shafa ruwa a fuska mumy yana kiran sunanta , naunayen ajiyar zuciya ta sauke sannan ta dinga sauke numfashi a hankali a hankali “sannu mumy suka hada baki gurin furta mata haka da kyar ta gyada musu kai idanunta na runtse ,Aliyu ya kamo kanta ya kai goran ruwa bakinta “ki sha ruwa mumy ” .
    Ta girgiza masa kai alamun bazata sha ba “dan Allah mumy ki rufa min asiri ki kwantar da hankalinki ya kalli kisna da idanunsa da suka rikice suka canza kala tamkar garwashin wuta ya soma magana cikin zafin rai “wallahi Idan wani abu ya same mumy a dalilin furucinki bazan taba yafe miki ba , kuma wallahi bazan cigaba da zama dake ba dole na yakiceki ta karfin tsiya daga jikina domin nafi bukatar rayuwa mahaifiyata akanki ya karashe maganar yana wurgi da rabon ruwa …….”
    kuka kisna take sosai tamkar ranta zai bar gangar jikinta tana rike da hannun mumy Sun yi matukar tausayawa halin da mumy take ciki , bazasu iya daukar halin da zata shiga a dalilin cikar burinsu ba …….
    Aliyu ya mike da hanzarin zai fita daga dakin domin kiran Samir dan sukai mumy asibiti ta rike hannunsa ya dawo da sauri ya daura hannunsa akan nata tare da zubawa mata idanunshi kamar zai yi kuka “mumy zanje na kira Samir ne mu kai ki asibiti” sake girgiza masa kai tayi ta zuba masa ido cikin sarewa tace “karku wani kai ni asibiti alhalin magani na gida , kune damuwata muradi , idan zanganku cikin farimciki da kwamciyar hankali wallahi nima zan kasance haka”bazan taɓa yarda da tsarinaku ba ,rabuwarku wani babban tashin hankali ne gareni bansan me yasa nake son kasancewarku tare da juna ba amma kafin na cigaba da magana ku amsa min wannan tambayar “?
    ta soma yunkurin mikewa zaune daga kwance da take jikinta na daukar zafi Aliyu da kisna suka kai hannuwansu da sauri domin taimaka mata hannun Aliyu ne ya riga na Kisna sauka a gadon bayan mumy sannan hannunta ya sauka akan nashi saurin kallon kwayar idanun juna suka tare da jin faduwar gaba mai tsanani zuciyarsu ta dinga bugawa a tare , zuwa wannan lokacin ko’ina ajikin Aliyu rawa yake yayinda zuciyarsa ke dokawa da sauri sauri fiyye dana Kisna , gabad’aya gabobin jikinsa sun yi sanyi, a hankali Aliyu yayi saurin janye kwayar idanunsa a kanta itama tayi kokarin dauke hannunta dake kan nashi suka yi shiru a tare suna satar kallon kwayar idanun juna ,karamin bakinta ta turo masa tana kashe masa idonta d’aya ..

    abinda tayi ya bala’i bashi haushi sosai and he don’t want any dilemma with her ko sake kallon inda take bai yi ba dan gani yake bata damu da halin da mumy take ciki ba kukan munafurcinta data saba ne …
    Cikin sanyin jiki ya kamo hannu mommy cikin laulausan tafin hannunsa tare da matsowa gefenta sosai itama kisna ta sake matsota suka sakata a tsakiya ya d’ago kanshi a hankali ya watsa mata harara itama batayi sanya a gwiwa ba ta mayar masa tana murgud’a masa baki yaji tamkar ya buge mata baki ko janyo ta ya yaryarfa mata maruka masu rai da lafiya sai dai ya kasa aiwatar da ko daya saboda shi a yanzu babu abinda yafi bukata kamar samun natsuwar mumy muryarsa a ƙausashe yace “malama ki dan matsa can mumy ta samu wadataccen iskaa kin wani manne mata kina kokarin …..”
    “kai ma ka matsa mana cikin ni da kai wa ya hanata shaƙar wadataccen numfashi ? ta kasheshi tana zabga masa harara ” nifa bana son damuwa dan Allah kowa yayi lamarin gabansa kawai zai yi magana mumuy tayi saurin d’aga masa hannu alamun yayi shiru umarninta yabi bai sake cewa komai ba ,mommy ta numfasa sannan ta cigaba da magana a tsanake” banason jin wata magana bayan amsar tambayar da zan muku yanzu “tsakanin kai da kisna idan kun rabu zaku iya manta junanku har duniya ta nad’e”?shiru ne ya sake biyowa baya , hatra d’akin ya sake daukar shiru tamkar babu wasu halitta acikinsa kisna ta d’ago idanunta a hankali ta kalleshi dan ganin yanayinsa wani kallo ya watsa mata wanda yasa take hantar cikinta kadawa , ta tabe masa baki qirjinta ya bugawa da karfin gaske .
    “ina tambayarku kun min shiru zaku iya manta junanku har abada ? Still shiru suka yi suna kallon mommy “Ni nasan bazaku iya manta junanku ba har duniya ta nade da tunanin juna zaku mutu amman idan amsarku ta kasance “eh zaku iya manta juna sai nasan abun yi ……..”

    Jin yadda suka yi shiru yasa ta waigo gefen da Aliyu yake da gefen da kisna take makale daita tamkar zata mata numfashi taga suna kallon juna tayi murmushi irin nasu na manya “mai yasa kuke kallon juna ku bani amsar tambayata mana kun min shiru suka sake yin shiru kowanensu na jiran yaji abinda d’an’uwansa zai furta “nasan baza ku iya amsa min wannan tambayar ba bari na faɗa muku abinda zai sa ku shiga hankalinku wallahi muddin kukayi kuskuren barin juna karshenku wahala mai tsanani ,kuma sai ta shafi rayuwar ya’yanku saboda zaku raba musu hankula , saboda kai Aliyu wata matar zaka aura kema Kisna wani mijin zaki aura kuma duk wanda zaki aura bazai kai uban ya’yanki ba ,hakazalika kai ma nawal bazata zama tamkar Kisna agurin su Aryan ba ,da zaran ta samu nata zata manta dasu ba kowace matar uba ke rike masa yaya tsakani da Allah ba ta karashe maganar tana sauke numfashi da kyar Aliyu ya sake tashi ya dauki goran ruwan da yayi wurgi dashi yaga da sauran ruwa aciki ya mika kai bakinta ta kurba tana lumshe ido “na gode muradi Allah yayiwa rayuwa albarka Allah ya yaye maka zafin zuciya “.
    “gara kan kina yi kina masa addu’a, wannan zuciya kamar ta mutanen farko ,zuciya a wuya kamar kuturu ba’a jin rarrashi bare hakuri kallonta kawai yayi ya furzar da iska tare da jan tsaki ,ta watsa masa harara tana hura masa hanci dan ta sake tunzura shi ,a ranshi yace kiyi duk iskanci da kika ga dama ganin idon mumy ne zamu hadu ne ..”
    “Kana magana ne ? tayi maganar cikin jan hankali .”

    “ke kisna ban son iskanci sa’anki ne”? tayi shiru “ki shiga hankalinki dan kice kika fara kawo zance rabuwa a tsakaninku da muradi bayan kuma kece za kiyi hakuri dashi domin kin zo gyara kuskurenki ne a gurin mutumin da yake tsananin fushi dake dan iskanci sai kina fada masa magana “kiyi hakuri mumy , “bani zaki bawa hakuri ga wanda zaki sake bawa hakuri nan kuma yanzu a gabana saboda ko babu aure a tsakanin ki dashi d’anuwanki ne bai cancanci wasu abubuwa daga gareki ba , muryarta a raunana tace “to ..to kayi hakuri “.
    “haka ake bada hakuri ki hada kalamanki guri daya ki bashi hakuri ta shagwabe fuska kamar zatayi kuka tace “kayi hakuri “.. shiru yayi yaki magana dan zafin da zuciyarsa keyi ba zai bar shi ya amsa mata ba ..”Kisna na kiraki da babban murya karki sake zance rabuwa tsakaninki da muradi saboda ina matukar sonku tare bana son ku rabu, rabuwarku daidai yake da shigata damuwa “Ni kuma zafin da zuciyata take akan shi fa mumy ni kadai fa nasan abinda nake ji kar a waye gari a iske bana numfa……..” Da ikon Allah babu abinda zai sameki idan kika zauna dashi tsakani da Allah zaki samu lada mai dimbin yawa sannan zaki jiyar da mahaifiyarki dadin da bata bata jin irinsa ba ,zata sake magana mumy ta dakatar daita kana ta maida hankalinta kan Aliyu …..
    “aliyu wacece ni agurinka “? da kyar ya iya bude bakinsa muryarsa can kasa yace “Mother ” yana riko hannunta cikin nashi “tabbas ni uwarka ce shiyasa ma nafika jin haushi akan abinda kisna ta maka ,abinda tayi ya balain tsaya min a rai ya dameni ya daga min hankali saboda na fahimci halin daka shiga a lokacin amman duk da haka yana da kyau ka yafe mata a karo na biyu dan Allah ku fahimci mahaifiyarku ina son ganinku cikin farinciki dan Allah ku zauna lafiya dan kwanciyar hankalina shiru suka yi zuciyarsu na dokawa da sauri iska ya furzar yana Kallon Kisna itama shi take kallo “mai yasa mommy zata masa haka akan kisna “? “Mai yasa zata sa igiya ta daureshi akanta ? “Aliyu ta sake kiran sunansa muryarta a sanyaye kamar zata zubar da kwalla ,” ka saki ranka nasan halinka kana da tsananin fushi da riko a cikin zuciyarka wanda ba’a son muslimi yana yin haka ta kamo hannu kisna ta saka cikin na Aliyu ta dunkule guri daya ” ka yafe mata wannan alfarmata ce na nema agurinka nasan ko numfashinka nace ka bani zaka mallaka min bare kalmar baki ,Shiru yayi har kusan second biyar “kayi shiru muradi kace ka yafe mata ? Da kyar ya sake buɗe baki yace “na yafe amman darajanki ne mumy wani sanyayiyyen numfashi Kisna ta sauke tana mai godiya ga Allah da ya furta ya yafe mata mumy tace “nasani darajana taci kuma na gode ko alahira wani nacin arzikin wani Allah yasa muci arzikin Annabi Muhammad Sallallahu alaihi Wasallama “ameen suka hada baki…”Sai abu na gaba Kisna zan baki wata biyar ki dawo da Aliyu daidai ,kaima Aliyu zan baka wata biyar ka dawo daidai da matarka idan ba haka ba zan ɗauki mummunar mataki akanku wanda a karshe bazai muku dadi ba, tana gama fadar haka ta mike da kyar ta soma kokarin barin dakin Aliyu ya mike zai taimaka mata tace “yi zamanka muradi na gode zan iya takawa da kaina ya koma ya zauna yana furzar da numfashi ..”

    Mommy na tashi daga mazauninta Kisna ta mike cikin sanyi jiki ta biyo bayanta ,mumy dake kokarin zama ta dubeta a tsanake tace “me kuma kika zo yi ? ” Maza ki koma gurin mijinki ki soma aiwatar da aikinki Allah ya baki nasara akanshi muryata a shagwabe tace “mumy wannan dan naki fa akwai wuyar sha’ani kanshi kamar kwakwa yake wallahi “ungo nan haka zaki daure , tun farko da bakiyi abinda kikayi masa ba kema kinsan yadda kike so zakiyi a gidansa ,hakuri zaki kara akan wanda kike yi , ki sanyawa ranki ibada kike yi kin san kuma duk abinda akace ibada ne dole sai an d’aure tare da sanyawa zuciya hakuri inshallahu ina ji ajikina zakiyi nasara akansa bazai sake wining zuciyarki ba “shikenan mumy adduarki ta Kara min karfin gwiwa daga sarewar dana yi da lamarinsa dan wallahi har na cire tsammani a kanshi “ba’a cire tsammani da rahmar Allah mamana ,kuma inshallahu sai kinyi alfahari da mijinki wata rana mumy ta dan dauki lokaci tana bata shawarwari daga karshe sukayi sallama ta koma dakin yana nan zaune a inda ta barshi yayi tagumi
    ta matsoshi sosai kamar zata shige jikinsa sauran kaɗan ta kwanto jikinsa tace ” maganar mumy gaskiya ne bazamu iya rabuwa da juna ba sai dai wallahi na gaji da irin rayuwar da muke ka saki ranka mu zauna lafiya , ni dai nasan a halin yanzu babu abinda nake son kasancewa dashi kamarka bazan iya rayuwa babu kai ba , ina sonka aliyu kaima nasan kana sona “? tayi maganar tana murza tafin hannunsa dake cikin nata …”No i can’t ya fada atakaice yana furzar da iska mai zafi tare da jan dogon tsaki , shiru tayi jikinta na ɗaukar rawa “you mean you don’t love me “? “yes I do ya sake bata amsa a takaice ,ta sake matsoshi tare da sanya kwayar idanunta cikin nashi, d’ayan hannunsa ta kamo ta mikar dashi tsaye “come with me ta nufi jikin bango dakin dashi bai mata musu ba yayi shiru yana biye daita kamar wani karamin yaro suna karasawa ta tsaida shi tana fuskartashi tare da kai hannuwanta duka kan wuyansa ta zagaye tana jifansa da wani irin kallo mai kashe gabobin jiki “meye haka kuma “?yayi magana yana kai hannunsa zai cire hannuwanta dake zagaye da wuyansa “tsaya mana ranka shi dade ka ga wani abu , ta cire hannuwanta dake zagaye da wuyansa ta zuge zip din gaban rigarta take dukiyar fulaninta dake cike bammm sunyi wani luhu luhu dasu ga kyau ga haske ga taushi suka bayyana a gabansa “wowwww is beautiful yaushe rabon na gansu ya faɗa acikin ranshi amman a zahiri tsaki yaja yana kawar da fuskarshi gefe kamar yaga mugun abu ,ta kai hannunta ta dawo da fuskarsa gareta ya sake dauke idanunshi akansu “duk fa wannan kayan marmari is for you Aliyu muradi “…. “for me”? ya furta yana watsa mata harara “Yes of course is for you don’t you like it ta sake turo masa su daidai bakinsa kasancewarta doguwa sosai kaɗan ya rage bata kamoshi ba yayi saurin runtse idaunshi qirjinshi na wani irin bugawa da karfin gaske “stop all this nonsense Kisna it not look beautiful “,kinsan wani abu “?ta girgiza masa kai tana tura hannunta cikin vest d’insa har tayi nasarar kife yatsunta a qirjinsa ya bude baki da niyyar zai yi magana ta muzra kan nipple’s d’insa duka tana wani irin narke masa ajiki … …tsarkewa yayi ya soma tari kamar wanda yaci wani abu mai yaji take ta rude tana masa sannu “na kawo maka ruwa “?Kai kawai ya girgiza mata alamun a’a ya zare hannunta daga jikinsa ya nufi gaban mirrow yana magana yana kwance agogonsa sai lokacin ya samu damar fadar abinda yake son fad’a mata ” duk wannan abinda kike yi basa burgeni saboda bana jin komai ajikina ji nake kamar namiji ne a kusa dani ,wallahi na gaji dake bazan dai iya fitowa na fad’awa mommy bane dan ita kadai zan iya gama rayuwata dake ba dan ina sonki ba,idan son samuna ne ma wallahi nayi nisa da rayuwarki zai fiyye min kwanciyar hankali..”

    “look I understand what’s in your heart ,ba Sai ka faɗa min ba saboda idan da sabo na saba da wannan kiyayyar ko zan iya baka tukuici akan wannan kiyayyar “?yayi shiru yana Kallonta ta cikin mirrow zuciyarsa na tsalle kallon wawiya yake mata ita kuma tana masa kallon mara wayo “bana bukata kuma karki dameni da shirmeki na banza on-expecting yaji ta sumbaci kumatunsa ta juya tana wata irin shegiyar tafiya tana kad’a masa jiki wanda ya zame mata jiki a tsorace ya juyo yana kallon bayanta “kina hauka ne kike irin wannan tafiyar “? “Haukan sonka ba ta bashi amsa tare da juyowa suna fuskantar juna “me kuma ya samu tafiya ta ? tayi magana tana matsowa a hankali ta karaso gabansa ta tsaya kirjinta na kadawa shiru yayi tare da tsura mata ido kamar zai cinyeta ganin taki ɗauke idanunta akanshi ya cire vest dinsa yabi gefenta zai wuce Kawai yaji ta rungumeshi a jikinta , hannuwanta ya sauka a daidai kan nipple’s d’insa wani irin shock yaji a ilahirin jikinsa “dan Allah ka bani wata biyar kamar yadda mommy ta fada ina tabbatar maka kafin lokacin soyayyata zatayi tasiri a cikin zuciyarka am very sure zaka soni kafin lokacin “no ya furta a zuciye “ya Aliyu Ni dai ka bani dama dan Allah nayi maka alkawarin muddin baka soni ba zuwa lokacin zan daina sonka gaba-daya zan rufe babin wani Aliyu a rayuwata zaka rabu dani batare da sanin kowa ba, zanyi nesa da rayuwarka a hankali take masa magana cikin rada tana shafa qirjinshi tana manna masa kiss a wuyansa, juyo wa yayi daita a hankali aiko ta fada cikin faffad’an qirjinsa mai kwance da kashi sai kamshi yake zubawa ” wayyo my world best wallahi bazan iya rayuwa babu kai ba sonka yayi mugun kamani ta karasa mgnr tana mirza kan nipples d’insa yayi saurin runtse idanunshi shi kadai yasan yadda yake ji a lokacin ,a hankali ta cigaba da murza nipples dinsa tana sauke ajiyar zuciya sannan tana lumshe masa idanu, ta zaro harshenta daga kwance da take ajikinsa tana lasar tsakiyar qirjinsa yayinda hannunta ke kan nipples dinsa tana zagayewa tana fitar da numfashi tana jin wani mugun feeling na taso mata a gaba-daya ilahirin jikinta kamar yadda shima yake ji ,gaba-daya gobobin jikinsa sun soma macewa saboda amsar sakonninta, jin yanayinsa yana neman sauyawa yayi sauri cire hannuta a kan nipples dinsa ya bude idanunshi sosai yana fidda numfashi yana kallonta yana jiran ta bar jikinsa ,sai dai bata d’ago ta kalleshi ba ganin idan ya barta ta cigaba komai zai iya faruwa dashi daga karshe tayi galaba akanshi tun ba’a je ko’ina ba ya fixegeta da karfi yana ƙoƙarin makata akan kujera ta janyosa ya fado jikinta tare da rungumeta .. “ashhhhh ta saki yar qara saboda q’irjinsa daya sauka akan dukiyar fulaninta ya kalleta da sexy eye’s d’insa , muryarta cike da shagwa’ba wanda ke kara burge mutane kuma take rikita duk wanda ya saurara tace “my world best ka bani dama dan Allah tsaki yaja ya mike tsaye yana fidda numfashi mai zafi sannan ya nuna ta da yatsan hannunsa alamun gargadi ” na yafe miki ba lallai sai na soki ba ki cigaba da tsayawa a matsayin ki na uwar Aryan da areef yana gama fadar haka ya shiga bathroom tayi dariyar jin dadi “yafa ji dadi haduwar da jikinmu yayi amman dan wulakaci ya wani maze Ina nan har ka fito …….”

    tana zaune a inda ya barta yayi wanka ya fito yana goge jikinsa da white towel ta mike zata taimaka masa ya dakatar daita “thank you..”
    “Please! please now !! Ka bari na taimaka maka gabad’aya ya haɗe rai fuskarsa babu walwala bare annuri ,sosai ta dinga rokonsa ganin nacinta yayi yawa ya barta sai dai babu abinda ya furta mata” you’re my life I love you muradi I can’t live without you duk duniya yanzu kai ne kawai abinda nakewa tsananin so dan Allah ka bani wata biyar din nan muddin ban shawo kanka ba na yarda ka sawwake min ko a boye ne naje nayi rayuwata a wani guri bazan sake dawowa cikinku ba zan barku kuyi rayuwarku i promise ajiyar zuciya ya sauke a hankali yana jin wani sabon yanayi na qara shigarsa muryarsa can qasa qasa yace “na baki ya fada a takaice …..”
    Wani irin sanyin dadi ne ya ziyarceta taji kamar tayi tsalle ta rungumeshi ajikinta amman tasan halinsa yanzu zai iya dangantata da kalmar hauka ko janye amincewarsa a hankali ta ji wani sabuwar qaunarsa na qara shigarta muryata a sanyaye tace “thank you my world best kuma inshallahu zan yi nasara” tsaki yaja jikinsa na qara mutuwa saboda har cikin jinin jikinsa yaji sautin muryarta data sauka a cikin kunnenshi shiyasa gabad’aya ilahirin jikinsa ya mutu murus …”

    Ya kalleta ta cikin mirrow yaga yadda take murna a fili ya girgiza kanshi yana tsuke karamin bakinsa “bazaki taɓa samun wannan damar ba shiyasa na baki dan bazaki taba zama acikin rayuwata ba bare zuciyarta “yayi maganar a kasan zuciyarsa itama zance zuci take tana kallonsa tana murmushi tare da watsa yatsun hannunta cikin tsananin farinciki “zan canza ka ya Aliyu na yiwa kaina alkwarin zaka soni da dukkanin rayuwarka “muje kaci abinci shiru yayi yaki cewa komai har tsawon minti goma ta sake yin magana ciki raunanniyar muryarta kamar zatayi kuka “dan Allah muje kaci abinci da alamun kana jin yunwa kalli yadda cikinka ya lefe ban san mai yasa kake kin cin abinci ba ko nayi maka tuwon shikafa da miyar wake ? ta karashe maganar a hankali , da kwantar da kai da rarrashi ta samu ya fito tana biye dashi abaya suka sauko parlou’n kasa lokacin babu kowa sai aunty zee da Samir zaune akan kujera suna kallo tayi saurin karasowa taja masa kujera “na zuba maka abincin da mommy ta girka ko na shirya maka wani?”no …. Ya fada tare da ɗaukar jug dake cike da ruwa ya kai bakinsa ta dauki plet ta zuba masa farar shinkafa da miya ta ajiye a gabansa tana jin kamar ta bashi a baki kusan minti biyar yana kallon abincin sannan ya fara ci hankalinsa a kwance saboda jin abincin mommy ne ,ta tsaya tana kallon shi fuskarta kwance da murmushi ta lumshe idanunta saboda tsananin dadi shi kuwa tunda ya soma cin abinci ko kallon inda take bai yi ba ,aunty zee ta zuba mata ido tana Kallon Kisna sai murmushi take tana kallon Aliyu ko kifta idanunta bata yi akan shi “ya Aliyu ya sauko daga dokin fushinsa ne yasa Kisna take murna murmushi haka “? abinda ya baka tsoro wata shi zai baka tausayi shiyasa Annabi Muhammad Sallallahu alaihi Wasallama yace “idan zaka so mutun ka so shi kadan haka zalika idan zaka ki mutun kaki shi kadan yau dai ga Aliyu ya tafi da rabin rayuwar kisna ya bar saura ,waigowa Kisna tayi aiko idanunsu ya haɗe dana aunty zee take ta sakar mata harara bata damu da hararar da aunty zee tayi mata ba , ta kai hannu ta tsiyaya masa ruwa garin rawan jiki ruwan ya zube a ƙafarsa daya tsaki yaja tayi saurin cewa “sorry ta warware tissu ta tsuguna ta goge masa ta bar gurin tun kafin tayi wani sabon laifi ta dawo inda aunty zee take ta kwanta ta daura kanta akan cinyar aunty zee tana jin dadi “ina miki fatan samu soyayyar wanda kike so dan ki damgwama cikin farinciki tayi maganar tana shafa sumar kanta kallon fuskar aunty zee tayi tana sake fadada fuskarta “Ameen auntyna Allah ya barki da ya samir “na gode sister ina miki fatan samun nasara ki samu soyayyarsa nan kusa sannan ku so juna har abada d’agowa tayi ta zauna idanunta cike da ruwan hawaye “mumy ta Bamu wata biyar mu daidaita kanmu ko kuma ta dauki mummunar mataki akanmu, ni kuma na nemi alfarma wata biyar agurinsa aunty zee zan yi ko’k’arin naga na shawo kansa duk da nasan da wuya hakan ta kasance ,wallahi ina tunanin halin da zan shiga idan na kasa shawo kanshi aunty “da Ikon Allah Zaki yi nasara akanshi mutun ne fa shi kuma mai jini ajiki, kuma bai fi karfin Allah ba ki tsaida zuciyarki kisa a ranki zaki shawo kansa hawaye ya soma gangaro mata a lokacin daya mike rike da wayarsa dake qara ya nufi haraban gidan …….”

    Da sauri aunty zee ta rungumeta itama ta rungumeta aunty zee gabad’aya jikinta yayi sanyi a hankali suka cigaba da tautaunawa zuciyar kowannensu cike da tunani har kusan 11 sannan suka yi sallama da juna ta nufi dakin mommy wacce tuni tayi bacci da jikokinta ta zauna a bakin gadon ta janyo man zafin dake gefen kanta wanda duk daren duniya dashi take kwana ta lakato ta mulka a kafarta tana mammatsa mata kafa zuwa kaurin gwiwarta mommy ta motsa a hankali tare da ɗan bude idanunta kadan “bakiyi bacci kisna ..”? “Yanzu nake shirin yi nace nazo muyi sallama sai gashi kinyi bacci numfashi ta sauke tana lumshe ido ta ɗan dade tana mammatsawa mommy jiki kafin daga baya mommy tace “mamana tashi kije ki kwanta kin bar mijinki shi kadai “to mommy har ta mike ta dawo daidai fuskar mumy ta tsugunna “mumy ki yafe min ” me kuma kika yi” bakiyi min komai ba mamana “Ni dai kice kin yafe min “
    “Na yafe miki mamana Allah yayi albarka ” ameen sai da safe ta karasa inda yaranta ke kwance ta shafa sumar kansu tare da shafa musu addu’a , ta manna musu kiss a goshi sannan ta nufi dakin baccin su har ta karasa shiga d’akin tunanin Aliyu take da irin badaudaden halinsa mai wuyar sha’ani tana tsaka da tunani idanunta ya sauka akan calander a manne a bango dakin jiki a sanyaye ta karasa jikin calander ta tsaya tana kallo a karshen shekarar ake ta dubu biyu da sha takwas “kenan a may yarjejeniyarsu da Aliyu zai cika “ya Allah ka taimakeni na shawo kansa kafin lokacin ta dauki bironsa dake ajiye akan table tayi mark din aikinta na farko data yi na nasarar janyo hankalinsa ya yarda da tsarin da mommy ta gindaya musu sannan tayi nasarar da yaci abinci cikin sauki batare da tashin hankali ba taja numfashi ta sauke sannan ta shiga wanka tayi ta fito ta goge jikinta ta dauko daya daga cikin kayan da aunty zeey ta kawo mata ta saka rigar bacci iya cinyarta mai bud’ad’d’en gaba sai wata yar igiya da’aka saka domin daurewa ta tufke sumar kanta a tsakiyar kanta dan taji dadin bacci ta fesa turare ta saki murmushin jin dadi ta haye saman lafiyayyen gadon mijinta ta kwanta ta rungume pillow a qirjinsa tana jin kamar shi ta rungume tana kwance taji shigowarsa tayi saurin runtse idanunta kamar mai bacci ,wayarsa yasa a handsfree muryar nawal taji ta karade d’akin take gabanta ya shiga dukan uku uku ta ɗan bude idanunta kadan taga ya dauko computer dinsa ya ajiye akan table ya jonata a caji still tana jin sautin muryarta har ya zauna “do you miss me nur? murumushi kisns taga yayi sannan yace “Yes dear I really miss you ya fada fuskarsa na wanzuwa da wani sabon murmushi data kasa fahimtar na menene a hankali yake operating din system dinsa yana saurarenta can ya ciza lip’s d’insa muryarsa a kasalance yace”okay tell me how much you love me ? ya fadi haka ne saboda lura da yayi idanun kisna biyu akanshi “I can’t discribe the way I love you amman kasa a ranka zan soka har karshen rayuwata kai ne kadai zaka mallaki zuciyata sannan ka zauna a cikinta har sanda za’a zare numfashina ……” ya rasa me mata suke gani ajikinsa suke leke masa har su maida shi duniyarsu da numfashinsu shiru dukkaninsu sukai na tsawon lokaci can muryarta ta sake bayyana “yasu aryan da areef sunyi bacci ko “? Yace “uhmmm yana cigaba da danne danne “ya tafiyar mommy tana nan jibi din “? ya sake cewa uhmmm “,okay zanzo airport inshallahu muyi sallama kuma gobe zan turo direbana “okay ya fada a takaice dan ya soma gajiya .
    a hankali kisna ta sauko daga sama gado ta bude wardrobe ta dauko bargo guda biyu ja da fari ta masa ja akan gado daga gefe guda tare da pillow , zata koma dayan bangaren katifa taji yayi gyaran murya ta tsaya haɗe da juyowa ta zuba masa kyawawan idanunta “ki dawo ki kwanta a kasa “inna lillahi ta furta a kasan zuciyarta yayinda a zahiri kuma tace “to tare da bin umarninsa daman yaso ya barta akan katifa dan yasan abinda ta tsana kenan kwanciyar kasa amman tunda ta tashi dan son jin gulma bazata koma saman gadon ba ,ta kasan idanunshi yake Kallonta kwance ranta a ‘bace tana mutsumutsu da jikinta ya cigaba da aikinsa yana waya da nawal ..”

    ******
    Washegari

    da safe tun karfe biyar ta tashi a barci duk da cewar bata samu isasshen barcin kirki ba saboda tunanin Aliyu da kwanciyar kasa da tayi , ta shiga Kitchen ta haɗa musu break fast, wata irin doguwar mika Aliyu yayi hade da salati yana gyara zaman jijiyarsa data mikewa sambal a hankali ya mike zaune yana yaye bargon daya lullu’ba dashi yayi hamma tare da runtse idanunsa yasa hannunsa a baki yana buɗe idanunshi aiko suka sauka akan calander ganin mark ajiki yayi mamaki, ya sauko yana taku a hankali ya tsaya gaban calander rike da kugunsa “waye yayi mark ajiki ya tambayi kanshi “waye zai yi banda wannan wawiyar yarinya wai ita nan tayi abin kirki shine har da rubutawa bayan totaly zero ce, abincin da mommy ce ta dafa kuma tasan dole zanci amman da yake dakikiyace tun ba’a aje ko’ina ta zuba min ruwa ajiki garin rawan kai yaja tsaki tare da ɗaukar biro yayi Cancel din mark din datayi ya shiga wanka .

    Bayan ta gama hada breakfast ta dawo dakin domin gyarawa taci Sa’a yana bayi cikin sauri ta soma gyarawa ko’ina ya dawo tsab ta feshe dakin da turaren roomfreshiner da turarenta na jiki tazo bude wordrobe d’inta taga anyi cancel mark din ɗaya tayi jiya ta tsurawa calander ido ita dai tasan mark tayi ba Cancel ba tayi shiru tana daga kwayar idanunta sama alamun tunani “babu wanda zai yi wannan aiki sai ya Aliyu ta fada a ranta, tana cikin tunani ya fito jikinsa daure white towel yana goge jikinsa da karami ya kalleta tsaye a gaban calander ya dauke kanshi yana tabe baki , ta numfasa ta karaso gabansa ta tsaya muryarta a shagwa’be “me yasa ka goge min Please ?
    “me kikayi da kwakwaluwarki ta fada shirme bakiyi abun arziki ba dan haka no need of mark ki dai yi wani abu amman na jiya da kikayi zero ne ya karasa maganar yana bude roban man shafawarsa ya soma shafawa “amman ni a ganina nayi kokari “
    “agurin kenan ba , dan ki yaba da kanki yasa kikace a baki dama ? ta girgiza kai ya wuceta ya bude bangaren kayansa ya dauko deep blue t shirt da wonda baki ya shiga bayi tabi shi da ido kawai ,ya saka ya fito ya dauki cumb ya gyara suman kansa duk tana tsaye tana kallonsa komai a natse yaje cike da tsafta ,Yana gama shirinsa ya fita ya bar mata dakin babu yadda ta iya ta shiga bayi dan yin wanka …”

    aunty zee ta janyo daya daga cikin akwatinan mommy dake cike da tsaraba ta dubi kisna data tafka uban tagumi tayi murmushi “to ranki shi dade ki tashi ki dauki wancan akwati mukai parloun Kinga gobe ba sai mun tsaya bata lokaci ba ,kisna da idanunwanta suka yi jawur tana duba agogon dake daure da hannuta “ina jin kamar mommy ta cigaba da kasancewa damu “kin jiki da wata magana ta cigaba da zama mijinta fa? Kinga my friend idan zaki koyi rayuwa gidan miji ke kadai ki koya basu dade da saukowa ba direban nawal ya karaso mai gadi ya kwankwasa kofa aunty zee ta bashi umarnin shigowa ya fada mata anyi bako ta mike ta fita ko cikakken minti biyu bata yi ba ta dawo hannunta rike da wata ƙatuwar jaka Kisna ta bita da kallo “sakon nawal ne ba tace komai ba ta runtse idanunta ita kuma tayi sama domin sanarwa mumy ..”

    Washegari gari

    mommy na taku a hankali Aliyu na bayanta rungume da aryan Samir na rungume da areef suka fice gabad’ayansu tunda daman a shirye suke ,suka dunguma zuwa filin jirgi a lokacin sauran minti talatin jirgin ya daga kisna ta dukar da kanta wai bata son ganin tafiyar mommy dan ba karamin so takewa mahaifiyarta ba, gashi bata san sanda zasu sake ganin juna ba,lokaci daya nawal da nasir da safy suka karaso nawal cikin fararen kaya komai fari ta saka hatta agogo da takalmi farare ne ta durkusa har kasa ta gaisheta da mommy “Ina kwana mommy ,mommy tayi saurin Kai hannu ta kamo kafad’unta “maza tashi karki bata kayanki ta mike ta koma kusa da Aliyu dake rike da waya ta gaisheshi tare da nasir da Samir ..
    Mommy ta Mike a lokacin da zasu shiga jirgi aunty zeey ma ta mike ta rungume mommy” Allah ya tsare ya kai ku lafiya “ameen diyata Allah yayi muku albarka kuyita hakuri da juna kunji , ganin kisna taki d’agowa yasa mommy ta karaso inda take ta d’agota ta rungumeta “haba mamana meye haka kamar bazamu sake had’uwa ba hawayen idanunta da take kokarin maidawa suka silalo saman kuncinta tace” zanyi missing dinki mommy Ina Jin kamar karki tafi ki barni itama mommy hawaye take “na fiki shiga damuwa mamana Amman duka sauran wata nawa ne zaki zo bikin muradi tayi saurin runtse idaunshi tana jin zafi acikin ranta “nasan yadda kike ji mamana amman ki kara hakuri kiyi kokarin shawo kanshi kafin wata biyar din dana baku ..”

    A hankali mommy ta zareta saboda har mutane sun fara shiga jirgin aliyu na sauke aryan ya kwaso da gudu ya rungume Kisna shima areef dake rike hannu nawal mutsu mutsun sauka yake ta sauke shi ya karaso ya rungume kisna, ta rungumesu gaba-daya tana kissing dinsu tana zubar da hawaye nawal ta karaso inda suke “mai yasa kike kuka haka kamar bazaku sake haduwa ba ? zaki sa yara nan kuka fa …..shiru Kisna tayi batare da tace mata komai ba dan duk abinda zata faɗa baganewa zatai ba tunda bata san ya ake daukar cikin ba bare tasan mahimmanci ya’ya ga rayuwar iyaye ….”

    Aliyu ya kalleta ya kawar da kanshi yana jan tsaki yace “kukan munafurci kawai “ya kukan munafurci tana kukan zata yi kewar ya’yanta kace munafurci “? Nasir ya fada yana jan tsaki “Ai nasan yanzu ka zama ɗan yankinta dole komai tayi bazaka ga laifinta ba “kai wallahi wani irin mutun ne to nayi yakinta sai kayi abinda zakayi ..da kyar mommy ta bambare yaran daga jikin kisna dan cewa sukayi bazasu bi mommy ba shi kansa Aliyu babu yadda zai yi ne amman da bazai bari a tafi dasu ba ,mommy ta sake kallon nawal “to nawal sai mun hadu a naija ko”?
    “Sure ta fada tana gyada mata kai cike da girmamawa, mommy ta juya zuciyarta cike da kewar ya’yanta suna tsaye jirgi ya lula sararin samaniya suna binshi da kallo kisna ta share hawayen fuskarta ta juya da sauri ta faɗa mota zuciyarta na bugawa sosai sai yanzu take kara jin soyayyar mahaifiyarta “lallai qaunarsu acikin jini juna take itama mommy hawaye take goge wa a zaunen da take acikin jirgi …”

    Nawal ta matso kusa da Aliyu tana jujjuya masa jiki hannuta rike da jaka tana sakar masa murmushin “nur zan wuce gida muje ka rakani na shiga mota ko “ta fadi haka ne dan tasan halinsa zai iya barinta agurin ya kama gabansa “okay muje ko suka jera a tare suna magana kasa kasa a natse kisna ta d’ago idanunta karaf ya sauka akansu sunawa juna murmushi take qirjinta ya shiga luguden bugawa “yaushe ne zata samu irin wannan damar da nawal ta samu a zuciyar mijinta “?
    “Ka yafe min mijina nayi kewar komai daya danganceka tana kallonsa ya bude ma nawal bayan motarta ta shiga ta zauna tana sake sakar masa murmushi “ko me yake ta fada mata haka yasa take ta faman murmushi “?ta tambayi kanta har sanda ya maida murfin kofar motar ya rufe direbanta yaja idanunta na kansu ..”

    Ko daya dawo gurin Samir bai gurin da gira ya tambayi nasir inda Samir yake shima da gira ya amsa masa alamar ya wuce ya kai hannu ya doki kadan nasir “kai fa nasir wani lokacin dan iska mutun ne ,” yan iska dai taya zaka min tambaya da gira “?”Kaga muje har ya juya nasir ya kira sunansa ya juyo ya tsaya tare da zuba hannunwansa ciki aljihun wandonsa “ya’akayi Sarkin matsala”?

    “Ai kai ne sarkin matsala wallahi daman akan yarinyar nan ce “wace yarinya kenan “?ya tambaye shi ,kisna mana dan Allah ka rarrashita idan kunje gida karka sa yarinyar mutane a gaba da bala’i bayan zuciyarta na cike da kewar mahaifiyarta da ya’yanta “kasan Allah bazan rarrasheta ba Allah yasa tayi ta kuka har ranar da zasu sake haduwa babu ruwana .

    Nasir yace “dan iska kana wani nunawa kamar baka sonta bayan nasan kana bala’in sonta kamar ka mutu “na taɓa faɗa maka da bakina ina sonta “?Nasir yayi shiru yana mamakin hali irin na abokinsa “kayi shiru na taɓa faɗa maka ina sonta ko ka taba ganin wata alamar data nuna ina sonta “? “Baka sonta ya’akayi har ka mata ciki ? “Wannan tsautsayi da rabo ne ya bashi amsa yana ƙoƙarin juyawa nasir ya dakatar dashi ” zaka san tsautsayi ne sai randa ka tsinci zuciyarka dumu dumu ta kamu da matsanacin soyyarta”babu wannan ranar nasir ba kuma na fatan zuwan wannan ranar a rayuwata, nawal kawai ta isheni rayuwa kasan wani abun farinciki “? Nasir ya girgiza masa kai “mommy ta bamu gud five month mu dawo daidai tamkar sauran ma’arata idan bamu dawo ba zata dauki mataki ka tayani addu’a Allah yasa mu cigaba a haka nasan karshe hukunci rabuwa ne zai biyo baya na huta da jaraba ..”

    zaro ido waje nasir yayi tare da cewa “ba ameen ba dan iskan Allah yasa wani tsautsayin ya sake shiga tsakani mu sake samun yan shida dan da alamun spam din abokina baya bada kwai daya “ba ameen ba dan iska kawai mai mugun baki yana gama fadar haka ya juya escort d’insa suka zagaye motar da yake kokarin shiga kowannensu na rige rigen buɗe masa kofar gidan baya inda kisna da safy suke zaune tana rarrashinta , ko kallon inda take zaune bai yi ba,
    Ya juyar da idanunshi yana kallon wani bangaren , ganin tsayuwarsa yasa safy tayi ma Kisna sallama ta fito ya shiga direbansa yaja motar

    *******
    Har suka karaso haraban gidan bai waigo ya kalleta ba direba na gama parking escort dinsa suka fito daga cikin nasu motar suka bude masa ya fito yana ciccin magani sannan ya soma daga zara zaran yatsun kafafunsa cikin isa da takama ,a hankali ta yunkura ta fito jiki a sanyayye ta shiga ciki , tun byn dawowar su Daga airport Aliyu ya shiga part dinsa ya kwanta bai sake yunkurin fitowa ba sai zuwa sanda yaji kira sallah sannan ya motsa ya shiga wanka ya fito ya sauya kaya riga dark blue da wando ligth blue ya nufi masjid bayan ya dawo a parloun kasa ya zauna ya kunna tv..”

    Da misalin karfe tara na dare ta sauko a natse cikin hadaddiyar rigar bacci wanda ta bayyana komai na jikinta ta sameshi yana danne danne a system dinsa ta zauna a gefensa gabanta na faduwa muryarta a raunane tace “ummmmm ammmmm Sai kuma tayi shiru ta kasa magana shima yana jinta yayi mata banza sake motsa lip’s d’inta tayi cikin in ina “kunyi waya da mommy na nemi layinta ban samu ba “uhmmm kawai yace atakaice ya cigaba da aikinsa , can ta kirkiro murmushin dole ta sanyawa fuskarta
    “yayana ka bar aikin nan haka ka huta ya d’ago da niyyar yayi mata Banza kallo qirjinshi ya buga da matsanancin karfi sakamakon ganin Brest dint tsaye suna kallonsa yana kallonsu dogon tsaki yaja , idan ban yi aiki ba uban me zan miki da zakice na bar aiki? Yayi magana a zafafe cike da jin haushi “Allah ya baka hakuri ka mayar da wukar na kawo maka abinci nan ne “,?
    “Bana ci kar kuma ki dameni plz. “dan Allah kaci wani ……..
    “oh my goodness Kisna kin fiyye damuwa wallahi idan zanci zanci bana jin yunwa ne ya mike yana kashe system dinsa ,ya bar mata parloun shiru tayi tana zance zuci har kusan minti talatin sannan ta mike ta nufi sama koda ta shiga dakin har yayi bacci dan kwance ta hangoshi daga shi sai boxcer da singlet yana fidda numfashi ta kai hannunta gefen kyakkywar fuskarsa tana shafawa a hankali tana lumshe idanunta a hankali taji saukar hannunsa kan hannunta ya fixgota yana ƙoƙarin bude idanunshi …….”

    Mmn sudais
    💗💗💗💗💗💗
    CUTAR DA KAI
    💖💖💖💖
    💗💗💗💗💗💗

    Note
    error: Content is protected !!