Cutar Da Kai – Chapter Four
by Aysha A Bagudo*PAID BOOK*
*AYSHA A BAGUDO*
*MASU ƁUKATAR A TALLATA MUSU HAJOJINSU ZA SU IYA TUNTUƁARMU TA LAMBOBIN 07045308523 MUN GODE*
…..tsuru tsuru tayi kamar mara gaskiya tana kallonsa “ki fito mana saboda baki da manners kin wani tsareni da wadannan shegun idanuwan naki masu kama dana aku common get out ya fada a fusace kamar zai dauketa da mari , k’arasawa tayi inda hijab d’inta yake ta d’auka don gabatar da sallah ,dan bata san lokacin da zai ɗauka ba kafin ya dawo gidan .”
cike da sanyi jiki take d’aga zara zaran yatsun kafafunta ta fito daga d’akin ta tsaya tana ci-gaba da kallonsa ,ya janyo kofar da karfi ya kulle haɗe da murd’a key “meye na wani tsayamin akai kamar kina bina bashi ? “dan Allah malama ki wuce banason ganin wannan banzar fuskar taki ,kin wani tsareni da ido kamar zaki cinyeni ko zaki cinye ni ne?” Yayi maganar a fusace yana zaro mata idanu ,Tayi saurin girgiza masa kai alamun “a’a “ko wani naga zai cinyeka ai sai inda karfina ya …”…
“ya isa dan Allah malama bance ki qara da dogon sharhi ba dan bana bukatar jin komai daga gareki hasalima na tsani ganinki a kuda dani bare wannan shrgiyar muryarta ki ,yana gama faɗar haka ya raba ta gefenta ya wuce yana d’aga kafafunsa kamar baya son taka kasa , wani sabon abin mamaki suna isa parlou’n kasa ya canza wuta kamar yadda ya saba a tun farkon zuwansu “bance karki yi changeover ba , kiyi duk yadda kike so jikinki ne zai gaya miki idan na dawo ,ya kama hanya ya fita yana furzar da iska mai zafi daga bakinsa .”
Naunayen ajiyar zuciya ta sauke da karfi tana dafe goshinta “daman haka Aliyu yake ?” “daman zai iya rashin mutunci da rashin imani haka ?” shiru tayi tare da kwanciya akan doguwar kujera , ta shiga tunanin rayuwa idan akace mata akwai wata rana da zata zo rayuwarta ta dawo haka zata karyata ,sai gashi tazo mata fiyye da tunaninta, nasan halinsa tunda na zauna dashi ban taɓa samun matsala dashi ba ,bai taɓa aikata min laifin komai ba, yasan duk abinda zai yi ya faranta min rai , idan nace wannan abun baki ne ,to muradi zai ce bakinkirin ne , bai taɓa sa’bawa umarnina ba, duk abinda ya biyo baya daga gareki ne kisna , ba kuma zan lamunta ba ……” wannan shine maganganun mahaifiyarta a lokacin da zasu baro Nigeria .
ta sauke numfashi “zan d’aure mummy ,Kuma zan sanyawa zuciyata hakuri sannan zanyi ƙoƙarin na nasan yadda zan janyo hankalinsa gareni.”
Shi kuwa Aliyu tunda ya bar gidan zuciyarsa a cukunshe take da bakinciki mara misaltuwa , ya kasa manta abinda tayi masa a baya “ka manta komai aliyu ko dan darajan iyayenta, sunyi maka komai arayuwa , mutun kan ci daraja wani nasa mai imani inji cewar wankakkiyar zuciyarsa “surukina kuma d’ana muradi , kai kasan halakar qaunar da take tsakanina da kai , ina sonka fiyye da komai a rayuwata ,ina rokon alfarmarka ka kasance tare da kisna muddin rai , kasan yadda nayi fama daita a can baya ,gashi a karo na biyu zata dawo hannunka , wannan abu bakaramin faranta min zuciyata yayi ba , bazan iya kwatanta maka farinciki da nake ciki ba , ada ta kasa fahimta komai ,amman a yanzu ta fahimci komai zaka ji dadin rayuwa daita, nasan kai mutun ne da d’aukaka ko matsayi bazai taɓa canzaka ba, ada tayi kuskure , a yanzu kuma tana son gyara kuskurenta na baya kayi hakuri ka bata dama ” nasihan mahaifiyarsa kuma mahaifiyar kisna kenan gareshi har ya isa ma’aikata tunanin magangagun mummy ne ke yawo a cikin kwakwaluwarsa “
“Wunin ranar kwance tayi sa tana saka da warwara , sallah ne kawai ke taddaita, yamma nayi ta shiga Kitchen domin girka abinci dare , bubbud’e wundunan Kitchen din tayi domin taga hasken aiwatar da aikinta ,abincin da tasan yafi so shi tayi ƙoƙarin d’aurawa , tuwon shikafa da miyar wake “Yau mijina zai ji dadi abinda yake so zan girka masa tayi maganar a kasan zuciyarta , shiru tayi bayan ta d’and’ana miyar , jikinta yayi sanyi sosai saboda tuno baudadden halinsa da tayi, “ban sani ba ko zai ci abincin nan ko bazai ci ba ? ” Tayiwa kanta tambayar ..
“komai nayi masa sai ya gwasaleni ya kama faɗa da zagina alhalin yasan banason daya daga ciki , ya zakiyi kisna haka zaki cigaba da hakuri dashi har zuwa sanda Allah zai sauko miki dashi , ta gama komai a tsanake ta shirya dinning ta shiga bayin dake manne da parloun tayi wanka ta sake maida kayan jikinta data cire tazo ta raku’be guri daya tana jiran dawowarsa “.
*****
Karfe takwas daidai ya shigo gidan a gajiye hannunsa rike da jakar laptop d’insa , ya zaro wayarsa ya kunna sannan ya d’aga idanunshi da suka koma ja , ya sauke akan abun canza wuta , ya canza haske ya haska gidan gabad’aya sannan ya soma daga kafafunsa da kyar saboda kanshi dake masa wani azaɓaɓɓen ciwo , ta mike da sauri ta karaso gurinsa “sannu da zuwa zata amsa jakar hannunsa ya watsa mata wani mugun kallo batare daya amsa mata sannu da zuwan data yi masa ba , ya wuceta ya ajiye jakar computer dinsa akan kujera dan akwai aikin da zai yi a daren , ya furzar da iska kana a hankali ya nufi step yana takawa ɗaya bayan ɗaya cikin izza tamkar wani jinin sarauta .”
tsayawa tayi cak tare da bin bayansa da kallo tana tunani abun yi “aliyu na tozartata dayawa yana wulakantata tamkar bai san daga inda ta fito ba ,ada can baya ba haka yake ba, ba haka tasan shi ba ,ta ina zata fara irin wannan rayuwar da yake muradi daita? bazata iya ba gaskiya ,dan haka duk yadda zatayi sai tayi ta shawo kanshi su zauna lafiya , sannan zata lalla’bashi yaci abincin data dafa masa koda kuwa zata samu tukuncin duka da mari ne daga garesa zata d’aure tayi iya kokarinta, bayansa ta biyo da hanzari koda ta shiga d’akin yana zaune a kan doguwar kujera ya rike kanshi dake sarawa da duka hannuwansa ,sosai zuciyarta ke bugawa da ganin yanayinsa ,ta karaso garesa ta kudurce aranta komai zai faru sai dai ya faru amman zata jure duk wata azaba daga garesa , tsugunawa tayi a gabansa ta zuba masa narkakkun idanunta tana jin zallar qaunarsa na ratsata “meke damunka aliyu ko baka da lafiya ne ?” tayi masa tambayar hawaye nabin kuncinta ji take duk duniya babu abinda take qauna sama dashi, ta kai hannu zata riko hannunsa yayi saurin fixge hannusa yana jan tsaki “karki taɓani wai dan Allah me yasa kike son kawowa rayuwata hari ne alhalin kinsan bana son kusancimu tare ?” shiru tayi tana ci-gaba da kallon yadda yake motsa lip’s d’insa ” kamar baya son magana komai nashi a natse kuma a yangance , “Baka son kusancimu gashi kuma Allah ya had’amu tare ,kuma ina Sa rai mutuwa ce zata rabamu …….”
Mtsssss ya ja dogon tsaki yana furzar da iska mai zafi daga bakinsa “wannan kuma damuwarki ce dan Allah ki fita daga d’akin nan banason damuwa kuma bana son Kallon fuskarki yana gama fadar haka ya mike ya soma cire kayan jikinsa yana ajiyewa a saman gado bata daddara ba ta dinga bin kayan daya bayan daya tana ɗaukewa tare da kai su ma’ajinsu , ya saura daga shi sai boxcer ya janyo towel ya da’ura a wuyansa zai shiga bathorrom tayi saurin rungumeshi tsam ta baya “ka bar zuciyata da rashin sonta da bakayi dan Allah , ka daina hukuntani haka ya Aliyu ,ka tausaya min idan kana careles dani zuciyata zata iya bugawa”.
“kece da kanki kika *CUTAR DA KANKI* “nasani wallahi nice, nasan nice , na *CUTAR DA KAINA* nasan ka d’and’ani damuwa mai yawa a tare dani , amman ka yafe min abinda nayi maka ,nasan nayi kuskure , dumin jikinsa ya ratsata tayi saurin runtse idanunta “jikinka da zafi ya Ali , “da alamun baka da lafiya , juyowa yayi tare daita ajikinsa suna fuskantar juna sannan ya zareta a jikinsa ya shige bathoroom batare daya bata amsar tambayarta ba “.
Bathtube ya shiga yai having shower ya dade yana sakarwa kanshi ruwa tukunna ya fito tana tsaye tana jiran fitowarsa , yana goge jikinsa ta karaso ta soma taya shi “,dakata dan Allah malama bana son kina ta’ba min jiki “amman da…..”enough I don’t want to hear anything from you ,cire hannuwanta tayi ta ajiye ƙaramin towel a mazauninsa ta ja ta tsaya rungume da hannuwanta duka a qirji tana kallonsa yana goge ko’ina ajikinsa ya d’auko kayan shan iska ya saka farin wando da farar riga , ya fesa turare mai sanyi kamshi , ya zo ya wuceta ya sauko zuwa falon kasa ta sake biyo bayansa da sauri ya zauna kanshi na matukar sarawa tare da janyo jakar system dinsa ya buɗe ya fito da computer dinsa ya kunna ya soma danne danne, ta karasa kitchen da sauri ta d’auko masa lemu da ruwa mai sanyi da glass cup ta tsiyaya ruwan acikin glass cup ta mika masa.” kasha ruwa dan Allah ya d’ago akaikace ya kalli fuskarta hannu ya kai ya zai amsa ,murmushin farinciki ne ya bayyana akan fuskarta tana kallon kyawawan fuskarsa har ya kai bakinsa yaga yadda take murna da farinciki kawai sai ya fasa shan lemun ya watsa mata ruwan lemun a fuskarta tayi saurin runtse idanunta tana sauke numfashi da ajiyar zuciya atare .
a hankali ta buɗe idanunta tana kallon jikinta dake jike da ruwan lemu ,ya ajiye cup din akan table ya cigaba da aikinsa “kina da damuwa wallahi nace bana son kusancimu amman sai sake makale min kike kamar dole babu yadda ta iya haka kame tsaye cikin tsananin jin tsoronsa .wayarsa ce ta soma kara ya ɗauka ya duba ganin mataimakinsa ne agurin aiki , ya ja tsaki yana jefar da wayar akan kujera dan yasan bai wuce akan sakon daya dawo daga naija ya iske bane , akan wani sabon kamfaninsu da zasu bude a kasar hollond da Austaraliya , kasar ta bukaci dole sai ɗaya daga cikin masu kamfanin sunzo sannan a basu damar fara aiwatar da abinda suke bukata , yana tunanin cikin shi da samir wani zai je domin ganawa da manyan kasar “
Jikinta ta cigaba da kallo kamar mai shirin yin kuka sannan ta sake kallonsa “na gode da abinda ka min ban yi fushi ba kuma ban ji haushinka ba sai ma sake kusanta zuciyata da ……”dakata banason long talk ” ya fada yana daga mata yatsan hannunsa tare da maida hankalinsa sosai akan computer ,” shekenan amman dan Allah ka dan sha lemun , idan ka gama aiki ga abincin daka fi so can na dafa maka ,idan zaka ci da kanka ne to , idan kuma ni zan baka a baki a shirye nake ta karasa maganar tana murmushi kamar yana kallonta ganin yaki d’agowa ya Kalleta yasa ta juya ta haye sama , dagowa yayi a natse yabi bayanta da ido yana tabe baki “da alamun ciwon hauka ya soma kamaki.”
kai tsaye bayi ta shiga ta cire kayan jikinta ta saka cikin washing machine ta kunna sannan ta soma wanka bayan ta gama ta fito ta shiya kanta cikin wasu kananan kaya masu shegen kyau wanda suka kama jikinta sannan suka tattaro dukiyar fulaninta guri daya ,sosai dukiyar fulaninta suka yo sama sai sheke suke , ta fesa turare a duk sansan jikinta sannan ta fito tunda ta soma taka step ya soma jiyo daddadan kamshin turarenta bai d’ago ba har ta karaso gabansa ta tsaya “oh my god ya Aliyu ba dai har yanzu baka sha lemun ba ?” banza yayi mata a zuciyarsa yace da haihuwar kare da barinsa duk daya ne agurina “.
“bari naje na kawo maka abincin ta nufi dining da sauri ta zubo masa abinci , plate din tuwo daban na miya dabam ta karaso ta ajiye akan table din dake gabansa ta shiga Kitchen ta d’auko ruwa ta fito ta zauna kusa dashi duk yana jinta kuma yana ganinta ta kasan idanunsa sai dai yaki d’agowa , tunda ta ajiye abinci ya soma had’iye miyo dan tabbas best food dinsa tayi , ta ɗauki plate din miya da spoon “Mr A …….” ta furta a hankali cikin zazzakar muryarta mai kashe jiki , tana zaune a gefensa kamar bazai waigo inda take ba, sai kuma ya waigo ya zuba mata kyawawan idanunshi masu kama da luhu luhu take gabanta ya soma fad’uwa , jikinta ya dinga rawa kamar mazari tayi saurin sanyawa jikinta jarumta ta kai spoon din abinci daidai saitin bakinsa “bude na baka a baki nasan baka ci wani abinci mai nauyi ba “shiru yayi yaki buɗe bakinsa sannan yaki ɗauke idanunsa akanta numfashinta ya nemi ɗaukewa tsananin tsoronsa ya sake mamaye zuciyarta ,hankalinta ya sake tashi a lokacin da taga ya sauke numfashin yana ƙoƙarin ɗauke idanunshi tace “dan Allah karka min haka abinci daka fi so ne na dafa maka dan daranja fiyyayen halitta ka daure kaci ko kadan ne saboda Allah ba dan ni ba , ya sake kallonta bata tsaya ‘bata lokaci ba ta kai spoon din abinci bakinsa on-expecting taga ya buɗe bakinsa ta lumshe idanunta tare da tura spoon bakinsa.”
a hankali ta dinga bashi abinci yana amsa har sai daya kawar da kanshi kamar wani karamin yaro ta tsiyaya ruwan fury a glass cup “uhmm tayi gyaran murya ya sake waigowa inda take ta kai cup bakinsa wannan karon amsa yayi yatsun hannunsa ya taɓa nata wani irin shock suka ji a tare ,a lokaci daya zuciyarsu ta buga da matsanancin karfin gaske ,tayi saurin mika masa kar ta janyo wa kanta wata maseefar , ya kai bakinsa ya shanye tasss ya ajiye cup “ruwa fa ? ya d’aga mata hannu alamun baya bukata , hamdala tayi acikin zuciyarta sannan ta tattare plate ta shiga Kitchen ta wanke ta dawo parlou’n ta kwanta akan kujerar dake kusa dashi ta d’aura kafafunta akan cinyarsa idanunta na kan tv ” Allah ka karkato min da hankalin mijina ba dan halina ba ta lumshe ido tana addu’a .”
Wayarsa ta sake ringing ture kafafunta yayi daga jikinsa ya ɗauki wayar ganin number Samir ya sashi murmushi kaɗan sannan ya manna wayar a kunneshi yana sarrafa yatsunsa akan system “ya’akayi samir ? “akan zuwa hollond din nan d’azu mu fara magana dady ya bukaci ganina ga ayyuka sun sakani gaba yanzu waye zai je acikinmu ?aliyu yayi murmushi yace “kai mana ya karasa maganar cikin tsokana bushewa Samir yayi da dariya yace “dole kace ni mana tunda yanzu ka samu mai dibe maka kewa, murmushi ya sake yi yace “of course saboda shine mana , kaga Samir ma yi waya gobe wallahi kaina ke wani irin azababben ciwo yanzu ma kwanciya zanyi , bai jira abinda Samir zai ce ba ya kashe wayar yana shafa qirjinshi .
kallonsa tayi cikin shagwa’ba tace “dan Allah ka kira min mummy naji muryarta a fusace ya kalleta yana watsa mata harara ,ta sake magana yayi mata banza dan ba son dogon magana , ya mike ya kulle ko’ina ya haye sama, mikewa tayi ta canza wutan parlou’n zuwa mara haske ta kullo kofar Kitchen ta hau sama yana kwance akan gado ta shigo zata kwanta kusa dashi ya dakatar daita “koma kasa yayi maganar atakaice yana cilla mata bargo da pillow daya “mu kwanta tare mana ka kalli wancan bangare ni kuma na kalli wannan bangare “bana bukatar haka ya fada atakaice batare daya kalleta ba .”
Babu yadda ta iya ta taja jikinta ta bar gurin direct kasan tayis ta karasa inda bargo yake yashshe a kasa ta shimfida tasa pillow ,bata kwanta ba ta shiga bayi ta d’auro alwala ta fito ta shimfida abun sallah ta sanya hijab ta kalli gabas ta tayar da sallah, bayan ta idar ta dade zaune tana kuka tana addu’a neman sausauci daga mijinta , duk abinda take son Aliyu ya zamanto gareta sai data roki Allah cikin kuka da kaskantar da kai , sannan ta shafa ta mike ta nad’e abun sallah ta maidashi inda yake ta nufi gurin shimfidanta ta kwanta tare da lullu’be rabin jikinta , lumshe ido tayi “zan iya bacci a kasa kuwa ? tunda take a rayuwarta bata taɓa bacci a kasa ba dan ko tayi kokarin tayi bata iyawa , ta rigada tayiwa katifa mugun sabo juyi kawai take yayinda shi tuni bacci ya d’aukeshi sakamakon maganin ciwon kan daya sha …”
A hankali ta mike tsaye ganin bacci ya dauke shi ta dauki pillow da bargon ,ta lullu’ba ta soma tafiya sad’af sad’af ta ajiye pillow akan katifa ta kwanta a kusa dashi ,
Kallon fuskarsa tayi tare da lumshe ido zuciyarta na wani irin dokawa ,ta Kai hannunta daidai saitin zuciyarta “wayo zuciyata na bugawa fiyye da kaida duk saboda shi ,ta sake waigowa inda yake kwance shi kuwa yayi balance yana sharar baccinsa hankali kwance.
a hanali ta Kai hannu zata Jan yo bargo ta lullu’be jikinta lokaci daya tana kokarin gyara kwanciyarta batare da tayi kwakwaran motsi ba tana KoKarin fuskantarsa ya juyo bangaren da take da niyyar gyara kwanciyarsa tayi saurin kame jiknta guri daya tare da juyar da fuskarta tana kallon wani bangare ,ganin bai farka ba bacci yake yasa ta juyo ta zuba masa ido tana kallonsa fuskarta kunshe da murmushi , ta rungume hannuwanta a qirji tana cigaba da kallonsa tana murmshi , ta cire hannuta a qirji tana gyara kwanciyarta “wannan shine kaidan baccin ma’aurata su kwanta suna fuskantar juna sannan wani shashi na jikinsu na haɗe tana wannan yanayin na shaukinsa onexpectig taji saukan hannunsa daya a kan ruwan cikita da sauri ta zaro idanuwa a firgce numfashinta na kokarin daukewa daga gangar jikinta , sake zaro ido waje tayi sosai jikinta na daukar rawa, dayan hannuta ta d’aura saman hannunsa ta daga tana kallo bagaren da yake har lokacin bacci yake sosai, tana kokarin maida hannunsa jikinsa hannun ya subuce ta kalli hannuta tare da dafe kanta tana jin kamar tayi kuka ,hanunta ta dunkule guri daya saboda rawar da jikinta yake, bata gama fita cikin wannan tashin hankalin ba ya d’aura kafarsa daya ajikjinta yai crosing leg’s d’insa still hannunsa na kan ruwan cikinta gabadaya ya rungumeta ajikinsa “wayyo no no this is to much for me dan Allah karka min haka me ma ya kawoni gashi Zan saka kaina cikin tashin hankali ?” Ban shiryawa kaina wannan tashin hankalin ba , yanzu yana farkawa shikenan na shiga uku ba zai d’aga min kafa ba cewa zai yi Ina sane ya Allah ka taimakeni, da nayi kwanciyata a kasa hannuta ta sake kaiwa kan na shi taji gabadaya ya zubo jikinta fuskokinsu na kallon juna yana fidda numfashi a hankali .”Inna lillahi ta furta a kasan ranta jikinta na sake daukar rawa batayi auni ba ya matso da fuskarsa sosai lips d’insa akan nata tana zuko numfashin yadda ya kamata ,shima yana zukan nata numfashin …..”
Domin bukatar karanta novel dina kyauta a sauke manhajar Aysha a bagudo ta hanyar shiga wannan link din dake kasa* 👇🏻
https://play.google.com/store/apps/details?id=aysha.a.bagudo.all.books.pro
Mmn Sudais
💗💗💗💗💗💗
CUTAR DAKAI
💖💖💖💖
💗💗💗💗💗💗