Search
You have no alerts.
    Cover of Ajiya A Duhu

    Ajiya A Duhu

    by Nadmin

    ……..Sosai ciwon kai yay ma Maanal rijib a wannan yinin isowarsu Abuja, shima kuma AA ɗin zuwa yamma dole aka saka masa drip ma, dan sam baya jin wani ƙarfin jikinsa. Har cikin dare ba’a gama saka masa ruwan ba dan kusan leda uku ne. Dole Fawzan ya kwana tare da shi bisa umarnin Abah. Oum taso yin magana amma tai shiru, dan ita so tai ta kawo Maanal a daren sashen AA ɗin, amma ta fahimci take-taken Abah so yake ya kawo wani sharaɗin hora AA ɗin, dan dama shine ya bata umarnin wucewa da Maanal sashenta sanda suka iso.

          Bayan sun baro sashen AA bin bayan Abah tai nasa sashen ta masa magana, amma sai ya nuna mata shi barci yake ji ta barsa dan ALLAH. Haushi ne sosai ya kamata, dan haka fuuu ta baro sashen. Da kallo ya bita ganin yanda ta wuce, sai kuma ya shiga girgiza kansa a fili ya furta, “Fateema son yaranki yayi miki yawa, in dai fushi ne ƙyama sakko dan sai na hora Ajwaad a gidan nan”. Daga haka ya shige toilet yana murmushi…

    ___________★

         Zuciyar Babban Yaya cike da wasi-wasi ya nufi sashen Oum ganin har goma saura na dare yau ma Maanal bata koma sashenta ba, ga AA ɗin kuma ma jikin nasa ya dawo dan yanzu haka wani ƙarin ruwa aka cire masa. Ganin bata a falo ya nufi bedroom ɗinta. Sai da yay sallama ta amsa tare da bashi izinin shiga sannan ya shigan. Yanayin yanda take a zaune da fiskarta dake cike da damuwa yasa gabansa faɗuwa, duk da yasan akwai damuwar yanayin da Auta ke ciki dai.

           “Oum baƙya jin daɗi ne?”.

       Ya faɗa cike da damuwa matuƙa yana kaiwa kusa da ita zaune. Idanu ta zuba masa kawai, dan duk yanda taso yin murmushi ko sassauta damuwar tata hakan ya gagara sam. Sai ma ƙwalla kaɗan da suka taru mata a idon. Ai sai babban Yaya ya sake rikicewa matuƙa.

       Hannunsa ta riƙo tana girgiza masa kai, “Kaga kwantar da hankalinka bafa wani abu bane ba.”

            “Haba Oum yazan yarda da hakan, kalla fa yanda damuwa ta bayyana a fuskarki sosai. Dan ALLAH in ma dan ciwon Auta ne ki daina tada hankalinki komai zai wuce kamar ba’ayi ba in sha ALLAHU. Dan yanzu hakama barci yake yi na cire masa drip ɗin dan ya ƙare. Jikinsa sam kuma babu zafi da ganin yanda yake barci ma kasan Alhamdullah babu wani damuwa ba kamar jiya da yinin yau ba. Yanzu haka ma nazo ne akan batun Maanal, nazata zata kwana a can ne yau ai tunda jikin da sauƙin itama?”.

              Sosai ɓacin ran Oum ya ƙara bayyana akan fuskarta, ta ce, “Akan hakanne ai Abanku ya ɓata min rai Fadeel, yace wai bazata koma can ba yanzu sai bayan salla ya koyama Ajwaad hankali. Wane hankali kuma ake buƙatar koyama yaron nan bayan wanda ya koya. Kama ajiye batun wahalar ciwo da yasha a shekarun baya, a kwanakin nan kawai kaga hanlin daya shiga fa da wanda yake a ciki yanzu. Kowa fa a rayuwa da irin yanayinsa da kuma ƙaddararsa, amma Abanku ya kasa fahimtar hakan, ya kasa fahimtar Ajwaad nada zurfin ciki ne. Yanda Maanal keda muhimmanci a garesa bana tunanin dole sai ya buɗe baki yace wani abu za’a yarda dashi. Shin so yake na rasa yarona ne saboda wannan tsaurin nasa?”. Ta ƙare maganar muryarta na rawa kamar zata saki kuka.

          Cikin sake rikicewa sosai Babban Yaya ya shiga girgiza mata kai nasa idanun na kaɗawa sosai shima. “Dan ALLAH Oum ki kwantar da hankalinki, ni bara naje na samesa yanzu. Ko kuma ki kira Baba ko Abba ki haɗashi da su…..”

    1. No chapters published yet.
    1. Zafin Kai Chapter 2: 2 Samirah ta rasu ne bayan da azabar tayi masu yawa ta girmi tinani da dauriyarsu harma da duk jarumtar da suke tinanin sunada ita, Cikin tsakiyar dare guraren…
    2. Zafin Kai Chapter 1: BismillahirRahmanirRaheem Allah yabamu ikon gamawa lafiya 1 Gyara tsayuwarta tayi ahankali tana sauke idanuwanta daga kallon dattijuwa kuma tsohuwar matar dake…
    3. Nihaad Chapter 3: ~ 3 8months earlier… Zaune yake saman farar kujera dake kusa da dakin mai gadi, ya fi awa daya xaune wajen, lkci lkci yake goge zufan fuskarsa da…
    4. Nihaad Chapter 2: ~~ 2 Dumbin gaisuwa da fatan alkhairi xuwa ga iyayen gidan Khaleesat’s Palace, my die hard fans🥰😍 Su Hajjaju Chamo me gwala-gwalai duk da jarin ya…
    5. Nihaad Chapter 1: ~ 1 All thanks to Allah SWT for giving me the ability and privilege to present to you this book. My mother Hajiya Hajarah Allah ya karo farin ciki da kwanciyar…
    6. (Download) NiDa Ya Ahmad – Complete by AsmaLuv: ABUJA A hankali manya manya motoci ke tafiya saman titi jiniya ce ta kardaye saman layin da xai sadaki da gwarinfa acikin garin abuja daga ganin motocin xaka…
    Note
    error: Content is protected !!